NAMA YA DAHU.... ROMO ƊANYE" GAWURTATTU UKU DAGA ALƘALAMIN BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI MARUBUCIYAR LITTAFIN NA FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA (LABARIN SHANONO DA OGA KAILA. NA SAKE DAWOWA DA WANI LABARIN MAI ƊAUKE DA DARASI, DA BAN TAUSAYI, SADAUKARWA, TSAGWARON ZUNZURUTUN SOYAYYA DA ƘAUNA, FARIN CIKI, BAƘIN CIKI DUK A CIKIN WANNAN LITTAFI MAI SUNA A SAMA. KU BIYONI KU SHA KARATU. ALƘALAMINA BAYA RUBUTA ABINDA BAZAI AMFANAR DA AL'UMMAR ANNABI BA. KAMAR YADDA NA SABA WANNAN LABARIN SHIMA YA FARU A GASKEN GASKE, KU BIYO NI DA HANKICI DOMIN SHARE HAWAYEN DA ZASU ZOBO A GURABEN IDANUWANKU. KU GYARA ZAMA DA KYAU KU BI LABARIN SANNU_SANNU ZAKU FAHIMCI INDA YASA GABA. Lamba ta 1 JIHAR KANO: Kano na ɗaya daga cikin manyan birane a ƙasar Hausa. Kano itace cibiyar kasuwanci ta Najeriya gaba ɗaya. Jihar ta Kano tana da ƙananan hukumomi guda arba'in da hudu. Kana gari ne da yake da masarauta mai ɗunbun tarihi, mai kwarjini a cikin kasashen Hausa da kewayenta. Haka zalika Kano gari ne babba wanda mazauna cikinta ke magana da harshen Hausa. Itace gari mafi yawan jama'a a Najeriya baki ɗaya. Kanon ta yi suna wajen kasuwancin da ta bunkasa a kai, har ya zamana ana cewa da ita Cibiyar Kasuwanci. Haka kuma tarihin Kano ya nuna daman can tana da suna wurin cinikayya tsakaninta da mutanen gabas ta tsakiya. Yawan mutanen da suke garin na Kano sun haura kimanin mutane miliyan goma (10.000,000) a ƙidayar da aka yi a shekara ta alif dubu biyu da shida. Jihar Kano tana da matuƙar tasiri a yawan mutane Najeriya, saboda ita ce ta fi kowacce jiha yawan mutane daga ko'ina a faɗin duniya, tun daga na kudancin Najeriya, har zuwa ƙasashen dake maƙwabtaka da Najeriya,hakq kuma za ka tarar da mutanen sin ( wato china) da kuma na ƙasashen larabawa har da turawan yammacin duniya mutanen Kano sun shahara wajen addini sosai. ƘOFAR MATA. Cikin wani layin masu rangwamen arziki na shiga. Duk da kasancewa safiya ce sosai. Hakan bai hana ganin yara suna kai kawo a cikin unguwa ba. Wasu suna kan layin siyan ƙosai, wasu suna kan layin siyan fanke. Wasu yaran da gasarar kokko na gansu a hannunsu. Kasancewar baifi ƙarfe bakwai da rabin safiya ba. Anata hada_hadar shirin karya kumallo. A bakin wani madaidaicin gida na tsaya marar fenti, mai ɗauke da ƙatuwar bishiyar durumi a ƙofar gidan ƙosasshiyar gaske. A ƙarƙashin wannan bishiyar na hango motoci biyu a fake, ɗayar golf 3 ce, ɗayar kuma Vectra ce. Da dukkan halama motocin ta masu gidance. Wani matashine ya fito daga gidan hannunshi riƙe da bokitin ƙarfe cike dumbul da ruwa, ga soson buhu a ɗayan hannun nashi. A gaban motocinnan ya ajjiye bokitin, nan take ya soma watsa ma Vectra ɗinnan ruwa. Daga cikin gidan dai na jiyo hayaniya na tashi kuma muryar namiji nake jiyowa, har da kukan mace daga bisani na jiyo. Ba shiri na faɗa cikin gidan dan ganin meke faruwa haka. Abun mamaki ashe gidan babbane sosai daga ciki, gashi da yalwar tsakar gida. Ɗakuna kuwa gasunan a jejjere kamar a zangon baƙi ( Hotel). Maza da matan gidan, harma da yaran gidan na tarar a tsakar gidan. Wani babban mutum na gani yana ta faɗa, muryarshi ce take fita har ƙofar gida. Babbane a shekaru, dan har da furfura a gemunshi da sumar kanshi. A gefenshi na hango wata doguwar fara kyakkyawar mace a tsaye jikinta sharkab da ruwa har ɗiga take yi tsabaragen jiƙewa, kuka take yi ƙaƙas tamkar wacce akayi ma mutuwa, gata ita dai ba yarinya bace. Wannan Dattijon cikin murya mai amon ɓacin rai yace. "Haula ki dena kukan ya'isa ki bari su fito inji in shi Gwadabenne yasa matar tashi ta watsa miki ruwan kashi sai in ji. Ke da gidan mijinki babu wanda ya'isa ya takura miki wallahi, zan ture zumunta in kori Gwadabe da iyalinshi a gidana, wannan ƙazanta ta buskuta samodarar matarshi ni ya isheni. Ina mai takaici da baƙin cikin haɗa zuriya da matar Gwadabe da mu ka yi" Ya ƙarashe maganar yana huci kamar zaki." Gwadabe:. Da sauri ya fito daga ɗakin nashi rigarshi a hannu, shimi ce a jikinshi da koɗaɗɗen wandon jeans wanda akayi ma wanki sama da sau saba'in, duk yayi yaushi, ya sake kala daga turarren bulu, izuwa kalar sararin samaniya. "Yaya Hambali kayi haƙuri dan Allah. Kema Yaya Haula ki yi haquri. Iyabo ba da saninta ta watsa miki ruwan kashi a jiki ba. Bata san kina banɗakin bane, amman kiyi haƙuri dan Allah, kuma zata kiyaye " Gwadabe ya faɗa cikin sigar kare iyalinshi, duk da abinda ya faɗan gaskiya ne. Amman dake a hasale suke da Iyabo shi yasa maganar take ƙoƙarin zama babba. Dama ƙiris suke jira ta kuskure su dirar mata a wuya, sabida tsantsar ƙiyayyar da suke nuna ma Iyabo wacce har idanuwansu suka rufe wannan ƙiyayyar tashafi ɗan uwansu gudan jininsu Gwadabe. Harisu wanda ya kasance wa ga Gwadabe, ƙani ga Hambali, ɗa na uku a wajen mahaifiyarsu yace. "To ita shafaffiyar da mai bamu da matsayin da zata iya fitowa ta ba Yaya Hambali da Yaya Haula haƙuri kenan ko yaya akayi ne Gwadabe?. Nifa na kasa gane wannan baƙin sha'ani naka da iyalinka kanka kalau yake kuwa" Yaya Hambali wanda maganar Harisu ta kasance tamkar zuga a gareshi yace. "Ta fito ta ba da haƙuri kuwa Harisu? alhalin ba ganinmu da gashi take yi ba. Gwadabe ya gama watsar mana da darajarmu a idanunta. Allah wadaranka Gwadabe ka cucemu daka cakuɗa mana iri da Iyabo, ba zamu taɓa yafe maka cutarwar da kayi mana ba." "Ya'isa haka Yaya Hambali dan Allah mana. Wannan maganganun tamkar cin fuskane a wajen Iyabo. Sannan ni banga aibu ko laifin Iyabo dan ta kasance Beyerabiya ba. Ni da ku, da iyabo duk musulmaine,kuma duk mutanene Allah ɗaya muke bauta ma, kuma kamar yadda muke sallah, da azumi haka take yi itama" Azabure Hambali yayi kanshi a zafafe yana shirin dukan ƙirjinshi. Harisu ne yai musu iyaka ta hanyar shiga tsakiyarsu dukan ya sauka tabb a tsakiyan gadon bayan Harisun tsabar zafin dukan saida ya gantsare. Jikin Yaya Hambali har rawa yake yi yana ganin Gwadabe kamar yayi mishi rashin kunyane. Barinma yana ganin Gwadabe tamkar shi ya tsugunna ya haifeshi tsabar girme mishi da yayi. Mutum huɗu ne a tsakaninsu kafin Gwadabe. Akwai Yaya Halima wacce ta kasance itace Babba a cikin ummansu, sannan shi Yaya Hambalin, ga Harisu, sannan ga ɗan Fodiyo, ga Sukairaju. Shi Gwadabe daga shi sai Da'u, daga Da'u sai Zakari, sai ƴar Auta Sauwama." Shi kanshi Gwadaben har cikin ƙoƙon ranshi baiji daɗin yanda yayi ma Yaya Hambalin ba, ko babu komai ya girme mishi, kuma shine makwafin uba a garesu baki ɗaya, gashi cikin ummanshi. Yaya Hambali ya bauta musu sosai, kasancewar tun suna ƙananu Allah yai ma mahaifinsu rasuwa. Shi ya maye musu gurbin uba, shine noma, shine kiwo, Fataucin dabino kuwa shi ya gaji mahaifinsu, yayi musu dukkannin wani gata har Allah ya cicciɓesu suka kai matakin mallakar hankali da girman jiki, dana haihuwa. "Lallai Gwadabe baka da hankali ba'acikin hayyacinka kake ba, matarka da danginta sun gama mallakeka, imma ka yarda, imma ka ƙaryatani, tunda ka soma sa'insa damu shingin duka ya rage.Yaya Hambalin kake mayarma da magana?" Cewar Ɗan Fudiyo wanda ya cike da mamakin ɗan uwan nasu Gwadabe" Yaya Hambali kuwa tsai yayi yana kallon Gwadabe, tare da ƴan uwanshi da suka dira mishi a ka, kowa na tofa albarkacin bakinshi a kan abunda matarshi Iyabo ta yi, da abunda ya aikata yanzu. Gabaki ɗaya Gwadabe sai ya dibibice, kasancewar ba halinshi bane raina na gaba an yi mishi wannan kyakkyawar shaidar sosai. Ya fusata ainun ne da yanda suke cin zarafin iyalinshi ba dare ba rana, ba tare da ta yi musu laifin zaune ba, balle laifin tsaye. ana cikin haka Sai ga Iyabo ta ƙaraso wajen a kidime, jikinta har rawa yake yi dan tasan Gwadabe ba karamin ruwa ya kirawo mata ba" Iyabo:. Tunda Gwadabe ya fito jikina yake ɓari, domin nasan danginshi kab ba ƙaunata suke yi ba, kuma ƙiris suke jiran kuskure na. Sai gashi yau azal ta hau kaina. Daman daren jiya cike na kwana da fargabar zuwa ƙauyansu Gwadabe da zamu je yau biki. Ina tsoron Allah ina tsoron abinda zai haɗa taron biki, ko suna a ƙauyensu Gwadabe ace kuma zanje nima. Ina muzanta, da takura fiye da tunani. Furucin da Gwadabe ya fesarma da Baban Nazifi ya fi firgitani fiye da dalilin rikicin. Ba shiri na buɗe labule na fito ina tura tsohon cikina gaba. Saye nake da leshi riga da zane. Rigar ɗinkin buba, zanin kuma ciki da alako irin ɗinkin yarenmu kenan. Idanu mu ka haɗa da Gwadabena tausayinshi ya sake dirarmun a zuchiyata, har nake jin ko ratayeni danginshi zasu yi, ni da Gwadabe mutu ka raba. Dan shi ɗin cikakken jarumin masoyine na haƙiƙa tunda ya aureni bai sake samun kwanciyar hankali da salama ta ɓangaren iyaye da dangi ba. A zamantakewata dashi kuma haƙiƙatan bai taɓa yi mun wani abun ashsha ba, riritani yake yi, gami da tarairayar zuchiyata tamkar ƙwai, hakanne yake ƙaramin ƙarfin zuchiya da jumurin shanye duk abinda danginshi suke yi mun. Sai dai irin zaman bashi da daɗi, yana raɓa rayuwata da dukkannin farin cikina. Damma Gwadabe na ƙoƙarin sharemun dukkan hawayena. Dan Allah Baban Nazifi kayi haƙuri. Umman Nazifi dan Allah ki gafarceni wallahi bansan kina cikin banɗakin bane, ban watsa miki da ganganba" Na faɗa ina mai ƙoƙarin haɗiye kukana tare da shanye fishina. Idanu Gwadabe ya lumshe mun cikin sigar ban haƙuri, nima nawa idanun na lumshe mishi cikin bashi amsar shima yayi haƙurin. Idanunshi ya rufe ya buɗesu tare da ɗan zare su, halamar ya samu sassauci a zuchiyarshi. Dukkan wannan maganar kuramen masoyan dake gudana a tsakaninmu babu wanda yasan me muke nufi, amman dai suna kallonmu, idanun kowa a kanmu yake. "Ke Iyabo kar ki sake zubar mana da kashi ta magudana, nan ba gidan yarbawa bane, dama ku yarbawa a cikin ƙabilu wama ya kaiku ƙazanta, da ɗaukar kashi ba abun ƙyama ba?. In banda ƙazanta yama zaki zubar da kashi ta magudana. Mu dai ana cutar damu da wannan kafirar ƙazantar ta yarbawa." Cewar Gude matar Yaya Sukairaju Kenan. Dama tafi kowa tsanata da caccaɓa mini maganganu kaifafa. Na ji zafin abinda ta faɗa a kan yarbawa, dan ina kishin yarena ina kuma alfahari da kasancewata Beyerabiya." "Gwadabe da mun dawo daga Takai biki ka tattare matarka da ɗanka ku bar mun gidana, na gaji da ganinku dukkanku." Da sauri na dubi Gwadabe, shi kuma ya kalli Baban Nazifi. Ba mu kaɗai mu ka jijjiga da furucin Baban Nazifi ba, sauran yayyen Gwadabe da matayensu, harma da yaransu wanda suke fahimtar abunda akeyi sai da su ka girgiza. "Haula mu je ki sake kayanki mu kama hanya banso takwas ta yi mun a gida ba. Sukairaju ku kama hanyar tafiya muma yanzu zamu kama hanyarmu" Take kowa ya watse ya barmu jijjunanmu a sanyaye sosai. Hannuna Gwadabe ya ja a hankali mu ka koma ɗaki. Muna shiga na zauna a kujera daɓas sai da kujerar ta yi ƙara kasancewata mai ƙiba da ɓaka_ɓakan mazaunai. Kuka mai gunji na fashe dashi. Gwadabe ya zauna a kusa dani ya dafe kanshi da hannu bibbiyu, idanunshi yayi jawur. Ya kasa furtamun kalma sai tubka da warwara kawai yake yi, tare da neman tudun dafawa. Mu da mu ke cin abinci da wuya ta ina zamu iya kama hayar muhalli? Dama dai burin dangin Gwadabe su ga mun tagayyara ne yau na sake tabbatarwa. "Ki yi haquri Iyabo da duk abubbuwan da kike gani, kike ji, da wanda zaki sake ji in mun tafi Takai. Ina mai ƙara baki haƙuri kuma ki sani ni Gwadabe ina tare da sonki, ina sonki Iyabo fiye da son da uwa take ma ɗan cikinta. Ina mai baki haƙuri Iyabo bisa abinda dangina da naki dangin suke yi miki duk sabida Aurenmu. Ina alfahari da soyayyar da ni Gwadabe nake yi miki. Wallahi Iyabo kece sanyi da farin cikin ruhina. Ki share hawayenku mu kama hanyar Takai Sukairaju ya ɗakko mana bus zamu tafi baki ɗaya." Hawayena na share jikina a mugun mace murus, kalaman Gwadabe sun kashe mun jiki. Haƙiƙa Gwadabe na yi mun soyayya mai yawan gaske. Amman ko ƙafar inda nake son shi bai kama ba, gashi a kullum zuchiyata sake jarabtuwa da Gwadabe take yi. Gwadabe yanzu in Baban Nazifi yace mu bar mishi gidanshi wanne tudu zamu dafa, ina zamu bi mu ga haske? Ka duba ka gani abinci da ƙyar muke ci. Wanke_wanke da sharar da nake zuwa yi albashin nera dubu biyu ne a wata, kuɗin ba yawa bane dashi. Kai kuma ba ko da yaushe oganka yake samun lodi ba balle mu samu ɗan kuɗin sallamar iyali da ake baku. Gwadabe ya zamu yi dan Allah?" "A'a Iyabo Allah zai yi mana mafita. Zamu tattauna maganar a gaban Babala in mun je Takai. In ta goyi bayan Yaya Hambali kan mu tashi mu bar mishi gidanshi. Ba makawa zamu tashi duk da nasan bani da ko ficikar da zan iya kama mana haya. Dukkanmu a ƙasanta mu ke tunda ita ta haifemu, kinga tsohon ciki gareki damuwa da kuka ai ba naki bane ƴar yarbawata. Oh Allah yayi ba Debisi bane mijinki, ni ɗin dai da basa so ni na yi sa'ar samun ki, Alhamdulillah. Ko mutuwa na yi nasan na zaɓarma yarana uwa ta gari, ba zasu tuhumeni ba." Dariya nayi harda ƙyaƙyatawa, shima dariyar yake yi. Muka shiga tuno gwagwarmaya da muka sha kafin mu kawo wannan matakin. Duk da dai har gobe tsugunne bata kare mana ba. Tuni nasa ƙafa na shure matsalolin dangin Gwadabe na miƙe na shiga ciki dan ɗakko mana jakar kayanmu. Toye yana kwance sai baccinshi yake yi a shirye yake tsab. Mayafi na ɗauko na jawo ƙaramin akwatin kayanmu da jakar kayan Toye. Ni banso tafiya ma dashi ba naso in Kai shi gidanmu, sabida nima fama nake da kaina cikina wata bakwai amman girmanshi yasa ake mun kallon haihuwa ko yau ko gobe. Toye shekararshi shida da haihuwa sa'anninshi na gidan duk sun shiga makarantar islamiyya mu bamu da kuɗin saka shi a makaranta, in yaje ma ana koroshi kuɗin laraba, inna samu ko ni ko Baban sai mu biya. Amman da zaran laraba tayi bamu biya ba ake koroshi, sai Gwadabe ya yanke hukuncin ni na dinga koya mishi Abacada, Gwadabe kuma yana koya mishi baƙin arabic. Shigowa yayi ya saɓa Toye a kafaɗarshi ya zari akwatin kayanmu. "Zaki iya ɗaukan jakar kayan Toye ko in kai wanna in dawo?" Murmusawa nayi na ɗauki jakar kayan da jakar hannuna, na bi bayanshi. Gaba su ka yi, ni kuma na tsaya na kulle ƙofata na biyo bayanshi. Da ƙyar fa nake tafiya gashi duk na yi kumburi, ga hawan jini na masu juna ina fama dashi. Ko da muka fito, sai muka tarar Bus ɗin ta cika duk sun ɗaura yaransu a kan kujerar sun babbake. "Motar ba zata isaba Gwadabe abinda za'ayi ku je ku hau motar haya zaifi." Cewar Sukairaju yana gama faɗar haka suka ja motar fu, Bus ɗin na gaba motar Baban Nazifi na biye, kana motar Harisu ta rufa musu baya. Yawu Gwadabe ya haɗiye muƙut jijiyoyin kanshi suka fito raɗa_raɗa. "Mu je tasha Iyabo" A daƙile yayi maganar. Ni kam ina biye dashi ko gani bana iya yi sosai tsabaragen tashin hankali da damuwa. Shikenan na yi sanadiyyar raba kan wannan zuriyar masu son juna da son zumunta? Gwadabe tunda ya aureni ya zama saniyar ware a dangi. Ina jin rashin daɗi da na zame mishi silar zama mujiya a cikin dangi. Har mu ka isa tasha banji Gwadabe ya ce komai ba, hakan ya sake damuna ainun gashi muna hanya babu damar in rarrasheshi ko zai samu ɗan sassauci. Ga wani ruguntsumin ma yana jiraye damu a Takai. Mota ya sama mana Bus ni da shi ne a can baya ta ƙarshe wajen window, Toye yana rungume a jikinshi yana baccinshi. Yaron na ƙura ma idanu ina mai cike da tausayinshi da abunda yake cikina ta yanda zasu rayu cikin rashin gatan dangi ɓangaren uwa da uba, Toye ko cikin yaran gida ya shiga bashi da damar yin wasa dasu, yaran zasu shiga yi mishi waƙar da iyayensu suka saba rerawa a tsakar gidan. Suna tafi suna cewa Yarbawa masu kwalo_kwalo da ɗuwawu suke tuƙin tuwo. Toye sai yai ta kuka abunka da yarinta, wataran ma da gudu yake dawowa ya faɗa jikina. Ta bangaren dangina ma suna adawa da aurena da Gwadabe sosai da sosai kasancewar shi Bahaushene ba Beyerabe ba. Rabon ƴaƴane da ƙudurar Allah ya tabbatar da aurena da masoyina Gwadabe. "Tunanin me kike yi haka Iyabo mai zurfin gaske. Kaddai akan furucin Yaya Hambali ne akan mu bar mishi gidanshi? Iyabo ni kaina inaso mu tashi a gidan ba tun yau ba. Ko dan kema ki samu yancin yin rayuwar ƴanci irin wacce ko wacce mace take fatan samu. Na yi imanin dangina ba zasu zo har gidanki su takura miki ba, ko zasu takura miki ba kamar in gidanmu ɗaya ba. Ni da na zame musu dole zanyi zumunci dasu..." A'a Gwadabe wannan ba zai ma yiwu ba. Babala ba zata bar Baban Nazifi ya tozartamu ba. In muka bar gidannan ina zamu shiga a ina zamu dinga samu kuɗin da zamu biya haya? Sannan yarannan zasu sake rasa dangin mahaifansu ta dukka ɓangarori biyu. Amman in dai muna taren a gida ɗaya su Toye zasu taso da sanin lallai su Nazifi ƴan uwansu ne danginsu ne, a gida ɗaya akayi tarbiyyarsu. Kar ka mance Babala ma burinta kenan ganin kun haɗe kawunanku da na iyalinku baki ɗaya. Ka yi haƙuri da batun tashinmu,madamar ba Babala bace ta goyi bayan Baban Nazifi akan tashin namu ba. Kasan sai ka ƙara mun baƙin jini a wajen danginka" Idanu ya lumshe kawai sai girgiza kanshi yake yi. Ɗan guntun siririn hawayen daya surnano mun na yi maza na share gudun kar Gwadabe ya buɗe idanunshi ya ga zubar hawayena. Har Bus ɗinmu ta cika muka fito daga tasha bamu sake magana ba. Ko wanne cikinmu aikin tubka da warwara kawai yake yi a zuchiyarshi. Motarmu sai gudu take shararawa bisa titi, tun muna wuce titinan cikin gari muna wuce manyan gidajen sama, da manyan shopping mall har mu ka soma wuce ciyayi da fasassun kwalta, jagab_jagab ɗin hanya ne yasa Gwadabe yai ta mun aikin sannu har muka shiga cikin ƙaramar hukumar Takai. TAKAI TA KAWO TA SABA DA SAUKAR BAƘI Takai ƙaramar hukumace take jihar Kano. Yanki ne wanda Allah ya albarkace shi da ruwan sama a sanadiyyar hakanne mutanen yankin su ke noma da kiwo da kasuwanci gashi Allah subuhanahu wata ala ya albarkaci garin takai da bishiyun dabinai masu yawan gaske, dabino ya wadaci jama'ar Takai sosai mota_mota ake fita da dabino domin kasuwancinshi. Garin Takai yankine wanda ya yi nesa da birnin kano da tsawon kilomita 80, yayi kusa da yankunan ƙasar Bauchi, yankin da yake yawan kawowa ƙasar kano farmaki a lokacin sarkin kano (Babba Zaki) Sanadiyyar hare_haren da yake yawan kaima birnin kano, Sarkin Kano Babba Zaki ya yanke shawarar a kafa ƙasar Takai, kuma ayi ganuwa a garin. Hakanne yasa ya tura mayaƙa domin su zauna a garin. Bayan an kafa dausayin yaƙi a garin Takai, Sarkin Kano Babba Zaki ya gina gidan sarkin kano a garin Takai kuma ya so ya koma garin Takai ɗin da zama." Muna sauka daga mota mu ka hau mashin ya wuce damu Unguwar Dibinai unguwa mai dogon tarihi kenan a garin na Takai. Dai dai ƙofar gidansu Gwadabe acaɓanmu ya tsaya, ƙofar gidan cike maƙil da maza, mata kuma sunata shige da fice. Bara'u Abokin Gwadabe ne ya tarbeshi da fara'arshi, yasa hannu ya amshe Toye ya rungume. "Madam Iyabo barka da isowa tsuntsun soyayya" Dariyar dole na yi mishi, dan muddun muka haɗu dashi sai ya furta wannan suna daya raɗa mana. Bara'u barka dai da gida, ya yara da Sakinar?" Dariya yayi yace. "Sakina tun safe tana cikin gida sun zo taya aikin biki. Yaran naku ma zaki gansu a ciki" Ɗan murmusawa nayi, Gwadabe ya dubeni yace. "Iyabo ki shiga ciki, zan gaggaisa da ƴan uwa da abokan arziki. Gasu Yaya Hambali can a ƙarƙashin bishiyar dabino suma " To shikenan sai mun haɗu, ka kawo akwati da jakar to" Dan nasan matsawar ban karɓa ba da ƴan uwanshi sun ƙilla ido suka ga akwatinan a hannunshi to zan sha habaici da maganganun banza" Bara'u yace. "Bashshi ki yi fama da kanki, yara zasu shigo miki dashi" Gwadabe yace. "Kaima ka faɗa mata, da ba dan bikinnan ya zame mata dole zuwanshi ba, ai da bama zata yi doguwar tafiya da ciki haka ba, baka ga wuyar da tasha a hanya ba wallahi. Bikin Auta guda in bata zo ba kai kasan akwai ƙura" Ni dai a wajen na yi shigewata cikin gidan na barsu a tsaye suna tattaunawa, Gwadabe bashi da aminin daya shallake Bara'u a wajenshi, tare suka taso, su kai wasan ƙasarsu, har shayi tare akayi musu. Komawar Gwadabe Cikin birni bai rage amintakarsu ba sam, dan Sakina matarshi tasha zuwar mana ita da yara, sai su fi sati biyu. Nima dolena in na zo Takai a gidan Sakina nake sauka. Zuwana na ƙarshe wanda daga shi ban sake zuwa ba sai yau ne kawai Babala tace bazan sauka a gidan Sakina ba, a cikin gida zan zauna, kuma ta kafa dokar ta haramta mun zuwa gidan Bara'u in kwana, ba dan komai ba sai dan a sake ƙuntatani. Gwadabe:. "Gwadabe lafiya irin wannan ramar da kayi haka?" Cewar Bara'u wanda ya kasa haƙuri sai da ya ja Gwadabe gefe dan su ɗan zanta,bayan ya bi mazan dake ƙofar gida an gaggaisa. Gwadabe ya girgiza kai yace. "Wallahi Bara'u kai kasan komai al'amuranne sai godiyar Allah kawai. Kasan in akace maka magidanci bashi da cikakkiyar sana'ar kanshi dole hankalinshi bazai kwanta ba. Karen mota nake yi har yanzu dai daka sani. Amman muna sa ran za'ayi mana freedom da yardar Allah muma a bamu mota, in hakan ya tabbata za'a samu sauƙi. A hakanma ban fa zauna ba, buga_buga akeyi babu dare bare rana, muddin akace maka safiya ta yi, to fa in na fice duk abunda na samu yi nake yi. Nine kwashe shara, nine kwashe kwata, nine bin masu Bus na zuwa unguwanni ina karen mota. Kaga duk sana'oene na cin abinci kawai, abincinma bafa sau uku a rana ba. Duk ranar data carke wallahi sai dai in tura Iyabo gidansu ita da Toye dan su samu abunda zasu kai bakin salati, haka iyayenta zasu ci mata mutuncinta in taje musu, to amman ni hakan yafi mun. Ni kuma haka zan wuni neman aikin yi. Babban abunda yake sani cikin juyayi shine a wannan halin da muke ciki ko Bara'u? To Yaya Hambali, da su Sukairaju, Fodiyo, Yaya Harisu kai dukkansu. Su a wadace suke da abinci, dan Yaya Hambali kullum da nama ake miya a tukunyarshi. Ni kuma na sama raina in yinwa ita zata zame mana ajali ni da iyalina sai dai mu mutu. Bara'u bazan sake tambayar tallafi ko taimako a wajen kowa ba. Wulaƙanci wanne ne ni Gwadabe ban gani ba? Yanzu nan yau Yaya Hambali yace mu tattare yamanu_yanamu mu bar mushi gidanshi. Dan kawai Iyabo ta watsa ma Yaya Haula ruwan kashi ba tare da saninta ba, fitintinun gidan kaɗai ya'isa yasa in yi rama wallahi." Mrs Bukhari ce Sai mun kasance a cikin wannan kayataccen labarin mai ɗauke da dumbin darasi. Tafiyar tana da tsayi sosai. Ku shirya tsab kafin fitowata Inanan tafe ba da jimawaba in sha Allah 👍🏻 https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm NAMA YA DAHU.. ROMO ƊANYE GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI Lamba ta biyu Gwadabe:. Numfashi ya ja, tare da jin wani irin turirin zafi a zuchiyarshi. Yana mamakin yanda ƴan uwanshi suka juya mishi baya sabida Iyabo. Bara'u ya ja ajjiyar zuchiya yace. "Wannan ja'iba har yanzu barta ta wuce ba Gwadabe?, Aure sama da shekaru shida, ga rabo a tsakani har yanzu basu sauke aƙidarsu akan Iyabo ba? Naga ma ana wanke Arniya a aureta ba tare da ta bar arnancinta ba, kuma addini bai haka hakan ba, ballantana Iyabo wacce take musulma gabanta da bayanta. Shawarata anan Gwadabe shine ka yi haƙuri ka ba Yaya Hambali haƙuri kuci gaba da zama a ƙarƙashin inuwar dukiyarshi. Kuma nima na mara maka baya kar ka sake ka nuna musu ka gaza akan iyalinka, gara ka dinga turata gidan nasu duk wulaƙancin da zasu yi muku. Gwadabe kai mutumin kirki ne sosai, bana mance alkhairanka gareni. Bazan mance ba lokacin kana samu kai ka biya mun sadakin Sakina, ka siyo mun turamen zani har guda biyar aka zuba a famtimoti banda abubbuwa da kai ta binmu mu abokanka dashi na alkhairi. Kai kayi silar fitan Tamu gada cikin garinnan na Takai ya shiga Kano. Ashe hanyar arzikin nashi kenan yanzu ina Tamu? Yana Habuja shi da iyalinshi, sun samu rufin asiri sosai. Allah bazai hofantar da mutum irinka ba, matsawar kaga ka roƙi arziki Allah bai baka ba Gwadabe ka ɗauka cewar arzikin ƙila ba alkhairi bane a gareka. Kar in cikaka da surutu gara ka shiga ka samu Iyabo, wala Allah dangi su sassauta daga tsangwamarta in suka ga kaifin idanunka." Hannu yasa a ajjihu ya zaro nera dubu uku ƴan muttala_muttala ya tura a aljihun koɗaɗɗen jeans ɗin Gwadabe. "Ka ba Babala gudunmawarka basai kace mun baka dashi ba, ta nuna a jikinka." Hannunshi ya ja suka nufi cikin gidan. Gwadabe sai murmushi yake yi gami da yabon ƙoƙari na Aminin nashi a kanshi. Jifa_jifa Bara'u na yi ma Gwadabe aiken gyaɗar miya, da shinkafa ƴar hausa. Abunda yake nomewa kenan, kuma ƴar gonar tashi ba wata babbar gona bace ga hidindimu masu tarin yawa a kan nashi. Iyabo:. Ƙafafuna har rawa suke yi wallahi dana ɗora ƙafata a cikin gidan. Da Yaya Halima na soma cin karo ta tawo ita da ƙawayenta, taci kwalliya, da halamun rakiya zata yi musu. Dariyar dole na ƙaƙaro nace. Yaya Halima rakiya zaki yi ne. Ina wuni? Na furta da hausar bakina irinta yarbawan da suka ƙware a yaren Hausa. Dan babu kalmar da take bani wahalar furtawa sai dai nakan furtatane da irin Hausar bakina. Harara Yaya Halima ta doka mun, ta ƙura ma titsetsen cikina idanu ƙur. Tsaki ta ja mai ƙarfi suka wuce ni ita da ƙawayenta fuu. Jikina ya sake macewa mus, da jan ƙafa na ƙarasa shiga babban gidan nasu mai ƙofofi huɗu, ko wanne shiyya da ƙofarshi, amman gidan gabaki ɗaya a haɗe yake, ƴan uwane dangin juna da yaransu da jikokinsu a cikin gidan. Babban wan mahaifin su Gwadabe shi ya tara kan wannan dangi a waje ɗaya, kasancewar mahaifinsu Allah ya albarkaceshi da yawan yara (kakan su Gwadabe kenan). Su rai Talatin da uku mahaifinsu ya haifa, matanshi biyu rak. Sai wan mahaifinsu Gwadabe yaji bari ya haɗe kan ƙannenshi su zauna waje guda domin ƙarfafar zumunci. Irin abinda Babala tayi kenan akan Yaya Hambali daya haɗe kan ƙannenshi waje guda suke rayuwa gida ɗaya. Su Baban Nazifi da su Sukairaju kowanne cikinsu yana da ɗakinshi da yake sauka in sabgar biki ta kawomu, akwai katifu da labuleye a ɗakin. Gwadabe ne kawai bashi da ɗakin sauka in mun zo. Hakan ya farune sakamakon ni ya aura ƴar ƙabilar Yoruba bai auri ƴar ƙalibarsu ta Hausa fulani ba. Ina shiga shiyyar Babala naci karo da su Yaya Haula, da Sawaiba matar Harisu, dasu Gude sune ƴan gaba gaban murhu anata tuƙa tuwon jama'ar biki. Duk suka kalleni suka watsar, nasu kam ai na daɗe da sabawa. Ko da nayi sallama ɗaiɗaikun mutanene suka amsani, suma baƙine da suka shigo daga wasu ƙauyukan dan taya iyalan wannan gida murnar biki. A sanyaye na gaishesu har zan wuce Yaya Haula tace. "Ai kamata yayi ki ci ɗamara da mayafinki ki zo ki tuƙa mana tuwonnan yayi sumul kamar Amala, kinsan dai a gidan surukai kike. Cijewa nayi nace mata. To bari in gaisa da su Babala sai in zo Yaya Haula" Shikenan iyakar abunda nace, Sai kawai Gude ta daka tsalle tace. "Lallai Iyabo wuyanki ya isa yanka sosai. Gwadabe ya ɗaure miki kugu sosai. Ke har kina da ta cewa a cikin zuriyarnan, ɗorin dosono dake? Ai da gidanku kika je bikinku na kwalo_kwalo dole ki zage kici aiki dama yarbawa ba'a sanku da hutu ba sai wahala" Hawayen da suke shirin zubo mun nayi saurin mayarwa dan hango Babala tana nufomu. Tana ganina ta zabga mun harara mai muni. Babu shiri na zube a ƙasa ko nauyin cikina banji ba. Barka da fitowa Babala" Tsaki taja. " In Kinga dama kin tashi daga wannan tsugunnon naku na gado. Kin shigo garin amman baki iya zuwa inda nake kin gaisheni ba, balle matan yayyena da ƙannena su ci albarkacina a matsayina na mahaifiyar Gwadabe. Sai da kika ganni zaki wani zube a ƙar, ai ni na ɗauka ba zaki barshi yazo bikin ba ma." Hawaye take ya tsinke a idanuna ya soma zuba shar_shar_shar, in furta kalma na kasa, in ɗago in bata hakuri na kasa bakina yayi mun nauyi ainun. "Haula menene yake faruwa nake jiyo hayaniyarku ne?" Babala ta faɗa cikin ɓacin rai. Abinda Yaya Haula take jira dama kenan ai kuwa sai cewa tayi da Babala. "Ce mata fa nayi tazo ta tuƙe mana tuwonnan yayi laushi irin nasu yarbawa. Shine ta nemi faɗa mun magana Babala, so take ta fake da ciki ta ƙi yin aiki. Lokacin bikin Rahina ma haka ta kwanta jinya ko tsinke taƙi ɗagawa. Ko a can Kano Gwadabe shi ke mata har shara da wanke_wanke, balle kuma wanki da wankan Toye" Baki Babala ta riƙe tana jijjiga kai kawai. "Ba shakka ashe har yanzu Yarbawa suna da baƙar zuchiyar yin agumu. Abunda na dinga jiye ma Gwadabe kenan yaƙi ganewa sabida tun ana neman aka gusar mishi da hankali. Ai sunan Gwadabe ya daɗe a hannun Baba lawo ( Bokan yarbawa)" Hawaye kawai nake zubarwa rana zafi inuwa ƙuna. Ana cikin wannan ruguntsumin Gwadabe ya shigo yana rungume da Toye ga jakar kayanmu yana ja, Bara'u na riƙe da jakar kayan Toye. A tsaye suke suna gaisawa da dangin Babala, amman hankalin Gwadabe na kaina yanda yaga ina tsiyayar hawaye gani a gurfane. Ba shiri ya iso inda muke. "Babala lafiya meke faruwa haka? Iyabo ke ba likita ya hanaki tsugunno ba, tashi tsaye" Ya faɗa a sanyaye. Babala ta sauke gwauron numfashi ta dubi Gwadabe tace. "Babu shakka Gwadabe, sannu me mata. Wato likita ya hanata tsugunno a tsaye kake so ta gaisheni kenan ko marar albarka? Yayi kyau ai ku sha kuruminku komai ma ya kusan zuwa ƙarshe da izinin Allah" Tana faɗar haka ta wuce fu tana share hawaye. Bansan me akayi mata har da zai sata zub da hawaye ba. A kullum naga Babala na kuka akanmu tsorone yake sake shigata dan kukanta a wajen Gwadabe babbar musibace wacce ko arziki bazai bari yayi ba. Gabana ya yanke ya faɗi, take na ji jiri na shirin kayar dani. Me take nufi da komai ya kusan zuwa ƙarshe to? Ko so take Gwadabe ya rabu dani kenan ya auri Bahaushiya ƴar uwarshi?. A baya haka Babala ta tursasa Gwadabe sai da yai mun saki ɗaya. Sakin daya sake rura wutar rikici tsakanin dangina da dangin Gwadabe kenan, wannan saki ba ƙaramin ta da zaune tsaye yayi ba. Dan Iya Debisi da Babala sai da suka kusan raba abun faɗe a layi. Har an kwashe mun jerena har ga Allah ko ni a wancan lokacin na haƙura da Gwadabe. Allah ne yayi shan ruwan aurenmu bai ƙareba ina dawowa na samu wannan ciki." "Tashi daga tsugunnon Iyabo ki shiga ciki ke da Toye ki huta. Zan je in nemo miki abunda zaki iya ci, ko in sa Sakina ta yo miki" Da ƙyar na miƙe tsaye ƙafafuna sun yi tsami ainun. Haula da sauran matan dake wajen duk sai suka riƙe bakinsu akan furucin da Gwadabe yayi. Shi kuwa kamar ya faɗa ne dan ma ya sake cusa musu baƙin ciki. A'a Gwadabe kar ka nemo mini wani abuncin. Duk abunda na samu zanci, ai jikin nawa da sauƙi." Hannu nasa na sauke Toye daga kafaɗarshi. Ya miƙo mun jakar hannun Bara'u na rataya. Jakar kayanmu kuma nace ya tafi mana da'ita gidan Bara'u tunda acan yake sauka mafiya yawan lokuta. Ina tafe ina jan ƙafata. Sai kallon banza aketa watsomun, harda masu tsaki, da tofar da miyau. Duk inda naga taron mata sai na gaishesu zan wuce, kuma fa saina rusuna mu a al'adarmu akwai wannan tarbiyyar. Wasu su amsa ciki_ciki, wasu ba sa amsaba a haka har na isa ɗakin Babala. Cike dam ɗakin yake da ƙannenta da yayyenta. Yaya Halima ma ta dawo daga Rakiya tana zaune tana cin tuwon shinkafa miyar kabewa sai ƙamshin man shanu take yi. Laila na zaune a kusa da'ita ta ci ado sosai, sai wani hararata take yi. Ina shiga na zube a ƙasa ɗaya bayan ɗaya na dinga binsu da gaisuwa, har Laila dana girma ban bari ba sai da na gaisheta. "Sai ki tashi maza ki shiga cikin surukan gidannan ki kama aiki, baki ci ta zama ba" Cewar Baba Iyatu ƙanwar Babala. Miƙewa nayi ina shirin fita na jiyo Yaya Halima na cewa. "Ki tafi da ɗanki babu wanda zai kular miki dashi" Yaron na kalla yayi tsuru_tsuru kamar ba dangin mahaifinshi ya shigo ba. Duk ƙin Gwadabe da dangina suke yi bai shafi abunda muka haifaba sam, amman banda dangin Gwadabe. Hannun Toye na kama muka fito tare. Da Gwadabe naci karo zai shigo ni kuma zan fita. "Ina kuma zaki je ke da ba ishasshiyar lafiya gareki ba?" Ban ce mishi komai ba gudun kar in faɗi wata kalma da zata zama lefi. "Aiki zata je ta kama ma su Haula. Ko su zasu girka mata abinda zata ci ne rasa kunya?" Cewar Baba Iyatu. Da sauri na wuce shi ina murmushi wanda yafi kuka ciwo. Shi kuma ina jiyoshi yana musu bayanin hawan jini ne dani, kuma likita ya hanani yawan aiki da zurga_zurga. Ni dai gaba na ƙara dani akaita hada hadar girki har sai da muka gama na zauna a kan turmi ina ba Toye abinci a baki. Sakina ce ta iso inda nake da fara'arta. Nima cikin fara'a na tarbeta. Kwanon hannunta ta ajjiye a gabana. "Maman biyu ga farfesun kifi Gwadabe yasa nayi miki. Yace shi kaɗai kike iya ci ya zauna" Ɗan murmushi na ƙaƙaro na dubi Yaya Haula bata kallonmu amman kunnuwanta yana wajenmu. Kai Sakina sai da ya saki wahala? Kinga ga tuwo nan ma ina jira Toye ya ƙoshi ne sai in cinye ragowar, jikin yanzu da sauƙi" Da sauri Yaya Haula ta yi ɓangaren Babala na yi imani wata fitinar zata je ta kunno mun. Ɗakin Goggo Innawo mu ka shiga, ita Goggo Innawo ƙanwar mahaifiyar Sakina ce a gidan take aure. Anan naci kifina muna hirar yaushe gamo. "Oh Iyabo ashe rabon ƴan biyu ne ya dawo dake ɗakin ki. Irin rikicin da akaita tayi babu wanda ya zaci aurenku zai dawo, sai gashi har da cikin ƴan biyu" Dariya nayi nace. Sakina kinsan duk abinda ya samu bawa da sanin Allah. Shan ruwan aurenmu ne bai ƙare ba. Duk rikici in Allah ya riga ya ƙadarto a dakin Gwadabe zan ƙare rayuwata, babu tsumi babu dabara ga duk waɗanda basa son tarayyyarmu. Ni aurena da Gwadabe ya ƙara mun tsoron Allah, anan na sake gane ƙudurar Allah. Irin badaƙalar da ta biyo neman auren ai me girma ce, amman da yake Allah ya yarda da haɗin ba gamu ba". Sakina tace. "Wannan gaskiya ne. Mu kammu ba mui zaton aurenku zai yiwu ba. Duk da dai Gwadabe yana tsantsar sonki da burin son aurenki. Amman bai samu goyon baya a wajen kowa ba sai Bara'u. Bara'u kuma bashi da ikon zartar da hukunci a kan Gwadabe. Ba da ban Baba Magaji ba da yanzu wani labarin akeyi. Ke dai Iyabo ki ta yin haƙuri wata rana sai labari. Ko wacce mace da irin ƙalubalen da take fuskanta a gidan aurenta, muna barma cikinmu sirrinne kawai. Murmushi kawai nayi ina hango lokacin da Gwadabe yake zuwa taɗi ƙofar gidanmu a idanuna. Tun yana zuwa ana barinshi da dai Iyaa Debisi ta ga abun da gaske ne na riga na kamu da son Gwadabe sai aka hana shi zuwa gida wajena. Ni da Gwadabe sai dai mu haɗu a wajen da nake sana'ar tuyan ƙosai da kafa da daddare a bakin titin unguwarmu. Gwauron numfashi na ja kawai mu ka ci gaba da hirarmu da Sakina. Sai da na huta na yi sallar azahar. Muna yin la'asar kuwa aka aiko yaran gidan wai in zo bakin murhu za'a ɗaura sanwar dare. Faɗan irin wuyar da nasha ɓata lokacine kawai, aikin kusan nice ƙarfin yinshi, sukaita zamewa suna barina. Ga tuwon gidan bikin ƙauye ba tuwo bane na wasa, ni na talga tuwonnan na dinga ɗiba da ƙoƙo ina zubawa a tukunya lamba talatin sai juyawa ruwan zafin yake yi. Bayan na gama talge sai na koma wajen su Zuwaira mu ka ci gaba da wanke kwanukan da aka ɓata da rana. Wanke_wanke ne bana wasa ba. Muna tsaka da wanke_wanken Su Yaya Hambali suka zo wucewa ta wajen. Dukkansu suke tafe harda Gwadabe wanda na ga idandunanshi sun kaɗa sun yi jawur. Duk da magriba ta kawo kai akwai ƙarancin haske. Kallona kawai yayi ya girgiza kai suka wuce zuwa shiyyar Babala. Haka kawai sai na tsinci kaina a cikin damuwa gami da faɗuwan gaba, take sai jikina ya mace murus. Cikin dauriya na iya tsaiwa muka kammala duk aikin daya kamata Gwadabe:. Tunda ya shiga ɗakin Babala, Babala ta tare shi da ruwan faɗa itace harda kukan ta ji labarin Iyabo ta shanye shi, ta mai sheshi Ɗan aikinta. Duk ta hanyar da yaso ya ɓullo mata dan ta fahimci dalilin da yasa yake mata aiki, amman Babala ta fututtuke. Su Goggo Iyatu suma suka ara suka yafa, mai makon su rarrashi ƴar uwarsu sai ma sake zugata da su kai ta yi. "Wallahi Kyauta wannan lefinki ne. Dan wallahi da nine Tanimu ya kwaso mun ƙabila da sunan matar dazai aura. In sama da ƙasannan zata haɗe bazai aureta ba. Ki duba yanda ya shure soyayyar ƙanwarsa Laila fa Kyauta. Da ba dan na kai zuchiyata nesa ba da zumuncinmu ai ya taɓu" ( Kyauta sunan da dangi ke kiran Babala dashi kenan. Babala kuma sunan da ƴaƴa da jikoki ke kiranta kenan) Cewar Goggo Iyatu kenan. Goggo Jummalo tace. "Ai yanzu ma bata ɓaci ba Iyatu. Har yanzu Gwadabe zai iya auren Laila. Tunda har Laila ta iya kaso aurenta domin tana son Gwadabe .Ya kamata a wannan karon ya aureta ko dan dole dan ubanshi a nuna mishi mu muka haifeshi ba shi ya haifemu ba. Wallahi a wannan karon aurenshi da Laila babu wata makawa." Da sauri Gwadabe ya ɗago jin labarin mutuwar auren Laila ba ƙaramin kiɗimashi lamarin yayi ba. Ga wata magana da Goggo Jammalo take faɗe, shi yanzu ina ya ga ta yin aure alhalin abinci ma da ƙyar yake iya kaiwa gidanshi, har yanzu bai soma sana'a a matsyin ogan kanshi ba. Ta yaya ma zai auri Laila? Wannan ma maganace da bata dace ace an ma tare shi da'itaba, duba da irin halin talaucin da yake ciki, da kuma babban dalilinshi na ƙin Lailan a bayan. Da ƙyar Gwadabe ya yakice ya bar ɗakin Babala yana yarfe zufarshi. Yana hanzarin barin shiyyar ya jiyo muryar Laila a bayanshi tana kiranshi. "Gwadabe ji mana dan Allah " Cak ya tsaya bai juyo ba, bai da niyyar juyowar. Sai itace ta tako har inda yake, ta fuskanceshi. "Gwadabe guduna kake yi ne?" Kallonta Gwadabe yayi, tare da girgiza kan shi. "Tayaya zan guje ki kina gudan jinina Laila? Na ga ai mun gaisa ko, ko akwai wani abunne bayan wannan?" Ɗan murmushi Laila ta yi tare da cewa. "Babu komai. Ka ji labarin mutuwar aurena, da musabbabin mutuwar tashi ko?" "Ai kina jiyo duk bayanin da su Babala suke yi mun. Allah ya daidaita tsakaninku da mijinki. Laila in da gaske dan ni kika fito daga ɗakin ki, kin tabka babban kuskuren da zaki jima kina cizon yatsan ki. Sam ni Gwadabe bani da ra'ayin ƙarin aure, lafiya lau muke zaune da Iyabo, bata rage ni da komai ba, ta bani dukkan lokacinta da zuchiyarta. Haka zalika ni ma zuchiyata tana gareta. Ina mai baki haƙuri a karo na biyu." Yana dasa aya ya wuce ya barta da jin kunya. Yana tafe yana mamakin irin ƙiyayyar da su Babala suke yi ma Iyabo, duk da dai shima irin wannan tsanar akayi mishi a gidansu Iyabo. Da dama a cikin gidansu Iyabo basa ko amsa sallamarshi. Bayan sallar la'asar kuma Babala tasa akayo mata kiran kab yaran nata, dan Haula ta tsokata mata abinda ya faru a can gida Kano da safe kafin su tawo. Shine wannan wucewa da Iyabo taga sunyi. Bayan sun gurfana a gaban Babala da Goggo Iyatu, da Goggo Jammalo, da Goggo Takura. Duk waɗannan ƙannen Babala ne, babban wansu Baba Magaji shi yana Maraɗi tare da iyalinshi. Nan Yaya Hambali ya soma yi ma Babala bayanin abinda ya faru, harda ma waɗanda suka wuce. "Babala Iyabo ta gama mallake Gwadabe, shi yake yi mata komai da kika sani. Wallahi Babala har ruwan wanka sai Gwadabe ya kai mata, haka zaki ga ta fito tana kallon su Haula ɗaɗɗaya. Duk abunda Gwadabe ya samu akanta yake ƙarewa tas. Ai kin ganta sai ƙiba take narkawa, shi kuma yana ƙarewa kamar wanda ake lasa. Ni shi yasa nace su bar mun gidana kawai, dan ba ƙaunar buɗe idanu nake in ganta a cikin gidan ba Babala. Tunda har Gwadabe ya soma takamun burki, wataran sai duka. Kafin akai ga hakan gara su tashi kawai, ina da buƙatar wajen nasu dama zan zuba dabino a ciki. Babala irin taɓarar da Gwadabe da matarshi suke yi a cikin gida kare fa bazaici ba. Wallahi sai ki ganshi da gajeren wando yana barbaɗa mata garin Amala ita tana tuƙawa sunayi suna waƙar yarbawa. Wannan baƙin ciki da mi yayi kama" Yaya Harisu yace. "Gaskiya ne gara ya kama mata haya a can nesa damu Babala. Ƙazantar da baka gani ba tsabta ce. Dan wannan yaron baya ko jin kunyar idanunmu, wallahi zaki ganshi a tsakar gida yana wanki tana mishi shanya, wataran har waƙar yarbawa zaki ji suna rerawa abun takaicin ya iya waƙar. Gwadabe ya rasa wacce yake so duk dangi, duk cikin ƙabilunmu na Hausa fulani kyawawa, sai wannan buskutar beyerabiyar ce ta ja hankalinshi." Haka ɗaya bayan ɗaya kowa ya goyi bayan Gwadabe ya bar ma Yaya Hambali gidanshi. Shi kuwa gogan yayi ƙuri yana jiran irin hukuncin da Babala zata yanke. Gyaran murya tayi tare da cewa. "Na ji bayananku kab, kafin ku koma za ku ji hukuncin dana yanke. Zanyi shawara da ƴan uwana, akan batun matarshi kuwa wannan ƙabilar? Alkadarinta ya riga ya kusan karyewa. Ku tashi kuje in Allah ya kaimu gobe zaku ji hukuncin dana yanke" A sanyaye Gwadabe ya bi bayan ƴan uwanshi. Zuchiyarshi cike da ƙuna gami da taraddadin me ka je ka zo. Iyabo: . Sai zuwa bayan isha na samu hutu. Duk mun baje a tsakar gida muna shan iska. Ina kwance akan tabarma nayi matashin kai da hannuna. Toye yana zaune a gabana. Ƴan uwa sai hira da shewa suke ta ta yi abun gwanin ban ƙawa, ni kuwa mujiya na kasance a cikinsu, komai a tsorace nake yinshi, bana son in ɓata ma dai_dai da yaron gidan na goye rai. Ina gani ɗazu yarinyar Asiya matar Lawal tana dukan Toye, babu wanda ya kula. Gashi ba sa'arshi bace dan zata yi shekaru tara da doriya ma. Sai da ta gaji dan kanta ta barshi. Ina kwance barci ya soma dibata Yaya Halima ta zo inda nake tai mun ƙerere a ka. "Mandiya hamshaƙiya sai ki taso ga can kayan miya da su alayyawo zaku gyara, gobe da asuba za'a aza tukunya" Da sauri na miƙe ina faɗin wash dan wani irin ƙara ƙuguna yayi mun mai zafin gaske. Toye na kwantar ya riga ya soma bacci a zaune. Tunda muka zauna zaman aikinnan ba mu bar aikin ba sai wajajen sha biyun dare, sannan kowa ya kwanta. Da asussuba kuwa washe gari muka tashi da aikin tuwo, dan kafin takwas na safiya mun kammala tuwonnan tas mun malmalashi mun jera a fantekoki. Zuwa ƙarfe sha ɗayan rana gidan biki ya cika danƙam da jama'ar biki, sai haya_haya kawai kake ji. Daga waje ma haka ƙofar gidan take danƙam da maza ƴan ɗaurin aure. Yaron Sakina ne yazo ya kirani. "Umman Toye wai inji ummata kizo ki yi wanka" Allah sarki ni Iyabo. Kowa a gidan sai wanka akeyi ana kwalliya, yara da manya. Amman ni babu wanda yai mun ta yin wanka. Bin bayan yaron nayi har zuwa gidansu. A falon Sakina na samu Gwadabe da Bara'u suna zaune suna cin tuwon biki. Ƙur ya ƙura mun idanu, take na ji hawaye na shirin zubo mun, har numfashina na karkatsewa. Fitowar Sakina daga uwar ɗakine ya katse kallon ƙudan da muke ma juna. "Maman biyu tun ɗazu nake ta jiranki ki zo ki karya ku yi wanka ke da Toye, sai mu ka ji shiru kuma" Kujera na samu na zauna duk illahirin jikina babu inda baya yi mini ciwo, kuma babu inda bai yi mun tsami ba, zazzaɓi ne kau a jikin nawa ma, ga jiri da ke damuna. Ke dai bari, aikin abincin bikine bai bani damar zuwan ba. Kinga ko karyawa ma ban yi ba. Bara'u ina kwana ya akaji da taro?" Na faɗa kaina a ƙasa. "Lafiya lau Iyaa Toye Tsuntsun soyayya, ya jiki_ jikin?" Alhamdulillah. Na dubi Gwadabe nace. Ekaro oromi ( ina kwana mai gida?) Ajjiyar zuchiya ya sauke kana yace. "Kin tashi lafiya, ya jiki_jikin naki? Wato kina ta aiki bayan kinsan likita ya hanaki aiki mai wuya ko? Gobe ma kowa zai watse daga yau biki ya ƙare, tunda yau za'a kai Amarya ɗakinta ai" Boyayyar ajjiyar zuchiya na sauke, dan jina nake tamkar a ƙaya wallahi. Zame jiki Bara'u da Sakina su ka yi su ka bar mana ɗakin. Suna fita Gwadabe ya dawo kusa dani ya zauna. "Iyabona" Ya faɗa muryarshi na rawa. Kuka na fashe mishi dashi. Gwadabe na roƙeka da girman Allah ka sauwaƙe mun zuwa taron biki ko suna na danginka. Ba ƙaramin muzanta nake yi ba. Ka ware mana wasu lokutan domin ziyarar danginka, amman ba lokacin wani sha'ani ba." Shiru yayi yana kallona idanunshi suka kaɗa su kai jawur. "Ki ƙara haƙuri bisa wanda kike yi da dangina Iyabo. Nasan kina takura sosai, kuma kina shan baƙaƙen maganganu marasa daɗin saurare. Amman ni ko na so barinki a Kano, kinsan ba yarda Babala zata yi ba. Kuma hakan zai ƙara haddasa wata fitinarne. Iyabo bana son kukan ki, ki share hawayenki gobe da wuri zamu bar Takai ki yi haquri kinji?" Sai na ji tausayinshi ya kuma kamani, ga ɓoyayyar damuwa ina gani shinfiɗe a fuskantar shi, duk da yana ta ƙoƙarin ganin ya ɓoye mun halin da yake ciki. Amman na san Tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi. A hankali na furta. Gwadabe na ganka a cikin damuwa meke damunka, kar kayi yinƙurin ɓoye mun, dan bama ɓoye ma juna damuwarmu. A kai nane ko Gwadabe?" Ajjiyar zuchiya ya sauke, tare da kamo hannayena dukka biyun ya ɗan matsesu kaɗan. Idanu na lumshe ina cike da tsantsar tausayin aurenmu. MRS BUKHARI *DAN ALLAH KUIMUN AFUWA NA SAURARI ƘORAFE_ƘORAFENKU AKAN KU WATA BIYU YAYI MUKU YAWA. AYIMUN AFUWA MU BARSHI A WATA BIYU, NA SAKE TURO WANNAN PEJINNE DOMIN IN MUKA DANNAR ƘIRKI DASHI. NAN DA WATA BIYU ZAKU JINI DA CI GABAN LABARIN NAGODE*🙏🏻🙏🏻 https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm NAMA YA DAHU. ROMO ƊANYE BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI Lamba ta uku "A game da abinda ya faru a gida can Kano ne kafin mu tawo. To da Yaya Hambali, da su Yaya Harisu duk sun amince akan Yaya Hambali ya tashe mu a gidanshi mu yi nesa dashi. To Babala tace dai a barta tayi shawara da su Goggo Iyatu. To kinsan Goggo Iyatu kusan ita take sake zuga Babala akan ki. Sabida Laila ƴar wajenta da Allah bai yi mun yi aure ba kamar yanda suka tsara tun muna tsumman goyo. To kinji abinda ya ɗaga hankalina kenan, tunda nasan bani da kuɗin da zan iya kama mana ko ɗaki ɗaya, balle ciki da falo." Ƙur na zuba mishi idanu. Gwadabe duk abinda Allah yayi a kan mu me kyau ne. Allah ba zai ba danginka ikon tozarta mu ba da ikon Allah. Kayi haƙuri jarumina duk a akaina ake yi ma hakan." Murmushi yayi gwanin tausayi yace. "A tunaninsu matsa mun lamba da zasu ci gaba da yi, shi zai sa aurenki ya sire mun. Billa aurenki kullum sake zame mun yake yi kamar yau aka ɗaura iyabo na. Kema ki ƙara haƙuri wata rana sai labari . Sannan ina da babban albishirin da na cancanci garjejen farin goro ɗan shagamu. Allah ya nufa nima na zama matuƙin Babbar mota na tashi daga karen mota. Ma'ana an mallakamun mota." Sakina ce ta shigo hannunta riƙe da langa da kofin silver ta dure shi a gabana. "Sakko ki ci abinci ki yi wanka mu samu mu koma gidan biki, yau biki zai ƙare Amarya zata kwana a ɗakinta" Godiya na yi ma Sakina. "Gwadabe Bara'u yana ƙwar gida wai kaje ku tafi" Da sauri ya miƙe, mu kai sallama ya fice dan yanzu za'a ɗaura auren ƴar autar tasu. Ni ko a gurguje na karya na yi wanka zuchiyata fal murna na san a ƙalla zamu samu sassauci daga talaucin dake addabarmu. , Sakina ta yi ma Toye wanka. Leshin ankon bikin Bose da mu ka yi wata shida daya wuce na saka. Leshi ne me tsada, dan ko sanda aka fitar da leshin na cire raina da yi, amman Gwadabe sai da ya je ya ciyo bashi yai mun domin ya fitar dani kunyar dangina, leshin ya sha ɗinkin buba da zani, na saka sarƙa fashion me kyau wacce Gwadabe ya siya mun a legas da suka je. Mayafina da takalmina ma sababbine wanda matar Tamu ta aiko mun daga Habuja, da naso in bari sai na haihu in yi fitar suna dashi. Gwadabe ne ya ƙi yarda yace lallai sai dai in sa a bikin gidansu nima in fito da kyau, dan su Yaya Haula suma sun yi ɗinke_ɗinken biki kala uku_uku. Ni kuma bamu da kuɗi leshin da na sa basu san na ɗinka ba, tunda mu ka yi bikin na ɓiyeshi a ƙasan akwati abunka da tattali irin na talaka. Fitowa nayi shar dani har ƴar hoda da jan baki na murza. Toye kuma riga da wandon Atampa na saka mishi da hular ashoke irin na yarenmu. Sakina ta riƙe mishi hannu muka nufi gidan bikin. Ƙofar gidan taƙi wutuwa sabida tsabaragen dandazon maza ƴan ɗaurin Aure, sai maƙota muka faɗa akan in an sassauta ma shiga cikin gidan. Sai wajajen kusan azahar ƙofar gidan ya sarara da mutane muka samu muka shiga cikin gidan. Da Laila na soma haɗa idanu, sai naga ta shiga ƙarame kayan jikina kallo har kirjinta na hawa da sauka irin na tashin hankali. Ni mamakine ma ya kamani. Ban bi ta kanta ba kai tsaye shiyyar Babala na wuce domin in sake gaishesu. Kowa na cikin ɗakin kallona yake yi baki a sake, Yaya Haula kuwa tsabar kallona da ta shagala tana yi sai da ta zuba ruwan miya a ƙafarta mai zafi kafin ta dawo hayyacinta. Koddibuwace babba a jikinta, amman leshina ya tsole mata idanu. Yaya Halima kuwa wuyana take ta kallo kawai. A tsarge na gaggsishesu bi da bi, suka amsa a daddaƙile in da sabo na riga dana saba tuni. Na ɗan zauna jim sai ga Amarya ta shigo ɗakin ita da ƙawayenta su su biyu. Ta tsugunna ta gaisa da kowa amman kallo wannan ban isheta ba. Sauwama Amarya an sha kyau" na ce mata ina ɗan yaƙe. In kun tanka yarinyarnan ta tanka. Abunda ya kawota ta yi ta fice da ƙawayenta. Bayan na zauna kamar na awa ɗaya haka sai na koma tsakar gida, dan naga atana alwalar sallar azahar. Ɗakin ƙanwar mahaifiyar Sakina anan nayi Sallah, mu ka ci tuwo da Sakina, na koma tsakar gida muka shiga rabon tuwo ka'in da na'in. Ban zauna ba sai da aka gama rabon abinci kab tukunna. Zuwa bayan laa'asar kuma dangin ango suka tawo da fantimotin aure, daga nan kuma zasu tafi da Amarya. Ayarin su Asiya na bi mu kai ta fita da kayan ɗakin Amarya ana sakawa a mota. Su Yaya Haula da Zuwaira harda su a ƴan kai Amarya, mutane sai da suka cika Bus guda, sai ƙaramar motar Amarya da ƴan ƙawayenta. Muna shiga cikin gida muka tsaida sanwar tuwon dare ba mu muka nitsa ba sai wajen takwas na dare, sai lokacin na samu kaina na galabaita sosai, marata ciwo take yi mun tun rana haka na kwana da ciwon marar nan. Da sassafe muka kuma tashi da aikin gyaran gida da karin kumallo. Kokko da ƙosai mu ka yi, bayan an kammala karyawa baƙi suka shiga haramar komawa garinsu, sai wanka akeyi. Sai da mu ka yi wanke_wanke muka share wajen tas kafin na samu bokiti na samu ruwan wanka mu ka yi ni da Toye. Gwadabe ne ya neme ni a tsakar gida ya same ni. "Ki hanzarta ki shirya yanzu zamu kama hanyar Kano. Ana mun lodi a mota zamu kai kayan Legas." Ajjiyar zuchiya na sauke nace. A shirye nake ni kam tsab. "To ki shiga ki yi sallama da matan gidan, sai ki same ni a ɗakin Babala" Yana faɗar haka ya juya da sauri. Ni kuma na shiga bin ɗakuna inai musu sallamar zamu koma, har na iso ɗakin Babala na shiga da sallama. Su Yaya Hambali duk suna ɗakin, waje guda na samu na raɓe. Babala dake magana taci gaba da magana. " Kai wannan yaron ka yi haƙuri ka bar Gwadabe ya zauna a tare da ku. Dan ina buƙatar a dinga sa mun idanu akan dukkan motsinshi. Amman ya dinga biyanka haya a shekara, in yaso sai ka kama shago da kuɗin ka dinga tara dabinon naka a ciki. Kai kuma Gwadabe duk shekara ka dinga bashi nera dubu ashirin kuɗin hayar ɗakinshi. Dan in ma baka bashin ba akan matarka zai ƙare. Gara ka ba ɗan uwanka dan babu irin hidimar da bai ma rayuwarka ba. Shi ya cicciɓaka har ka kai wannan matsayin. Ke kuma Iyabo zan gargaɗeki duk randa kika sake yi musu gwale a tsakar gida, ni na basu umarnin su watso miki da kayanki waje. In shi kin shanyeshi sai abunda kike so yake yi, to ni na sha tabara na sha yaseen ke har da lahaula duk na haɗa na sha na fi ƙarfin Oremi ma uwar bokayen yarbawa balle ke karan kaɗa miya. Ni dai kaina na ƙasa numfashi mai ƙarfi na saka fesarwa, in tashi in fita ina jin tsoron fassarar da zasu yi mun, in ci gaba da zama zuchiyata ta buga, hawaye na soma zubarwa. Yaya Hambali da su Harisu ransu yai fari fes dan jin irin hukuncin da Babala ta yanke mana. "To Shikenan Babala dan kin sa baki ne zan barsu su biya haya, amman da ko hayar basu isa na basu ba, dan dubu ishirin ɗaki ɗaya zai iya kama musu. Babala ki faɗa mishi na bashi sati ɗaya ya biya kuɗin haya, dan haya zata soma daga yau. Ban yarda kuma a sake sa mun kaset ɗin yarbawa a gidana ba." Ni sabida tsabar mamaki daskarewa nayi a zaune ina jin ikon Allah. Gwadabe kuwa kasaƙe yayi in wannan yayi magana sai ya juya ya kalleshi, har sai da suka gama maganar tsab yace. "To na ji Babala zan dinga biyan kuɗin hayan kamar yanda kika gindaya mun in sha Allah. Yaya Hambali kayi haƙuri a bisa dakatar da kai da na yi. Kuma in sha Allah in akwai wata doka ma da kakeson gindaya mana, zamu yi ƙoƙarin ganin mun bi, ai kai ubane ba wa a gareni ba. Babala shikenan inason mu tafi ana ma motarmu lodi legas zan wuce a yau ɗinnan?" Babala ta yi murmushi tace. "Me kake ci na baka na zuba, yanzu zan sallameku ai." Baki ta kada ta kira Laila har sau biyu kafin ta amsa daga uwar ɗakin Babala. Fitowa tayi tana wata irin tafiya ta jan hankali. Kallonta nayi inason in karanci yanayinta, ita kuma idanuwanta akan Gwadabe suke. "Kin gama haɗe kayan tafiyar naki dai ince?" Babala ta tambayeta, sai da ta yi murmushi har da sin da kai kafin tace. "Na gama haɗawa tun jiya Babala" "To ki fito da fantimotanki zaku wuce yanzu ko?" Laila ta kalleni muka haɗa idanu kafin ta koma uwar ɗakin. Babala kuma tace da Gwadabe. "Ga Laila zaka tafi da ita ta zauna a hannunka. In kun daidaita kanku falillahil hamdu, mu haka muke so dama. Kai na ɗauki amanar Laila na ba, sai ka kula da'ita yanda ya kamata. Ka kuma tuna ƴar uwarka ce, gyatumarta ni na saki nono na bata" Ba ƙaramin razana nayi da jin wannan zance mai kamar saukar aradu ba. Meke shirin faruwa dani ni Iyabo a wannan karon? Ta ya za'a bamu riƙon gansamemiyar bazawara irin Laila. Lailan da ada mijina ita zai aura, kuma har yanzu data fito naga son Gwadabe a idandunanta. Tabbas an shirya hakanne dan a nuna mun iyakata, ai mun kora da hali. In zan iya ɗaukar duk irin samfurin wulaƙancin da dangin Gwadabe suke yi mun, bazan iya jurar wannan ba, tabbas sai dai Laila ta mayema Gwadabe gurbina dan tafiyata zanyi gidanmu, abun ya isheni haka" "Babala taya zan iya riƙon Laila ina ƙarami alhalin ga Yaya Hambali, ga Yaya Harisu, sannan ga Sukairaju. A tunanina su yafi cancanta su rike Laila tunda sune a gaba dani. Sannan Babala..." "Ya isheka nace. Na riga da na yanke hukunci kai baka isa ka koya mun yanda zan yi ba. Ka tashi kawai ku wuce in ba so kake ranka yai mummunan ɓaci ba" Cikin faɗa sosai Babala take yin magana, har muryarta tana rawa. Ba shiri na miƙe har wani jiri nake gani tsabaragen kishi. To Babala zamu koma, sai mun sake zuwa kuma. Amarya Allah ya zaunar da'ita lafiya a gidanta" A mugun fusace Babala tace. "Ameen in da gaske kike yi baƙar muguwa kin rabani da abunda na haifa. Kema in sha Allah haka wata zata rabaki da ɗanki kiji in da daɗi" Bance uffan ba na ja hannun Toye muka fita bana ko gani da kyau. Ji nayi duniyar na juyawa dani, kaina na wani irin saramun tamkar zai rabe biyu. A ƙofar gida na nemi dakali na zauna jikina na rawa. Tsawon shekaru shida ina shanye dukkan abunda dangin Gwadabe suke yi mun. Amman ji nake yi kamar ma zamana da Gwadabe ƙarshe yazo kawai. Wallahi bazan iya dai dai da kwana ɗaya a ɗaki tare da Laila ba. Gara ni in matsa sai su aura mishi ita zaifi. Wasu zafafan hawayene suka gangaro a kumatuna. Ƴar ƙaramar wayata ce ta soma kuka, wayar da tunda nazo ba wanda ya kirani sai yanzu. In zaro wayar a jakar na kasa sabida tsabar turirin da zuchiyata take yi. Laila ce ta fita kici_kici da fantimotai guda uku hawan hawa, harda wata ƙatuwar jaka. Sai fara'a take yi tamkar wacce akaima bushara da gidan aljanna. Kawar da kaina nayi dan bana ƙaunar sake ganin fuskar Laila. A sanyaye Gwadabe ya fito daga cikin gidan. Duk yanda yaso mu haɗa idanu naƙi bashi damar hakan. Bara'u da Sakina ne suka katse mana tunaninmu. Gwadabe ya janye Bara'u zuwa gefe. Sakina ta zauna a kusa dani hannunta riƙe da baƙar leda. Laila tana daga gefe tana amsa kiran waya. "Meke faruwa Iyabo duk na ganku a birkice haka, naga Laila da fantimotan aurenta?." Hmm Babala ce ta danƙa amanarta a hannun Gwadabe, suna nufin tare da kishiyata zan zauna, bayan ta gama sanin sirrina sai a bashi umarnin aurenta." A hasale nayi maganar kuka na tunkuɗo kanshi. Sakina ta riƙe haɓarta tare da sakin baki cike da ta'ajibi tace. "Danƙari maƙari. Kika ce me, Lailan ce zaku tafi da'ita ta zauna a wajenku? Lailan da duk ƙauyannan ba wanda baisan irin son da take ma Gwadabe ba. Ke a wata ruwayar fa cewa akayi sabida Gwadabe ta kaso aurenta. Haka naji a wajen Goggona, kuma hakanne Bara'u ma ya sani. " Kaina ne naji yayi wata iriyar buɗewa, gabana yaci gaba da harbawa. Zuchiyata ta shiga watsa jini bisa rashin ƙa'ida, take na soma haki tamkar numfashina zai dakata. Yawu nake so in haɗiya in jiƙa maƙoshina da nake jin tsabar bushewa ya shiga daddarewa. Kika ce me Sakina?" Da ƙyar na jawo numfashi daga huhuna zuwa cikin bakina, harshena kuwa da ƙyar na iya sarrafashi. "Wallahi Allah kinji na rantse Laila sabida Gwadabe ta kaso aurenta, kowa ya sani." To gata ga Gwadaben, dan ni muna isa zan tattare inawa inawa in bar musu filin ɗakin, tunda dama abinda suke so kenan. Wallahi Sakina bazan iya zama inuwa ɗaya da Laila ba, gidanmu zan koma" Hawayena yaci gaba da zuba a kan kumatuna. Dafa kafaɗata Sakina tayi tace. "Bazan ce kar ki ƙwaci ƴancinki ba Iyabo. Haƙiƙa kin shanye abubbuwa masu yawan gaske tun daga aurenku kawo iyanzu. Amman barma Laila gidanki ba mafita bane Iyabo. Kiyi tunani kafin yanke hukunci, kar ki aikata aikin da zai jefa ki cikin dana sani marar amfani." Murmusawa kawai nayi dan banji akwai abinda Sakina zata faɗa yai tasirin hanani barma Laila Gwadabe ba." Gwadabe Yana fitowa ya dubi inda Iyabo ta zauna, zamanta kawai ya duba yasan tana cikin damuwa mai yawan gaske. Amman da zata tona taga irin damuwar da yake ciki zata san damuwarshi ta dame damuwar da take ciki ta shanye. Ya jima akan Iyabo yana son su haɗa idanu domin karantar yanayinta amman fur taƙi yarda ta ɗago. Dama muddin Iyabo na cikin ɓacin rai bata yarda ta ɗago kanta, sannan bata iya furta kalma. Isowar su Bara'u ce ta dawo dashi hayyacinshi. Gefe guda abokin nashi ya jashi. "Wadannan fantimotan ba na Laila bane Gwadabe. Kano zaku tafi da'ita ko me? Kasan zamanta gida ɗaya da matarka ba zai haifar da ɗa mai ido ba ko? Iyabo fa tasan irin soyayyar da Laila take yi ma, a lokacin da take ƙarƙashin inuwar auren waninka ma, ta kasa barin zuchiyar Iyabo ta nutsa, balle yanzu da nayi imanin farautar zuchiyarka zata je yi. Gwadabe ya kamata su Babala da Goggo Iyatu su ƙyale Iyabo ta nutsu, ta sha ruwa a gidanka. Yarinyace mai hankali da biyayya, gata da tausayinka, son da take yi ma mai tsananine. Shin ko dan so da ƙaunar da take yi ma ba hujja bane da zai sa Babala ta haƙura ta barku kuyi rayuwar Aminci ba?" Ajjiyar zuchiya Gwadabe ya sauke yace. "Ni bansan da wanne idan ma zan kalli Iyabo ba. Kar kaso kaji irin cin fuskar da Babala ta gama yi mata yanzu. Ba wanna ba Bara'u kasan ni Babala ta ba riƙon Laila a ɗakina zata zauna? Bayan hakan har tana ƙarawa da faɗin in mun daidaita kammu su hakan suke so. Ina cikin tsaka mai wuyar fita, ina jin nauyin Iyabo sosai, tana haƙuri da yawa da dangina." Bara'u ya dafe ƙirji tamkar wata mace yace. "Gwadabe kace Babala ce da kanta ta baka riƙon Laila, alhalin tasan ɗakinka ciki da falone kuma ƙananu, a haka take so ku zauna da Lailan duk abinda kuke yi tana jiyowa? Zaman ma bazai yi kyau bane Gwadabe kuma in akace an yi hakan to tabbas an zalinci Iyabo kuma an shiga hakkinta. Tana da damar yi maka bore ko tawaye. Kuma itama Babala dole ayi mata biyayya a matsayinta na uwa. Amman Gwadabe kar in tsayar daku kuje. Ni kuma zan shiga in samu Babala mu tattauna wala Allah zata fahimcemu. In yaso Laila ta zauna a wajen Haula tunda ita babbace kuma tana da ɗakin ƴan matan yaranta. Duk da hakan zaman ba kyau zai yi ba, amman in muka samu hakanma dama_dama. Dan Allah ka ba iyabo haƙuri ni wallahi kunyarta nake ji ma" Kai Gwadabe ya ƙyaɗa yace. "Kar ka wahalshar da kan ka da yawun bakin ka Bara'u. Ni nasan ko sama da ƙasa haɗewa zata yi, Babala ba zata saurareka ba balle ta fahimceka. Ko kasan yanzu haya zan dinga ba Yaya Hambali har nera dubu ashirin a shekara, ina nake da irin wannan kuɗin Bara'u?" Jijjiga kai Bara'u yayi yace. "Maganar tana da tsayi, da girma Gwadabe. Ungo Bakonnan shinkaface, da masara, sai kuka da daddawa, da gyaɗa da Sakina ta saka muku, ku kama hanya. Zanzo da zaran ka dawo daga legas, sai mu tattauna. Ta yi haƙuri ita Iyabo kafin mu tsayar da mafita. Muje suna jiranmu" Iyabo:. Ni dai ina zaune kamar mutum mutumi . Ita kuma Sakina sai gargaɗi take yi mun akan duk rintsi kar in kuskura in bar Laila taci nasara a kaina, kana kar in kuskura tasan logona na zafin kishi dan zata wahalani dashi. Jinta kawai nake yi, dan banga abinda zaisa in zauna inuwa ɗaya da Laila mu gauraya numfashi a ɗaki tare ba. Duk wannan abinda akeyi Laila na tsaye a gefe da Samarin cikin gidansu Gwadabe tana hira, duk da nayi imanin hankalinta na garemu. Su Bara'u ne suka nufo mu. "Tsuntsun soyayya to shikenan Allah ya tsare hanya. Aita haƙuri duk abinda yai farko ƙarshenshi yana tafe ko mu jima, ko mu daɗe. Allah ya yi miki albarka bisa bin mijinki da kike yi mun gode, in Allah ya saukeki lafiya Sakina zata zo da wuri ayi komai da'ita. Kuma a miƙa mun saƙon gaisuwa zuwa ga Iya Debisi, da Debisin" Ameen nagode sosai." Iyakar abunda nace kenan dan muryata shaƙewa tayi." Mashin Sakina ta tarar mun na hau, ta ɗaura mun fantimotina a gaba, ta miƙo mun ledar hannunta. "Amshi Atampa ce, kya ɗinka ki ƙara a kayan cin suna" Kafin in mata godiya har ta shige gidansu Gwadabe. Gwadabe ya hau mashin shi da Toye, da jakar kayanshi. Itama Laila ta hau nata aka ɗaɗɗaura mata kayanta muka wuce. Ina zaune akan acaɓa tunani duk ya addabeni, na rasa inda zan tsoma kaina. In na bar gidan Gwadabe na tafi gidanmu, bani da tabbacin Iya Debisi zata amsheni, kuma ko bata amsheni ba, sai ta yi mun kwakwazo da tonon sililin da kab ƴan gida sai sun sam halin da nake ciki. Ƙauyan da mahaifiyata take Aure kuma sau ɗaya na taɓa zuwa, shima a lokacin ina da shekara goma sha biyu ne. In wuƙa za'a ɗaura mun bisa wuya ko sunan ƙauyan bazan iya tunowa ba. Kuma har ga Allah bazan iya zama da Laila a ɗakina ba. Ajjiyar zuchiya na sauke wanda yayi dai_dai da isowarmu inda zamu hau mota. "Cikin gari ne, Alhaji, Hajiya kuzo ga mota" Cewar ma'aikatan tashar, suka yo kanmu suna rige_rigen sauke mana kayanmu zuwa wata cinyayyar Bus wacce ta ga duniya. Ni dai ina biye da mijina. Waje ya sama mun na zauna, Laila kuma ta zauna a jerin kujerun farko. Sai ajjiyar zuchiya nake faman yi. Ina hango Gwadabe ta taga yana biyan kuɗin motarmu, bayan ya biya ya shigo cikin motar. "Ga waje na samama kamar zaifi cikin sanyi ko?" Cewar Laila, tana yi tana kashe muryarta kamar tsohuwar karuwa. Tsaki ya ja bai ce mata uffan ba ya wuto inda nake a baya, yana riƙe da Toye. Zama yayi a kusa dani baice mun komai ba, amman naji jikinshi yayi zafi kau halamun zazzaɓi. Idanu na lumshe hawaye suka zubo mun suka diga a tsintsiyar hannunshi, kasancewar a mugun matse muke a motar. Ɗagowa yayi ya kalleni, ni ko kaina na kallon waje. "Iyabo so kike ki ƙarasa sukurkutamun lissafi kenan, ni da zan kwana a hanya ina tuƙi. Shin in ban samu sassauci a wajenki ba ina zan shiga in ji daɗi? Dubi yanda kike asarar hawayenki ke da baki da ishasshiyar lafiya" Da raɗa_raɗa yai mun maganganun. Zuchiyata ta tsinke, sai naji sababbin hawaye suna gudu a kumatuna. Allah ya gani bazan iya zama da Laila ba zaman da bansan irin sharrin da aka tanadar mishi ba tunda abun shiryayyene. Hawayena na share dan in sama ma Gwadabe ƴar nutsuwa. Amman sai na kulle idona kawai kamar mai bacci. Har motarmu ta fice a tasha, ta ɗauki hanya ban buɗe idandunana ba, banda niyyar buɗewa. Amman idanuna biyu zuchiyata na faman yi mun turiri. Ina jiyo muryar Toye yanai ma Gwadabe yarbanci, yana bashi amsa da yarbancin. Duk da ba iyawa yayi sosai ba, amman yana ƙoƙari wajen koyo, dan lokaci mu ka saka na musamman a tsakankanin magriba ruwa isha, ina koya mai yana maimaitawa in ya haddace sai ya rubuta. Wasu kalmomin da ƙyar yake iya furtasu. Muna nishaɗi sosai dan dariya muke yi sosai har tsakar gida ba za'a rasa jiyomu ba. A tsakanina da Gwadabe rayuwa muke yi mai aminci, muna ƙoƙarin bama junanmu farin ciki, da bama juna cikakken lokacin juna. Wannan irin zaman ke ƙaramun so da tausayin Gwadabe a ko wanne daƙiƙa. Shima hakan ke ƙara mishi sona. Bama iya ɓoye ma juna dukkan wani sirri. Haka naita tunane_tunanen daddaɗan zaman da muke gudanarwa da Gwadabe na. Zamanne danginshi basa so, sabida na fito a ƙabilar da ba tasu ba." Nasha wuya da wannan tsohuwar Bus sosai. Kafin mu sauka jikina yayi likib. Muna sauka muka samu abun hawa ya kawo mu har ƙofar gidanmu. Ni dai ana isowa na sauka abuna, ɗan mabuɗin ƙofar na ciro a jakata na buɗe gidan. Dukkanmu ko wacce ita da mijinta suna da safaya ki da mijinta. Ɗakina na buɗe na shaga, ban zauna a falo ba na shige uwar ɗaki na rufo ƙofar garam. Zama nayi a bakin gado, kamar am tsikareni na miƙe. Cikin ƙarfin hali na buɗe akwatina na soma loda kaya, ina jin Gwadabe yana kiciniya da fantimotan Laila . Da gudu Toye ya shigo yana dariya, rungumeni tsam yayi. Tunda muka tafi Takai sai yanzu da muka dawo gida yaron ya sake. Dariya nayi mishi nace dashi. Keeni ( Menene)? Na tambayeshi da yare. "Kiyasi (Ba komai) Ya faɗa cike da nishaɗi. Muna cikin haka Gwadabe ya shigo da sallama. Hirar sama data ƙasa na haɗe. Ku meye shawarar da zaku ba Iyabo. Shin ta zauna da Laila a ɗaki ɗaya. Ko kuma tayi tafiyarta su Babala burinsu ya cika, shin inta koma gidan kuna ganin zaman zai mata daɗi. Sannan inta zauna tare da Laila me zai faru? Ina saurarenku MRS BUKHARI https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm NAMA YA DAHU... ROMO ƊANYE BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI Lamba ta huɗu (4) *(SANARWA DUKKAN WAƊANDA SU SAYI WANNAN LITTAFIN TAMKAR SUN TAIMAKAMA MARAYUNE DA IZININ ALLAH. DOMIN KUƊIN KAI TSAYE ZAI TAFI ASUSUNMU NA GIDAUNIYATA MAI SUNA AMILA FOUNDATION NE. GIDAUNIYAR TAFI ƘARFI WAJEN TALLAFAMA MARAYU, DA TAIMAKON MARASA LAFIYA, SAI KUMA TALLAFAMA ZAWARAWA DA JARI MUSAMMAN WAƊANDA MIJI YA MUTU YA BARI DA ƳAƳA. SIYAN WANNAN LITTAFIN TAMKAR TALLAFAMA MARAYU DA IYAYEN MARAYUNNE. KUZO MUYI TARAYYA AKAN AIKIN ALKHAIRI)* *( KAR KU MANCE INA SAIDA TURARUKAN WUTA DA HUMRORI, DA DUK DANGIN ƘAMSHI MASU INGANCI NA MATAN KANURI. KANURI MUNE ƘAMSHI MEDUGURI GIDAN ƘAMSHI)* Ƙur yai mun da idanunshi wanda suka kaɗa su kai jawur. "Toye Wa Nibi ( zo nan)" Da gudu Toye ya je wajenshi. Murmushi yayi mishi yace. "L'o pade Anty re ( Je ka samu Antynka) Ya turashi zuwa falo. Yana fita Gwadabe ya mai da ƙofar ya rufe. A gabana ya tsugunna. "Ifemi (masoyiyata) me kike shirin yi, ɗakin ki kike son bari, Gwadaben naki kike son gujema? Duk irin juriya da gwagwarmayar da muka sha a baya bai sa mun rabu ba, sai dan akan Laila banzar bazara?. Ifemi ( Masoyiyata) kema kinsan dole zanyi wani abun ko dan samo mana mafita. Na fiki jin zafin tawo da Laila da mu ka yi. Iyabo kar ki yarda shaiɗan ya rinjayi zuchiyarki. Ki tuna Gwadabe ne naki wanda kikai mishi Alƙawarin mutuwace kaɗai zata iya gibtawa a tsakaninki dashi, ki rufa mun asiri ki zauna a ɗakinki" Shiru yayi yana jiran abunda zance. Gwadabe a gaskiya bazan iya zama da Laila a ɗaki ɗaya ba. Bayan tana ɗakin mijinta ma bata dena turo maka da saƙonnin ƙauna ba. To ka sani in ba baka san na san sabida kai Laila ta kaso aurenta ba, to na sani. Dan haka bazan zauna da kishiyata ɗaki ɗaya ta gama gane mun sirrina ba, in aurenta zaka yi basai an turota yimun c.i.d ba." Yanda nake maganar ina haki yafi komai ɗaga ma Gwadabe hankali ƙuri yayi mun da idanu yasan tabbas naje maƙura dan tsakaninmu yi nayi ne, bari na bari. Kafin ya tuno lafazin da zai rarrasheni dashi akayo kiran wayarshi, ya zaro a aljihu. Oga Lurwanu naga an rubuta, shine ogan Gwadabe wanda yake ma karen mota. Da sauri ya ɗaga, murya a sanyaye yace. "Oga Lurwanu yanzu na shigo Kanon, zan tawo yanzu in sha Allah, an gama lodinne?" Daga cikin wayar Oga Lurwanu yace. "Ka hanzarta Gwadabe, an yi rabin lodi, ana gamawa zaku kama hanyar Ikko da izinin Allah. Karen motarka yana nan tare dani tuntuni." "To Oga Lurwanu abinda zan barma iyali fa? Wallahi ɗari ukune a jikina da zanyi kuɗin motar zuwa inda kuke. Kuma a gidan babu komai. Kasan lamarin sai godiya" Oga Lurwanu yace. "Wannan babu wata matsala. Kai dai ka tawo ɗin. Ko yaro ka ba saƙo ya ajjiyema Iyalan. Kai muke buƙata yanzu" A haka su kai sallama da juna. Yana sauke wayar a kunnenshi ya dubeni. Hawaye nake ta faman sharewa. "Iyabo gashi bani da lokaci a halin yanzu. Kina jina da Oga Lurwanu. Abinda zance miki shine ki tausayama masoyinki ki yi zamanki a ɗakin ki, ki toshe kunnuwanki, ki ɗauke idanuwanki daga gani ko jin komai. Dana dawo zan nema mana mafita, amman in sha Allah Laila ba zata zauna tare damu ba. Ki kuma kwantar da hankalinki Laila ba zata taɓa samun gurbi a zuchiyata ba. Ba zata iya ruɗata da komai ba, a gabana ta yi wasan ƙasanta. Ni naki ne ke kaɗai Iyabo. Nasan kishi ke nuƙurƙusar zuchiyarki. Kinga hanya zan hau, taya hankalina zai kwanta in na barki kika koma gida. Sannan ke kan ki in kin koma gidan wani sabon damuwarce kika jefa mu a ciki. In ci albarkacin soyayya haba tauntsun soyayya" Duk wannan kalaman cikin sigar so gami da rarrashi yake yinsu. Gabaki ɗaya sai jikina ya mace mus. Ance tsakanin mata da miji sai Allah. Duk da ina jin bazan iya zama da Laila ba. Amman ya kamata in ma mijina uziri tunda shima umarni aka bashi, kuma bazan so akan faranta mun ya saɓama wacce tai sababin zuwanshi duniyar ba. Ajjiyar zuchiya na sauke kana nace. Kana da girman daraja a guna. Kaje Allah ya tsare maka hanya. Ya kareka da sharrin ƙarfe da sharrin hanya. Allah yasa sai dai ka ajjiye motar da hannunka ba dai ta ajjiyeka ba. Allah yasa a soma a sa'a, Allah yasa ƙarshen wahalarmu ne yazo. Ka kular mun da kan ka Gwadabe, dan akwai tarin tulin maganganu marasa daɗin ji a kan ku direbobin manyan motoci, sunan masu sana'ar tuƙin manyan motoci yayi ƙauri, sun san sirrin ajjiye daduro ni bana zarginka amman ina tunatar dakai jin tsoron rabbissama wati wal ardi. Kar ka zama daga cikin irinsu dan Allah, duk da a ko wacce sana'a akwai nagari, akwai na banza." Murmushi yayi ya rungumeni dani da ƙaton cikina yace. "Kamar yadda kika faranta mun raina, Allah ya faranta miki kema. Mala'ikun Allah ku shaida na ɗaga ƙafafuna domin Iyabo matata ta shiga Aljanna" Dariya mu ka saka dukanmu. Ka hanzarta jiranka akeyi dai kar ka shagaltu" "Wallahi kuwa. To ni zan tafi, zan aiko da ɗan kayan abinci da kuɗin da zaki riƙe a hannunki. Ki kula da kanki da abinda yake cikin ki. Da zaran kin soma jin naƙuda ki sanar ma Bose, nima ki yi gaggawar sanarmun, Bara'u sai ya zo ya tsaya. Ballema ina roƙon Allah yasa sai ina nan zaki haihu. Sannan ki kula sosai, Laila ɓarauniyace ta bugawa a jarida, ko ɓera bai kaita iya sata ba, kuma bai fita dabarun iya sace abuba, har hannu take sawa a wandon jeans na maza a kasuwa ta yashesu, gidan biki ko suna kuwa sata take yi tamkar tana bacci dan sauki. In zaki je gidan aiki ki kulle uwar ɗakin ki kar ki sake ki bar mana ƙofa a buɗe. Dan komai ɗauka take yi" Sumbatata yayi a baki, tare da riƙo hannayena muka miƙe tsaye a tare. To in sha Allah zan kiyaye, Allah ya tsare. Mu je in rakaka" Tare muka fito zuwa falo. Laila na tsaye a gaban hoton aurenmu dake manne a falon. Na ci lace da gwaggwaro. Gwadabe ya sha rigar asheke da hular ashoke kai ka rantse beyerabe ne shima. Jin motsinmu ne yasa ta zauna a kujera mafi kusa da'ita. "Fita zaka yi ne Yaya Gwadabe?" Ta furta da zazzaƙar murya ba irin tawa ba, dan muryata tana da ɗan girma gami da kauri. "E tafiya zanyi ma. Ni sai na dawo. Iyabo ki koma ki kwanta ki huta zuwa azahar kya tashi ki yi wanka ki yi salla." Kafin in ce wani abun muka jiyo sallamar Uwani Tabalbalin ƙawata tun ta ƙuruciya, ƙawarda banda madadinta. "A maraba lale Tabalbalin kece a tafe? Ai kuwa kinci sa'a dawowar ƙawar taki kenan daga ƙauye" Cewar Gwadabe daya tari Uwani da fara'a sosai. Cikin dariya tace. "Gwadabe na Iyabo ikon Allah tsuntsun soyayyar daya tashi daga kan Debisi sai ya hau kan Ɗan hausawa. Fita zaka yi ne?" Dariya muka saka dukkanmu, wannan suna yaƙi fita a bakunan waɗanda suka san gwagwarmayar da muka sha kafin aurenmu. "Wallahi tafiya zan yi ma zuwa Ikko. Ya yaran, ina Hafizu Oga ba?" Dariya mu ka yi duka. "Hafizu na baroshi a majalisarsu" A wajen mu kai sallama da Gwadabe ya fita, mu kuma muka koma uwar ɗaki ni da Tabalbalin. "Ashe tafiya kuka yi Iyabo. Kaddai bikin ƙanwar mijinnan naki marar kunyar nan, wacce ta watsa mun miya a zani lokacin sunan Toye kuka je?" Zama na yi a bakin gado. Na yi shiru kawai dan batun zaman Laila na ci mun tuwo a ƙwarya. Zama Uwani Tabalbalin ta yi a kusa dani tace. "Akwai wata matsalar ne Iyabo? Nasan ai ba zata wuce irin wulaƙancin da dangin Gwadabe suke yi miki ba ko. Balle kunje ƙauye an shiga taron biki" Wallahi da shine ma da sauƙi Uwani. Ai kinsan Laila tsohuwar budurwar Gwadabe, ƴar uwarshinnan wacce kwanakin baya muka samu saɓani?" Kai ta gyaɗa tace. "Na ji na ji. Wacce take turo da saƙon batsa tana gidan wani ko, ai kece banza da baki zaune ƴar banza ba. Halan wani abun tayi miki a cikin taro?" Itafa ƙawata. Ana baki kina karɓa Tabalbalin" Bata labarin abinda ya faru nayi kab ina share hawaye. Uwani da ba dan in na koma gidanmu tamkar na tozarta aurena bane, da wallahi kafin Gwadabe ya dawo na bar gidannan." "A'a kar ma ki soma. Dan in ma kika je Iya Debisi sai ta kusan illataki banda kwakwazon da za tai ta yi miki, maƙotanku ma sai sun ji meke faruwa. Amman gaskiya kar ki kuskure ki yarda kici gaba da zama da'ita ɗaki ɗaya maganar gaskiya. Ba zata zo har ɗaki ta iskanta miki miji ba. Amman ko da wasa kar ki sake ki bar ɗakin ki, yo kin bata dama ta kwace miki miji cikin sauƙi kenan ma. Nifa dani Gwadabe yake Aure da tuni na seta kan ƴan uwanshi. Ki kwantar da hankalinki tunda Gwadabe yace zai samo muku mafita kema kinsan bazai barki haka ba. Ya kika baro Sakina da mijintannan nata mai barkwanci Bara'u?" Ajjiyar zuchiya na sauke nace. Suna lafiya lau Uwani, ya Hafizu da yaran?" Shiru tayi na ɗan lokaci tace. "Iyabo yau haka muka wayi gari ko lomar da zamu kai bakinmu babu wallahi. Yaran sai turasu gidan Hajiyata nayi nasan ko ba komai ba zasu rasa abinci ba, tunda Hajiya na yin ɗanwaken saidawa. To mu ɗin bamu ci komai ba, ga ni da ciki na wata uku ban baki labari ba, wallahi bansan ina da cikin ba. Ga hayarmu ya ƙare gobe mai gidan zata zo karɓar kuɗinta, ko ficika bamu ajjiyeba, babu wanda muka ba ajjiya. To shine na sha maganin zubar da ciki cikin ya zube yau ɗinnan, Iyabo bazan iyaba, Hafizu bashi da zuchiyar nema. Ni rayuwarma ta isheni Iyabo, Talauci masifane ƴan uwanka ma sai su gujeka su ƙi taimakonka" Kuka ta fashe dashi kawai. Ban hanata rera kukan ba, domin kusan ni na fita sanin zafi da raɗaɗin talauci da wayar gari babu abinda za'a saka a ciki. Tunda Hafizu da yana da rufin asirinshi direban ƙaramar motane yana lodin Kano to Gomber, da Bauchi. Motarshi ce tayi haɗari ta yi rugu_rugu. Har yanzu bai samu wata motar ba. Shi kuma ya ɗaurama kanshi girman kan neman wata sana'ar. Daga haka ya ɓige da zaman kashe wando. Shi yasa rayuwar ta ɗaure musu. Amman ni dama a haka na shigo gidan Gwadabe na sameshi. Dama bashi da cikakkiyar sana'a duk abinda ya fita ya samu yi yake yi kawai. Numfashi na ja kana nace. Kiyi haƙuri Uwani da sauyin rayuwa. Mu yi ta yi musu addu'a babu dare ba rana. Ubangiji rabbissama wata wal ardi zai bamu mafita, zamu ji daɗi a gaba komai lokaci ne. Tashi mu je mu hura wuta, ga ɗan abinci mun samo daga ƙauye, ko fara ce in dafa mana, ina da yaji, mai ne babu dai." Tire na ɗakko na zuba shinkafa ƴar hausa Gongoni biyar, Uwani ta karɓa ta fita. Kurfot ɗina na zaro a ƙarƙashin gado da ƙullin gawayin hamsin a kai, nima na fito tsakar gidan. Wuta na hura da leda, Uwani na zaune a kujera tana tsintar shinkafa tace. "Ji gidan shiru kamar ba shi bane mai tarin hayaniya da bataliya ba" Yatsana nasa a leɓena nai mata nuni da tai shiru sabida Laila. Dole mu ka zama kuramen dole. Tashi nayi na ɗakko tukunya na buɗe randata dake bakin ƙofa cike da ruwa na zuba ruwan a tukunya, na ɗaura a wuta. Ruwan na tafasa Uwani ta wanke shinkafar ta zuba. Alwala muka ɗaura dukkanmu muka shiga ɗakin. Da sauri Laila ta ajjiye kwanon samira dake ajjiye a gefe guda. Kallonta nayi itama ta kalleni. Kai na girgiza na nufi hanyar shiga ciki. "Am Iyabo a ina zan ajjiye fantimotaina naga kamar basu dace su zauna a falo ba" Kallonta nayi na ƙara. To a ina kike ganin ya dace ki ajjiyesu in ba falon ba?" Na bata amsa cikin danne fishi, dan ji nake wallahi kamar in dira a wuyanta. "A uwar ɗaki mana, taya zan ajjiye kayana a falo?" Ta faɗa a gadarance irin ta dangi miji dan halinsu ne wannan kam. Cikin cusa haushi nayi dariya nace. Haba Laila, ai uwar ɗakina mallakinane tafi ƙarfinki, iyakar taki a falo take. Uwani mu shiga ko?" Na yi shigewata ciki na bar Laila tana surutai ni bansan ma me take cewa ba. Abinci na zuba mana a tire. Na zuba na Laila a kwanon silver, na zuba ma Toye nashi. Wani ƙaramin kwano na jawo a ƙasan gado, ragowar manjan miya ne a ciki nama mance dashi na tsiyayama Laila da Toye ragowar na ajjiye a gaban uwani danta soma cin abincinta ma gaya abunta. Falo na fita da zummar in ba Laila abincinta na tarar bata cikin falon. Ajjiye mata nayi a inda na barta. Na jawo hannun Toye yanata wasanshi muka shiga ciki na zaunar dashi. Kabbarar Sallah nayi. Ina cikin sallah muka jiyo sallamar namiji. Uwani ce ta fita dan dubawa. Sai da na idar sai gata da leda mai zane, da kuma baƙar leda da kuɗi dubu biyu. "Saƙone Gwadabe ya aiko miki. Gwadabe akwaishi da ƙoƙari akan komai ma, gaskiya ki sake gode ma Allah. Gwadabe ya riƙe miki amanar ƙaunarki. Iyabo kar ki kuskura wannan mai idanu a tsakar kan ta rabaki da mijinki." Tabalbalin sai na dage da tsaiwar dare. Domin tsorona bansan da wanne irin shiri tazo ba. Nasan kyanta, ko farinta, da kyan durinta bazai taɓar ruɗar Gwadabe ba. Na yarda da irin son da yake yi mun. Kuma na yarda yana ganin kyauna a hakan da nake, ko babu komai yakan yabeni ya kurantani. Kuma yasan da'itan ya tsallaketa ya auroni. Ni dai da sallar dare zan dage kar su je su nemar mun miji ta hanyar asiri. Uwani ina cikin damuwa sosai wallahi. Ke dai mu ci abinci kinji. Muna hirarmu muna cin abinci, anan na ba uwani labarin abinda ya faru a cikin gidannan ranar da zamu je Takai, da kuɗin hayar da zamu soma biya. Uwani tayi mamaki ainun ta jinjina irin ƙiyayyar da dangin Gwadabe suke yi mun. Sai bayan la'asar Uwani ta shiga haramar tafiya. Shinkafa da taliya, da kayan miya, da ɗanyen kifi, manja, maggin da Gwadabe ya aiko yaro ya kawo duk sai dana ɗibar mata, na bata ɗari biyar. Bata tafi ba sai da ta ɗoramun miyar tumatur a gawayi, da kanta ta leƙa ta kai mun niƙan maƙota. Sai da na rufe uwar ɗakina sannan na rakota. Mun fito mun samu Laila tana cin gurasa da lemun koka kola, abincin dana ajjiye mata kuma ta tureshi gefe guda, ƴar ƙaramar rediyo ta kunna tana jin waƙat barmani choje, waƙar gwarne ikon Allah. Tana yi tana karkaɗa kafaɗarta. Wucewa muka yi jiki duk a sanyaye. A sanyaye mu kai sallama da Uwani tana sake jan kunnena kar in kuskura in bar gidana sabida wata. Ko dana dawo ban shiga falon ba, a tsakar gida na zauna ina tsintar shinkafa ina shaƙar iskar ƴanci. Dan da masu gidan na nan, da ananan ana zubar mun da habaici, gami da maganganun cin fuska marasa daɗin saurare. A taƙaice dai ko dana gama girkin dare na sake zuba ma Laila a wajen ta sake bar mun. Ta fita ta siyo tea da biredi. Ni ko tunda na janye yarona na shige ciki nasa sakata, ban sake sanin halin da Laila take ciki ba. Misalin ƙarfe goman dare sai ga kiran Gwadabe ya shigo wayata. Cike da zumuɗi da kewa na ɗauka. Daman a zaune nake dan tunda cikina ya tsufa ban fiye samun baccin dare ba. Allah sarki Gwadabe da yana nan da yanzu yana matsa mun ƙafafuna. Amincin Allah ya tabbata a gareka gwarzon gwaraza. Barka da hanya, da fatan kana cikin aminci?" Murmushi yayi mun yace. "Barka sa dare sarauniyar zuchiyar Gwadabe, da fatan kina cikin ɗakinki na sunna cikin aminci ko?" Farin ciki ne ya lulluɓeni bansan sanda na lumshe idanuna ba. Ina lafiya, sai kewarka dake nuƙurƙusar zuchiyata. Ya hanya fa?" "Ba daɗi hanya. Kin ganmu a Tafa mun tsaya cin abinci da Sallah. Shine nace bari in ji lafiyarki. Ina Toye?" Gashi nan yayi bacci. "To masha Allah babu dai wata matsala da Laila ta baki ko?" Baki na taɓe kafin nace. Babu wata matsala a halin yanzu. Amman abincin rana dana dare dana bata duk bata ci ba. Fita tayi ta sai abunda ranta yake so" Faɗa ya soma yi akan karma in ƙara saka mata abincin in nayi tunda abun iskanci ne. Ni dai nace. Ba za'ayi haka ba. Ai da duk take_takenta so take in ƙi zuba mata a kafa mun hujjar na hanata abinci ita da gidan ɗan uwanta. Kai dai ka yi tunanin nemo mana mafita kawai. Dan wallahi Allah bazan zauna da gansamemiyar bazawara kamar Laila ba." Dariya Gwadabe ya dinga yi mun yana tsokanata kan na fiye kishi. Nima da dariyar na bishi kawai. A haka mu kai sallama dashi. Bacci bai zo ma idanuna ba, ƙarfe sha ɗayan dare na ɗaura alwala a cikin bahun babba. Na raba dare ina neman tsarin Allah ga dukkan masu son cutar dani da mijina, da masu son ganin bayan auren. Na roƙi Allah yai mun katangar ƙarfe da Laila ya karemu da dukkan sharrin data kwaso. Gwadabe kuwa alkhairi duniya dana lahira na roƙar mishi. Sai zaman lafiya, da jin daɗi wanda bana gajiyawa wajen sake roƙa mana, kusan duk addu'o'in maimaicine ba dare ba rana. Sai dai yau na ƙarama adda'ar tsawo da wasu salon roƙon. Sai wajajen jefin assalatu bacci ya kwasheni ina daga zaune. Amman ana kiran sallar farko na buɗe idanuna. Yinƙurawa nayi na tashi na buɗe ƙofata na fito da bahun ɗina na fice. Laila na saman doguwar kujera tana bacci saye da wandon bacci iyakarshi guiwa, rigar wandan mai shara_ shara ne har kan mamanta ina iya ganowa. Gabana ya doka da ƙarfi, kifiyar kishi ta soki tsokar jikina. Kai kawai na girgiza domin nasan tabbas dama a rina. Laila da kyan sufa da launin fata take son Jaye Gwadabe daga gareni. Dan tana da kyau tubarkalla masha Allah. Kuma ko a ƙauyen ita idanta a buɗe yake tar. Fita nayi na kama ruwa, na ɗaura alwala na koma ɗakin. Dai _dai da farkawar Laila tana tsaye tana miƙa. Na ƙarema wandon baccinta kallo shima shara_sharenne ina hango zaratan cinyoyinta farare luwai_luwai dasu. Ya kamata ki sani cewar nan ɗakin matar wanki ce, ba ɗakin aurenki ba. Wannan shigar a ɗakin mijinki kaɗai ya dace ki yita ba anan ba. Zan iya lamuntar komai, banda shigar banza mai nuna tsaraici, ki kiyaye sosai" Hararata Laila tayi tare da yin shewa tace. "Ashe ana tsoron iya inji ƴaƴan maiya. Babu rami me ya kawo rami Iyabo? Ashema baki yarda da nagartarki ba a matsayinki na mace ba." Murmushi nayi mata kawai domin bani da lokacin misayar yawu da'ita. Bayan na idar da sallah na yi azkar da adda'a, na jima sosai ina tunanin yanda ƙarshen zaman Laila a cikin ɗakina zai kasance. Ta yaya, kuma ya za'ayi tabar ɗakinnan alhalin Babalace ta bata umarnin zama, kuma dani da Gwadabe duk a ƙarƙashin ikonta muke. Wata zuchiyar tace. "Ai matsawar ba barin gidan kikayi ba Iyabo. To tabbas Laila babu inda zata fita taje. Babu makawa Gwadabe sai ya aureta. A daddafe na miƙe na shiga gyaran ɗaki, sai da na kintsa komai, na fitar mana da wankin kayayyakinmu na soma wankewa inayi ina rera waƙar yarbawa, amman wani shashe na zuchiyata a cike yake da tsoro da fargabar zamana tare da Laila. Kafin takwas na safe na gama komai har shara da wanka duk mun yi. Abinci na ɗunɗuma mana, kamar jiya na sake zuba ma Laila nata dai na dire mata. Ina gama karyawa na fito cikin shiri, na yi kaye_kayen kayana masu amfani na kulle uwar ɗakina. Laila na falo tana cin abincin dana ajjiye mata na yi ficewata ina jaye da hannun Toye, har zuwa bayan layinmu gidan da nake yin aikin shara, wanke_wanke, da goge _goge, sai wanki amman injinne yake wankewa, ya ɗauraye, ya busar gogewa ne dai nawa, sai in jera a sib, sai kuma girki amman shi ba ko da taushe bane. Babu wanda yasan ina yin wannan aiki, domin yana daga cikin sirrinmu ni da Gwadabe. Matan gida dai suna gutsiri tsomarsu akan fitar da nake yi tun safe, bani zan dawo ba sai azahar, har Gwadabe Yaya Hambali ya tara da zancan dan a tunaninsu gantali nake zuwa kawai. Yaya Haula kuwa cewa tayi bin gidajen maƙota nake yi yawon tsogumi, dan babu wanda ya kai yarbawa gulma da munafurci a cewarta. Da sallama na shiga madaidaicin gidan. Matar gidan tana ciki, dan na hango ƙofar falon a wangale. Bayan sallama kai tsaye na shiga falon. Tana zaune tana duba wasu kayayyaki da take ta warewa na maza da mata. "Yauwa Iyabo ashe kin dawo. Kar ki so kiga yanda wanki ya taru mana, kinsan yara da ɓata kaya" Dariya nayi cikin girmamawa da ɗan risinama wanda kake mutuntawa wanda ya zama ɗabi'a mai kyau ga ƙabilar yarbawa nace. Ina kwana Alaja ya yaran?" "Lafiya lau, an yi biki lafiya dai ko? Yau da Toye akazo bai je makaranta bane?" Wallahi kuwa bai je ba sai dai zuwa ƙarshen wata. Wannan kayan har da su a wankin Alaja?" Na tambaya ina kiciniyar kwashesu tace. "A'a kayane muka fitar na kwalima, za'a tura ƙauye a buhu zaki zura mun su. In akwai wanda kike so sai ki ɗiba" Baki na washe nace. Ahhh irin na yarbawa" Alaja nima inaso, bari in tsakura tunda mabuƙatan muna da yawa. Amman duk sanda akayi a dinga cira mun. Alaja tace. "To ki kwashe duka wannan na matan ki bar na mazan, ai ban gama kwaso kayan ba ma" Ba shiri na tsugunna ina ta faɗin. Ahh_Ahhh_Ahh Alaja na mazan ma inaso in da hali, zan bama mai gidana shima yana da ƙarancin suturu' Shiru tayi tana kallona, mamaki na bata ko tausayina taji sai Allah, sai da ta sauke ajjiyar zuchiya tace. "To ki haɗa duka ki kwashe, zan fito da wanda na ware a ɗakina sai ki zuba mun a buhu. Akwai takalman maza ƙafa biyu a dokin ƙofa ki haɗa dasu in zai ma me gidan naki, ni zam shiga ciki." Ahhh Olorun bukun fun o ebi re ( Allah ya albarkaceki, ya albarkaci iyalinki) Na faɗa da yaren yoruba. Na fassara mata da hausa dana tuna bata jin yaren. Da "Ameen_Ameen" ta amsa ta yi shigewarta ciki. Bayan na tattare kayan na shiga aikin share_share ka'in da na'in. Ina yi ina wanki a injin. Bayan na ƙalƙale ko ina kuma sai na shiga ɗakin yaranta, sai da na goge kayayyakin dana wanke tas kafin na miƙe lokacin anata kiraye_kirayen sallar azahar. Na jera na yaran a sib ɗinsu, na Alaja kuma na kai mata ɗakinta na saka mata a sib. Na gyare mata ɗakin tas. Kafin nayi salla kuma. In idar da sallah sai na tsinci kaina da rashin aha'awar komawa gida. Sai na tsiri gugar kayan da Hajiya ta bamu, tunda a wanke suke, sai ƙamshin turare mai daɗi suke yi. Dana gama wajajen biyu da rabi dai dole na fito daga ɗakin yaran ina riƙe da buhun kaya da Toye. Robar da take zuba mun abinci ta miƙo mun, da wata farar roba babba mai murfi tace. "Miyar ganye ce a cikin robar nan, ta ɗan jima a firji ne bazan iya amfani da'ita ba bansan ko kina so ba?" Karɓar ledar nayi nace. Inaso Alaja. Aidupe ( Nagode) Nayi mata sallama muka kama hanyar komawa gida. Ga buhu a kaina, ga leda a hannun hagu, ga Toye ina riƙe dashi, ga uban ciki mai tsini a gaba, ina tafe da ƙyar duk jikina ciwo yake yi mun. Da sallama na shiga gidan, tsakar gidan tsit kamar ba gidan hayaniya da shewa ba. Turus na tsaya a daidai tagar ɗakina bakina a sake, furucin Laila na ƙarshe a waya ne ya daki kunnena. "Ai in sha Allah na shigo kenan sai dai ta fita ta bar mun ɗakin, Gwadabe nawane halak malak" Sai ta saki Dariya. Murya a daƙile nace. Salamu Alaikum. Nasa ƙafa na shiga, tayi saurin kashe wayar da take yi. Na ƙare mata kallo da kyau. MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm NAMA YA DAHU.. ROMO ƊANYE BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI. Lamba ta biyar (5) Saye take cikin shuɗiyar atampa, ta ci kwalliya da jan baki da hoda, fararen idandunanta rambaɗe da kwallin daya sake fito da hasken fatarta. Sai wani ƙamshi take yi ita da falon. Haƙiƙa na tsorata da Laila da muguwar nifaƙar dake tafe da'ita. Amman in ta san wata ai bata san wata ba. Wanda ya riƙe Allah shi ke da gagarumar riba, nasara tana biye dashi. Dan duk nisan jifa dole ya dawo ƙasa. Kallon dana cikata dashi shi ya jefata cikin taraddadin daya kasa ɓoyuwa a fuskarta. Murmushin dole na sakar mata na yi shigewata ɗaki, na zauna daɓas a kan gado ina sauke numfashi kawai. Tagumi na zuba ina tunani. Na jiyo murya a falo kamar ta Burodami Debisi. Da hanzari na leƙo ai kuwa shi ɗinne a tafe da abubbuwan arziki. A guje Toye yaje ya ɗafeshi, shi kuma yayi maza ya rungumeshi tsam a jikinshi. Ɗagowa yayi ya ƙuramun idanunshi, nima shi nake kallo. Burodami barka da zuwa" Na faɗa tare da ƙoƙarin kawar da kallon da yake yi mun. Hijabi na zura , ban fito ba sai da na zuba mishi abincin dana dawo dashi daga aiki. Jallof ɗin taliyace ta ji bushasshen kifi, na zuba ruwa a kofin roba, na ɗaura a tiran roba, sai na fito. A gabanshi na dire tiran, na sake komawa na zubo ma Laila da Toye abincin bai yi ragowa ba, ga raina ya biya ina fatan Burodami Debisi ya ci ya rage in samu in lasa. Miƙoma Laila abincinta nayi, Toye ma na zaunar dashi a leda ya soma cin nashi. Ekabo Burodami ( sannu da zuwa Yaya) Ya gida, wa ni Iyawo re bawo ni ebi re? ( Ya Iyaninka) Murmushi yayi mun yace. Awon ti wani ol atanran. Bawo ni o se wa ( suna lafiya, ya kike?) Ohh mowa daa_daa ( lafiya Ƙalau) Ga abinci kaci karya huce. Abincin ya kalla nima ya kalleni, saurin kawar da kaina na yi gefe guda. Murmushi yayi tare da girgiza kanshi. "Ba zama nazo yi ba. Kuma in naci abinci anan, in na koma gida Emisi ba zata ji daɗi ba in nace mata na ƙoshi, dan na barota tana ta faman dakan sakwara" Wani yawu ne na jarabar kwaɗayin masu juna biyu ya tsinko mun jin an ambaci sakwara, muƙut na haɗiyeshi kawai, dan bani da yanda na'iya. "Ga TV da dvd, da kafet na kawo miki, na sauya ma Emisi kayan ɗakine shine na raba muku tsofaffin. Yanzu haka daga gidan Simbin Maman Kokodeen nake na kai mata labulaye da kujeru" Har ƙasa na tsugunna ina ragargazo mishi godiya, dan nayi farin ciki sosai, a cikin gidan ni kaɗaice bani da kayan kallo. Wataran matan gidan suna haɗuwa a ɗakin mutum ɗaya su harhaɗa kuɗi a yo renting ɗin kaset sai dai in jiyo sauti, muna dai da rediyo da muke sauraren labarai, harma wataran in saka kasetin waƙar yarena, dan Allah yayi ma yarbawa baiwar iya waƙa da son rerata, dan ko karatu zamu yi da waƙe muke yinshi, gamu da son sha'ani a taru taci asha ayi ashobi. Dubu biyu ya zaro ya ajjiyemun mu kai sallama ya fice. Kinkimar komai nayi na shigar ɗaki, na dawo na ɗauki abincin nayi shigewata, Laila na zaune bakan a zaune tayi tsit da halama saƙa take yi da mugun zare a ranta. Da daddare Gwadabe ya kirani mu ka ɗan taɓa hira ba mai yawa ba dai haka, yai mun albishirin ƙila jibi ko gata ya dawo da izinin Allah. Fatan alkhairi nayi mishi, tare da samun alkhairai. Washe gari ma kamar jiya ina gama komai na tafi wajen aiki abina. Ina dawowa tun daga bakin zaure na fahimci masu waje sun dawo mai tabarma dole ya naɗe, dan muryoyinsu har waje nake jiyosu ana mayar da yanda akayi da yanda za'ayi. Da sallama na shigo amman babu wanda yaji balle su lura da shigowar tawa. Karab a kunnena na jiyo Laila tana faɗin. "Ai ku baku ga irin kallon soyayyar da take ma farkan nata ba. Wai ni zasu ninke baibai. Ya kawo TV da dvd harma da kafet ƙato, ga kuɗi fa. Bai tashi zuwa ba sai da ta ga ba idanun Gwadabe" Yaya Haula tace. "In banda abinki Laila yarbawa ai sun saba iskanci wannan ba wani abu bane. Su da suke zaman wa jo ko, yarinya tana gaban iyayenta saita koma ɗakin saurayi, wai da sunan gwajin mahaifa, sai ya ɗirka mata ciki zata dawo gidan iyayenta. Kiga anata murna abu yayi kyau zata auru. In kuwa juyace shikenan an shata musulla. To su da suke haka har dan tsohon kwarton Iyabo ya biyota ɗakin aurenta wani abunne?" Ƙirjina take naji yana fat_fat_fat take numfashina na soma jin yana karkatsewa. Ban yi aune ba na jiyo muryar Gude tana cewa. "A can gidansu ma fa ɗakinsu ɗaya akace, tare suke gwamutsuwa su yi baccinsu, kinsan yarbawa dai sai a hankali basu cika hankali ba. Ni dai na rasa uban abunda Gwadabe ya gani a jikin beyerabiya wacce ƴar uwarshi Bahaushiya bata dashi. Ita ba kyauba, sai gandar baki da kayan ɗuwaiwaka ɓaka_ɓaka iyakar abinda matansu ke dashi kenan fa" Dariya suka saka dukkansu. Da Suwaiba muka haɗa idanu ina tsaye kasaƙe ina jin irin sharrikan da ake bina dashi. "Ahh kin dawo ne Iyaa Toye shine ba ko sallama?" Ta kula ni ne domin ta ankarar da abokan gulmar tata tai musu isharar wanzuwata. Ai kuwa sai su kai kamar ruwa ya cinyesu kawai. Hmmm e nadawo, ai nayi sallamar hira ce tayi daɗi shiyasa baku ji ni ba. Sannunku da hanya." Ina kaiwa nan na yi wucewata zuwa ɗakina. A saman kujera na zauna ƙirjina na soya mun. Da ƙyar na iya sa abinci a bakina, salla ma a daddafe nayi, kawai sai na ji na zama marar lafiya gaske. Sai tubka da warwara nake yi a zuchiyata hakanne ya hana ni sukuni da numfashi me kyau. Tun dawowar su Yaya Haula daga Takai, al'amuran gidan suka sake jagwalgwale mun. Sabon gulma da tsigudidi aka buɗe sabo. Laila kuwa irin ado da kwalliyar da take yi yana firgitani sosai. A tsakar gida suke wuni gulma da shewa, a gabana suke yi ma Laila adda'ar samun damar warce zuchiyar Gwadabe, tana amsa musu da Ameen. Ranar da Gwadabe ya faɗamun zasu shigo Kano da safe ina zaune ina wanki a ƙofar ɗakuna, ina ɗan waƙe_waƙenmu na yarbawa. Baban Nazifi ya fito daga banɗaki, dake banɗakin gidan a kusa da ɗakinmu lungun yake. Har ya wuce sai ya dawo da buta riƙe a hannunshi. "Wadannan randunan naki, da gayyar tarkacen robobinki, da wannan kwantenar da kike girki a ciki sun tsushe hanyar wucewa ban ɗaki. Sabida haka ki tattare komai a wajen ki sam inda zaki ajjiye, irin wannan tarkace suke lalata gida. Yana gama faɗar hakan ya wuce yana mita. Sukairaju wanda fitowarshi daga ɗaki kenan yace. "Yaya Hambali magana kake yi ne?" Ya tambayeshi. Cikin ɗaga murya dan in ji yace. "Da wannan masu kwalo_kwalon nake yi, kasan yarbawa da ƙazanta gasu ta tarin shirgi, ca nayi ta kwashe randunanta sun tare hanya." Harisu dake ɗaki sai ya amsa da cewa. "Yaya Hambali ai nima fa na jima ina son ince tarkacen lungun su Gwadabe yayi yawa, in zaka je banɗaki sai ka ta ture bokatai kafin ka wuce" Kaina na sauke ƙasa kawai. Gabaki ɗaya akan wannan maganar sai da kowa ya tofa albarkacin bakinshi. Ni dai da zafin zuchiya na gama wankina na nufi bakin rijiya zan ɗebi ruwa. Laraba ƙanwar Nazifi ƴar Yaya Haula kenan, tana bakin rijiyar tana ɗiban ruwa. Laraba ɗan zuba mun ruwa guga biyu nayi ɗauraya bayana ya riƙe" Ai ina rufe Baki Suwaiba ta iso inda muke da bokatanta da bahunanta itama zata ɗebi ruwa. Da safe duk matan gidan muke ciccika kayayyakin aikinmu, da randunanmu da ruwa. Buɗar bakinta tace. "Harda su kaza acin danƙo. Akanme yarinya uwarta ta sata aiki, zaki dakatar mata da aikin da aka sata kice ta zuba miki? Laraba in kin gama bani gugar" Ina tsaye Laraba ta gama jan ruwanta ta tsab sai ta miƙo ma Suwaiba guga. Ni ko nasa hannu na warce gugar a hannun Laraba. Na zura a rijiya. Suwaiba ta nemi kamani da kokawa a bakin rijiya, ai kuwa na dubeta nace. In ki kai wasa zan miki hajijiya in jefaki cikin rijiyarnan Allah, ki shiga taitayinki ba fa tsoro nake ji ba, ina dai son mu zauna lafiya ne. Da sauri Suwaiba ta matsa dan ni ɗin ƙatuwace tubarkalla masha Allah, kun dai san matan yarenmu akwai ƙiba babu laifi, gani da mazaunai a sama ɓaka_ɓaka masha Allah. Nan matan gida su kai mun ca a kaina, kowa na tofa albarkacin bakinshi, Gude har tana zunguremun kaina. Mazajen gidan a lokacin sun fita nema. Ni dai har na gama kab aikina na tsakar gidan, basu dena kwashena iyayena da dangina albarka ba. Ina shinfiɗa kafet ina hawaye harna gama shinfiɗawa, na saka tv da dvdn a inda ya dace, ɗakin sai ya sake sosai. Randunana na kwasosu na saka ɗaya a bayan ƙofar falo, ɗayar a uwar ɗaki, bokatan na ɗaurasu akan randar falo, bahunan kuma na ɗaura a saman randar uwar ɗaki, na fita na share wajen tas na shigo ciki. Duk fa wannan aikin ina jin ciwon mara da nake kyautata zaton haihuwace. Ina ninkin kaya na ji ciwon na ƙaruwa mun, ina jiyo ɓuruntun Laila a falo. Waya na ɗaga na kira Uwani Tabalbalin ,da Bose na sanar musu ina naƙuda, Bose kuma ta kira gida ta sanar, a cikin ƙasa da awa guda sai gasu dukkansu afujajan. Gashi ko reza bamu ajjiye da sunan haihuwarba, ta abinda zamu sa a bakin salati muke yi. Zaman dirshan nayi a ƙasan leda, sai zufa nake yi, ina ɗan nishi sama_sama su nai mun sannu. Ana cikin haka sai ga Yaya Mulka matar Burodami kokodeen, babban ɗa a gidanmu ta iso. "Yaya jikin nata Bose? " "Gashi nan dai tana ta fama, ko dai zamu kaita asibiti ne? Ƴan biyu ne fa a cikin ina tsoro" Ni da naketsakanin rayuwa ko mutuwa na shiga ɗaga musu hannu, ina musu nuni da su barni bazan je asibiti ba. Amman da ciwon yai tsanani gashi harna soma galabaita, babu shiri suka ɗaukeni, Burodami kokodeen ya zo da mota ƙofar gida. Matan gidanmu sai gani su kai an rirruƙoni mun fita. Sai faɗi suke "Au naƙudarce mu da muke cikin gida bamu sani ba, sai danginki kika kira? Yarbawa munafurci a jininku yake. Wannan ai iskanci da rashin daraja dangin mijine" Bansan wacece ta yi maganar ba, amman babu wacce ta tanka mata. Uwani maza je ki rufo mun uwar ɗakina. Na ƙarashe faɗe ina nishi. Tabalbalin:. A guje ta shiga gidan, tana shiga ɗakin Iyabo taga matan gidan a ɗakin cirko_cirko. Turus tayi da ta gansu, suma kansu sun dibibice da ganin Uwani. A zatonsu babu mai dawowa, sun shigo gulmar ganin gyara. Tsaki Uwani tayi ta shige ciki tare da cewa. "Aikin banza wallahi duk matar dana fito na sameta uwarta zanci danni ba Iyabo bace." Karo taci da Laila a cikin uwarɗakin gaban sib ta ɗauko sabuwar atampa tana hannunta. "Sata ce ta shigo dake ɗakin kenan? Iko sai Allah wai na kwance ya faɗi. Amman dai su Kulu anyi asara, an yi faɗuwar baƙar tasa, ko kuma ince ƙarkon kifi daga ruwa izuwa wuta, ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta." Laila kuwa ba bakin magana ai da kunya an kama uwar miji na sata a ɗakin suruka. Fisge Atampar Uwani tayi. Sum_sum ta fice, Uwani kuma ta rufo ƙofar ta fito ba kowa a falo, tsakar gidanma data fito duk sun yashe. Abundai ba haka akaso ba, wai an yi gulmar uwar miji ta ji. Tana shiga motar suka ja sai asibitin nasarawa." Asibitin Nasarawa. Da taimakon Allah, na haifi yarana biyu, mace da namiji da kaina, sai ƙari da akaimun kaɗan. Tubarkalla yaran manya kamar ba ƴan biyu ba. Sai dai fa ina sauka ma'aikatan kiwon lafiya suka soma tambayar dangina kayan da za'a saka ma jarirai, da abubbuwan da ake buƙata. Ko allura bamu da'ita. Burodami kokodeen ne ya ba matarshi Antimi Mulka kuɗin dukkan abinda ake buƙata aka kawo babu ɓata lokaci. Cikin ƙasa da awa guda yarana an kintsasu tsab a cikin seti me ruwan toka, sun yi kyau sosai. Ɗakin hutu aka dawo dani. Da iyaa Debisi na soma haɗa idanu, tayi kicin_kicin da ranta, da gani kasan ta cika ta batse ƙiris take jira. Ko ma dama can haka take, kullum a cikin faɗa da kumfar baki take. "O ye koju ti e ( Kinji kunya) Ki duba kin haihu a wulaƙance, babu mijinki, babu dangin mijinki, babu kayan jarirai, ba kuɗin asibiti, jibi ramarki. Da ace kinji abinda aketa faɗa miki daba haka ba, da ɗan uwanki kike aure yarenku da kin fi haka daraja, kuma babu mai ƙyamatarki, ballema ya tsangwameki." Duk wannan maganar da yare take yi mun. Tana yi tana buga cinya, tana ɗaga murya tamkar faɗa, bil haƙƙi ita ba faɗa take yi ba maganarta ce haka, ko kuma ince mafi akasarin yarenmu suna da ƙarfin murya, da ihu a cikin magana. Ni dai bani da bakin cewa, dan nasan Gwadabe na ƙoƙari sosai, banso zuwa asibitin ba sabida gujema tashin hankali da tarzoma irin wacce ta afku lokacin haihuwar Toye, an yi ɗauki babu daɗi sosai. Dan ranar suna anci dambe an gode Allah. Burodami kokodeen ne ya katse Iyaa Debisi ta hanyar cewa. "Yarinyar nan Iyaa Debisi ya kamata a barta haka, ko dan rabon dake tsakani, ni ina ganin dukan yayi mata yawa" Miƙewa tayi tsaye, ta tafa hannu tace. "Ahhhh Ahhhh kokodeen Oya were ( baka da hankali)" Nan fa ta sake shiga wani babin, ta inda ta shiga ba tanan take fita ba. Shigo da yaran da ma'aikatan kiwon lafiya suka yi ne yasa ta yi shiru. Ɗakin kuwa Hausawa sai kallonmu suke yi. Iyaa Debisi take ta soma rera waƙa tana rawa na murnar zuwan jikokinta. Suma su Burodami kokodeen nan suka soma rawa suna mata tafi. Tana rera waƙar yarenmu ta musamman da akema ƴan biyu. Gabaki ɗaya ɗakin hankalinsu yana kanmu. Murmushi kawai nayi musu, Uwani kuwa sai zolayar Iyaa Debisi take yi dama sun saba. Taiwo Iyaa Debisi ta riƙe, Burodami kokodeen kuma ya karɓi Kahinde. Sai murna suke yi, domun a ƙabilarmu babban abune haihuwar ƴan biyu, mun ɗaukesu a matsayin wata babbar baiwa da Allah ya bamu. Kuma yarenmu su kansa yaƙinin rayuwar ƴan biyunnan mai albarka ce. Ni dai a haka baccin gajiya ya kwasheni, bani na farka ba sai jefin la'asar. Ƴan uwana sun cika asibiti danƙam sai tayani murna suke yi. Ga abinci iri_iri an kakkawomun. Burodami Debisi ya zubo mun amala da miyar ewodu, da miyar wake, da jar miya dukka, ga ganda haka_haka. "Ga abinci kici ko zaki samu ƙwarin jikin naki, gida zamu tafi" Karɓa nayi na mishi godiya. Ƴan uwa kuma aka shiga yi mun ya jiki, tare da murnar zuwan Taiwo da Kahinde duniya. ( Hassana da Usaini ) Amalata naci nayi ƙat na kora da kunun akamu me zafi, take naji na yi gyatsa mai ƙarfi, bana jin komai garau nake jina tamkar ba ni bace na haifi ƴan biyu ba. Wajajen shidan yamma aka sallamemu muka fito asibiti mota biyu. Duk tare muka ɗunguma mazanmu da matanmu zuwa gida. A tsakar gidan muka tarar da matan gidan kamar dai kullum ana zaman gulma da kace_nace. "Ahh ƴan biyu aka samu kenan? Kai masha Allah barka da arziki Iyabo." Cewar Yaya Haula. Yauwa sannunku" Iyakar abinda nace kenan. A ƴan uwana kuwa babu wacce ta kulasu, suma basu kula kowa ba, mu kai shigewarmu ciki. Mazan a falo suka zauna, mu kuma muka shige cikin uwar ɗakin. Anty Mulka tace. "Abun girkin ki na ganshi a falo. Anan zan dafa miki ruwan wankan ne, ko zan iya fita ƙaddararren tsakar gidan naku?" Sai da na ja numfashi nace. Zaki iya fita dashi ki sa ta gefen ɗakina, kafin Gwadabe ya zo ya kawo itace" Sai lokacin Bose tace. "To wai shi gogan bai san kin haihu bane?" Kafin in yi magana Uwani tace. "Na kirashi na sanar dashi. Yana hanyar dawowa daga legos ne, da ƙyar ma na samu wayar tashi ba sabis. Amman yace abokinshi Bara'u zai tawo daga ƙauye, duk abinda ake buƙata zai yi kafin shi ya iso, dan yace mun zasu iya kaiwa ma ɗayan dare basu shigoba, wata ƙila sai Asuba ma zasu shigo kanon." Tsaki Iyaa Debisi tayi tace. " Isokuso asan. ( Banza marar amfani)" Haƙiƙa naji zafi ainun, kuma maganar ta dokeni, ai ko banza Gwadabe uban ƴaƴanane." Anty Mulka ta fita bakinta a taɓe. Bose ta fita da zanin jini da muka dawo dashi daga asibiti, Uwani kuma ta ci gaba da mun gyaran ɗaki, sauran ƴan uwa kuma suka fita falo wajen su Burodami. Zuga su Yaya Haula su ka yi, suka shigo da sallamarsu, Iyaa Debisi ce ta basu izinin shigowa. Suna shigowa ta miƙe ta koma falo" "Iko sai Allah, Iyabo dama kunsan ƴan biyu ne a cikin naki, ko kuwa sai da kika haihu tukunna?" Cewar Gude uwar son jin ƙaƙa aka haifi mutum. A'a dama tun cikin ma yana wata huɗu da akayi mun sikainin akace ƴan biyu ne. Kun gansu mace da namiji. Taiwo da Kahinde kenan" Yaya Haula tace. "Au suma sunan yarbawan za'a liƙa musu, babu ko karar a saka sunan Mahaifin shi Gwadaben, ita kuma macen asa sunan Babala, sai wani Taiwo da Kahinde?" Uwani ce ta juyo tace. "Ba tana nufin sunan yarbawa za'a saka musu ba. Taiwo da kahinden yana nufin Hassana da Usaini kamar yadda muke cewa a Yaren Hausa. Tunda ai kunsan ba ko waɗanne ƴan biyu bane ake sake musu suna ba, ko a cikin hausawa " "To wannan ko dole a sake musu wallahi. Kun mayar da Gwadabe sai kace sususu kawai" Cewar Yaya Haula wacce da gani ta fusata. Uwani ba kanwar lasa bace na santa sarai shi yasa na katse zancan dan gudun kar su kira mun ruwa, dan ƙyas su Bose suka ji wata hayaniya zasu shigo ayi ɓatacciya, dan kowa cike yake da haushin kowa, sai kace ba Allah ɗaya muke bautama ba. Ya'isa haka Uwani dan Allah. Yaya Haula Gwadabe na da ikon ya zaɓama jininshi duk sunan da yake da buƙata. Ni bani da ikon sashi yayi abinda baya so. Ko Toye ma shi ya zaɓi ya saka domin yai na mahaifina Allah ya jiƙan rai takwara" "Tunda ya kasa yi ma nashi Allah ya ji ƙan ran takwaraba. Ai baki zo kin ganshi da mahaifinshi a raye ba. Dama yarbawa akuyarku ai tayi kuka wajen juya miji da jarabar bin baba lawo" Ta sake faɗa da karfi . Na riga da nasan tarzoma take son tayarmun, ayi rikici su sake kafa hujja akan jarabar yarbawa, da ƙin zaman lafiya. Haka dai suka fice a ɗakin bayan sun yi mun barka. Ni dai ban basu yaranba, dan a al'adarmu bama ba da yaro jariri ga mutane aita jagwalgwalashi. Suma sun sani tun a haihuwar Toye, kuma sun yi rantsuwar ko yara ɗari zan haifa ba wacce zata sake yinƙurin ɗaukar jaririn. Cikin ikon Allah a ƴan uwana babu wanda yaji kace_nace ɗin data faru, bayan fitarsu Uwani tace. "Iyabo sai fa kin yi da gaske dangin Gwadabe zasu iya barinki kici gaba da rayuwa a gidannan, wannan ƙiyayyar ta yi yawa. Wallahi ko ahalul kitabi ce ke ya kamata su sarara miki haka. Duk da su kansu Iyaa Debisi sunƙi su zubar da makaman yaƙinsu. Amman ɗazu fa kinsan ina dawowa rufe miki ƙofa da kikace. Su Haula suna falonki suna kallon ɗakin. Ita kuwa baƙar kadararcan a Uwar ɗakin ki muka ci karo tana miki bincike a sib, har ta ɗakko wata atampa mai ruwan malmo, kai gaskiya kina cikin wani yanayi." Shigowar Sakina ne ya katse mana hirar. Ah Sakina kune a tafe da yamma sakaliya haka? Maraba" Na faɗa ina dariya. Uwani tace. "Kaga uwar gida, kuma Amarya a gidan Bara'u, Sakina lale." Cewar Uwani. "Lale Uwani, ashe Iyabo uwar biyu an samu kai. Sannu fa mai jego. Bara'u yana falo yace a kawo mishi yarin zai musu huɗuba." Miƙewa nayi na saka mayafi, Sakina ta riƙe Taiwo ni kuma ina riƙe da Kahinde muka fito falon. Bara'u yana kujera shi kaɗai, babu kowa a falon, duk yanda akayi su Burodami kokodeen sun tafi gida ne, ko sun je su dawo. Sakina ta miƙa ma Bara'u Taiwo. Ina wuni Bara'u. Da wannan yammar Gwadabe ya taso ku?" "Haba dai ai Gwadabe ya wuci haka a wajena. Kuma dama muna shirin shigowa cikin garin jikin Babala yaƙi yanzu haka tana asibitin Murtala. Yaya Hambali da Sukairaju suna wajenta, amman ƙila ba gado za'a bata ba dai." Allah sarki, ai ban sani ba. Zan shirya in je zuwa bayan magriba in dai basu dawo ba." Sai Sakina tace. "Ke da kike fama da kan ki kuma?" Bara'u daya fita sanin dawar garin yace. "A'a in dai akayi magriba sai ki rakata ta je ta dubo jikin ai dai ba za'ace bata nuna kulawarta ba ko ba gaskiya ba" Huɗuba yayi ma yaran da suna Hassana da usaini kamar yadda yace Gwadabe ya bashi umarni. "To yara na yi musu huɗuba da asalin sunayen da ƴan biyu suke zuwa dashi, wato Hassana da Usaini. Taiwo da Kahinde a yarenku kenan. Sabida haka a ɓangarenmu Hassana da Usaini suke. A naku ɓangaren kuma Taiwo da Kahinde Allah ya raya su da imani" Miƙo mun yaran yayi na amshi ɗaya Sakina ta amshi ɗaya muka shiga ciki. "Me za'a ɗaura na dare ne Iyabo magriba ta kawo kai ma?" Cewar Uwani kafin in bata amsa Iyaa Debisi ta shigo da ruwa a bawo na wankan yara ta dasa kujera. "Fun mi ni omo ( Bani yaron) Ta furta ranta a mugun haɗe. A sanyaye na miƙa mata ina fatan kar a kuma samun matsala makamanciyar ta haihuwar Toye. Uwani ai inaga ba sai an yi girki ba, ga Amala a kuka da faten wake, ai ya ishemu, gobe a ɗaura girkin." Nabata amsarta. Anty Mulka ce ta leƙo tace dani in je in yi wanka ta kai mun ruwan. Wanka nayi na gargasa jikina sosai na ji daɗi. Ina fitowa Su Anty Mulka suna shirin tafiya gida Burodami kokodeen yazo zai kaisu gida. Godiya nayi musu sosai, mu kai sallama suka fita ni kuma na koma ciki. Anan naga kayan abincin da su Sakina suka kawo mana, garin tuwon masara, kuka daddawa, busassun kayan miya, albasa, shinkafar hausa, da gyaɗar miya harma da man ƙuli jarka guda, da bushasshen kifi" Godiya nayi sosai gami da yaba ƙwazon Bara'u, ya kuma yi dace da macen da bata hanashi yin aikhairin sai ma taimakonshi da ƙara ƙarfafashi da take yi." MRS BUKHARI https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm NAMA YA DAHU... ROMO ƊANYE. GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI Lamba ta shida Shiryawa nayi cikin doguwar rigar Atampa, ɗaya daga cikin kayan da Alaja ta bani, atampar mai kyauce kuma tana da tsada da gani. Hijabi mai roba_roba na saka kalar atamfar sak. Na ɗauki Taiwo na goya, Kahinde kuma Sakina ta goya shi. Uwani zamu je asibitin Murtala Babala tana can bata da lafiya gara in je kar in yi wani babban laifin. "To sai kun dawo, nima ƙoƙari nake in gama gyare miki uwar ɗakin yadda ya kamata. Gobe za'a zazzo da yawa. A nan ma ni zan kwana gobe na koma gida Hafizu baya nan ya tafi Lahadin makoli mahaifinshi bashi da lafiya. Yaran kuma suna gidanmu " nace da'ita. To Shikenan ma, sai mun dawo to. Sakina muje." Shigarmu ward ɗin mata ke da wuya na hangi su Yaya Haula dukkansu a zazzaune a tabarma da mazajen nasu. Kallona suka shiga yi da suka hangoni. Sannunku Yaya Haula ya mai jikin?" Sai da ta taɓe bakinta tace. "Jiki da sauƙi" Gaishe da su Sukairaju nayi tare da yi musu ya mai jikin. Yaya Harisu cikin murtukewa yace. "Da'u ka kai su wajen Babala su gaisheta" Da'u yayi gaba muka bi bayanshi har bakin gadon Babala, tana zaune ta jingina bayanta da matashin filo. Yaya Halima kuma tana tsaye tana haɗa mata tea. Muna isowa Babala ta kawar da kanta gefe. Sannu da jiki Babala, ya ƙarfin jikin? Na furta muryata har tana rawa. "Da sauƙi" Ta bani amsa ciki_ciki. Yaya Halima kuwa nunawa tayi bata ma san Allah yayi ruwan tsaron mu ba. Gaisheta nayi tare da yi mata ya mai jiki. Babu yabo babu fallasa dai ta amsa mun. Da Sakina ne dai su kai fara'a. Sunto Taiwo nayi na miƙa ma Babala ita, tasa hannu ta amsheta, Sakina ta ƙara matsa da Kahinde. "Ba shakka gashi nan yara sun ɗebo ƙoƙon asali. Kamanninsu sak da dangin uwarsu dai kamar yadda Toye yabi sunanshi." Iyakar abinda tace kenan ta miƙo yaran. Raina ya sosu ainun ko Allah ya rayasu bata ce ba, balle ta yi musu adda'a a matsayinta na kakarsu. Yaya Halima kuwa ko kallo yaran basu isheta ba. Bayan na gama goyo ne ta kalleni sak tace. "Na ji saƙonki na gode da har kike tunanin mahaifinki ya fi mahaifin Gwadabe daraja a wajenshi. Burinki ya cika yaranki uku babu wanda Gwadabe yayi ma takwara a danginshi. Har ni da na ɗau jimirin renon cikinshi na wata goma ya kasa saka sunana ma ƴarshi. Taiwo da Kahinde ɗin dai da kika sanar, shima shi ya jaddada a matsayin sunan yaranshi. Ko da yake dama tuni kun gama tsarin komai tun ma yaran suna ciki." Baki na buɗe inason in ba Babala haƙuri amman sai ɗaga mun hannu tayi. "Kije kawai, bana son ganinki, bana kuma ƙaunar zamanki da Gwadabe, zuchiyata ba zata taɓa samun salama ba madamar kina amsa sunan matar Gwadabe abadan" Cikin razani da tashin hankali mai girma na shiga. Lokaci guda Gwadabe da aurenshi ya fice mun a raina kwata_kwata. Na yi alkawarin inayon arba'in zan tursasama Gwadabe sakina ko dan ya ga haske a rayuwarshi, domin na fahimci har abada Babala ba zata taɓa ƙaunata ni da abinda na haifa ba, wannan shi ake kira NAMA YA DAHU ROMO ƊANYE. Ko Gwadabe bai sake ni ba, ni kuma zan fice a rayuwarshi.Wata wawuyar ajjiyar zuchiya na sauke a hankali na soma tafiya dan barin ɗakin. In sha Allah ƙarshen aurena da Gwadabe yazo, ko da kuwa soyayyarshi ita zata zam silar numfashina. Fitowa daga ɗakin ke da wuya, na jiyo Harisu yana zagina tare da ƙorafi kan sunayen yara da aka saka. Sai ji nayi na muzanta ko fita ma bazan iyaba. A tsaye Sakina ta iskeni. "Ki ƙara haƙuri dai Iyabo damo sarkin haƙuri. Mu je kinji" Da taimakon Sakina na iya fitowa, amman har muka isa guda ban iya furta ko kalmar A ba, sai ajjiyar zuchiya kawai nake saukewa. In sa abinci a cikina wallahi na kasa sabida tsabar damuwa. Sakina da Uwani sai aukin rarrashina suke yi, amman na kasa ce musu komai. Ni tunanina ya na ga samarwa Gwadabe sauƙi dan fishin iyaye masifa ne, nayi imani fishin da Babala take kwana ta tashi dashi akan Gwadabe shi ya hana shi yin arziki. Kullum cikin faɗi tashi yake, ta hana kowa ya taimaka mishi. Yaya Hambali shago gareshi babba a kasuwa da yake siyar da dabino da gyaɗa, buhu_buhu yake siyarwa yana da yaran shago sosai. Amman Babala ta hana shi ya ɗauki Gwadabe ko da a matsayin yaron shago. Yaya Harisu shi kuma mota yake ja zuwa ƙauyuka a haka ya sai wasu motocin guda biyu ya bayar anayi mishi hayarsu. Sukairaju kifi bushasshe yake saidawa a kasuwa, shine zuwa argungi, shine zuwa maiduguri, da Yawuri saro katan katan na kifi, kuɗi yake samu sosai da sosai Ɗan fodiyo kuma Kafinta ne kuma ogan kanshi ne. Da'u shi kuma Yaya Hambali ne ya buɗe mishi shagon sai da kayan masarufi dangin shinkafar hausa, gyadar miya, masara, wake. Duk wannan matakan sun haushine da taimakon Allah da taimako da jajircewar Yaya Hambali, domin Yaya Hambali guda ne harda ɓari ga ƴan uwanshi, yana musu tsananin so. Ina lokaci yayi da zan fita fit a cikin wannan ahalin, nima in je in yi rayuwa mai kyau. In ba haka ba bala'o'e iri_iri zasu iya saukar mana a sakamakon fishin da Babala take yi da Gwadabe. Abubbuwa nawa Gwadabe ya kama suka lalace, yayi sana'o'e a ƙalla iri huɗu karen mota shine na biyar. Amma tafiyar bata wani nisa sai abun ya lalace, ko mai gidanshi ya koreshi, ko a yi mai wani ƙazafi, ko na sata ko na ƙashin tsiya." "Iyabo ga tea ki daure ki sha, wala Allah ruwan nono yazo miki. Kinga Taiwo da Kahinde kuka suke yi baki ma sani ba. Kar ki kuskura waccan munafukar ta falo ta fahimci kina cikin matsala, yanzu ta shigo. Surukar taki ma an sallamota tana ɗakin umman Nazifi." Hannu nasa na amshi tean hannun Uwani na sha, dan jikina har rawa yake yi tsabaragen yinwar da nake ji. Sakina ta miƙo mun Taiwo da take ta canyara ihu kamar wacce ake zare ma rai. Ga man zaitun da audiga Sakina bani in goge kan mamana in gwada musu ko zasu jawo ruwan yazo" Miƙomun Sakina tayi, na bi kan mamana na goge da man zaitun tas na ba yaran suka soma ja. Cikin ƙudurar Allah sai ruwan nono ya soma zuwa. Nan kuka yaƙare aka shiga tsotseni. A wannan daren bana ce na yi bacci mai kyau ba. Misalin ukun dare sai ga Gwadabe, a lokacin duk su Uwani suna kan gado sun yi bacci ya shigo. Ganinsu ne yasa ya koma falo, ni kuma na ɗebo jariran na biyo bayanshi, yana zaune a kan kujera. Laila kuma tana kwance tana bacci ta yi baje_baje cinyoyinta duk a waje. Miƙa mishi yaranshi nayi yasa hannu ya amshesu yana fara'a. "Maman biyu barka da sauka, ina fatan babu inda yake miki ciwo ko?" Babu, sannu da dawowa" Iyakar abunda na faɗa kenan shima ciki_ciki. Idanunshi yana kan yaranshi yace. "Ya dai akwai wani abu dake damunki ne, ko an yi wani abunne? Iyabo a yanzu ya kamata ace kin saba da komai. Ki toshe kunnuwanki dan abubbuwa da yawa zasu faru kafin ayi suna kema kuma kin sani. Yanzu haka nafi awa ɗaya da shigowa Babala naketa ba haƙuri tayi fishi wai ban mata takwaraba ita da mahaifinmu. Nace mata zan sake yin sabuwar huɗuba in hakan zai bata farin ciki. Amman taƙi fur tace mun in na sake ma yaran suna bata yafe ba, wallahi kar kiji......." Ɗan yatsana nasa a kan laɓɓana nayi mishi halama da yayi shiru, nuni nayi mishi da Laila dake kwance. Ai ba shiri ya haɗeye maganarshi. Mu ka ɗan taɓa hirarmu kaɗan, ya miƙo mun ledoji manya biyu, mu kai sallama dashi zai kwana a ɗakin zaure, ɗakin su Nazifi, Bara'u ma yana ɗakin. Da tunane_tunane na ƙarashe daren nawa, sai jefin asuba bacci mai nauyi sosai ya ɗebeni bani na farka ba sai taran safe lokacin ƴan uwana sun ƙaraso, har an yima ƴan biyu wanka sun fito ras dasu, dan Gwadabe ya kawo kayan jariri kala biyar biyar, sai nawa na fitar suna kala biyu, da takalmi da mayafi, sai sarƙa, dasu nabkin, da paints na yara, da man shafawa, da sabulu. Ɗayar ledar kuma kayan abinci ne a ciki. Ina farkawa Yemisi tace. " Lo we. ( Je kiyi wanka)" O dara ( To) Kawai na iya ce mata na ɗauki zani na lulluɓe jikina dashi na fita. Ina fitowa maƙotanmu suka soma shigowa barka. Matan gida kuwa babu wacce ta leƙo, sai aikace_aikacensu suke yi kawai. Bayan jama'a sun ragu sai na fita zuwa ɗakin Yaya Haula dan gaishe da Babala. A falon na tarar da Gwadabe da Bara'u gurfane a gabanta. Ɗan fodiyo yana gefenta yana ɓallo mata magungunanta. Gaisheta nayi da jiki, da ƙyar ta kada baki ta amsa mun. Ɗan fodiyo na gaishar kafin na gaishe da Bara'u da Gwadabe. Ni dai anan na tafi na barsu. Da tuwon masara miyar kuka da bushasshen kifi Uwani ta tare ni, harda tea mai madara, ina bacci Gwadabe ya shigo da kayan tea. Anty Mulka ce ta shigo ciki tace. "Wai Iyabo su dangiin mijinki basa zuwa taya aikine? Tun sassafe muke ta aiki a tsakar gidanku, amman babu wacce ta taya mu komai. Mun fitar miki da randunanki tsakar gida, wata bushasshiyar mace tazo tana faɗar maganganun banza, har tana dangantamu da ƙazanta. Mu fa ba zamu ɗauki irin wulaƙancin da sukai mana lokacin sunan Toye ba. Bga won ( ki ja musu kunne) sai in zaune mace ni yadda nake da ƙibarnan" Nan Bose da Kauliya suka ɗauka suma sai yare suke ta yi mun. Uwani ce tai ta basu haƙuri ni kam kuka na saka musu kawai. Ganin kukan nawa ne yasa su kai haƙuri. Tun ganin da naima Gwadabe a falon Yaya Haula ban kuma saka shi a idanuna ba. Da rana Iyaa Debisi ta aiko mun da farfesun kan akuya cikin kwano shi naci da rana, su kuma suka dafa taliya. Uwani na kira nai mata raɗar ta zuba ma Babala ishasshe a kai mata. Amman ko da aka kai sai dawo dashi Uwani tayi Babala tace bata cin abincin Yarbawa, da akayi tuwon dare ma na kuma sa Uwani ta kai mata, amman bata karɓa ba. Har magriba babu Gwadabe ba dalilinshi sai wajajen taran dare muna zaune dani da Sakina da Uwani suka shigo shi da Bara'u da ƴar baƙar ledarsu a hannu. Idanu ya zuba mun tare da lumshe su. Na fahimci akwai gajiya da tarin damuwa dake damun Gwadabe. Ko wanne halin zai shiga in na barshi oho, nasan Gwadabe yana sona so mai tsanini, duk da na fishi zurfi a soyayyar da nake yi mishi, jin Gwadabe nake tamkar shine mahaɗin numfashin da nake yi dan in rayu. Amman dole in fita daga rayuwarshi shima ya samu ya nutsa. "Ayi mun afuwa uwar biyu. Abubbuwanne su ka haɗu suka caɓe mun. Mun fita da Bara'u fafutukar yanda za'a samu na abincin suna da abun haƙiƙa a fita kunyar ƴan uwa." Murmushi nayi mishi nace. Babu komai, sannunku da dawowa ina wuninku?" A tare suka amsa duk aka gaggaisa baki ɗaya. Sakina ta tafi kawo musu tuwo. "Tamu ya kirani da magriba madam ɗinshi tana son tayi miki barka, yace ma ana gobe suna zata zo. Bari in kira ku gaisa" Kiran layin Tamu yayi bayan ya ɗaga wayar sai ya miƙo mun muka gaisa tare da yi mun barka. Daga ƙarshe ya haɗa ni da Ayashe itama tayi mun barka tare da faɗin. "Kayan fitar sunan ƴan biyu dana Maman ƴan biyu yana wuyana in sha Allah. Ana gobe suna zan tawo in zo ayi komai dani." Dariya nayi nace. Muna godiya Ayashe Allah dai ya bar so da ƙauna, mun gode ƙwarai" Mu kai sallama na miƙa ma Gwadabe, nan Tamu yake sanar mishi ya ɗauki nauyin rago ɗaya. Mun yi farin ciki matuƙa gaya. Sun jima a falo muna hirarmu gwanin ban sha'awa daga ƙarshe su kai mana sallama, suna fita muma muka tafi kwanciya. Haka dai ranaku sukaita tafiya, duk da kauce ma rikici da dangina suke yi sai da akayi rikici a tsakanin Anty Mulka da Yaya Haula. Wai an jiƙa tsakar gida da ruwan wanki, shine fa Yaya Haula tai ta zage_zage tun su Anty Mulka basu tanka ba har suka tanka. Akaita gwabza rikici har sai da manyan unguwa suka shigo akaita basu baki tukunna. Ni dai ranar naci kuka sosai sabida Babala har ɗaki ta shigo ta ƙaremun tanadi tas. Har ta gama babu wanda ya tanka mata, sai da tayi mai isarta ta fita. Ana gobe suna da yamma sai ga su Gwadabe da raguna tiƙa _tiƙa guda biyu sun ɗaure, da kayan cefanen suna niƙi_niƙi. Daf magriba Ayashe ta ƙaraso da yaranta biyu. Gaskiya ta gwangwajeni da ƴan biyu sosai. Shadda ta ɗinka mun taji aiki sosai, harda mayafi da takalm. Taiwo kuma bulawus mai tsada ta siyo mata irin mai takalmi da abun kai na yara, Kahinde kuma riga da wandon jins ta kawo mishi. Godiya na dinga yi mata. A ranar Bose, da Kauliya, da Anty Mulka a nan suka kwana. Washe gari asubar fari aka shiga aikin abinci. Da asubar Burodami Debisi ya kawo mana nama cikin leda mai zane, Burodami kokodeen kuma ya turo masu rumfa suka kafa runfuna biyu da kujeru. Yasa yara suka shigo da koka kola kireti huɗu. Ƴan uwa masu daɗi, ƴan uwa abun wuya wannan ya kawo nashi wannan ya kawo nashi sai kaga ashiri ya rufu ruf, a gaskiya ba yabon kaiba muna da hadin kai sosai. A ƙofar gida suka kafa murhun girki, masu Amala nayi, masu yin jallof nayi, ga nama jingin anata yankawa ana soyawa, wasu suna gyaran kayan miya. Tun asussuba ni da ƴan biyu muka yi wanka, ina ɗaki a zaune Bose tanai mun kwalliya ta kece raini. Ba yabon kai ba mu yarbawa mun iya kwalliya da sanin darajar kaya masu tsada. Domin mazan yarenmu basu san siyama mace ƙaramin zani ba, ko ashobi zamu fitar muna zaɓar mai tsada mu fitar. Domin matan yarbawa har adashe akeyi na musamman domin kece raini, ko wacce mace tana son asan mijinta na kulawa da'ita. Ko ni duk talaucinmu tun cikina na wata ɗaya nake zubin dashi a shagon Iyaa Beji me shagon atampa da lace ta bakin layinmu. Da kaɗan_kaɗan na tara kuɗin les ɗaya, sai naci gaba da tarawa, in ƴan uwana sun kawo mun ziyara sun ban kuɗi a ciki zan zari wani abu in zuba dashi, da haka na sake tara kuɗin leshi na karɓi lace biyu iri ɗaya na bayar da ɗinkin nawa a wajen Yemi, na gwadabe da Toye na bayar a shagon ɗinkin maza. Lace ɗinne a jikina tun sassafe nasa aka miƙama Gwadabe nashi shi da Toye dan tare suke kwana a ɗakin zaure. Sarƙa Bose ta saka mun a wuyana. "Wannan karon mai gidanki yayi ƙoƙari ba kamar lokacin haihuwar Toye ba. wannan lace ɗin da sarƙar babu laifi ba sui arha da yawa ba, ba sui tsada can can ba. Ga raguna manya_manya" Harara na doka mata, ta kwashe da Dariya ta doki kafaɗata. Dole nima na murmusa, dan Bose a lokacin da nake cikin matsi a gida sakamakon soyayya da Gwadabe, a wajenta kawai nake samun sauki. Yaya Haula ce ta shigo ɗakin da sallama tana wani gatsine, ta sha kwalliyarta da wata shadda mai maiƙo tayi kyau sosai, dan Baban Nazifi yana ƙoƙarin sosai a kan iyalanshi, bama su kaɗai ba harda iyalan ƙannenshi. Turus tayi data ganni na fito shar dani kamar ba ni ba, ba wata kwalliya bace a fuskar tawa ba, hoda ce sai jan baki, sai kwalli da Bose ta ziraramun, ko ja gira banyi ba sakamakon akwai gashi sosai a girata. Ɗan kunne da sarƙar da Ayashe ta tawo mun da'ita ta ba da gudunmawa sosai wajen ƙawata kwalliyar tawa, sannan dinkin buba ɗinkine dake fito da kyawun ko wacce irin mace, musamman masu jiki duma_duma irinmu, kwalliya da ado na fito da masu ƙiba ainun. "Iyabo gashi kayan yarinya na ɓangaren dangin miji." Ta dangwararmun da leda mai zane_zane. Kafin in yo godiya ta ƙara watso mun mugun kallo tace. "Na ga anata aiki babu wacce ta buƙaci ganinmu a wajen. Amman ki sani duk tsiya dangin uba sun fi power fiye da dangin uwa. Amman ke kinfi son duk abunki ƴan uwanki su tsaya a wajen, dan ku aikinku kenan ƙabilanci, tunda kika haihu ake yare a gidannan dan masifa." Murmushi nayi dan har ga Allah bana son cusa ma zuchiyata baƙin ciki a irin wannan rana mai albarka. Ai bansan basu neme ku ba Yaya Haula tunda ni bana wajen." Jijjiga kai tayi tace "Ai ba zaki sani ba tunda dai Gwadabe shi ya baki ƙofar raina danginshi. Babala tana gidannan a kasa zuwa a kiramu mu kama aiki a matsayinmu na dangin miji, ai shikenan hausawa na cewa sai bango ya tsage ƙadangare ke samun mafaka." Tana gama faɗar haka ta fice fuu kamar kububuwa. Ajjiyar zuchiya kawai na sauke na jawo ledar data dire mun. Riga ce ƴar ɗari uku uku guda biyu ta mace da na namiji, sai sabulu sanda biyu da omo mudu ɗaya shikenan abinda ke ciki. Bose ta riƙe baki tace. "Wannan kayan shine kayan dangin miji ke da kika haifa musu ƴan biyu? Lallai Anty Iyabo dangin mijinki basa ƙaunarki.. Ya isheni Bose ki barni in ji da abinda ke damuna dan Allah." Ina faɗar haka na miƙe zuwa uwar ɗaki, na tarar da Ayashe tana shirya Taiwo da Kahinde sun fito sun yi kyau sosai. Dubana tayi tana dariya tace. "Kai masha Allah mai jego kin fito shar dake kamar ba ke ba." Dariya mu ka yi dukkanmu. Simbi ce ta shigo niƙi_niƙi da buhu ta dire a gabana, Sai ga Taufiq shi da Lekan suma sun shigo da ghana most go. Yaran Burodami kokodeen ne Taufiq, Lekan kuma yaron Iyaa Kokodeen ne, Simbi shekararta goma sha takwas haka, wannan shekarar ta game sakandare ɗinta. Taufiq kuma yarone shekararshi sha biyu, yana jss 2. Lekan kuwa saurayine Buhun sobeniya ne na robobi, da kofuna, mafificin roba, moɗa da sauran kayayyakin roba mai manne da sikitar dake ɗauke da sunan Taiwo da Kahinde. Wanda ya ɗauki nauyin yi naga an rubuta Burodami Debisi Adebayo. Ghana most go ɗin kuma shaƙe take dam da kayan jinjiraye da atampopi , omo, sabulu da su nabkin. Hawayene ya gangaro a kumatuna mahaifiyata na tuno tana can ƙungurmin daji, babu waata hanyar da za'a iya sanar mata na haihu balle itama tazo ayi komai a gabanta. Duk da bani da maraicin uwa sam balle uba, Iyaa Debisi itace makwafin uwa a gareni, Burodami Debisi kuma shi ya zame mun makwafin uba. Shi yaita ɗawainiya da rayuwata har tasowata yanzu ma da nake gidan mijina bai fasa turo mun abun alkhairi ba, kuma yana kawo mun ziyara lokaci zuwa lokaci, duk da matarshi na tsananin tsantsar kishin kulawar da mijinta yake bani, sabida alaƙar data tafa gibtawa a tsakaninmu na soyayyar da Allah bai nufi shine uban ƴaƴana ba. Kafin ƙarfe takwas na safe tuni an gama girki tsab an zuzzuba a kuloli, An yanka raguna harma an gyara kayan ciki, kayan cikin dabba ɗaya nace a miƙa ma su Babala su soya da kansu kar suce an musu coge. Abinci ma ni da kaina na tsaya saida aka basu duk abinda ya dace, har sobeniyarsu nasa an cire musu Anty Mulka da Uwani suka kai musu har ɗakin Yaya Haula. Takwas da rabi Alfa Abdulsallam Abdulganiyu ya iso, ƙofar gida, zuwa lokacin ƴan uwa maza da mata duk suna waje a cikin rumfa a zazzaune. Gwadabe ne ya ratso cikin mata yana saye da leshi da hular ashoke, Kahinde ya riƙe Ni kuma ina riƙe da Taiwo, Ayashe da Sakina ne suka mara mana baya har zuwa ƙogar gida inda Alfa Abdulsallam Abdulganiyu ya soma wa'azi. A gabanshi muka gurfana, ya soma ragargazo ma ƴan biyu adda'a tare da roƙa musu alkhairan duniya dana lahira, tare da samun nasara gami da rayuwa mai tsayi, mai albarka. Duk wannan cikin yaren yarbanci yake yi, yanayi da waƙa dukkanmu muna amsawa da. Ameen" Muma cikin salon rerawa kamar masu waƙa. Yaran muka miƙa mishi ya shafa kansu yai musu adda'a ya miƙo mana su. Sannan ni yai mun adda'ar samun lafiyar shayar dasu cikin lafiya, Gwadabe kuma yayi mishi adda'ar samun tagomashi ta yanda zai ciyar dani lafiyayyen abincin da zan raini yarana cikin ƙoshin lafiya. Iyaa Debisi ta fito itama tayi nata addu'o'in, aka miƙa ma Babala abun magana, "Allah ya raya su da imani" Kawai tace shima sabida idon mutanene da taga sun yi yawa a kanta. Iyaa Kokodeen itama ta yi nata, su Burodami kokodeen da Burodami Debisi duk dai kowa yayi nashi.Daga nan kuma akayi adda'a kowa ya shafa. Sai Bose ta ɗauki kwano ta dinga bin mutane ɗaya bayan ɗaya sunata zuba kuɗi, mu kuma muka koma cikin jama'ar suna. Dangina rankatakab ɗinsu ankon atampa mai ruwan kunun kanwa ce a jikinsu maza da matansu. Abinci aka soma rabawa masu kalangu kuma suka amshe fagen. Haka dai akaci gaba da gudanar da shagalin suna bamu muka tashi ba sai ƙarfe biyun rana. Daga nan kowa ya watse, duk wani gudunmawa a wajen aka bani, sai da muka cika bahun biyu da kaya da atampopi, kuɗi kuwa na same shi sosai ƴan biyu sun yi goshi sosai. Bayan mun koma gida sai na sake wanka na kwalliye da shaddar da Ayashe ta bani na fito shar dani. Sai lokacin na samu nutsuwa naci abinci na ba ƴan biyu nasu abincin. Kafin la'asar har an gama soye naman suna tas Anty Mulka ta ƙuƙƙullama duk waɗanda suka dace, ni dai da Gwadabe cikin ƙaramar samira kawai muka tsira dashi a matsayin rabonmu. Ragon ɗaya sukutum aka ba su Babala, ɗayan kuma ni da ƴan uwana duk muka rataya akai, wanda na samun ma Babala ta aiko laraba wai in ƙara mata nama ƙawayenta na Takai basu samu ba. Dan haushi samirar duka na miƙa mata na yi kwanciyata dan in ɗan huta. Washe gari Ayashe ta ɗau hanyar garinsu, da rana su Sakina suma suka wuce. Uwani dasu Bose ne suka gyara mun ko'ina su kai mun girkin dare kafin magriba duk suka watse ɗakin daga ni sai ƴaƴana misalin taran dare sai ga Gwadabe ya shigo furkarshi ɗauke da fara'a, nima murmushi na sakar mishi. MRS BUKHARI 3064127935 Buhari Ibrahim Ladan First bank Sanya nera 500 ɗinki kuɗin karatu anan. Wannan asusun gudauniyarmu kenan. Ki sani in kika siya wannan littafin tamkar kin taimaki iyayen marayune, dama su kansu marayun Kuzo mu yi tarayya cikin aikin lada. Ƙarƙashin Amila Foundation gidauniyar da muka buɗe ni da megidana domun iyayen marayu, ko tainakon marasa lafiya. Waɗanda suke cikin group dina mai suna (NAMA YA DAHU ROMO ƊANYE) 300 kacal zasu iya kuɗin karatu NAMA YA DAHU.... ROMO ƊANYE GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI INA MIƘA SAƘON GAISUWATA A GAREKU. KHADIJA MAIDOKI MRS BASH MAMANMU (HAJARA ALIYU) MAMAN SAFWAN ANTY YABI YUNUSA JIBRIN ( AZARE) MAMAN ANNUR KHADIJAN MAKAWA UMMU NABEEHA MAMAN YASEER SISTER FARIDA ( ƘAWAR UMMU NABEEHA) MAMAN MUHSEEN RUƘAYYA YAWURI UMMU AFFAN ABUJA UMMU AFFAN SADFAT RAMLEX MMN LAMIDO MAMAN ABDULRAHMAN INNAR BASMA ANTY ZEE MUSA A.A NAFAƊA MAMAN INTEESAR KUNA DA YAWAN DA BAN ISA JEROKU A PEJI ƊAYA BA, A BOYONI BASHI DUK ZAN ZANA SUNAYENKU, INA ALFAHARI DA MASOYANA NA FAƊIN DUNIYA. ( JIYA WATA BEYERABIYA TA KIRANI A WAYA TAKE CEWA DANI TANA BIBIYAR LITTAFINA, KUMA TANA JIN DAƊINSHI SOSAI. SOYAYYAR GWADABE DA IYABO TA BURGETA, KUMA ITAMA HAKA TAKE FUSKANTAR ƘALUBALE A CIKIN AURENTA. ITA KANURI TAKE AURE TANA BEYERABIYA) Lamba ta bakwai (7) Saye nake da doguwar rigar leshi, ɗaya daga cikin kayan da aka bani a gidan aiki. Toye na kwance a kan bargo a ƙasa yana bacci. Ƴan biyu kuma suna kan gado suna baccinsu sun sha overoll farare tas. Yaran ya zuba ma idanu da kyau sai murmushi yake faman yi. Zama yayi a bakin gadon ya ɗauki Taiwo dan tafi kusa dashi. Zama nayi ina fuskantarsu yayi kyau da yarinyar a hannunshi. Rabon yarannan ne yasa iyayenmu suka amince da aurenmu bisa dole, dan wannan rabon ka iya ajalin duk wanda ya kafe ba zamu auri juna ba. Gwadabe ina alfahari da aurenka, ina alfahari da soyayyarka gareni. Hakanne yake sa in mance da kyara, tsangwama, ko ƙyamata daga danginka. Domin kai kam ka zame mun komai, ka cike duk guraben dake da giɓi a rayuwata madallah da samun miji nagari irinka" " Ifemi ( masoyiyata) Na gode da soyayyarki, ina jinjina juriya gami da haƙurinki, samun mace irinki abune da sai an tona shi a wannan zamanin, musamman a ƙabilarku da matan yarbawa suke da zafin rai da saurin faɗa. Mala'ikun Allah ku shaida ni Gwadabe na ɗaga ƙafafuna Iyabo ta shiga aljanna, ku sake shaidawa ita da kishiya sai ta gidan aljanna, a can ma itace shugabar su " Dariya mu ka yi dukkanmu kafin ya ja fasali yace. "Ina da tarin tulin tambayoyi kin shirya?" Ahaf ni dama nasan ba zaka barni ma zuwa gobe ba. Tambayeni in baka amsa, amman kafinnan bari in kawo maka abinci, kana ci kana kora koka kola zai fi. Miƙewa nayi abincin na gefen sib a tiran silver ɗauke da duk abun buƙata. Tuwon shinkafane miyar bushasshen karkashi wacce ta ji kayan cikin rago, iyakar kayan Cikin miyar shine iyakar rabon da muka samu a raguna biyu tiƙa_tiƙa. Zuba mishi nayi na matsar gabanshi, Ajjiye Taiwo yayi tare da sakkowa ƙasa, ya tanƙwashe ƙafarshi yanata kallo ina hidima dashi. Lomar tuwon farko a bakina ya sauke mun, tare da yankan saifa. "Bani labarin tv da kafet tukunna, dan dasu na soma cin karo" Sai da na saisaita nutsuwata, na sake tausasa muryata kafin nace. Burodami Debisi ne ya sake ma Yemisi kayan ɗakinta, shine ya bibbimu da tsofaffin" Kafeshi da idanu nayi ina karantar yanayinshi, dan Gwadabe bashi da daɗi sam ta wajen kishi. Ya zafafa kishinshi sosai akan Burodami Debisi. Alhalin shi babu ni a zuchiyarshi sam, bana mance lokacin da Iyaa tace zata haɗa aurenmu ayi tuwona maina. Har hawaye Burodami Debisi yayi ma iyaa dan ta tausaya mishi ta janye maganar auren. Ba dan ƙiyayya ba sai dai kawai bana daga cikin jerin kalar matan da yake burin rayuwar aure dasu. Ni ina da ƙiba sosai, gani da cikar kumatu dan har idanuna da hancina sun shige ciki, ga mazaunai masha Allah. Shi kuma baya ra'ayin mace mai irin zubina. A cewarshi siriraya doguwar mace yake so, wacce zai iya bi da gudu ta zura ya rufa mata baya. Akan wannan dalilin ya kafe dole cikin fishi da hasala Iyaa ta janye batun aurenmu dole ta ɗauki idanu ta zuba mishi, har kwsnciya jinya ssida yayi. Bayan aurena da shekara biyu ya auri Yemisi ƴar ƙawar Iyaa. "Me yasa daya kawo baki bari na zo kin nuna mun ba?" Kai na sauke ƙasa ganin yanda fuskar Gwadabe ta sauya launi. Ka yi haƙuri in karɓar da nayi ya ɓata maka rai. Amman ba roƙa nayi ba, har gida ya kawo mun. Gwadabe ka rage ƙiyayyar da kake yi ma Burodami Debisi, dan shi ya ɗauki ɗawainiyar rayuwata tun daga yarintata har tasowata. A matsayin wa nake ganinshi, shima bani da wani matsayi a wajenshi daya wuce na ƙanwa" "Ki tsahirta mun haka nan Iyabo. Ai nasan wanki ne, sai dai ai wa ne irin wanda akwai aure a tsakani. Danni na kasa gane menene manufar Debisi sonki yake yi ko tausayinki" Zim naji jikina yayi, ba wannan bane karo na farko da Gwadabe yake ƙumaji sabida debisi ba, kuma ba fa zargina yake yi ba ni na ɗauka a matsayin yana tsare mutuncina da nashi ne baki ɗaya. Gwadabe..." Hannu ya ɗaga ya dakatar dani. Ya soma cin abincinshi zuchiyarshi cunkushe da kishin Debisi har ya gama tsakanin ni dashi babu wanda yayi ko tari, sai ja da sauke numfashi da muke yi. "Batun kuɗin asibiti kuma shima Debisinne ya biya ko, so kike ya samu hujjar ganin kamar bana ƙoƙari a kan ki ko? Bayan kinsan komai da irin tsanar da ake nuna mana. Kina fa gani ƴan uwana ma bana neman taimakonsu" Nasan idanun Gwadabe ya rufe da kishine, shi yasa nayi murmushi nace. Ashe na fika dauriya da haƙuri tunda har na iya haɗa ɗaki da matar da akeson a aura maka. Matar data baro gidan mijjinta sabida kai. Haba Gwadabe in hankali ya gushe hankali ake turawa ya nemo shi. Ko da Burodami ne ya biya kuɗin asibitina bai kamata ace an yi fishi dashi ba, ballema Burodami kokodeen ne ya biya komai da komai." Shiru yayi mun, yasha jinin jikinshi, dan maganata tamkar na ɗaureshi da jijiyoyin jikinshi ne. "Kiyi haƙuri da fishin dana nuna, kishinki ne yai mun yawa. Amman nasan har ga Allah kin fini dauriya da mayar da komai ba komai ba. Mala'ikun Allah ku shaida na sa ma rayuwar Iyabo albarka." Ajjiyar zuchiya na sauke tare da yin dariya. Shima dariyar yayi. "To leshi da kika ɗinka mana shi kuma ta ina kuɗin ya ɓullo?" Labarin yanda akayi na tara kuɗin na bashi tare da kayan kwancen da aka bani a gidan aiki. Miƙewa tsaye nayi na ɗebo mishi duk kayayyakin da na samu na suna, da duk kuɗaɗen da aka babbani. Ka gansu duk albarkar haihuwa ne, kasan ƴan biyu akwaisu da farin jini" Dani dashi mu kaita wauware kayayyakin muna kallo, muna hirarmu ta yaushe gamo, ina bashi labaran abubbuwan da suka faru shima yana bani labarin yanda suka kwashe da Babala kan batun sunan yara da ya saka. Da ankon leshi da muka yi, ashe Babala har kuka saida tayi, wai Gwadabe ya zama beyeraben dole. "Kaya sun yi kyau an gwangwajeki da kaya gaskiya, babu abinda zance sai Allah ya amfana. Sunan yazo mun da sauƙi wallahi ko da yake ance ko wanne yaro da arzikinshi yake tafe" Gaskiya ne kam. Allah ya ƙara rufa mana asirinmu fid duniya wal akira" Gwadabe yace. "Ameen dai Maman ƴan biyu. Toh yanzu me kike ganin ya dace kiyi da kuɗinnan tunda kinga suna da kauri, in yaso sai ki haƙura da zuwa gidan mutane aiki, dama ba asan raina kike zuwa ba, tunda na samu aiki ƙwaƙƙwara a hannuna kema ki miƙe ƙafarki ki huta kamar yadda ko wacce mace take hutawa ko?" Miƙewa nayi na tattare kwanukan daya gama cin abinci na fito falo dasu. Abun mamaki Laila na gani a laɓe tana sauraren hirarmu da Gwadabe. Tana ganin fitowata tayi kamar maiyar da aka kamata ƙiri_ƙiri tana lashe kurwar surukarta, har wayarta tana faɗuwa a ƙasa tsabaragen kaɗuwa. Tsaki nayi mai ƙarfi na harareta. A cikin bahun na zuba kayan wanke_wanken na rufe da bahun na yi komawata ciki. Gwadabe ya sake dawo da maganar sana'a tsabaragen ɓacin rai yasa ban iya ce mishi komai ba, na tuɓe kayan jikina na zura doguwar rigar baccina, nayi hayewata gado na juya bayana ina hawaye." Cikin ɓarin jiki Gwadabe ya hayo gadon yasa hannunshi a kafaɗata, yayi amfani da ƙarfi wajen juyo dani, hawayen da yaga yana tsiyaya ta gefen idanuna ne yasa ya kasa magana. Cikin rishin kuka nace. Yaushene Laila zata bar ɗakinnan Gwadabe ka sanar dani a darennan, wacce hanya ka sama mana ta yanda Laila zata bar gidannan? Ni da ɗakina Laila bata Isa ta hanani zaman lafiya ba, nagaji Gwadabe ni gidanmu zan tafi" Na ƙarashe zancen da rushewa da kuka mai gunji, ji nake yi zuchiyata na yi mun tuƙuƙi. Rungumeni Gwadabe yayi tsam a ƙirjinshi yana rarrashina, amman fur naƙi rarrasuwa. Ana cikin hakane muka jiyo wani ihu daga falo mai razanarwa, wanda yai sanadiyyar farkarmun da yara daga bacci suka saki kuka a tare. Kafin in ɗaukesu muka sake jiyo ihun a karo na biyu. Da sauri Gwadabe ya fita na mara mishi baya da ƴan biyu a hannuna. Me zamu gani hmm Laila muka gani a kwance tana burgima tsaraicinta na fitowa, sai ihu take kwarmayawa. Har ɗan diras ɗinta muna hangowa fari sol dashi, da sauri Gwadabe ya kawar da kanshi gefe. Kafin kace me matan gidan sun cika ɗakin, Laila na ganin haka saita soma kwaɓe suturarta tana fatali da'ita. Ba shiri Gwadabe ya fice a ɗakin. Sai adda'a aketa faman tofeta dashi ita kuma tana ta surutai. Mamanta na ƙurama idanu farare sol dasu luwai_luwai ko wacce mace nayi imani zata so dama itama mamanta haka yake. Kuma Gwadabe fa ya ga maman nata, dan sai da ta yar da rigar maman kafin ya fita har yana tuntuɓe hawayena na share dan nayi imani babu wata iskar dake damun Laila tsagwaron iskanci da makircin data riƙa a matsayin makamin da zai fitar dani daga ɗakina ita ta maye gurbina kenan. Ina tsaye a gefe na kasa daidai da motsawa jiri ne ke shirin zubar dani, da zanyi gigin ɗaga ƙafata tabbas da jiri ne zai kwasheni ya zubar a ƙasa tim. "Sannu Laila Allah ya baku haƙuri. Haula kawo ruwa a bata tasha, ƙilama wani agumun aka mata danta bar gidan a haukace, tunda mu a iyakar saninmu Laila bata da iska." Cewar Yaya Halima wacce take riƙe da kafaɗun Laila. Gude ta ɗauki zani a kujera ta suturta mata ƙirjinta dashi. Ni dai ina tsaye ina kallon bariki. Ruwa aka bata tasha, Babala tace ta kwanta ta rufe idanunta. Ta ko kwanta ta rufe idanta ruf. "Toh Allah shi kyauta, Allah yasa ba mayu bane ma suka kama mata kurwa ba, kunsan jiya an yi taron na ayya" Cewar Babala wacce take hanyar ficewa daga ɗakin. Ina tsaye duk suka watse suka barni, sai muryoyinsu nake jiyowa a ƙofar ɗakina. Rigar maman Laila na bi da idanu kawai na yi ƙuta tare da shigewa ɗaki na kwantar da ƴan biyu da suka koma baccinsu nima na kwanta ina share hawaye mai zafi. A wannan dare Gwadabe ya sha rarrashi sosai, dan birkice mishi nayi kamar lalatacciyar besfa, da ƙyar ya iya shawo kaina a wannan dare. Washe gari muka wayi garin babu walwala sam daga ni har Gwadabe, dan shi kanshi ina ankare dashi da damuwar da tafi tawa ya kwana. Bayan sun dawo daga sallar asuba ya shigo, sai yace "Bari in ɗan kwanta kaina saramun yake yi sosai, zazzaɓi ne ma yake son kamani" Sai jikina yayi sanyi, a tausashe nace dashi. Allah ya ƙara afuwa, sannu inka karya ina da fanadol sai in baka ka haɗiya" Har ya kwanta sai kuma ya tashi, ina shirin ficewa a ɗakin kenan zan juyo ruwan wankan ƴan biyu. "Dawo ki zauna Iyabo mu yi magana " Babu musu ko kafiya a tsakaninmu, cikin saurin bin umarninshi na zauna ina fuuskantarshi. "Wallahi Iyabo ko tsirara Laila zata yi a gabana ba zata taɓa burgeni ba, domin bana daga cikin mazan da suka fifita kyawun mace, ko dirinta. Ni kyawun halinki, da haƙurinki ya fi ye mun komai. Ai mace ta gari farin cikin rayuwar duniya ce. Zance na gaskiya bani da wata hanya da zan bi in kori Laila a ɗakinnan. Ina gudun yawan fishin da Babala take yi a kaina. Dani dake mu yi haƙuri ki taya ni mu yi mata biyayya ta zauna ɗin,in taga dama ta zauna har mahadi ya bayyana, zata ɓata ma kanta lokaci a banza, dan ko matan duniya sun ƙare Gwadabe ba mijin Laila bane. Iyabo na ƴar duma_duma mai hanci a tsakiyar kumata itace nutsuwata. Kiyi haƙuri nasan na danneki da yawa" Shiru nayi kawai ina wani tunani, har ga Allah Ni kam ina yaye Taiwo da Kahinde aurena da Gwadabe yazo ƙarshe ma, nasan ina tafiya babu makawa Laila burinta zai cika na mallakar Gwadabe a matsayin miji. Iyakar son da zan yima Gwadabe kenan in zama tarihi a cikin labarinshi, ko dan ya samu rabauta, dan fishin iyaye bala'ine babba akan yara musamman fishin uwa al'amarin da girma yake" "Baki ce komai ba Iyabo" Ɗagowa nayi muka haɗa idanu nace. Babu komai Gwadabe, zan tayaka biyayya ma Babala ka samu aljanna ta hannunta, Laila taci gaba da zamanta kuma in sha Allah bazan sake asarar hawayena akanta ba. Dukkan wata ƙaddara ko jarabtar da zata samu bawa daga Allah ne, dukkannin wani tsanani baya dauwama face sauƙi ya samu." Ina gama faɗar hakan na miƙe na fita cikin dakiyar zuchiya muka gaggaisa da matan gida suna tsakar gida anata hada_hadar aikin daya zamema mata jiki a rayuwa. Ɗakin Yaya Haula na shiga na durƙusa a gaban Babala na gaisheta, saida nayi baki biyu kafin ta amsamun a yatsine. Yaya Halima kuwa ciki ciki ta amsa, ni banji sautin muryar tata ba ma, sai dai labɓanta da naga sun motsa. Har zan fita Babala tace. "Zo ki zauna Iyabo inason magana dake" Dawowa nayi na zauna kaina a ƙasa ina wasa da gezar majanyin ashoke dana goye Taiwo da Kahinde dukansu a gadon bayana. "Ba komai bane yasa nace kizo ba dama. Kuɗi nake son ki bani kamar dubu talatin haka, inason zan sai taki in tafi dashi, nayi magana da Baban Nazifi hidima tayi mishi yawa, ke kuma naga kin samu kuɗi a wajen suna sosai" To Babala bari in kawo miki" Na miƙe na fita ina jinjina wannan lamari. Nera dubu talatin cib na ƙirgi na kai mata, tako sa hannu ta amshe ba sannu bare madallah. Harna yi ma ƴan biyu wanka na shiryasu ina ta'ajibin wannan al'amari. Toye na ja muka fita tsakar gida nayi mishi wanka a ƙofar ɗaki ya shigo. Ban gusheba sai da na ɗauraye kayan da ƴan biyu suka cire da wanda nasa naci suna, da wanda nasa jiya, dana Gwadabe duka. Kafin in gama wankin matan gidan suka cike igiyoyin da shanya tsab. Sai mayafi na yafa na shiga gidan maƙota na yi shanyata. Ɗaki na shiga na shinfiɗe ƴan biyu a gado, Toye kuma na shafa mishi mai, yasa kaya. Ina juye ruwan wanka na mayar da ruwan kunu kan wutar. Ina fitowa na dama kunu na juye a jug ɗin silver na mayar da ɗumamen tuwon jiya. Ɗaki na shiga na shirya tsab cikin jar atampa sabuwa fil ɗinkin dai buba da zani, yana cikin kayan suna da Iyaa ta hado mun dashi, na murza kwalli da jan baki, na bi jikina da body milk na Mrs Bukhari, na shafa har a ƙasan mamana kunsan masu jego sai da ta'amali da ƙamshi. Ina gyaran falo Gwadabe ya fito daga ɗaki. Murmushi nayi mishi, shima murmushin ya sakar mun. Yallaɓai ka tashi, ya kan naka?" Bai amsa ba sai da ya haɗe jikinshi da nawa, Laila fa duk abinnan tana naɗe a doguwar kujera tana bacci. "Lafiya lau Iyabo, sai kewarki a shinfiɗata. Irin wannan kyau haka Babbar mace kenan, cinyar sa maganin mai haɗama" Dariya muka kwashe dashi kamar babu matsalar dake damun mu. Inason in ji Gwadabe ya kirani da Cinyar sa maganin mai haɗama, ko Babbar mace, daya faɗa sai in jii ƙibata ta sake burgeni, barenma in nai kwalliya, dan kwalliya tafi amsar masu jiki irinmu. To yanzu dai karyawa zaka soma yi ko wanka?" Ido ya kashe mun yace. "To ba sai ki zaɓar mun ba kawai, tunda dai ni mijin Hajiya ne" Ina dariya ciki_ciki nace. To ka soma da wankan, zaka fi jin daɗin karyawar. Ina faɗar haka na fita, har na juye mishi ruwan a bokiti zan je rijiya in sirko, sai ya riƙe hannun bokitin ƙarfen yace. "In banda fitina irin taki kina jego ina ke ina aiki, gafara cus kawai." Ya ɗauki bokitin yayi bakin rijiya dashi. Baban Nazifi dake zaune a turmi yana rage ƙasumbarshi da aska, ya ja tsaki yace. "Allah wadaran naka ya lalace, Laila da majnun ma ƙarshen tarihin soyayyarsu sam babu armashi a ciki. Gwadabe kayi asara shanyayye fitsararre" Ya ci gaba da askinshi, ni kuma na shigewata ciki. Ina haɗa mana abun karyawa a tire mandiya hamshaƙiya ta tashi. Tsaki ta buga, ta fice fuu. Ni kuma na girgiza kai kawai na dure mana abincin a gefe, ni na tattare mata kayan rufarta na sa mata a saman akwatunanta. Na kunna turaren tsinke na Baba flora ɗakin ya biɗe da ƙamshi. Ina zaune ina kallon wani kaset ɗin yarbawa, shiru_shiru yau Gwadabe zai shigo, gobe ne, har goman safe bai shigo ba. Ni kuma yinwa sai sasiƙata take yi, abinci na zuba na soma cin abuna. Ina kan ci wayata na jiyo kukanta daga uwar ɗaki, da sauri na shiga ɗakin. Wata number ne ba suna, ina karawa a kunne na jiyo muryar Gwadabe. "Nine Iyabo. Kiyi haƙuri muna asibiti tare da Babala. Na je dubata na tarar zasu koma asibiti shine muka tafi tare, muna gamawa zan dawo. Kici abincinki kinji? Zan tawo da cefane" To Shikenan Gwadabe Allah ya ƙara mata lafiya, sai kun dawo. Dan Allah ka gaisheta sosai da jikin." "To shikenan Babbar mace zata ji, ki kula mun da kan ki" Mu kai sallama na ajjiye wayar. Ina gama karyawa sai na shige ɗaki har bacci ya soma ɗibata sai naji ana tattaɓani kamar a mafarki naji ana kiran sunana. Ina buɗe idanu naga ashe Uwani ce." Kai Uwani irin wannan duka haka" Na faɗa ina miƙewa zaune. "Ke dai bari Iyabo, damuwace ta ciyo ni shine na kasa haƙuri sai da na tawo. Amman kafinnan akwai abinci a gidan in ɗan sama cikina, tun duku_duku na bar gida babu abunda naci" Ki fita falo zaki ga tire akwai dumamen tuwo da kunu" "Yanzu kuwa zaki ji labari Iyabo in na take cikina" Fita tayi sai gata da tuwo shaƙe da kwano da kununta cikin ƙaton kofi, bayan taci ta yi gyatsa tace. "Tun safe ni da matan gidanmu muka fita muka bazama gari neman aikin yi yinwa na shirin halakamu da yaranmu. Da ƙyar muka samu aiki mu huɗu. Wani sabon asibiti da aka buɗe a bakin titin layinmu to anan ni na samu nawa aikin na wanke bayangidun asibitin, Hafizu kuma Allah ya so shi ya samu gadin get da ƙyar wallahi, a hakanma saida nayi mishi jan ido ya karɓa, gani yake shi yafi ƙarfin gadi, matar gidanmu kuma nata aikin shara da goge gogen ƙasa ne. Iyabo albashin bashi da yawa sam wannan rayuwa ni nama rasa yadda zan tsoma kaina a ciki ga matsalar gidan haya. Shaddarmu fa wata biyu kenan data rufza me gidan yace bazai gyara ba mu da muke haya a gidan mu zamu gyara. To mu bamu ci ba balle har mu iya gyara masai sai dai fa ko wacce mata tayi kashinta a po ta ɗauka taje ta watsa. Gabaki ɗaya gidan sai wari kawai" Jigum nayi ina saurarenta, yinwa bata da daɗi sam ni kaina a baya mun sha kwana da yinwa mu wayi gari babu abinda zamu ci sai ruwa. Uwani rayuwar ta zama sai a hankali, gashi mutane basa son taimako daga ƙwauri sai guiwa kowa nashi ya sani. Amman a ƙalla aikin zai rage muku sosai, sai ku gina rayuwarku akan albashin da kuke ɗauka kusan yanda zaku tsara komai. Allah yasa dai mu dace kawai amman rayuwarma wataran sai kaji duniyar ta fice maka fit a ranka in matsaloli suka haɗu suka cakuɗe maka. Jiya da kinga irin tashin hankalin dana faɗa da daddare da kin tausaya mun sosai" Nan na kwashe labarin iskancin Laila na bata. "Kusun uwa kuma baki yi kukan kura kin dira a wuyanta kin narki shegiya ba?" Kai na girgiza tare da cewa. Hmmm motsi ma wannan na kasa. Ni da nake zaune a ɗofane Uwani ai ina taɓata zata jijjigemun auren nawa ne, kinga burinta ya cika ai ko?" Sai kuma ta sakko tace. "Sai dai dan hakan amman in ba haka ba wallahi da saita gane kuranta. Amman ke haka zaki zuba ido kuci gaba da zama da'ita ko yaya kike so?" Miƙewa nayi tsaye na ɗauki Taiwo na saɓa a baya, na sake sa hannu na ɗauko Kahinde sima na sashi a kusa da ƴar uwarshi, na ɗamaresu tamau da zanin goyo na bisu da majanyi. Hijabina na zura, na saƙa hannu a ƙasan kayana dake jere a wadrop na ciro kudaɗe na soke a giyo. Mu je ki rakani in yo cefane kinji in ɗaura abincin rana, dan Gwadabe suna asibiti da Babala, bansan ko gado za'a kuma basu ba, ko zasu dawo gidaba, ya kamata in gama abinci da wuri" Fita a gidan mu ka yi muna tafe sai tauna matsalolin dake ci mana tuwo a ƙwarya muke ta ta faman yi. A wajen wata beyerabiya mai kayan miya da niƙa na sai tumatiri da albasa da attaruhu, rabi na gyara a wajen na wanke ta niƙa mun, dama mun fito da robar fenti, rabi na ƙunso abina na sayi ɗanyan kifi shawa da su maggi a wajenta, Uwani ma na sai mata haɗin kayan miya na ɗari da hamshin, maggin hamsin, man hamshin, sai kifi ɗanye na hamsin, sai murna da godiya take yi mun. Muna dawowa gida na shiga aikin abinci, ni ina jajjage Uwani na yi mun tsintar shinkafa. Matan gida sai shewa suke yi, ko wacce tana girkinta a ƙofar ɗakinta, Yaya Haula kuwa kajine cikin tukunya take ta aikin musu jar suya gidan ya karaɗe da ƙamshi, Suwaiba kuma kifi take soyawa sukumbiya ɓula_bula, ga jajjage kayan miya tana yi, ga alayyawo ta baje akan tabarma. Kullum su kam a cikin cin daɗi suke kullum baren ma Yaya Haula tunda mijinta kusan shine mai kuɗin familyn baki ɗaya ma. Tukunya na ɗaura na zuba mai na jefa ɓararriyar tafarnuwa guda, man yana yin zafi na zuba jajjagena, na wanke kifina tas na tsaane a kwando, ai sai matan gidan baki ɗaya kallo ya dawo gareni kawai dan hakan sabon abune a tukunyarmu gaskiya, barmu dai da yin fara da mai, ko tuƙa amala da miyar ewodu ko mai babu. Yaya Haula tace. "Lallai bana abun arziki muma ya biyo ta layin gidanmu har mun samu, ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta" Sai suka saki shewa dukkansu, ni kuwa ko in kula na gama tsayar da sanwar girkina nasa ma uwani hannu muka ci gaba da tsinta. Sai bayan azahar girkina ya sauka na juye tumaturina a tukunya na mayar kan gawayi. Waya na ɗauka na kira Burodami Debisi nace inason nama na dubu biyu dan Allah ya turo yaro dashi. Bayan mun gama cin abinci sai ko ga yaro da nama cikin ƙaramar baƙar leda dam harda kayan miya cikin leda mai zane, yace kuma in bar kuɗin naman. Allah sarki ɗan uwa mai daɗi kiranshi nayi na dinga yi mishi godiya, ina ajjiye wayar sai ga kiran Gwadabe ashe sun dawo Yana ɗakin Umman Nazifi. Abinci na tafi musu dashi, na gaishe da Babala da jiki, na ɗan jima a ɗakin kafin na fito." MRS BUKHARI 3064127935 Buhari Ibrahim Ladan First bank Sanya nera 500 ɗinki kuɗin karatu anan. Wannan asusun gudauniyarmu kenan. Ki sani in kika siya wannan littafin tamkar kin taimaki iyayen marayune, dama su kansu marayun Kuzo mu yi tarayya cikin aikin lada. Ƙarƙashin Amila Foundation gidauniyar da muka buɗe ni da megidana domun iyayen marayu, ko tainakon marasa lafiya. Waɗanda suke cikin group dina mai suna (NAMA YA DAHU ROMO ƊANYE) 300 kacal zasu iya kuɗin karatu NAMA YA DAHU... ROMO ƊANYE GAWURTATTU UKU BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 8 A kwana a tashi A haka rayuwarmu tai ta garawa, yau fari gobe tsumma, babu laifi Alhamdulillah yanzu kam munfi ƙarfin abinda zamu saka a bakin salati. Koda yaushe Gwadabe a cikin tafiye_tafiye yake, duk garin da ya je yakan siyo mana tsarabar garin, su bushasshen kifi, manja, doya, wake, gawayi duk yana siyowa ya kawo. Babala ta jima sosai a gidan sai data warke tsab, ana gobe zanyi arba'in ita kuma ta tattara ta koma ƙauye. Irin ƙoƙarin da taga Gwadabe nayi a kanmu sai ya sake dagula komai. A tsakar gida Babala bata da aikin daya wuce faɗin an ma ɗanta asiri sai wahala nake bashi, ya shiga tarkon yarbawa jikokin oduduwa. In hakan baiyi mata ba sai ta sameni har ɗaki ta ƙaremun tanadi tsab, ni dai zaman gidan gabaki ɗaya ya gundureni, haka naita haƙuri har Allah yasa ta koma Takai. Gwadabe ma haka yasha haƙuri da Babala, damuwa duk ta haɗu tayi mishi yawa, ga matsala da yake samu a wajen ƴan lodi akwai wani bawan Allah da yasa Gwadabe sosai a gaba, domin yawan tashi da motar Gwadabe take yi wajen sufurin kaya, ada yafi kowa ƙwazo a matukan tirelolin har ana mishi kirari da giya dubu, akwaishi da sharara gudu a hanya dandanan sai ya isa ikko, yana isa zai sauke lodi ya sake nauso hanya. To samuwar mota a hannu Gwadabe sai ya doke giya dubu wajen ƙwazo da kazar_kazar bil haƙƙi Gwadabe yake komai. Wata rana ana ma Gwadabe lodi giya dubu shi kuma shigowarshi ƴan lodin kenan, da ya kalli Gwadabe sai yace. "Wata rana ma ba zaka samu ƙafafun da zaka taka mota ba, balle hannayen murza sitoyari in dai muna tasharnan gasa da ni ba daɗi." To daga ni har Gwadabe sai muka shiga damuwa daya dawo yake sanar dani, mu kaita adda'ar neman tsari harda sadaka, ga wannan damuwar ga damuwar Babala abubbuwa suka cakuɗe goma da ashirin. Washe garin ranar da Babala ta tafi muka cika kwanaki arba'in. Ƴan biyu sun yi kuɓul kuɓul dasu gwanin sha'awa. Tun sassafe naketa kaye_kaye dan yau kam a gidanmu zanje in wuni yawon arba'in. Kafin sha biyu na gama duk abinda ya dace, Toye na dawowa daga makaranta, na kwaɓe mishi inifom na watsa mishi ruwa, na shiryashi tsab, naima matan gida sallama. Atampa mai haske nasaka da sabon takalmi da mayafi, ina fita tun kafin in sauka daga kan tudun gidan na soma jiyo hayaniyar muryoyinsu suna gulmar da suka saba. Muna zuwa titi na tari Bus sai ƙofar Nasarawa inda anan gidanmu yake. Cikin layinmu na shiga tun daga titi nake gaggaisawa da mutane, wasu dole ma in tsaya su ga ƴan biyu a haka harna isa ƙofar gidanmu. Gidane mai ɗauke da karamar ƙofa gefe da gefen ƙofar shagunane biyu. Ɗaya na Iyaa Debisi daya na Iyaa Kokodeen. Iyaa Debisi soson danga dasu lagwani, ashana, sitati, gyalu, bula, kayan robibi. Su take siyarwa tana da injin niƙa har biyu dana wuta dana ruwa. A shagonnan mu kai rayuwarmu, akwai ƙofa a cikin shagunan wanda zaka ɓulla babban tsakar gidan namu. Iyaa Kokodeen kuma albo, garin Amala, daddawar kalwa, da bushasshen rogo, garin rogo su take siyarwa harda ma kamun jar dawa. Wannan sana'ar tasu da ita muma mu ka yi wayo muka gansu akai, gashi har yanzu ana takusawa. A bencin dake ƙofar shagon Iyaa Debisi na zauna dan na gaji sosai. Toye kuma yayi cikin gida da gudu. Iyaa Debisi tana zaune a cikin shago taci leshi ɗinkin buba ɗaurin ɗankwalinnan a cukurkuɗe sai gyangyaɗi take ta yi abunta, dama kullum aikinta kenan wannan gyangyaɗi ba'a rabata dashi, kuma a zaune ake yinshi. Iyaa Iyaa!! Na kirayi sunanta tare da ɗan buga benci kaɗan sai ta buɗe idanunta muka haɗa idanu. "Ahhh Iyabo kece da tsakar ranar nan da yara, ku yaran zamani baku da hankali ai mace mai goyo ko ciki bata fitowa sa'ilin da rana ta take. Maza shiga ciki gani nan zuwa. Mahaifiyarki ma yanzu isowarta ko awa ɗaya ba'ayi ba tana ciki" Miƙewa nayi ina fara'a dan na jima banga Mamana ba. Shagon Iyaa Kokodeen na shiga na durƙusa a gabanta na gaisheta , itama tace maza in shiga ciki rana ta take. Ko da na shiga samarin gidan basa nan kowa na wajen aiki, babu ƴan mata a gidan tuni sun jima da aure, Bose ce da aka bari itama gashi tana gidan mijinta. Sai matan ƙannen su Iyaa su su uku Iyaa Beji, da Iyaa Lekan, sai Iyaa Amope. A ɗakinmu na ya da zango mahaifiyata tana tsaye tana sallah goduwa farar bafulata siririya, gata da alkunya da sanyin hali bata iya sakewa tayi hira dani, iyakarta dani gaisuwa da tambayar ya nake ni da mai gidan nawa. Iyakar hirata da'ita kenan saita tsuke bakinta tayi shiru kanta a sunkuye." Tana idarwa ta juyo tace. "Jabu kune a tafe? ( Jabu sunan da dangin mahaifiyata suke kirana dashi kenan, dangin mahaifina kuma iyabo)" Data juyo sai naga ta rame sosai idanunta sun zurma da yawa" Dada kinzo lafiya ina wuni?" Bata amsaba sai miƙo mun hannu da tayi na tashi na sunto yaran na saka mata a cinyarta. Tayi ƙuri tana kallonsu tana musu adda'a. Take Naji hawaye na kwarara a idanuna, Allah ya ɗaura mun tausayinta sosai a zuchiyata. Inna dubeta sai inga kamar tana cikin ƙunci da matsi a gidan aurenta. Dada baki da lafiya ne naga kin rame?" Cikin gurɓatacciyar hausarta ta fulanin daji tace " E jinya nayi kusan wata shida sai dai a kwantar sai dai a tayar, shine dalilin da yasa ban ɓulloku ba." Sai kuma taci gaba da magana dani da yarbanci, dan Hausa mugun wahala take bata, dama da yarbancin muke magana." "Ashe kin samu ƙaruwa Allah ya raya. Ina ɗayan jikan nawa?" Ajjiyar zuchiya na sauke nace. Yana ɗakin Iyaa Beji can na baro shi, ya wajen Baɗɗo da mai gidanta? ( Boɗɗo ƙanwatace a gidan da Dada take aure yanzu, sau ɗaya na taɓa ganinta tal a rayuwata) "Ɓoɗɗo ta haihu tana goyon Daso an yi mun takwara" Sai naji ina kewar ƙannena da dangin mahaifiyata ma, sai naji inason kasancewa dasu. Dada inaso in zaki koma zan tambayi izinin mai gidana zan biki in gano rugarku, inaso lokaci zuwa lokaci in dinga zuwa ziyartarki ke da danginki nima ya kamata yarana su san dangina na wajen uwa su saba" Da sauri ta ɗago ta dubeni tace. "Kar ki soma, kiyi zamanki na yafe miki. Ni zan dinga zuwa ina dubaki kamar yadda na shafe sama da shekaru ashirin ina zuwa ganinki." Ƙur nayi mata da idanu ina karantar yanayinta, duk sai naga ta ruɗe, tashi tayi ta bani su Taiwo ta haye ƙaramin gadon Iyaa ta kwanta ta juya mun baya. Na rasa me ake ɓoye mun ne da Dada bata ƙaunar in ziyarceta, bata son danginta su sanni, to meke faruwa ne tabbas tana ƙasa tana dabo. Iyaa ce ta shigo tana faɗa sosai kamar zata ari baki, tana yi tana dukan cinyarta tanata faman yare. Ashe da Debisi take yi shigowarshi cikin gidan kenan. Da yare yace da'ita. "Kiyi haƙuri Iyaa nifa ba cewa nayi yemisi ta ajjiye aikinta ba, gani nayi ta fifita aikinta fiye da zaman auren da muke yine. Kuma tama ga damar zuwa ta haɗa mun jarfa ne" Ya ƙarashe a sanyaye. Iyaa Kokodeen ce ta shigo ɗakinnan tace. "Haba Iyaa Debisi wannan yaron fa yana da gaskiya kuma ma ai yayi ƙoƙari sosai Ya kamata itama yemisi ta dena zuwa tana yawon kawo ƙararshi wajenki ko wajen mahaifiyarta. Ai ga irinta nan abunda ake hango muku daban abinda kuke hango ma kawunanku daban, ku kun ɗauke mu ba wayayyuba. Dama duk namijin da zai auri soja ai dole sai dai ayi zaman haƙuri." Wannan maganar tamkar ingiza iyaa Debisi Iyaa Kokodeen tayi dama har gobe da mikin ƙin aurena da Burodami Debisi yayi a zuchiyarta. Dan da ƙyar ma aka shawo kanta bayan aurena ta zubar da makaman yaƙinta, macace mai kafiya da binbinni, gata da mita. "Basshi ai duk abinda na guje mishi kenan, shi yasa naso ya auri ƴar uwarshi Iyabo. Musamman dana fahimci ita iyabon tana sonshi. A gida ma ita ke kula da komanshi ina ga ya aurata. Yaronnan ya buɗa mana ƙasa a idanu, dana matsa ya je ya haɗoni da dangin ubanshi akazo aka danneni. To yanzu me yake so ayi mishi? Ai haka zaka je kaita kwashe takaici da baƙin cikin zama da Soja, kuma ban yarda ka sake takurama Yemisi akan batun aikinta ba." Daga ni har Burodami Debisi muka yi tsamo_ tsamo tamkar kazar data faɗa ruwa, ya ɗago mu haɗa idanu ya kasa sabida kunya tare da nadamar abinda ya aikata. Lokacin na shiga tunanowa a zuchiyata, a lokacin da Burodami Debisi ya murtsuke idanunshi yace shi Allah ya kashe shi bazai aureni ba. Ji nayi tamkar alƙiyamatace ta tsaya. Abun bai zo mun da daɗi ba, domin jaririyar zuchiyata da so da tsantsan kaunarshi ta ginu, ban taɓa tunanin zuchiyata zata iya son wani mahaluki bayan Burodami Debisi ba. Ni ban iya sa abu a zuchiyaba, ban iya son abuba. Da wasa da wasa Gwadabe ya maye gurbin dana adana Burodami Debisi a ciki, harya samu matsayin da shi kanshi Burodami Debisi bashi da irinshi. Yanzu kuwa da Gwadabe ya riga ya lasamun giyar sonshi na shiga mayen ƙaunarshi jinshi nake tamkar numfashina, ko kuma bugun zuchiyata, ina ma mijina irin son da har abada bazai iya samun macen da zata so shi kwatan son da nake yi mishi ba. Muryar mahaifiyata ne ya katsemun tunani, cikin ƙwarewa a yaren yarbanci ta soma magana kamar ba bafulatana ba. "Ai aikin gama tuni ya gama. Abinda zai faru ya faru. Jabu tayi aure harda albakar aure. Shima Debisi yayi aure harda ƙaruwar haihuwa. Ni ina ganin Toyosi ki yi haquri ki kawar da wannan batun. Kai kuma Debisi aure ai cike yake da ƙaɗdarori iri daban _daban. Ita kanta Jabu kana ji da ganin irin matsalolin da take fuskanta da dangin mijinta, auren ba daɗinshi take ji ba ana dai zaune zaman yara ko ba haka ba Alima?" Ta kai dubanta kan Iyaa Kokodeen wacce ainihin sunanta Halima, to a harshen yarbanci kuma sukan maiyar da harafin H a matsayin a misali Alima a madadin Halima auwa a madadin Hauwa, Abu a madadin Habu. To itama Iyaa Kokodeen manya da Alima suke kiranta. Ta dubi Dada tace. "Gaskiya ne sosai, mu kanmu wanne haƙurinne ba mu yi ba, namu haƙurinma na mutan da ba irin na yaran zamani ba. " Ranar Burodami yasa mita, sai an kawar da maganar sai can ta dawo da zancan baya. Har Burodami Debisi ya gaji ya bar gidan amman bata sauya zani ba. Haka dai wunina ya kasance bamu muka tashi shirin tafiya gida ba sai da magriba ta kawo kai. Akamu Iyaa Kokodeen ta bani da garin albo dana amala, bata taɓa gajiyawa muddin zanzo sai ta bani. Dada kuma ta miƙo mun ƙunshin bakon da tayo mun tsarabata. Dada yaushe zaki koma, amman zaki zo gidana ko Dada?" Kawar da kai tayi tace. "Me zai kaini gidanki Jabu, ai babu. Jibi zan koma ni kam in sha Allah " To Dada gobe zan dawo akwai saƙo da nake son baki ki ba su Baɗɗo." Kai kawai ta gyaɗa mun. Iyaa kuma ta dire tace ban isa in dawo ba, in Lekan yananan in je ɗakin zaure in kirawoshi in yaso sai ya bini ya amso saƙon" Ba dan naso ba akayi hakan. Da Lekan muka dawo gida. Ƙannena su su huɗu ne, biyu mata biyu maza. Matan na cira musu atampopi guda ɗaɗɗaya sababbi dal. Na cire ma Dada lashi da Atampa coddibuwa, Baffa kuma na cire mishi shadda guda ɗaya ce rak. Na cirama ƙannena mazan kaya kala ɗaɗɗaya a cikin kayan da Hajiya ta bani in ba Gwadabe. Dada na ƙara mata da mayafai da hijabi, da sabon takalmi dan naga takalmin da tazo dashi a ƙafarta takalmin robane duk ya sha liƙi gashi har ɓulewa yayi. Nera dubu goma na zara na miƙa ma Lekan. Yasa hannu kenan zai karɓa Laila ta shigo babu ko sallama. Banji daɗin shigowar tataba sam, bin Lekan da kayan da na soma cusa mishi a bako tayi da kallo. Lekam muje nayi ma bayani a ƙofar gida" Biyoni yayi a tsakar gidanma da idanu yuuu su Yaya Haula suka bini. Baban Nazifi ya daka mun wata tsawa fitowarshi daga ban ɗaki kenan. "Waye wannan sannan wannan kayan da Za'a fita dashi menene a ciki?" Ya jufo mun tambayar bayan ya iso gabanmu. Ɗan fodiyo dake zaune a tabarma suna ƙirga kuɗi shi da Da'u ai sai ya taso yasa hannu ya fisge ledar hannuna ya zazzageta a ƙasa komai suka zubo ƙasa. Ganin matan gidan a gaban kayan Yaya Haula harda salati yasa na fashe da kukan baƙin ciki. Jin amon muryar Yaya Harisu ne yasa na sassauta. "Ina za'a kai kayan. Shi wannan gona_gonan ƙaton da kika shiga ɗakin mijinki dashi alhalin kinsan Gwadaben bayanan fa, ko gwalen naku na yarbawan zaki shigo mana dashi?" Lekan sarkin zuchiya har zai yi magana na dakatar dashi da yarbanci cewar kar ya sake yace komai. Na mayar da hankalina kan Da'u da Baban Nazifi ya bashi umarnin wauwara kayan. Kayan maza da suka gani yasa Baban Nazifi ɗago rigar yace. "Wannan ba rigar Gwadabe bace Iyabo. Wato sace kaya kike yi ƙannenki suna zuwa da daddare suna fitarwa ko? Kenan doguwar rigar Haula data ɓata muna tunanin ruwan sama ne ya gudu da'ita ta rariya ashe kece kika sata? Asirinki ya gama tonuwa a gidannan ƙila harda ƙarshen zamanki " In kada baki in yi magana na kasa. Lekanne yace. "Wannan kayan data samu a sunan Taiwo da Kahinde ne, sauran kuma nata ne na gida, sai kayan mijinta guda biyu. Mahaifiyarta ce tazo daga ƙauye shine ta bayar a kaima ƙannenta, kuna da matsala da hakanne to? Batun sata kuma Antimi Iyabo ba ɓarauniya bace ba'a mana wannan tarbiyyar ba." Salati Gude ta saka tace. "Au ita Iyabon dama tana da ƙanne mu bamu sani ba? Sannan iyakar saninmu uwarta ma ita kanta ba tace ga inda take ba, yasar da'ita tayi tun tana ƙarama ai." Yaya Harisu yace. "To munji babu kayan da zai fita a gidannan. Kai kuma fice mana a gida" Kamar kuwa jira Lekan yake yi ya fita fuu yana sababi da yare. Da manuniya Yaya Haula ta nuna ni tace. "Wabillahillazi huwarrahmanu sai kin biyani doguwar rigata, nera dubu takwas na siyeta , tunda na kama ɓarauniyar rigar." Nan su Gude suka soma tafi tare da yi mun kururuwar naji kunya. Tsugunnawa nayi jikina na rawa na kwashe kayana zan shiga ɗaki dasu, Baban Nazifi ya warce buhun yace. "Har sai kin biya kuɗin rigar da kika sata zaki samu kayanki, Allah wadaran halinki." Tiɓi_tiɓi da kayan mazaunai na tafi ɗaki da gudu na faɗa akan gado na sau rikitaccen kuka irin wanda ban taɓa yin irinshi ba a duniya. A wannan halin Gwadabe ya dawo tafiya ya tarar dani, dan wallahi ko sallamarshi ma banji ba, sai jin hannunshi nayi a jikina, ina ɗagowa da naga shine na kife na sake rugujewa da kuka. A ƙagauce yace. "Wani abunne ya faru da kika je wunin gida ko? Iyabo kiyi haƙuri ki dena kuka akan matsalolinmu dan Allah." Banza nayi mishi da ƙyar ya iya nasarar shawo kaina na faɗa mishi abinda ya faru" Shiru yayi kamar ruwa ya cinyeshi yana riƙe da kumatunshi. Amman naga ranshi ya ɓaci ainun har jijiyoyin goshinshi sun tsaya. "Yanzu kayan suna ina, ina shi Lekan ɗin?" Cikin rawar murya nace. Kayan suna hannun Baban Nazifi, Lekan kuma Yaya Harisu ne ya koreshi." Numfashi ya ja dogo yace. "Ina zuwa ki goya Kahinde da Taiwo zamu fita." Gwadabe na kirayi sunanshi da gaggawa, kulawa ma yabawa dan ko juyowa bai ba. Ina zaune a bakin gado da goyo a bayana, sai na soma jiyo maganganu sama sama ina jiyo tashin muryoyi daga tsakar gida. Ni dai ban ko yi yinƙurin miƙewa ba, hayaniyar sai ƙara tsananta take yi, jin kamar ana titirniyar dambe ne yasa na fito da gudu, aikuwa ƙafafuna suka harɗe na faɗi rib cikina da Manana suka daku da ƙasa. Take wasu hawayen wahala suka wanke mun fuska. Abunka da mai ƙiba sai fa da dabara na miƙe ƙafata naji ta nai mun mugun zafi, a haka na daure na fita. Da'u Gwadabe ya damƙa yake ta kai mishi mahangurɓa, Yaya Harisu na riƙe da Gwadabe ta baya yana jayeshi, Ɗan fodiyo na riƙe da Da'u ga Auwal a tsakiya yayi musu iyaka. Baban Nazifi kuwa yana gefe yana sharce hawaye Yaya Haula tana rarrashinshi kamar wanda jaki ya kada shi da ƙasa. Su kuma matan gidan suna cure waje guda da yaransu maza da mata. "Ni zaka duba ka ce matata ɓarauniyace, me aka kamata ta sata da za a ci zarafinta ita da ɗan uwanta? Kaya kuma ga kuɗin rigarki Haula ku bamu kayanmu" Ban san Gwadabe na da zuchiya haka ba sai yau. Ƴan uwanshi suka rufu a kanshi da zagi da cin zarafina. Baban Nazifi ne ya jefo mana bugun kayan ya sauka a ƙirjina tab, ba da ban ina da ƙiba ba da sai na faɗi. Yaya Haula kuma ta fisge kudin hannun Gwadabe. "Gobe_gobe ku tattare yanaku _yanaku ku bar mun gidana, tunda ba da uwa da uban Iyabo aka haɗa kuɗi akasai gidan ba. Ku kuma ko wacce ta koma ciki ta ja ƴaƴanta" "Kullo ɗakin mu je mu dawo kinji Iyabo?" Ya faɗa yana haki. Da ɗingishi na koma na kullo ɗakin muka fita. Amman fa har muka isa gidanmu babu wanda yace da wani komai. Acanma mun shiga mun samu kab matan gidan da samarin gidan a tsakar gida Iyaa tana ta faman kwakwaso da sababin abinda ya abku. Ai muna shigowa ta dira a wuyan Gwadabe da zagi, har kakan kakanshi sai da ta zaga. Mahaifiyata ta kaɗa kanta ta shige ciki, Gwadabe ya miƙo mun buhun kayan na shiga ɗaki na sameta, na baro Gwadabe na ba iyaa haƙuri amman kamar ƙara ma zigasu yake yi. Ina jiyo sanda Iyaa Kokodeen ta koreshi shima waje. Da ƙyar mahaifiyata ta yarda ta karɓi kayannan, shima sai ajjiyewa nayi a gefenta. Ina gunjin kuka na nufi hanyar waje. Muryarta na rawa tace. "Jabu ki yi ma mijinki biyayya. Muddin shi yana ƙaunarki kar ki sake wannan rikice_rikicen banbanci ƙabila da aketa gwabzawa kice zaki kaso aurenki. Ko beyerabe kika aura ba tsira zaki yi ba. Dan a ƙarƙashin ko wacce igiyar aure akwai ƙalubale, in kika ji na wasu naki ba komai bane. Kice ina gaisheshi bamu samu damar gaisawa ba" Kasa amsata nayi na fice ina dingishi, a ƙofar gida na tad da Gwadabe idanunshi sun rine sosai. Haka muka rankaya gida, a daren dai ɓarawon baccine ya kwashemu muka wayi gari da labarin Baban Nazifi yace dukkansu zasu tafi Takai akwai meeting da za'a gabatar. Ni dai har Gwadabe yai mun sallama ya fita ina sharar hawaye. Ga ƙafata ta aune ta yi him. Tsabar ɓacin rai Gwadabe bai ga ƙafarba bai san ƙafar ta samu rauni ba. Haka na wuni ni dai sukuku ba laka, ƙafa fa kafin la'asar ta sake hayewa da ƙyar nake takawa. Ina zaune akan kujera ina kirɓa sakwara sai ga ƴan Takai sun yi sallama. Gwadabe na ƙura ma idanu sai naga har ya faɗa. Yana isowa ya cafe taɓaryar a ƙoƙarinshi na ganin ya kore damuwar dake cin ranshi. Ya hau dukan sakwara a turmi, dan da nan ya kammala tsab. Durƙusawar da zaiyi ya taya ni kai filas ɗin abinci ciki, sai yaga ƙafata a kumbure. "Me ya samu ƙafarli ta aune haka, kuma kike zaune kina aiki? A'a taso muje maza_maza" Babu shiri muka fice a gidan. "Ɗan iska na mamaji" Cewar Baban Nazifi kenan. Ashe targaɗe naji a idanun sawuna, mai ɗori ya gyara mun muka dawo gida. Bayan sallar isha muna zaune muna cin abinci yke bani labarin yadda akayi a takai. "Abun babu daɗi. Babala dama kinsan sai dai ma ta daɗa kwaye mun baya, gashi Goggo Iyatu tana nan mahaifiyar Laila, itama tai ta kunnawa abun wuta. Mun tsaya akan dukkan abinda ya ɓace a gidannan kece kika sace kuma ni zan biya. Wallahi nayi iyakar yina dan in fahimtar dasu fur sunƙi. Ni dai roƙon da nake yi miki kiyi taka tsantsan kuma ki iya takunki, kisa ma Laila ido sosai, kinsan na faɗa miki ƙasurgumar ɓarauniyace." Kuka na fashe dashi. Kana nufin a haka zanci gaba da zama tare da kai anai mun kallon ɓarauniya, harma duk abinda aka nema aka rasa sai na biya? Gwadabe haƙurina ya ƙare ni na...." "Kul kika bari mala'ilun Allah su yi fishi dake, Allah yayi fishi dake. Iyabo wallahi dukkan wannan abun so akeyi a samu a ukun da da kanmu zamu ji mun haƙura da junanmu, abinda suke so kenan. Nayi duk iya iyawata in kare ki, abun yafi ƙarfinane bazan tsaya ina jayayya da Yaya Hambali ba, domin uba ne, a kafaɗunshi muka girma, Balle kuma Babala da goggo Iyatu. Kiyi haƙuri ni zan dinga biyansu duk abinda suka ce an sace musu." Ya batun korarmu kuma da Baban Nazifi yayi, ba gara mu bar gidan ba, tunda in bana gidan ba mai cewa nayi sata?" Kanshi ya dafe kafin a tausashe yace. "Babala tace ko bayan rants bata yafe ma duk wanda ya bar gidannan ba. Ashe Yaya Hambali da Yaya Harisu sun sai gidajen su Malam Audi, da gidansu Baturiya, wata mai kamawa ma za'a soma aikin fashe katangun a haɗe gidajen. Kinsan bikin Nazifi da Laraba ya ƙarato, nima fa duk yau nake jin labari. Nazifi zai zauna a cikin gidannan da matarshi. Itama Laraban a cikin gidannan zata zauna. Ai kinsan Ilum ɗakin Goggo mai Yaɗiya ko? To shi zata aura, Yaya Hambali zai ɗaukeshi aiki a kasuwa. Ni dai Iyabo abinda nake so dake shine kar ki sake fita tsakar gidannan sai in fita daga gidan zaki yi, ko ban ɗaki zaki shiga. Su girki, wanke_wanke wanki duk kiyi a ɗakinki, kiyi haƙuri damo.." MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI NAMA YA DAHU... ROMO ƊANYE BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI Lamba ta tara (9) "Kinga can wajen tudun?" Gwadabe ya nuna mun da hannunshi. Wani dan tudune karami akayishi a falon kamar wajen cin abici. ( Daining )Amman bashi da girma, a wajen na saka kayan kallona. "To ki fito da kayan kallon gobe zan siyo miki teburi da dirowar da zaki dinga zuba kayan abinci a ciki. Zaki dinga amfani da risho, ke ko gawayinne in kika kunna a ƙofar ɗaki daya ruru ki shigo dashi, ki sa labule wajen ya zama miki kicin. Iyabo bana so ki sake fita na kuma na jajjada miki. Kiyi haƙuri wata rana sai labari. Ki daure wallahi ba'a sona haka ke faruwa ba, naso mu bar gidannan muyi nesa da ƴan uwa Kuka babu irin wanda banyi ba, washe gari kuwa sai ga Gwadabe da tebur, da durowarshi gajera ta kicin ɗin ƴan gayu. Tare muka jera kayan tukwanena da ɗan kayan abinci da nake dasu, har randunana a cikin wajen na jera, Gwadabe ya hau ya kafa mun labele, Laila sai zirga_zirga take yi tsakanin tsakar gida da ciki. Bai fita ba sai da ya ciccika mun randunanan da ruwa tab, kana ya fice kasuwa. Ni kuma na shiga aikace, aikacen gidan. Bani na fita tsakar gida ba sai da na gama komai nawa na fito da ruwa bokiti uku na sheƙar a rariya, bokitin dana shake shi da wanki na fita dashi na je maƙota na shanya. Ina dawowa na yi komawata ɗakina. Haka al'amuran rayuwar su kaci gaba da gudana yau fari gobe tsumma. A kwana a tashi, gashi yau mun wayi gari jama'ar Takai suna hanyar shigowa Kano. Gidan namu shaƙe da matan anguwa suna ta faman taya mu aikace_aikacen biki. Dan Yaya Haula hantsice leƙa gidan Kowa, babu gidan da bata shiga, kowa a layinnan ya santa. Gida ya ɗau fenti, ga girma da gidan ya ƙara, sakamakon gidaje biyu na jere damu da Yaya Hambali ya siya, aka rushe katangun gidan ya ƙara girman gaske, kuma yasha gyara sosai. Ɓangaren Amarya Laraba da Ango Nazifi ya sha gyara na musamman. Wajajen la'asar sai ga ƴan Takai sun iso Bus biyu su da gayyar yara raɓe_raɓe, gida ya kacame da hayaniya, amman nifa babu wanda yazo daidai da ƙofar ɗakina . Washe gari aka shiga biki ka'in da na'in. Ranar ɗaurin aure tun duku_ duku muka game jallof ɗin shinkafa, da tuwon shinkafa, harda masa. Su Gwadabe kuma suka kama hanyar Takai dan acan za'a ɗaura auren kasancewar duk haɗin gidane. Ko akwatin Amaryar Nazifi baa'a kaiba, ance in aka kawota sai kawai a miƙa. Akwatuna masu taya suna nan a ɗakin Yaya Haula, ina dai gani matan waje sunata shigowa kallon kaya. Ni ko da nake gidan babu wanda ya neme ni da in zo in ga kaya, nima ban ɗaɗa kaina ba. Bayan azahar maza ƴan ɗaurin aure suka dawo tare da bataliyar maza ƴan Takai. Da yamma lis kuma sai ga jerin gwanon tsofaffi da Amarya an tawo da'iya. Harda Sakina aka tawo, suma sun sha ankonsu na Takai. Muma duk mun ci namu ankon na cikin gida, shaddace mai ruwan toka na iyaye, sai wani yaɗi haka na ƙawayen Amarya dai. A haka taro ya watse, duk da ina kaffa _kaffa sai da Yaya Halima ta ci mun mutunci a cikin mutane, daurewa nayi na shanye dan a ranar ma Takai zasu komai. A dangina babu wanda yai mun kara yazo, Uwani ce dai na matsama bata da yadda zata yi shi yasa tazo. A kwana a tashi asarar mai rai. Wasa wasa ƴan biyu shekararsu guda, har suna dabo, Toye kuma yanata zuwa makaranta. Fitinar gidanmu kuma babu abinda ya ragu sai ƙaruwa, dan sau huɗu Gwadabe na biyan kayan da aka sata. Na huɗun ma har ƙarƙashin kujerata akazo aka saka mun, da suka shigo bincike suka zaro. Nayi imanin Laila ce ta aikata mun hakan ba kowa ba, dan tuggu da munafurci iri iri take haɗawa, tsaraicinta da aljanun ƙarya fa babu abinda laila ta dena, a wannan shekara guda ɗin abubbuwa masu dama sun faru. In baku mance ba nace ina yaye ƴan biyu zan bar gidan, to maganar tana ɗamfare a zuchiyata. Ga zawarawa kullum a cikin sallama da' Laila suke, tare da kawo mata ƙwalam da maƙulashe, amman mayyar tana kan bakarta ita sai Gwadabe. Gwadabe ne yaita bani haƙuri nima ganin na kusan yaye in barshi ma baki ɗaya shi yasa ma ban yi tafiyata ba na haƙura na zauna, na cire damuwar kowa da komai a raina. Kamar wasa wata ranar juma'a sai ga Oga Lurwanu shi da karen motar Gwadabe sun riƙo gwadabe ko iya taka ƙafarshi bayayi, suka shinfiɗe mun shi a doguwar kujera. "Gashi nan kin ganshi, mota ya shiga, amman wallahi sai zaro shi akayi ƙafa taƙi takuwa. Muna kyautata zaton sammu akayi mishi. Dama in dai a raba mutum da kafa ko hannune a harkar tuƙi ba kanshi farau ba. Sai ku dage mishi da maganin gargajiya" Hannu na ɗaura aka ina kuka, shima Gwadabe kukan yake yi yana girgiza mun kai halamar in yi shiru. "Ki gode ma Allah ma, da ba haɗarin mota akasa yayi ba ya ragargaje ba. Dan shima anayi kana tsaka da tuƙi sai kaga zaki ko kura, kana ɗauke hannunka magana ta ƙare. Wasu kuma teku suke gani a gabansu duk sai su dibibice" Ni dai sai mamaki da tsoron sha'anin mutan Duniya duk ya kamani. Nera dubu biyar ya ajjiye mun. "Mu kam zamu koma Gwadabe Allah ya ƙara sauƙi" Su kai mana sallama suka tafi. Kifewa a jikinshi nayi ina kuka kamar fitar rai. "Iyabo ki yi ta mun adda'a Allah zai bani lafiya, ta Allah ba dai ta mutum ba. Ni na ɗauka wannan jarabawace ubangijina ya jarabceni dashi. Bazan ɗaura hakkin akan kowa ba Allah yana madakata yana ji da ganin kowa. Ki yi ta mun adda'a. Kafin in amsa shi Yayyen nashi su kayo sallama suka shigo. Baban Nazifi yace. "Gwadabe haka abun ya faru? Ni ina kasuwa ma shigowata kenan mata suke sanar dani wai an shige da kai a hannu baka tafiya, haɗari ne ya afku kome? Koma dai menene Allah ya kyauta gaba. Ke bamu waje ko?" Ya juyo yana mun kallon tsana, ƴan biyu na kwashe dan kar su damu Babansu. Ina daga uwar ɗaki na kira Iyaa nake sanar mata halin da Gwadabe yake ciki. Halin ko in kula ta nuna, tsaki ma tayi ta kashe wayarta, sai Burodami kokodeen da Burodami Debisi na kira na sanar musu, sai ƙawar arziki Uwani. Su Baban Nazifi sun daɗe sosai a falon kafin daga bisani suka tafi, ni da yaran muka fito. "Iyabo inaso zan ɗaura alwala, gashi ina jin fitsari ma. Zaki iya kuwa?" Murmushi nayi ina hawaye lokaci guda nace. "Ai ko ɗaukarkane kacokam zan iya mijina. Nice a haƙƙu in yi maka duk abinda kake da buƙata" Miƙewa nayi na kai yara uwar ɗaki na kulle, falonma na kulle na tawo da ƙaton po mai murfi, cikin dabara na zamo Gwadabe izuwa kan po ɗinnan. Yayi fitsari na mai tsarki, na sake mayar dashi kan kujera. Daga ni har shi sai muka fashe da kuka na faɗa jikinshi. Allah kenan mai yin yadda yake so da bayinshi. Mutum ya fita da ƙafafuwanshi amman yanzu jibeshi a kwance, abunda yafi ƙarfi yanzu ya fi ƙarfinshi. Su Baban Nazifi daya kamata ace su zasu mai duk wannan amman kowa ya tafi ya barmu. Gwadabe kayi haƙuri kuka ba namu bane fa. Akwai Allah shi zai yi mana sakayya. Ka rungumi ƙaddararks sai Allah ya kawo maka ɗauki. Zaka warke bi izinillahi rabbi" "Iyabo ki duba dangina jinina yanda suka nuna halin ko in kula da abunda ya sameni, babu wanda ya tambayeni ko ina jin wata lalura. Yanzu ko Da'u da ba sai ya zauna ya kula dani ba?"... A'a Gwadabe kar ka ɗaura musu nauyin da ba nasu ba. Ni ya kamaci da in jinyata maka. Karma ka sake tada wannan zancan. Ga bawo kayi alwala." Shi da kanshi yayi alwala ni kuma na wanke mishi ƙafafuwanshi. Gwadabe ka daure in kai ka kan gado kaji, sai kayi zamanka acan. Yanzu nan anjima kaɗan Laila zata tashi kwanciya." "Ba zaki iya kaini ba Iyabo, ki je ki kira Da'u ko Nazifi ɗayansu yazo ya kaini, ko du su biyun." Bana so in mishi musu da To" Na amsa mishi, na fita da po ɗin da yayi fitsari na zubar, sai da na mayar ƙarƙashin gado sannan na je kiran Nazifi da Da'u tare da sanar dasu saƙon dake tafe dani. Abun mamaki ko da suka kinkimeshi su biyun dukkansu sai mitar yayi nauyi suka dinga yi, ƙafarshi ɗaya ma basu kama ba sai janta su kai kii. Ni ko ina durƙushe ina hawaye har suka fice ina kuka. A wajen su Yaya Haula suka shigo suka sameni idanuna sun ƴi luɓu_luɓu dasu. "Ohh ni ƴarnan mutum ba a bakin komai yake ba, yau_ yau ɗinnan Gwadabe ya zama musaki sai an kwantar sai an tayar. Sannu Iyabo kinji sannu" Kalmar musaki data faɗa ya dafani sosai. "Kaimu muje mu yi mishi sannu ko. Laila sai ki kwashe kayanki ki ko ɗakin su Halima da Ƙauwama sai ki koma kinga ƴan zuwa dubiya zasuita sunturi kuma dole falo za'a dinga fito dashi" Ni dai gaba nayi suka biyoni. Suka gama gaisheshi suka fita. Ni kuma ina gefenshi ina tofa mishi adda'a a ƙafar tashi, shi kuma yana kallon silin yayi wani irin sanyi" "Iyabo kinga irin riƙon wulaƙancin da Da'u su kai mun? Kinga yatsan ƙafata ya fashe. Daga kwanciya lalura yau _yau harna soma fuskantar wulaƙanci, sai kace ba ciki ɗaya muke ba. Wannan ƙiyayyar dame tayi kama, ki duba fa yanda su Yaya Hambali suka zo suka dubani wallahi babu damuwar komai a fuskokinsu, sai cewa su kai nima karambanine yasa na shiga sana'ar da bani da ilimi a kanta. Wai sana'ar hatsari gareta." Hawayene suka gangaro daga idanunshi izuwa fuskarshi. Rarrashinshi na dinga yi, a ƙoƙarina na ganin na faranta mishi rai, wala Allah ya samu sassauci. Ruwan ɗumi na zuba a bawon na tsoma tsumma na ɗan gargasa mishi yatsan nashi da yake jini. Ya samu yayi sallah, na bashi abinci a baki da kaina, ina bashi ina sake yi mishi nasihu masu ratsa jiki, akan ya gode Allah ma da ba hatsari yayi yaji raunuka masu yawa ba, da izinin Allah muddin muka dage da adda'a koma sammunne Allah zai bamu nasara, amman zuwa gobe zamu je asibiti. "Babu ko ficika a jikina Iyabo, kuma kinga asibiti sai da kuɗi Iyabo" Haba Gwadabe, zan siyar da atampopina in samu ɗan kuɗin da zamu riƙe a hannunmu, mu gode ma Allah muna da abinda zamu ɗaga mu siyar ma. Ina zuwa da zafi_zafi akan daki ƙarfe. A zabure na miƙe na shiga zaro atamopin sunan ƴan biyu, kala goma na fitar na zuba a bako. Gwadabe bari in je shagon me sai da atampopinnan ta bakin titi yarenmun nan, bazan jima ba, ga yara a falo" Ban tsaya jin abinda zaice ba na fice, sai dai kunsan mutane in suka ganka cikin matsuwa ka fitar da abu zaka siyar, sai su dinga yi maka tayin wulaƙanci. Dubu goma sha biyar ta taya atampopinnan kuma manyan atampopi harda Holland, da ƙyar muka ƙarƙare a sha bakwai da ɗari biyar. A cikin daren yau daga ni har Gwadabe kusan kwana mu kai muna Sallah muna adda'a, wallahi har akai sallar asuba bama ko jin digon bacci sai jarababben ciwon kai daya jarabeni. Ana fitowa Sallah na jiyo sallamar maza a ƙofar ɗakinmu. Baban Nazifi ne yake sanar dani dattawan unguwane suka zo duba Gwadabe. Hijabi nasa kafin nace su shigo. Gaggaisawa mu ka yi dasu, tare da yi mun jajen abinda ya faru, daga bisani kuma suka shiga ciki dubo shi. Ni dai jigum nayi a wajen na rasa me ke yi mun daɗi, a wajen suka fito suka taddani, su kai mun sallama suka fita. Ruwan wanka na juyo a bokiti na shiga da sallamata. Na samu Gwadabe yayi jigum yanata aikin tunani, na sani ban isa na hanashi tunani ba, domin jiya uwar haka da lafiyarshi ras ya fita. Gwadabe bari in ɗan goggoge maka jikinka da tawul sai ka yi asuwaki mu samu mu je asibitin ko?" Sai da ya sauke nannauyar ajjiyar zuchiya yace. "Na yi ma Yaya Hambali magana kan batun asibiti da muke son zuwa. Bai goyi bayan hakan ba, yace ciwon yafi kama da sammu, tunda babu inda yake yi mun ciwo, sai nauyi da ƙafafuna su ka yi, kuma Oga lurwanu ma yace sammu ne" Hakane Gwadabe, amman zuwa asibitin ai yana da amfani, in muka je suka auna basu ga komai ba shikenan sai a yi na gargajiyan "E haka na ce mishi nimaa. Ya dai ce Da'u zai tsaya mu tafi asibitin tare." Goggoge mishi jikinshi nayi tas, na saka shi a po ya rage mararshi, yayi asuwakin zamani, kana na bashi tea da burodi, da ƙyar yaci burodi yanka ɗaya, ni ko iyaka shayin kawai na kurɓa, mu ka jiyo sallamar Uwani. Miƙewa nayi na fita falon ina sharar hawaye, ita kanta uwanin kuka take ta faman yi. Muna cikin haka Da'u da Nazifi suka shigo, basu kula mu ba, ciki suka wuce abinsu. Ni kuma na sallami Toye ya tafi makaranta. Fitowa dashi suka yi, Da'u sai tsaki yake yi. Mu dai bayansu muka bi, ashe sun kira tasi tana tsaye a ƙofar gida. Asibitin Murtala muka wuce, ganin halin da muke ciki sai wani likita yace bari ya bamu gado ayi duk binciken daya dace a tsanake zaifi. Hakan kuwa akayi aka bamu gado a Ward ɗin maza, Da'u da Nazifi kuma jin an riƙe mu a asibiti sai suka yi tafiyarsu. Hawaye kawai nake sharewa, likita yace mu zauna daga waje. "Yanzu tsabaragen ƙiyayya yana ciwon ma ba zasu taimaka mishi ba, a lokacin da yafi buƙatar taimakonsu ba. Tafiya fa suka yi Iyabo" Takaici da damuwa duk suka taru su kai mun yawa sosai. Muna zaune aka fito da Gwadabe a keken da ake tuƙa guragu zasu tafi ayo mishi hoto. "Baiwar Allah ya kamata ace akwai wani namiji da zai tsaya tare da marar lafiyan ba ke mace ba, kinga da su zasu sashi a keke, kuma su tuƙashi zuwa ɗakin hoto. " Nurse ɗin daya tuƙo Gwadabe ne ke magana. Gwadabe na kalla, shima ni yake kallo ya dafe kanshi da hannun dama, idanuwanshi tamkar garwashin wuta. To mun gode, suna hanya masu kula dashi ɗin." Na faɗa mishi haka, kafin ya miƙo mun wata takadda. "Ki je wancan tagar ki biya kuɗin hoto, in mun fito sai ki bari in mun dawo ki bani" Karɓa nayi jikina na rawa, su kuma suka wuce. Kuka na fashe dashi babu ƙaƙƙautawa, Taiwo da Kahinde suna ganin ina kuka suma sai suka soma kukan. "Iyabo kije ki dawo, wannan kukan ya isa haka kinga ga yara suma sun soma. Jakata na kinkima na je na biya kuɗin hoto na dawo. A taƙaice sai da muka wuni zumbur babu wanda yazo daga dangina ko na Gwadabe, Hafizu mijin Uwani ne ya kawo mana abincin da muka ci, da naga magriba na shirin yi na dubi Gwadabe nace. "Inaso zanje gida in dafo ruwan zafi, in tawo da tabarma." A'a su Babala suna hanyar zuwa. Ɗazu da likita ya kiraki Yaya Hambali ya kira ni a waya" Baima gama bayanin ba sai gasu sun iso dukkansu, harda Yaya Haula tana riƙe da filas na ruwan zafi da kular abinci. Da sauri na tashi a kujera na ba Babala waje ta zauna. Abu na farko daya fito daga bakinta shine. "Ba ga irinta ba, akan son gwanance mace kaje ka kai kan ka mahallaka. Waya sani ma ko daga danginta ne aka bugo maka wani agumun. Duk da sammu a tsakanin direbobi abune mai dogon tarihin gaske muma munsan tarihin. Gwadabe bazan yi maka baki ba, amman kaji na rantse maka da girman wanda yayi ni yayi ka buwayi gagara misali. Kana tashi zaka sallami wannan matsiyaciyar ka auri Laila, in ba haka ba sai in tsine maka ka bi duniya uban kowa ya rasa ka. Banga riba a aurenta ba sai ci baya da koma baya da rayuwarka tayi. Ke kuma na dawo kan ki, ki zauna da shirinki, Allah na tasan kafaɗarshi ƙarshen zamanki kenan dashi, ya'isa haka, inason yarona ya dawo yanda yake. Kin shigo cikin zuriyarmu kin tarwatsa mun kan yara." Da kuka taƙarashe zancen, yaranta na bata baki kan ta dena kuka. Baban Nazifi ya ɗaura da cewa. "Ya zame mishi dole ya rabu da'ita matsawar mune danginshi. In kuma zai sake iyaye da ƴan uwane sai mu gani. Sabida wannan baƙar kadarar matar tashi marar asali yasa na kasa tallafama Gwadabe Babala, amman a baya wanne irin so ne banyi mishi ba." Wannan yace wannan, wannan yace wancan kowa sai da ya tofa albarkacin bakinshi. Mu dai mun yi shiru kamar ruwa ya cinyemu. "Babala kima Allah kar ki zama silar rabani da Iyabo, son gaskiya take yi mun, bazan iya samun macen da zata soni rabin nata ba. Iyakar zamana da'ita babu abunda ta taɓa yi mun na assha." Miƙewa Babala tayi tace. "To gaka ga Iyabo. Ta maye maka gurbina dana ƴan uwanka da baka da tamkarsu. Ta zauna tayi jinyarka, ni kuma babu ni babu kai. A cikinku duk wanda ya tsaya ya kula dashi ban yafe mishi ba, ko ya cire dukiyarshi ya ba Gwadabe. Haula ɗauki abincin da kika kawo mu koma dashi. Da gudu nasha gaban Babala ina haki nace. Babala kiyi haƙuri ni nayi miki alƙawarin Gwadabe na warkewa a ranar zan bar gidanshi rabuwa irinta har abada. Bazan iya tafiya in barshi a wannan halin bane, ko babu komai uban Ƴaƴanane, kuma a zamanmu bai taɓa cusgunamun ba. Nima dashi da aurenshi ya fice mun a raina, wallahi ko baki ce ba ya zama dole in rabu da Gwadabe dan ba shi bane autan maza ba, kuma ba mutuwa zanyi ba. Amman fishinki masifa ne, yana buƙatarku yaya Harisu, Babala Gwadabe na buƙatar adda'arki" Duk wannan maganar cikin dimuwa nake yinta. Majinyatan dake kwance, da masu jinyarsu kab hankulansu a kanmu yake. Tsawa Babala ta daka mun. "Gafara dallah. Ke baki da uwa dama da sai in ce ki je kisa ta mai adda'ar mana. Tunda akan ki wannan ciwon ya same shi, ke zaki yi mishi jinya dan ubanki" Fuu suka fita suka barni. Bansan sanda na durƙusa a ƙasan ɗakin ina salati ba, Allah nake ambato a lokacin wani irin duhu ne ke mamaye mun idanuna. Uwani ce ta ɗaga ni. "Tashi Iyabo meye haka kike kuka kamar ƙaramar yarinya, ɗakinnan kab ke suke kallo. Rabuwa da Gwadabe shi ya fiye miki." Jaye ni tayi ta zo ta zaunar dani a kujera. Gwadabe yana kwance idanunshi a buɗe suke amman yayi zurfi a cikin tunani hankalinshi baya tare damu. "Bara in fita bakin asibiti in siyo muku ko da tuwo ne. Zan yi ma Hafizu filashin in ya kirani zan sa ya kawo ruwan zafi." Bani da niyyar bata amsa, itama bata buƙaci amsar tawa ba ta fice. Ƴan biyu suna ƙasa na shinfiɗa musu ɗankwalina suna bacci. Har Uwani taje ta dawo ni da Gwadabe babu wanda ya tanka ɗan uwanshi. Tayi yin duniya muci abinci mun ƙi yarda, damuwar da take gabanmu ta wuci a tsaya ana saka lomar tuwo a baki, ni in banda ɗaci babu abunda bakina yake yi. Mijin Uwani ma yazo yayi roƙon duniya kan mu ci abinci, ni ko magana na kasa, Gwadabe ne ma yake iya cewa a ƙoshe yake. "Iyabo ki taso mu je gidana, in yaso Hafizu zai kwana gobe mu ma dawo" "Ku barta tare dani, ina buƙatarta a kusa dani, damuwar zata yi mun yawa" Cewar Gwadabe, sai lokacin hawaye suka surnano da idanun Gwadabe wasu sirara. Uwani ta tattare yaran su kai mana sallama suka tafi. Da ƙyar ma'aikatan kiwon lafiya suka barni zan yi jinyar Gwadabe kasancewar ward ɗin na maza ne, akwai wata mata itama ita take ma mijinta jinya, sai muka zama mu biyu. Shiru wajen ya ɗauka na kasa rarrashin Gwadabe shima ya kasa rarrashina. Wannan daren na ba makaranta gari ku hasaso da kawunanku. Washe gari sassafe aka sake zuwa aka fita da Gwadabe zuwa wani hoton. Kafin a dawo dashi sai ga Yemisi da Burodami Debisi, da Lekan. Hannunsu riƙe da lodoji. Shigowarsu ke da wuya aka shigo da Gwadabe. Da Burodami Debisi aka kinkimeshi zuwa gado. "Sannu Gwadabe ya jikin, ashe abunda ya faru kenan?" Cewar Burodami Debisi. "Jiki sai godiyar Allah, Iyabo likita yace yana son ganinki" Tashi nayi na nufi ofishin likita. "Duk binciken mu ya tabbatar mana komai nashi lafiya suke. Mun yi hoto har sau biyu bamu ga komai ba. Mun sallameku inaga ku nemi na gargajiya zaifi. Ina mai baku shawarar ku sai mishi keken tuƙa marasa lafiya, yafi muku sauƙi da a dinga kinkimarshi. Ga takaddar sallama, kije ki biya Allah ya ƙara sauƙi" Sai da na share hawayena kana na amshi takaddar bance mishi komai ba na fita. Kuɗin hannuna sai da suka ƙare tas ban tsira da ko ficika ba. Burodami Debisi da Lekan su suka taimakeni wajen ɗaukar Gwadabe muka samu Taxi ta kaimu har ƙofar gida. Baban Nazifi da Yaya Harisu suna tsaye a ƙofar gida su Lekan suka zo suka shige da Gwadabe, na mara musu baya. Tunda muka dawo maƙota sukaita tururuwar shigowa gaishe da Gwadabe, su Iyaa Debisi ma sun tawo kusan dukka gidan, sun kawo abinci da dubu biyar, haka mu kaita karɓar jaje daga mutanen arziki. Babala kuwa a bakin Gude nake jin wai ta koma Takai Laila ma ta je ganin gida. Atampopi na na ɗura a buhu kab harda ma ɗinkakkun bar bari ba, kala huɗu na ware kawai, na ɗauki buhunnan na fita hankali da nutsuwata basa tare dani sam. Siyan wulaƙanci sosai akaima kayan, amman biyan buƙata yafi godon buri, Gwadabe mutum da ɓari ne a wajena. Keken ɗaukar marasa ƙafa ko tsofaffi na siyo ta hannu akan nera dubu ashirin da biyar da ɗari takwas. Ina shigowa gidan kallo ya dawo gareni, ni dai babu wanda na kalla takaina kawai nake yi. Ko Gwadabe yasha ruwan mamakin ganina da wannan wul ciya sosai. Ni dai bance uffanba na tallafeshi na sashi a kan wul ciya ɗinnan. Hawaye ya soma sharewa, ni kuma ina mishi murmushi. "Mala'ikun Allah ku shaida na sama rayuwar Iyabo albarka, kuma na ɗaga mata ƙafafuna domin ta shiga aljanna. Allah yai miki albarka ya kawo mana mafita akan jarabawar da take kanmu" Ameen Gwadabe, ka dena kuka. In sha Allah tunda ina nan kafi ƙarfin zubar da ruwan hawaye." Daga haka muka shiga suntirin bin masu magungunan gargajiya, mu ke nan kullum a tafe, amman babu canji kullum jiya e yau. Tafe tafe sai da mu ka kwashe tsawon wata uku muna abu ɗaya. Dangina da suke ɗan tallafamun suma suka gaji suka watsar. Babala sau biyu kaɗai tazo ta duba Gwadabe, amman ƴan Takai kam sun zazzo sosai. Sakina da Bara'u kam mayar da gidanmu su ka yi kamar aje kasuwa a dawo. Duk wata jigilar zuwa nemo maganin makarin sammun da akaima Gwadabe, tare da Bara'u da Sakina muke zuwa. Abincin da zamu ci Bara'u ke kawo mana. Ayashe da Tamu suma sun mana ƙoƙari sosai. Babbar damuwata ɗaya ce tak har yanzu babu wani sauƙi da aka samu." MRS BUKHARI 3064127935 Buhari Ibrahim Ladan First bank Sanya nera 500 ɗinki kuɗin karatu anan. Wannan asusun gudauniyarmu kenan. Ki sani in kika siya wannan littafin tamkar kin taimaki iyayen marayune, dama su kansu marayun Kuzo mu yi tarayya cikin aikin lada. Ƙarƙashin Amila Foundation gidauniyar da muka buɗe ni da megidana domun iyayen marayu, ko tainakon marasa lafiya. Waɗanda suke cikin group dina mai suna (NAMA YA DAHU ROMO ƊANYE) 300 kacal zasu iya kuɗin karatu https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm NAMA YA DAWU ROMO ƊANYE GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 10 Duk wannan ƙibar tawa da kuka ji labarinta, wallahi ta zuge sosai, na gama ramewa na fice a hayyacina sosai. Shi kanshi Gwadabe yafi tausayina fiye da kanshi. Bara'u kullum a cikin jinjina ma ƙoƙarina gami da amanaa suke yi. A kullum roƙona shine Allah ya ba Gwadabe lafiya, ya yanke mishi wannan zaman. In zaman cikin ya isheshi shi da kanshi yake tuƙa kekenshi ya fita ƙwar gida ya sha iska. Mun gama siyar da komai namu kuɗin ya ƙare a magani, ɗakina goduwar kujer da kafet kaɗai ya rage, sai tarkacen kwanuka da katifa , itama sabida Gwadabe na barta Wata rana ina zaune ina wankin kayana dana yara sai ga Uwani ta shigo, Gwadabe kuma yana ƙofar gida ya ɗan fita shan iska "Uwar biyu wanki kike yi ne?" Wallahi kuwa, daga ina haka na ganki afujajan?" Na tambayeta tare da kallonta. Sai da ta cire mayafinta kana tace. "Hmm wata harkar arziki na samo Iyabo. Kin ganni daga cikin gari nake gidan Hajiya salamatu, wata matace dake kai ƴan mata da matan aure ƙashashen larabawa ko ƙasashen turawa. Amman kafinnan na samo miki maganin karya sihiri garanti, daga cikin ayayoyin Qur'ani mai girma. Bari in karanto miki, muddin kuka riƙe wannan da izinin Allah kuka yazo ƙarshe a cikin kwana na bakwai Gwadabe zai miƙe da ƙafafuwanshi." Ina jin haka na zabur na saki wanki. Na juyo na zuba mata idanu. Dan Allah faɗi ina saurarenki Uwani" Dariya tayi tace. "Ɗakko biro da takadda ina faɗa miki kina rubutawa, da izinin Allah waraka ta zo." Da sauri ba shiri na yago takadda, na ɗakko fensirin Toye na dawo. "Da farko zaki samu ruwanki mai tsabta. Sai ganyen magarya koraye bushewar inuwa guda bakwai. Sai a karanta suratul fatiha a cikin ruwan da aka zuba magaryan, a dinga karantawa numfashin baki na komawa cikin ruwan Sai a karanta Ayatul kursiyyu ( aya ta 255 na cikin suratul baƙara). Sai a karanta suratul a'afaaf daga kan aya ta 106 zuwa kan aya ta 122. Sai a karanta yunus daga kan aya ta 79 zuwa kan ta 82. Suratul kafirun ƙafa ɗaya. Falaƙi da nasi ƙafa uku_uku Sai a karanta wannan adda'ar. Allahumma rabban nas,azhibil ba'as ashfi wa antash shafila shifa'a illa shifa'uk shafi'un la tugadiru sakaman Ƙafa uku za'a karanta. Sannan za'a iya karawa da wannan adda'ar "Bismillahi urkika min kulli shai'in yu'uziyaks wa min sharri kulli nafsin Allahu yashfiyka, bismillahi urkika Shima ƙafa uku In sha Allah ta'ala idan aka karanta wadannan kuma mutum ya dinga sha sau biyu a rana safe da yamma, yana kuma wanka dashi a waje mai tsabta, ko kokuma a jiƙa tawul a goge jikin marar lafiyan da ruwan maganin. Da izinin Allah cikin sati ɗaya mutum zai warke in dai sihirine a jikinshi. ( Kuma zaku iya jarabawa. Wasu malaman sun ce yana da kyau wanda yake da lafiyarshi ma yayi, domin hakan ka iya zama rigakafi kafi magani kareshi. Wallahu mista'al) Wawuyar ajjiyar zuchiya na sauke tare da yaƙinin sauƙi ya zo ma Gwadabe. Duk da abaya masu magani sun bamu wasu mayuka tare da tofin ayoyin Allah a ciki mun yi amfani dasu da dama. Wasu kuma mu da kanmu muka zubar dasu, dan ganin shirka ta shiga cikin lamarin, amman wannan sai naji na samu nutsuwa dasu ainun. Nagode sosai ƙawata Allah dai ya bar zumunci. Bari ki ga da zafi zafi ake dukan ƙarfe bari in wanko ganyen magaryana, ina da ruwan sama cikin robar fenti sai in yi dashi. Sai fa na gama zan samu nutsuwa." Da sauri na je na ɗebo ganyen magarya adadin na buƙatar na wanko, na kinkimo ruwa da Qur'ani izu shittin. "Af na mance sai an daddaka ganyan magaryar ake zubawa." Cewar Uwani kenan. Da haanzari na ɗauko turmi na daka na zuba a cikin ruwan da bismillahi. Sai da muka kammala na samu nutsuwa har na sauke ajjiyar zuchiya. Daki na kai ruwan maganin na adana kana na fito." "To bani labarin abinda ya kai ki gidan Hajiya Salamatu, uwar shige_shige Uwani" "Wallahi Iyabo ƙasar zan bari zan tafi nemo kuɗi. Amman shekara biyu kawai zan yi in dawo" Zare idanu nayi ina dubanta da mamaki. Ƙasar fa kika ce, to aurenki da yaranki a hannun wa zaki barsu Uwani?" Ajjiyar zuchiya ta sauke tace.."Hafizu zai lura dasu Iyabo. Wannan talauci namu yayi yawa. Duk abinda Hafizu fa ya soma babu albarka sam a ciki. Kuma shi ba jari ba. Ke yanzu haka maganar da nake yi miki ma ina gidanmu fa da yaran. An koremu a gidn haya ko ince miki an watso mana kayanmu tsakiyar layi da ranar Allah. To Hafizun ma shi ya bani shawarar ko zan nemi aikatau na ƙasashe da ake zuwa, ƙanwarshi ma yanzu haka tana Canada a gidan aiki, shima in ya samu tare zamu tafi. Ni fa Iyabo wallahi tafiya zanyi. Su Hajiya ma basu san me ake ciki ba. Babbar damuwar shine ita Hajiya Salamatu tace sai dai in ajjiye dubu Hamsin da kuma ni zan yi ma kaina fasfo. In kuma ba haka ba duk zata yi mun amman zan kai wata shida kafin in gama biyan kuɗin da duk ta kashe mun. In kuma na yi fasfo na ajjiye dubu hamshin, da zaran na tafi a cikin wata biyu zan gama biyan kuɗin girji" Ajjiyar zuchiya na sauke nace. To amman babu wani haɗari a cikin tafiyar dai ko. Kuma ina fatan bata ɓarauniyar hanya za'a tura ku ba Uwani, kuma kin tabbatar Shekara biyun zaki yi ki dawo, kuma zaki iya kare mutuncinki a matsayinki na matar aure, bahaushiya ƴar Najeriya, najeriyarma Arewa?" "To Iyabo ina kyautata zaton hakan. Ke kinga mata aure masu tafiya kuwa? Wallahi sun fi ƴan matan yawa, harda dattijai fa baki gani ba. Kuma ba ta ɓarauniyar hanya zamu bi ba, ta hazo zamu keta " Shiru nayi ina ɗan nazari. Kafin ince da'ita wani abun sai ga Gwadabe ya shigo akan kekenshi. Wannan dalilin yasa dole muka katse hirar tamu. Uwani tai mana sallama ta tafi. Tun daga ranar na soma ba Gwadabe ruwan addu'o'in nan safe da yamma, haka kullum sai na goge mishi jikinshi da ruwan maganin. Allah al Hakim cikin kwana na tara da rana kawai sai ƙafar Gwadabe ta motsa kamar da wasa. "Iyabo ƙafata na motsawa" Na ji ya faɗa cikin zabari. Kafin ma in ƙaraso inda yake harya miƙe tsaye. Suddajar godiya ga mahalicci mu ka yi a tare. Muna ɗagowa Gwadabe ya rungumeni tsam a jikinshi yana shafar bayana, tare da sama rayuwata albarka. "Iyabo kinga ikon Allah ko? Haƙiƙa na sake tsinkewa da lamarin Ubangiji Allah. Allah na gode maka daka bani lafiya. Ya Allah dukkanmin mai ruwa da tsaki akan wannan rashin tafiyar tawa ya Allah ka nuna mishi iyakarshi" Ni kuma sai amsawa da ameen nake yi. Ko yara da suka shigo suka ga Abbansu akan ƙafafunshi sai suka shiga murna harda tsalle. Rungumesu yayi dukkansu. Farin ciki da jin daɗi bazai misaltuba, bazai rubutu ba balle har mai karatu ya fahimta" Bara'u shine mutum na farko daya samu labarin warakar Gwadabe. Ni kuma ta ɓangarena Uwani na soma sanarma, kafin na sanar da gida. Na leƙa tsakar gida duk suna tsakar gidan ko wacce tana aikin girki nace. Ku ta ya mu murna Allah ya ba Gwadabe lafiya, ciwo ya warke" "Warkewa fa kika ce Iyabo?" Cewar Gude, kafin in bata amsa Gwadabe ya fito tsakar gidan. Ai sai suka riƙe bakinsu. "Allah ya bani lafiya haka tace. Gani akan ƙafafuna. Godiya ta tabbata ga Allah" Yana faɗar haka ya koma ciki riƙe da ƴan biyu. A masallaci abun sha'awa Gwadabe yayo sallar magriba, bashi ya shigo gida ba sai bayan isha sabida mutane sun baibayeshi ana mishi barka. Hatta su Baban Nazifi a masallaci suka haɗu da Gwadabe, kamar yadda ya labarta mun sun yi mamakin ganinshi akan ƙafafunshi. Ƙafa mai daɗi yau sai ga Gwadabe a bayan gida yana yin wanka da kanshi, Allah abun godiya ne A daren ranar Gwadabe yasha labarai sosai. Hira mu kai ta zabgawa muna murna da farin ciki. Furucin Babala yananan ɗamfare a zuchiyata ya zame mun ciwo. Na yi alkawarin washe gari zamana a gidan Gwadabe yazo ƙarshe kenan. Har yayi bacci idanuna biyu ina tunanin inda zan nufa in na bar gidan Gwadabe. Wata zuchiyar tace mun. "Ga mahaifiyarki da kike ganin kamar tana da wani ciwo a zuchiyarta me zai hana ki koma hannunta da zama. Tunda yanzu kin mallaki hankalinki?" Idanuna na lumshe wasu siraran hawaye suka gangaro kumatuna. Na jima ina karanta wasiƙar jaki kafin na daure na taso na fito falo na ɗaura alwala na soma Sallah. Bani na tsagaita da sallar ba har sai da naji kiran sallar farko tukunna. Takun fitowar Gwadabe na jiyo. Ƙura ma ƙofar ɗakin idanu nayi. Shine ya fito yana saye da jallabiyya fara. Idanu ya ƙuramun yana sakarmun murmushi me kyau da tsayawa a rai. Take zuchiyata ta sake yin rauni ainun. Ruwan hawaye suka ɓallo daga idanuna zuwa kumatuttukana. Tsugunnowa Gwadabe yayi a gabana, ya shiga share mun hawayen nawa. Abun mamaki ruwan hawayen sam sun ƙi ƙarewa. "Iyabo na yi tunanin hawayen farin cikin ganina akan ƙafafuwana kike yi ai. Amman na fahimci akwai ciwo mai raɗaɗi dake damun ruhinki. Faɗa mun menene matsalar? Naso in kwanta dake daren jiya, ko dan kewar juna da muka yi, amman na rasa gane dalilin da yasa kika kasa bani kan ki, mu raya daren da yake cike dam da farin ciki. Daren da babu daren da zai iya tureshi a ƙwaƙwalenmu" Kuka na fashe dashi mai gunji, na rasa yanda zan yi da raina. Zugi zuchiyata take ta tayi mun. Gwadabe cike ruhina yake dam da farin cikin samun warakarka. Gefen zuchiyata kuma cike da fargabar yanda rayuwata zata koma bayan rabuwarmu. Gwadabe ya zama dole mu rabu, muddin muna son juna so na gaskiya. Mu ɗauka rabuwarmu itama ƙaddarace. Har abada sonka zaita wanzuwa a cikin rayuwata, kullum sake halittar sabo za'ayi. Ta yiwu rabuwarmu ka iya kawo ƙarshen numfashina, ko ya zama silar kamuwa da wani ciwon da zai ta cin naman jikina har sai ya kaini ga kushewa. Amman Gwadabe na sani har duniya ta naɗe ba zaka manta da gudunmawar dana ba rayuwarka ba....." Tashi nayi ina shirin shigewa uwar ɗaki domin soma shirya kayana. Gwadabe kuwa duk illahirin jikinshi rawa kawai yake yi mun. Cikin kaurin murya irin ta cikar mazantaka yace. "Iyabo..." A maimakon in tsaya sai na shige ciki da gudu na saka sakata. A jikin ƙofar na jinjina ina jawo numfashi daga cikin huhuna da ƙyar. Iyabo ki buɗe ƙofarnan dan Allah na roƙe ki kar ki sa zuchiyata ta buga." Ya faɗa hakan a mugun raunace, tsabar ɓarin da jikina yake yi ma na kasa ko da motsawa, jin za'a shiga Masallacine yasa ya fita dole, ina jiyo rufo mana ƙofar falo da yayi. Sai da na haɗa ƴan tsunmokaraina a ƙaramin akwati, na ajjiye gyalena a saman akwatin kafin na tada kabbarar sallah. A lokacin ƴan biyu sun tashi daga bacci. Ina idarwa saina gyara zama na soma azkar, ina yi ina kallon yarana. Toye yana tsakankanin ƴan biyu yana wasa dasu. Sai dariyarsu suke yi. Yara kenan su basu da matsalar komai. Iyaka su yi bacci su tashi su ci abinci. Ku sakko ku je ku yi alwala ku yi salla, na faɗa musu da yaren yarbanci. Dukkansu sai da suka rungumeni kafin na buɗe musu ƙofa suka fita. Ai sai na kife a dadduma na shiga rera wani irin kuka na tashin hankali. Inayin kukan nan ban mance da ambaton Allah ba. Jin hucin mutum nayi a gefe na, Gwadabe ne nasan babu makawa. Riƙo hannuna yayi gam, ya rarrasheni ya kasa, yayi magana wallahi ya kasa. Duk dauriya da irin shanye abu na Gwadabe yau zuchiyarshi a tsinke take. Shima hawayen yake fitarwa a gidanunshi. Mun fi minti goma a haka, yara dai ban sake jiyo ɗuriyarsu ba ma. Sai can Gwadabe yayi ajjiyar zuchiya kana yace. "Iyabo yanzu me kike so in yi, ina alƙawarin da muka ɗaukarma kawunanmu zai kwana, babu rabuwa a tsarin da muka tsaroma rayuwar gidan aurenmu...." Dakata Gwadabe, kar so ya rufe maka idanu, ka kai rayuwarka ga halaka. Wallahi zaman mu babu alkhairi, kuma ba zamu taɓa ganin haske ba. Tunda Babala ko da yaushe a cikin zubar da hawaye take. Ta yiwu bijerema iyayenmu da mu ka yi ne ya jefa mu a cikin halin da muka shisshiga a baya. Siraɗi nawa muka tsallake Gwadabe? Ka tsayar da zuchiyarka kul sona ya ruɗeka, uwa tafi gaban a tsaya ana jayayya da'ita wallahi. Dukkanmu ba zamu so yaranmu su yi mana taurin kan da mu ka yi ma namu iyayen ba, Gwadabe mun zuba taurin kai sosai da sosai. Allah ya jarabcemu da talauci sosai da sosai sakamakon fishin iyaye da muke ciki. Ka daure ka sake ni kawai in tafi" Cikin dashasshiyar murya yace. "Ko dai har yanzu da ragowar soyayyar Debisi a zuchiyarki ne Iyabo? Ni fa bazan iya rayuwa babu ke ba. Da maraici kike so yaranmu su taso ne?" Cikin jin haushi, gami da tausayinshi a haɗe na dubeshi. Nayi mishi uziri dan tabbas a cikin tsaka mai wuyar fita yake, dole nice dai zan lallaɓashi ya sauwaƙe mun. Billa babu ko sofanen son Debisi a zuchiyata. Mutumin daya gujeni sabida halittar ƙibar da Allah ya hore mun, to shin me zan yi dashi a cikin rayuwata. Ka sake ni kawai, domin cika umarnin Babala da cika alkawarin da nayi mata. Ce mata nayi a ranar daka samu lafiya ko kwana da igiyoyin aurenka bana kumawa" Mun fi awa guda muna tataɓurza tsakanina da Gwadabe. Muna cikin haka, Allah da ikonshi muka jiyo sallamar Babala a cikin falo, tana tambayar Toye ko muna ciki ne" Jijjunanmu a mace muka fita falon, ita da Baban Nazifi ne, sai Yaya Harisu. Gurfana nayi a gabansu cikin rawar baki na gaishesu, babu wanda yayi yinƙurin amsawa. "Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya. Gwadabe yau zan yi bacci harda munshari sabida wannan jikar oduduwan zata bar gidannan, igiyoyin aurenka zasu sauka a kanta. Kuma bari kaji danginta ne su kai ma Agumu ( sammu) ba kowa ba, domin ba ƙaunarka suke yi ba. Wajen malamai har biyar muka je, duk maganar ɗaya ce dai. Maza saketa ta kama gabanta yanzu_yanzu. Ko wallahi in tsine maka" Idanuna na runtse bakina, harshena suna kakkarwa kunnena na baza ina jiran kalmar saki. Kamar saukar aradu naji ya furta. "Na sake ta saki ɗaya Babala" Wani wuji_wuji naji yana dibata, take mashashshara ta saukar mun. Ajjiyar zuchiya Babala ta sauke kana tace. "Cikace mata ya zama uku ɗan albarka" Na sake ta saki biyu, in aka haɗa dana baya dana yi uku kenan." Ya faɗa muryarshi a mugun dashe kamar wanda aka shaƙe. Miƙewa nayi tsam, duk da jirin da nake gani, amman bazan iya jure shaaƙar numfashin Gwadabe ba. Uwar ɗaki na shiga, Toye da ƴan biyu suna katifa suna wasansu. Ganina yasa Toye cewa.. "Mama kinga Kahinde yana dukan Taiwo ko, bayan itace yayarshi" Sai da na zari jakata kana nace. Kahinde ka dena dukanta, yayarka ce. Kai kuma Toye ka kula sosai da maraicin ƙannenka. Zan yi wata ƴar tafiyar da bansan yaushe zan dawo ba" Duk da yaron yana da ƙarancin shekaru amman sai naga yayi jigum kamar mai tunani. Kayukansu na shafa tare da saka musu albarka, na fito daga ɗakin a sanyaye, har na kai bakin ƙofar fita na jiyo muryar Babala tana cewa. "Yaran wa kika barma, wa kike tunanin zai riƙe yaran yarbawannan? Maza koma ki kwasosu..." "A'a Babala yara kam zan rayu dasu, ni yafi dacewa in kula dasu tunda dana aurota iyayenta ita gayanta suka bani, kiyi haƙuri dan girman Allah " Gwadabe ya katseta da hanzari. Kai nasa nayi ficewata daga ɗakin. Matan gidan duk suna tsakar gida da yaran gidan, suna hangoni ko wacce ta sau abunda take yi kallo ya koma sama wai shawo ya ɗau giwa. Ni ko murtuke fuskata nayi sosai ta yanda ba wacce zata iya samun fuskar tambayata, nayi ficewata zazzaɓin dake jikina sai tsananta yake yi. Ko da na shiga Bus ɗin unguwarmu na kifa kaina a bayan kujerar dake gabanku ban ɗago ba har sai da muka iso. Duk wannan abun babu ko ɗigon hawayen daya sake zubo mun tunda kunnuwana suka saurari kalmar saki. Ko gidanmu ma bansan ya akayi na iso ba, ganina kawai nayi a ƙofar shagon Iyaa. " Ahh ahhh ahh Iyabo kini o ti sele? ( Me ke faruwa )" Iyaa ta faɗa cikin kwakwazo da kuzuzuta lamarin. Kafin in mata amsa sai ga Iyaa Kokodeen ta fito daga cikin gida, itama ganina ne yasa ta nufo ni. "Iyabo lafiya da sassafe haka harda jaka a hannunki?" Jin haka yasa Iyaa fitowa a kidime zaninta na suɓucewa. "Ahhh ahhh ya sake ta ba? Ai dama mu munsan zaki dawo, ba riƙe aure suke yi ba saki ko da yaushe, da laifi ba laifi saki. Kinga abunda muke guje miki tun ba'aje ko ina ba har ya faru. Da yarenki kika aura da kin samu kwanciyar hankali. Ai sai ki shigo mu ci gaba da zama kafin Allah ya ɓullo miki da wani. In ce dai babu wani ragowar igiyar da tai saura? Dan wallahi kin bar komawa wannan auren, an yi na farko, gana ƙarshe yayi." Duk wannan maganar cikin yare take yi, tana yi tana buga cinya tare da tafa hannaye. Jiyo muryar ta ne ya tilastama su Iyaa Beji fitowa da sauri. Suna fitowa ni kuma na shige cikin shagon Iyaa na ɓulle cikin gida abuna. Ina shiga ɗakin Iyaa na tarar da Yemisi a kwance a ƙaramin gadonmu a kwance da dukkan halamu itama a gida ta kwana. Zama nayi a ƙasa jiɓur. Zaman nawa ke da wuya sai ga su Iyaa sun shigo da duk matan gidan, suka tutsiyeni kan sai na faɗi silar mutuwar auren. Daga masu cewa gwara da aka rabu, sai masu cewa zasu je su ɗebo yaransu su girma a cikin yaren mahaifiyarsu. Ni dai suka sak sani a tsaka mai wuya. "Ki buɗe baki kiyi magana mana kin ma mutane shiru" Babu abunda ya haɗa ni dashi.mahaifiyarshi ce ta bashi umarnin ya sake ni. Igiyoyin auren sun ƙare duka" na faɗa a sanyaye. Da hanzari Yemisi ta tashi zaune zumbur kamar wacce aka tsikara. Idanu muka haɗa, dan na riga na gane manufarta na wannan zabura haka. Iyaa ce ta katse mun kallon Yemisi da nake yi dafe da kirjinta. "Sai da kika gama mishi jinya tas ba, iyayen nashi ba ke suka bari da ɗawainiyarshi ba? Kika kaɗar da kayan ɗakin ki tas komai ya ƙare a nemo lafiyarshi, to ga sakamako kin gani. Wanne irin bijere mana ne baki yi akan Gwadabe ba, amman shi gashi ya nuna miki yafi son uwarshi sama dake" Cewar Iyaa da take magana a tsawace. Iyaa Kokodeen ce tace. "Ahh ki barta haka ta ji da zafi gami da raɗaɗin mutuwar aure, daga baya ayi wacce za'ayi." Da ɗaya da ɗaya suka watse ɗakin ya rage daga Iyaa sai ni da Yemisi. Da ƙyar Yemisi ta amsa gaisuwata har tana hararata. Ni abunda yake damuna shine a gabana da ta kwantar da hankalinta ma ƙila wannan itace gamuwata da'ita ta ƙarshe daga ita har mijinta. Dan a wannan karon garin Kano ta yi mun zafi ainun, na fi son in je rugar mahaifiyata in zauna a cikin danginta da ƙannena nima. Ina cikin zancen zuchi sai ga sallamar Debisi ya shigo. Irin kallon daya watso mun da dukkan halamu Iyaa ta labarta mishi abinda ya faru dani. Kaina a ƙasa na gaisheshi cike da ladabi. "Lafiya lau Iyabo. Sai kuma naji mummunan labari marar daɗin sauraro?" Ɗan murmushi kawai nayi kaina a ƙasa. "To Allah yasa hakan shine a'ala gareku baki ɗaya. Allah ya fito muku da waɗanda za su yi dai dai da rayuwarku. Kar ki saka damuwa a ranki. Shi aure rai gareshi nasan kin sani" Duk wannan maganar da yayi yana tsaye a kaina yake yi. Shigowar Burodami kokodeen, da Anty Mulka, da iyaa, da iyaa Debisi, da duk masu ruwa da tsaki na gidanmu ne yasa Burodami Debisi ya nemi waje ya zauna. Alfa Kulle shine ya shigo a ƙarshe, Wa yake ga mahaifina, ƙani ga Iyaa Debisi cikinsu ɗaya. Kuma ya kasance shine mai ƙarfin faɗe aji a family kasancewar shi kaɗai ne namiji da yai ragowa. Gidanshi yana jikin namu gidan. Amman iyalinshi suna Ibadan da zama, sai dai duk shekara yana kai musu ziyara. Burodami kokodeen ne ya buɗe taron da adda'a kafin Alfa Kulle ya tambayeni cikin yaren yarbanci. "Meye silar rabuwarki da mai gidanki?" Murya na rawa na labarta mishi a taƙaice, sai Iyaa tayi carab tace. "Dama tun auren a difane fa take a gidan auren. Dangin miji kullum cikin ƙyamatarta suke suna aibanta mata yarenmu. Buradomi Kulle meye kai baka zaunar da yarinyar nan ka faɗa mata ba, ba ƙafa tasa tashure ba, sabida ganin ba mu muka tsugunna muka haifeta ba, ƙasa ta rufe ma Toye idanu. Cikinmu nan babu mai son wannan auren " Alfa Kulle yace. "Ta faru ai ta ƙare. Ba shikenan ba auren ya ƙare kan kat ba. Sai. Ki zauna zuwa lokacin da Allah zai ɓullo miki da wani mijin. Inason in koma Rugar mahaifiyata can inda kowanta yake. Dan Allah kar ku hanani wallahi bazan iya zaman Kano ba" Ina jiyo ajjiyar zuchiya da Yemisi ta sauke mai ƙarfi. Iyaa kuma ta dire akan ban fa isa in bar hannunta ba. Sai da kowa dake wajen ya sa baki kafin ta amince sai zubar da hawaye take yi. Burodami Debisi kuwa ya kasa cewa komai. Zahiri bai ji daɗin amince mun da kowa yayi akan komawata ruga ba. "Zuwa yaushe kike son tafiya Iyabo?" Burodami kokodeen ya tambaya. A sanyaye nace. Zuwa gobe in Allah ya kaimu" A haka dai taron ya watse, duk yanda Burodami Debisi yaso keɓancewa dani Matarshi ta hana shi wannan ƙofar. MRS BUKHARI 3064127935 Buhari Ibrahim Ladan First bank Sanya nera 500 ɗinki kuɗin karatu anan. Wannan asusun gudauniyarmu kenan. Ki sani in kika siya wannan littafin tamkar kin taimaki iyayen marayune, dama su kansu marayun Kuzo mu yi tarayya cikin aikin lada. Ƙarƙashin Amila Foundation gidauniyar da muka buɗe ni da megidana domun iyayen marayu, ko tainakon marasa lafiya. Waɗanda suke cikin group dina mai suna (NAMA YA DAHU ROMO ƊANYE) 300 kacal zasu iya kuɗin karatu https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm NAMA YA DAHU... ROMO ƊANYE GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA SHA ƊAYA (11) *ASSALAMU ALAIKUM MASOYAN IYABO MUNA MIƘA SAƘON GAISUWARMU A GAREKU. IYABO TACE IN SANAR DAKU TANA GODIYA DA KUKA TAYA TA JIN ZAFIN RABUWARTA DA GWADABE. TANA MIƘA ƊUMBUN GAISUWA GAREKU* *(Na sha ƙorafi akan in yi haƙuri inyi har asabar da lahadi. To duba da irin son da kuke nuna ma labarin ƙorafinku ya karɓu a yanzu. Amman da zaran free page ya ƙare zaku dinga samun posting ne daga monday zuwa alhamis kaɗai, juma'a asabar lahadi na hutune. Kuyi mun afuwa kunsan bana wasa da yin posting ina da lalurar idanune shi yasa. Amman zaku samo readmore masu yawa in sha Allah nagode)* Duk yanda Burodami Debisi yaso ni da shi mu samu keɓewa Yemisi ta kulle wannan ƙofar a tsakaninmu. Ta cikin idanunshi nake iya karanto labaran dake cikin zuchiyarshi. A haka na wuni cur a waje ɗaya tamkar mutum mutumi. Maƙotanmu da ƴan uwanmu yarbawa su kai ta shigowa jajanta ma Iyaa. Da ƙyar cikin tursasawa da lallami Burodami Debisi yasa na sa lomar abinci a bakina. Har zuwa wannan lokacin hawaye bai zubo mun ba fa, face ruhina dake gasuwa, haƙiƙa kuka rahamane. Sai dab magriba Burodami Debisi ya shigo hannunshi riƙe da baƙar leda shaƙe da yankakkun kayan marmari ya miƙo mun. Harara matarshi ta watsa mana ta dubemu daga sama har kasa ta buga tsaki. Hannu nasa na amshi ledar nayi godiya ciki_ciki, dan wallahi ko magana akayi mun sai in ji kamar in sa hannu a ka inta kwarmata ihu. Ga mita da Iyaa take ta faman yi da kutuntumama Gwadabe da Babala ashariya. Dan da ƙyar Alfa Kulle ya hanata wai ita sai taje ta ɗebo yara ta dawo dasu. Ni kuma wallahi a wannan lokacin har yaran bana son gani, da duk abinda ya danganci Gwadabe. Iyaa ce ta shigo tai ta ma Yemisi faɗa ita da Burodami ashe saɓani suka samu har ta kai da duk haƙurinshi da kau da kanshi sai da ya ɗaga hannu ya mareta. Ita kuma tana taƙamar soja ce ita shine ta rama, rikicin daya tilasta mata baro gida a daren jiya. Nasiha tayi musu sosai, ya ɗauki matarshi suka koma gida. Fitarsu ke da wuya sai ga uwani da Hajiyarta sun yi sallama idar da sallana kenan ban tashi akan sallayar ba ma, ina jan carbi na amsa sallamarsu. "Hajiya kune da magriba haka a tafe, lamarin Iyabo ya tasoki ko?" Cewar iyaa dake gyara zamanta. Hajiya ta kalleni cikin tausayi tace. "Yanzu sai da aka sako yarinyarnan Toyosi duk irin faɗi tashin da tasha, amman dangin mijinnan nata sai da suka ɗauketa akan yaranta?, jiya Tabalbalin take faɗamun samuwar lafiyar mijin fa." Baki Iyaa ta taɓe tace. "Ai tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan duka. Ni Hajiya ina murna da mutuwar aurennan, domin in banda wahala babu abunda take sha a wannan gida. Sai da ta game mishi jinya ta sai da komai nata ɗakinta daga robobi sai tukwane fa, shine zai sako mana ita. Ko da yake kiyi haƙuri Hajiya ku Hausawa baku fiye riƙe aure ba" Gaggaisawa mu ka yi, Uwani ta matso inda nake, su Iyaa ma suna hirarsu ta manya. "Yanzu a wanne hali shi Gwadaben yake sai Allah. Nayi imani duk inda yake cike yake da tashin hankali babu mamaki in akace yana gadon asibiti ma. Amman Iyabo me yasa kika baro su Toye? Kinsan fa wuya zasu sha ƙila ma a mayar dasu ƙauye kinga shikenan an kashe musu rayuwa" Inata ƙoƙarin ganin ƙwalla ta zubo a idanuna amman ina, abu yaci tura, idona ya soye. Sai da na sauke ajjiyar zuchiya nace. Gara su yi zamansu a dangin mahaifinsu zai fi. Wuya bata kisa Uwani da wuya na kisa mu yaran yarbawa da tun muna ƙanana zamu dinga mutuwa, ke kinsan irin gwale_gwalen da muka sha. Gobe asubar fari garin zan bari, kinga in na tafi bazan sake waiwayo garin Kano ba, na barta har abada. Kinga zanyi irin tafiyarnan ai bai dace in tafi da yaran mutane ba. In Gwadabe ya ga yaran a kusa dashi a ƙalla zai ji sanyi" Na ƙarashe maganar a raunace. Ƙirji Uwani ta dafe tace. "Ni Uwani Tabalbalin ina zaki koma to iyabo?" Can Adamawa wajen mahaifiyata nake son in je in rayu cikin ƙannena, domin in samu kafaɗar da zan jingina in yi kuka. Ita kanta Dada akwai wata boyayyar damuwa wacce take cin ruhinta ainun, tun tasowata da wannan ƙuncin nake ganinta. Baki ga yanda take ta ramewa ba Uwani" Uwani dai bata so ba, amman babu yanda ta'iya dole haka mu kai sallama. "Iyabo ni ko duk randa na dawo daga Canada, zan zo Iyaa ta bani adireshinki ko a bangon duniya kike zan ziyarceki. Sannan dan Allah ki kwantar da hankalinki ki rungumi ƙaddararki da zaran kin samu mane mi kiyi aurenki kema ko Allah zai sa ki samu nitsuwa." Nagode sosai Allah ya ƙaddara saduwarmu. Kya dinga leƙa yaran in kin samu lokaci." Na sake magana a raunace. Basu suka tafi ba sai wajen taran dare su kai mana sallama bayan sunci Amala. Inayin sallar isha na naɗe a gado bana son ma Iyaa ta cakaleni da faɗa ko hargaginta, fruit ɗin da Burodami ya kaqo mun shi naci. Wajajen goman dare Alfa Kulle ya kawo mun adireshin rugar da mahaifiyata take da inkiyar shi mijin nata da take aure Mahaifin su Baɗɗo. "Tashi ki zauna Iyabo mu tattauna kinga gobe asubar fari ya kamata ki kama hanya dan tafiyarki mai nisan gaske ce. Kece baki sani ba, sanda muka je ƙauyannan kina yarinya ƙarama" Miƙewa nayi daga kwance na zauna kamar yadda ta uwarceni. "To tunda kin nace sai kin koma hannun mahaifiyarki ai shikenan, bazan hana ki ba. Amman fa...." Sai tayi shiru akwai abunda take son sanar dani, amman kuma kamar bata son faɗe ko nauyi yake yi mata ne ni dai ban sani ba. Sai kawai ta ɓige da yi mun nasiha tare da cewa. "Mijin Uwarki ance jarababbene sosai, dan haka sai ki kula kar ki je ki haɗata rigima dashi a wannan gidan yawa, ga kishiyoyi" Ni dai da Toh" kawai nake amsata harta gama na koma na kwanta. Tsawon wannan dare tunanuka ne barkatai sukaita kai komo a ƙwaƙwalwata da tunanin irin rayuwar da zan fuskanta a rugar da mahaifiyata take, da irin karɓar da shi kanshi mijin nata zeyi mini. Gefe ɗaya kuma tunanin Gwadabe da yaran duk ya addabeni, wayata a can gidan na baro mishi abarshi dan bana son damuwa. Washe gari sassafe na kintsa tsab, Iyaa ta ɗan harhaɗa mun tsarabar Kano, da ƴan canjina. Iyaa Kokodeen kuma ta kawo kuɗin mota nera dubu biyar ta ce in ji Burodami kokodeen yace a bani na mota. Matan gida mai ishirin mai hamsin sai aka gagganɗa mun, nayi musu sallama. Ina fita sai ga Burodami Debisi a mashin bespa, hawa nayi ya kaini tashar mota inda na samu motar Adamawa, na ci sa'a ma motar zata shiga har ƙaramar hukumar GIRAI, daga girai in na sauka sai in kuma hawa motar wata rugar kuma, kafin na sake hawa motar asalin rugar da Dada take Tafiya ce bata wasa ba a gabanmu. Dubu biyar Debisi ya bani tare da miƙo mun wata jakar leda. Nagode sosai Allah ya bar zumunci. Allah ya ƙaddara saduwarmu" Idanu ya lumshe yace. "Ki gaishe mun da Dada sosai. Sai na zo in sha Allah " Sallama mu ka yi ya figi besparshi ya fice. Hanyar da yabi na bi da kallo ni kaina bansan tunanin da nake yi ba. Mu biyu ne rak a motar ni da wata bafulatana mai yara biyu, kuma a seat ɗin tsakiyar Bus muke, Bus ɗin babbace sosai mai layi huɗu ce zata ci mutum goma sha huɗu harda direba. Ga motar ragwargwajajjiya ce soai. Mu dai muna zaune jigum. Ita bafulatana ta kusa dani sai wasa take da yaranta suna yara yaren fullanci. Sai lokacin hawaye ya ɓalle mun dana tuno da nawa yaran. Shikenan su da hawa jikina kuma ya ƙare, haka suma zasu taso ba a hannuna ba, kamarr yadda nima na taso ba'a hannun mahaifiyata ba. Suma haka zan haifo musu ƴan uba ko? Kamar yadda Dada ta haifo su Baɗɗo. Kukane sosai ya ciyoni, dole na saka fuskata tsakankanin cinyoyina na yi mai isata ba tare da Bafulatanar kusa dani ta san halin da nake ciki ba. Shigowar wasu fasinjojinne yasa na share hawayena na ɗago. Suma fulaninne amman maza, harda sarƙar fulani mai duwatsu kala kala a wuya da hannunsu, ga gashi sun tara sosai a kawunansu, ga sandunansu da takalmin roba, sai ƙosai da biredi suke ci suna korawa da lemun limca na kwalba. Murmushi ne ya suɓuce mini kawai. Da ɗaya da ɗaya aketa taruwa a cikin motar, kujerar da nake zaune naci sa'a duk mata ne mu huɗu a kujerar, dukkansu da gani fulanin usil ne, gasu da yara a hannu ga goyo raɓe_raɓe, tun kafin motar mu ta tashi suke ta aikin ciye_ciye. Kasancewar sammako duk muka bugo a tashar duk suke takaryawa masu abincin tasha sai ciniki suke zabgawa. Ni ko ko ruwa bana sha'awar sha balle inci abinci, yinwarma da kanta ta hutasshe da tumbina. Sai da rana ta fito ƙal kafin motarmu ta cika tab, nan aka shiga binmu muna biyan kuɗin mota. Dubu ɗaɗɗaya da ɗari biyar kuɗin motar haka muka bayar, waɗanda suke zaune a injin ɗari biyar. Motarmu ta fita daga cikin tasha ta hau lafiyayyen titi. In banda hayaƙi da jijjiga babu abunda motarnan take yi. Ji kake tututu_tuturtu, gashi bata da gudu sam. Kaina na bakin taga ina kallon mutanen dake tafe a ƙasa ɗaiɗaiku. Wasu kasuwannin ƙauye da gani zasu je ciyo kasuwa, yayinda wasu kuma suka fito neman kuɗi, wasu tallace a kansu maza da mata, yara da manya. Tun ina ganin mutane har na soma ganin bishiyoyi. Jama'ar motarmu kuwa sai hirar nishaɗi da jin daɗi suke yi, yayin da wasu suke gyangyaɗi, a yayin wasu suke ciye_ciyensu, wasu kuma suna kame kamar ni haka. Tafiyace miƙaƙƙiya mu kai ta ta faman yinta. Da azahar tayi muka tsaya a wani gidan mai mu kai sallah a masallacin gidan man. Aka firfito kowa na sayen abunda zaici, dan direba yace ba zai sake tsaiwa ba sai mun isa inda zamu sauka. Masu fitsari nayi, masu ba haya nayi. Gurasa da ƙuli na siya na ashirin, na sha ruwa a randar masallaci, nayi komawata cikin mota. Kai mun ɓata lokaci sosai a wannan gidan mai kafin mu ka kama hanya. Mune har bayan la'asar bamu isa ba, sai yamma sakaliya sai gamu a ƙaramar hukumar girei Allah ya iso damu. Ƙauyan abun sha'awa, fulani makiyaya sunata wucewa da garkunan shanayensu zasu koma gida, shanayen manya lafiyayyu gwanin sha'awa, masu tallar nono mata suma sai wucewa suke da ƙoransu a ɗoɗɗore a kawunansu. Sakkowa mu ka yi kowa ƙafafuwa a kumbure. Matar da muka zauna waje guda na tambaya. Baiwar Allah a ina zan samu motar Jere Banyo?" Cikin kwaɓaɓɓiyar hausa tace. "Nima can zani, mu je daga can gaba zamu samu mota sai mu tafi" Ajjiyar zuchiya na sauke, na bi bayanta tiryan_tiryan har zuwa wajen akori kurar dana ga ta cika ta batse da mata da mazan funani. Duk masu tallar nononnan da sukaita wucewa ashe duk can zasu je. Iko sai Allah tafiya mabuɗin ilimi kenan. Haka na haye akori kura na biya nera ɗari, a cakuɗe muke da maza, motar an cika mutane har bana iya shaƙar numfashin kirki, baka jin komai sai warin hammata da ƙarnin nono. Ga hanyar babu kyau, haka mu kaita cuccurewa waje guda da mazan da matan. Na sha ɗan karen wuya ainun kafin mu isa Jere Banyo. A mugun galabaice na fito, ina mayar da numfashina. Masu acaɓa ne naji suna ta ihun faɗin. "Jaɓɓi lamba zaki je, kuzo mu je" A galabaice na isa gaban acaɓar nace. Jaɓɓi lamba zani, nawa ne?" "Nera hamsin ne, hau mu je" Hawa nayi ya ja muka nitsa. Ya Allah birni ma rahamane, kwazazzabo muka dinga shiga, acaɓarnan tana sama tana ƙasa damu tamkar zamu kifa. Ƙarafan acaɓar na riƙe dam, na runtse idandunana inata karanto adda'a,. Ga ƙurar jar bushasshiyar rairayi data cika mun idona da hancina dam. Wallahi na ɗauka kafin in sauka daga acaɓarnan zamu rikito mu afka wani ƙaton ramin, babu kwalta ko guntu. Bani na buɗe idona ba har sai da mai acaɓa yace. "Mun iso madakata fa" kana na buɗe idanuna a hankali na ganni a tashar ƴan acaba. A mugun gajiye na sakko daga acaɓar tare da sallamarshi. Jarabawar dana samu duk yaro ko yarinyar da na tambayeta inane gidan Modibbo Yuguda mai nagge. Sai dai su bini dana mujiya basu iya yaren hausa ba, ni kuma ban iya fullanci ba. Ga duhu ya soma doso kai. Wata baiwar Allah ce ta ja hannuna zuwa gidan wani dattijo. Bayan sun yara yaren fullanci mai daɗi da garɗin saurare sai ya fuskanceni cikin gurɓatacciyar hausa yace. "Gidan Modibbo Yuguda mai nagge kike nema ko yarinya? Dan Ɓingel tace iyakar abunda ta gane a bayaninku kenan" E gidanshi na zo Baba. Ni ƴar wajen matarshi Daso ce, yayar su Ɓodɗo ce daga birnin Kano " Baki ya rike tare da girgiza kanshi, ya dubeni da mamaki maɗaukaki yace. "Kika ce ke ƴar Daso ce kuma daga birnin Kano, to Daso dama tana da wata ƴa?" Take naga ya sauya kala daga fara'a zuwa kicin_kicin. Wata dattijuwar fara sol ɗin bafulatana mai yala yalan gashi ya kirawo ta shiga dani cikin asalin gidan. Bayan yace mun zai tura yanzu a tawo da Dadan. Cikin wata bukka aka shiga dani, sai da na sunkuya sosai kafin na iya shiga cikin bukkar, irin gidajen da suke dashi kenan a rugar . Ban taɓa ganin ɗakin gargajiya a zahirance ba sai yau, ɗakin ya burgeni ya ƙayatar dani. Jeren ƙorene kyawawa masu zanen tsuntsaye da masu zanen ƙadangare gasu nan iri iri an mammanna su a jikin bangon bukkar. Daga kusurwa biyu kuma wasu ƙwaryane hawan hawa a jejjere ko wanne anyi mishi murfo da faifal mai kala_kala. Ɗayar kusurwar kuma jeren kwallane masu hoton tsuntsaye da korayen ciyayi, ga wasu tukwanen ƙasa a kikkife a gefe. Abun al'ajabi baya ƙarewa sai gani ga gadon ƙasa da katifar yayi. Ƙasan cikin bukkar kuma buhune aka ɗinka aka shinfiɗa a matsayin ledar tsakar ɗaki. A gefe na zauna ƙuri ga duhu_ duhu a cikin ɗakin. Wannan dattijuwar ce ta shigo hannunta rike da fitilar aci bal_bal, akwai wani ɗan gini da akayi a saman ɗakin kamar anyi gininne musamman domin ajjiye wannan aci bal_bal ɗin. Bayan ta ajiye sai tace dani. "Use ɓilgel ( sannu yarinya)" Sai naga ta fita. Inaso ince zan yi alwala in yi sallah amman bansan me zance ba, dole haka nayi gum. Can bayan duhu ya mamaye sararin samaniya duniya tayi baƙi ƙirin sai na jiyo muryar Dada. Murya mai zaƙi da siranta, muryar dake raunata zuchiyata take kara mun so da tausayin uwata. Cikin bukkar ta shigo da sallama. Tana saye da wata iriyar jemammiyar atampar dana taɓa sai mata a shekarun baya. Sai ɗan wani yalolon tattararren mayafi mai ruwan ƙwai. Ƙafafuwanta kuwa duk ƙura. Idanu ta ƙura mun ƙur, sai naga guraben idanunta tab da ruwan ƙwalla. "Jabu kece a Jaɓɓi lamba a darennan? Kinsan fa kin tambayeni zaki kawo mana ziyara nace miki a'a. To me yasa zaki yi gaban kanki ki zo, ita kuma uwar taki ta barki bacin tasan...." Sai ta ja bakinta ta tsuƙe tare da sauke gwauron numfashi. "Tawo mu tafi to, kawo jakar in riƙe miki" Ta kai hannunta zata ɗauki jakata nayi wuf na ɗauka. A'a Dada zan ɗauka. Kuma kiyi haƙuri dole ce tasa na zo gareki, dole ce tasa Iyaa ta barni nazo, ba a san ranta na tawo ba" Duk fa maganganunnan da yarbanci muke yinshi. Babu dai abinda tace dani sai naga ta sunkuya ta fice. Bayanta nabi muka fita, muna tafe a jere da juna abinda bamu taɓa yi ba kenan. Tiryan_tiryan mu kaiya tafiya, muna wuce samari da ƴan mata. A yadda na lura kab garin gidajensu iri ɗaya ne, gidajen bukka zagaye da jinka, basu da dangar gini ko da na laka ne. Wani gida muka shiga ƙatoton gaske, mata da yaran gidan nono_nono kowa ya ja zugar abokan hirarshi. Ga aci bal_bal kashi kashi, sai fullanci akeyi ana dariya. Mijin Dada yana zaune akan tabarmar keso da rediyo a gabanshi yana ji, ga abinci da kofi a gabanshi. Sallamar Dada yasa wani yaro namiji da ƴar budurwa suka nufota da sauri suna faɗin. "Use Dada" ( Sannu Dada) Mijinta ya juyo ya dube ni, ya dubi Dada dana fuskanci tun shigowarmu jikinta yake rawa. "Je ki gaishe da Babanku gashi can" Ta dubi wannan ƴar berar da tazo ta tareta sai tai mata yare. Shi kuma namijin sai ya amshi jakar hannuna, ita ƴar budurwar kuma tai mun jagora zuwa wajen mijin Dada, gashi ni ban iya Fullanci ba. Haka dai na durƙusa a gabanshi gaisuwar dai ta kurame mu ka yi, sannan muka zo mu ka tarar da Dada tsaye inda muka barta ta nausa a cikin tunani mai nauyi, har sai da ƴar rakiyata ta jijjiga hannayenta. "Dada am" Tace kafin Dada ta dawo cikin nutsuwarta, bayan ta ja fasali sai ta dubeni tace. "Mu je in kai ki ki gaisa da abokan zamana" Binta nayi a baya ta nuna musu ni, nai musu gaisuwar kurame biyu a cikinsu suna ɗan jin Hausa sai muka gaisa da kyau. Daga cikin ƴan mata da yaran gidan ma suna jin Hausa hakan yasa na ɗan ji sanyi. Amman bansan me Dada tace dasu a kaina ba ni dai. Zungul_zungul na bi bayanta har cikin bukkar da nake da tabbacin nata ɗakun kenan. Babu komai a ɗakin sai tarkace kawai, sai gadon ƙasa da katifar yayi taji zanin gado. A bakin gadon tace in zauna. Bayan na zauna Dada sai ta fita. Wannan budurwar kuma tana wajen tulu tana ɗebo mun ruwa a ƙoƙo, bayan ta bani na sha, sai nace. "Inason zan shiga bayan gida, banyi sallar la'asarba ƙila isha tayi ma ko?" "E muma mun yi sallar Isha. Muje in kai ki" Cikin gurɓatacciyar hausar da ba ko wacce nake ganewa ba tayi maganar. Muna fitowa tsakar gidan sai muka tarar da Dada da abokan zamanta a tabarmar da mijinsu yake zaune. Sai faɗa yake zubowa yana ambaton Daso_Daso. Jikina tuni ya bani a kaina ake tattauna maganganu, da jin ƙarfin muryar kuwa ba magana bace ta daɗi. Na sake gasgata hakanne da na ji muryar Dada na rawa, da kuma irin yanda kab yaran gidan su kai ciko_cirko kuma suka ƙura mun idanu kamar maye yaga jariri. MRS BUKHARI NAMA YA DAHU.... ROMO ƊANYE BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI Lamba ta sha biyu (12) Da jan ƙafa na bi wannan ƴar budurwar da nake kyautata zaton kanwata ce uwarmu ɗaya. Wani waje ne aka ɗan keɓeshi aka zagaye da kara, nuni taimun da hannunta halamar nanne ban ɗakin. Ruwa ta zuba mun a buta ta miƙo mun nasa hannu na karɓa, tare da shiga ban ɗakin. Ƙasace a ban ɗakin , sai ɗan gefe guda da akayi daɓe inaga a wajen suke wanka, sai ramin shadda a gefe. A ƙyamace nayi bawali na fito, inda zan ɗaura alwala ta nuna mun, naga gidan kamar komai da tsari suke yinshi. Nayi alwala muka fito a tare. Har zuwa wannan lokacin Ina jiyo muryar Dada tana magana. Da ƙyar nayi sallolin da ake bina nayi jigum akan buhun da aka shimfiɗa mun nayi Sallah. Abinci wannan budurwa ta kawo mun a cikin ƙwarya an rufe ƙwaryar da faifai. Ya sunanki ne?" Na tambayeta ina ɗan fara'a. "Sunana Cubu" Kin sanni?" Na sake jefo mata tambaya. Sai ta girgiza mun kanta halamar A'a. Sai na yi ɗan murmushi nace. Ke yarinyar Dada ce?" Sai da tayi dariya sosai kana ta bani amsa ta hanyar ɗaga mun kanta halamar e" Kwaryar abincin na buɗe tuwone da wata miya baƙa ƙirin ba koriya ba, sai wani irin ƙamshin ganye take yi marar daɗi, amman dake ina jin ɗan karen yinwa ba shiri na nutsa hannuna a cikin tuwon. Wallahi da ƙyar na iya haɗiye tuwonnan, ko da na haɗiye dambe mu kai ta tayi, yana shirin dawowa ni kuma ina ƙoƙarin mayar dashi, dan gudun kar suce na ƙyamacesu. Inaga Cubu ta fuskanci bazan iya cin tuwon bane, sai ta miƙe ta kawo mun madarar shanu. Dana kafa kaina sai da na shanye madarar tas. Ina sauke kofin nayi gyatsa, sai ga Dada ta shigo tana sharar hawaye cikin dabara, dan ita a tunaninta ma bamu ganta ba. Zargina ya tabbata akwai wani babban abu da aketa ɓoyemun tsawon shekarunnan da ba'ason ni in sani. Ni kuma ina ganin lokaci yayi daya kamata in sani. Bakin gado ta zauna kanta a ƙasa kamar yadda ta saba tace. "In kin gama cin abincin Cubu ta rakaki gidan Ɓoɗɗo acan zaki kwana, ƙanwatace a gidan itace uwar mijin Baɗɗo uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya babu wata matsala. In Allah ya kaimu gobe na dawo tallan nono zan biyo gidan in same ki. Cubu ƙanwarki ce ƙanwar Ɓoɗɗo, yar Yusuf. Amma. Akwai Amaduyal shine a sama da Ɓoɗɗo sai dai shi baya zama, yanzu haka suna togo, sun fita kiwon shanu tsawon shekara biyar basu dawo ba, amman ana jin labarinsu, suna yo aike gida, matarshi Sa'ada tana cikin gidannan, da yaranta biyu" Kai na gyaɗa. mamakin daya kamani shine jin Dada ta ambaci tallan nono, kenan itama tallah take yi kamar yadda na ga wasu guggun mata a Jere Banyo da ƙoren tallarsu? Iko sai Allah ai yaci ace Dada tana zaune ne tana morar haihuwa ba wai ace har yanzu aikin wahala take yi ba. Miƙewa nayi tsaye Cubu ta ɗaukarmun jakar kayana. To sai Allah ya kaimu goben Dada" Na yi magana a mugun sanyaye. Cubu da Yusufu ne suke gaba ina biye dasu a baya, ina kallon gari maza suna kwakkwance a tabarma, wasu kuma sunyi da'ira suna cin abinci. Yayinda samari masu jini a jika suke ta sha'aninsu kawai. Ta wani dandali muka zo wucewa nan naga kyawawan ƴan mata farare, da kyawawan Samari. Ƴan mata na waƙa samari na yi musu tafi. Wasu kuma keɓe suke a gefe guda suna musayar kalaman ƙauna. Rayuwar ƙauye akwai ban ƙawa a cikinta, bugu da ƙari akwai nishaɗi sosai. Tafiyace miƙaƙƙiyar gaske mu kayi kafin mu iso gidan Boɗɗo, duk na gama galabaita, ga gajiyar hanya da dama ban huceta ba, ga wannan tafiya me nisa da muka sake yinta. Suna kwance a tsakar gida mu kai sallama muka shiga, mazan gidan kuma kafin mu shigo sai da mukai musu sallama. Da sauri Boɗɗo ta taso ta tare mu." Ina tsaye bansan me Cubu tace da'ita ba. Kawai sai naga ta rungumeni ta fashe da kuka. "Adda Jabu ashe zan sake ganinki a rayuwa? Cike zukatanmu suke da maraicinki" Ta faɗi hakan da kwaɓaɓɓiyar hausa. Nima hawayene suka gangaro kan kumatuna. Nan Boɗɗo ta shiga dani cikin gida tana ta nunani, ni dai Adda Jabu kawai nake jin tana ambato. Ɗakin Yafendo Kaɓoji ta kaini ƙanwar Dada surukarta kenan. Kanta ta dinga jijjigawa tana nanata sunana. Abunda na fahimta ƙanenane kaɗai sukai farin ciki da ganina. Hannuna Baɗɗo ta jawo muka shiga cikin bukkar data kasance ɗakinta, Su Yusufu na biye damu. Boɗɗo ta kalli su Cubu tace. "Sunanta Adda Jabu. Yayar Amaduyal ce, Dada ce ta haifeta itace yarinyarta ta farko. Ina tunanin sanadintane ke sa Dada ƙunci da zubar hawayen da tun tasowarmu muka tsinci Dada a wannan halin." Runguma suka kawo mun dukkansu ukun, babu nuna ƙyama ba komai. Hawaye masu ɗumi sukaita zurubtu a kumaruna, hankalina a madadin ya kwanta sai ya sake tashi. Ni kaina na jima ina tausayama rayuwar Dada, na daɗe ina zargin bata jin daɗin rayuwa akwai wani babban lamari data ƙunsa a cikin ranta yake nuƙurƙusar rayuwarta. A wannan daren mun yi hira sosai da ƙannena na yaushe gamo, dan su Cubu sunƙi tafiya a cewarsu sai dai du mu kwana a zaune. "Adda Jabu ki ce su tafi, Baffa zai yi faɗa sosai, ko ma yazo gidannan a darennan. Gobe Cubu zata kai nono cikin gari, Yusufu kuma zai fita da Shanu kiyo Kuma zata burga madara ta fitar da man shanu da asuba." Jim na kuma yi jin abinda Boɗɗo take faɗe. Cubu tunda kinsan hakane, ku yi haƙuri ku tafi gida. Ni ina nan na dawo rugarnan kenan, daku zanci gaba da rayuwata" Da kyar na lallaɓasu suka tafi, suna tafiya sai ga mijin Boɗɗo ya shigo ya miƙo balangu a baƙar leda. Boɗɗo ta gabatar mishi dani a matsayin babbar yayarsu. Cike da jin kunya ya sake gaisheni yana sosa ƙeyarshi shi a dole kunyata ce ta kamashi. Kai fulani a kwaisu da kunya da kawaici sosai. Fitar mijin Boɗɗo ke da wuya mu ka jiyo sallamar wata mata da Boɗɗo ta yo kiranta da suna Hama Ƙwarya ta ajjiye mun a gabana tace. "Use baƙuwa" Farar bafulatana doguwa gata da baƙin gashi. Da fara'arta muka gaisa duk da hausar kamar ta yara ƴan koyo suke yinta. "Adda wannan matar wan su Yuguda ce, mijinta shine Babba a gidannan, yana fita aiki cikin birni. Allah sarki, sannu Hama nagode sosai da fura" Murmushi ta kuma yi mun haƙoranta kamar ƙanƙara dan haske, a gaskiya Hama kyakkyawar macece banga wata makusa a tattare da'ita ba face ta rashin wayewa, da ƙazanta kuma dan ƙafarta duk faso fasonnan ya ɗebi wata annakiya ya adana. Ga gashi iya gashi amman kitson a furje kuma cike da yayin katifa. Boɗɗo tace. "Hama wanna itace Babbar yarmu Adda Jabu, ba lallai bane ki san labarinta ba. Nima naci da bin diddigi yasa na san labarinta. Ta taɓa zuwa rugarnan da daɗewa lokacin muna yara ƙananu." Tare da Hama mu ka ci balangunnan mu ka taɓa hira dai haka. Duk da gajiyace ainun a jikina, ga tunane _tunane da suka haɗu suka cukurkuɗe mun rayuwata. Duk wani bugun zuchiyata bugawa yake yi da so da ƙaunar Gwadabe na. Haka tausayin mahaifiyata da son jin matsalarta suma su ka dabaibayeni. Ina fatan in zame mata sanyin idaniya, maganin zubar hawayenta.amman ta yaya tunda mijinta ma bai karɓeni a matsayin ƴa ba, tunda gashi a darennan ya kasa haƙuri ko da kwana guda ne in yi. Ko ma Iyaa Debisi ta faɗa mun yana da faɗa, bauɗaɗɗen mutum ne ainun. Tunani, da zafi, da sauro su suka hanani huce gajiya ta hanyar saka haƙarƙarina a ƙasa, katifar yayin dana kwanta akai sai sossokeni kawai take yi. Babu shiri na miƙe na fito tsakar gidan, duk yawan matan gidan suna kwance a tsakar gida bisa katifun yayi. A kan tabarma na kwanta iska na ɗan hura ni kaɗan. Da haka ɓarawon bacci yayi awon gaba dani izuwa asubar fari, kwaramniya da kukan shanu ne ya farkar dani. Ashe nonon shanu ake ta tatsa, su kuma sai kuka suke yi. Wasu daga cikin matan na gansu suna burga nono da wani itace mai kama da maburgin miyar yauƙi, wasu kuma suna ta aikin dahuwar madarar shanu, yayin da wasu suke sharar garken Shanu, wasu kuma girkin safe suke yi. Ina buɗe idanu Hama dake shara tace. "Jabu kukan nagge ya tashe ki ko? " Tai maganar tana murmushi. Nima Murmushi nayi mata kawai, na miƙe Boɗɗo dake zaune a cikin jerin matan da suke ta burga nono ta miƙo mun buta, tai mun nuni da ban ɗaki. Ruwa na kama na fito na ɗaura alwala na shige ciki. Na jima ina roƙon Allah yayi mun mafita, ya kuma sassauta mun soyayyar Gwadabe a ruhina, bazan roƙi ya cire mun soyayyr ba dan abadan Gwadabe bazai gaza samun gurbi a rayuwata ba. Tunano ƴaƴana yasa hawaye suka zubo mun a kumatuna, ba shiri na miƙe na fita. Ɗaya bayan ɗaya na dinga bin matan gidan muna gaisawa, mun shiga ɗakin ƙanwar Dada ma mun gaisa. Cikin garken shanu Boɗɗo ta jani wai in taya ta mu tatsi nonon Saniya ta dafa mana mu sha. A baya na bita zuwa cikin garken shanun a nan muka tarar da Hama a ciki ita da mijinta suna shafa ma wata saniya magani jikinta duk kuraje ya fito. "Wannan itace baƙuwar tamu Boɗɗo? Ai Hama yanzu take faɗa mun cewar mun yi bakuwa kuma ma ƴar uwa" Cewar mijin Hama wani dogo siririn bafulatani sosai, ga gashi a kwance a kanshi lub, na lura kamar yafi kowa tsayi a gidan, ko dan ya fi kowa sirantane oho. "E Yaya Hamma itace baƙuwar tamu, Ita ce sama da Amaduyal, daga ita sai shi, a birni take aure can Kano" Murmushi ya sake faɗaɗawa yace. "Sannu da zuwa, baki tawo mana da yaran ba?" Ɗan murmusawa nayi bayan mun gaisa nace dashi. Na baro yara a gida sabida makaranta" Baice komai ba sai ɗan murmushi da yayi, ya kaɗa shanu sama da talatin suka bi bayanshi da ƴar sandarshi da halama kiwo zashi. Ni dai ina raɓe a bayan Hama tsoron shanun nake yi, ina dai kallo Boɗɗo na tatso nonon wata farar ƙatuwar saniya mai baƙin ido, ita kuma Hama tana dai ta shafama wannan saniya magani a duk jikinta, kuɗa sai damun saniyar suke yi tana ta kaɗa kanta. Fitowarmu daga cikin garken kenan sai ga su Cubu sun shigo gidan, amman ta wata ƙofa da ban ba ta ƙofar da muka shigo jiya ba. Idanu na ƙura musu, su basu da fari can ɗinnan . Yanda duk suke kallona a kunyace su nai mun kallon so da ƙauna shi yafi komai burgeni sosai. A barandar dake ƙofar bukkar Boɗɗo muka zauna. "Adda Jabu wadannan duk ƙannenki ne iyakarmu mu huɗu ne, shi Amaduyal shi baya nan. Iyakar yaran Dada kenan, nasan baki san iyakarmu ba, kamar yadda suma duka babu wanda ya sanki sai ni, nima saninna gani ɗaya ne." Daɗi ya lulluɓeni ganina a cikin ƴan uwana cikin Dadana, kuma sai kirana suke da Adda Jabu fuskokinsu da zuchiyoyinsu a cike da fara'a. Nawa bazai ma musaltuba. Tuwon farar masara aka kawo mana ɗumame da baƙar miya kamar kwalta, ko miyar meye wannan oho, sai madarar shanu mai zafi, tuwon sai ƙamshin man shanu yake yi. Loma ɗaya da nai karambanin sakawa a bakina da ƙyar da maƙyarƙyata na iya haɗiyewa tare da danneshi da Madara mai ɗumi. Muna zaune a wajen ina ɗan musu tambayoyi suna bani amsa, wata hausar ma da ƙyar suke fahimtar me nake nufi sabida tayi musu girma. A bakinsu naji ai kullum Dada tana zuwa cikin bini kai nono, fura, da man shanu. Tsawon tasowarsu da hakan suka san iyayen nasu, su kuma yara maza kiwon shanu suke fita yi, in suka girma har gari_gari suna iya fita kiwon shanun. Boɗɗo tace. "Ko ni ma kullum ina fita tallar nono, mu da kuɗin wannan nonon muka dogara, bamu da wani abunyi sai kiwo. In mace ta siyar da nono, a ciki zasu ci su sha, su yi sutura, har su tara kuɗin magani in wata saniya ba lafiya a nema mata magani dashi. Ƴan mata kuma da ba aure a kansu, da kuɗin tallar nononsu ake yi musu kayan ɗaki da komai da komai, wata ma har ta tara kuɗi itama ta sai ɗan maraƙi da haka har su zama garken da yaranta zasu ci gado suma. Matan ma a wasu gidajen suna fita kiwo. Ko su Cubu suna zagayawa amman da awaki ba shanu ba." Jigum nayi ina ta kallonsu jikina a mugun mace. Dama duk uba uban tsarabar da Dada take yi mun in zata zo ganina da kuɗin tallar nono take yowa?" Sai naji zubar hawaye masu zafi, tare da saka ɗamarar sauya ma Dada wannan rayuwar tallan da izinin Allah. Ana cikin haka sai muka jiyo sallamar Dada ita da wasu mata su su biyu, sai namiji guda ɗaya sun shigo kai tsaye kasancewar gidan duk dangin junane. Ɗakin Yafendo Kaɓoji suka nufa, mu kuma muka mara musu baya zuwa cikin bukkar. "Zo Jabu ki zauna a kusa da Yafendonki." Wata mai kama da Dada ta faɗa. Kusa daf da ƙafafunta na zauna kaina aƙasa na gaishesu cike da ladabi. Suma cikin karramawa da haba_haba suka amsa. "Wannan ƙannenane duka. Ga Yafendo A'i, ga yafendonki mai sunanki kin zauna a kusa da'ita. Zai Baffanku Musa gashi, sai Yafendonki Kaɓoji gata nan itace surukar Baɗɗo,. Ta nuna mun mahaifiyar mijin Boɗɗo. Kafin ta ɗaura da nuna mun su Cubu tace. " Wadannan kuma duk ƙannenki ne kece babbarsu, Amaduyal baya nan shi kuma na faɗa miki tun jiya." Murmushi kawai nayi dan na lura a damuwa Dada take sosai. Yafendo Jabu ce tace. "Zan ɗaukeki in tafi dake gidana, can ma akwai Daso shekarunku zasu yi ɗaya mijinta rasuwa yayi ya barta da yara tara. Zan zagaya dake dangi su ganki, zaki ɗan jima kafin ki koma ko?" A sanyaye nace. Na dawo nan da zama baki ɗaya ne, auren nawa ya ƙare. Kuma dan Allah a hannun Dada nake son zan zauna" Gabaki ɗaya suka kalleni, banda Dada domin ita bata wani gane Hausa har sai da ƴan uwanta su kai mata tafintar abinda na faɗi. Da sauri ta ɗago ta kafe ni da ido cikin yaren yarbanci tace. "Yanzu sai da wannan auren ya mutu, dangin mahaifinki sun ƙi barinki kiyi zaman auren ko? Dama tun farko da dan tani akabi da Debisin dai zaki aura domin shi yafi cancanta da sanin daraja da kimarki. Ita Iyaan taki ce ta amince miki ki dawo hannuna da zama alhalin tasan komai, zamana tare dake Jabu bazai yiwu ba. Tun jiya da kika shigo garinnan ban runtsaba har zuwa wayewar garin yau. Abinda nake so dake shine ki bi Yafendonki ki zauna a hannunta akwai Daso zaku dinga zuwa tallar nono tare, komai ma zaku ringa yi a tare. Amman ina mai baki shawarar ku koma birni inda kika fi wayo ki ci gaba da zama rayuwar Ruga cike take da ƙalubale, kumama ba iyawa zakiyi ba. Nima in kuɗaɗena suka haɗu zan je in dubo yaran naki. A hannun dangin ubansu kika baro su?" Wasu zafafan hawayene suka gangaro kan kumatuna, tabbas akwai matsala shin mijn Dada baya ƙaunar ganina kenan, baya son ya samu ladan riƙon marainiyar Allah, ko da wani abunne wanda ni ake ta ɓoye mun ne? Duka waɗannan amsoshin na adanasu inaso duk lokacin dana samu lokaci mai kyau da Dada zata amsamun, ta bani tarihin mahaifina cikakke. Dan bansan wasu abubbuwa a game dashi ba sosai. Na dai san sunanshi, sai hotonshi babba dake kafe a falon Iyaa, sai hirarshi da watarana ke shigowa cikinn zance haka in su Iyaa na yi a tsakar gida. Baffa Musa yace. "Allah shi kyauta. Ni ina ganin tabi Jabu ta zaunaa a hannunta ko babu komai zasu dinga ɗebe ma juna kewa ita da Daso. Kuma komai zasu iyayi. Dan in hanuna nace ta komo bani da wata budurwar ƴa a gabana ma. Tunda tace tana son zama a zuba mata ido, in taji wuyar da bata sababa da ƙafafunta zata koma Birni aradu" Yafendo kaɓoji tace. "A barta a hannuna tana ganin Boɗɗo sai hankalinta ya kwanta, kuma anan akwai Hama naga tun jiya da tazo suke hirarsu tare, kuma akwai matan ƙannenta a cikin gidan ƙila tafi jin daɗi. Kema Adda Daso zuwa ganinta zai fi miki sauƙi. Zasu dinga zuwa tallar nono da Hama dan kar damuwa ta dameta." Baffa Musa yace. "A'a ki barta dai Jabu ta tafi da'ita can wajen nata. Ita kanta Daso tana buƙatar wacce zasu dinga shawartawa dan gudun damuwa. Ke Jabu ki je ki ɗebo kayanki sai ku tafi, Allah bashi in ita Daso mahaifiyarki ta samu daidaito da Mijinta kya dawo hannun nata, duk da nasan mutumme bauɗaɗɗe ga taurin kai da dagiya. A kan ki meye ba'ayiba a shekarun baya da suka shuɗe. Ita yar mahaifinkiToyosi ai tasan komai yaƙi an yishi" Bani da zaɓi dole haka na kinkimi jakata na bi Yafendona zuwa gidanta, tafiya mu ka yi mai ɗa karen nisa, kamar ma ba ƙauye ɗaya suke da Dada ba, kuma fa a ƙafa su kamar ma basa son hawa Acaɓa. Gidanta kam ita kaɗaice a yadda na lura daga ita sai mijinta da yaranta. "Jabu ga ɗakin Daso ki shiga ki ajjiye jakarki, zan tafi tallar nono yanzu, ki shirya sai in kai ki wajen Daso ku zauna kina tayata miƙa Nono. Mu nan ba'a zama daga masu kiwo sai masu fita tallar Nono " Ɗan murmushi na ƙaƙaro kawai. Bukkar data nuna mun ciki na shiga na ajjiye kayana a gefen gadon ƙasa, a kusa da inda naga jakar kayan da nake zaton na mai ɗakin ce Daso. Taya Yafendo ɗaukar ƙwaryar nono ɗaya da buhun bakonta nayi. Muna tafe muna cin karo da mata da yara kowa da ƙwaryarshi ta nono a ka za'a tafi talla. Maza da samari kuma sai wuce mu da garke_garken shanu suke yi suna shiga jeji kiwo. Rayuwar ƙauyen ta matuƙar bani sha'awa, gasu da tsabta ainun kamar ba ƴan ƙauye ba ma, ƴan ƙazaman basu da yawa. Wannan akori kurar muka kuma shiga cike da mata masu tallar Nono, sai yarata yaren Fulani suke ta faman yi, ni dai ina cikinsu ƙwalam har muka iso babban titin mota inda matafiya ke wucewa, anan naga mata da yara jejjere a titi sai ƙulla Nono a leda suke yi, wasu kuma suna damawa. "Mu je kinga ga can Daso bari in kai ki wajenta, ni cikin gari can nake zuwa tallan nono ni da Daso uwarki" Zungui_zungui na bita har gaban wata siririyar fara sol ɗin mace kamanninta kamar an tsaga kara ita da Dadarmu, har kaminnin ya ɓaci. A cikin yaranta ma babu wadda yayi kamannin da ita irin haka. Dariya Yafendo tayi ganin irin yadda na ƙure Daso da ido. "Daso kenan mai kama da Adda Daso sak. Sanadiyyar kamanninsu ne yasa taci sunanta. Daso ga ƴar uwarki tazo daga birni . Zata taya ki siyar da Nono, in yaso zuwa gobe itama sai ta fito da nata ƙwaryar." Hannuna Daso ta jawo ta matso dani kusa daf da'ita. Sai farin cikin ganina take yi kamar dama can ta sanni. Da Yafendona ta yarata mata wacece ni da yare ai sai ta rungumeni tana mai cike da farin ciki. Nima sai naji zuchiyata ta ɗan yi wasai. Anan Yafendo ta sake hawa abun hawa ita da tawagar wasu mata. Mu kuma duk motar da tazo wucewa sai mu tawo da gudu ana turereniya a tsakani, yayinda kowa ke son asai nashi. Haka suke yin tallarsu. A gefen titin cikin ciyawa mu kai sallar azahar, Daso ta dama mun fura da nono da siga cikin ƙoƙo. Tas na shanye furarnan ga nonon ba tsami sai garɗi. Wajajen bayan la'asar lis muka ɗau hanyar komawa gida, nono da furar da Daso ta ɗauko ya ƙare duka. Ko da muka doso ƙofar gidan sai mu ka ci karo da Yaya Hamma mijin Hama a tsaye a ƙofar gidan hannunshi riƙe da ƴar baƙar ledarshi. Yana ganinmu yayi murmushi. "Yaya Hamma kaine a tafe da yamma sakaliya haka?" Cewar Daso kenan. "Nine Daso, kin ganni na jima ina sallama ashe babu kowa ne a gidan? Jabu har dake baƙuwa aka je tallan Nono, har kin huce gajiyar tafiya kenan?" Kaina na sauke ƙasa ina wasa da zoben azurfar da Gwadabe ya sai mun lokacin muna nema. In ma na zauna Ni kadai a gidan, ba daɗi zanji ba, tunanine kawai zai addabeni. Amman kaga dana shiga cikin mata ƴan uwana sai na ji daɗi." Shiru yayi baice komai ba. Daso tace. "Yaya Hamma mu shiga daga ciki mu zauna ai hirar zata fi daɗi ko?" Bai mata musu ba, ya kutsa kai cikin gidan muka mara mishi baya muma. Kano Gwadabe:. Tun bayan fitar Iyabo daga ɗakinta bayan Babala ta tursasa yayi sakin. Hawaye suka zubo daga guraben idanuwanshi. Yana jin wani zafi da turirin zuchiyarshi, ji yake tamkar rayuwarshi ce aka tsayar mishi. Maganar Yaya Hambali ne ya dawo dashi cikin hayyacinshi. "Shikenan ɗan uwanmu ya dawo mana, kai yau zan zuba ruwa a ƙasa in sha. Babala ni sabida jin daɗin wannan sakin ko? Zan buɗe ma Gwadabe katafaren shagon kayan masarufi, uwar kuɗince kawai tawa amman dangane da riba ko ta miliyan zai samu babu ruwana da kuɗinshi." Murmushi Babala tayi tace. "Ato yanzu ne shi kanshi zai dawo cikin hayyacinshi daya rabu da ala ƙaƙai. Kasan Allah duk abunda Gwadabe yake yi ba'a cikin hayyacinshi yake ba sam yarinyar ta game dabaibayeshi da asiri baya ganin kowa da gashi. To ta faru ta ƙare, ni naso ma ta tafi da yaranta da zai fi, dan babu wanda zai ƙaunacesu, kuma bazan bari Laila tayi wahalar yarannan ba wallahi." Yaya Hambali yace. "Yanzu ma ai sai dai ki tafi dasu ƙauye Babala kafin yayi wani auren sai a dawo ma da Laila su, ki dai yi haƙuri Lailan ta riƙesu" Sai da aka ambaci Laila ne Gwadabe ya ɗago idanuwanshi da suka rine ya kalli Yaya Hambali kallon tsab. Ya dawo da kallonshi ga Babala itama. Ai ko karen haukane ya cijeshi ba ya auro Laila ya ajjiyeta a gidanshi matsayin mata ba. Yarinyar data kasa riƙe amanar aurenta take turo mishi da saƙonnin soyayya da igiyoyi uku a kanta itace zai auro ya ajjiye a gidanshi matsayin uwar ƴaƴa. A ɗauri kashi ko a ɓata igiya. Kab ƙauyan Takai waye bai san Laila ɓarauniya bace, ko ɓera sai dai ta zama yayarshi shi ƙaninta. Bai dai ce dasu uffan ba har suka gama maganganunsu da baya fahimtar komai suka fice. Toye ne ya fito daga ɗaki yace da Abbanshi. "Abba yinwa muke ji" Hannun yaron ya jawo ya ɗaurashi a cinyarshi yana kallonshi. Bakinshi irin na iyabo babu maraba, hawayen dake shirin zubo mishi yayi saurin ɗaukewa da hannunshi. "Bari in kawo muku abinci ko, ina Taiwo da Kahinde suke?" Ya tambayi yaron. "Suna ɗaki sai kuka suke yi" Ba shiri ya miƙe tsaye, hannun Toye ya ja suka shiga ciki. Taiwo ce take ta kuka ta kifa cikinta akan gado. Kahinde sai bubbuga bayanta yake yi yana gwarancenshi. MRS BUKHARI 3064127935 Buhari Ibrahim Ladan First bank Sanya nera 500 ɗinki kuɗin karatu anan. Wannan asusun gudauniyarmu kenan. Ki sani in kika siya wannan littafin tamkar kin taimaki iyayen marayune, dama su kansu marayun Kuzo mu yi tarayya cikin aikin lada. Ƙarƙashin Amila Foundation gidauniyar da muka buɗe ni da megidana domun iyayen marayu, ko tainakon marasa lafiya. Waɗanda suke cikin group dina mai suna (NAMA YA DAHU ROMO ƊANYE) 300 kacal zasu iya kuɗin karatu NAMA YA DAHU... ROMO ƊANYE BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 13 Tausayi gami da ƙaunar yaran ta shigeshi ainun. Harma yake ganin ganinsu ne kaɗai ka iya rage mai zafi da turirin rashin Iyabo. Haƙiƙa yayi rashin macen kirki, macen da tafi kowa sonshi da sanin hamimmancinshi. Ji irin wuya da ɗawainiyar da ta dinga yi a sanadiyyar ciwonshi. Amman ji irin sakamakon da su Babala suka yankar mata na tarwatsa duniyarta, tare da farraƙata akan ƴaƴanta da mijinta. Rungume yaran yayi jikinshi babu laka sam, rarrashin Taiwo yayi har sai da tayi shiru. "Toye zo ka kula dasu bari in siyo muku waina kuci" Yana faɗin haka ya fice, babu ko nera biyar a jikinshi, bashin mai wainar ta bashi na wainar hamsin, ya dire musu suka ci, suka sha ruwa. Fita yayi ya shiga kitchen ɗin Iyabo ya kunna risho ya ɗaura musu ruwan wanka. A kitchen ɗin yayi zamanshi tare da tariyo irin rayuwar da su ka yi da Iyabo, da irin nutsuwa da farin cikin da take samar mishi babu dare babu rana. Yana kitchen ɗin Babala ta leƙo da kwanon abinci a hannunta, ganin yanda yayi tagumi ya tusa risho a gaba ne yasa tayi turus a tsaye da kwano a hannunta. Yaran kuma tana jiyo ƙiriniyarsu. "Gwadabe au so kake yi tunani ya halakamun kai. Alhalin ita tana can hankalinta a kwance?. Yanzu me kake yi a ɗakin girki" "Ruwan wanka nake tafasawa zanyi ma yaran wanka Babala" Harara ta watsa mishi tare da cewa. "Ba cewa nayi maka zan tafi dasu ƙauye ba, ka ganni abinci na leƙo in ajjiye maka fa, sai in ɗebesu danyanzu zan juya yau muna da biki a gidan mai gari" Ajjiyar zuchiya ya sauke, tare da tasowa jiki ba kuzari, kirjinshi kuwa sai harbawa yake yi, zuchiyarshi na watsa jini jikinshi bisa rashin ƙa'ida. Hakanne ya haifar mishi da jin jiri da mashasshara mai zafin gaske, dan har hucin zafi yake ji a fuskarshi. Bakinshi kuwa tamkar maɗaci aka zuba mai haka yake ji. Inda Babala take tsaya ya isa. "Babala yarannan ni zan riƙesu da hannuna. Inaso zasu yi karatu mai zurfi ba zasu yi rayuwa a Takai ba. Kab yaran gidannan a cikin gidannan su ke rayuwarsu, wasu muna tare dasu, wasu kuma sun yi aure. Dan haka nima zan riƙe yarana" Babala tace. "Da kyau Gwadabe. Dama ni dan in tausaya maka in ɗauke maka nauyine a matsayinka na namiji. Amman tunda har kana ganin reno abune mai sauƙi, gaka ga yaran. In sun ga dama suga ƙarshen biro. Duk karatunsu ai basu isa ganin ƙarshen biro ba. Kuma ka shirya sati me zuwa ka tawo zance wajan Laila ka shiga sahun manemanta, dan manema sun yi mata ca a halim yanzu kowa so yake ya ɗauketa, ni kaga tafiyata" Ta dure mishi kwanon abincin nashi ta fice tana surutai tare da kutuntumawa Iyabo da yarenta zagi. Idanu Gwadabe ya lumshe kawai. Shi yaima yaranshi wanka fes, ya ja hannunsu har zuwa islamiyya kasancewar ranar asabar ce babu boko. A hanyar shi ta dawowane yaci karo da yaya Hambali a mota zai tafi kasuwa sai ya ɗan dakata. "Gwadabe daga ina kake haka? Kaga takalmin ƙafarka ɗaya naka ɗaya na matarka ne fa. An ya Gwadabe asirin da dangin Iyabo su kai maka ya gama sakar ka kuwa, sai kace wanda akace ma Babala ta riga mu gidan Gaskiya" Numfashi dogo Gwadabe yaja, ya kai duba kan ƙafafuwanshi, zahiri takalmin Iyabo ya ƙaƙaba a ƙafarshi duk rabin dunduniyarshi a ƙasa yake, takalmin ma kuma mai ɗan tudu. Ɗayar ƙafar kuma takalminshi taka teba ya saka. Allah yana gani baya cikin hayyacinshi balle har ya fahimci ƙafarshi a matse take, ko yaji yafi tuɗu ta ɓarayi guda. Murmushi kawai yayi. "Kaga yara na miƙa makaranta, bansan wari da wari na saka ba, hankali shine gani, idanu ƙululun kawai ne." Kallonshi Yaya Hambali yayi wata ƴar dariya harda shewa kafin yace. "To sai zuwa yaushe zaka soma zagayawa kasuwar, tunda dai sauƙi ya samu, kuma Iyabo data raɓeka ta raba mu da kai ta zama tarihi a rayuwarka. Kaga ai sai ka zo mu ringa tafiya kasuwa, kwanannan kaima zaka sai motar da kake so ka dinga tuƙawa" Murmushin yaƙe wanda yafi kuka ciwo Gwadabe yayi, yace. "Nagode da tayinka Yaya Hambali. Amman bana jin zan amshi wannan tayin naka. In na warware da kyau zan nemi sana'a dede dani in soma. In Allah ya dafa mini sai kaga na yi gida harda mota, yarana sun samu ilimi ingantaccen" Iyakar abinda Gwadabe ya furta kenan Yaya Hambali ya fusata har yana doka sitiyarin motarshi. "Ni kake faɗa ma magana haka gatse_gatse gwadabe? Ka mance sanda nake goyonka muje gona, nake cire kudina in biya maka kuɗin makaranta, in kama hannunka in kai ka makaranta. Kaci kasha naima sutura duk da dukiyata, kuma nake matsayin uwa da uba duka a wajenka? Ko Harisu bai isa faɗa mun maganar banza ba, balle kai wanda a haife na haifeka?" Sai zazzare idanu yake yi yana kumfar baki, Gwadabe dai baice mishi komai ba. Har ya gama hargaginshi. "Hmmm Yaya Hambali kenan. Shagone dai ni Gwadabe bana so bana buƙata. Bana nema a wajenka a wajen Allahn daya baka nake nema, kaima ba dabararka bace ta baka ba ka san da wannan." "To Shikenan na cire hannuna a kan ka tunda dai taimakonka da nake son yi ne baka so. Kaje kayi Abinda kake ganin ya dace da kai ba shikenan ba? Amman in sha Allah dakai da yin kuɗi har abada Gwadabe muddin ina raye baka ba yin arziki da Hambali kake magana, ɗan iska marar kunya fitsararre Allah dai ya kwashe maka albarka" Yana gama faɗan haka fuu ya ja motarshi ya buɗe Gwadabe da ƙura, ya cika mishi idanu fal da kasa. Idanunshi a runtse suke hawayen bakin cikin danginshi na tsiyaya a idanunshi. Shin wai me yasa ƴan uwanshi su ka fi sha'awar ganinshi a cikin halin damuwa da ƙunci ne, anya kuwa Babala itace mahaifiyarshi ta asali kuwa, ko dai shi ɗin ɗan riƙone bai sani ba? Amman da ace ɗan riƙone da dole ƙauye su sani domin a ƙauye kunne ya girmi kaka. A wajen Gwadabe ya ci alwashin bazai taɓa tambayar kowa komai ba, bazai karɓi ko ficika daga hannun kowa ba. Zai fita nema, kamar yadda Yaya Hambali ya fito nema shi shi kaɗai a shekarun baya, kuma Allah ya buɗa mishi. Shima Allah shine gatanshi ba Yaya Hambali ba, zai nuna musu shi namijine mai zuchiya ba mai hangen na wani ba. Idanunshi ya buɗe ya karkaɗe fuskarshi da idanunshi ya ci gaba da tafiya. Haka Gwadabe ya kwana a tsakiyar yaranshi, yanda rana ta kasance mishi haka darenma ya zame mishi. Sai juyi yake yi, yana tunanin irin rayuwar soyayya da kulawar da suka yi da Iyabo. Da irin abubuwan da akaita yi mata, kuma ta shanyesu duk dan ta zauna tare dashi. Amman daga karshen ƙarshe duk kiyayewarta sai da sakin ya afku a kanta. "Iyabo ina roƙa miki Allah ya baki mijin da zai jarabtu da sonki fiye dani, Wanda ya fini komai a rayuwa. Ya Allah ka kai baiwarka Iyabo gidan hutu da jin daɗi, mala'ikun Allah ku shaida ni dai a zamana da Iyabo babu cutarwa, kuma kune shaidar ni dai na ɗaga mata ƙafa dan ta shige aljanna. Allah ka haɗata da abokin rayuwar da zai ɗaga mata tashi ƙafar shima." Sambatu kawai Gwadabe yake ta faman yi kamar zararre. Haka Gwadabe yai ta tunane_ tunane har gari ya waye musu. Kamar jiya bashin wainar ya kuma karɓoma yara su ka ci ya kaisu makaranta Yana shiga gidan ya tadda dangin Iyabo suna tozarci a tsakar gidan. Sun zo dibar ragowar kayanta da yayi ragowa, da suturunta dai da kayan aiki haka. A wannan rana ya yasha zagi da ele a wajen su Iya Beji. Har tukunya Iyaa Kokodeen ta kwaɗa mishi a gadon bayanshi. Da yaga tozarcin ya isheshi sai ya koma ƙofar gida yai zamanshi. Yaya Hambali kuma sai sababi yake yi cewar duk Gwadabe ne sila, daya haɗe musu jini da jikokin oduduwa. Gwadabe na zaune a ƙofar gida ya hango Bara'u tafe. Ƙuri yayi yana kallon tahowar abokin nashi har ya iso gareshi ya zauna daf dashi. Amman fa kafin yace wani abu sai ga su Iyaa Beji sun fito suna zage_ zage Yaya Hambali na biye dasu shima sababin yake yi. Kan kace me unguwa ta ɗinke, mata har ta katanga leƙe suke yi, kunsan mata akwai gulma ko ince son ganin ƙwaƙwaf. basu dena baloƙoƙinsu na gado ba, sai da Yaya Hambali ya cukume Iyaa Beji, a tunaninshi zai daketa. Ai kuwa taron dangi suka haɗu suka yi mishi da ƙyar mazan unguwa suka karɓeshi a hannunsu duk haushin Gwadabe suka saukeshi akan Yaya Hambali. Bara'u da Gwadabe suna zaune suna kallon ikon Allah kawai. Yaya Hambali ya matso kusa dasu Gwadabe a zafafe yace. "Allah wadaran naka ya lalace. Kaji dai kunya Gwadabe ace waɗannan gayyar na aiya gayyar na yadadan sune surukanka. Mu kanmu ka cutar damu daka dage sai da muka haɗa iri da yarbawa. Duk irin matan dake cikin hausa Fulani ka rasa wacce zaka so sai Iyabo. Jibi yadda mata suka dakeni har suka fashe mun baki dan iskanci kuna zaune" Bushasshen yawu Gwadabe ya haɗiye muƙut. Bara'u ne yace. "Yaya Hambali ayi haƙuri. Komai ai ya riga ya daya ƙare. Allah dai ya ƙara rufa mana asiri" "Gafara can. Bara'u ai ko kisa Gwadabe yayi ba zaka iya ganin laifinshi ba. Aikin ɓur in ji tusa" Ya buga kafarshi ta dama a ƙasa, kana ya shige cikin gida. Bara'u ya sauke ajjiyar zuchiya yace. "Kayi haƙuri Gwadabe na roƙe ka da girman Allah. Ka ɗauka wannan ƙaddarace daga cikin sinnar rayuwa. Iyabo kai mata adda'a gaba Allah ya bata miji na haƙiƙa. Ni kuma da nazo da zummar in tafi da yaran duka can wajena Sakina ta haɗe da nata ta riƙe. To ina cikin mota sai Tamu yai kiran wayata Allah da ikonshi na kwashe zance tas na sanar mishi, to sai yace shi zai riƙe ƴan biyun a hannunshi zai sa su a makaranta. In kanaso zaka iya barinsu a hannunshi. In kuma kayi aure zaka iya zuwa ka ɗebi yaranka ka baiwa matarka taci gaba da kular maka dasu. To nasan zaka fi son yarannan a hannunka Gwadabe. Amman sauƙi muke nemar maka kayi haƙuri ni zan tafi da Toye tamu zai riƙe Taiwo da Kahinde, tausayin yaran muke yi a hannun su Babala. Na ji daɗin samuwar lafiyarka, babu abinda zamu ce da Allah zai godiya. Ka yi haƙuri ka daɗa" Wata wawuyar ajjiyar zuchiya ya sauke mai nauyi yace. "Bara'u yau ko ni kuka ce zaku ɗauka da kai da Tamu ba yaran ba, bana jin zanyi muku musu. Yarannan naku ne ku yi yadda kuke so dasu. Nagode da soyayya Allah ya bar zumunci. Sannan Bara'u wallahi na rungumi ƙaddarata, ina fatan Iyabo ma ta rungumi tata ƙaddarar. Amman fa ni da Iyabo Allah shi ya haɗa zukatanmu. Ko anan gaba in nayi aure, matar zata tsaya ne kan iyakar matsayinta, bata isa hawa matsayin Iyabo ba. Ita kanta nasan hakanne ta ɓangarenta. Bara'u Iyabo mutum ce har da ɓari" "Zahiri Iyabo Mutum ce guda da ɓari. Allah yai mata sauyin alkhairi, kaima Allah yai maka sauyin alkhairi. Yanzu mu je mu shirya yaran, tunda jikinka yayi kyau ai sai mu je Abujar tare mu kai ƴan biyun. Daga nan sai mu wuce Takai. Dan Malam magaji ya zo jiya. Inajin su Yaya Hambali basu sani ba tukunna dai" Ai kuwa haka akayi. Bara'u da kanshi ya haɗa ma ƴan biyu kayansu a jakar buhu, ya haɗa na Toye. Gwadabe ya rufe ɗakin da ko tabarma babu. Yaima su Yaya Hambali sallama kan zashi Abuja daga can zai zarce Takai gaishe da Baba Magaji da yazo. Yaya Hambali yaso jin dalilin tafiyar, amman Gwadabe sai ya ɓoye mishi dan ko fuska bai bashi ba, yana kan turmi Yaya Haula na gasa mishi baki. Bara'u shi ya biya misu kuɗin mota. Cikin Awa shidda sai gasu a Gwagwalada. Da mota Tamu yazo ya ɗaukesu har zuwa dan madaidaicin gidanshi. Bayan sun yi sallah sun huta, Ayashe ta kawo musu abinci Falo ƙanwar Tamu na biye da'ita da plate a hannu. Ayashe ta shiga da yaran ciki, bayan ta jajantama Gwadabe abinda ya afku cike da jimami. "Kaga Shafs ce wannan data shiga ciki yanzu. Da shine nake tunanin Bara'u ba zan ba Gwadabe Shafa ba kawai. Kaga a matsayin wa kake a wajenta, kuma ta ɗanyi karatunta yanzu haka karatun diploma take haɗewa anan Gwagwalada. Da in ta kammala sai ayi auren ko ya ka gani Bara'u?" Bara'u yayi dariya suka tafa da Tamu kafin yace" "Yarinya zuƙeƙiya son kowa, gata budurwa sharab. Shafa a gabanmu aka haifeta. Bana mance taron sunanta, kasan gida _gida mu ka dinga bin abokanmu muna raba musu alawar gaiyata. Kowa yazo da sile da sisinshi. In abun ya tabbata zaiyi kyau sosai " Tamu yace. "Wato kai Bara'u baka da mantuwa sam. Ni ai tunanina in rama halaccin da Gwadabe yayi mini, ko banyi mai daidai da abinda yayi mun ba, in kamanta mishi. Gwadabe na baka Shafa halak malak. Nine maɗaurin aurenta dama. Zan mata bayani duk lokacin da ka samu nutsuwa sai ka neme ta, a hankali tunda ba sauri akeyi ba sai ku daidaita tsakaninku. Yara kuma zanci gaba da riƙonsu ko kun yi auren ma, in sha Allah ni zan aurar dasu da hannuna. Zan kuma so in haɗe su aure da nawa yaran dakan ɗaka shiƙan ɗaka" Gwadabe bai yi musu jayayya ba bare turjiya. Kwana ɗaya su kayi a garin Gwagwalada suka juya washe gari, bayan Gwadabe yayi sallama da ƴan yaranshi, abinka da yara sun shige cikin yara ƴan uwansu sai adabo ma suke ma uban. Ganin yaran sun sake ne uban ya ɗan ji ƙarfin guiwa kuma. Ruga Iyabo:. Tabarma Daso ta ɗauko ta shimfiɗama Yaya Hamma daga can gefe guda. Jatau ne ya shigo da garken shanunshi guda yana tafe yana waƙar fullanci, hannunshi da ƴar tsaraba. "Jatau yau kai ka soma shigowa gidan?" Da Hausa tayi mishi wannan tambayar. Shi kuma hankalinshi duka yana kaina, ina son in ɗebo ruwa a randar ƙasa in kawo ma Yaya Hamma. "Baƙuwa mu ka yi ne Daso?" "E baƙuwa ce kuma ƴar gida, Yayar su Boɗɗo ce tazo daga birni" Sai ya washe bakinshi muka gaisa cikin girma da arziki. Na dure ma Yaya Hamma ruwan sha a gabanshi na koma kan turmi na zauna. Jatau da Hamma nan suka kacame da yare, daga bisani Jatau ya wuce da shanunshi izuwa maɗaura. "Jabu zo ki zauna sabida ke nazo gidannan da yammannan" Daso dake hura wuta tace. "Ko ni na faɗa a rayina, sabida Jabu ne kazo Yaya Hamma" Sai tayi murmushi, nima murmushin na mayar mata, na ƙarasa kan tabarmar da Hamma yake na zauna a gefe. "Na ji labarin mutuwar aurenki ƙanwata. Abun ya dake ni ainun, naji tausayinki sosai. Amman mu zamu baki farin cikin da har sai kin mance da komai a matsayinmu na dangin uwa, muma zamu taka tamu kalar rawar, tunda kika zaɓi ki rayu damu a ruga, kika haƙura da rayuwar maraya duk da acan ki kai wayau. Kiyi haƙuri kinji am?" Wasu hawaye ne suka gangaro mun. Ban aune ba sai kuka mai gunji ya tawomun babu zato. A tiɓi tiɓi_tiɓi da kayan mazaunai na shige bukkarmu na zauna akan gadon ƙasarnan na shiga sana'ar kuka. Wani tuƙuƙin baƙin ciki da takaici sai yanzu ne komai ya soma dawo mini. Kuka na zage nayi na ban mamaki. Ƴan uwana suka bani sarari na dirji kukana yadda yayi mun nayi shiru dan raɗin kaina. Sai zuchiyata ta ɗan washe ta rage nauyi. Na yi zaman tunani a zaune bansan iyakar adadin ba. Sai shigowar Yafendo na gani kawai. Da sauri na share guntun hawayena ina duban fuskarta. Sai naga fuskarta cike da damuwa, da dukkan alamu damuwa da damuwata ce take yi. Ledar hannunta ta miƙo mun nasa hannu na karɓa kafin tace. "Ban isa hana ki kuka, ko hanaki damuwa da tunanin yaranki ba Jabu. Kinga Daso tun bayan rasuwar mijinta kullum sai ta yi kuka zuchiyarta babu daɗi. In Hamma yazo gidannanne ma take samu tayi farin ciki. Ni kuwa ban taɓa hanata kuka ba. Rabuwa da miji ciwonshi bashi da misali sam, musamman mijin da kuke soyayya da zaman lafiya. Ace mutuwace tayi muku yankan ƙauna. Ko kuma wata ƙaddararce ta raba ku ba da son rayukanku ba. A lokacin da mahaifinki ya rasu Adda Daso ta shiga wani irin mawuyacin hali. Mahaifiyarki har jinya sai da ta kwanta na tsawon wata shida masu kyau. Har gaban abada ba zata dena tunanin mahaifinki ba. Musamman data haɗu da azzalumin namiji magoki. Da girmansu haka bai bar dukansu ba. Zuwan da ki kayi ma dan kawai ta roƙeshi ya barki ki zauna a wajenta har ki gama kwanakinki ki tafi. A daren zagi da cin zarafi babu wanda baiyi mata ba, har marinta sai da yayi" Da mugun sauri na ɗago. Wata kibiya ta soki ƙawon zuchiyata, siraran hawaye suka gangaro kan kumatuna masu zafi. Yafendo yanzu kamar Dada da girmanta da yaranta manya sai mijinta ya daketa harda zagi, a halin da take rayuwa kenan?" Zama Yafendo tayi a kusa dani tace. "A haka Adda Daso take rayuwa da azzalumin mijinta. Har da tsohon ciki a jikinta dukanta yake yi. Ko a cikin Boɗɗo yayi mata wani dukan da tai ta zubar da jini, duk muka cire rai da cikin. Sai daga baya cikin ya tashi. Amman sai da Boɗɗo ta shekara biyu cir a kwance a cikinta kafin ta haifeta. Wannan kuma ana tunanin da sa hannun uwar gidansu akan lamarin. Kuma ya karɓe shanunta na gado ya haɗe da nashi shanun, Adda Daso bata ribatar komai. Shanune masu tarin yawan gaske, kinga gaa nawa garken can Jatau ya dawo dasu, sai hauhawa suke yi. Ita kuma bata san adadin yawan haihuwar da nata shanun suka yi ba, dan nata mata ne, namijin guda ɗaya ta samu. Ke Jabu in nace zan ta baki tarihin mijin mahaifiyarki zamu kwana mu wuni a nan bamu ƙare ba. Shi yasa ko da yaushe take cike da tunanin marigayi mahaifinki. Soyayya da kulawar daya bata ne, yasa ta fifita soyayyarki fiye da soyayyar duk yaranta. Duk ɗan abinda ta samu burinta ta tara in zata kai miki ziyara ta miki hidima, kinji na rantse miki tun bayan rasuwar mahaifinki ban sake ganin annuri akan fuskar Adda Daso ba, sai yau data zo gidannan tana sanar dani zuwanki garinnan, damma a hakan ta kwana cikin tashin hankali akan mijinga." Kukane yaci ƙarfina, zuchiyata sai luguden daka take ta faman yi. Ina jin duniyata na wujijjiga rayuwata. Tausayi da zunzurutun kaunar Dada ya sake ɗamfaruwa a raina. Yafendo ta dafa ni nayi firgigit na kalleta. "Ki tashi ki ɗauro alwala ki yi sallah. Wannan ledar dana baki Hamma ne ya ce a baki. In ki ka yi sallah sai ki fito tsakar gida in gabatar dake ga ƴan uwanki" Jikina a sanyaye na ɗauro alwala nayi sallah. Na daɗe ina adda'a, a lokacin zazzaɓin dake jikina ya rabkeni ainun, ko idanuna bana iya buɗewa. A halin da Daso ta shigo ta same ni kenan. Abu kamar da wasa_wasa sai na rasa numfashina, jikina kuwa kamar garwashin wuta. Sai da na shafe tsawon wata biyu da kwana goma sha ɗaya cur a kwance babu lafiya, sai maganin gargajiya akeyi mun, hatta ruwan wankana da ganyen magani a ciki, kuma Yaya Hamma suke kawo mun magani da ɗan abinda zan sa a bakina, Yaya Jatau ma yana kawo mun ɗan abun kwaɗayi, matarshi ma kullum zata shigo ta duba lafiyata, kuma in Yafendona, da Daso sun tafi tallen Nono, Hari itace ke zama dani matar Jatau. A wannan jinyar naga gatan dangin uwa. A wannan kwanciyar sai da dangin Dada suka zo kab suka gaisheni da jiki, a lokacin na gansu suka ganni. Dada kuwa kullum cikin suntiri suke ita da su cubu da Yusufu, Boɗɗo kuwa da hama suma kullum babu fashi sai sun zo dubani. " A cikin wata uku cib jikina yayi ƙwari babu laifi, lokacin iddata ta cika cib, lamarin da ya ɗan ƙara jagula lafiyar jikina kenan, sai da Yaya Hamma ya dinga bani baki, tare da lafuzza tausasa, har mamaki nake yi in naji yana furta wasu lafuza masu kwantar da zukata. Da yamman wata asabar bayan Daso ta dawo daga tallar nono muna ɗaki mu na ɗan taɓa hira, fuskarta cike da farin cikin ganin jikina yayi kyau yau. Duk da na rame fiye da tunanin masu karatu, fuskata ta yi fayau. A jinyar dana kwanta na samu kulawar mutane uku da bazan mance da hidimar da su kai mun ba. Daso, Yaya Jatau, Yaya Hamma. Duk kwanan duniya Daso itace mai bani abinci a baki, tare da gyara mun kwanciyata, ko amai nayi itace ke kwashewa. To a wannan kwanciyar jinyar nayi jinin al'ada hatta da tsumman jini da ɗan kamfaina Daso ke wanke mun da ruwan toka ta shanya su, wanda zai maka irin wannan aikin ba ƙaramin masoyinka bane. Yaya Jatau kuma kullum in zai dawo daga kiwo yana kawo mun wani gashasshen hanta mai yaji, shi nake ci da daddare, shi kaɗai ne nake iya ci ba tare da naji tashin zuchiya ba. Yaya Hamma kuwa shi ya dinga bin ƙauyuka ruga_ruga dan sama mun magani, wani gari wani ganye, ko kiwo yaƙi ya mai da hankali akai har sai da ya ga samuwar lafiyata. Kuma kullum a cikin yi mun nasiha da tattausan laffuzza yake. Muna ɗan hirarmu muka ga an buɗe labulen kaban dake ƙofar bukkarmu. Yaya Hamma ne ya shigo hannunshi riƙe da kwano. Daso ce ta miƙe ta karɓi kwanon ta dure a gabana tana dariya tace. "Nasan ai nata ne ko Yaya Hamma? Shi yasa na dure mata a gabanta" Dariya yayi tare da nunata da yatsa yace. "Kin ganki akwai zolaya. Ai itace marar lafiya a gidan, shi yasa na kawo mata tasha romo" Sai tace. "Nima in na kwanta jinya ashe zaka kula dani sosai irin kulawar da ka ba Jabu?" Dani da'ita duka sai muka kafe shi da idanu. Sai da ya zauna a ƙasa ya tanƙwashe ƙafarshi kana yace. "Ai kamar ratayayyen hakkine a kaina in kula daku, ko da a gidan mazajenku kuke balle kuma kuna gabanmu. Jabu ya ƙarfin jikin, yaya haƙuri ds rayuwa, da haƙurin zaman ƙauyanmu mara wuta balle ruwan daɗi?" Ɗan murmushi nayi nace. Jiki Alhamdulillah sauƙin yana samuwa sosai. Babu abunda zance sai godiya. Kuma ina godiya da wannan ɗawainiya da kukaita yi dani" Bayan na bashi amsar na sauke kaina ƙasa. "Ai ya zame mana dole, ki daina godiya ma Jabu" Miƙewa tsaye yayi. "Ba dai tafiya ba?" Cewar Daso. "Tafiya zanyi. Dama abinci na kawo mata. In kuma ƙara ganin jikin nata. Amman dai ku shirya zuwa dare zan zo mu leƙa dandali Jabu taga yadda muke wasanninmu gwanin sha'awa, wala Allah hakan ya rage mata raɗaɗi." Dariya nayi musu kawai. Aini na rabu da nishaɗi tunda na rabu da Gwadabe, dan nishaɗi na wajen tsuntsun soyayya. Amman a fili saina amsa da cewa. Allah ya kaimu" Ko dan in ƙarfafasu tunda burinsu suga na saki jikina na mance komai. Da haka mu kai Sallama, bamu muka fito daga cikin bukkarmu ba saida mu ka sallaci sallar isha. A tsakar gida muka ci fsrfesun da Yaya Hamma ya kawo mini harda Yafendo da Jatau, dama Hari Matarshi. MRS BUKHARI ce. *Ƴar uwa ina fatan baki mance da kayan ƙamshin Mrs Bukhari gidan ƙamshi ba ko? Ƴar na gata ba take haye ba, Kanuri gidan ƙamshi. Matso kusa ƴar uwa ina da turarukan wuta nau'i daban_daban. Turaren kaya da zaki turare gidanki ƙamshi ya riƙe miki surura, sannan inada kabbasiyya turaren ruwane da ake fesama sutura a yayin da ake turara kaya a kabbasa, kana inada turaren wadrop da ake saƙawa a tsakankanin kaya. Turarukan wutana kuwa in kika turara gidanki yana sati guda yana ƙamshi. Inada turaren turara jiki gangariya wanda yake kama fata. Akwai kulaccam ta matan aure mai sirrin rikita maigida, ga gyaran fata. Akwai kuma kulaccam ta gashi, haɗe da turaren fesawa a gashi. Mai gayya mai aiki humrata ta matan Aure mai sirrin ƙara dankon soyayya, kiga oga na shinshinarki kamar mage taji ƙamshin kifi ɗanye. Inada humrori kala_kala. Ina da room freshener, da mopping mix mai sirrin ƙamshi. Kar in ta lissafo muku duk wani nau'in ƙamshin da kikeso in kika samu Mrs Bukhari ƴar mutan Maiduguri kin samu ƙamshi. ( Albishirinku akwai package na musamman dana tanadarma masoya wannan littafi nawa. Package ne mai ɗauke da abubuwa huɗu manya kuma a kan kuɗi ƙalilan karki bari garaɓasarnan ta wuceki zaki ciji yatsa kwasha_kwasha nayi da kayana domunku)* NAMA YA DAHU.... ROMO ƊANYE GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM 14 Muna gama ci sai ga Yaya Hamma ya shigo. Yana saye da wani yadi mai ruwan bula ɗinkin ƴar shara, yadinnan duk ya gaji yayi laushi sosai sai laɓewa a jikinshi yake yi. Wandon jikinshi kuma na koren yadi ya saka ya ɗauko hular tashi ka fiye naci irin hular da fulani suke mugun so ɗinnan ƴar madina mai fara da baƙa a jiki, ƙafarshi kuma saye da takalmin roba mai ruwan bula duk ya fashe, sai ƙamshin wani turare mai gafin ƙamshi yake yi, daya isa wajensu Yafendo dake akwai fitilar aci bal_bal na gango kwalli rambaɗe a fararen dara_daran idanunshi har zazzagowa yayi. Bayan ya gaisa dasu Yafendo yayi ma Baba bayanin yazo ya kaimu dandaline, sai ya fita waje ya bamu sarari dan mu kintsa. "Daso maza ku tashi ku shirya abun nema ai yau ya samu ko?" Dariya mu ka yi mata kawai. Ni dai mayafi kawai na ɗauka, saye nake da koɗaɗɗen riga da zane. Saɓanin Daso da sai da ta shafa kwalli harda janbakin majigi tasa ma labɓanta. Cikin zaulaya nace. Harda kwalliya ko za'a samo mana bazawari ko?" Dariya tayi kawai tace. "Kayya, ai tunda na rasa Chubaɗo ban sake tsaiwa da kowa ba. Ni abunma wani iri ba fasali yake yi mini" E dole zaki ji banbarakwai wai namiji da suna Hajara. Amman ya muka iya haka Allah ya zaɓar mana. Fatan shine Allah ya sadamu da mazajen da zasu ji tausayin rauninmu. Gara ma ke Daso mijinki rasuwa yayi fa. Ni fa Gwadabe yana doron duniyarnan rabamu akayi a bisa tursasawar mahaifiya da danginshi" Siraran hawayene ban aune ba suka biyo kan kuncina. Dafa kafaɗata Daso tayi jikinta a mace tace. "Mu yi haƙuri kawai mu rungumi ƙaddararmu. Allah yana sane damu, bai mance mu ba. Ta yiwu ya shirya mana kyakkyawar rayuwa a gaba. Ta yiwu kuma wahalar rayuwarmu ne zai fara. Amman duk abinda ya samu bawa ya fauwala shi ga Allah " Wannan gaskiya ne. Muna fatan kyakkyawar rayuwar a gaba. Allah ya sadamu da mazajen da dan so zasu ji kamar su mallaka mana numfashinsu dan mu daɗe mu yi ƙarko. Mu je mun bar Yaya Hamma a waje yana ta faman jira" Kafinma in rufe baki muka jiyo Yafendo tana kwaɗa kiran sunanmu tana yaren Fullanci. Ba shiri muka fito tare da ficewa a gidan. Ko da muka kama hanya, sai cin karo muke yi da mata da samari suna nufar dandali. Ina gefen hannun daman Yaya Hamma, Daso na gefen hagunshi mun sanya shi a tsakiya. Sai hira yake janmu dashi, Daso ce ke bashi amsar duk abinda ya tambaya. Ni tunanin Gwadabe da yarana, da kuma tunanin ta wacce hanya zanbi dan ganin na sanya Dada a farin ciki dariya da walwalarta ta dawo kawai nake. Wani shashe na zuchiyata sai kawai katsaham yace. "Me zai hana ki nemi Uwani in dai bata tafi ba, kema tayi miki hanya ki tafi. In kika tara kuɗi ne kawai zaki iya ɗauke mahaifiyarki ki rabata da azzalumin mijinta, ki kuma rabata da tallan Nono. Wannan shine hanya mafi sauƙi. Tunda ba kya kashe mata aure ba tare da kin shirya mata gidan da zata rayu da yaranta ba, kuma ba zaki hanata tallan nono ba har sai ke kin samu abun yi, ko kuɗi a hannunki da zaki ma rayuwarta hidima kamar yadda mahaifinki yayi mata kafin ya rasu" Nan take sai nake ganin kamar ma na samu mafitar cire Dada cikin ƙangin rashin ƴancin da take ciki. Dan a shirye nake ko matakin shari'a ne zan bi muddin yaƙi sauwaƙe mata igiyar ƙaddararran autenshi. Lokacin dana kwanta jinya take yawan sintirin zuwa dubani. Cubu ranar ta shigo da kuka take labarta ma Yafendo cewar Dada tana gida Baffansu ya daketa ya kumbura mata fuska, sabida sintirin zuwa dubani da take yi wai ya isheshi sai kace nice kaɗai ƴar data haifa. Lamarin da yasa ƙannena suka haɗe kansu suna kuka, tare da adda'ar Allah ya kawo ma Dada mafita ya cireta a wannan ƙangin. Daga ranar kullum ƙwaƙwalwata cikin tunanin sama ma Dada mafita nake, ko da kuwa zan rasa tawa mafitar. Sai yau Allah yayi na tuna abinda nake ganin zai iya kawo ƙarshen hawayen Dada. Tafiya Kano ya kamani gobe da izinin Allah, dan bahaushe gwanin iya tsara zance cikin hikima da azanci yakance da zafi zafi ake dukan ƙarfe, ko kuma yace da safe ake kamun fara" "Jabu tunanin me kikeyi haka mai zurfi har mun iso dandali baki sani ba? Na lura jefa ƙafafuwanki kawai kike yi" Cewar Daso wacce ta kafeni da idanu, Yaya Hamma shima ido ya zubamun, suna sauraren abinda bakina zai furta da sunan amsa. Iska na jawo daga huhuna na furzar kana nace. Tunanin rayuwa kawai nake yi Daso. Ai baka isa ka raba zuchiya da tunani, ko da ayyane_ayyane ba" Na ja bakina na tsuke. Na kura maa wutar karar dake ci bal_bal a tsakiyan dandalin ido, wajen yayi haske sosai ina iya hango kwalliyar mata da maza. Wutar nake kallo yanda take tartsatsi. Amman abinda zuchiyata take ciki yafi ƙarfin tartsatsin wutarnan, jin zafi nake yi daya wuce doka da oda. Hannuna Daso ta kama muka nemi wani benci da babu kowa muka zazzauna. Ƴan berorin ƴan mata sai wasannin gaɗa da waƙe_waƙen su na fulani suke yi. Samari sun kewayesu sai tafi da ɗaga sandunansu suke yi. "Kinga dandalinmu ko Jabu?, Allah yasa wasannin al'adunmu sun burgeki?" Cewar Yaya Hamma wanda yake zaune kusa dani. Murmushi kawai nayi mishi na sauke kayina ƙasa ina kallon yatsun ƙafata. "Jabu tunanin menene ya bujuro miki duk ya sauya kamanninki? Kinga lafiya abun tattalawace ga duk wani rayayye. Me zai hana ki tausaya mana ki dena wannan tunanin ko dan lafiyarki da farin cikin masu son ganinki cikin ƙoshin lafiya?" Kallonshi nayi na mai murmushi idanuna cike da ruwan hawaye. Shima murmushin ya bini dashi, kafin ince wani abun sai ga wani matashi ya ƙaraso gabanmu da sandarshi rataye bisa kafaɗunshi. "Hamma in babu damuwa inaso ka bani dama mu zanta da Daso. Na jima ina bibiyarta domin ta bani damar ko sauraren abunda ke tafe dani taji amman ta ƙi ya" Yaya Hamma ya dubi wannan matashin, ya dubi Daso wacce ta turɓune fuskarta kamar bata dariya. "To jeka zata zo yanzu. Kuma ni Hamma na baka damar zuwa zance wajen Daso Manga daga yau kuma yanzu. Daso tashi kije Manga zai yi magana dake" Nasan ganin rashin wasa gami da murtukewar fuskane yasa ta bishi ba dan ranta ya so hakan ba. Tafiyarta ke da wuya Yaya Hamma ya ce. "Bani labarin abinda yake damun zuchiyarki. Nayi miki alƙawarin magance miki matsalar duk girmanta" A'a Yaya Hamma babu komai. Ni dai inaso gobe zan je garin Kano. Amman nayi maka alƙawarin kwana biyu rak zanyi zan dawo." Da sauri ya kalleni har tsoron da yake son ɓoyewa ya kasa ɓoyuwa. "Kano kuma, ba dai wajen tsohon mijinki kike son zuwa ba, ko ganin yaranki ba? Kinsan yin hakan a wannan halin da kike ciku ka iya fama miki ciwon dake zuchiyarki" Da sauri na katseshi da cewa. Ko ɗaya ba abinda zai kaini Kano ba kenan. Akwai wani shiri da nake son in yi ne a can Kanon. In abun ya tabbata kaine mutum na biyu da zan faɗa ma bayan Daso" Ajjiyar zuchiya ya sauke yace. "Au ashe Daso ta fini matsayi a wajenki? Sai ta sani kafin ma in sani ko. Nagode" Yanda ya turɓune ƴar kyakkyawar fuskarshi sai ya bani dariya ainun. Ba haka nake nufi ba. Sabida ita ɗakunmu ɗaya da'itane. Amman kana da matsayi a wajena gaya. Ko tafiyar nan da zanyi gobe babu wanda na sanarma sai kai. Sai mun koma gida zan sanarma da Yafendo" Daɗi yaji sosai, sai kuma naga damuwa ta maye gurbin daɗin. "Allah yasa ba ƙauyenmu bane ya isheki kike son komawa maraya ba, sai da muka shaƙu dake kike son ki gudu ki barmu da kewa." Daso ce ta dawo ta zauna jagwab a gefena tana rishin kuka. "Ni Yaya Hamma bana son Manga. Bazan iya rayuwar aure da abokin Chubaɗo ba, gani zanyi kamar naci amanar Chubaɗo ne. Gashi kai kace ka bashi izinin zuwa zance, kuma kab garinnan waye baisan zafin kishin matar Manga ba. Ni ban shirya jefa rayuwata a cikin haɗari ba gaskiya " Dubanta yayi ranshi a bace, ko me ya tuna oho sai ya shiga aikin rarrashinta gami da yi mata nasiha. Mijintane dai ta rasashi har abada, ya zame mata dole yin sabon aure ko ba dan sha'awa ba ko dan tsira da mutunci. Ya ɗaura da cewa. "Kuma kinsan Baba ba zuba ido zaiyi ya barki kita zama a gabanshi babu aure ba ko. Lokacin da zai matsa miki da fito da miji nake jiye miki, dan in baki fitarba al'ada zata haɗaki aure da wani ɗan uwanki ko kina son hakan, ko bakya so. Ni abinda nake jiye miki kenan. Sannan Manga kab Rugar nan ansan mutumin kirki ne, gashi da yawan shanu, kuma jarumine sosai. Ko wacce bafulatana burinta auren jarumin namiji." Zaman dandalin dai haka muka ƙareshi babu armashi, Yaya Hamma ya mayar damu gida. Muna shiga a daren na sanar ma Yafendo inaso zanje Kano in Allah ya kaimu gobe, kwana biyu zanyi. Sai da ta ɗanyi jim kamar ba zata yarda ba, kamar tana son tambayata Allah ya soni bata tambayeni ba, sai cewa tayi dani. "Allah ya kaimu goben cikin rayayyu, sai ki shirya da wuri tafiyace mai nisan gaske" Da tunanin tafiyar na kwana a raina harma da mafarkin wai naje amman ban samu Uwani ba sai Hafizu mijinta. Washe gari tun asussuba nayi wanka. Ina yin sallah na fito da ƴar jakata ta hannu da kuɗaɗena a ciki. Kaya ko kala ɗaya ban ɗauka ba, nayi musu sallama akan zan biya wajen Dada da Boɗdo mu yi sallama. Daso ce ta fito domin yi mun rakiya. Muna fitowa muka ci karo da Yaya Hamma a zaune a bakin wata bishiyar darbejiya yana kallon ƙofar gida yaga yaushe zamu fito. Ba Daso ba ni kaina nayi mamakin ganinshi a wajen. Dan sai da nayi turus. Tasowa yayi ya nufo inda muke. "Yaya Hamma kaine da sassafe haka a ƙofar gida, zaman me kake yi a wajen?" In ji Daso kenan. Dariya yayi mata kawai kafin yace. "Tunda dai Allah ya ƙaddari ganawarmu ai shikenan. Babu gaisuwa sai tuhuma ko? Da fatan kun tashi lafiya" Muka amsa a tare, sannan mu ka gaisheshi cikin girmamawa. Gidansu Yaya hamma muka soma zuwa. A ɗakin Yafendo muka zauna, a gurguje mu ka gaisa na sanar mata inaso zanje birni amman kwana biyu zanyi. "To Allah ya dawo dake lafiya. Hamma sai ka kaita har tasha ka tabbatar motarsu ta tashi kafin ka dawo. Allah ya tsare. Hama da Boɗɗo suna garken shanu kuje ku samesu ko? Ke kuma Daso kizo in kin taso tallan Nono zamu yi magana muhimmiya dake" Kan Daso a sinne ta amsa da "To Yafendo" A garken shanu muka yi sallama da Hama da Boɗɗo. Sai adda'a su ke yi miki, daga nan sai wajen Dada. Ni da Daso ne muka shiga, Yaya Hamma fur yaƙi shiga yace Baffa faɗane dashi bai fiye son baƙi suna shigar mishi gidanshi ba. Mu ma muna shiga ya taremu harda sanda kamar zai dokemu. "Kai ku tsaya nan kar ku sake ko taku ɗaya a wajen" Ya faɗa da fillanci, Daso ce ta fassaramun abinda yace. Wannan kalma daya faɗa kamar ance Dada ta fito ta duba sai firit ta fito daga bukkarta. Su Cubu kuma da su Yusufu suna tsakar gidan, suna aikin dafa madara. Da sassarfa ta iso inda yake tsaye. Wallahi ɗaga sandar shi yayi kamar almara sai ya kwaɗa mata a goshinta jini ya yayi tsartuwa har a hijabina" Cikin hargagi yake yi mata magana da fillanci. Hannunta ta dafe da goshinta ta yi saurin juyawa, na fahimci umarni ya bata. Yusufu da Cubu ne suka yi kanta Cubu ta riketa zuwa ƙofar bukkarta. "Ku je Jabu. Zan dinga zuwa dubaki. Na mancene ban sanar miki ba ya kafa dokar kar ƙafarki ta tako mishi gidanshi" Da yarbanci tayi mun Magana. Ajjiyar zuchiya na sauke ina hango irin yadda sandar ta sauka a goshinta, ba tare da wani babban daliliba, ko da dalili addini ya bada umarnin a daki mace har a zubar mata da jinine? Ko da ma suna da ƙarancin ilimin addini, rayuwarsu a kiwo da tallar Nono take ƙarewa. Ji nayi na sake jin ƙarfin guiwar hukuncin dana yanke dan cire Dada a cikin wannan uƙubar. Hawayen daya zubomun nake shirin gogewa Baffa ya ɗaga sandarshi ya sauke mun a kafaɗata, zafin ya ratsa dukkan ƙasusuwan jikina kau,. Kafin in tantance tsakanin mamaki da tsoro naji Daso tayi ihu ta jani mun rufa waje a guje. A guje muka wuce Yaya Hamma. Sai biyo mu yayi da sauri yana tambayar ba'asin abinda ya haddasa gudun. Daso ce ta bashi labarin abinda muka tarar. Ni kam hawaye kawai nake sharewa ina kallon mayafina da jinin Dadana a jiki, sanadiyyar zuwa ganinta kawai aka zubar mata da jini. "Jabu kiyi haƙuri. Mu kanmu mun rasa yanda zamu yi mu tsamo Dada daga cikin halin da take ciki a wannan gidan. Amman abinda nake so dake shine dan Allah ki taya ta da adda'a, kuma zan baki shawarar kada ki sake zuwar mishi gidanshi, Dada zata zo har inda kike ta dubaki. Kar hakan yasa in kika tafi ki ƙi dawowa, hakan ka iya jefata a halin da yafi wanda take ciki yanzu. Zamanki tare damu zai iya kawo mata sauƙi sosai, kece babba ke zaki dinga rarrashin ƙannenki, kinga Boɗɗo kullum a cikin kuka da damuwar da Dada take ciki take." Ajjiyar zuchiya na sauke kawai nace. Babu komai, nagode da shawara. Daso ku koma daga nan ni zan tafi" "A'a ai kinji abinda Dadanmu tace dan haka har sai na tabbatar da fitar motarku a tasha. Daso ki koma gida ke" A wajen mu kai sallama da daso. Ni dai har muka gama wannan gwajab_gwajab ɗin fita zuwa gari hankalina baya ma tare dani. Wai duk haka Aure yake cike da ƙalubale kowa da irin nashi? Oh ya Allah ka kawo mafita a zamantakewar aure, ya Allah ka ba ma mata mafita. Har muka shiga cikin babbar tashar Adamawa babu wanda yace da wani ƙala a tsakanin ni da Yaya Hamma, dukkanmu sai tubka da warwara kawai muke yi, tare da karanta wasiƙar jaki. "Fullo Kano ne, ko Kaduna, ko Zaria ga motar Haɗejiya?" Cewar ma'aikatan tashar da suka nufo kanmu har suna rige_ rige. "Kano zata je, nawa ne kuɗin motar?" Cewar Yaya Hamma, tare da cusa hannu a aljihunshi. "Nera dubu da ɗari biyu zata biya" Kuɗin ya zaro ya kirga ya basu, ni kuma ya miƙo mun dubu da ɗari biyar. Ƙin karɓa nayi, ya dubeni rai a ɓace yace. "In baki karɓaba zaki barni cikin damuwa, da kokontan dawowarki rugar mu. Ni kuma dana tuna zaki iya ƙin dawowa, ko zaman rugarmu ya isheki take sai inji fargaba ta dirarmun. Jiya ɓarawon baccine ya ɗebeni shima cike da mafarkai akan tafiyar taki. Ungu kuɗinnan ko tsaraba kya yi musu" Nagode sosai Yaya Hamma, in sha Allah bazaan wuce kwana biyun ba. Kuma dan Allah ka je ka dubo Dada, ko a ɓoye ne ka kai mata magani, kai mata bayani kwana biyu zanyi" Yaya Hamma bai bar tasharnan ba har sai da ya ga fitar motarmu. Sai da motarmu ta yi nisa sosai na dena hango hannun Yaya Hamma a sama yana yi mun Adabo., ban dena waige ba har sai da na dena hango shudiyar rigarshi, Ajjiyar zuchiya na sauke na lumshe idanuna ina tunano yanda Baffa ya kabɗama Dada sanda. Wannan dalilin ne yasa kullum in zanga Dada sai in ganta cikin rashin guzari da rashin walwala, kullum cike take da tunani. Ta haɗu da azzalumin miji mai kafiya, tallar Nono ya cinye mata lafiyarta da kuzarinta. A shekarunta ya kamata ace tana zaune a nutse yaranta na hidinta mata, ba wai tai ta fita tallar nono, kuma mijinta na cin zarafinta harma da fitar mata da jini. Wallahi da Baffa zai iya amincewa in fanshi tallar Nonon Dada, da tuni na famsheta na zama ƴar tallar Nono kamar yadda ya zama al'adar matan fulani musamman mazauna rugage. Ya zame mun dole in yi duk abinda ya dace dan ganin na kawar ma da Dada Ƙwallar data daɗe tana zuba a idanunta. Gaga_gaga haka mukaita cin hanya, azahar, la'asar sai dab magriba muka shiga garin Kano, a unguwa uku muka sauka, ina fitowa titi na samu Bus har ƙofar layinsu Uwani. Na ko yi sa'a tana gida, tana tsakar gida tana kwasar tuwo Hafizu kuma yana shanya kayan yara a igiya. Tana ganina ta sau marar hannunta ta miƙe a zabure. "Iyabo kece haka afujajan?" Tana faɗin haka na fashe mata da kuka a tsakar gidan kamar ƙaramar yarinya. "Uwani jata kuje ciki maza" Cewar Hafizu. Hannuna Uwani ta ja muka shiga ciki, wallahi na fi minti talatin ina kuka take zazzaɓi mai azabar zafi ya rufeni. Uwani da Hafizu suka rufu a kaina suna ta rarrashina da ƙyar na haɗiye kukan nawa bakina na ambaton Allah. Ganin na ɗan samu nutsuwane Hafizu ya fita ya bamu waje. "Kawata lafiya kuwa kinga yanda ki kai baƙi kika rame kuwa? Gabaki ɗaya kin koma wata ƴar ƙauye, meke faruwa haka?" Cikin shessheƙa nace. Labarin da tsayi Uwani, amman bari in rama sallolina sai mu tattauna tunda abinda ya kawoni wajenki kenan" Ina gama faɗar hakan na miƙe jiri na kwasheni na fito tsakar gidansu dan kama ruwa da alwala. Uwani kuma taci gaba da aikin tuwonta, ina kan yin alwala yaran Uwani suka shigo gidan da sallamarsu. Matar gidan buɗar bakinta tace "Wannan wacce iriyar rashin tarbiyyace zaku shigoma mutane gida da gudu, kalan ku zubar mun da miyar da ko kayan ɗakin uwarku in an siyar bazai siya miyar ba?" Yaran su kai turus, ni dama nasan irin matsalolin da Uwani take fuskanta a gidannan shi yasa ban yi mamaki ba, gashi uwani ta kasance kamar zawayi wajen rashin haƙuri ai kuwa nan ta tanka. "Maman Shamsu kenan. Baƙin cikin ki takashinki zai koma da izinin Allah. Ni Uwani nafi ƙarfinki, kuma in mijinki yafi nawa mijin kuɗi, ai ni na fiki more aure tunda mijina bai taɓa zagin iyayena ba. Kuma bai taɓa korata da watan azumin ramadana ba, dan haka ki iya bakin ki" A mugun zafafe Uwani tayi maganar cike da hargowa. Yaran na kaɗa ciki dan gudun kar su kantamo kalmomin da suka shige shekarunsu. Da Uwani da maman Shamsu sun ci uwar sabada har sai da mazajensu suka dawo daga masallaci suka raba wannan ja'iba, dan wallahi na kasa riƙe Uwani sam, har zani Maman Shamsu ta fincike mata ya rage daga ita sai gwari na tsuma ( siket ɗin ciki). Ɗayar matar gidance ta ɗaukoma Uwani zanin ta ɗaura. Baban Shamsu cikin son bin goyen matarshi ba tare da bin ba'asin abinda ya faru ba yace. "A ɗayan biyu ya kamata ko ku ku bar gidannan, ko kuma mu tashi mu bar muku gidan. Wannan bala'in yayi yawa dan watarana wannan jarababbiyar karyar matar taka zata iya illatamun mata'" "Karya kace mata Ƙasimu? Uwani ba karya bace tunda bata leƙen mazan mutane in sun shiga bayan gida. Uwani Iyabo ku shige ciki kar ku tanka musu" Shigewa mu ka yi mu ka barma Hafizu faɗan. Matan gida sai ihu suke yi. Nifa harna rama sallolina ba'a dena gwabza habaice_habaice ba. Wannan ta jefa ma wannan, waccan ta rama, Uwani na tsaye a bakin ƙofa riƙe da labule sai ɓarin zance take ta faman yi. Yara kuma sai cin tuwonsu suke yi a yinwace." Uwani dan Allah ki rabu da Maman Shamsu ki shigo mu tattauna matsaloli" labulen ta saki muka shige uwar ɗakinta duk muka yada zango a kan katifa" Wai Uwani me matarnan take nufi dake ne haka?" "Sharri mana, baƙin ciki take yi mini. Jiya jiya fa na kamata tana barbaɗa mun garin magani a ƙofar ɗakina, kinga ɗauki babu daɗin da mu kaita yi kuwa? Mune har gidan mai unguwa fa. Amman kinga ta sake takaloni" Ajjiyar zuchiya na sauke . Labarin duk matsaloli na ba uwani, da ƙudirina da dalilin zuwana wajenta" "Lallai rayuwar mata cike take da ƙalubale mai tarin yawa. Wata matsalarta uwar miji irinki, wata matsalar ta ƙannen miji, wata jarabawarta maƙotane marasa ƙaunarta irina. Wasu dangin mij, wasu matan maƙota, wata ma abokin mijina, ko matar abokin mijinta sune matsalarta, banda kishiya da shegiya facala su ba'a lissafinsu ma. Na tausaya ma Dada aimun. Kuma ya kamata ku yaranta ku haɗe kai lallai ku nema mata takaddarta. Iyabo amman ramar da kika yi da sauyawarki ta ban tsoro" Hawayena na share. Uwani ƙauyene fa sosai can inda na koma. Babu ruwan famfo, sai wata rijiya guda ɗaya jol anan ake ɗiban ruwa, ba wutar lantarki, babu sabis ɗin waya, ba titi, amman suna da makaranta, sai dai al'ummar cikin ƙauyen aikinsu kenan kiyo, matansu kuma tallar Nono, suna da ƙarancin ilimin addini, ai dole ki ganni haka. Kuma jinya nayi magashiyyan sai an ɗaga sai an ƙwantar" Mun jima muna tattaunawa, sai da mu kai sallar isha mu ka ci abinci sannan Uwani ta zura mayafi muka nufi gidan Hajiya Salamatu. "To naji bayaninku. Amman Uwani kin mata bayanin komai da komai dai ko?" Cewar Hajiya Salamatu tana hakimce taci gwala_gwalai kunne da wuya, da tsintsiyar hannu. "E Hajiya na yi mata bayani. Sai dai itama bata da kuɗi kamar dai ni. Amman Hajiya in muka je can za'a cire a kuɗin aikinmu har mu gama biya. Mu ba ma daɗewa zamu yi a can ba shekara uku ya ishemu, dan da ita Iyabo shekara biyu ma tace" Hajiya tayi dariya tare da girgiza kai. MRS BUKHARI 3064127935 Buhari Ibrahim Ladan First bank Sanya nera 500 ɗinki kuɗin karatu anan. Wannan asusun gudauniyarmu kenan. Ki sani in kika siya wannan littafin tamkar kin taimaki iyayen marayune, dama su kansu marayun Kuzo mu yi tarayya cikin aikin lada. Ƙarƙashin Amila Foundati https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm NAMA YA DAHU ROMO ƊANYE GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 15 Kafin tace. "Ba dai shekara biyu ba, dan a ƙalla ba a ƙasaru ba, zaku iya kaiwa shekara guda kuna biyan kuɗin jirki da duk abinda aka kashe muku. Sai dai in babban gida kuka samu suke biyanku kuɗi da kyau, amman in ba haka ba shekararnan sai kun yita. Babu rufa_rufa sai kun gama biyan kuɗin jirgi zaku samu damar yin aikin hajji da umara baki ɗaya. Amman muddin kuka zama masu hazaƙa da kazar_kazar to gidan da za'a kaiku aiki zasu soku, kuma in dawowarku najeriya tayi, su hadoku da goma sha tara na arziki." A nan na fahimci Saudiyya zata turamu, sai naji hankalina ya ƙara kwantawa. Kafin mu baro gidannan mata da tsofaffi a ƙalla mutane fin ishirin sai da suka shigo, duk akan batun tafiyar. Ni dai mun tsayar da magana akan gobe da safe in zo mu je hajj kam aimun fasfo kafin in koma garinmu, nan da wata ɗaya da kwana goma jirginmu zai ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki. Muna tafe muna ɗan tattaunawa har bus ta saukemu a unguwar su Uwani. Muna sauka muka ci karo da mijin Uwani yana zaune a wata majalisar maza ƴan sa ido. Zumbur ya miƙe da ganinmu ya nufomu gadan_gadan. "Ke Uwani daga ina kike?" Ya faɗa a fusace. Tsaki uwani ta ja tace. "Aikin banza aikin wofi, ka dai ji kunya ka kuma yar da zuchiyarka kare ya cinye. Maza majiya ƙarfi masu zuchiya, ka gansu a titi suna aikin sufuri dan su rufa ma iyalinsu asiri. Banda kai Hafizu baka da aiki sai zaman majalisa, duk matar data wuce kuna ƙarema surarta kallo, ka barni da buga_buga mata a layi duk sun rainani" A faɗace take maganar tana yi tana kumfar baki. Shima zabura yayi ya ce. "Duk macen da take fita dai ba da sanin mijinta ba mala'ikun Allah har taje ta dawo suna tsine mata. Shashasha kawai." Tsaki ta buga fuu ta wuce ta barmu a tsaye. Hafizu ka ƙara haƙuri dan Allah. Dama har yanzu irin wannan zaman na rashin daraja kuke yi ma junanku? Ga yara sai sake girma da mallakar hankali suke. Ko dan su ya kamata ku sarara dan kune allon kwaikwayonsu, kai tunda kaine babba ka dena biye mata" "Shikenan Iyabo. Amman Uwani da kike gani bata da daɗi. Kwananta goma cib tana gaba dani, bansan sam abinda na aikata mata ba. Motsi kaɗan sai habaice_habaice" "Iyabo wai ki zo mu tafi kin kuma tsaya wani lallaɓashi" Ƙwafa tayi ta kawar da kanta. Har muka isa gida tana zazzago mun mita. A falo na kwanta ni da yaran, kafin gari ya waye kuwa suka jiƙani shakab da fitsari sai da nayo wanka kamar mai kwanan turaka dan har kaina sai da ya jiƙe da fitsari. Ai kuwa Uwani ta shiga jibgar yarannan kamar Allah ya aikota, haya_haya tsakaninta da Hafizu bai tsaya ba sai da ya gaji ya bar mata gidan tukunna. Ni na fitar musu da katifar na zuba ruwa katifar ta hau yarari tana gudana a tsakar gidan. Uwani kuma ta wanke musu kayan tas ta goge ledarta tsab da ruwan toka, gabaki ɗaya zarnin ya ɗauke. Dumamen tuwo tayi mana bai ma isaba saini na ba da hamsin aka siyi gasara da siga Uwani ta dama mana. Muna karyawa Hafizu ya leƙo "Ki kawo mun abincina ina tsakar gida" Yana faɗa ya saki labulen tare da jan dogon tsaki. Kai mishi abincin tayi ta dawo muka ƙarashe namu, a gurguje muka fita a gidan bayan ta sallami yara ƴan islamiyya. Ni ko Uwani kin je kin dubo su Toye kuwa?" Ɗan murmushi Uwani tayi tace. "Na yi tunanin Hamma ya goge miki tunanin Gwadabe ne ai Iyabo da baki tambayesu ba" Dariya nayi nace. Ko kusa meye tsakanina da Hamma da har zai ture matsayin uban ƴaƴana a zuchiyata? Shi fa Gwadabe Mijinane, shi ko Hamma ɗan uwanene kuma wa a gareni mai kulawa dani. Uwani kinsan Allah son Gwadabe nunkuwa yake yi a duk ranar duniya, bana jin zan iya sauraren wani da sunan aure a zahirin gaskiya" Ajjiyar zuchiya na sauke take ƙirjina su kai mun nauyi. "Naje kusan sau uku dubo ƴan biyu. Allah cikin ikonshi ban samu ganinsu ba, har shi Gwadaben. Sai da mu kai zageni in zageka da wanna figaggiyar matar wan Gwadabe Haula take ko Zuriya oho" Gabana ya yanke ya faɗi nace. Shikenan duk yanda akayi rayuwar yarannan ta koma ƙauye, ni da naso yaran su samu ilimin zamani tunda ni da Baban nasu iyakarmu kammala sakandare. Yarana sun zama ƴan ƙauye shikenan" Kuka na saka a hanya muna tafe kafin mu samu abun hawa. Da ƙyar da siɗin goshi Uwani ta shawo kaina. Amman fa har muka isa gidan Hajiya Salamatu bana cikin hayyacina, muna zuwa aka kwashemu a golf kusan mu tara zuwa hajj kam, anan muka amsa tambayoyi dai haka bamu jima ba duk yawanmu kuma akwai sanayya sosai tsakaninsu da ita Hajiyar. Muna bakin ƙofar Hajj kam ɗin a tsaye Uwani na kuma tausata wata mota fara sol tayi tsaye a gabanmu, ita bata wuce ba, gashi ta tare mana ganin gari" Wani dattijone baƙi mai haiba da kwarjini ya fito. Saye da yadin boyel mai ruwan ƙasa, kansa saye da hular zanna bukar, ga zobe ga agogo, ga takalminshi sau ciki irin na ƴan gayun maza. Abun almara sai muka ga ya tsaya a gabanmu. Gemu mai shi kombineshon ɗin fari da baƙi na kalla "Assalamu alaikum ƴan mata" Ya furta da muryar kamana muryarshi da kauri irinta tsayayyi dakakkun maza, sai buso ƙamshi yake yi" "Ba dai ƴan mata ba. Ko wacce da yaranta, kuma ai ko da wasa ba mui kama da ƴan mata ba" Cewar uwani balbalin kenan, ni ko fa bance komai ba. Wannan dattijo yayi murmushi har haƙorin makanshi fari ya bayyana. "Allah ya ba manyan mata haƙuri. Dan Allah kuna da aure ne?" Ya tambaya, sai naga fuskarshi ta cika da fargaba. "Ni dai ina da aure. Amman Iyabo a kasuwa take" Sai ya sauke ajjiyar zuchiya tare da murmusawa yace. "Alhamdulillah. To Hajiya in ko babu damuwa inaso mu ɗan yi magana a gurguje, dan gudun kar in katse muku hanzarinku" Carab uwani Tabalbalin tace "Babu komai bari in matsa in baku waje" Ai kuwa sai ta karasa wajen matan da muka zo tare dasu tayi tsaiwarta "Sunana Buhari Namoriki. Nazo shiga Hajj kam ne Allah yasa nai tsuntuwa dake. To a gurguje zanso jin sunanki da unguwarku sai in zo gida in sameki yafi mutunci" Ajjiyar zuchiya na sauke. Idanuna suka cika bam da ruwan hawaye, sai nake jin kamar tsaiwa da wani namiji da sunan soyayya tamfar cin Amanar Gwadabe ne" "Malama Iyabo baki ce komai ba" Na ji sunana raɗau a bakinshi. Sunana Iyabo kamar yadda ƙawata tace. Unguwarmu kuma ni ba ƴar garin bace ma, zuwa nayi gobe zan koma ina mai baka haƙuri" Murmushi yayi yace. "Ai mai son ɗan tsuntsu shi ke binshi da jifa. Kuma garin masoyi baya nisa, in kika bani dama ko adireshi zaki ganni" Ba ko wanne garin na masoyi bane baya nisa. Ka ganni ƴar ƙauye ce a jeji nake rayuwata, babu wutar lantarki balle har sabis ya isa mana, gashi ban shirya aure ba. Wallahi ko zan yi aure bazan auri ƙabilar da zata zama tana ƙin ƙabilar dana fito ba" na ƙarashe zancen cikin rishin kuka. Hajiya Salamatu na hango ta fito, a wajen na tafi na bar Buhari a tsaye. Har motarmu ta fice fit yana tsaye yana ƙarema motarmu kallo. Ko da muka isa gida Uwani Tabalbalin ta balbaleni da faɗa akan me zance ma Buhari haka? Ta tambayeni ne na bata labarin yanda mu ka yi. Uwani ai ni da Bahaushe sai dai zumunci. Amman bazan sake auren Bahaushe ba. Bama yanzu zan yi aure ba kin ganni nan. Mu da muke da tafiyar da zamu yi har tsawon shekaru uku, da dakon soyayya kike son inje inyi wanna shekaru? Dame zanji, da mutuwar aurena, ko da mayar mun da yara ƙauye, ko da matsalar Dada?" Da rishin kuka na masifa nake maganar. Uwani sai ita ta sakko, zama tayi ta dafani. "Kina da gaskiya ƙawata. Amman da ba irin rabuwar da kuka yi ba kenan. Rabuwa salamun_salamun yafi, domin bakasan inda rana zata faɗi ba. Batun yaranki da zan baki shawara ki ɗauka da kin sa ƙafa kin yi fatali da sha'anin, domin yafi ƙarfinki. Ba dole sai sun yi karatun boko darajarsu zata ɗagu ba, akwai arzikin da yafi noma ne? Babu shi da noma yaranki maza zasu iya azurta Iyabo, ita mace aure dama ka iya kaita jeji ma, ki bisu da adda'a zata bisu har gadon baccinsu Gwadabe kuma nasan ya cika jarumi, kuma yayi miki halacci. Amman cireshi a zuchiyarki wajibun ne saki ukune a tsakaninku. Ke ko saki ɗaya yayi miki yaci ki haƙura kema kiyi fatan samu sabuwar rayuwa a gaba. Kawo ɗari a siyo taliyar murji mu ɓararraka ina da maggi da ragowar manja. Kullum aikin kenan nike faɗi tashin neman abun rufin asirinmu, ke Iyabo har wanki da guga inayi a cikin gidannan, yawon wanke_wanke a gidajen masu hali ko shagunan cin abinci har ya zamemun jiki" Ɗari da hamsin na bata dan yara ma in suka dawo sa lasa. Ita da kanta ta fita ta siyo, tare mu kai hidimar komai muka baje a tsakar gida, Maman Shamsu tana zaune a kan turmi tana fige kasa tana waƙoƙin neman masifar da ta saba. A tukunyar muke ci, mun ɗebama yara nasu, Hafizu kuwa nayi roƙon duniya ta dibar mishi Uwani tace bai isa yana zaune a majalisa yana aikin bin matan mutane da ido ta ajjiye mishi abinci ba. "Amman iyaa Debisi da shi kanshi Debisin basu san kin shigo Kano ba?" Sai da na haɗiye taliyata na tsotse yatsuna daya jiƙe da romon da ya ji kafi zabo kafin nace. Babu wanda yasan na shigo. Gobe zan daka sammako in koma. Zanje inci gaba da jiran lokaci in Allah ya kaimu. Kuma inaso in tattauna sosai da Dada ta san ƙudurina, ta goyi bayana akan tafiyar da kuma batun Mahaifin su Baɗɗo. Zan soma zama dasu Boɗɗo tukunna mu tattauna in ji ra'ayinsu. Kuma naso in ɗan dinga ba matan Rugar ilimin addini iyakar abinda na sani, ko dan karatun sallarsu ta yi kyau. To basu ma da lokacin kayinsu ne shine matsalar. Amman su ƴan uwan nawa zan tsaya a kansu kafin in tafi in ɗan gyara rayuwar tasu" Washe gari asubar fari Uwani ta rakani tasha, ta ɗan tsintomun kayanta kala biyu da wanda na sauya a jikina uku kenan. Naso in mata turjiya amman taƙi sam dole haka na karɓa. A tashar na ɗan sai maganin ciwon kai, da maganin ciwon ciki, da maganin zazzaɓi , dana rage zugi ko wanne kati_kati. Inaso in bayar a kaima Dada ta ɗan dinga sha, sauran kuma in ajjiye a wajena. Taran safe motarmu ta ɗaga. Gwadabe:. Takai. Tun a ƙofar gida ya hango motar Yaya Hambali a gefe guda, kuma ya ga Nazifi na zance da Nana ƙanwar Layla. "To Gwadabe ni da Toye zamu wuce gida, in kun gama ganawa da Baba Magaji dasu Babala ka sameni a gida" Cewar Bara'u kenan. "To Shikenan sai nazo. Ka isar da saƙon godiyata ga Sakina" Yana faɗar haka ya shige cikin gidan. Da Nazifi da Nana babu wanda ya kalli Gwadabe balle su gaisheshi. Zumunci ya riga da ya taɓu, ana rikice_rikice a gaban yara suna ji suna gani, sai su taso da raini da rashin ganin girman wanda aka watsar a gaban idanunsu. Wanda ake mutuntawa kuma a gabansu, sai su taso da ganin girmanshi ainun. (Wannan kuskuren namu ne iyaye. Mu guji yin abinda bai dace ba a gaban yaranmu. Shi fa zumunci da haɗin kan haula babu abinda ya kai shi daɗi) Gwadabe yana tafe yana girgiza kai, ciwo yake ji a zuchiyarshi sosai ta yanda zumuncin gidansu ya lalace. A falon Babala ya tarar da kowa da kowa. Babala da nata tawagar haka ma ƙannenta su Goggo Iyatu Baba Magaji yana tsakiya. "Gwadabe kaine tafe da yamma haka?" Cewar Baba magaji. "Nine Baba Magaji. Mun same ku lafiya?" Gwadabe ya bi kowa da gaisuwa Babala da Goggo Iyatu fur su ka ƙi amsawa. Baba Magaji yace. "Zauna nan." Ya nuna mishi kusa da Yaya Hambali. Yana zama Yaya Hambali ya matsa, har yana share sangalalun hannunshi inda jikin Gwadabe ya gogeshi. Da mamaki Gwadabe ya dubeshi, shi kuwa ya zuba mishi Uwar harara. "Marar kunya ji yanda kake ƙare mishi kallo sai kace sa'anka" Cewar Yaya Halima da bata fiye son a zauna lafiya ba dama" Baba Magaji ya yi mata daƙuwa tare da cewa. "Ungo naki Yau ga mutuniyar banza. Shi Hambali baki ga share hannunshi yake yi in da jikin Gwadabe ya goga ba? Sai kace wani karfa. To magana dai ta ƙare kai Gwadabe meye hujjarka na nuna zafin ƙiyayyarka ga ƴar uwarka Laila? Dan naji labarin komai" Gwadabe ya ɗago kanshi yace. "Ba ƙin Laila nake yi ba, face ƙin munanan halayanta abun ƙi. Na farko Laila babu wanda bai san ɓarauniya bace. Ko yanzu a taronnan in ba'ai da gaske ba sai ta raba wani da abunshi. Sannan da aure a kanta bata dena bibiyata tana turo mun da saƙonnin ƙauna ba. Wannan manyan dalilan yasa bazan taɓa iya auren Laila ba" Kafin ya rufe baki Goggo Iyatu da Laila suka fashe da kuka wi_wi. Ganin haka yasa Babala soma shessheƙar kuka itama. Baba Magaji yayi tsam yana bin kowa da ido ɗaya bayan ɗaya yana karantar yanayinsu. Yaya Hambali cikin zafin ranshi yace. "Uwar ƴaƴan naka ma naga ɓarauniyace. Wacce iriyar sata ce bata tabka mana a cikin gidaba? Ai kai kasan komai tunda kai ke biyan kuɗin duk abinda ta sata. Ita ka zauna da'ita sai Laila jininka ce ba zaka iya aura ba?" Gwadabe yace. "Wallahi ko tsinke Iyabo bata taɓa sata ba. Duk wannan kitumurmurar Laila ne. Ita ke satowa ta jefa ma Iyabo a ɗaki. Ni kuma ina biya ne dan ba son ganin ana tashin hankali nake yi ba" "Babu shakka Gwadabe " "Duk ya isheku haka ku saurara mun. Iyatu ku yi mun shiru ya isa haka nan" Sai da ɗakin yayi shiru kana yace. " Duk wannan kumfar bakin da kuke yi ba daidai bane sam. Layla dai kowa yasan mai dogon hannuce, tunda har maraɗi wajena Iyatu ta kawota ai mata magani. A lokacin hekarunta baifi goma ba. Sata kuwa da ta dinga yi a ƙauyannan abun yayi muni. Ina bayan Gwadabe na ƙin amincewa da auren Laila. Tunda kunce satarta shafar aljanune sai ku dage ku nema mata magani. Kuma da ace ni nasan irin tsangwamar iyalin Gwadabe da kuka yi da tuni nayi ma tubkar hanci tuni. Ko yanzu ma dan saki ukune a tsakani da ko kun ƙi ko ku so sai ta dawo tunda itama musulmace ahalul kitabi ma aurensu akeyi ballantana ita musulma gaba da baya." Falon yayi shiru sai hawa da saukar numfarfashi kawai. Baba Magaji yace. "Yaran dasu ta tafi ne Gwadabe?" "A'a Baba Magaji bata tafi da su ba. Shi Toye yana hannun Bara'u Sakina zata ci gaba da kulawa dashi, za'a sa shi a makaranta. Su kuma ƴan biyun na kaisu wajen Tamu a can Abuja shi ya buƙaci hakan" Baba Magaji ya jijjiga kai yace. "To Allah ya saka musu da alheri. Faɗuwa tazo dede da zama ni zan tafi da Gwadabe maradi yaje ga su Auwala can suna aikin haƙar zinariya, yaje shima ya jaraba wata ƙila arzikinshi yana can. Akwai ƙannenka mata ma a cikin gida, in kuka daidaita da ɗaya daga cikinsu kaga sai ayi tuwona maina ku yi zamanku a can. In ma aikin haƙar zinariyar bai maka ba akwai aiyuka da zasu dace da kai" Ajjiyar zuchiya Gwadabe ya sauke kuma yaji daɗin hukuncin da Baba Magaji ya zartar, shi kanshi yana da buƙatar yin nesa da danginshi ya fita neman na kanshi. Kuma yaji aikin haƙar zinariyar ya kwanta mishi a rai. Ya je can maraɗi ya samu sababbin ƴan uwa da zasu so junansu. Babala ba haka taso taron ya watse ba, amman bata da ikon cewa komai. Haka tana ji tana gani washe gari Gwadabe da Baba Magaji suka wuce maraɗi a bisa jagorancin Bara'u zuwa tashar mota. Wannan shine dalilin barin Gwadabe Kano, ya koma maraɗi hannun wan mahaifin Babala" JIHAR MARAƊI DAKE CIKIN JUMHURIYAR NIJER Cikin unguwar Ali ɗan tsoho. GWADABE:. Bayan saukar su Baba Magaji a abun hawan da suka hau zuwa layin Ali ɗan tsoho. Duk inda Baba Magaji ya sauke kafarshi nan Gwadabe yake ajjiye tashi turyan_turyan har zuwa ƙofar gidan Baba Magaji mai ɗauke da cikowar almajirai yara da ƙananu. Almajiran malam suna hango malam magaji, wasu gardawa biyu suka taso suka nufo su. "Malam maraba da dawowa sannu da zuwa baƙo? Malam baƙin gaddi mu ka yi ne" Baba Magaji yayi Dariya ya dafa wanna gaddi yace. "Ba baƙin gaddi bane. Ɗan wajen ƙaunata ne cikin ummata. Amman da dare zai zauna ya dinga biɗar karatu, da kuma Asuba. A karɓi jakar hannunshi ku shige dasu wajen Fhatsima." Gwadabe ya bi bayan Gaddawannnan biyu har zuwa cikin gida. A tsakar gida suka tarar da matan malam Magaji su hudu reras ko wacce da abinda take yi. Haka yan matan gidan, wannan na sukola, wannan na girkin abincin siyarwa, wannan na dakan fura, duk dai gasunan. "Almu baƙi mu ka yi ne, cewar Baba Fhatsima. Wanda ta kira da suna almu yace. "Malam ne ya tawo da shi ya. Kuma yace mu kawo shi wajenki." Fhatsima ta yi murmushi tace. "Yaro shiga wannan ɗakin ka zauna. Ke I'ne zo ki kai ma baƙo ruwa ya sha" Gwadabe har ƙasa ya durƙusa ya gaishe da matan Kawun nashi. Babu dai yabo babu fallasa suka amsa mishi, cikin su ukun babu wacce ta yi mishi kallon arziki. Baba Fhatsima tace. "Tashi yaro kaji ka shiga daga ciki, za'a kawo maka ruwa" Jakar Baba Magaji ya amsa a hannun Almu da ɗan kunshin kayanshi kala biyu wanda Bara'u ya ƙunshe mishi. Ɗakin ya shige da sallama. Wata budurwa tana kwance a ƙaramin gadon bono ta juya bayanta ta yanda mai shigowa ba zai ga fuskarta ba. Kayinta babu ɗankwali sai baƙin madaiaicin gashi mai walƙiya da yai ma kan nata ado. Ba gashi bane mai yawan daya wuce misali ba. Gashi ne wanda bai ko kai tsakiyan bayanta ba, iyakarshi gaba da kafadunta kaɗan. Gashin dai ya sha gyara sai walwali yake yi. Gwadabe ya ɗauke idanunshi daga kallon gashin ya bi ɗakin da kallo, ɗakin ya sha labule mai ɗawisu zagaye da bangon ɗakin dukka. Ga ɗan katakon kwalliyar labule zagaye da ɗakin, a saman labulen an yi jeren kwanukan sulba ƙananu sai ɗaukar idanu suke yi. Ga gadon bono ga gado mai rumfa maulidi, ko wannne gado ya sha lallausan zanin gado mai geza da heart a tsakiya. Kasan ɗakin kafet ne ja mai kwalliya malale takota ina. A gefen gadon bonon an ajjiye babban tulun ruwa mai fenti, an rufe bakin tulun da faifayi. Ga wasu manyan kumbuna da kwallaye anyi ado dasu, banda wata kwaba mai ƙofofin tangaran ita kuma kwabar an ƙawatata da kwanuka da fileti na tangaran nau'i daban daban. Sallamar da Gwadabe ya ji ne yasa ya nutsu ya dena ƙarema ɗakin kallo. Wata farar doguwar yarinyace ta shigo, hannunta riƙe da kofin sulba mai murfi ƙato. A gabanshi ta dure kofin, ta zauna harda lanƙwashe kafarta kamar mai ɗaukar karatu. "Ga ruwa Yaya ka sha kafin abinci ya nuna sai ka ci" Murmushi Gwadabe yayi mata. "To nagode ƙanwata" Kofin silban ya buɗe ya kafa bakinshi a kofin ruwan ga sanyi, Gwadabe sai da ya sha fin rabin kofinnan kana ya ajjiye ya rufe kofin. "Gidanku Malam ya je, ko kaima almajirci kazo yi?" Ta jefo mishi tambayar, kafin ya bata amsa suka jiyo ana kiranta. "Ine ke dibo fito ku tafi ga musa mai baro yana jiranki" Zumbur ta miƙe ta dubi Gwadabe tace. "Zan fita tallen abinci, amman ba jimawa nake yi ba. In na dawo ma ƙarashe hirarmu" Da idanu Gwadabe ya bita kawai, ta fita cikin hanzari. Tana fita Baba Magaji ya shigo, Baba Fhatsima na biye dashi. A ƙasa Baba Magaji ya zauna, Baba Fhatsima kuma ta zauna a bakin gadon bono. "Fhatsima kin gane ɗana Gwadabe kuwa, ɗan wajen ƙaunata Babala, yaro mai yawan ƙuraje?" Baba Fhatsima tace. "Ohh naji naji, shine haka ya zama babban mutum haka? Oh Gwadabe rabona da saka ga idanuna shekara talatin baya, kana yaro kyatunarka na yawan kawo mana ziyara a lokacin kana goye a bambunta" Gwadabe sai murmushi kawai yake yi yana sinne kanshi ƙasa. Wata budurwace doguwa itama mai jiki ta shigo hannunta da kwanon abinci ta dire mishi a gabanshi. "Wannan Ƙaunarka ce Habi kenan. Ashirin ga wanga wata za'a ɗamra amrensu su bakwai cib. Habi wannan wankine Gwadabe." Gaisheshi Hari tayi da ladabi, ya amsa cike da fara'a, ta saka kai ta fita. "To Fhatsima ga Gwadabe na damƙa amanarshi gareki, ki zame mishi uwa tunda kece babba a cikin gidannan. Rigingimu ne na dangi su kai yawa shine na yanke hukuncin tawo dashi in gameshi da su Auwala suna tafiya haƙan zinariya. Sauran bayanin in kwananki ya zagayo zan zaunar dake mu tattauna. Labulen ɗakin aka ɗaga. Wata baƙar dattijuwa mai zanzana ce tsaye ɗayan hannunta riƙe da faranin silba shaƙe da kwanonin silba a kai. Ɗayan hannun kuma riƙe da labulen ɗakin. Dukkansu suka ɗago suna kallonta. "Abincin ɗakin Yaya zaka ci, ko in kai shi turaka?" Babu yabo babu fallasa tayi maganar. Sai da malam ya girgiza kai, Baba Fhatsima kuma tayi murmushi tace. "In banda abinki kema kinsan ai a turaka zaici. Me zai sa yaci abinci a ɗakina ke da ranarki" Guntun murmushi tayi tace. "To wa ya sani abu a dubu Yaya." "Ki kai mun turakata gani nan zuwa" Malam ya bata amsa da kaurin murya da halamun ɓacin rai tattare da shi. Tana sakin labulen ya miƙe ya fita. Baba Fhatsima tace. "Kaci abincin, sai a nuna maka shashen samarin gidan ko?" "To Baba Nagode " Gwadabe ya bata amsa a dalabce. MRS BUKHARI B4B GIDAN 3064127935 Buhari Ibrahim Ladan First bank Sanya nera 500 ɗinki kuɗin karatu anan. Wannan asusun gudauniyarmu kenan. Ki sani in kika siya wannan littafin tamkar kin taimaki iyayen marayune, dama su kansu marayun Kuzo mu yi tarayya cikin aikin lada. Ƙarƙashin Amila Foundation gidauniyar da muka buɗe ni da megidana domun iyayen marayu, ko tainakon marasa lafiya. Waɗanda suke cikin group dina mai suna (NAMA YA DAHU ROMO ƊANYE) 300 kacal zasu iya kuɗin karatu *Ƴar uwa ina fatan baki mance da kayan ƙamshin Mrs Bukhari gidan ƙamshi ba ko? Ƴar na gata ba take haye ba, Kanuri gidan ƙamshi. Matso kusa ƴar uwa ina da turarukan wuta nau'i daban_daban. Turaren kaya da zaki turare gidanki ƙamshi ya riƙe miki surura, sannan inada kabbasiyya turaren ruwane da ake fesama sutura a yayin da ake turara kaya a kabbasa, kana inada turaren wadrop da ake saƙawa a tsakankanin kaya. Turarukan wutana kuwa in kika turara gidanki yana sati guda yana ƙamshi. Inada turaren turara jiki gangariya wanda yake kama fata. Akwai kulaccam ta matan aure mai sirrin rikita maigida, ga gyaran fata. Akwai kuma kulaccam ta gashi, haɗe da turaren fesawa a gashi. Mai gayya mai aiki humrata ta matan Aure mai sirrin ƙara dankon soyayya, kiga oga na shinshinarki kamar mage taji ƙamshin kifi ɗanye. Inada humrori kala_kala. Ina da room freshener, da mopping mix mai sirrin ƙamshi. Kar in ta lissafo muku duk wani nau'in ƙamshin da kikeso in kika samu Mrs Bukhari ƴar mutan Maiduguri kin samu ƙamshi. ( Albishirinku akwai package na musamman dana tanadarma masoya wannan littafi nawa. Package ne mai ɗauke da abubuwa huɗu manya kuma a kan kuɗi ƙalilan karki bari garaɓasarnan ta wuceki zaki ciji yatsa kwasha_kwasha nayi da kayana domunku)* NAMA YA DAHU... ROMO ƊANYE GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI CE 16 Kwanon da aka ajjiye mishi ya jawo. Tuwon ɓula ya gani da miyar bushasshiyar karkashi. A tsanake ya soma ci, wannan tuwo ya bashi mamaki matuƙa dan a ido bashi da kyan gani, amman a baki akwai daɗi sosai. Zama ya gyara yaci gaba da kantara loma. Wannan budurwar dake kwance a gadon bono ce ta yi miƙa ta tashi zaune tana salati. Wankar tarwaɗace kyakkyawa ma'abociyar siririyar fuska da siririn hanci, laɓɓanta suna da ɗan girma kuma a ɗane suke, haƙorinta biyu manya na gaba a waje suke ko da bakinta a rufe yake. Masu irin wannan haƙorin ana ce musu masu haƙorin zomo. Leɓenta baƙine wukul duk da ya fahimci duk mata da yaran gidan bakinsu duk baƙaƙene kuma kamar wani abun suke yi dan leɓen ya zama haka. Bata da idanu manya ƙanana ne idanunta kamar an huda sakwara, ga gashin ido da yaima idanun rumfa, in ba zaro idanun tayi ba ma baka isa ka ga ƙwayar idanun ba." Ganin Gwadabe a zaune yasa ta rarami mayafi ta rufe jikinta ruf. "Kayi haƙuri bansan kana ciki ba" Ta yi magana muryarta na rawa. A gaggauce ta gaisheshi ta fita. Itama doguwace mai kauri yar duma_duma fatar jikinta luwai_luwai dashi gwanin ban sha'awa, ga mazaunai ɓaka_baƙa. Iyabo ce ta dawo mishi rai, da irin yanda in ta yi walliyar ɗinkin buba da zani take burgeshi, da yanda in ya kallli tudun mazaunanta ta bata yake ɗimaucewa. Ajjiyar zuchiya ya sauke a fili yace. "Ina miki fatan samun namiji lafiyye wanda zai kula dake, ki huta a gidan mijinki irin hutawar da kika rasa a gidana. Allah ka sa jin daɗi da nutsuwa a rayuwar Iyabo ta gaba. " Gabaki ɗaya abincin sai ya fice mishi a kanshi ma, rufe kwanon tuwon yayi ya sha ruwa. Yana zaune ƙwalam wannan basamudiyar budurwar ta sake shigowa dan doguwace ingarma. "Baba tace in ka gama in raka ka shashen samarin gidan ka je ka yi wanka ka huta" Ledar ɗan kayanshi kala biyu ya cacuma ya soke a hammata, baice mata komai ba ya biyo bayanta suka fito. Iyayen gidan basa tsakar gidan, sai tsirarin yara matasa masu wasa kawai. Tiryan_tiryan yana biye da'ita har zuwa wata ƙofa da suka shiga yaga ɗakuna kusan bakwai a jere, da ba haya mara ƙofa sai labulen buhu yana kallosu, sai durom biyu na ruwa, da ƴan butoci, da bokiti. Wani ɗaki ta tura ta shiga. "Bismillahi ka shigo" Bayanta yabi zuwa cikin ɗakin. Katifun yayi ne guda huɗu a jere, sai akwatunan ƙarfe suma guda huɗunne, ginine na jar laka, ba fulasta ba komai, ƙasan ɗakin ma ba daɓe ba komai, rairayin ƙasa ne takota ina sai ƴar tabarma da ke shimfiɗe, saman ɗakin kuma jinka ce, sai ƙwan lantarki guda ɗaya jol. "To bayan gida yana waje, akwai botiki, da ruwa zaka iya watsa ruwa. Lokacin sallah ma yayi sai ka sami malam a waje" "Nagode sosai, sai dai bansan sunanki ba har yanzu." Ya faɗa yana ƴar dariya. "Sunana Hadiza" "Ke yar Ine ce?" Ya tambayeta. "E yarta ce ni" Sallama tayi mishi ta fita. Shi kuma ya shiga kewaye yayi wanka tare da ɗauro alwala. Farin yadi ya saka, wanda ya cire kuma ya saka a botiki ya zuba ruwa, kafin ya fita waje wajen Malam. A ƙofar gidan Malam yai musu limanci. Bayan an idar da sallah almajirai sai suka soma karatu. "Gwadabe ga allo da tawada ka iya rubutu ko?" Sai da Gwadabe ya amshi allo da tawada da alƙalami yace. "E na iya Baba, a can Takai ma makarantar allon mu ka yi, sai dai karatun baiyi zurfi ba, banfi izifi huɗu ba" "Hakane na sani Gwadabe. To yanzu daga farkon izifi huɗun zamu soma. Yau ka bar rubutun kayi muraja'a yau da gobe, jibi kuma sai ka soma rubutun allo. Bana son wasa da karatu. Sannan ka zama jajirtacce sai Allah ya dafa maka. Na sani mahaifiyarka bata da daɗi, iyayenmu kansu sun sha yin kuka da'ita. In banda fitina ta Babala ina ita ina kafewa sai ɗanta ya auri ɓarauniya sabida Allah fa?" Ana cikin haka sai ga su Auwala, da Mammada. Baba Magaji ya gabatar musu da Gwadabe, sannan ya mikashi ga Auwala akan zuwa gobe zai soma fita tare dasu. Su Auwala suka karɓeshi hannu bibbiyu, kuma su kai maraba da shi. Baba Magaji yaranshi maza su rai goma sha ɗaya ne ras. Uku daga ciki sun yi aure, suna cikin gidan tare da iyalansu, tara kuma kowanne yana neman kudi, amman shida a ciki kowanne da budurwarshi da tsayayyar magana. Ukun yarane. Washe gari Gwadabe yabi zugar su Auwala zuwa can garin Ɗan Issa inda anan ya ga dandazon dubban al'umma masu haƙan zinariya. Tun daga nesa dai ya hango tudun laka kawai, sai da suka isa wajen ya ga dubban al'umma. Da rijiyoin haƙon zinariya sama da ɗari. Mammada ne ya ja hannun Gwadabe ya kaishi ga shugaba mai kula da ƴan ƙwadagon wajen ya sanar dashi malam ne yace a kawo shi ya dinga ganin aiki kafin a hankali kuma ya shiga ayari. To Alhamdulillah haka rayuwar Gwadabe taci gaba da tafiya, da safe su hau abun hawa zuwa ɗan Issa, da yamma su dawo gida, su ɗau karatu daga magriba zuwa taran dare, da asuba bayan sun yi sallah kuma zasu yi muraji'a kafin kuma su karya su tafi nema. Duk dabdala a ɗakin Baba Fhatsima Gwadabe yake yinta. Mace mai kawaici da son jama'a kenan. A cikin sati guda da Gwadabe yayi a gidan Baba Magaji, ya fahimci ana buga kishi sosai da sosai tsakanin matan Baba Magaji, yaran ma suna taɓawa dan ko wacce ta jaye yaranta, sun haɗe kawunansu isu_isu. Ko wani abune ya faru da ɗan wani ɗakin, sai aita rurrufewa sai dai in na alkhairi ne, ko dan fahari a fito tsakar gida a faɗeshi. Baba Suwaiba da Amaryar Malam sune suka fi gwabza kishi a tsakankaninsu, kasancewar sunfi Baba Fhatsima da Baba Asshi karancin shekaru, sune Baba Magaji ya aura a baya_baya. Dan Amaryar malam yarinyace da bata wuce shekarun Hadiza ba. Yaranta uku duk maza, sune ƙananu sosai a gidan. Fitinarta tafi ta kowa a cikin matan Baba Magaji, sabida tana ganin ai itace Amarya. Su kuma sauran matan kishinsu yafi tsananta akan Baba Fhatsima da yaran ɗakinta da suka kasance manya, masu jam ragamar komai a gidan. Yaya Tasi'u shine Babban yaron Baba Magaji, babban ɗan kasuwane da yake harkar riɗi da gero, kuma yana kiwon tsuntsaye masu darajar gaske, dangin su ɗawusu, da gigs, da Aku, da dai manyan tsuntsaye na ƙasashe da dama. Kasancewar shine Babba shike ciyar da iyalan gidan baki ɗaya, kuma shi ke yi ma yaran gidan Aure, da duk abinda uba yake yi ma ƴaƴanshi. To kasancewar Yaya Tasi'u ya fito a ɗakin Baba Fhatsima sai yaran ɗakin Baba Fhatsima suka zama yara daban a cikin gidan, yana basu kulawa ta musamman, Baba Fhatsima kullum a cikin shigar daraja take. Kuma matar Yaya Tasi'u mai Suna Badi'a tana yawan yin dabgen kaza ta ciko kwano ta kawo ma Baba Fhatsima. Ko Shi Yaya Tasi'un yasa ayo mata miyar kaji cikin tukunya, sai dai su dinga ci, dan ko abincin ɓarayin bata ci, daga can barayin Yaya Tasi'u ake kawo mata ishasshen lafiyayyen abinci. Ko da Sallah Yaya Tasi'u shi ke ma su malam da iyayen nashi mata layya. To ko akan ragon layyar duk shekara sai an samu yamutsi kan na Baba Fhatsima yafi na saurn matan gidan girma da ƙoshi. Haka dai ake wannan rayuwa a wannan gida. Ranar da Gwadabe ya cika sati guda bayan sun tashi daga karatun dare sai Malam ya zaunar dashi. "Gwadabe banyi maka batun mace bane dama nace bari in bari ka nitsa. To kaga akwai ƴan mata a gidana da yawa, duk da bakwai daga ciki am sa lokacin bikinsu. To shine nace ga Hadiza nan ina ganin kamar tafi sauran yaran hankali kasancewar bazawarace ita. Wata biyar kenan da mutuwar auren nata. A halin yanzu dai bata soma fita zance ba, in dai kana ganin tayi maka sai kayi ƙoƙari ku sasanta kanku. In kuma batayi ba, kar kaji nauyi ka faɗamun wacce tayi ma kai ko wacce tayi ma tana cikin waɗanda za'a aurar ne, zan iya baka ita, shi wancan yayi haƙuri. In kuma dukka basu yi maka ba to Shikenan sai in taya ka da adda'ar Allah ya kawo maka wacce zata zame maka alkhairi. Duk da dai mun soma maganar da Fhatsima, Tasi'u da kanshi sai yayi sha'awar maka Hadiza tunda dukkanku Zaurawane. Amman kaje kayi tunani. Gwadabe take zufa ta keto mishi, zuchiyarshi ta shiga harbawa da ƙarfi. Shi a halinnan da yake ciki na alhini da damuwar rashin Iyabo. Ina shi ina wata soyayya? Ta ina ma zai soma wata soyayya, baya jin akwai wata mace da zai iya bata zuchiyarshi harta samu gurbi. To taya zai kuɓutar da kanshi daga wannan tayi na Baba Magaji? Kuma ko yaya ya nuna baya son ko ɗaya daga cikin yaranshi tabbas bazai ji daɗi ba. Kuma shima nauyi da kunyar Baba Fhatsima zata iya hanashi zaman ƙasar. Gashi har ya soma sakewa, ya soma jin daɗin sabon wajen aikinshi, kuma Alhamdulillah shima harya soma shiga rijiyar tono, duk da yanda akaita tsoratashi, da irin yanda ake samun haɗarin ɗaruruwan mutane su rasa ransu ta dalilin rubtawar ƙasa, amman yasa a ranshi tunda anayi, shima zaiyi in sha Allah sai yayi kuɗi. Tunda yanzu zumuncin ma sai kana da hannu da shuni akeyi da kai. "Gwadabe kar ka damu, na baka sati ɗaya kaje ka yi tunani da kyau. Kuma ka kalli yaran da kyau ka zaɓi ka darje, in yaso shekara mai zuwa sai a haɗa auren naku dana su Mammada ayita ta ƙare. Akwai babban filina gashi can, a cikin filin almajiraina suke wanki, da duk wasu harkoki. To anan zaku zauna dukkanku, Tasi'u zai gina ma kowa ciki da falo_falo" Da haka Gwadabe ya tafi ya bar Baba Magaji akan zasu haɗu nan da sati mai zuwa yaji wacce ya zaɓa. Jikinshi a mace ya shiga cikin gidan. Ɗakin Baba Fhatsima kai tsaye ya shiga. Anan ya tarar da Auwala da Mammada suna zaune da abinci a gabansu, da dukkan halama shi suke jira su ci abinci, dan tun zuwansu suke cin abinci a tare. Hadiza, da Ine suma abincin suke cii daga can kusa da gadonsu na bono. "Yaya Gwadabe ya aikin?" Cewar Ine kenan. Sai da ya gaishe da Baba Fhatsima kana ya amsa Ine. Hadiza ta kalleshi da murmushi a fuskarta tace. "Yaya Gwadabe da safe naje nemanka ɓarayinku ban sameku ba yau kun fita da wuri ko?" "Sa hannu Malam muna ci kana amsa musu tambayoyinsu. In wanna yaranne sai mu kai sha ɗayan dare ba mu ci abinci ba" Dariya duka suka yi, dan Auwala baya wasa da harkar cin abinci. Baba Fhatsima tace. "Ato da gaskiyarshi ai. Maza kuci ku samu ku yi wanka sai ku kwanta. Allah dai ya sama nema albarka." Suna cin abincin ana hira baki ɗayansu a haka dai suka ƙare cin abincin. Sai ga Yaya Tasi'u ya shigo. "Kuna nan ba? Anzo a cinye ma Baba ɗan naman nata ba? Baba Yarannan ya kamata a matso da maganar aurensu, a samu suma su mallaki iyalansu, su dena zuwa suna cinye miki kayan daɗi" Ɗan darawa su ka yi, duk suka miƙe suka gaggaisa, Yaya Tasi'u yace. "Gwadabe ya ciwon jikin? Mammada ya faɗa mun ranar daka shiga rijiyar haƙon zinariya kasa bacci kayi, jikinka yaita ciwo?" Kai Gwadabe ya sosa yace. "Wallahu Yaya Tasi'u ai naji jiki sosai. Amman dai yanzu ina ɗan taɓa aikin, ciwon jikin yana ja baya" "E dama a hankali zai bi jikinka. Kama yi ƙoƙari ni naga jarumtarka sosai, dan wannan aikin bana malalata bane." Baba Fhatsima tace. "Ni kaina na ga juriyarshi sosai. Allah yayi muku albarka dukanku Allah ya baku abinda kuke nema duniya da lahira" Da "Ameen" Suka amsa dukkansu. Hadiza tace. "Yaya maganar kuɗin angon baka bamu ba, kar mu rasa ɗinkin" tsaki Yaya Tasi'u yayi yace. "Ana maganar kayan gado dasu katifa yayi kuɗi. Ku ta ango ma kuke yi ko? To kuje dai wajen Antynku Badi'a zata baku atampopin ta siya muku, dan ni ban bata ko sisi ba. Kunga ni an hutasheni, sai in yima Mamana" Nan suka yi mishi godiya. Baba Fhatsima tace "Ai Babannan ( haka Take kiranshi, kasancewarshi ɗan fari kuma mai sunan Mahaifinta) Babu abunda zamu ce da Badi'a sai dai muce Allah ya saka mata da Alkhairi. Tana yi mun abinda ko su Hadiza iyaka kenan. Yarinyace adala. Ina ma su Auwala fatan Allah yasa yaran da zasu auro mana su kasance masu hankali. Sai kaga zumunci ya sake ƙarfi sosai. Kuma naji daɗin yadda Malam ya yanke hukuncin ware su wadannan yaran a gida daban. Ƙila suma kansu su Sabitu su daure ayi zumuncin duka tare da matansu. Kuma kuyi ƙoƙarin haɗe kawunan yaranku waje guda, kar ku sake a raba muku kan yara. Ni bana jin daɗin irin yanda kowa yake jaye ɗanshi jikinshi kaɗai." Auwala yace. "Tabb ni kuma Baba gani nake yi wannan haɗemu da za'yi waje guda ba zai haifar da ɗa mai ido ba. Sabitu da baya ko iya gaishe da mutane cikin daɗin rai. In fa zai gaishemu kamar zai haɗiyi zuchiya haka yake yi, dan ƙaniyarshi dan yasan kashi zan bashi in baiyi gaisuwar bane. Ni wallahi bana son wannn haɗemun da za'ayi" Yaya Tasi'u yace. "Gaskiya ne za'a iya samun rikici sosai, musamman dag ɓangaren su matan da za'a auro bare. Mun tattauna da Malam sosai akan matalolin da ka iya faruwa. Mum kuma yi magana akan irin nasarorin da zasu iya faruwa. Dan a wannan karon Malam ya shirya ɓatawa da duk wanda ya nemi ƙetare umarnin abinda zai gindaya. I zuwa yanzu ya kamata ace an watsar da duk abinda ya shige, a fuskanci rayuwa. Malam bashi da wani buri daya wuce yaga kan iyakanshi a haɗe. To matsalar Baba Asshi itace zata fi kawo matsala acikin lamarin. Amman Baba shi fa malam so yake filin Ɗan Abhuja dake jikin filin da malam ya bayar a gina, ya siya a faɗaɗa harni da Usman, da Jamilu duk mu koma can, sai ya ware ku kuma daban, muma daban. Ni a matsayina na babba sai in kula dasu baki ɗaya" Cikin damuwa da tunanin rashin yiyuwar haɗin kai ga iyalan Malam Baba Fhatsima tace. "Tab aikin da Malam ya ɗebo babbane sosai. Kuma abun zai yi matuƙar wahala asamu abinda akeso. Sai dai zamui ta adda'a kamar yadda muka kwashe shekaru sama da hamsin muna yi. Malam ya matsantama kanshi da damuwa, da tunanin abinda zai dawo mishi da farin ciki da haɗin kan iyalinshi. Akan ɗan wani dalilin da bai kai an kirashi dalili ba duk wannan abun yaketa faruwa, har waɗanda aka auro a baya_baya suma suka shigo da nasu fitinar. Amman in sha Allah komai zai zo ƙarshe a kwana a tashi" Sun jima sosai anata tattaunawa sai kusan sha ɗaya su kai sallama da Baba Fhatsima, su Auwala suka nufi shashensu, Yaya Tasi'u ma ya nufi nashi ɓarayin. A daren wannan rana Gwadabe ya kasa runtsawa, duk da tarin gajiyar wahalar aikin daya kwaso. Kwakwalwarshi sai hasko mishi hotunan ƴan matan gidan kawai take yi. Da wannan tunani ya wayi safiya, suna kan shirin fita Hadiza ta kawo musu abincin karin kumallo. Kunu ne a jug, sai ɗunamen tuwon ɓula da lafiyayyar miyar kuɓewa ɗanya. Da idanu Gwadabe ya bita bayan ta gaishesu tana shirin ficewa. "Hadiza" Auwala ya kirayi sunanta hakan yasa ta dawo cikin ɗakin. Komanta da sanyi take yi, kuma yanayinta na nuna halamar kunya tsantsa. "Ga kayanmu kala bibbiyu ki wanke mana, Gwadabe bata kuɗin sabulu, ko kai ko Mammada" Gwadabe ne ya zaro sefa ya miƙa mata, tasa hannu ta amsa. Auwala kuma ya bata kayan nasu daya cusa a cikin wando ɗaya. Kafin su dawo Hadiza ta wanke musu kayannan tas, harma ta yi musu kwalima ta haɗa da zannuwan katifunsu du ta wanke. Dama su kan yi ma yayyen nasu hakan lokaci zuwa lokaci. Wanki dama suke yi musu kasancewar su basu da lokacin kansu. Yau samarin gidan a mugun gajiye suka shigo sharkab_sharkab da zufa, hakanne ma yasa basu shigarma Baba Fhatsima ɗaki a haka ba suka nufi shashensu. Anan suka tarar da sabitu yana kutuntumama Hadiza zagi tare da faɗin kalma marar daɗi a kanta. "Ƴar iska dama naji labarin ƙazamin kishine irinna gado yasa aka sakoki ai. Dama yaushe zaku iya zaman aure, yara an sangartaku, an ɗaure muku ƙugu, an ɗauraku akan bigiren kishi" Karab a kunnen su Gwadabe. Sabitu na ganinsu yazo da sauri zai wuce, Auwala yayi zafin naman riko hannunshi ya fincikoshi ya dawo gabanshi. "Ai ba ka zazzageta ka tafi a kyauta ba. Dan Allah sai munje gaban Malam yaji duk abinda ya haɗaku har ka zaɓi cin zarafin mahaifiyarmu da shi kanshi Malam ɗin. Kai dai Sabitu baka ƙaunar buɗe idanu ka ga muna rayuwa kyakkyawa. Wannan ciwon hassadar ne ya hanaka ci gaba sam, kuma gashi munfi ƙarfinka nesa ba kusa ba. Hadiza wuce muje gaban Malam. Da ƙarfin damtse Auwala ya figi Sabitu suka ratso tsakar gidan iyayen nasu, duk suna baje a tsakar gida suna shan iska. Baba Asshi taga Auwala riƙe cab da Sabitu, ba shiri ta cire hannunta a cikin abincin da take ci ta bi bayansu har da gudunta, daga ita sai fallen zani babu ko ɗan dires a jikinta. Baba Fhatsima ganin harda Hadiza aka fita yasa itama ta miƙe ta rufa musu baya." Anan na kawo ƙarshen free page. Wasa farin girki, labarin yana da tsawo ainun, dan ba mui komai ba. Sannan akwai tarin rikita_rikita da abubbuwa da dama na darasi, kar ki yi sake ayi wannan tafiyar babu ke. Akwai tarin abubbuwa da zasu biyo baya. Sannan akwai kyautuka da zan rabama masu yin dogon sharhi na musamman. Ki biya kuɗinki kisha karatu. Wasu suna roƙon in buɗe VIP To 1000 ne VIP ɗin normal group 500 ne. Nagode sosai da soyayya Nagode nice taku a kullum Mrs Bukhari. Mu haɗu a paid group dan jin yanda zata kasance. +22785548912 Ƴan Nijar ga number da zaku turama da kati nan nera 500 a kuɗinmu na najeriya. Nagode 3064127935 Buhari Ibrahim Ladan First bank Sanya nera 500 ɗinki kuɗin karatu anan. Wannan asusun gudauniyarmu kenan. Ki sani in kika siya wannan littafin tamkar kin taimaki iyayen marayune, dama su kansu marayun Kuzo mu yi tarayya cikin aikin lada. Ƙarƙashin Amila Foundation gidauniyar da muka buɗe ni da megidana domun iyayen marayu, ko tainakon marasa lafiya. Waɗanda suke cikin group dina mai suna (NAMA YA DAHU ROMO ƊANYE) 300 kacal zasu iya kuɗin karatu *Ƴar uwa ina fatan baki mance da kayan ƙamshin Mrs Bukhari gidan ƙamshi ba ko? Ƴar na gata ba take haye ba, Kanuri gidan ƙamshi. Matso kusa ƴar uwa ina da turarukan wuta nau'i daban_daban. Turaren kaya da zaki turare gidanki ƙamshi ya riƙe miki surura, sannan inada kabbasiyya turaren ruwane da ake fesama sutura a yayin da ake turara kaya a kabbasa, kana inada turaren wadrop da ake saƙawa a tsakankanin kaya. Turarukan wutana kuwa in kika turara gidanki yana sati guda yana ƙamshi. Inada turaren turara jiki gangariya wanda yake kama fata. Akwai kulaccam ta matan aure mai sirrin rikita maigida, ga gyaran fata. Akwai kuma kulaccam ta gashi, haɗe da turaren fesawa a gashi. Mai gayya mai aiki humrata ta matan Aure mai sirrin ƙara dankon soyayya, kiga oga na shinshinarki kamar mage taji ƙamshin kifi ɗanye. Inada humrori kala_kala. Ina da room freshener, da mopping mix mai sirrin ƙamshi. Kar in ta lissafo muku duk wani nau'in ƙamshin da kikeso in kika samu Mrs Bukhari ƴar mutan Maiduguri kin samu ƙamshi. ( Albishirinku akwai package na musamman dana tanadarma masoya wannan littafi nawa. Package ne mai ɗauke da abubuwa huɗu manya kuma a kan kuɗi ƙalilan karki bari garaɓasarnan ta wuceki zaki ciji yatsa kwasha_kwasha nayi da kayana domunku)* An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels