Showing 69001 words to 72000 words out of 80273 words
ubangiji yabar qauna tareda zumunci me ɗorewa, Sonso Fisabilillah❤*
_Page:45_
__________ A kwana a tashi babu wuya a gurin Allah yau tayi daidai da ranar da aka sallami
mamie daga Asbiti Sakamakon doguwar jinyar datayi, don haka gaba ɗaya Ahalin Na Alhaji
Mahmoud Muhammad suka kaure da Tarin farin ciki da samun lfiyar Mamien, sedai har yanzu
zukatansu a cike suke tab dason sanin maƙasudin shigar Mamien cikin wannan Mawuyacin
yanayin data shiga a lokacin datayi arba da surikin nata wato Maheer, sedai babu me ƙwarin
gwiwar daze iyayi mata wannan tambayar don gudun sake afkuwar wani abun na daban ga
lfiyar mamien.
Tunda Mamie ta fito daga Asbiti har xuwa yanzu addu'a kawai takeyi Allah yasa abinda idanunta
suka gane mata ba gaskiya bane Gizo ne kamar yanda idanunta sukeyi mata a kowace rana,
lallai dole ne tayi wani abu guda ɗaya ta haka ne kawai zata tabbatar da abinda take zargi akan
abinda idanunta suka gane mata ɗin a tareda Maheer, ajiyar zuciya ta sauke me nauyin gaske
wadda taja hankalin Abba zuwa gareta wanda ke kwance rungume da Ameerah wadda ke bacci
yace " Badi'atou!!
Ɗagowa tayi tareda maida kallonta ga Abban batareda tace dashi ƙala ba,
A nitse Abba ya fara magana cikda dattako yace "Badi'atou har zuwa wani lokaci zaki ɗauka
kina wahalar da zuciyarki gamida addabarta da dogon tunani ne?
"kin sani sanin kanki cewar a halin yanzu condition ɗinki ya tsananta fiyeda na kullum ko? Me
kika tanadarwa kanki a gaba da kike ƙoƙarin kashe kanki a banza duk a sanadin abinda kika
gina akan zargi?
Kallonsa kawai mamie keyi tunda ya fara magana batareda tace dashi ƙalaba seda ta tabbatar
da cewar ya gama faɗar abinda zece sannan tace " Alhaji duk yanda zan gaya maka cewar
nima ba'a son raina nake shiga wannan yanayin na yawan tunani mara amfani ba bazaka taɓa
yarda ba, amma ya kamata ka fahimci cewar nima ɗiyace ga wasu kuma wadda takeda burin
gyara alaƙarta da mahaifinta tun kafn mutuwa ta riskeni nasan zakayimin uziri fiyema da yanda
nake zato. Ta faɗa idanunta na zubar da hawaye
Daƙyar ta iya dakatar da kukan dake shirin kufce mata tacigaba da cewa "taya zan kwantar da
hankalina bayan na rabuda mahaifina tsahon shekara 20 batareda na sanyashi a idanuna ba?
Wllh wannan kaɗai ya isa ya zama ajalina ma ba iya rashin kwanciyar hankali ba!!!!!
Ta faɗa tana sakin kukan data daɗe batayi irinsa ba.
Sosai jikin Abba yayi masifar sanyi, inda kuma wani ɓangare na zuciyarsa yacika da tsantsar
tausayinta, janyota yayi zuwa jikinsa sannan ya shiga rarrashinta da tausasan kalamai masu
ratsa zuciya tareda yi mata alƙawarin cewar ze koma yola a karo na biyu kodan ya bin ciko
mahaifinta wata ƙila itama ta samu farin ciki kamar kowace ƴa a doron duniya, da wannan
zancen ya samu nasarar shawo kanta tabar kukan sabida Condition ɗinta.
A hankali Mamie ta zare jikinta daga na Abba sannan ta Miƙe a hankali Batareda tace dashi
ƙala ba ta buɗe ƙofar ɗakinta ta fita, a nitse take sakkowa daga kan step ɗin, kallo ɗaya zakayi
mata ka fahimci irin Ramar da tayi sakamakon ciwon data kwanta. Harta gama sakkowa
bataga kowa a perlorn ba se Khabeer dake ta faman dannar System, cikeda girmamawa ya
gaisheta tareda tambayarta ya ƙarfin jikin nata?
Murmushi Mamie tayi wanda ya baiyana ramar dake tattare da ita sannan tace "jiki
Alhamdulillah Babana daga haka bata sake cewa ƙala ba sabida sam yanzu bata iya jurar yin
doguwar magana dashi sabida illar da ɗiyarta tayi masa kansa taji kunya yayinda take magana
dashi ɗin, a nan perlourn ta barshi ta nufi ɗakin Umaisa wadda tundaga ranar da Abba yabada
Aurenta ga Maheer Lamiɗo ta ɗauke ƙafarta se A yau.
Zaune take bisa gefan gadonta sekace wata munafuka kunnenta ɗauke da wayarta suna hira
da Maheer Kamar haka
"ina fatan jikin Mamien yayi sauƙi sosai ko Queen?
Da uhmmm kawai ta amsa masa tamkar an mata dole, gaba ɗaya ji take hirar dukta gundireta,
tun daga lokacin da Mamien ta ta kwanta rashin lfy a sanadiyar Ganin maheer yasa ta canza
masa matsayi, bata jin hakan zesa ta tsaneshi sabida wani irin so take masa wanda batajin zata
iya misaltashi ga kowani mahaluki a duniya, tafi yarda da cewar a jininta son yake.
Katseta yi yace "Queen gobe nefa ranar dazamu kasance da juna a ƙarƙashin inuwa ɗaya, shin
bakya farin ciki da hakan ne?
Fashe masa tayi da kuka tace "uhmm ni bana farin ciki Sabida zaka rabani da Yaya Khabeer
ɗina, ni a halin yanxu dashi kaɗai nakeso na zauna, wllh banajin zan jure rashinsa a tareda ni!
Ta faɗa cikeda rashin ƙwarin gwiwa.
Cikin sigar Rarrashi Maheer yace "haba Queen kefa matana ce, khabeer kuma yayanki ne
nasan dole wata rana ze dinga zuwa yana ganinki, Kuma Aurena dake bawai yana nufin kawo
ƙarshen alaƙarki da ƴan uwanki ba Yazu dai don Allah kiyi shiru bana son Inajin kukanki.
Ƙara sautin kukanta tayi Sabida ganin gaba daya ma be fahimci inda zancenta ya dosa ba,
rarrashinta ya dingayi tareda gaya mata kalamai masu sanyi gamida tsayawa a rai sannan tayi
shiru, seda suka ɗan taɓa hira sannan yace " queen barina barki haka time ɗin tashin flight ɗin
mu yayi,
Addu'ar sauka lfy tayi masa sannan ta ajiye wayar wanda hakan yayi daidai da shigowar Mamie
ɗakin, tsayawa tayi tana kallonta kima nin mintuna biyu sannan ta shiga da sallama.
Miƙewa Umaisa tayi tsaye tana kallon mamin da mamki Kwance a kan kyakkyawar fuskarta,
sabida idan har zata iya tunawa daidai mamie tafi wata biyu batazo ɗakinta ba, murmushi
Mamie tayi lokaci guda kuma murmushin ya ɓace ɓat daga kan fuskarta, takawa tayi har xuwa
gaban dresing merior ɗin dake ɗakin tace " Ina Fatan ba wannan yaron da sukazo da mujaheed
bane zaɓin Ran naki?
Kasa magana Umaisa tayi sabida yanda tambayar mamien tazo mata a bazata, gabaɗaya
daburcewa tayi sabida rashin sanin takamaiman ta inada zata fara bata amsar tambayan nata.
"dake nake magana Fatimah!!
Jikinta ne ya qara masifar sanyi tunda taji Mamie ta faɗi Ainihin sunan ta, tabbas tasan yau a
kwai magana a bakin mamien don haka a sanyaye ta sunkuyar da kanta tace "shine Mamie,
Shiru mamien tayi kimanin wani ɗan lokaci sannan tace " masha Allah da kyau Fatimah Allah
ya sanya alkhairi, idan kunyi waya dashi inaso ki sanar dashi cewar ya gayawa iyayensa su fara
shirin karɓar baƙuncin ki a matsayin suruka a cikin satin nan.
Da wani irin sauri ta ɗago da fararen idanunta waƴanda ƙwallah ta cikasu tab tana kallon
mamien, sosai idanunta suka baiyana irin kaɗuwar da Umaisan tayi duk a sanadin furucin
mamie wadda ke tsaye tana kallonta, da sauri ta isa ga Mamie ta riƙe ƙafafunta tana me sakin
kukan daya taso mata tace " don girman Allah Mamie kiyi haƙuri kiyafemun laifin dana aikata a
gareki, wllh mamie kuskure da ƙuruciyane suka sa na saɓa miki harna Auri mutumin da Ba
shine zaɓin daya dace da ra'ayinki a kaina ba Mamie na!
Nasani na tabka kuskure me girma dana bijire miki amma ba laifina bane laifin ƙaddarar data
gifta a tsakani na da maheer ne...! Ta faɗa tana fashewa da wani irin kuka me taɓa rain duk
wanda ke sauraronta
jikin mamie ne ya ƙarasa sanyi a lokacin da kunnuwanta ke sauraron ɗiyar tata, don haka tasa
hannu ta ɗagota cikin wani irin yanayi me baiyana shaƙuwa irinta ɗa da mahaifi tace " it OK
dear wipe your tears maminki ta daɗe da yafe miki kukan ya isa haka nan, dukda irin kukan da
takeyi hakan be hanata sakin murmushin jin daɗin kalaman mahaifiyar tata ba, ko babu komai
yanzu ta rake kaso 80 a cikin damuwar dake damunta.
Washe gari da safe gaba ɗayansu Ahalin gidan na Alhaji Mahmoud muhammad suka hallara a
makeken daining table ɗinsu suka gabatar da breakfast ɗinsu ciki kuwa harda Baban gano
tamkar babu wani abou daya faru a cikin gidan.
Sosai Umaisa kejin kunyar Ummie da Abba duk a sanadin abinda ta aikatawa gudan jinin ɗansu
naƙin amincewa da Aurensa ta Auri wani can daban, a haka kowa ya watse ya koma ɗakinsa
akabar khabeer kaɗai da Umaisa wadda keta faman juya tean dake gabanta tana haɗawa da
satar kallonsa, kasancewar yau lahaɗin ƙarshen mako ce Babu aiki,
shan tean sa kawai yakeyi yanata faman ɗannar wayar dake hannunsa batareda yama lura da
wata aba me rai wai ita Umaisa ba, takaici Da baƙin cikine sukayi mata dirar mikiya a lokaci
guda, mata irin mayatacciyar soyayyar khabeer ce take cinta kamar zata zauta ta, miƙewa tayi
jikiba ƙwari zatabar gurin taji sautin Husky voice ɗin sa yace "wa kika barma wannan tean da
kika gama yima ƙazanta a nan ya shanye miki?
kukan datake dannewa ne ya samu nasaran ƙwace mata, miƙewa yayi cak hannunsa ɗauke da
mug ɗin tean dayake sha ya bar mata gurin sabida bayaso ta fahimci rauninsa a kanta.
Durƙushewa tayi a gurin tana aikin gursheƙen kukan da baze taɓa canza ƙaddarar da Allahɓya
aika mata a cikin rayuwarta ba.
********
*_ƁANGAREN MAHEER KUWA_*, basu suka sauka a Nigeria ba se wajen ƙarfe 3:00pm tun
kafin ya iso ƙasar Abdul ya kasa ya tsare a babban filin jirgin na Dr. Inamdi Azikwe dake babban
birnin na taraiya Abuja, a lokacin dayayi Arba da ɗan uwan nasa wanda ya maye masa gurbin
mahaifiya a gareshi ba ƙaramin daɗi yaji ba, cikeda farin ciki ya isa gareshi ya ƙanƙameshi yana
me baiyana farin cikinsa, shima a ɓangaren na Maheer Lamiɗon hakan take a haka suka
rankayo zuwa gida, tun kafin su shiga gidan mamaki ya baiyana a fuskar Maheer ƙarara sabida
duk inda ya kalla a cikin gidan seyaga an sanya wata alama tayi masa barka da dawowa ta
hanyar sanya wasu irin ƙayatattun fure masu launin Ja da Ruwan ɗorawa Sunyiwa wani
babban allo kawanya wanda akayi rubutu kamar haka a jiki *_"WLCOME HOME MY DARLING
SOM MAHEER LAMIDO!,_* Wani irin farin ciki ya samu zuciyarsa a ciki yayinda yayi arba da
wannan allo da kuma rubutun dake jikinsa, tabbas koba'a faɗa masa ba yasan aikin Dadynsu
ne sabida shi kaɗaine ze iyayi masa hakan, nan da nan kewar momynsu ta dawo masa sabuwa
a cikin zuciyarsa, wata irin ƙwallace ta cika Zagayayyiyar ƙwayar Idanunsa a lokacin daya
hangi Dady da sauran danginsu na Adamawa sun fito tarbarsa, Rabon dayaga an taru haka da
sunan tarbarsa tun sanda ya kammala karatunsa na scondry schl, a hkaa suka ƙarasa cikin
gidan kowa yana nuna farin cikinsa akan nasarar da Maheer ɗin ya samo, bayan lafawar komai
ne Maheer yaja Abdul Yace " Boy wai wannan taron duk na menene haka?
Kashe masa ido ɗaya Abdul yayi sannan ya kalli mutanan dake falon yace "ga wata tambaya
amma inji Maheer Lamido ba inji ni ba wai duk wannan taron daya gani na jama'ar yolo duk na
menene haka ?
Abdul ya faɗa yana Dariya tareda kallon maheer wanda yaji kamar ya nitse A gurin sabida
abinda qanin nasa ya Faɗa,
Da wani irin gudu Maheer ya nufi Abdul nan suka nufi ɗakin da Abdul ɗin ya nufa yana ihun
kiran Dady.
Dariya jama'ar falon sukayi zuciyar kowa a wanke tass suna masu shi'awar irin qaunar dake
tsakanin Brothers ɗin.
*******
Bayan kwana huɗu, kamar yanda mamie ta faɗa kuwa hakance ta kasance, don haka yau
mutanan gidan suka tashi da hidimar taron biki kamar yanda Abba ya Zartar akan ɗiyar tasa
Umaisa, tunda sanyin safiya Ummie tasata a mota itada Rumana da Aunty Maryam yayar
Beebah ƴar ƙanwar Ummie suka tafi gidan Hajiya ƴar borno don Ayi mata gyaran jiki, sosai
Umaisa ke zubawa Ummie darun ita bazatayi wani gyaran jikiba a ƙyaleta haka nan batason
komai, seda Ummie taci ƙaniyarta sannan aka samu ta nutsu ta shiga motar suka kama hanyar
gidan Hajiyar dake Gwarinpha 35 road opp fifth Avenue Abujah.
Sosai Hajiya Asma'u ta gyara Umaisa ciki da waje, cikim ƴan awanni Umaisa ta fito tayi wani irin
mugun kyau fiyeda ynda take se faman shaining take kamar walƙiya, cikin ƴan awannin da
bazasu gaza uku ba jikin Umaisa ya kama ƙamshi.
Bayan ta gama mata dilkan da kuma halawan ta shiga toilet ɗin dake ɗakin ta haɗa mata ruwan
wanka me ɗan ɗumi wanda aka ƙawatashi da wasu sunadarai na musamman a cikinsa masu
fitarda wani irin ni'imtaccen ƙamshi me zaburar da zuciyar duk wani wanda ya shaƙeshi. Tana
fitowa ta kalli Umaisa tace "Amarya tashi ki shiga kiyi wanka ki fito mu ƙarasa na gaba kuma,
turo baki Umaisa tayi tana ƙunƙuni ta shige toilet ɗin.
dariya Aunty maryam tayi sannan ta kalli Ruman tace "huh Kuna fama da rikicin ƴar gidan Abba,
ta faɗa tana dariya
Dariya Rumana tayi sannan tace ai mun kusa hutawa da rikicinta taje can tayiwa mijinta kuma.
_*KIYARDA DANI...!*_
*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى ASSɷ✍*
*DEDICATED: to Sis naja'art*
_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_
*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*
_Page:46_
NOTE EDITED♀️
___________ dariya sukayi gaba dayansu ciki kuwa harda Hajiya Asma'u ƴar Borno A haka
Umaisa tafito se faman tura baki takeyi, murmushi Aunty maryam tayi sannan tace "zo da sauri
ki shirya ƙanwata kar mutane su fara taruwa babu Amarya, ƙwallace ta ta cika idanunta
batareda tace dasu ƙalaba ta nufi gefan inda Aunty maryam ɗin ke zaune tace "Aunty ina kayan
to dazan saka?
Dariya Rumana tayi tareda tarar numfashin Aunty maryam tace " Ran Amarya ya daɗe Ai ga
kayan can akan kabbasa Ana turara miki shi da special turaren da aka tanada domin Amaren
da iyayensu ke matiƙar jidasu, ta faɗa tanayi mata dariya irinta tsokana.
Narai-Narai tayi da ido zata fara kuka da sauri Aunty Maryam tajata jikinta tareda gallawa
Rumana harara tace "Ruman banson iskanci fa kinji ko.
Haɗiye dariyarta Rumana tayi batareda ta sake cewa ƙala ba, a haka Hajiya Asma'u ta fito
hannunta ɗauke da wani ƙayataccen mai me masifar ƙamshi na musamman sannan ta miƙawa
Umaisa tace shiga ciki ki shafe duk ilahirin jikinki dashi amma banda privet part ɗinki, karɓa
tayi har lokacin bata dena tura baki ba ta nufi ɗakin da Hajiya Asma'un ta nuna mata, cikin
mintunan da bazasu gaza 3ba ta fito sanye da wata rantsattsiyar Doguwar riga baƙa wadda aka
ƙawata da rantsatsun Fararen stons masu masifar ɗaukar ido tamkar madubi, sosai rigar ta
baiyana kyawunta gamida hasken fatarta tamkar daga tsatson larabawa ta fito ba'a jinsin
baƙaƙen fata ba,
"Masha Allah! Shine kawai abinda Aunty maryam ke faɗa a ƙarƙashin zuciyarta, ƙarfe biyu
daidai sukabar gidan Hajiya Asma'u suka nufi inda za'a rangadawa Amarya kwalliyar kece
Raini, wata katafariyar plaza suka nufa dake Wuse 2 Abuja, wani ƙayataccen shago suka
wanda Akayi rubutu cikin wani irin salon na burgewa a samansa kamar haka *_SUSHMAH
GLAM,_* A nan na fahimci cewar shagon shararriyar makeup artist ɗinnan me matiƙar jida
kanta gamida iya kwalliyar kece raini sukaje, a hankali suka tura ƙofar glass ɗin ta buɗe wata
matashiyar mata suka gani a zaune da budurwar ɗiyarta wadda aka caɓawa uban ado se baza
kyau da sheƙi takeyi, seda suka matso dabdasu sannan Rumana ta washe baki tace "La Aunty
Rumaisa kece yau nake gani a gabana? Rumana ta faɗa with so much surprise at her face
Da mamaki su Umaisa suka kalli Rumana cikeda som sanin inda Rumana ɗin tasan ta, dariya
Rumana tayi sannan tace *_RUMAISA SALMAN CE fa jarumar cikin littafin Rumaisa Salman
mallakin Hauly (maman khausar)_* murmushi matar da aka kira da Rumaisa tayi wanda haka
ya ƙara baiyana kyanta tace " banyi mamakin jin sunana danayi a bakinki ba tunda nasan cewar
labarina ya bazu a duniya tayanda ni kaina ban taɓa tsammani ba balle zaton hakan. Ta faɗa
tana murmushi
Gaisawa sukayi dasu Aunty maryam sannan sukai sallama da juna RUMAISA SALMAN ta tafi
ta barsu da begen halaiyar ta ta kirki da kuma son jama'a.
Zama sukayi sannan Aunty maryam ta sanar da Sushmah irin kwalliyar datakeso ayiwa
Umaisan, murmushi kawai tayi sannan ta kalli maryam da fararen idanunta cikeda yarda dakai
tace "indai wannan ne bakida matsala my sister, zan fito muku da Amaryarku kamar yanda kuke
fata koma fiye da hakan.
cikin mintunan da bazasu gaza biyar ba aka sanyawa Umaisa wata rigar leda don gudun kar'a
ɓata a bayar ta shiga fesa mata kwalliya ta kece raini, cikin abinda baze gaza awa guda ba ta
gama mata wanda hakan yayi daidai da kammala kwalliyar da akewa Rumana itama, roling
Sushmah tayiwa Umaisa me wani irin filawas kamar toban a samansa wanda hakan ya ƙara fito
da kyan kwalliyar sosai.
baki Ruman ta saki tana kallon Umaisa a lokacin da aka fito da ita daga ɗakin kwalliyar bayan
an kammala mata, ƙuri tayi mata da ido tana kallon irin kyan da Umaisan tayi, tabbas tasan
Umy tanada kyau amma bata taɓa zaton kyanta ya zarta zatonta ba seda