Showing 276001 words to 279000 words out of 306587 words

Chapter 93 - DAUDAR GORA 1 AND 2 COMPLETE HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

22068

ta farka a wani irin firgicen da yafi wanda ma Doctor ya ce zata iya tsintar kanta a ciki. Yanda jikinta ke rawa haka gadon ke rawa, ta fasa wata irin gigitacciyar kara ganin halittun da suka firgitata a cikin barcinta zahiri muraran a cikin dakin. Gaba daya sunma gadon zobe ga wani kalar kuka da sukeyi mara dadin saurare a cikin kunne., Sotake ta ambaci sunan ALLAH koda sau daya ne amma bakinta ya gagara furtawa, sai rawar da lips dinta keyi kamar yanda jikin nata ke rawa. Duk da sanyin ac dake dakin ita a jike take sharkaf da zufa kai kace wanka tayi.

"Hahahaha!!!!"

Uwa ta bayyana cikin mummunar dariyarta. Kamar koda yaushe a kan kujerar tata take cikin jajayen kayan nan. Mummunar fuskarta ta tsufa ta sake munancewa tsabar itama bata a cikin hayyacinta.Dariyar ta sake kyakyalewa da shi da fadin, "Kikace zaki ¡ya hahaha! Dama na fada miki ke karamar mara kunyace Bushirat, k! Karamar tsagerace!! Hahaha!!!!! Daga yanzu zuwa ranar cikar burina saina dandana miki azaba, kisa a ranki yanzune wasan zai fara na gaskiya. Kuma dole ne ki biya diyyar da jinin dan da mune mukai sanadin samuwarki garesa (Wa'iyazubillah🙏) da ga karshe zan tona miki asiri ta yanda jama'arki su zasu idasamin rayuwarki karamar yar iska kawai butulu. Hahahaha!!! Kuje gareta, ku sauyamun kamaninta". Ta fada cikin bada umarni ga munanan halittun nan ita kuma tana bacewa. Wata irin zabura sukai kanta, hakan yay dai-dai da bude kofar da Jasrah tayi a rikice, dan ta farka saboda kiran sallar asuba kawai ta dinga jin kamar dokuna na sukuwa a cikin masarautar, shine ta fito a zabure, amma maimakon jin da take duka masarautar ne sai taji kamar a dakin Malikat Bushirat din ne kawai, shine ta nufo nan a rikice. A take duk suka bace batare da taga komai ba, sai Malikat Bushirat da gaba daya ta gama fita a hayyacinta. Sallallami ta dauka tare da haurawa gadon a rikice, bata kawo komai a ranta ba face maganar doctor da yace dama zata iya farkawa a rude, ita kuma ta koma daki ne dan taji yace zata iya kaiwa ma safiyar gobe bata farkaba saboda nauyin allurar da yay mata.

Rikota tai ta rungume a jikinta hawaye na ciko mata idanu na tausayin yar uwar tata. Zuciyarta ta fara bata kodai asiri akai mata ne wai....





**..




Itama a gabanin asubar ta farka a razanen da ta saba a duk sanda tai mafarki mai nauyi irin haka. Ta dafe kanta dake sara mata tana mai karanto addu'a. Taja kusan minti biyar a haka kafin nutsuwa ta dan dawo jikinta. Hannunta ta janye da ga saman kanta tare da kai dubanta ga Tajwar Eshaan da ke getenta yana barcinsa hankali kwance. Fuskarsa ta tsurama ido kamar mai son karanto komai data gani a cikin mafarkinta kan fuskar. Ta jima batai mafarki mai sakata a rudani irin wannan ba. Itakam wadan nan abubuwa sun fara damunta, Shikenan da ga wannan sai wannan kullum babu hutu, da anyi maganin wannan sai was su sake ballowa wace irin rayuwace wannan. "Ya rabba ka kawo mana iyakar wadan nan
musibu". Ta fada a hankali tana sauke ajiyar zuciya. Yunkurawa tai zata sauka a gadon taji an rikota. Juyowa tai ta dubesa dan sam batai tunanin ya farka ba. Maidota yay ta hawo saman jikinsa, cikin yanayin muryar wanda ya tashi a barci ya kai hannu saman wuyanta da fadin,"Zazzabin ne?".

Kai ta girgiza masa a hankali. Cikin yar damuwar mafarkinta da bai gama sakinta ba ta ce, "A'a na farka ne kawai asubama yay". Ajiyar zuciya kawai ya dan sauke batare da ya sake cewa komai ba. Itama sai ta sake yunkurawa ta mike....




Tana idar da sallar asuba ta fito a dan harzance, dan so take taje ta dawo kafin ya dawo da ga massalaci. Sashen Malikat Bushirat ta nufa a yanayin badda kamar data fito. Kasancewar da dan sauran duhun asuba duk da ko'ina zagaye yake da haske babu wanda ya fahimci wanene a cikin tsirarun hadiman da suka fara ayyukansu. Koda ta shiga sashen ma tsirarune a hadiman suka fito fara shara. Cikin dabara ta dinga wucesu batare data yarda kowa ya ganta ba. Koda ta iso kofar dakin da zuciyarta yafi karkata da samunta sal data dan nutsu a kofar domin tabbatar da babu motsin komai sannan ta murda handle din a hankali ta shiga. A hankali ta sauke ajiyar zuciya tana bin dakin da kallo, babu kowa a ciki sai Malikat Bushirat din da ke zaune jingine da gado tana sallah a haka. Da alama bazata iya yi a tsaye ba. Key ta murzama kofar sannan ta karasa shigowa cikin dakin, dai-dai da ta idar. A dan yatsine Iffah ke mata kallon mamakin gain yanda tai wani irin zuru-zuru, duk rashin gane abubuwan mutum idan ya kalleta yasan akwai matsala a tattare da ita....

"Miya kawoki nan?".

Ta fada muryarta a shake sai dai cikin bacin rai. Baki Iffah ta labe itarna cikin tunzura ta bata amsa. "Kin san abinda ya kawo ni ai. Wai ke dan ALLAH bazaki dawo cikin hayyacinki ba. Inata nuna miki hanya, inata miki kanta farga amma kin kasa fahimta saboda son zuciya ya toshe tunaninki. Wai shin dole ne sai kin saka rayukan masoyanki cikin kunci da bakin ciki ne. Wlhy ki fadama bokanyarki ta fita a hanyata, danni nafi karfin ta da izinin UBANGIJI, hakama shi wanda kuke fadan a kansa yanzu duk da dank ne. Ta shiga hankalinta ta tsaya a iya kanki ke da kika gayyaceta a rayuwarki. Why duk randa ta sake gigin zuwa sashenmu sai kunyi nadama da ga ke har ita. Ni babu abinda ya shafeni da abinda zata miki matsalarkice wannan, tunda na nuna miki qujema irin wanna ranar tun kan tazo amma kika nun ban kai ba. Idan kuma ta cika cikakkiya dan ALLAH ta zo gareni a zahiri taga ikon ALLAH, wlhy sai na sauya mata kamannin halitta da tambarin da harta mutu bazai gogu a jikinta ba".

Tana gama fada ta juya tal tafiyarta fuuuu ta fice tana bugo kofar. Da kallo kawai Malikat Bushirat ta iya binta, zuciyarta na.raya mata anya kuwa (wannan yarinyar mutum ce? Koma dai wanda aka kira uban nata bashi bane Aljanun Ammarah din ne suka mata cikinta).…... Fitowar Jasrah da ga bayi ya katse mata zancen zucin. Sai kuma yanda Jasrahn ke mata kallon tuhuma da rudani ya sata shan jinin jikinta, ita sai yanzu ne ma hankalinta ya dawo jikinta. Duk da abinda yarinyar nan ta fada kenan Jasrahn ta jisu tunda tana a cikin bathroom...

"Akia!".

Jasrah ta katse mata tunanin. Dan firgigit tai ta dubeta. Sai dai ta kasa amsa mata. Babu alamar wasa tattare da Jasrahn ta sake fadin, "Akia kamarfa maganar Zawjata-almilk naji, shin wane maganganu take fada miki haka masu rudarwa? Mike faruwa ne?".

Dauke idanunta tai da ga kan Jasrahn zuciyarta na wani irin gudu a kirjinta......

"Hakan na nufin hasashena nakan gaskiya kenan,Akia akwai abinda kike boye mana tsakaninki da yarinyar nan? Taya kamarki da ke matsayin mahaifiyar mijinta, shugabanta amma tazo tana datsa miki irin mijinta, shugabanta amma tazo tana datsa miki irin wadan nan maganganun cikin kaushin harshe amma ko tari bakiyi ba. Anya kuwa Akia.....

"Jasrah!!"

Ta fada a zafafe cikin dakatar da ita, muryarta adan kausashe da bata fita. Shiru Jasrahn tayi sai dai ta kasa dauke idanunta da ga kanta. Babu abinda ke mata kai da kawo a zuciya sai kausasan kalaman Iffah masu nuni da akwai wata jikakkiya a kasa tsakaninsu. Sannan kalmar bokanyar nan ya matukar tsaya mata a kahon zuciya ya kasa fadawa...





**.




Koda ta koma ta iske ya dawo sai dai ya wuce Gym.Ajiyar zuciya ta dan sauke ta canja kayan jikinta ta nufi kitchen. Yau ma da kanta ta hada masa abincin breakfast din, suko masu girkin duk sun tsargu duk da tare da su take yi. Sai dai aikinsu kawai bani kaza yankamin kaza wanke mun kaza. Amma komai ita da kanta ta hada abunta. Ta kuma tsaya a kansu har sai da aka kawo komai dining room din.

Ya fito da ga wanka kenan ta shigo da sallama hanunta dauke da tray mai dauke da kofin shayi da keta faman turiri. Ido ya dan tsira mata har ta iso gabansa ta ajiye. "Good morning ". Ta fada tana zuba zuma kadan a shayin. Cikin dan lumshe ido da budewa ya amsa mata da "How Are you".

"Alhamdullah".

Ta amsa masa itama tana mika masa kofin shayin.Amsa yay dan dama shi yake jira. ya ce, "Thanks". Kai kawai ta dan jinjina masa tana murmushi. Da ga haka ta wuce bathroom dan yin wanka. Kallo ya bita da shi kasa-kasa zuciyarsa na masa kaikawo.



Lokacin da take fitowa har ya kammala shiryawa,dan haka ya taimaka mata itama ta shirya cike da tattali da kulawa. A tare suka fito cin abincin gwanin sha'awa. Duk abinda take kallonta kawai yake cike da so da kauna harta kammala hada musu komai. Bismillah ta masa tana masa nuni da abincin da ido ya make kafadarsa yana kauda kai gefe. Hannu ta kai ta dan ja masa kunne tana murmushi, sai hakan yay dai- dai da fitowar amintaccensa da basu san da shi ba da ga cikin karamin falonsa ya gyaro. Da wani masifar sauri ya juya har yana cin ban tuntube dan idonsa ras akan hanun Iffah da ta ja kunnen Shahan-shan din nasu. Itama idanu ta waro da sauri ta mike da sauri ta rungumesa. Dan harga ALLAH bata san bayan su akwai wani a wajen ba. Da kyar ya danne dariyar dake taso masa ya danna mata mintsini a gefen ciki shima, tako zabura gaba dayanta ta haye saman cinyarsa……✍️

DAUDAR GORA
Book2
80

……..• KOTU * Yau din ma kotun ta cika sosai,harma wanda basu halarta a jiya ba yau kam sunzo, Sai dai babu Malikat Bushirat. Dan tana can wani irin zazzabi mai masifar zafi da ciwon kai sun lullubeta har sai da Jasrah ta sake kiran likita ya dubata. Ta gama shirya ana gama zaman kotun nan gida zataje, dan ita kam har yanzu a cikin rudani take. Zataje ta sanar da babban yayansu da a yanzu shine kamar uba a wajensu komai tunda ita taki fada mata. Maybe su sai suzo su binciki wane irin TAKUN SAKA ne tsakaninta da surukar tata da har irin wadan nan maganganu ke shiga tsakaninsu. Yanke wannan hukuncin ya sata nufo kotun kamar yanda kowa ya hallara. Iffah tare da su Daneen Ammarah da su Ummu yau ta shigo. Dan suna kammala breakfast sashen Malikat Bushirat taje ta gaishesu kasancewar lyyani da Ummu a can suka kwana. Barrister Abdallah Aas da Abu Zainab kuwa tun a jiyan suka wuce gidajensu da iyalansu. Kaka ma kin kwana yay, sai suka wuce gida shi da Babiy da Hanash akan yau sa dawo. Ya kumayi hakane dan yana so suje su tattauna inda za'a nemawa Daneen Ammarah (Mammy) wajen zama itama. Saboda Tajwar Eshaan ya sanar musu ana yanke hukuncin nan zuwa jibi insha ALLAHU Mammyn (Daneen Ammarah) zata tare gidanta.

Shine karshen shigowa. A take kotun ta sake nustuwa kayin kowa a kasa har sai da ya kai zaune.Kamar ko yaushe Sayeed Hanifud-Din ya fito hannunsa rike da takardu. Bayan yay gaisuwar girmamawa da Shahan-shan aka fara gabatar da Shariar.

"Bayan jiya kotu ta gama sauraren bayani da ga bakin Arshaan wata shari'ar mai alaka da juna ta sake shigowa a cikin zaman. Inda muka saurari babban al'ararin da ya rikita kowa har sai da aka yanke wannan zama da alkawarin yau za'a kawo karshen komai. To Alhamdullah domin tabbatar da abinda muka ji a bakin Arshaan. Da wanda muka ji a bakin dattijon nan gamu yau rike da hujjoji. Hujja ta farko zamu saurari recording din da aka shirya saurara a tun farkon shari'ar ta jiya hakan bai faru ba. To a yanzu zamu ji domin sake tabbatarwa. Sannan zamu gabatar da hadiman da sukai aikin kisan gilla ga Sayeed Khairul-Bashar bisa sawar su Jasim, da kuma bokansu mai suna Barbushi dorin jin karin bayani da ga garesu. Hakama bayanan wanna dattijo duk da a jiya Daneen Ammarah ta tabbatar mana da abinda mukaji itama wanna kotu mai adalci ta saka anvi gwaje-gwaje da zasu sake tabbatar mana da komai.,
Shugaban jami'ai bismillah"

Bayan shugaban jami' ai yay gaisuwa ga Shahan- shan shima ya cika umarnin kotu na saka recording din da aka nada a zaman su Miran Jasim cikin kurkuku batare da sun sani ba. Kotu tai tsit kowa na sauraren kasancewar an saka speaker mai karfi a kowacce kusurwa kowa radam yake ji. Rikicin Miran Jasim da Miran Arshaan tun da ga ranar farkon kasancewar tare a cikin kurkuku daki-daki suna fallashe kansu da zagin juna da tsinema juna har zuwa jiya da safe. Tiryan-tiryan sai ga abinda Arshaan ya fada na fitowa harma da wanda bai fada ba. Jikin kowa da ke kotun duk sai ya kara sanyi. Yayinda aketa la'antarsu da ALLAH wadi da mummunar hallayar tasu duk da fa suma yan zaman kotun akwai masu wasu boyayyun al'amuran a cikinsu suma. Sai dai tunda tasu bata fitoba mai sauki ce. An fito da boka Barbushi shima da tunda aka kawosa masarautar aka rabashi da duk kayan tsafinsa aka aske masa kai da basa kaya bayan an sashi wanka. Gaba daya sai kamanin nasa suka canja kamar bashi ba. Sai faman sinne kai yake kuwa da satar kallon su Miran Jasim kamar yanda suma suke masa kallon mamaki. Shima yay gaisuwa ga Shahan-shan sannan Sayeed Hanifud-Din ya fara jefa masa tambayoyi.

"Kane mushirikin da ke basu tsubbun da zasu cutar
da mutane ko?".

"Ina neman afuwa kuskurene ranka ya dade".

"Tun yaushe kake tare da su?".

"Mun kai shekara goma sha takwas".

"Kace ka dade kana basu lakanin kashe mutane da
musu illa?"

Shiru ya kasa cewa komai,

Sayeed Hanifud-Din ya cigaba da fadin, "Kotu na bukatar jin duk tsiyatakun daka jagorancesu aikatawa".

Cikin rawar murya data baki ya shiga zayyane komai. Da ga karshe ya dora da fadin, "Naki fada musu gaskiya ne tun farko saboda karsu daina bani kudin da suke bani. Amma ni nasan anfi karfinsu a duk inda suke kai hari. Bakuma zasu samu cikar burinsu ba har abada".

Ba wanda suke a kotun ba hatta Miran Jasim da Miran Arshaan wan irin kallo suke masa mai ban mamaki, sai dai ko sau daya yaki yarda ya dubesu shikam, Bayan shi an fiddo hadiman da suka kashe Sayeed Khairul-Bashar. Inda suka zayyane komai har yanda Miran Jasim ya sakasu aikin, da yanda suka sacesa lokacin da yake fitowa da ga sashensa zaije sallar asuba. Sun azabtar da shi matuka, dan azabtarwarce ma ta kaisa ga rasa rayuwarsa. Sosai wasu ke kuka, iyalansa kam su kadai suka san irin zafin da sukeji a zukatansu. Babu abu mafi ciwo sai gain amintaccen hadiminsa a cikin wadanda suka halakashi.

Sayeed Hanifud-Din ya ja numfashi da fesarwa yana mai sake fuskantar kotu. "To Alhamdullah wanna kenan. Sai kuma gwajin kwayoyin halittar da wanna kotu ta bada akai mata tsakanin Zawjata-almilk da mahaifanta guda uku, inda gwajin ya tabbatar da Zayyan ibn Abbas da Ammarah bint Abdul-majeed Ally Qutb matsayin mahaifanta na gaskiya. Wadan nan sune gwaje-gwajen, gashi za'a jaranto.", tiryan-tiryan ya karanto komai, a take matasan nan da Iffah yanzu ta jawo jikinta suka cika kotun da kabbara. Da kyar aka tsawatar suka lafa.Miran Jasim kam sai kawai yaji ya fashe da kuka tsabar yanda zuciyarsa tai wani irin kunci da takurewa waje daya a kirjinsa,

Bayan shirun da kotun ta dauka kowa ya zuba ido da baza kunne na jiran yanke hukunci ga Shahan- shan da kuma makarrabansa da ke zaune yau a kusa da shi domin yanke hukuncin. Yaja tsahon mintuna hudu shiru kafin yaja numfashi mai sanyi, cike da nutsuwar nan tasa da kamewa ya motsa tausasan lips dinsa idanunsa kyam akan Iffah ta cikin bakin gilashin daya sakaya su. Tana kwance ne a jikin kafadar Malikat Haseenat idanunta a lumshe da alamar har yanzu batajin dadin. Janyewa yay a hankali ya maida ga takardun gabansa ya sake motsa lips dinsa.

"A bisa hujjoji da kwararan shaidu da ji da ga bakin masu laifin wannan kotu mai adalci tayi dubi da nauyin laifukansu da hukunce-hukuncensu masu nauyi daya dace ta musu. Domin saukaka wahalarwa ga kotun ta yankema Miran Jasim da Miran Arshaan hukunci ta hanyar rataya a tsakkiyar al'ummar wanna kasa a dunkule bisa laifukansu.....

A take kotun ta dauki kabbara cikin motsuwar zukata da tsananin rudani musamman ga Miran Jasim da Miran Arshaan da sukai wata irin zabura. Da kyar aka samu aka lafa ya cigaba da fadin. "Za'a yanke musu hukuncinne a ranar bikin al'ada dake hada kowa da kowa da za'a iya bukata da fatan su shaida Kafin hakan zasu cigaba da zama a cikin kurkuku, zakuma su bayyana dukkan laifukansu a gaban yan jarida. Bama bukatar wata kungiya a duniya wajen mana katsalandan akan hakan, zakuma su biya diyyar ran yarinyar Sayeed Hifzur-rahaman da ta Sayeed Khairul-Bashar ga iyalansa. Hakama zasu biya kudade masu nauyi ga ahalin Fhareedah bint Zayyan da suka wahalar bisa son zuciya. Bokansu an bashi damar zaman kurkuku na daurin rai da rai idan yana da rabon shiriya ALLAH ya shiryar da shi. Hakama hadiman da sukai musu ayyukansu an yanke musu hukuncin daurin rai da rai suma. Wannan kotu ta sallami wanda ya samar musu da dafin macizai abisa gargadin kiyayewa. Idan ya sake sakaci makamancin wanda yay zai yabama aya zakinta. Haifah za'ai mata hukuncin bulalar aikata Zina tare da zaman kurkuku na shekara goma bisa yunkurinta da hadin bakin son yin kisa. ALLAH yasa mufi karfin zukatanmu, ya yafe mana kurakuranmu mu da zuri'armu da al'ummar mu baki daya". Da ga haka ya mike. Babu wanda ya iya motsawa har sai da ya fice. Kotun tai wani irin harmutsewa kowa na ALLAH wadai da halayyar su Miran Jasim da kuna da tashin hankalin karshen su Miran Jasim da kuna da tashin hankalin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login