[14/12, 12:54 pm] π™½πš˜πš˜πš›π™Έπš–πšŠπš—βœ¨: πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡ HOORAIN MAI KUSUMBI (The hunch back girl) πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡ _NoorEemaan_ _*hoorain zai zo da wani salo na daban wanda baku taba gani ba, novel din na daban, ya sha bambam da duk wani Novel nawa, ban ce alkamina yafi na kowa ba, amma alkalamina na daban ne, just follow my pen, and i assure you that you Will never regret*_ In the name of Allah, most gracious, most merciful. Chapter 1️⃣⏩2️⃣ *BUKAVU BARRACKS KANO* Babban barikin sojoji ne mai matukar girma, yana Ι—auke da waje je daban-daban, yayinda kabilu mabambamta hadi da addinin ne a cikin barikin, sosai suke zaman lafiya ga hadin kai gwanin sha'awa. Ko wani soja da iyalan sa da area da suke zama, ya danganta da ranka(muΖ™amin) Mutum. Misali akwai officers mess, batcher, White House, da sauran su, haka ma akwai asibiti da suke kira MRS duk a cikin barikin. Zaune yake a officer dinsa, in da aka kawata office din da kayan k'awa irin na sojas... fuskar sa a murtuke yake amma hakan bai hana kyawun sa buya ba. Kyakkyawan matashi ne mai shekaru talatin da biyu a duniya, sanye yake da kakin soldier da yayi matuΖ™ar yi wa farar fatar sa kyau, duk da a zaune yake amma hakan bai hana mutum ya gane cewa shi din dogo ne ba, mai fadaddar kirjin, a takaice dai giant wanda ya sha training sosai. Gashin kansa mai tsayi ne, har parking yake, domin yazo masa har saman kafadun sa, sai dai bai barin shi a baje, always Yana parking gashin. Sajen sa mara yawa kwantacce ne daya kara masa wani sirrin kyau, zagayayyen fuska ne dashi mai dauke da cikakken gira hadi da eyelashes masu yalwa, hacin sa dogo ne mai tsari, idanun sa madaidaita ne masu Ι—auke da eyeball sky blue, sai bakin sa madaidaici red color, a takaice dai he's damn handsome! System ce a gaban sa yake operating da hannu biyu at the same time cike da kwarewa, yayinda lokaci zuwa lokaci yana Ι—an sipping coffee dake kan table din shi, sam bai damu da abinci ba, mafi yawan lokuta yafi gane wa coffe. Alamun sako ya gani an Turo ta Gmail din shi, hakan yasa bayan ya gama abinda yake ya shiga. sunan field marshal ya gani, wanda hakan ya nuna cewa shine ya Turo masa sakon, a nutse ya karanta komai in less than five minutes duk da yawan rubutun... Hannu ya sa ya shafa kwantaciyyar sumar sa, sanan ya furzar da iska daga bakin sa hadi da lumshe rikitattun idanun sa. Amsa ya rubutawa marshal da cewa ya gan sakon, sannan ya kashe system din gaba daya mikewa yayi tsaye... Masha Allah dogo ne sosai wanda ya dace da tsarin halittar jikinsa, hular sa ta sojas ya saka wanda ya Ζ™ara masa kyau sannan ya saka wani brown sunscreen (gilashi) ya dauki wayar sa ya nufi hanyar barin officer Ι—in cikin tafiyar sa mai cike da izza, takama, hadi da burgewa... Jefi-jefi yana haduwa da sojas daya girma a rank suna gaishe shi cike da girmamawa, hannu kawai yake daga musu ba kuma Ι—an wulakanci ba, sun san halin shi na rashin son magana shiyasa basa damuwa. Haraban office din na da matukar kyau an kawata shi da flowers masu ban sha'awa green sai kamshi furanni suke ga Nigerian flag da wasu tambari na sojas da aka kawata Haraban da shi... Wajen hadaddiyar motar sa kirari Bugatti ya nufa, ya buΙ—e murfin ya fada ciki, har ya ta da motar ya ji an K'wank'waso glass din motar. Zuge Glass din motar Ζ™asa yayi, kasancewar ya rufe kuma tinted ne... a hankali, ta tsakankanin lips din shi ya furta "Imran" ta yanda babu wanda ya ji, shi ma Imran lips din shi ya karanta da bazai ji ba. murmushi yayi, domin tun yana mamakin abokin shi ya gane cewa haka halin sa yake sam baya son magana, domin da fari ya dauka wulakanci da girman kai ne, sai da ya zauna dashi har suka kulla abota sannan ya gane cewa halin shi mai kyau ne. "Yes Captain, ina zaka je ne haka?" Saurayin nan da aka kira da Captain yace "Ammi.... I wanna see her" ya fada yana jan sunan Ammin. "Uhmmmm mummy's boy" Imran ya fada cike da tsokanar. Murmushin da iyakar sa lips kaΙ—ai yayi. "Sai ka dawo toh, ka gaishe min da ita please" Imran ya fada. Jingina kai Captain yayi yana rufe Glass din motar, kana a 360 ya bar haraban office din. *Nassarawa GRA Sultan road* Had'add'en unguwa ne mai dauke da had'add'un gida irin na masu hannu da shuni, ko ina shiru kowa na cikin gidan sa. A gaban wani babban gate mai ruwan goro ya danna horn, mintuna biyu kacal aka wangale masa gate din... a guje kamar yadda ya saba tuki haka ya yi parking motar a parking space dake gidan sannan ya bude kofar motar ya fito. Part hudu ne a gidan, wanda daya na Ammi ne, daya nasa duk da baya zama a gidan, daya na yan'uwan shi, daya kuma babu kowa wanda hasali na mai gidan ne da Allah yayi masa rasuwa. Part dake tsakiya wanda ya kasance na Ammi ya nufa, gaban hadaddiyar kofar ya tsaya, inda da kansa kofar ta bude ya shiga bakin sa dauke da sallama, da bana tunanin akwai wanda zai ji shi, saboda yadda ya furta sallamar kamar wanda aka yi wa dole. Macece mai shekaru 50 a duniya, Zaune take cikin shigar less buba Mai kyau da tsada irin na mayan mata, ta sanya medicated Glass, kyakkyawa ce sosai domin kamanin su daya da Captain, kamilalliyar fuskar ta dauke da murmushi mai kyau ganin yaron ta da take matukar so. "Welcome home My Captain" ta fada tana ware masa hannu. Cikin tafiyar sa ta lafiyayyen namiji ya karasa gaban ta ya rungume ta, yana fadin "i miss You first love" hadi da zame kanshi ya kwantar kan cinyar ta. Murmushi Ammi tayi, ta cire hular kansa, shafa kansa tayi, kullum sai yazo ya ganta amma hakan baya hana shi cewa he miss her. "Miss you too my jarumin jarumai" ta kira shi da sunan da takan kira shi a wasu lokuta. Dakin ya dauki shiru kamar ba mutane a ciki, hannun Ammi daya sha jan kunshi ya kama yana kallo, murmushin da bai fito ba Ammi tayi, domin ta fuskanci yayi masa kyau ne amma fada ne ba zai yi ba, girgiza kai tayi, kaf yaranta halin shi ya sha bambam da sauran, komai nasa na daban ne, tun yana karami ta lura yana son kunshi musamman ja. burinta Allah ya bashi mace ta gari, ita kuma tayi alkawarin sai ta sa wa matar ra'ayin kunshi ko da bata da ra'ayin hakan. Amma abin da kamar wuya domin ko budurwa bai da shi, baya kula kowa, ga kannen shi suna da budurwa amma shi kam sam ba ya son maganar ko wacce mace, duk da kawo kan su da suke gareshi. Tun Ammi na yi masa magana har ta gaji, domin har cikin dangi ta zabar masa ya nuna baya ra'ayi, haka ta cigaba da yi masa addu'a da fatan Allah ya bashi mace ta gari. Can ta dago kan shi tace "ka ci abinci?" Yamutsa fuska yayi, cikin yanayi mai kama da shagwaba daya saba yi wa Ammi yace "Am full Ammi..." "Ba wani You re full, kullum haka kake cewa, banason wanna rashin cin abincin naka fa, Ni har mamaki nake duk da baka cin abinci amma ko rama baka yi, oya tashi mu je lemme give you something to eat" ta karasa tana rike hannun shi suka nufi dinining table. Zaunar da shi tayi kamar karamin yaro Sannan ta shiga serving din shi hadaddiyar fried rice Daya Sha namomi da coslow a gefe, da kanta ta shiga bashi a baki, a hankali ya dinga bude bakin sa yana karba ba dan kuma Ι—an yana jin yunwa ba, sai dan farincikin Ammi, a rayuwar baya kaunar Ι“acin ranta. Samari uku ne suka shigo cikin falon suna surutai da alama musu suke a tsakanin su, sai dai ganin Captain a zaune Ammi na bashi abinci sai duk suka nutsu kowa ya tsuke bakin shi domin sun san baya son hayaniya, domin yanzu ne zai yi kasa-kasa dasu. "Ya Hamdan sannu da zuwa" duk suka hada baki wurin fadin hakan. Kai ya jinjina musu ba tare da ya ce komai ba, cikin kasa da murya daya daga cikin su mai suna Anas yace "kabeer, Omar, ku kalli yadda Ammi ke bawa ya Hamdan abinci kamar jariri" Dariya ya bawa su Abbas amma babu halin sakin ta, haka suka kunshe abin su, sannan suka sanar da Ammi zasu fita dubiyan abokin su da bai da lafiya, adawo lafiya Ammi ta musu sannan tace su yi masa sannu... Ganin Ammi bata da niyyar daina bashi abincin sai ya kama hannun ta ya na yamutsa fuska, yace "Please Ammi"sarai ta fahimce shi, sai ta ajiye cokalin ta zuba masa ruwan gora a Glass cup ta bashi, ya Ι—an sha sannan ya ajiye, kan kujerar falon suka dawo... "Ammmmiiiiiii...." ya kira sunan ta da husky voice din shi. "Na'am" Ammi ta amsa tana kallon shi hadi da bashi hankalin ta, numfashi ya furzar ya ma rasa ta yanda zai yi mata wanna bayanin mai tsaho da marshal ya turo masa, domin shine abin da zai bashi wahala. Wayar sa kirar iPhone 12promax ya mikawa Ammi bayan ya shiga ta Gmail din. Karban wayar Ammi tayi kana a nutse ta shiga karanta inda karatun ya dauke ta tsahon mintuna bakwai kafin ta gama. Gwauron numfashi ta saki a lokacin data gama karantawa, hannun Hamdan ta kama cikin nata, tace "na karanta, kai ne zaka jagoranci wasu sojas zuwa kwantar da tarzoma, sam bana kaunar ka zuwa duk wani abu da ya shafi yaki, duk da nan cikin Nigeria ne, zuciya ta cike take da tsoro, amma bani da zabi daga wuce ka je din..." Kara rike hannunsa da kyau tayi tace "ya Allah! Ka tsare dana daga mugun gani, ka raba tsakanin shi da mugaye azzalumai, ya Allah ka dawo min da shi lafiya, ka basu nasara kan wanna aikin da zasu je yi, ya Allah ka tsare shi da sauran sojoji" ta karasa kwalla na cika idanun ta, amma bata bari ya gani ba, domin ta san cewa matukar ya ga kukan ta, zai ce ya fasa zuwa, ba kuma ta so ta ruguza mafarkin shi, domin tun yana dan karamin yaro yake kaunar zama soja da kuma yi wa Ζ™asar sa hidima. Rungume ta Hamdan yayi, har abada yana alfahari da Ammin shi "Ameen ya rabb! thanks Ammi, i love You so much" "I love you too my captain" ta faΙ—a tana shafa bayan sa. Haka ya cigaba da zama da Ammin har yamma ta yi sosai, ya kuma ji dadi kasancewar su tare, Domin itace mutum mafi soyuwa a duniyar sa, bai san so ba sai a kanta, hakan yasa wasu lokutan yake kiranta da First love. Sai bayan magriba ya yi mata sallama cike da kewar ta ya tafi, a hanya Isha tayi masa, sai kawai yayi sallar sa a masallacin gadon k'aya sannan ya cigaba da tafiya har ya shigo cikin barracks... bangaren da gidan sa ya ke ya nufa ya faka motar sa, sannan ya shiga cikin gidan, wayar hannun sa kawai ya ajiye ya cire duka kakin jikin sa ya jefa cikin laundary basket, towel ya daura a jikin sa sannan ya shiga had'add'en toilet din sa. Shower ya sakar wa, kansa, yana dafe da bango inda ruwan ya shiga dukan sa, ya dauki mintuna goma sannan ya fito, short nicker mai zanen soldier ya saka, sannan ya fada kan gado, lumshe ido yayi, iska mai dadi dake kadawa yana shigowa ta window'n sa, hannunsa kan six packs dinsa Yana shafawa, ya dauki mintuna biyar a haka sannan yaji wayar sa na ringing, bude lumsassun idanunsa yayi da suka yi nauyi saboda gajiya da yake tattare da ita kana ya mika hannu ya dauki wayar.... 07082281566 NoorEemaan loves you all habibte'sπŸ’ž Tue, 17 2022. 7:38am [14/12, 12:54 pm] π™½πš˜πš˜πš›π™Έπš–πšŠπš—βœ¨: πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡ HOORAIN MAI KUSUMBI (The hunch back girl) πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡ # _NoorEemaan_ The writer of Rayuwar faheemah Mijin Ammina ne sila Papi ne Kyautar koda Abraham And nowπŸ‘‡ HOORAIN MAI KUSUMBI (The hunch back girl) Chapter5️⃣⏩6️⃣ D'ago fararren idanun ta masu d'auke da brown eye ball tayi, kana ta kalli wacce ta kira ta. murmushin da za a kira shi na yake matar ta sakar wa hoorain, martani hoorain ta mayar mata har jerarrun hak'oranta suka bayyana, a hankali matar nan da a kalla zata yi shekaru talatin da tara ta karaso ta zauna a gefen ta, cikin kauna mai tsanani da take wa yarta tace "Hoorain ga abinci a daki, na dauko miki?" "A'a Mami.... na koshi" hoorain ta fada cikin sanyin muryar ta mai dad'in amon. "Me kika ci da zaki ce kin koshi, ko bakya son wanna abinci wani kike so?" Mami ta tambaye ta with so much care. Murmushi hoorain ta sakar wa Mami tana kokarin mayar da kwallar ta, abinda zasu kai baki wahala yake musu, amma domin farincikin ta Mami ke tambayar ta idan wani abu take so, hak`ik`a idan taci abincin nan bata kasance y'a mai jikin kai hadi da tausayin mahaifiyar ta ba. "Allah Mami cikina a cushe yake, bana jin yunwa, yanzu ma da daga band'aki nake" ta karasa tana sakar wa Mami murmushi domin kwantar mata da hankali. Jinjina kai mami tayi, kana ta mike ta shige daki... Yamutsa fuska Hoorain tayi sak'amak'on wani murdawa da cikin ta yayi kamar y'a'yan hanjin ta zasu fito saboda yanda cikin ta yake wayam babu abinci, amma bazata iya ci ba, domin ta tabbatar Mami ta fita jin yunwa, domin a daren jiya dan guntun abinci daya rage musu ita ta cinye, Mami ta ce ta koshi saboda ita ta samu ta ci, cikin dare tana kallon Mami ba tare da sanin ta ba tana murkususu hadi da yin ruf da ciki, a jiya tayi kuka sosai mara sauti domin bata so mahaifiyar ta taji... ⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐ *HAMDAN* Da misalin k'arfe uku da mintuna arba'in suka isa kogi kauyen Oguma. Sai dai ba cikin kauyen can ciki ba. Tunda daga wajen kauyen Hamdan ya fahimci cewa tabbas kauyen nan ba lafiya, haka dai suka nufi inda aka tanadar musu, already an riga anyi musu abinci, nan mutanen da aka bawa contract din abincin suka shiga gabatar musu dashi. Kallo daya hamadan yayi wa abincin ya dauke kansa, sam baya jin zai iya cin wanna abincin da ya tabbatar hannu da yawa ne ya dafa ta, sannan bai san yaya tsaftar mutanen yake ba. Nannade hannu rigar shi yayi, sannan ya fara ciri bakin safa da Boot din kafar sa, inda take farar lafiyayyen kafar sa ta bayyana tamkar bai taba taka Ζ™asa ba. Dan jan wandon sa yayi sama kad'an, ya cire agogon hannun sa ya d'aura kan wani babban dutsen dake gefen wajen, cike da nutsuwa ya shiga yin alwala, bayan ya gama ya mayar da safar sa da takalmi, zai dauki agogon sa dake kan dutse karaf ya kama Godiya tana kallon sa, macen soja ce yar garin Jos, kara daure fuskar nan yayi tamau fiye da baya, sannan ya bude motar su ya dauki sallaya kana ya fuskanci gabas ya fara sallah cike da nutsuwa, sallar daya dauke shi mintuna goma kafin ya iddar, addu'a sosai yayi, kan Allah ya basu nasara a wannan aikin da suka zo yi, wayar sa ya ciro daga aljihun wandon sa, ya danna number'n Ammi.... Bayan ta daga yace "first love ina wuni, nayi kewar ki" Murmushi tayi kana tace "Lafiya Lou Captain, ya hanya? Ina ta son kiran ka amma ban samu zama ba, iyalan baba Dalhat ne suka kawo min ziyara" Lumshe rikitattun sky blue eyes din sa yayi kana yace "Mun isa kauyen Ammi" Ajiyar zuciya ya ji Ammi ta saki, ta shiga fadin alhamdulillah, daga nan suka Ι—an yi hira, yana jin Muryar Ayiyah da su Omar suka hira, kafin su yi sallama Ammi ta jadadda masa lallai ya ci abinci k'ar ya zauna da yunwa, ya dai amsa mata, amma bazai iya cin wanna abincin ba, rather he prefer ya sha coffeen sa. Bayan sallar Isha ne, duk sojas din sun kasance cikin shiri, dama yan ta'addan nan cikin dare suke kawo farmaki kauyen, cike da k'warewa Hamdan yake basu umarni da nuna musu direction din da kowa zai bi cikin kauyen ba tare da yan ta'addan sun sani ba, sannan wasu sojas din ya basu umarnin zaga gidajen kauyen domin tabbatar da tsoro... haka dai ya rarraba su ta yanda za a samu komai ya tafi yanda suka tsara... *10:00pm* Duk da tsoron dake lullub'e a zukatan jama'ar kauyen Oguma, amma hakan bai hana wasu kwantar da hak`ark`arin su domin bacci ba musamman yara marasa wayo cikinsu, Manyan kuma na zaune cikin zullumi da tsoro mai tsanani. Karan bindigan da kauyen suka ji yayi sanadiyar karin tashin hankalin su, hakan kuma ya sanar musu cewa azzaluman sun shigo... Masu tsananin tsoro har fitsari suka saki saboda tashin hankali, wasu kuwa cikin su ne ya shiga murd'awa suna shiga ba haya, domin rage ciki, wanda tashin hankali ya haifar musu da shi, masu buyo har a k'ark'ashin gado na yi, wasu na neman hanyar guguwa, wasu kuma sun fito waje, gaba-daya kukan su ya cika kauyen, ga yan ta'addan da suka fara cinna wuta a wasu gidajen... Ta bangaren Hoorain da mami kuwa suna cikin gidan su basu fito ba, bama zasu iya gudu ba saboda lalurar hoorain bazai bari su tsira da ran su ba tare da an kama su ba, sai dai wani ikon Allah. Mami baiwar Allah na zaune kan kod'ad'iyyar sallayar su tana rokon Allah ya kawo musu dauki, hoorain dake gefe hawaye na zuba daga idanun ta ma addu'a sosai take a ranta tana fatan Allah ya kawo musu karshen wannan kashe-kashe rayukan da ake a duniya, tana mamaki mutane marasa imani da zasu iya kashe rai da bai yi maka komai ba saboda son duniya, me suka tanada da zasu kare kan su da shi idan Allah ya tambaye su ranar gobe kiyama? Daga Ι“angaren yan ta'addan nan kuwa, harbi kawai suka fara ji from no where, wanna hakan ya tabbatar musu da cewa sojoji ne, maimakon su yarda makaman yakin su sai ma kara sakin harbin da suke, nan fa zugan soldiers dinnan suka bayyana kansu kana suka cigaba da sakar musu ruwan alburushi... suma yan ta'addan na sakar musu, yan kauyen Oguma suke dawo yan kallo, tsoron daya lullube zukatan su na raguwa, wasu sojas dake tsaye a kofar ko wani gida suka umarci wadanda suka fito waje kan su koma cikin gida gudun kada harbi ya same su, ai kuwa da gudu duk suka shiga har da saka sakata, dama tsananin tsoro, rudu, da rashin sanin abin yi ne ya fito da su. Nan fada ya dawo tsakanin SOLDIERS da yan TA'ADDA, sai musayar wuta harbi suke cike da kwarewa... yan ta'addan nan kamar kara tunkudo su ake, ana kashe su suna kara fitowa, abu fa yaki karewa har karfen dayan dare, inda a lokacin shugaban su da wasu zugan suka kara cika kauyen, suna cigaba da harbi. Al'amarin fa ya girmama tunanin sojas dinnan, domin basu dauka haka abin yayi muni ba. Godiya soja da itama take cikin masu harbin ta koma gefe ta yanda ba za a ganta ba, wayarta ta fito dashi, number'n Hamdan ta yi dialing wanda Allah kadai ya san ina ta samu... ******* Safa da marwa yake, cikin farfajiyar gidan da suke, ya kira number'n wasu sojas din da yake da shi, amma basa dagawa, ya tabbata har yanzu basu kamalla bane, gashi manyan sa sun bashi umarnin cewa kada ya shiga yakin, na shi bada umarni ne da jagorantan su kawai. Amma ya fada a ransa cewa dole idan fadan ya Ι“aci zai shiga cikin su... yana cikin wannan tunanin yaji wayar sa na ringing, bakuwar number'n ya gani, latsa kore yayi ya Ζ™ara a kunne sa ba tare da yace komai ba Cikin muryar ta mai amon sauti da jarumta kamar ba mace ba tace "sir! Godiya ce, yan ta'addan nan kara yawa suke, domin har sun kashe mana mutane biyar...." Bai jira ta gama maganar ba ya kashe wayar ya jefa a aljihun wandon kakin sa, cikin zafin nama ya dauki bindigogi bayan ya cika musu bullet, tsakanin cikin kauyen Oguma da gidan da aka tanadar musu tafiyar mintuna talatin ne, ba kuma yaso yayi amfani da abin hawa, saboda hakan zai sanar wa yan ta'addan zuwan sa, so yake yayi musu dirar ba zata, da direction da aka basu ya dinga bi, cikin sauri-sauri gudu-gudu cike da taka tsantsan domin isa wajen...✍️ NoorEemaan 07082281566 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JxzoG62bUENBfExeNPbRSu [14/12, 12:54 pm] π™½πš˜πš˜πš›π™Έπš–πšŠπš—βœ¨: πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡ HOORAIN MAI KUSUMBI (The hunch back girl) πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡ _NoorEemaan_ Chapter 3️⃣⏩4️⃣ "FIELD MARSHAL" Shine sunan daya gani a rubuce baro-baro kan screen din wayar sa. Latsa kore yayi hadi da kara wayar a kunne sa, cikin girmamawa wa marshal yace "Good evening sir!" "Evening captain, hope you are good?" Hamdan yace "very well sir" "That's nice, am... kan maganar da zaka jagoranci wasu sojas zuwa yaki ya tashi daga sati mai zuwa, domin mun samu labarin yan ta'addan nan sun sake kai farmaki wa kauyen, suna cikin wani hali matuΖ™a, dan haka jibi ne tafiyar ku in Sha Allah, domin gobe za a kamalla muku komai na tafiyar, all the Best captain Hamdan" "Thank you sir" ya amsa yana taune jajayen labban'sa masu daukar hankali. Ya jima yana tunane-tunane kana bacci ya dauke sa, kasancewar a matukar gajiye yake. ⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐ *WASHEGARI* Misalin karfe goman safiya ce, zaune yake cikin motar sa yana sharara gudu kan lafiyayyen kwaltan, sanye yake da three quater wando na soja, sai singlet shi ma na sojas daya bayyana karfafan kafadun sa masu fadi, babu hula a kan shi yayi parking gashin sa as usually, kafar sa sanye da sandal fari mai igiyoyi, hannunsa dake murza sitiyarin cike da kwarewa sanye yake da tsad'add'en agogo, yayi mugun yin kyau... Karatun Alqur'ani ke tashi cikin surutal Al-furqan, a nutse yake bi cikin zuciyar sa, wayar sa dake kan kujerar mai zaman banza ya dauka ya yi danne-danne kana ya kara a kunne sa, bayan seconds hamsin aka daga kiran daya Ι—ayan bangaren. Kasa-kasa kamar mai tsoron kar a ji shi yace "Assalamu alaikum, ina kwana first love, am on my way coming" Abinda yace kenan ya katse kiran, bayan mintuna goma ya shigo unguwar su Nasarawa GRA, horn ya danna aka bude masa ya shiga, a tsakiyar gidan ya yi parking motar kana ya nufi part Ι—in Ammi. A bakin kofar glass ya tsaya, kofar ta buΙ—e ya shiga, runtse ido yayi sak'amak'on ganin Ayiyah a Zaune, a ransa yace "damn it! Meyasa matar nan ta dawo" domin idan akwai abinda yake gudu toh Ayiyah ce, duk da kasancewar ta kakar sa, amma mugun ciwon kai take bashi. Ware rikitattun idanun sa yayi, kamar yadda ya saba ciki-ciki haka yayi sallama, yana k'ara daure fuskar sa tamau, gudun kada Ayiyah ta kawo masa wargi amma bai tsira ba... Cikin muryar ta mai cike da k'arsashi duk da ta tsufa tace "fuska Fara, zuciyar ka baka, idan ka ga dama ka dawo da fuskar ka ta shanu bai dame ni ba, wallahi sai nayi magana, domin ni idan nayi shiru ban yi magana ba bakina wari yake, wanna gantalewa da bakin halin har ina, a cewa kullum mutum fuska a murtuke kamar na kashin asuba " Ammi dake jin su kuwa matse dariyarta tayi, Hamdan kuwa kara bata rai yayi ya nufi wajen Ammi ya zauna kusa da ita, Cikin kaunar mahaifiyar sa ya kalle ta kana yace "Ammi hope you are Fine?" "Am very fine Dan albarka, ya aiki?" "Fine first love" ya amsa yana Ι—ora kansa kan kafadar ta. Wani tabe baki Ayiyah tayi tace " haka fa, sai karyar turanci, yanzu fisabilillahi ko kunya baka ji, katoto da kai ka wani zo ka manne wa uwar ka, ko su Abbas da suke kannen ka basa wanna iyayin, ko da yaΖ™e laifin uwar ka nake gani, domin ita ke shagwaba ba" ta bantali goro tana tauna, jikake karas karas ta kuma baza kunne domin jin yayi magana amma bai kula ta ba, hakan ya dame ta, domin ita kam bata iya shiru ba, ba kuma ta so a yi shiru, "nayi magana kayi shiru kamar baka ji ba, gaskiya dai sai na fada, kuma bari ka ji ka yi ka nemo matar aure domin mun gaji da ganin ka haka, ko kuma na je kauyen su wata kawata na samo maka mata a can...." Daga kansa yayi daga kafad'ar Ammi ya watsa wa Ayiyah, tilas ta tsuke bakin ta, domin tsoron kwayar idanun sa masu launin sky blue (kalan sararin samaniya) take, domin duk masifar da take mishi bata kallon fuskar sa. Daga karshe ma mikewa tayi ta fara tafiya tana kananun surutai, Hadi da kwala wa mai aiki kira kan ta kawo mata abinda tace ta dafa mata. Tana barin wajen Ammi ta saki murmushi mai sauti, sannan ta kalli Hamdan tace "ka dinga hakuri da halin Ayiyah son, ka san rikicin tsufa ke damun ta, kaji ko" Jinjina mata kai yayi alamun toh. Nan ya sanar da ita cewa an dawo da tafiyar su gobe, sosai Ammi tayi masa addu'a tare da fata na gari, duk da jikin ta yayi sanyi. Suna zaune a haka su Abbas suka shigo, cikin girmamawa suka gaishe shi, hannu ya mika musu alamun su yi musabaha ba tare da yace komai ba, dadi ya kama su, Anas shine farkon mika hannun sa saboda farinciki, duk ranar da Hamdan ya shiga harkan su dadi sosai suke ji Kallon su Ammi tayi cikin burgewa, da godewa Allah daya bata zaratan samari masu kyau da nutsuwa, duk da cewa Hamdan baya shiga harkan su, amma yana matuk'ar kaunar kannen sa, halin shi ne haka, baya shiga harkan mutane sam, ga wanda bai gane ba sai ya dauka wulakanci ko girman kai ne dashi, shiyasa a kullum take rokon Allah ya bashi mace da zata Sanja masa wanna halin nasa ko da ba duka ba, but at least ya kasance mai walwala kamar kowa.. "Anas, kabeer, Omar." "Yes Ammi" suka amsa a tare. "Kuyi wa Captain addu'a gobe zai jagoranci wasu sojas zuwa kwantar da tarzoma da yan ta'addan suka tayar a garin Kogi" kasancewar labarin a bayyane yake, domin duk wata kafa ta sadarwa sun fadi halin da wannan yan garin suke ciki. "Addu'a sosai suka yi masa, a kasan makoshi ya amsa da "Ameen" sun karanci hakan ta lips din sa, sai suka kalli juna suka yi murmushi... Anas daya fisu surutu ne yace "Ammi, ina Ayiyah?" "Yanzu ta gama drama da yayan ku, ina tunanin tana dakin ta" Dariya suka yi, kana suka mike, domin tafiya wurin ta, su kam suna kaunar Ayiyah a gidan, ko ba komai zasu ci dariya. Hamdan bai bar gidan ba sai karfe biyar na yamma, bayan ya bawa Ammi makud'an kudade, sannan ya bawa su Anas har ma da Ayiyah, duk da basu rasa komai ba amma hakan baya hana shi ya basu kudi. Domin har yau akwai kamfanunuwan mahaifin su daya bari kafin ya rasu kuma su Anas ke kula da shi. Addu'a Ammi ta kara yi masa, ya rugunme hallita mafi soyuwa a rayuwar sa cikin jin dadi samun ta a matsayin uwa mai kulawa da tsananin son y'ay'an ta. Da haΖ™a suka yi sallama Ammi na daga masa hannu har ya fita kana ta share hawaye tana rokon Allah ya dawo mata da shi cikin koshin lafiya. *BUKAVU BARRACKS* Hilux Masu dauke da zanen sojoji hadi da motocin amoka da yawa suka jeru reras, kimanin soldiers da zasu kai dubu dari biyar ke tsaye ko wanin su ya kame cikin kayan sojoji, sai jaka irin na sojas dake rataye a bayan kowanne su, ga bindigan AK-47 dake rataye a kafadar su, kawai jiran umarni suke domin su fara tafiya. Cikin tafiyar nan tasa ta lafiyayyen namiji mai ji da kuruciya hadi da takama ya nufo inda motocin suke,... Wajen commander dake tsaye ya nufa, ya kame hadi da tsara masa, hannu shi commander ya kama suka dan koma gefe, yayi masa wasu maganganu da basu wuce mintuna uku ba sannan suka dawo inda commander'n ya tsaya dazu, wani Kurt soja ya bude wa hamadan kofa, cikin jarumta ya yi tsalle ya fada cikin motar amoka domin irin mai tsayin nan ce, umarnin tafiya ya bayar, nan motocin suka fara tafiya, a jere... Sauran sojas da babu su a yak'in tsaye suna daga musu hannu hadi da yi musu fatan dawowa lafiya, haka suka ratsa gate suka fice... ⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐ *KOGI STATE* *(Kauyen Oguma)* Kauye ne mai girma hadi da tarin jama'a, ga ni'ima mai sanyi da Allah ya albarkaci kauyen da shi. A yau ya kasance ranar cin kasuwar su ne, amma babu halin hakan, saboda tashin hankali da tsoro da suke ciki, sakamakon yan ta'adda da suka kawo wa kauyen farmaki, wanda hakan ya sa suka rasa kwanciyar hankali, fuskar su a lullube da tsoro kallo daya za ka musu ka fahimci hakan, ko yaran su basa iya zuwan makaranta, dare da rana cikin addu'a suke kan Allah ya kawo musu dauki, domin har sun rasa yan'uwa da abokan arzikin da yawa. Gida ne dan madaidaici mai dakuna biyu ginin jar kasa, irin na kauye, har rubewa ginin ya fara yi, kallo daya mutum zai yi wa gidan ya fahimci cewa ko a talakawan kauyen, wanna gidan nasu talaucin ya munana. Yarinya ce yar shekara goma sha bakwai ta buΙ—e wata kod'add'iyar zanin atamfa daya kasancewa kofa ga banΙ—akin su da ko rufin sama babu ta fito. Abin mamaki da al'ajabi ga wanna budurwa mai kananun shekaru shine Bata tsaya kan kafafun ta ba, ta tsunkuya irin yadda tsofaffi masu tarin shekaru da basa iya tsaye kan kafafun su haka take, sakamakon kusumbi (hunch back) dake bayanta, kusumbin ya kumburo sosai a bayanta tamkar an kifa katon kwarya. Kyakkyawar ce, sannan fara ce, sol irin mai daukar idon nan, duk da cewa suna fama da talauci, amma skin dinta na nan fresh wanda hakan baya rasa nasaba da ni'imar kauyen da suke dashi Butar hannun da ko albarkan murfi babu, ga shi duk ya faffashe ta ajiye a gefe kana ta yi tafiya irin na masu kusumbi ta zauna kan matacciyar tabarman dake shimfide a gefen dakin su. Numfashi ta sauke bayan ta juya lulu eyes dinta masu girma hadi da haske... tagumi tayi, bazata ce rayuwa bata mata adalci ba, sai dai akwai tarin kalubale a rayuwarta da take fatan ya zama nasara ko samuwar farinciki ga rayuwar ta, duk da hali da lalurar da take ciki tana godewa Allah, domin akwai wadanda suke cikin hali daya fi nata muni, sai dai raunin ta na bayyana ne a duk lokacin da ta fita, yammatan kauyen ke sata a gaba da tsokana da kiran ta *HOORAIN MAI KUSUMBI* ga zallan kishi da take hangowa a idanun su wanda bata san ko na menene ba, duk da lalurar ta... Kara juya fararren idanun ta tayi, wanda hakan dabi'a ne a gareta, sannan ta rufe idanun ta ruf, tunanin tashin hankali da suke ciki a wannan k'auyen take, addu'a take a ranta kan Allah ya kawo musu mafita da kwanciyar hankali. "HOORAIN!" Taji an kira sunan ta... Share share share fisabilillah πŸ™ NoorEemaan 07082281566 [14/12, 12:54 pm] π™½πš˜πš˜πš›π™Έπš–πšŠπš—βœ¨: πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡ HOORAIN MAI KUSUMBI (The hunch back girl) πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡ # _NoorEemaan_ *DEAR LOVELY FANS DA MA MAKARANTAN HOORAIN PLEASE KU KARANTA WANNAN BAYANIN NAWA IT'S VERY IMPORTANT* _Zan yi wanna dan tsokacin ne idan ma akwai mai irin wanna tunanin a ransa_. _Kila wasunku zaku ce meyasa Noor ta rubuta cewa HAMDAN yana da gashi, bayan ba a san sojojin da gashi ba_. _Yeah it's possible soldiers su tara gashi, amma mafi yawa na nan Najeriya basa yi_... _Abin da ya saba dokar soja shine askin banza ne ba a so_... _Amma bawai basa tara gashi bane, sai dai mafi yawan su basa tara mai yawa_... _Dan haka Habibte's ina sane da abinda na rubuta, domin ina da experience a akan soldiers, ina da friends da yan'uwa sojas, and also tun Ina pre-nursery har na gama secondary school a barrack din sojoji nayi karatu na, to Cut it short_... _Haka nake son HAMDAN ya kasance a littafin HOORAIN, shiyasa na rubuta cewa yana da suma_. _Abu mafi muhimmanci a novel shine sakon da marubuciya take son isar wa yaje inda ake so_. _A karshe dai makaranta na da suke bibiyata tun daga farkon book dina sun san cewa duka book dina fictional story's ne, ban taba rubuta true live story ba, Dan haka a Novel ba komai ne dake faruwa a gaske za a rubuta ba, dole akwai nishadantarwa domin kawata Labarin_. *Thank you all da yanda kuka karbi littafin HOORAIN MAI KUSUMBI Allah ya bar kauna, son so nake Muku.πŸ’ž Chapter 7️⃣ ⏩ 8️⃣ Tafiyar da ya kamata yayi a Mintuna talatin, a 20 minutes yayi shi. A lokacin daya isa wajen yayi mamakin yadda abu ya Ι“aci haka, ba tare da bata lokaci ba ya shiga cikin sauran soldiers aka cigaba da fafatawa cike da kwarewa wanda hakan ya nuna cewa sun sha training mai zafi... A takaice dai sai karfe hudu saura aka samu komai ya lafa, inda yan ta'addan nan da suke rage takwas har da shugaban su suka yi kokarin guduwa, domin bullet din su ya kare. Cikin sa a hamdan ya samu nasarar sakarwa biyar arbi a kafafun su biyu, sauran ukun ma wasu soldiers din suka karbe su, hakan yasa suka zube a kasa suna ihu azaba... Umarnin Hamdan ya bayar cewa a kamo su duka. Sannan ya ce wa wasu soldiers din su tsaya a kauyen har safiya domin tabbatar da tsoro, cikin girmamawa suka amsa da "yes sir!" Bayan sun isa gidan da suka sauka nan aka kulle yan ta'addan nan a wani daki. *WASHEGARI* Kusan ko wani kafa da sadarwa sun samu labarin abinda ya faruwa, sun kuma bayyana wa jama'a, zuciyar mutane cike da farin ciki nasarar da Allah ya bawa wadanda jaruman sojas din masu kishin kasar su. Field marshal wanda shine mai 5 star rank general, haka kuma shine highest rank a Nigerian army, Ya kira Hamdan ya yaba masa. Ammin ma ta gani a news din karfe shida da ta kalla, ta kira hamdan tayi masa murna sosai da addu'ar Allah ya dawo da su lafiya. Da misalin k'arfe taran safe yan jaridu sun cika k'auyen oguma domin cigaba da daukar rahoto, Sannan an kai yan ta'addan nan babban kotun Abuja kasancewar daga kogi zuwa Abuja babu wani mugun nisan, an saka su a prison zuwa ranar da za a yanke musu hukunci... *BAYAN KWANA ƊAYA*. Ta bangaren yan k'auyen oguma kuwa sosai suka tashi da nishadi a safiyar yau, tsoron da fargaban su ya kau, sun dawo hada-hadar su kamar yadda suka saba cikin walwala. ******** Tafe take cikin tafiyar ta irin na masu kusumbi, hanyar rafin kauyen su ta nufi, duk da yanda mami ta hanata zuwa, amma bazata iya kallon Mami da girman ta na zuwa diban ruwa yayinda ita ke zaune ba. Jefi-jefi tana haduwa da mazan garin suna gaisawa a mutunce. Allah yayi wa Hoorain wani mugun farinjini wanda hakan ke bak'anta ran yawancin yammatan kauyen, ganin su lafiyayyu marasa nakasa mazan basa Kula su kamar yadda suke wa Hoorain magana. *** babba rafi ne wanda yake kashi uku, bangaren daya wasu na wanka, dayan wasu na wanki, dayan kuma na diba ne, a sha a kuma yi girki ba a shiga cikin sa. Ga wani babban maciji mai jan abu a kansa kamar hula yana gefen ruwa ba tare da yayi wa kowa komai ba, haka ma mutane dake rafin basa tsoro, abu ne wanda sun riga sun saba da ganin sa, domin duk wani d'a ko y'a a k'auyen haka ya tashi ya tarar da macijin nan a rafin. Sannan abin mamaki da tsoro, ga wanna macijin shine matuΖ™ar mace na period bata wanka cikin rafin, sannan idan akwai janaba ko da datti a jikin Mutum ya shiga rafin dan wankan toh sai macijin nan ya sare shi. Ga yammatan nan da yawa wasu na wanki, wasu na wanka, wasu na hira a tsakanin su. Ko kallon su Hoorain bata yi ba ta cigaba da tafiyar ta a hankali domin isa wajen diban ruwa, tana jin yammatan nan na mata dariya, ta gefen ido ta ga wata na k'waik'wayon irin tafiyar ta, Murmushi Mai ciwo tayi wanda ya taho da zubar hawaye mai dumi daga idanun ta, hannu tasa ta share fuskar ta. Saka madaidaicin bucket Mai hannu tayi ta diba ruwan ta kana ta fara tafiya domin barin rafin, ta ji sun sakar mata ihu suna karin "Mai kusumbi" cikin shekiyanci hadi da tsokana, hadiye kukan ta tayi har ta Ι—an yi nisa da rafin kana ta ajiye bokitin ta fashe da kuka mai ban tausayi hadi da taba zuciyar mai sauraron ta, har wani shesheka take saki.. Ji tayi an dafa ta a baya, cikin sauri ta juyo, "Aramani!" Ta kira sunan matashin daya dafa ta tana sakar masa Murmushi, a kokarin ta na boye damuwar ta. Wanda aka kira da Aramani ya dauki bokitin data ajiye, cikin tausayawa ya ce "hoorain kada ki min murmushin da bai kai zuciyar ki ba, bayan ga tarin damuwa kwance cikin idanun ki, kiyi hakuri da abubuwan dake faruwa watarana komai zai wuce, ki daina barin maganganun wasu yana damun ki, domin ke din ta daban ce, kin fisu komai, ki manta da lalurar ki, You re a special Creator from God, Dan haka cheers ok?" Hannu ta sa ta kara goge fuskar ta da kyau, bayan Mamin ta, Aramani kadai ne mutum na biyu dake son ta hadi da bata karfin guiwan ta da rasa, take kuma kan rasawa a duk lokacin da aka tozarta ta a kauyen oguma. sanyin ta ji a ranta, atleast ta dan samu karfin guiwa, cikin sanyin Muryarta tace "Nagode omaye mie" Aramani"(omaye mie na nufin dan'uwana da Yaren Igala) Murmushi kawai ya sakar mata, suka fara tafiya yana jan ta da hira hadi da bata labarai masu ban dariya domin ta saki ranta. Murmushi take yi kasancewar aramani na da barkwanci sosai. Tun daga nesa hoorain ta hango Taheer dan mai gari da zugan sa a zaune suna kallon duk wata mace data wuce, kuma matukar yana son mace dolenta ta amince masa, kasancewar baban sa mai kudi gashi kuma a Abuja yayi karatu hakan yasa matan kauyen ke rububin sa, wasu ma da gangan suke hucewa sau goma domin ya kyasta. Gaban Hoorain ya fad'i, tana matukar tsoron Taheer domin sam baya da d'aa bare Magana mai dadi a bakin sa, sannan ta rasa me ta masa, da duk lokacin da ya ganta sai ya jefa mata kallon tsana, bata mantawa ranar da ya ke faΙ—in ya tsane ta, ita din mummuna ce, mai tawayar hallita baya kaunar ganin ta, haka ya disga ta cikin tarin jama'a a ranar tayi kuka kamar ranta zai fita, ta rasa me ta tsare masa, haka suka wuce sam bata bari sun hada ido ba, sai dariyar abokan sa data ji cikin tsokana, alamun yayi wata magana data shafe ta, duk hirar da Aramani yake mata sam bata fahimta a yanzu. Har cikin gida Aramani ya shigar mata da ruwan, suka gaisa da Mami kana yayi musu sallama ya tafi... ⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐ Press up yake cikin sauri-sauri ya had'a uban gumi domin kimanin mintuna talatin ya dauka yana yi, sai daya gaji dan kan sa kana ya mike yana goge fuskar sa zuwa wuyan sa da farin towel dake rataye a wuyan sa, direct toilet ya wuce ya yi wanka, kana ya fito, cikin blue jeans da farar T-shirt ya shirya, gashin sa daya zo masa saman wuya ya cire rubber band daya riΖ™e gashin, kana ya shafa oil ya taje... As usually ya kara parking gashin a kasan keyar sa, facing cap ya sanya, ya fashe turaren sa, palm sandal ya saka a kafar sa sannan ya dauki wayar sa ya fito... Wajen gidan da suka sauka ya tsaye, haka kawai ya ji yana son zuwa kauyen, cikin tafiyar sa ta birgewa ya shiga taka wa yana jin yanda idanun jama'a ke yawo a kan sa, bai damu ba duk da baya son kallo... abinda ya faranta masa rai shine ganin yanda yan kauyen ke ta walwalar su ba kamar ranar da suka zo ba, a ransa ya raye cewa zaman lafiya ya fi komai dadi, haka kuma yana saka al'umma samun cigaba. *HOORAIN* A hankali ta fito daga cikin gidan su tsintsiya dauke a hannun ta, share kofar gidan su ta fara yi... hakan yayi daidai da lokacin da hamdan yazo wucewa, bai san me ya kai idanunsa kan farar kagun ta dake sanye da jigida(waist bead) ba, wanda ita Hoorain bata san cewa rigarta ta Ι—an dage ba, saurin dauke idanun sa yayi, ya cigaba da tafiya, zazzak'ar Muryar ta ya ji tamkar busar sarewa... cak ya tsaya da tafiya saboda yanda wakar ke fita daga bakin ta kamar haka...✍️ Ga masu son shiga hoorain group ga linkπŸ‘‡ https://chat.whatsapp.com/JxzoG62bUENBfExeNPbRSu NoorEemaan 07082281566 [14/12, 12:54 pm] π™½πš˜πš˜πš›π™Έπš–πšŠπš—βœ¨: πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡ HOORAIN MAI KUSUMBI (The hunch back girl) πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡ _NoorEemaan_ *The love and affection he has for her totally made him a changed person. Labarin da yazo da wani salo wanda baku taba ganin irin shi ba, fadakarwa, zafaffan soyayya, tsantsar kiyayya, sadaukarwa mai girma and a lot of more* Chapter 9οΈβƒ£β©πŸ”Ÿ 🎻🎻 _I wanna come home to roses_🌹 _And dirty little notes on post-it's_πŸ“ _And when my hair star turning grey_...πŸ§‘πŸ½β€πŸ¦³πŸŽ»πŸŽ» 🎻🎻 _He will say I'm like a fine wine better than age_🍷 _I guess i learned it from my parents, that true love starts With friendship_β™₯️ _A kiss on the forehead_πŸ’‹ _a date night_πŸŒƒπŸ _Fake an apology after a fight..._🀫 _i need a man who's patient & kind gets out of the car and hold the door_πŸš— _i wanna slow dance in the living room like_... _we're 18 at senior prom_. _And grow old with someoneπŸ§‘πŸ½β€πŸ¦³πŸ‘¨πŸΌβ€πŸ¦³who makes me feel young_πŸ’ƒπŸ•Ί _i need a man who loves me likeee... My father loves my mom_β™₯️🎻🎻 ta kai Ζ™arshen wakar nan da wani slow tone mai tsayawa a rai. *HAMDAN* Ji yayi Kamar ruwan kan shi ya kone, wani yanayi mai wuyar fassaruwa ya dinga ratsa shi, ba tare da ya shirya wa hakan ba, kasan makoshi ya furta " ya rabb! what a melody voice" Hoorain kuwa sam bata san da tsayuwar sa ba, domin ita kanta dake wakar ratsa zuciyar ta yake, sosai take matukar son wakar nan, wanda a wayar Aramani ta fara ji har ta haddace ta saboda kaunar da take wa wakar... Idanun sa ya kai kan fatar hannun sa...kofofin gashin jikin sa sun bubud'e wanda hakan baya rasa nasaba da yanda wakar ta yi tasiri har jinin jikin sa, bai kara bari ya kalle inda take ba ya fara takawa cikin tafiya mai kama da sassarfa ya bar wajen. Bayan ya isa gidan da suka sauka kan gado ya fada, yayi matashi da karfafa hannun sa, yana sauke tagwayen ajiyar zuciya tamkar wanda yayi gudun tsere, ya rasa yadda zai fassara wannan yanayin da ya shiga yanzu... ********** *HOORAIN* Zaune suke a karamar tsakar gidan su, kafar ta na cinyar mami tana gyara mata farcen ta abin so adorable. Mafi yawan mutane na mamakin yadda Hoorain ke fara sol, yayinda Mami baka ce. Shakuwa da soyayyar da suke wa juna abin burgewa ne, tamkar ya da kanwa haka suke. "Mami mie" Hoorain ta kira Mami da taushin murya. "Na'am" Mami ta amsa cikin kulawa tana kallon ta. A karo na uku take son furta Abinda ke ranta amma ta rasa yanda zata fara tambayar Mami amsar da ta dade tana son ji. Numfashi ta sauke kana tace "Abbi! Mami Please ina yake?" Kod'add'iyar rezar dake hannun ta Mami ta ajiye, damuwa mai yawan gaske ya bayyana a fuskar ta, hannun Hoorain ta rike da har ta fara hawaye tace "Hoorain! Sau nawa nace Miki kada ki kara min maganar Abbin ki? Shin akwai abinda na gaza Miki a matsayin uwa? Akwai? Na sani cewa muna cikin matsin rayuwa wanda nake fatan ya zama tarihi watarana, ko kin gaji da zama da ni bana miki yadda kike so?". Cikin sauri ta rungume Mami tana sakin kuka mai taba zuciya, kan kusumbin ta da kamar kullum kara masa girma ake Mami take shafawa... cikin so, kauna, da tausayin tilon yarta. Hak'ik'a tana ganin rayuwa wanda babu wanda zai kawo mata sauyi face Ubangiji, bata damu da kanta ba, kullum addu'ar ta shine Allah ya kawo sauyi Na alkhairi a rayuwar Hoorain... Sam bata son jin Maganar mahaifin Hoorain wanda ya wofintar da su, ko yar sa bai kara waiwaya ba yau shekaru sha biyar kenan, Meye laifin su da suka cancanci wannan sakamakon daga gareshi?... *********** A yau su Hamdan suka samu sanarwar daga manyan sa kan gobe zasu dawo, domin an riga an yanke hukunci wa yan ta'addan nan daidai da laifin su... Sai dai abin mamaki sai ya ji ba dadi a lokacin daya samu wanna sanarwan duk da yanda yake a k'age ya bar kauyen, gaba-daya sai ya rasa abinda ke masa dad'i, yana ji kamar zai bar abu mai muhimmanci ya tafi wanda bai san menene shi ba. Haka ya wuni cikin wani yanayi mara dadi a gare shi. *WASHEGARI* Bayan sallar asuba duk suka yi shirin tafiya amma banda hamdan. Jin shiru ya sa wani soja ya zo ya k'wank'waso dakin sa, yana kan sallaya yana addu'o'i... shafa addu'ar yayi kana ya mike ya bude Kofar, cikin girmamawa sojan ya kame ya sara masa, jinjina masa kai Hamdan yayi ba tare da yace komai ba. Sir! Kai kadai muke jira" inji sojan. Boyayyen ajiyar zuciya hamdan ya saki kana yace "am not going with you guy's" ya fad'a yana yin hanyar waje, bayan sa sojan nan ya bi. "Good morning sir?" Duk suka fada suna tsara masa. "Morning!" Ya fada cikin husky voice din sa, yayi shiru na seconds hamsin duk sun zuba ido da kunne suna jiran yayi magana. "Ban zan tafi da ku ba, akwai abinda zan yi a nan for some days, already nayi magana da commander, safe trip guys" Yana gama fadin haka ya juya zuwa cikin gidan, yana mamakin yanda ya kasa sarrafa kan sa, balle ya bijirewa umarnin da zuciyar sa ke ba sa. Haka ya wuni cikin gidan, ba tare da ya sake fita ba.. ta bangaren sojas dinnan kuwa misalin k'arfe hud'u na yamma suka isa bukavu barracks motocin su a jere reras... Da ihu suka shiga babban gate din *quarter guard* suna buga band, hadi da rera wata waka ta soldiers, gaba-daya Muryar sa ta karade barrack din daya kasancewa shiru, yawancin sojas dake barrack din suka fito waje murmushi dauke a fuskar su suna daga musu hannu, domin wanna ihun da sojas din keyi ya tabbatar da cewa sun samu nasara a fita wannan yakin da suka je. Commander dake tsaye cikin tsantsar farinciki na kallon su har suka gama faka motar su, kana duk suka zo wajen sa, cikin girmamawa suka kame kam kana suka tsara masa... Hannu ya dora a kansa yayi musu alamun jinjina, wanda hakan yayi nuni da cewa ya jinjina wa jarumtar su, ya kuma ji dad'i, bai wani tsayar da su ba ya sallame su domin su huta gajiya... *NASARAWA GRA SULTAN ROAD* "Falmata! Wai har yanzu wannan gantalafaffen inuwar yakuwar Hamdan din bai dawo ba? Bayan ga shi mun samu labarin sauran sojojin sun dawo, duk da bai da kirki, amma Ni na damu da shi saboda banda bakin hali irin nasa, yadda nake fara a fuska haka zuciya ta take tas, na rantse da Assamadu da ina nan lokacin da Yaron nan zai tafi soja da ban bari ba, yo ya lafiyar kura ma, ace banda bakin hali da murtuke fuska babu abinda ya karo" Ayiyah ta karasa cikin kumfan baki, kai kace zata rufe Mutum da duka. Su kabeer dake zaune a wajen dariya kawai suke ba ma kamar kalmar gantalafaffe inuwar yakuwa da ta ce. Ammi dake zaune ta kalle ta kana ta ce "Ayiyah bari na kara kira number'n sa, Ni kaina na damu da rashin dawowar ta sa wallahi". Ammi ta karasa tana latsa tsad'ad'iyyar wayar ta wanda hamdan ya siya musu iri Ι—aya. *HAMDAN* Zaune yake ya jingina kansa da bangon dakin, idanun sa a lumshe, Muryar ta dake rera waka na amsa kuwwa a kunnen sa tamk'ar yanzu ne ta ke yi, ringing din wayar sa ne ya dawo da shi duniyar tunanin daya fada, rikitatun idanun sa da suka dan Sanja launin ya ware kana ya latse kore hadi da karawa a kunnen sa... "HAMDAN!" Ammi ta kira real name din sa wanda zai yi wuya ka ji ta kira shi da suna sa. "Yes first love, good evening?" Bata tsaya amsa gaisuwar ba tace "Are You okay? talk to me kana lafiya dai ko?" Murmushin da iyakar sa labb'a ya saki, yana matuΖ™ar kaunar Ammi fiye da zaton mutum, ita din rayuwar sa... "Ammi ina lafiya" "Then meyasa baka dawo da sauran sojas dinnan ba, am pretty sure baka dawo ba, na san da ka zo gida". "Dan taune lips din sa yayi, cikin yanayin sa na rashin son magana yace " ina Kogi..., amma zan dawo soon, wani abu zan yi ne, amma karki tambaye ni please Ammi nah" Jikin Ammi ne yayi sanyi, ajiyar zuciya ta sauke ta ce "kana boye min wani abu ne?" "Not at all first love" "Hmmmm..." Ammi tace tana sauke numfashi, kana ta kara da cewa "i wish you all the best son" "Thank you first love, how are my siblings doing?" "Fine alhamdulillah" daga can ya ji muryar Ayiyah na cewa "ka ji dan k'wal uban yaro mara kirki, ina nan na tada hankalina a kan ka amma ko kace a bani way..." Ai bai jira yaci karshen maganar ba ya katse wayar, domin Ayiyah zata iya saka masa ciwon kai da surutun ta. ******* *BAYAN KWANA DAYA* da misalin karfe shadaya ya shirya cikin polo T-shirt black sai wando ash color, kasancewar akwai dan rana yau sai ya sanya facing cap, fess da shi looking handsome sai tashin k'amshin sanyayyar perfume yake na company'n D&G. Hannun sa duka biyun soke Cikin aljihun ya fice daga gidan, cikin kauyen oguma ya nausa, bai san abinda zai kai shi, sai dai zuciyar sa na mamari da kwadayin zuwa kauyen..... Bai wani hadu da mutane sosai a tafiyar sa ba sai jefi-jefi, kasancewar yau talata ranar cin kasuwar su ce, yawanci suna kasuwa yayinda wasu ke gona, daidai yazo Kofar gidan da ya ga Hoorain na shara sai ya kasa cigaba da tafiya, kamar an rike kafafun sa, mamakin yake, yadda gaba-daya ya fara sauyawa daga ainahin HAMDAN MALEEK BUMSA zuwa wani daban....✍️ _manage Please, yau nayi busy da yawa_... Share share share fisabilillahπŸ™ NoorEemaan 07082281566 Thank you for reading my novel πŸ₯° Ga mai son shiga group din Hoorain mai kusumbi ya danna wannan link dinπŸ‘‡ https://chat.whatsapp.com/JxzoG62bUENBfExeNPbRSu [14/12, 12:54 pm] π™½πš˜πš˜πš›π™Έπš–πšŠπš—βœ¨: πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡ HOORAIN MAI KUSUMBI (The hunch back girl) πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡ *Korafi ya karbu, zan kara yawan typing. Ina godiya sosai masoya da yanda kuka karbi littafin Hoorain, ku cigaba da bin alkamina domin jin yadda labarin zai kaya, wannan littafin ya sha bambam da duk wani Novel nawa, sosai na jima da son yin book din nan tun a Novel din papi, Amma Allah bai nufa ba sai yanzu, Muje zuwa... Noor na muku sahihiyyar kauna*πŸ’•πŸ˜˜ _written by NoorEemaan_✍️ Chapter 1️⃣1️⃣⏩1️⃣2️⃣ _________Mintuna goma masu kyau ya dauka a tsaye yana murza hannun sa cikin na juna, duk wani tunanin sa ya tsaya cak, zuciya da idanun sa ke son ganin ta, duk yanda ya kai ga son bijirewa zuciyar sa ya kasa... Kamar wanda ake bawa umarnin haka ya ga yana jefa kafar sa cikin gidan, sautin bugun zuciyar sa na sauyawa... Sai daya tsinci kansa a dan soron gidan su kana hankalin sa ya dawo jikin sa, a ransa ya furta "Hamdan me hakan kake yi akan mace? Please come back to your normal self, this is not you"... Cikin sauri ya juya domin barin gidan... saura bai fi taku uku ba yace an ce "waye nan?" Runtse rikitattun idanun sa yayi, kana ya ware su ya juyo ga Mami dake tsaye, duk da yanayin mai wuyar fassaruwa da yake ciki ba zaka taba fuskantar hakan a saman fuskar sa ba. "Me zaka ce kazo yi cikin gidan su?" Wata zuciyar ta tambaye sa. A hankali ya tako ya zo gabanta, cikin girmamawa ya dan dukar da kan sa yace "Good morning ma" domin a lokacin sha biyu saura. " Good Morning, lafiya dai ko?" Mami ta fada Cikin sakin fuska, a ranta tana mamakin Meye kawo shi gidan su? Ta bangaren hamdan ma ya dan yi mamakin jin Mami tayi Hausa, kasancewar kallo daya mutum zai mata ya gane cewa ita din Ζ™abilar igala ce, amma bai nuna ko alama ba. Kamar yadda ya saba yake kuma dabi'a a gareshi ya buΙ—e bakin sa kamar bayason magana yace "nazo ganin ta ne" ya ji ya fadi maganar da bai san ta ina ya fito ba. A ransa yana fatan kada ta kara masa wata tambayar, domin wanna karon bai da wata sauran amsa. Dariya ya bawa Mami, amma bata yi ba, ta maimaita abinda ya fada " nazo ganin ta ne" ta lura kamar bai da son yawan magana, "shigo daga ciki" Mami tace yana yin gaba, ta san cewa bazai cuce su ba, domin yanayin sa bai yi kama dana mugu ba, duk da ance mugu bai da kama. ga agogon soja dake hannunsa wanda ya tabbatar mata da cewa yana daga cikin sojojin da Allah ya aiko suka kawo musu karshen azzaluman yan ta'addan nan. **** Da kallo Hoorain dake zaune kan yagagiyyar tabarman su ta bi su da kallo, hannunta cikin sakin masara da man ja Sai yaji... Kasa hadiye na bakin ta yi sakamakon ganin Mami da wani Balarabe a tunanin ta sun shigo... Da kallo ta bisu, mamaki fal fuskar ta, cikin Yaren Igala tace Mami tace "Hoorain wajen ki yazo" Duk da tayi mamakin abinda Mami tace amma bata nuna ba, cikin ladabi tace "toh Mami". Daga haka Mami ta shige daki abun ta. Sauke idanun ta kasa tayi, cikin rashin sanin abinyi ta cigaba da taunan abincin ta a hankali... *HAMDAN* Tsurawa k'ananan labb'an ta masu kala biyu yayi, wanda ya kasance pink sai zagayen baki kamar ta zana da eye- pencil sai dai ba haka bane, naturally haka lips din ta yake... Yanda take taunan yafi komai tafiya da shi, idanunsa ya kai kan sakin masara da yayi fari kamar ma ba a sa masa manja ba, alamun bai ji ba. Ya kasa yarda cewa mutum ke cin irin wanna abincin da a wajen shi sai dai ya kira shi guba, domin a tunanin sa zai iya sa mutum rashin lafiya, saboda ganin da yake wa abincin yanzu wani tashi zuciyar sa ke yi, dauke idanun sa daga kan abincin yayi, a fakaice ya kalli tsakar gidan su, a rayuwa bai taba ganin gida daya lalace irin wannan bare har ya shiga, amma saboda bawa abinda zuciyar sa ke so yau gashi a cikin gidan da a wajen shi gwara kwalta a kan sa. "Tsawon wani lokaci suka dauka cikin irin wanna gidan? Allahu Akbar and they survive" Ya fada a ransa, yana jin wata matsananciyar tausayin su, dama akwai mutane da suke cikin zallan talauci haka? Bayan ga masu hali bila adadin suna facaka da kudi kan abu mara muhimmanci..... Ajiyar zuciya amma boyayye ya saki a Lokacin da ya ji melody voice din ta. "Good afternoon, Please sit" tace tana nuna masa tabarman bayan ta dan matsa. Kallon tabarman daya yayyage ga jan kasa duk ya cika shi, kamar mai tsoron kar wani abu ya cije shi haka ya fara kokarin zama, cikin sauri Hoorain ta zabe dankwalin atamfar kanta daya sha ruwa ya kode ta warware kan tabarman, ta kuma yi hakan ne gudun kada wandon shi ya bace, kana ta yafa wani bakin dankwali dake gefen ta, wanda ya dawo ruwan kasa-kasa saboda tsabagen d'ad'ewa. Ajiyar zuciya ya sauke, kana ya zauna, amma kafafunsa na kasa, bai cire takalman sa ba. "Bismillah" tace tana dan turo masa kwandon samiran da duk jikin sa ya gama tsatsa. Can kasan makoshi ya girgiza kai hadi da furta "Thanks" kasa cigaba da ci tayi, sai wasa take da hannun ta cikin abincin. Cikin tausaya wa ya kalle ta, a ransa yake fadin abincin ba dadi shiyasa ta kasa ci, shi a hakan ma ya ga kokarin ta, domin a cewar sa ko dabbobi aka bawa bazasu iya ci ba, zuciyar sa ce ta kasa hakuri ya ce "ba dad'i ko" da dan mamaki ta kalle shi jin yana Hausa, amma bata ce komai ba, cikin murmushi daya taho da cikowar kwalla tayi, wanda ya lo6a one side dimple dinta tace "tun ina shekara biyu na fara cin irin wanna cimmar, kaga ya zame min jiki, kawai nayi loosing apatite ne" Lumshe rikitattun idanun sa yayi kana ya bude su, Muryar ta na matukar tasiri a jikin sa... Haka suka yi zaman kurame babu wanda ya Ζ™ara magana, can Hoorain tace "kana cikin sojas da kuka taimaki kauyen mu ko?" Jinjina mata kai yayi, ba tare da yace komai ba, murmushi tayi tace "mun gode kwarai, may Allah reward You guys" "Ameen" ya amsa slowly. Daga nan babu wanda ya kara magana cikin su, kallon hunch back din ta yayi, abinda yake ji a labarai yau gashi ya gani a bayan Hoorain, tausayi take bashi sosai da wanna abu dake bayan ta, can ya kalle ta yace "I shall take my leave, take care" "Toh sai anjima" hoorain replied tana kallon sa har ya fice... Haka kawai taji ya burge ta, baya ga Mami da Aramani shine mutum na uku da ya zo kusa da ita haka ba tare da kyama ba, komai na shi ya burgeta, musamman tsananin tsafta da iya gayun sa, ajiyar zuciya ta sauke kana ta kalli dakin da Mami take, cikin siririyar Muryar ta, sannan a ladabce tace "Mami! Bacci kika yi?" "A'a omami" (a'a diyata) Mami ta fada tana fitowa. "Ya tafi kenan?" "Eh Mami, yana da kirki sosai, amma baya son magana" ta fada cikin yanayi mai kama da shagwa6a... Murmushi Mami tayi ganin Hoorain ta sake sabanin dazu da take zaune shiru, tana son yarta, burinta ta kasance cikin farinciki a kullum, shiyasa a kowacce sallar ta Hoorain take Fara yi wa addu'a. "Dama kin san shi ne?" Mami ta jefa mata tambayar. "A'a faa, yana dai cikin soldiers da suka yi mana maganin yan ta'addan nan" Jinjina kai Mami tayi cikin gamsuwa, lallai wannan yaro da abin mamaki yake, ta san dai dan mai kudi ne, domin yanayin sa ya nuna hakan baro-baro, amma gashi yazo har gidan su wajen Hoorain wanda Bata gama sanin dalilin zuwan sa ba,amma ko ma menene dai zai bayyana, domin yaron ya kwanta mata a rai.. Haka suka cigaba da hirar su gwanin sha'awa. *BUKAVU BARRACKS KANO* Zaune commander yake a tsararren office din sa, wayar sa ce ta dauki kara, hannu ya kai ya dauka hadi kara wa a kunne su.... Daga can bangaren field Marshal ke tambayar sa " wai har yanzu Captain Hamdan Maleek Bumsa bai dawo ba, domin na kira wayar sa bata shiga ba". Nan commander ya sanar da shi cewa "Yes sir! har yanzu dai" marshal yace "Yakamata ya dawo hakan nan kusan sati kenan, sunyi namijin kokari a aikin da suka gudanar, gashi ya yi shekara biyar a matsayin Captain, matsayi za a kara masa, and we can't do nothing tunda baya nan" "Haka ne sir! Nima zan gwada kiran layin sa, idan ya shiga zan sanar da shi lalle ya dawo cikin gaggawa" cewar commander, nan suka yi sallama da Marshal. ********* *Kogi state* (Kauyen Oguma) Kwance yake a kasa ba amma duka ba, domin hannu da kafafunsa ba a kasa suke ba, cike da jarumta yake yin kasa da sama, a turanci dai ana kira shi da presa up, ya riga daya saba kullum sai yayi wannan excerise din yake jin dadi... Cigaba da yayin excerise din yayi, fuskar Hoorain na mai yawo ciki idanun sa, komai na yarinyar na yayi masa, a ganin farko ya kamu da son ta, Abinda turawa ke kira love at first sight . Yana jin zai iya rayuwa da ita a ko wani yanayi da ko wani hali, ta samu matsayi mai yawa cikin zuciyar sa, baya ga tsananin son da yake mata, yana mata kallon kanwa, wanda bai da shi, hakika ta samu matsayi wanda babu wata mace data taba samun irin shi a zuciyar sa... Ammi ce ta fado masa, ya san cewa matukar ta samu labarin cewa yayi masoyiya zata yi farin ciki, domin abinda ta dade tana so kenan, ko kusa bai taba kawowa zai fada so mai zafin gaske haka ba, abinda yake ji a kan Hoorain bazai fadu a baki ba. Amma babu wanda zai gane hakan saboda dakiya, jarumta, da zurfin cikin sa... Ya jima cikin tunanin Hoorain din sa, kana ya mike, ya nufa toilet domin yin wanka, saboda a kage yake da son ganin ta, tun yana mamakin sauyawar halayen sa har ya daina, Hoorain has totally changed him from Captain Hamdan to another new person duk da ba sa wani hira, amma ganin ta kusa da shi na sanya zuciyar sa yin sanyi... _nayi alkawari gobe in Sha Allah zan yi update_ Share Share Share Please as much as you canπŸ™ NoorEemaan 07082281566 Thank you for reading hoorain the hunch back girl.πŸ™πŸ₯° *(Not edited)* [14/12, 12:54 pm] π™½πš˜πš˜πš›π™Έπš–πšŠπš—βœ¨: πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡ HOORAIN MAI KUSUMBI (The hunch back girl) πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡ _written by NoorEemaan_πŸ“šβœοΈ ELEGANT ONLINE WRITER'S πŸ“šβœοΈ Chapter 1️⃣7️⃣⏩1️⃣8️⃣ Daga can bangaren Ammi kuwa a zafafe ta daga wayar domin sauke masu tsananin fushin da take dashi, saboda kullum cikin damuwa take, musamman data daina samun sa k'watak'wata a waya... Sabanin fadan da take da niyyar masa, sai jikin ta yayi laushi sak'amak'on muryar sa da ta ji yayi kasa sosai ya furta "my first love". Ajiyar zuciya Ammi ta sauke tana jin fushin da take da shi na raguwa, sosai take son Hamdan, amma ta rasa meka damun sa gaba-daya ya sauya mata, kamar ba zakin sojan ta ba, duk da babu gazawa a muryar sa amma ta66as akwai canje-canje a tare da shi. "Captain dina, ka Ι—auke ni matsayin ammin ka kuma first love dinka kamar yadda kake fada?" "Of course yes Ammi" ya fada yana mikewa zaune, domin da kamar bacin rai Hadi da damuwa a tattare da Muryar ta. "Then why kake boye mun damuwar ka, ko ban cancanci sani ba?". "A'a Ammi, kin fi kowa dacewa ki sani" ya fada cikin wata murya daya kashewa Ammi jiki. Amma ta daure tace "in hakane then tell me, me kake a kogi bayan ba dangi uwa bare na uba a can, meyasa bazaka dawo ba, na kasa gane maka fa, You re behaving strange these days, ko so kake ka samun damuwa a zuciya, baka bani ciwon kai kana yaro ba sai yanzu daka mallaki hankalin ka Hamdan? answer me am taking to you" wanna karon a dan tsawace tayi maganar domin she can't take it anymore. A Zuciyar sa yaji wani daci sosai, idanun sa ya runtse da karfi, abu ne wanda kowa na gidan su ya sani, matuΖ™ar Ammi ta kira real name dinsa toh lallai fushi take da shi, boyayyen ajiyar zuciya ya sauke kana cikin Muryar sa da yayi bala'in yin kasa yace "Am sorry Ammi, please karki yi fushi dani, You know I have you first love, bana kaunar ganin fushin ki..." Numfashi ya dan sauke yana datse jajayen labb'an sa da jerarrun hak'oransa sannan ya cigaba da cewa "as soon as na dawo zan baki labari mai dadi wanda kika jima da muradin jin shi daga bakina" Sanyin sosai Ammi taji a ranta, fuskar ta dauke da murmushi. Hamdan ya dan yi gyaran murya yace " pray for me, ki sa ni a addu'ar ki, Allah ya bani ikon yin abinda ke raina, kinji first love?" "My handsome son, a kullum ina maka, sannan zan dage da tashin dare domin yi maka addu'a, Allah ya tsare mun kai a duk inda kake, ya baka Sa'a, Please do take care of yourself for Ammi ok, i love You" "I love you too first love" yayi mata reply. "Yawwa nace yaushe zaka dawo ne?" Shiru yayi na yan Mintuna sannan yace "Ammi ban sani ba, but a kodayaushe zaki iya gani na, just pray for your son" Jikin Ammi ya fara sanyi da lamarin Hamdan. Definitely something is fishy somewhere, amma bata matsa masa ba, addu'a ta k'ara masa, da haka suka yi sallama. Ya jima zaune idanun sa a lumshe yana tunani.. can hoton fuskar Hoorain ya mamaye idanunsa, ajiyar zuciya ya sauke kamar ita din ya gani a gabansa, tuno halin daya barta a ciki ne yasa shi mikewa, yayi kewar ta ba kaΙ—an ba, musamman zazzak'ar Muryar ta da murmushin ta dake sanya zuciyar sa yin sanyi, mikewa yayi ya shirya, kana ya nufi cikin kauyen nasu.... ******* Kansa tsaye cikin gidan bakin sa dauke da sallama kasa kasa kamar yadda ya saba, dan tsakar gidan nasu shiru, babu motsin kowa. Mami data ji Muryar sa kasa_kasa ta fito tana amsa sallamar, cikin girmamawa ya dukar da kansa ya gaishe ta, Mami ta amsa fuskar ta a sake, kana ta warware masa matacciyar tabarman su dake nannad'e sakamakon hakan k'urar jar dake jikin tabarman ya tashi, kawar da kansa gefe yayi, juyowa Mami tayi ta ce "zauna ko, bari na taso Hoorain, tun jiya taki bacci sai dazu na samu baccin ya d'auke ta" Sabon tausayin ta ne ya kamashi, so yake ya ce wa Mami ta barta tayi bacci amma ya kasa magana saboda miskilancin sa da rashin son maganar sa. *Hoorain*! kwance take kan kafita wanda sabagen yanda kafitar ta dade gaba-daya ya cinye, har gwara tudun wani tabarman a kan shi. Gaban kafitar Mami ta karasa hadi da tattaba Hoorain a hankali, a dan zabure ta farka, ganin Mami yasa ta saki ajiyar zuciya hadi da k'amk'ame hannun ta, cikin kulawa Mami tace "Hoorain tashi, Hamdan yazo" Lumshe ido tayi cikin baccin da bai ishe ta ba, amma ta ji sanyi a ranta a dalilin zuwan ya Hamdan dinta. A hankali ta tashi, bayan ta gyara dankwalin kanta ta nufi waje...ido suka hada tayi masa Murmushi, zura mata ido yayi baya ko kiftawa, wajen da fashashen butar su yake ta nufa, ta zuba ruwa cikin tafin hannun ta ta kuskure bakin ta, sannan ta kara diba ta wanke fuskar ta, tana juyowa suka hada ido, saurin Ι—auke kanta tayi ta zo gefen sa ta zauna. Cikin siririyar Muryar ta daya dan tsarke da bacci ya kuma bada wani amo na musamman tace "ya Hamdan! Ina kwana" Lumshe ido yayi, kana ya ware su a kanta, kasa tayi da kanta, a ranta tana mamakin wanna yawan kallo da yake mata a yau, Hamdan kuwa abubuwa da yawa yake ji a kanta wanda baki bazai iya fada ba, sai dai a bar wa zuciya, ga wani mugun kyau da ya ga ta kara masa a yau, musamman manyan idanun ta da suka kara haske tarrr... Dankwalinta daya dan zame kadan, wanda ya bawa gashin gaban kanta bayyana. Abin kafita ya gani makale a gashin ta, hannu yasa ya cire hadi da nuna mata sannan ya jefar, kunya taji ya kamata. Haka suka yi zaman kurame a wajen, daman yawanci ita ke magana, amma damuwa dake manne a ranta yasa ta kasa magana a Yau din. Bayan azahar sai ga Aramani yazo, Hoorain ta ji dadin ganinsa, tana son Aramani domin Allah, tana jin shi kamar wan ta. Hira ya dinga janta da shi, abin ka da mai barkwanci nan da nan Hoorain ta Ι—an saki jiki tana murmushi. Hamdan yaji dadi ganin babe dinsa ta fara walwala sak'amak'on labaran barkwanci da Aramani ke bata, although Yana Jin kishin Aramani a ransa duk da yasan babu komai a tsakanin su, amma tsananin son da yake mata yasa baya kaunar ko wani da namiji ya rabe ta, amma bashi da zabi da ya wuce ta kasance cikin farinciki. Sai bayan la'asar aramani ya tafi, duk da ba a samu cikon na bakwai ba, domin babu wanda ya yarda zai kara bin su, saboda tsananin hadarin duniyar mutuwa. Sai bayan magriba Hamdan ya yafi cike da kewar Hoorain. haka ma ta bangaren Hoorain sam bata ji dadin tafiyar sa ba, ga damuwar da take ciki ya dawo sabo saboda gobe ne su Aramani zasu tafi, a ranar bacci ya kauracewa idanun ta, kuka mara sauti ta dinga yi... WASHEGARI *5:55am* Zaune yake kan sallayar dakin da yake kwana, ya gama addu'o'in sa da azkhar. Yayi shiru tunani mabambamta na zagaye brain din sa wanda yasa jijiyoyin kansa suka fito, wayar sa ya janyo ya rubuta wa Ammi text kamar haka... _saba'ul khair ya Ammi, ki min addu'a kinji yau ne zamu_........ sai kuma ya kasa karasa wa ya tura mata. Dalili kuwa shine bayason ta shiga damuwa, infact ya yi imanin cewa idan tasan inda zai je bazata taba amincewa. Kara rubuta mata yayi _i love You so much Ammi, you re the sweetest mum ever, ki yafe min if I have ever offended you in any way_ Ganin massage din ya shiga, sai ya kashe wayar da sauran 2percent ya jefa cikin jakar sa irin ta sojoji da ya so da ita, toilet ya shiga yayi wanka hadi da brush wanda ya dauk'esa Mintuna ashirin sannan ya fito, goge jikin sa yayi da mini towel, ya shafa mai hadi da fesa body spray, wasu bakakken kaya riga da wando body hug na kamfanin DOLCE AND GABBANA (D&G) ya sanya, hair cream dinsa na kamfanin XPEL ya shafa bayan ya cire dan rubber band din, ya jefar, tajewa yayi, sannan ya kara kamawa da sabon rubber banda kamar yadda ya saba a kasan keyar sa, jelar har wuyan sa. Wani turare mai sanyin k'amshin na kamfanin Christian Dior ya fesa sama-sama, sannan ya rufe gidan ya fito...cikin tafiyar sa ta sojojin masu ji da jarumta hadi da cikakken lafiya ya fara lafiya. Kusan a tare shi da dan baiwa suka zo kofar gidan su Hoorain, ko kallon sa bai yi ba. Gidan ya shiga bakin sa dauke da sallama, Mami da Hoorain ya gani zaune sunyi jugum abin tausayi, gaishe da Mami yayi, ta amsa cikin muryar damuwa, Hoorain da idanunta suka kumbura alamun ta sha kuka ta kallesa ba tare da ta samu karfin gaishe sa ba, saboda mutuwa da jikin ta yayi kamar wacce aka wa duka. Jin hayaniyar mutane ya sa suka fahimci cewa dan baiwa yazo, a sanyayye suka fita, Hamdan dake tsaye shima ya bi bayansu, ganin damuwa mai tarin yawa a fuskar abin kaunar sa (Hoorain) ya sanya yaji wani iri ba dadi a ransa... Suna fitowa Hoorain ta ga su Aramani, wani sabon kuka ya kufce mata, wajen shi ta nufa ta rike hannunsa gam, cikin shesheka tace "Aramani karku je, banason rasa ku, nace Muku zan rayu a haka, a hakan ma na yaba da tarin kaunar da kuka nuna a kaina. Mami! ya Hamdan! ku musu magana dan Allah" ta karasa wani uban kuka ya kara kufce mata. Murmushi Aramani da sauran mazaje biyar din suka yi, sannan suka ce "Hoorain muna kaunar ki domin Allah, ki mana addu'a kawai, idan Allah yayi bazamu dawo ba ki dinga samu cikin addu'o'in ki kinji" Kara raunata zuciyar ta yayi, ta dinga kuka kamar ranta zai fita, kukan da sautin sa ke fita da zallan damuwa hadi da tsoro. Maganar dan baiwa ne ya dawo da hankali mutanen kan sa yace "Alhamdulillah! Allah yasa an samu mutane shida, sai dai babu cikon na bakwai, shin akwai wanda zai zaba cikon dan bakwai, domin taimakawa rayuwar Hoorain?" Ya fada yana raba idanunsa kan jama'ar wurin. waje ya dauki shiru, wasu har boye fuskar su suke kamar irin za a musu dolen nan. Hamdan da tun ranar da dan baiwa yayi wannan Maganar ya riga ya sa a ransa cewa koda babu wanda ya yarda zai je, shi din zai je domin dauko wa Hoorain magani. Cikin tafiyar sa ta burgewa ya karasa wa wajen da su Aramani ke tsaye alamun shi din ne cikon na bakwai su, ba tare da yace komai ba. "Alhamdulillah! Komai yayi daidai" dan baiwa ya fada yana kallon Hamdan da fuskar nan ke daure tamau kamar ko yaushe. Sosai sauran jama'ar wurin suka cika da mamaki, ganin bare wanda ba dan kauyen ba zai je, duk da basu san Meye alakar shi da Hoorain ba, amma sun yi mamaki ainun, domin abu ne wanda babu wanda ya ta6a kawowa ko kusa zai aikata. Mami ma ta cika da zallan mamaki, ta bangaren Hoorain kuwa sabon shock ne ya shige ta, baki ta bude, ta kafe Hamdan da ido hawaye na zuba daga cikin su. Can taja wani ajiyar zuciya mai tafe da sheshek'a tamk'ar jaririn da yayi kuka sosai, hannun Mami ta rike tace "Mami, kin ga ya Hamdan ko? Kice kar ya mun haka, ki masa magana mamiiiiiiiii" ta fashe da wani sabon kuka fiye dana dazu. Mami bata da karfin magana, wanna wace irin zallan soyayya zaratan samarin nan ke wa yarta haka? Mutane bakwai sun sa kansu a abinda suka san akwai tarin hadari domin Hoorain, har abada bazata taba manta wanna abin alkhairin da suka musu ba. Dan baiwa yayi gyaran murya yace " lokaci na tafiya, ga wata addu'a zan baku ku rike, ku dinga yin ta, kamar yadda na fada zaku gamu da mugayen Aljanu, mayu, hadi da Wasu hallitu marasa kyau a tafiyar ku da dawowar ku, ina so ku karfafa zuciyar ku, kada ku bari yayi rauni, duk wata yaudara da zasu muku kada ku amince dan Allah ku kiyaye, addu'ar da zaku dinga yi itace _Innalillahi wa inna ilahi raju'un_ _Allahumma ajirniy fiy musibatiy, wa akhlif liy khairan minha, ko la'ilaha ilah anta subahanaka inni kuntu bina zalimin_. Ya maimaita musu sau uku. Ku rike wannan addu'ar a duk lokacin da kuka ga wata masifa ta shigo hanyar ku, Allah ya dawo da ku lafiya ya tsare ku" yana kaiwa nan ya fara tafiya sa da sauri sauri kafin kace min har ya bace musu kamar walkiya saboda tsabagen saurin sa. Su Aramani na ta sallama da yan'uwa da iyaye, wasu na kuka wasu na musu fatan dawowa lafiya ga masu Ζ™arfin hali kenan, duk da iyayensu sun hana su tafiyar amma sun ki, sai kawai suka bisu da addu'a, fatan su Allah ya dawo da su lafiya. *HAMDAN* A hankali ya juyo ya kafe Hoorain da idanunsa masu cike da zallan son ta, ya san he will miss her a lot, dauke kan sa yayi ya fara tafiya a hankali duk da bai san direction da zasu bi ba... Wani tight hug ya ji anyi masa ta baya... ta kifa kanta a bayansa tana kuka sosai, wanda hakan ya sa ko wani kofoffin mahudan gashi dake jikinsa suka bude, har cikin jikin sa kukan ta ke ratsa shi, zare ta yayi daga bayansa, ya dawo da ita gaban sa, gabanta ya tsugunna tsayin su yazo daya duk da ba a tsaye yake ba, domin lalurar ta ta kusumbi ya sa ta gajarce, janyota yayi ya sanya ta cikin faffad'ar kirjin sa, yasa hannuwan sa ya zagaye ta, ajiyar zuciya mai karfi ya saki, wani yanayi da bai ta6a jin irinsa ya shiga ratsa shi, sai dai hakan bai yi tsari sosai ba sak'amak'on halin da ake ciki. Hannunsa kan kusumbin ta yana shafawa a hankali, ba tare da yayi magana ba, sunyi Mintuna biyar a haka sannan ya cire ta a jikin sa ya bata wani sumbata mai dumi a goshin ta. Cikin husky voice din sa da yayi kasa yace "babe! Promise me you won't cry, i love You so much, and I will forever love you" "I.. love...you...too ya...ha...m..dan" ta fada a rarrabe sak'amak'on sheshek'ar da take saki a kai a kai. Hannun ta ya kama ya sumbata sannan ya mike cikin sauri ya fara tafiya, Aramani ya zo ya kara bata baki sannan duk suka bi bayan Hamdan.... Zubewa tayi a kasa ta dinga kiran sunan su daya bayan daya, amma duk babu wanda ya juyo Cikin su... A hankali Mami dake share hawaye ta zo Bayan ta hadi da dafa ta. _*one Free page left*_πŸ€ΈπŸ’ƒ *Ku hanzarta biya Habibte's domin na sa ku a original group, it's #300 via, 2261488155 Rukayya haruna zenith bank.*. *Ko katin MTN ta wanna number'n 08131237178* *Marasa banki kuma zaku iya zuwa pos ku biya ni #250 sai ku bawa mai pos #50 kudin charges din sa, nayi wanna ragin ne domin makaranta na da suka min maganan basu da banki* *Wadanda suka biya, ina godiya sosai*πŸ™πŸ€πŸ₯° NoorEemaan 07082281566 Share Share Share fisabilillah Habibte's πŸ™πŸ₯° Thank you for reading my story, πŸ‡#hoorain Mai kusumbi πŸ“ [14/12, 12:54 pm] π™½πš˜πš˜πš›π™Έπš–πšŠπš—βœ¨: πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡ HOORAIN MAI KUSUMBI (The hunch back girl) πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡ _NoorEemaan_βœοΈπŸ“š Chapter 1️⃣3️⃣⏩1️⃣4️⃣ Mintuna arba'in ya dauke shi shiryawa, kana ya dauki hanyar cikin kauyen oguma. Yana zuwa kofar gidan ya hangeta daga dan nesa da shi tana tafiya da bokitin rike a hannun ta, nan ya fahimci rafi zata je, wani iri ba dadi haka ya ji a ransa. So yake ya kira ta amma ya rasa ta yanda zai fara bude murya..., hakan ya sa cikin zafin nama irin na su na soldiers ya shiga bin ta, taku biyar zuwa shida ya iske ta... *HOORAIN* Ji tayi an karbi bokitin hannu ta, a tsorace ta juyi, ganin Hamdan ya sa ta sauke ajiyar zuciya mai sauti kana tayi murmushi. Hamdan so yake yace mata sorry ya razana ta amma ya kasa. Cikin sanyi da dadin Muryar ta tace "ina kwana ya Hamdan" ta ji sunan shi ne a lokacin da Ammi ta tambaye sa. Wani yanayi na musamman yaji a zuciyar sa, kannen sa ya tuno, domin haka suke kiran shi, amma nata dabanne, domin tamkar da wani salo daya kawata sunan ta yi amfanin wurin kiran shi, wanda ya ji ya tsaru sosai a kunnuwan sa. "Lafiya" shine abinda yace cikin maganar sa da yafi kama da rada, domin idan baka da kunnen ji bazaka ji abinda yace ba. Hoorain bata kara magana ba suka cigaba da tafiya, duk wanda suka hadu da shi a hanya su dinga bin su da ido kenan cikin mamaki, wasu har tuntube suke garin kallo, babban mamakin su shine ganin lafiyayyen namiji handsome uwa uba dan gayu a tare da Hoorain mai kusumbi. ashe duk iya wakan Taheer dan mai gari da suke gani wasa ne, domin Hamdan ya dama ya shanye shi... Hamdan kuwa kara dinke fuskar nan yayi tsaf ganin kallon yayi yawa. Bayan sun zo rafin Hoorain ta kalle shi, tace "ya hamdan kawo bucket din na debo ruwan" Wani kallo ya jefa mata, shi ba harara ba gashi nan dai, kasa da tayi da kanta, domin k'wayar idanunsa mai kalar sararin samaniya yana matuΖ™ar tasari a gareta tare da saukar mata da kasala, sam bata jurar kallon cikin su. Kan wani babban dutse ya nuna mata yace "sit!" Ba musu ta zauna. Kamar ruwa ya cinye Yammatan dake rafin nan, mutuwar tsaye suka yi ganin Hoorain da Hamdan, hassada k'arara ya bayyana a fuskar su, tsanar Hoorain ya kara cika zuciyar su. Hamdan kuwa bakin rafin ya nufa, ba tare da ya kalli fuskar kowa ba, kamar kullum macijin 🐍 nan mai gadin ruwa na nan bakin ruwan...kallo daya yayiwa macijin ya dauke kansa, bucket din ya sa cikin ruwan ya diba kana ya nufi wajen da Hoorain ze zauna, alama yayi mata da ido kan su tafi ba musu ta tashi ta bishi, a ranta tana mamakin yau yammatan basu tsokaneta ba... Yau karon farko a kauyen oguma da bata yi kuka ba, sak'amak'on babu wanda ya nemi tsokanar ta. Sun dan yi nisa da tafiya Hoorain taji an kwala kiran sunan ta. A tare da suka tsaya, amma shi Hamdan bai juyo ba, murmushi Hoorain ta sakarwa Aramani daya taho hannun sa rike da kayan aikin gona. Bayan ya karaso suka gaisa cikin yanayin su na shakuwa, sannan ya gaishe da Hamdan, gogan bai amsa ba, sai hannu daya bashi suka yi musabaha, wani dadi Aramani yaji ganin classic handsome guy ya bashi hannu sun gaisa ba kyama. Kallon Hoorain yayi da yare yace "waye wanna kyakkyawan?" Murmushi tayi, cikin yaren ita ma tace "sabon yaya ne" ta fadi hakan domin bata san matsayin daya bata a zuciya ba kar ta zafafa da yawa. "Gaskiya ya hadu, kuma wallahi kunyi kama fa" Dan kwabe fuska tayi tace "dan'uwa Aramani haka zamu yi da kai, kai ma kasan ba gaskiya bane" Dariya Aramani yayi kana ya yi musu sai anjima ya tafi... Kamar kullum taheer da mutanen sa na zaune, gaban Hoorain ya fadi a lokacin data hange su...amma abin mamaki har suka wuce bata ji ko gyaran murya sun yi ba, hakan yayi matuΖ™ar daure mata kai, a yau duk masu tsokanar ta da ci mata fuska da lalurar da take da shi amma yau first in history Babu wanda yace komai, taji sanyi a ranta sosai, yau taji itama mutum ce kamar sauran mutane. Kasancewar yanzu an saba kan sa tsaye ya nufi cikin gidan bakin sa dauke da sallama, Ya ajiye ruwan kana ya zauna kan matacciyar tabarman su da har ya saba da zaman kan sa yanzu, hakika babu abinda so baya iya mayar da mutum, bare shi da wannan ne farkon shigar sa, ba karamin kamu yayi masa ba. "Thank you ya Hamdan" Hoorain ta fada. Lumshe rikitatun idanun sa yayi batare da yace komai ba, yana kewar Ammi yana son jin Muryar ta, gashi garin saurin zuwa ganin Hoorain ya manta da wayar can gidan. "Where is Mami?" Ya tambaye ta ganin bai ji motsin ta ba. "Ta fita, amma bazata dade ba" ta karasa tana zama kan tabarman. "Tell her abinda ke zuciyarka hamdan, for how long zaka cigaba da yin shiru" zuciyar sa ta bashi wannan shawarar. Numfashi mai dumi ya furzar, cikin confidence din sa yace "babe" Da mamaki ta kalle shi jin sunan daya kirata. Hamdan kura mata ido yayi baya ko kyaftawa, saurin yin kasa tayi da idanun ta. "I love You babe, did you love me?" Kamar saukar aradu haka taji kalaman sa, shin kunnen ta ne bai ji daidai ba? *LOVE* dama akwai wanda zai so ta da wannan lalurar? ko mai nakasa bata taΙ“a kawowa zai so ta ba, balle had'add'en guy ajin karshe kamar Hamdan, wasu hawaye suka wanke mata fuska, Muryar ta na k'ak'arwa domin abin ya girmama brain dinta tace "You love me ya Hamdan?" Bata kaunar ganin hawayenta ta, domin ya na taba masa zuciya, a hankali ya sa babban dan yatsar sa ya dauke hawayen fuskar ta, cikin husky voice din sa yace "shhhh! Yeah i do, i Love You so much, i love You for no reason" Wani sabon kuka ta rushe da shi, ta rasa wani yanayi take ciki, but all she knows this tayi farinciki da duk abinda yace, wacece ita da zata ki shi? shine mutum na farko a duniya ya ta6a furta mata kalmar so ba tare da ya damu ko duba lalurarta na kusumbi dake kara girma a kowacce rana ba....lallai wannan shine tsaftataciyyar soyayya da samun irin sa ke wuya a wanna zamanin. Cikin muryar ta da bai dawo daidai ba tace "ya Hamdan....ina... ina...son ka nima" ta karasa tana rufe fuskar ta hadi da fashe masa da sabon kuka mai ratsa zuciya... *MAMI* Duk maganar su ta ji, domin tsaye take a soron gidan zata shigo ta ji abinda su ka ce. Hawayen idanun ta ta share, ta yi farinciki sosai wa tilon yarta, tabbas alamun Nasara ne wanna, yau taji abin farin ciki Wanda rabon da ta ji irin sa tun mahaifin Hoorain ya bar su, fatan alkhairi ta yi musu a ranta, maimakon shiga gidan da zata yi, sai ta juya waje. *HOORAIN* Ta Ι—auki Mintuna tana kuka a ranta take furta "ya rabb! What a blessed day in my life" Hamdan da kukan ta ke masa zafi a kirji ya kalle ta da idan sa da suka dan Sanja launin kadan Yace "did i say anything wrong?" "Nooo ya Hamdan, kukan farinciki nake" ta karasa tana share idanun ta, sosai idanun ta suka kumbura abin ka da farar mace. "Stop those tears ok" ya fada mata calmly. Jinjina masa kai tayi tana Murmushi mai tsayawa a rai. Sai ta dan kalle shi da kumburarun idanunta tace "kayi hakuri ya Hamdan, na manta ban Maka ruwa ba" ta karasa tana Ζ™oΖ™arin mikewa. "No Thanks" yace mata. komawa tayi ta zauna, shi kam bazai iya shan ruwan garin nan ba, bare ya ga maciji a rafin nan, domin har yayi imaging cewa macijin na yawo cikin ruwan. *BAYAN WASU MINTUNA* Tsaye ya mike yana soke hannun sa cikin aljihun wandon sa, "i will see you tomorrow babe, i love You bye" yace yana barin gidan, ba tare da ya tsaya ba, wanda hakan yasa Hoorain bata samu nasarar amsa masa ba har ya fice...murmushi mai sauti ta saki sai ta sa hannu ta rufe fuskar ta cikin jin kunya, duk da ya Hamdan baya magana, amma yana burge ta, infact komai na shi na burge ta kuma tana son shi. Bata wani jima da zama ita kadai ba Mami ta shigo, cikin farinciki tayi wa Mami sannu da zuwa, cike da kulawa Mami ta amsa ba tare da ta nuna ta ji maganar su ta dazu ba, amma kasan ranta farinciki ne fal cikin sa... ************ Zaune yake kan katifar dakin, wayar sa dake hannun sa ya shiga jujuyawa kana ya danna power button wayar ta kawo haske domin a kashe take. Messages masu yawa ya fara gani a inbox din shi amma bai duba ba, manjahar WhatsApp ya shiga Bayan ya kunna datar sa, massages masu yawa ne suka dinga shigowa.... Ajiye wayar yayi for like two minutes har massages din suka gama loading... Sakon abokon sa Corporal Imran ya shiga, domin shi ne a farko, yaga ya rubuta masa _hey dude! Kwana biyu shiru hope You re fine_? Dubawa Hamdan yayi ya ga yana online, hakan yasa ya fara yi masa reply kamar haka _my fine Imran, what's up_? Typing Imran ya fara masa kamar haka... _dude wai bazaka dawo bane? ana ta neman ka anan barrack, Please come back, wai me kake a kogi ne?_ _you won't understand imran_ shine amsar da hamdan ya bashi. _then make me understand_ Imran ya fada. Shiru Hamdan yayi for some minutes har Imran ya fidda rai da jin reply din sa sannan ya ga yace _i love her Imran_ "What!?" Imran yace a zabure yana mikewa tsaye, shin mafarki yake, CAPTAIN HAMDAN MALEEK BUMSA ne ya furta yana son wata, duk zurfi ciki hadi da miskilancin sa? Murmushi Imran keyi hannunsa na rawa wurin rubuta masa reply... _wait! Are You sure is person iam speaking with is Captain Hamdan?_ ya karasa yana saka emojin tsokana (😜) Share sa hamdan yayi ya mayar da idanun sa ya rufe. Karan sakonin yaji sun dame shi, sai ya sake buΙ—e wayar... _Am sorry dude! Wasa nake, Please gayamin who's the lucky girl data samu gagarumin nasarar sace zuciyar da yammata bila adadin ke rububin saman sa_? Abinda Imran yace kenan cikin zallan zumudi, dama gashi mayen love ne . _*The hunch back girl*_ hamdan ya bashi amsa. _what! Like seriously You mean tana da kusumbi a baya_? Imran ya tambaya da zallan mamaki yana saka emojin dariya. _yeah! You think she's no body on the outside? Well I can assure you that on the inside... She's the whole fucking queenπŸ‘‘ that rules the kingdom of my heart_ Daga haka ya sauka a online gabadaya hadi da kashe mobile data din sa, yaso kiran Ammi amma baya so yaji muryar ta da damuwa a dalilin rashin dawowar sa. duk son da yake wa aikin sa na soja a yanzu bai damu ko da ya daina saka kaki ba, ba kuma zai bar kauyen nan idan ba tare da Hoorain ba, bai san yadda zai kasance ba, amma bazai iya tafiya ya bar ta ba. Daga bangaren Imran kuwa wani abu ya ji game da kalaman hamdan na karshe, sosai kalaman suka taba masa zuciya, hakika so yayi wa abokin sa mummunan kamu, wanda zallan soyayya ne da babu algus a Cikin ta, kamar karamin yaro ya dinga tsalle yace "yes!" Kana ya dunkule hannu irin abin ya mai sugar, Sannan ya kara da cewa "Ina tare da kai dude, indeed this is true love" *NASARAWA GRA SULTAN ROAD* 5:09pm Omar, Anas da kabeer ne suka dawo daga kamfanin da mahaifinsu ya bari kamar yadda suka saba, sallama dauke a bakin su suka shigo part Ι—in ammi, a sanyayye Ammi dake zaune kan kujera ta amsa tana Ζ™oΖ™arin boye damuwar fuskar ta bayan ta amsa sallamar su... Duk kusa da ita suka zauna, sai ya zamana tana tsakiyar su. Anas yace "Ammi You look cold, har yanzu wayar ya Hamdan bai shiga bako?" Ajiyar zuciya ta sauke tace "i just hope and pray yana lafiya Anas, yayanku na da zurfin ciki, na san akwai wani abu a kasa definitely" "Kiyi hakuri Ammi in Sha Allah yana lafiya, kin san yaron ki jarumi ne, he can take care of his self". Cewar kabeer "i know, Amma kun san baya son cin abinci, kila yana can yana barin kan sa da yunwa" ta fada cikin karyewar zuciya. "Ammi karki damu zai ci da yawa saboda ke, You know yaya na kaunar farinciki ki" Omar ya fada domin kwantar wa Mata da hankali "Allah yasa" Shine abinda Ammi tace tana dan murmushi, ta Ι—an ji sanyi a ranta sak'amak'on abinda su Hamdan suka ce. Hira suka dinga jan ta da shi har Ayiyah ta fito daga dakin ta zo aka cigaba hira, tana musu halin nata ana dariya. *_Thanks to everyone for the warm prayers, Ina muku fatan alkhairi tare da fatan gamawa da duniya lafiya, fans dina dana sani da wanda ban sani ba alkhairi Allah ya kai mu a duk inda kuke, masu tayani sharing novels nawa jazakallahu khair Habibte's_* πŸ™πŸ₯° NoorEemaan 07082281566 Thank you for reading my story πŸ‡#hoorain the hunch back girlπŸ“ 2:48pm Tuesday 24/5/2022 [14/12, 12:54 pm] π™½πš˜πš˜πš›π™Έπš–πšŠπš—βœ¨: πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡ HOORAIN MAI KUSUMBI (The hunch back girl) πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡ #sacrifice #hotlove #heart touching #hatred #betrayal _written by NoorEemaan_πŸ“šβœοΈ Chapter 1️⃣5️⃣⏩1️⃣6️⃣ Safiyar alhamsin ne, jama'ar kauyen Oguma sai fitowa suke sak'amak'on jin Muryar dan baiwa Ashimi, domin su san matuΖ™ar ya fito yana magana, toh fa yayi mafarki ne, kowa fargaban sa Kada a kira daya daga cikin sunan ahalin sa. *TAKAITACCEN TARIHIN DAN BAIWA ASHIMI* Asalin sa dan kauyen oguma ne, ya samo inkinyan sunan dan baiwa ne sakamakon idan yayi mafarki yana kasancewa gaskiya, tarin baiwa da ilimin sa ya sa ake ganin shi kamar wani sha takwas, wanda azahiri ba haka bane, tarin baiwa da ilimi ne ya sashi kasance hakan, farko idan yana sanar yayi mafarki, Zai kuma ce ayi sadaka mutane domin Allah ya yayyafawa abin ruwan sanyi, sai ana daukar abin wasa, har ya zama abin dariya ga yan kauyen. Ranar da yayi wata mafarki basu Ι—auke shi da Muhammanci ba, har abinda ba a so ya hafku, domin exactly munanan mafarkin da yayi ya faru a zahiri. hakan yasa tun daga wannan ranar idan Allah ya sa yayi mafarkin mutum mara kyau, sai yace ayi sadaka, ko kuma yace a dage da tashi sallan dare, in Sha Allah sai mutum ya ga komai lafiya sakamakon addu'a da sadaka da ya yi, hakan yasa da yayi mafarki ya bayyana suna daukar shi da gaske... *BACK TO STORY* ********** Sai daya zo daidai kofar gidan su Hoorain ya ja ya tsaya, kana yace "Hoorain Yusuf a yau Allah ya bani ikon ganin maganin lurar ki a mafarki" ya maimaita hakan sau uku abinka da yan kauye gaba-daya sun zagaye shi, ana ta kallon sa. Ta bangaren Hoorain kuwa zaune suke ita da Hamdan da kullum sai yazo ya ganta yake samun nutsuwar zuciya. Mami tana daki a zaune, yayinda Hamdan ke bare mata cashew nut da Aramani ya kawo mata soyayye tana ci, kawai kallon dan tsut din bakin ta yake with much admiring on his face, komai nata na burge shi, kamar ya hadiye ta Ι—an so amma sam ba za ka taba gane hakan ta fuskar shi ba. A lokacin da suka ji Ashimi dan baiwa ya kira sunan Hoorain gaban Mami da ita Hoorain yayi mummunan fad'uwa, cikin rashin fahimta Hamdan ke kallon hanyar soro ta inda yake hango kafafun mutane, gashi hayaniyar su ta cika wajen... Mami ce ta fito daga daki, sannan ta mikawa Hoorain hannu domin taimaka mata wurin tashi, cikin mugun sanyi da jikin ta yayi ta kama hannu Mami ta mike... cikin tafiyarta ta masu kusumbi ta bi bayan Mami, Hamdan ma mikewa yayi ya rufa musu baya, nan fa idanun yan k'auyen ya bisu Mami da suka fito zuuuuuuuuu Cak Ashimi ya sayar da idanun sa masu kwarjini sosai ga fuskar Hoorain, kasa tayi da kanta domin idanun sa tsoro suke bata sakamakon tarin baiwa daya cika cikin su. "A yau Allah ya nuna min ke Hoorain a mafarki" Sai ya kalli Mami da idanun ta ke dauke da hawaye yace "wannan kusumbi ba da shi kika haife ta ba, tana da Shekara daya a duniya aljanin daya yi sha'awar surar ta ya sanya mata sakamakon wata rana kin kwantar da ita tana bacci babu wando a jikin ta, kina band'aki, shi kuma ya bayyana gareta, surar Hoorain ya burge shi kana ya bashi sha'awa duk da karama ce, hakan yasa ya mika hannunsa daidai bayanta wani koren haske ya bayyana ya shiga ratsa bayanta, bayan wasu Mintuna ya bace bat. Manufar sa ta yin hakan shine saboda kada wani da namiji ya aure ta ko ya so ta, shi kadai ne zai mallake ta. Kamar wasa a hankali kusumbi ya fara tsiro wa har yayi wanna girman, a ko wacce rana wannan Aljani mai suna mushkaf sai ya zo ya kara mata girman sa, shiyasa kullum kusumbin ke cigaba da mamaye bayan ta, idan kuma aka cigaba a haka watarana zai rinjaye ta ta yanda ko tashi zai gagare ta..." Salati, ihu, hadi da surutai kala-kala ke tashi a wajen, Mami hawaye take abin tausayi, tabbas Ashimi dan baiwa bai yi karya ba, ba haka ta haife yar ta ba, nadama sosai ya rufe ta, domin bata manta lokacin da mahaifin Hoorain ke yawan cewa ta daina barin Hoorain ba kaya, ashe ita ta ja wa yarta wanna lalurar sai ta rushe da kuka hadi da saka matacciyar hijab dinta da shi kadai ta mallaka ta toshe bakin ta dashi .... Muryar ASHIMI dan baiwa daya cigaba da tashi ya sa wurin ya dawo so slient kamar ba hallitu a wajen duk suka kasa kunne suna sauraron sa "Alhamdulillah! Allah ya nuna min maganin, wanda maganin warakar kusumbi Hoorain yana world of dead (duniyar mutuwa)" Salati aka kara saki, wasu har da dora hannu a kai. Ashimi dan baiwa ya cigaba da cewa "world of dead na da matuΖ™ar hatsari fiye da tunanin ku, mugayen Aljanu, mayu masu shawagi da rana hadi da wasu hallitu marasa kyauwu ne suka cika duniyar mutuwa, duk mun san cewa babu wanda ya taΙ“a zuwa ko yin hanyar duniyar mutuwa. Toh anan maganin warkar da kusumbin Hoorain yake cikin wata kwarya a karkashin bishiyar kuka..." Shiru ya dan yi yana bin mutane da kallo kana ya cigaba da cewa "zaratan samari bakwai ne zasu yi wanna tafiyar zuwa duniyar mutuwa domin dauko kwaryan nan, ba karya zaku hadu da miyagun hallitu da zasu yaudare ku, domin da siffa mai kyau zasu zo muku amma kada ku yarda da su daidai da Ζ™wayar zarrah, ku karfafa zuciyar ku, ku rike addu'a, ga wadanda suka shirya wannan tafiya zan baku wasu addu'o'i domin kare kanku, Hoorain na da kyakkyawar zuciya, ga duk wanda ya ga zai taimaka mata Allah ya biya shi, jibi ne tafiyar, na barku cikin aminci" yana kaiwa nan ya juya cikin tafiyar sa ta sauri_sauri ya bar wajen... *HOORAIN* Kamar wacce aka datsa haka ta cigaba da tsayawa idanunta kurrr kan dan baiwa Ashimi har ya tafi ta kasa kyafta idanun ta a wajen da ya tsaya, tsananin shock yasa ta kasa motsi, sai ruwan hawaye dake bulbulowa daga idanunta kamar an kunna famfo... *HAMDAN* Kallo daya zaka masa ka hango tsantsar damuwa daga cikin blue eyes dinsa daya Sanja launi, gaba-daya ransa a bace yake, duk da kasancewa mushkaf ba a jinsin bil'adama yake amma wani mugun kishi ke caccak'ar zuciyar sa game da shi, tausayin babe din sa ya kara yawaita a zuciyar sa. Mutane ne suka fara watsewa kowa da abinda yake cewa, cikin sauri Hoorain ta fada cikin gidan tana kara sakin kuka mai tsuma zuciya, Mami ta biyo bayanta, kana Hamdan ya mara musu baya... hannunsu zube cikin aljihun wandon sa ya kafe ta da idanun sa masu Ι—auke da tausayi, tsananin so, zallan kishi, hadi da bacin rai amma bai ce komai ba. Abin tausayi haka Mami ta zube gaban Hoorain hadi da dafa ta, cikin sauri ta dago, ganin Mami ce yasa ta fada jikin ta hadi da kiran "Mami mie" cikin kwarewar zuciya. Hugging dinta back Mami tayi tana rarrashin ta, kana tace "Hoorain haka Allah ya Ζ™addara Maki, amma har da laifina ciki domin tabbas kina yar karama ban fiye son saka Miki kaya ba, ki yafe....." "A'a A'a Mami, wallahi bazaki taba Zama mai laifi a gareni ba, ke ce duniya ta, ke kika kila da Ni har na kai iyanzu, Mami kada ki ci komai dan Allah, ina son ki Mami mie" Kuka Mami ta sa, kauna da tausayin tilon yarta na kara mamaye zuciyar ta. Hamdan kuwa bai taba ganin abinda ya ta6a zuciyar sa hadi da bashi tausayi kamar Hoorain ba, karamar innocent girl da take cikin K'addarar rayuwa. Kasa jurar kallonsu yayi ya fita waje ya samu wani benchi na karfe a dan nesa da gidan su Hoorain ya zauna hadi da nausa hannunsa cikin sumar kansa yana mai rufe idanun sa. **************** Da misalin K'arfe biyar din yamma, sai ga Aramani tare da wasu samari biyar sun zo gidan su Hoorain. Abin mamaki suka sanar cewa zasu je duniyar mutuwa domin dauko maganin nan da zai warkar da kusumbin ta, sun kuma sanar da su cewa zasu Yi wannan sadaukarwan domin son fisabilillah da suke wa Hoorain, hakika ta sha gwagwarmayar rayuwa da tarin kalubale, ya kamata zuwa yanzu ta ji dadi ko yaya ne. Suka kara da cewa suna saka ran in Sha Allah su samu cikon na Bakwai din zuwa gobe tunda jibi ne tafiyar. Mami tsabagen al'ajabi yasa ta kasa magana. Hoorain kuwa kuka ta samu musu tana cewa "Aramani, Danjuma, salihu, yakubu, oshimana, Abu, dan Allah karku je, bana so ku mutu, karku jefa rayuwar ku cikin hadari saboda Ni, ina farinciki da godewa Allah a yanda nake, dan Allah bazan iya jurar rasa ku baaaaaa" ta ja karshen maganar sakamakon mugun kukan daya kufce mata. "Tafiya babu fashi Hoorain yar'uwar mu, matukar kana son mutum zaka iya sadaukarwa mai girma domin shi, ki mana addu'a kin ji ko? In Sha Allah zaki mike kina tafiya kan kafafunki kamar kowa" samarin suka hada baki wurin fadin haka, daga nan suka fice a gidan. **** A ranar kam har dare Hoorain idanun ta jike suke da ruwan hawaye, ta kasa daina kukan, Mami kallon ta kawai take cikin tausayawa domin babu wani karfin guiwa a tare da ita, jikin ta gaba-daya ya mutu, a ranar sun manta sunan abinda ake cewa *YUNWA* saboda tsananin damuwa daya cika zuciyar su, ko lokacin da Hamdan ya tafi ma basu sani ba. Ta bangaren yan kauyen Oguma kuwa, ko wani gida da ko wani majalisa hirar Hoorain ke tashi kowa na fadin albarkacin bakin sa. *WASHEGARI* *HAMDAN* Tun ranar da suka gama chat da Imran bai kara kunna wayar ba sai yanzu, kallon percentage din wayar yayi ga sauran masa 10% a hakan ma ya ga kokarin ta, domin iPhone baya mugun rikon chargi, gashi tunda yazo kogi bai yi mata chargi ba. Contact list ya shiga, inda ya tsayar da idanun sa kan number'n Ammi, wata karfafar ajiyar zuciya ya sauke, kana ya danna number'n ta hadi da kara wayar a kunnen sa yan sauraron ringing din da yake... *Mun fara shigowa cikin labarin, i swear basan yadda zan kwakwanta zafin book din nan ba. Abubuwan ciki na daban ne, just continuing following my pen, sahihiyyar kauna Noor ke wa masoyan ta na fili dana boye* *Naso kara yawan typing amma banda a enough charge* *_guys Meye ra'ayinku kan page din yau_?* *Two free page left karku ji dif*πŸ€ΈπŸ’ƒ NoorEemaan 07082281566 Thank you for reading my story πŸ‡#Hoorain the hunch back girlπŸ“ Share Share share PleaseπŸ™ 9:07 26/5 2022 [14/12, 12:54 pm] π™½πš˜πš˜πš›π™Έπš–πšŠπš—βœ¨: πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡ HOORAIN MAI KUSUMBI (The hunch back girl) πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡ _written by NoorEemaan_ πŸ“šβœοΈ Chapter 1️⃣9️⃣⏩2️⃣0️⃣ Hannun Mami ta rungume gam tana cigaba da kukan, ga muryar ta ya fara dashewa... haka ta cigaba da kallon su har ta daina ganin su. Mami ta kamata da k'yar domin ita ma babu karfi a jikin ta suka nufi dan gidan su. Mami ta shigar da ita daki, Hoorain ta sulale kan yoluluwar kafitar su ta kwanta, babu jimawa wani zafaffan zazzab'i ya rufe ta, jikinta ya dau zafi, hak'oranta na had'ewa dana juna yayinda jikinta ke rawa kamar mazari... Hankali tashe Mami ta dauko yan jike-jike irin na su na kauyen ta bata ta sha, sannan ta dauki zanin ta ta rufa mata, bayan Mintuna talatin wani bacci mara dadi ya dauke ta cike da mafarkin su Hamdan. ********* *NASARAWA GRA SULTAN ROAD* _10:00am_ A dai-dai lokacin Ammi ta tashi daga bacci, domin raba dare tayi tana ibada, bayan tayi sallar asuba kuma bacci ya dauke ta, sai yanzu ta tashi. Mikewa tayi tana dan yamutsa fuska abinka da jikin tsufa, toilet ta nufa tayi wanka sannan ta fito ta shirya cikin had'add'e kuma tsad'add'en atamfar *English gold* ta shafa humra da wasu turaren ta masu dadin k'amshi. Ammi macece mai son gayu, tsafta, hadi da k'amshi, a takaice dai a wurin ta y'ay'an ta suka gado hakan. Bakin gado ta zauna, ta latsa wayar ta, inbox dinta ta gani ya nuna an turo message, hakan yasa ta shiga, ganin number'n Hamdan ne yasa ta danna da sauri... Sau uku ta maimaita abinda ya rubuto mata, jikin ta yayi sanyi sosai kalaman sa sun ratsa zuciyar ta, tausayin sa da son sa sosai taji ya kara shigar ta har hakan yasa wasu hawaye Masu dumi suka biyo kuncin ta, hannun ta daga sama a fili tace "ya Allah ka fini sanin abinda yarona ke yi, ya Allah ka bashi Sa'a, ka zaba masa abinda yake mafi alkhairi, ka tsare shi da tsarewar ka ya Allah, ka kiyaye shi da kiyayewar ka, mugun ji, mugun gani ya Allah ka raba shi da su, sharrin mutum sharrin Aljani ya Allah ya kiyaye shi, Allah ka dawo min dashi cikin koshin lafiya" ta shafa addu'ar wasu hawayen na kara zubo mata. "Falmata! Falmata!! Wai baccin ne yar yanzu? inci dai Lafiya ko?" Ayiyah data zo bakin kofar yanzu ta fada. Cikin gaggawa Ammi ta share hawayenta, sannan ta dai-dai ta Muryar ta ce "gani nan Ayiyah" ta fada tana nufar bakin kofar, ta bude, ta wani dogon corridor ta bi sai ga ta a babban falon ta wanda ya kasance kamar general falo domin duk a nan suke jin abincin. Ayiyah ta gani zaune ta kurawa tv ido, kamar idanun ta zasu fado ciki, jin takun tafiyar Ammi yasa ta waiwayo, ta zubawa Ammi idanunta da ta rambada musu kwalli har yaso yayi yawa, tace "Falmata! wanna wani irin Bacci mai nauyi kika yi haka? Hankalina ya tashi ba shiri na kwashi kafafuna nace bari na dubo ko lafiya, yo Allah na tuba kana zaune da mutum yanzu, daya shiga daki babu jimawa sai dai ka ji ya zarce lahira, su Anas ma sun tambaya nace baki tashi ba, har sun wuce aiki domin sun ce basa son tashin ki" Murmushin k'arfin hali Ammi tayi a ranta tana jinjina surutun Ayiyah ko full stop babu, rissinawa tayi kamar yadda ta saba ta gaishe da Ayiyah, cikin kulawa Ayiyah ta amsa tana sa mata albarka, domin ta kasance mace mai son a girmama ta, sannan tana yawan yabon Ammi a ranta domin duk da danta Wanda shine mijin Ammi ya rasu, amma hakan bai sa ta fasa girmama ta ba. "Kiyi karin kumallo ko? yau kin makara... Nace wai ya wanna dan fadin rai da miskilancin tsiya, ince kun yi waya mara kirki ko neman kakar sa baya yi" Danne damuwarta Ammi tayi sannan tace "eh Ayiyah yana lafiya, yace ma ce na gaishe ki" ta karasa domin faranta ran Ayiyah. Ta kuwa washe hakoran ta tace "Masha Allah, dan k'wal uba yau ya ga daman tambayata kenan" ta karasa tana sakin dariya irin nasu na tsofaffi. Ammi bata kuma cewa komai ba ta nufi kan dining table, tea da Irish kaΙ—ai ta ji domin sam bata jin yunwa, haka ta wuni curr jikin ta ba dadi, Mintuna kadan sai tayi wa Hamdan addu'a a ranta. *********** *KOGI STATE* Sunyi tafiya mai nisan awannin goma kana suka shigo *land of death (duniyar mutuwa)*. Ko gida daya babu bare ka saka ran ganin wata hallita, sai ciyaye hadi da bishiyoyi, kasan wajen tsaf kamar akwai masu sharewa kullum, da shigar su duniyar mutuwa komai ya sauya, ita kanta duniyar abar tsora ce ga duk wanda ya kalle ta, sai kukan wasu abubuwa kamar na tsuntsaye marasa dadin amo ke tashi. Yamma sosai yayi domin duhun almuru ya fara, sam babu gazawa a tare da su duk da dare ya fara amma basu fasa tafiya ba, bare Hamdan sam babu alamar gazawa a fuskar sa bare gangan jikinsa su gaji. Da sun daidaita lokacin sallah sai suyi taimama su gabatar da sallar su. Ga yunwa ga k'ishirwa daya fara sanyayyar wa su Aramani jiki, amma haka suka daure, domin babu ruwa balle ka saka rai da samun abincin. Har taran dare suna tafiya, wanda zuwa wannan lokacin Danjuma da Ya fi kowa gajiya cikin su ya tsaya, hakan yasa sauran dakatawa fuskar su cike da karin bayani. Cikin Muryar galabaita yace "wallahi na gaji, har jiri ya fara diba na, dan Allah ku bari da asuba mu cigaba da tafiya, bazan iya ba, yunwa sosai nake ji" Cikin tausaya wa duk suka kalle shi, ko wa yasan Danjuma baya wasa da cikin sa, Hamdan dake jikin su ya Ι—an kalli Danjuma sannan ya motsa bakin sa a hankali yace "mu huta zuwa asuba sai mu cigaba" yana fadi hakan ne domin saukaka musu, dan ta shine bai gaji ba, kuma baya jin yunwa ko dan bai damu da abinci bane... Tabbas yasan akwai sauran lafiya sosai a gaban su, tunda ko alamar bishiyar kuka basu gani ba. Gwara su huta domin kada karfin su ya Ζ™are, ya aiyana hakan a ranshi, sannan ya cire takalmin kafar sa ya zauna a kai yana mai lumshe idanun sa. Su Aramani ma zama suka yi, bayan sun ajiye addinan su a gefen su, aramani Sarkin barkwanci kuwa ya dasa hira, nan suka saka bak'i aka cigaba da hira. Hamdan kuwa sam bai san abinda suke cewa ba, domin ya zurfafa kogin tunanin Hoorain din sa, a ransa yana addu'ar Allah basu nasara....Tuno yanayin daya barta dazu ya sa zuciyar sa sosuwa, kukan da take yi hadi da kiran sunan su a lokacin da suka fara tafiya sai amsa kuwwa take a kunnen sa tamkar yanzu ne take yi, iska mai zafi ya furzar daga bakin sa, yana fatan ace ta daina kukan yanzu. Sai sha biyun dare su aramani suka hakura da hiran da suke, Sakamakon baccin daya fara cika idanunsu, nan duk suka kwanta a kasa babu jimawa bacci ya dauke su... Hamdan karewa wajen kallo yayi baya iya ganin ko tafin hannunsa ne, sakamakon tsananin duhu daya kara mamaye wajen, ga wasu Kuka iri daban-daban marasa daΙ—in amo daya cika kunne sa... Da misalin Ζ™arfe dayan dare wani irin dariya mai matuΖ™ar tsorata rai hadi da sanya Mutum cikin rudu da tashin hankali ne ya cika kunnen su tamkar zai fasa musu dodon kunne... A firgice su Aramani suka farka daga nannauyyan baccin daya d'auke su, a tsorace suka fara kalle-kalle amma basu ga komai ba, sai can suka kalli sama inda suka ga wasu hallita masu tsorata ruhi suna shawagi a sararin samaniya tamkar suna tseren jirage yayinda kawunan su ke kallon kasa... Hamdan ya bude idanun sa ya kalli saman sannan ya dawo da kansa kasa, sam babu wani tsoro a tare dashi, domin a cewarsa bai ga amfanin tsoro ba, addu'a kadai ce babban muk'amin mumuni. Addu'a ya fara a ransa, cike da nutsuwa, a tsorace Danjuma da yafi kowa tsorata ya dawo gefen sa ya rakube, kallon sa hamdan yayi ya dauke kansa, gaba-daya Danjuma ya jike da gumi barin ma fuskar sa. "Kuyi addu'a kada ku bari tsoro yayi tasiri a zuciyar ku" ya fada hankali a kwance cikin k'asaitacciyar Muryar sa. Nan suka samu sukunin fara addu'a, Danjuma saboda sabar tsoratan da yayi har addu'an shiga banΙ—aki ya dinga karantowa da karfi cikin fitar hayyaci, abin so Funny da a ce suna cikin yanayin mai kyau babu abinda zai hana su Aramani dariya. Bayan kamar mintuna arba'in dif suka ji dariyar ya daina kana wadannan addu'an suka bace. Still hakan bai hana su shiru ba, addu'a suka cigaba da yi... Babu wanda ya Ζ™ara gingin komawa Bacci cikin su, har asuba ta gabato suka yi taimama, Hamdan ya ja su sallah, bayan sun iddar suka cigaba da tafiya domin haske ya Ι—an fara bayyana kadan-kadan. HOORAIN! Zaune take ta kurawa waje daya ido bata ko kiftawa yayinda hawaye ke sauka a k'yak'yawar fuskar ta, da alama ta zurfafa a kogin tunani. Ammi data fito a sanyayye ta zauna kusa da ita, sannan ta Ι—ora hannun ta kan kafad'ar Hoorain trying to comfort her, Wani sabon kuka Hoorain ta fashe da shi tana shigewa jikin Mami gaba-daya... "Ya isa Hoorain! kuka baya magani, addu'a zamu dinga musu kinji" Cikin Muryar kuka tace "Mami ina tsoro ne, banason wani abu ya same su, a wani hali suke ciki oho? Na san ko abinci basu ci ba mami, ga ya Hamdan bai saba da wuya ba amma saboda ni yasa kan sa a hadari, ina tausaya musu Mami, fatana su dawo cikin koshin lafiya bana son rasa masoyan asali masu nagarta kamar su mamiiiiiiiii" ta ja sunan cikin kuka. Bubbuga bayanta Mami ta dinga yi tana rarrashen ta kan tayi shiru. Ta b'angaren Mami ma tana cikin damuwa kawai dannewa take a zuciyar ta. *BUKAVU BARRACKS KANO* Cikin yanayin mai nuni da fushi FIELD MARSHAL ke wa commander magana kan rashin dawowar Hamdan wanda ya saba ka'ida da doka. A tausashe commander'n Wanda ya kasance dan kabilar Nupe ya dinga bashi hakuri hadi da tausar sa cewa jiya ya ce gidan su dake Nasarawa GRA ya kuma tattauna da Ammi inda tace a kara masa hakuri soon zai dawo, domin yanayin ta ya nuna cewa akwai wani Abu a kasa kan rashin dawowar Hamdan din. "Zan kara masa wasu kwanaki matukar bai dawo ba, he will be punished, domin ya saΙ“a dokar aiki" Marshal ya fada yana katse wayar sa, duk da kasancewar yana son Hamdan domin Allah ya had'a jininsu, amma baya so sam a dinga wasa da aiki... Commander numfashi ya sauke yana son gano menene ya hana Hamdan dawowa, amma ya kasa, domin abu ne wanda kowa ya riga ya sani cewa baya wasa da aikin sa, kara kiran Ammi yayi ya sanar mata abinda Field Marshal yace, kana ya dora da cewa idan ta same shi a waya ta sanar masa, shima zai dinga gwad'a kiran nasa, idan hakan ma bai yu ba sai a aika wasu soldiers din chan kogi a dubo shi. Da haka suka sallama Ammi tayi masa godiya, jikin ta ya kara sanyi sosai, sam bata so damuwar ta yayi tasiri a kan Hamdan balle har ya kasa samun sukunin zuciya a duk inda yake, hakan yasa take kai zuciyar ta nesa tana masa addu'a. *DUNIYAR MUTUWA* (Land of death) Tun suna tafiyar marmari har gangan jikinsu ya fara gajiya, kafafuna su ya yi tsami, ga yunwa ga Ζ™ishirwa. Hamdan shine karfin guiwan su, domin ganin babu gazawa a tare da shi yasa suma suke bada himman wurin bin sa, tafiya suke amma ko alama basu zo inda kwaryan maganin kusumbin Hoorain yake ba... Sai da suka daidaici lokacin magriba yayi sannan suka tsaya domin yin Sallah. Taimama duk suka yi, amma banda Danjuma dake zaune yana sauke numfashi daidai alamun yunwa na k'walk'walan sa gwanin tausayi. Bayan sun daidaita tsaho Hamdan ya juyo ya kalleshi, tsaf Danjuma ya gane Meye ma'anar Kallon, marairaicewa yayi yace "zan yi sallah amma bari na huta kaΙ—an wallahi na gaji" ya karasa kamar numfashin sa zai dauke saboda tsabar yunwa da gajiya. Hamdan bai ce komai ba ya shiga jansu sallah, Danjuma ya kafe su da ido yana kallon su....Can yaji alamun mutum a gefen sa, a dan firgice ya juyo, wata k'yakk'yawar budurwa ya gani zaune gaf dashi tana sakar masa Murmushi mai sumar da mutum, dan zabura yayi zai mike tayi saurin riko hannunsa, lumshe idanunsa yayi saboda tsananin taushin hannun ta, so yake yayi addu'a amma kamar an sa kwado an rufe mai baki. Cikin wata murya mai dadin gaske budurwan nan tace "kar ka ji tsorona, naxo taimaka maka ne, kaji" ta karasa da mayaudariyar muryar ta. Zuciyar Danjuma ta kasu kashi goma, yakasa tsayar da ita wace daya, before he could think of any other thing yaji ta kama hannunsa cikin wani salo ta fara cewa "ka yarda dani, bazan cutar da kai ba, abinci na kawo maka, kasan yunwa kake ji" ta karasa tana mika hannun ta bayan ta take wani bowl mai sheke da lafiyayyen abinci ya bayyana, ta dawo da shi gaban ta hadi da jefan sa da wani kallo mai kona ruwan Ζ™waΖ™walwar mutum sannan tace "kaci, idan baka koshi ba zan kara maka kaji" ta fada calmly. Wani dunk'ulallen yawu Danjuma ya hadiye, yayinda cikinsa yayi kiran ciroma, yunwar da yake ji ta karu sosai, lashe baki yayi, duk da yanda ran sa ya biya da abincin, amma kasan zuciyar sa yana tuno maganar dan baiwa inda yake cewa _Kamar Yadda na fada zaku gamu da mugayen Aljanu, mayu, Hadi da Wasu hallitu marasa kyau a tafiyar ku da dawowar ku, ina so ku karfafa zuciyar ku, kada ku bari yayi rauni, duk wata yaudara da zasu muku kada ku amince_ Numfashi ya sauke ya kalli su Hamdan dake sallah cike da nutsuwa, da alama basa jin Muryar budurwan, wanda hakan ya bashi mamaki. "Ka ci ka ji kada yayi sanyi, har ruwa mai sanyaya makoshi zan samo maka" ta fada tana mika masa abincin. Hannu yasa ya karba Kamar wanda aka umarta, cikin gaggawa ya sa hannun sa cikin bowl din ya dibi abincin fuskar sa kuri kan na budurwan dake ta faman jan hankalin sa cikin salon k'issa da kisisina. Bakinsa na rawa tsabar yunwa ya kai loma daya bakin sa, ya ma manta bai yi bismillah ba, wani lumshe ido yayi domin tunda yake bai taba cin abinci mai dadi dandano irin wanna ba... Cikin sauri-sauri ya dinga ci... ya kusan gama cin abincin ya ga budurwan ta dawo wata mummunan hallita mai tsoratarwa, ta jefa masa wani kallo da jajayen idanunta kana ta bace bat. Wani tashin hankali yaji ya shiga, abincin bakin sa kuwa ya kasa hadiye wa, bowl din hannunsa ma ya bace kamar a mafarki, wani sabon tashin hankali ya shiga, tamkar an yaye masa komai sai yanzu ya dawo cikin hankalinsa... wata mahaukaciyar murdawa Cikin sa yayi, ya dinga ji kamar ana saka mashi ana huda masa cikinsa, zubewa kasa yayi ya rike wuyan sa da yake jin wata azaba a cikin ta, yayinda kumfa ya dinga bulbulowa daga bakin sa, tsananin azaba ya sa ya dinga shure-shure da kafafun sa.... Daidai lokacin ne su Hamdan suka sallame sallah idanun su ya kai wajen Danjuma da har ya daina shure-shuren, jikinsa ya saki alamun rai yayi halin sa, da wani mugun sauri suka yi kansa hankalin su a matuΖ™ar tashe...... *Alhamdulillah!* _*A nan na kawo karshen free pages na Hoorain mai kusumbi, ga mai son cigaba da karanta wa ya biya #300 ta wannan asusun 2261488155 Rukayya haruna zenith bank. Marasa bakin kuma zaku iya zuwa pos ku biyani #250 sai ku bawa mai pos #50 kuΙ—in charges din sa, na yi wanna ragin ne saboda mutanen da suka min maganar cewa basu da banki, idan kun biya sai ku nuna min shaidar biya ta wannan number'n 07082281566*_ _*Yan nijer kuma su min magana domin na gayamasu yanda zasu biya*_. _*fadin zafin littafin nan bata lokaci ne, ya kunshi abubuwa da dama wanda baku saba gani a novels ba, wandanda suka sanni sun san salon rubutu na, sai dai wannan ya sha bambam, ina kaunar baku dukkanin littafina a kyauta, sai dai tanadin daya yi Hoorain yasa bazan iya sakin sa a free ba, dan haka ku hanzarta biya. Mu hade a original group Habibte's wanda a nan ne zan cigaba da posting ga wandanda suka biya*_ *Shin zaratan samarin nan zasu dawo da ransu*? *Shin kusumbin Hoorain zai warke ta dawo cikakkiyar mace kamar kowa*? *Shin akwai sauran kalubale da Ζ™addarar rayuwa da zai sake shigowa rayuwar Hoorain*? *Da sauran wasu tambayoyi dake zuciyar ku, inda duka amsoshin ku na tafe a paid book*. _Sai na jiku, soyayyar da zasu nuna min kadai shine ku siyi littafin HOORAIN THE HUNCH BACK GIRL_. _i love all my fans, known and unknown_πŸ’–πŸ” Thank you for your patronageπŸ™πŸ₯° NoorEemaan 07082281566 I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available. *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 0806626851 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels