Showing 18001 words to 21000 words out of 93605 words
text ɗin ki To ya kike so na miki, so kike naje na rufeta da duka ne, taya kike tunanin zansan dalilin da yasa take son raba tsakanin mu, kinga Sadiya nifa wannan ba damuwa ta bace, dan haka ya rage tsakanin ki da ƴar uwarki."
" Ya Garkuwa!!! Ba damuwar ka ba kace, ƙoƙarin raba mu fa ake amma kake kiran bai dameka ba, ko ka manta da soyayyar dake tsakanin mune, ko kuma dama yaudarata kake jikina kawai kake so, me kake nufi..................?"
*Ki biya Nairar ki 100 kacal ƴar uwa, sannan ki cigaba da karanta wannan labarin cike da nutsuwa, biya ta wannan hanyar*
*0006064512 Rashida Usman jaiz Bank ko mtn card ta wannan numbern 08147537180 sannan ku turo shaidar biya, karku manta Naira 100 ne kacal Araha tafi bashi🥰*
*UMMU NASMAH CE*
[4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺
*GELLE ƁINGEL*
🏺🏺🏺🏺
*Story*
*Rasheedat Usman*
*(Ummu Nasmah)*
*Littattafan marubuciya*
Sauyin Rayuwa
Nasmah Ko Nasirah
Sara Da Sassaqa
Indo A Birni
So Bai San Jini Ba
Akan ƴar uwata.
Hatsabibiya Saude
Ruɗanin Zuciya Biyu.
Doctor Hassan.
Ƙauyenmu.
And now *GELLE ƁINGEL*
*SADAUKARWA*
Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah.
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_________________________________*
*FREE PAGE*
➰➰ *19 to 20*
" Khalil har kana da zarrar ɗaurawa mahaifiyata bindiga a cikin gida na, Oh kai gaka jami'in soja bari ka taka kowa to kayi ƙarya wallahi zan iya rabuwa da kai akan Mamma, baka isa ka ci mata mutunci ba, muddun kana neman albarkata a rayuwarka dole kabi Mamma, wai ma na tambayeka wannan gidan naka ne ko nawa."?
Khalil kansa na ƙasa cike da ɓacin rai, dama ya sani zuwan Mamma cikin gidan nan babu alkairi tazo ne kawai ta tarwatsa musu farin cikin gida, girgizawa Daddy kai yayi alamun a'a.
" Okay shine kuma bari ka takurawa Uwata, to ta fika iko da gidan nan kai ko nima ta fini iko da wannan gidan bare kuma kai, wallahi khalil ka shiga hankalinka idan ba haka ba, zaka barmin gidana, kaje ka sunkuya ka bata haƙuri shasha, shima mai gadin zai haɗu dani ne, wannan ai rashin hankali ne, Kai Garko haura ka kira min uwarku naji idan tane ta ɗaure muku gindi ku ci mutuncin mahaifiyata."
Shi dai Garkuwa bai ce komai ba kasancewar sa mutum da bai shiga cikin hayaniya, aiken Daddy ya haura, shi kuwa khalil tamkar zai danna ihu tsabar takaici da haushin Mamma, bai cewa Daddy komai ba yaje gabanta ya tsugunna tare da cewa.
" Kiyi haƙuri Mamma Allah ya huci zuciyarki."
Taɓe baki Mamma tayi tare da kaiwa khalil ranƙwashi a kai tace.
" A yanzu dai na haƙura amma wallahi a kiyaye gaba a daina shiga gona ta idan ba haka ba, wallahi na fika iskanci, kai ga ɗan iska har wani zare min idanu kake kana nuna min bindiga, to wallahi duk wanda yaci tuwo dani miya yasha."
Cije bakinsa khalil yayi cike da jin haushin ta, ya miƙe tsaye ya bar gidan gaba ɗaya, Momy tare suka sauƙo da khalil ya nemi waje gefe ya zauna yana cigaba da danna wayarsa, Momy gefe da Daddy ta zauna tace.
" Sannu da dawowa Alhaji."
" Bana buƙatar sannun ki ki riƙe kayanki, yanzu ke Zainab kece zaki wulaƙanta min mahaifiyata, ki watsar da ita a falo ki shige kiyi tafiyar ki, saboda baki san daraja da girman uwa ba, idan ke baki tashi a gaban mahaifiyarki ba, shiyasa baki san girman ta ba, to ni na tashi a gaban tawa kuma nasan daraja da kimarta, muddun za ki cigaba da nuna rashin kulawa akan Mamma zamu samu babbar matsala dake, ba fuska zaki haɗa ba ko mutuwa zakiyi Mamma ta dawo cikin gidan nan kenan da zama idan hakan bai miki ba, kina iya tafiya, amma dai ki sani bazan yadda da cin mutuncin mahaifiyata ba."
Momy shuru tayi tana sauraron Daddy, harya gama cikin sanyin murya tace.
" Cin mutunci kuma Alhaji ta yaya zanci mutuncin Mamma, nima fa.........."
Dakatar da Momy Daddy yayi ta hanyar ɗaga mata hanu yace.
" Excuse me Malama, ƙarya Mamman zata miki, baki da bakin kare kanki a wajena, ki tashi ki tafi ki bamu waje."
Bata kuma cewa komai ba Momy ta miƙe tare da furta.
" Allah ya baku haƙuri."
Tayi Maganar tana barin wajen, Daddy Sosai ya dinga bawa Mamma haƙuri har ya samu ta sauƙo da kansa ya nuna mata bedroom ɗin da zata zauna, a ƙasan, sannan ya haura nasa bedroom ɗin domin ya watsa ruwa, A'illo ma haurawa tayi bedroom dinsu ita da Zarah ya rage daga Jummo sai Garkuwa a falon da hankalinsa ke kan wayarsa, Jummo tashi tayi daga inda take zaune ta dawo kusa da Garko ta zauna, muryar ta yaji ta daki kunnen sa.
" Ya Garkuwa na, shine bazaka ce nayi kyau ba, kai fa na yiwa kwalliyar nan."
Shuru ya mata tamkar bai jita ba, ƙara ce masa tayi.
" Ya Garkuwa ka kalleni fa wallahi nayi kyau."
Cike da tsawa Garkuwa ya ɗago kansa yana daka mata tsawa cikin sauti mai amo sanda Jummo ta razana.
" Ke dalla!!! Mahaukaciya jaka!!! Ni ina ruwana da kwalliyar ki, kin bi kin cika min kunne da zancen banza zancen hauka ke a hakan gani kike kinyi kyau, da kinsan yanda wannan kwalliyar ta mayar dake kamar jaka da baki zo kince min kinyi kyau ba, dubeki dalla wata mummuna dake ko tsari baki dashi tashi a gabana kona hanɓareki!!!"
Jikin Jummo sanyi yayi tayi shuru tana duban jikinta wai batayi kyau ba, wai kuma jaka, hawaye ne ya zubo mata, ta tashi da gudu ta haura sama tana kuka, runtse idanunsa Garkuwa yayi harga Allah idan yace batayi kyau ba, ya faɗa ne kawai saboda son ranshi, domin kuwa sosai ta masa kyau, sanin rashin mutuncin Jummo da rainin ta yasa yace mata batayi kyau ba, domin shi mutum ne wanda baya son raini, haka kawai yaji zuciyarsa bataji daɗin abunda ya mata ba, ji yayi zaman falon ma ya isheshi tashi yayi ya fice compaunt ɗin gidan.
Bedroom ɗin Aunty Zarah ta faɗa tana kuka, Aunty Zarah zaro idanunta tayi tare da cewa.
" Subahanallah Jummo lafiya."
Cikin kuka tace.
"Aunty wai banyi kyau ba, wai kamar jaka na koma, wai mummuna ce ni?"
Murmushi Aunty Zarah tayi tana girgiza kanta tace.
" Ikon Allah waye yace miki haka.?"
" Aunty Ya Garkuwa ne.?"
" Garkuwa kuma!! Hmmm ya faɗa miki son ranshi ne kawai amma shima yasan kinyi kyau, wama ya isa ya kiraki mummuna, ai a cikin kyawawan ma ke ta daban ce, rabu dashi zolayarki yake dan kawai ya saki kuka."
Sai yanzu Jummo tayi dariya tace.
" Allah Aunty zolayata yake, da har naji haushi."
" Ki daina jin haushi haka shi yake ya fiye tsokana."
Dariya kawai Jummo tayi tace.
" Aunty bari na tayaki aikin."
Tare suka ci-gaba da gyaran bedroom ɗin da Jummo, kafin suka koma kitchen.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*Bayan sati biyu*
Sosai zaman gidan yake yiwa Jummo daɗi domin kuwa Aunty Zarah ta zamo mata tamkar ƙawa komai tana mata, haka komai tare suke yi, har ya zamanto Jummo ta fara iya girki da kanta, wannan yalon hakwaran nata duk ya goge, kwalliya kuwa sosai take yinsa Aunty Zarah da kanta ta saya mata sutura, yayin da zaman su da A'illo suke zaman doya da manja babu mai shiga sabgar wani, Mamma ma Sosai take jin daɗin zaman gidan Aunty Zarah na kula da ita yanda ya dace tamkar ƴar da ta haifa a cikin ta, Momy kuwa tana takure da zaman Mamma domin kuwa bata isa tayi koda motsi bane sai Mamma ta saka mata ido kullum cikin mita take yiwa Momy, hakanne yasa ta fara neman hanyar da zata kori Mamma daga cikin gidan cikin sauƙi ta tafi da kanta ba tare da Daddy ya zargeta ba, ta kira ƙawarta Asabe suka shawara, yayin da suka shirya zuwa wajen boka domin ya kora musu Mamma daga cikin gidan koda Momy zata samu sauƙi a cikin gidan, Zarah sosai taji daɗin zuwan su Mamma domin kuwa a cikin kashi ɗari na wahalar da Momy take bata babu kashi hamsin duk Mamma ta tare mata shi, shi kuwa khalil baima shiga sabgar Mamma iyakarsa da ita ya gaishe ta, da safe sai kuma idan yaga dama ya zauna da ita suyi hira sa'i da lokaci amma duk abinda zatayi ido yake zuba mata, haka take shiga cikin bedroom ɗin ta tasha tabarta ta ƙoshi babu wanda ya isa ya hanata, ganin da khalil yayi Mamma na son Jummo Sosai kuma tana jin maganarta, hakan ya sashi ya ƙudiri niyyar jawo Jummo jikinsa yayi amfani da ita wajen haramtawa Mamma shan sigari.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
" Wallahi wallahi na rantse da Allah Zee wallahi billahil'azim nice ƙalubalen Garkuwa a Wannan Duniyar wallahi muddun ina numfashi bazan taɓa barin wata mace ta kusance sa ba, sai yayi danasanin ɓatamin rayuwata, yau na dawo daga Egypt kuma a yau zan fara bibiyar rayuwarsa, da wannan yaron daya batawa suna yasa muka samesa ta hanyar banza, dashi zanyi amfani wajen ganin ƙarshen Garkuwa Zee koda komai na zai ƙare nayi yawo tsirara na rasa farcen susa muddun zanga bayan Garkuwa wallahi sai nabi Wannan Hanyar, a yanzu gani yake farmaƙin daya saka aka kawo mana duka mun mutu nida iyayena, na tsani Garkuwa duk sanda na tuno shine yayi sanadiyar mutuwar iyayena sai naji tamkar naje na kashe nasa ahalin Bayan ya rabani da mutunci na ya min ciki hakan bai isheshi ba sanda ya kawo ƙarshen iyayena Abbana Ummina Brother Saleem Aunty ummu lil Saleem duk ya saka an kashe su, da badan mahaifinki ba, da nima yanzu babu labarina, ni da abinda yake cikina wannan gidan yaron ne baya son na Haifa, kuma gashi yazo duniya dashi zan tozarta GARKUWA."
Numfashi Zee taja tana kallon *SAFREENA* da ke rungume da wani ƙaramin Yaro yana bacci hankalinsa kwance, tausayinta ya kama Zee TABBAS SAFREENA taga ƙalubalen Rayuwa, Soyayya ta zamo mata mungun dafi ta ajiye mata munguwar tarihi, da ana tariyo Rayuwar baya da yanzu SAFREENA cikakkiyar mai gata da iko ne lallai ne Maganar Hausawa *mutum mungun icce ne*
🤔🤔 Wacece SAFREENA menene alaƙar ta da Garkuwa waye mahaifinta duk zaku samu wannan cikakkiyar amsar sanƙame cikin wannan littafin mai matuƙar sarƙaƙiya da cakwakiyar soyayyah ku dai ku biyoni ta hanyar.
*Ki biya kuɗin ki Naira 100 ta wannan account numbern 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank ko hoton Mtn card ta Wannan numbern 08147537180 sai kiyi screen short ki turo shaidar biya*
*ki biya tun yanzu kafin LITTAFIN ya koma 300 domin kuwa ya kusa komawa*
*Kuyi haƙuri yau na muku typing kaɗan hakan ya faru ne sakamakon uzuri da yayi min yawa sorry*
*UMMU NASMAH CE*
[4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺
*GELLE ƁINGEL*
🏺🏺🏺🏺
*Story*
*Rasheedat Usman*
*(Ummu Nasmah)*
*Littattafan marubuciya*
Sauyin Rayuwa
Nasmah Ko Nasirah
Sara Da Sassaqa
Indo A Birni
So Bai San Jini Ba
Akan ƴar uwata.
Hatsabibiya Saude
Ruɗanin Zuciya Biyu.
Doctor Hassan.
Ƙauyenmu.
And now *GELLE ƁINGEL*
*SADAUKARWA*
Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah.
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_________________________________*
*AFWAN AFWAN!!! AFWAN FAN'S JIYA BAN SAMU DAMAR TYPING BA GASHI KUMA BAN BAKU UZURI NA BA, INA NEMAN AFUWAR KU MUSSAMAN ƳAN PAID GROUP AMMA TABBAS UZURI NE MAI ƘARFI YA RIƘENI A JIYA*
*FREE PAGE*
➰➰ *21 to 22*
Nisawa Zee tayi tana gyara zamanta tare da saka hanu ta ɗauki Abdul ta dawo dashi jikinta, duban SAFREENA tayi ta fara magana cike da nutsuwa.
" SAFREENA karki sake wani kuskuren na biyu, domin zai iya jawo miki tashin hankali da yafi na baya, sanin kanki ne ba imani bane da Garkuwa zai iya aikata komai akanki domin ganin ya kawo ƙarshen ki a wannan duniyar saboda ya fahimci baki da wani burin da ya wuce ki tozarta shi, ki daina kafa hujja da Abdul zai iya kasheki ya ɗauki wannan yaron ya fitar dashi daga Nigeria ya kaisa can wata ƙasar yayi Rayuwa ba tare da kowa yasan jinin sa bane, gudun kar asirinsa ya toni a gane shi fasiƙi ne, ubansa sanannan ɗan kasuwa ne kin sani babu wanda bai san Alhaji Buba Garko ba, kinga kuwa dole ya nemi duk hanyar da zai tseratar da mutuncin ubansa, kasheki a wajen Garkuwa ba komai bane, SAFREENA ina tausayinki yasa nake faɗa miki iya gaskiya ta, kina da tarin a hali sai dai ba su da amfani a gareki SABODA basu ƙaunar mahaifinki bare kuma ke, Daddy shi kaɗai ne gatanki a duniya kuma yanzu babu shi, ki riƙe maraicinki SAFREENA karki sake shiga safgar Garkuwa, a baya soyayya ta jefaki cikin mungun yanayi harta yi sanadiyar rasa farin cikin ki, a yanzu kuma na hango ƙiyayya tana shirin ƙara jefaki cikin masifa, dan Allah SAFREENA karki sake hasashena ya zamo gaskiya, ki barsa da Allah ki rungumi ɗanki ki basa tarbiyyar da ta dace, ki manta da Garkuwa a rayuwarki karki sake koda wasa yaga Abdul domin zai rabaki dashi."
Hawayene suka zubo daga ƙwayar idanun SAFREENA cikin sanyin jiki da rawar murya tace.
" Na sani Zee bani da gata yanzu na rasa gata na ta sanadiyyar Garkuwa Da son zuciyata, dalilin da yasa nake jin bazan taɓa samun sukuni ba, idan banga Garkuwa a ƙasƙance a wulaƙance ba, na rantse miki da Allah bazan bar Garkuwa yaji daɗi a rayuwarsa ba, sai na toshe duk wata hanyar da farin ciki zaizo masa, sai na ɗanɗana masa baƙin ciki fiye da wanda ya sani a cikin sa, dan haka ki adana kalamanki domin bazasu shiga kunnuwa na ba, saboda suna toshe babu abinda yake yawo a cikin su sai sautin ƙara da ihun iyayena, ina jin sautin su acikin kunnuwa na, suna ihu wuta na cinsu, Abba da ummi sun mutu ne da sunana a bakin su, sai ni kuma na kasa ɗaukar fansar su, muddun ban ɗauka musu fansa ba, rayuwata bazata taɓa samun nutsuwa ba, Zee na San a baya soyayya ce ta jefani mungun halin da nake ciki yanzu dalilin da yasa naji na tsani soyayya da duk wani mai yinta, na tsani maza bana son ganin su, wallahi Zee da wannan hanun nawa zan kashe Garkuwa nayi wannan alƙawarin kuma sai na cikasa koda nima zan mutu, menene a rayuwata ban yiwa GARKUWA ba, numfashi nane kawai ban basa ba, amma ki duba kiga a ƙarshe abinda ya saka min dashi, ko wannan yaron idan na kallesa na tuno jinin Garkuwa ne sai naji na tsanesa, ji nake tamkar na shaƙesa masa wuya ya mutu, bazan ɓoye miki ba Zee bana son ganin fuskar Abdul saboda babu inda yabar Garkuwa, Baba ne yafi ƙarfina wallahi da bazan shayar da shi ba."
" Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!! Me kike faɗa ne haka SAFREENA shin ƙiyayyar Garkuwa tasa kin haukace ne, sai abubuwa kike ta famar yi irin na mahaukatan da aka saka a turu, shi wannan yaron meye laifin sa, sanda zakuyi zina ku samu cikin sa ya sani ne, shima baiƙi ya fito ta hanyar halak ba, SAFREENA karki haɗawa kanki zunubi biyu akan Abdul, ga zunubin kawosa duniya ta hanyar zina ga kuma zunubin azabtar dashi, baisan komai ba tsakanin ku, dan Allah karki hukuntasa da laifin da ba nasa ba, tunda kince bazaki haƙura kibar Garkuwa ba, shikenan amma shi dai Abdul dan Allah karki cutar dashi ki jashi a jikinki a yanzu bashi da wani gata idan ba ke ba."
" Ni ba gatansa bane ki daina kirana a matsayin gatansa, Abdul bashi da laifi kike cewa, karki manta da cewa ƙaddarar haihuwar sa ta hanyar da bata dace ba, shiya jawo min duk wani tashin hankali da nake ciki,. Sannan kice bashi da laifi, HMMM!!!! Idan kika ambato min kalmar zina sai inji tamkar zagina kike, kinsani ni na mazinaciya bace ƙaddara ce ta faɗa min da duhun Soyayya, kin sani rashin kuɗi yake sa ayi zina, ni kuma ban rasa komai ba a rayuwata sanin kanki ubana ya ninka uban Garkuwa goma a kuɗi ki dinga saka lamarina cikin kaddara."
Tana gama faɗin haka ta miƙe ta fice tana kuka, hawayen daya ɗan taru a idanun Zee ta goge tana goya Abdul a bayanta ta hau jijjiga sa.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
" Asabe yanzu kina nufin goben dole sai da sassafe zamu tafi kin sani fa Alhaji bazai barni nayi fitan sammako ba."
" Haba dai Hajiya Zainab, ya kamata ki nemo duk wata hanyar da zai barki ki fice domin kuwa uban layi ake samu wajen bokan nan, idan ba sammako mukayi ba, ƙarshen ta musha wahalar banza ne bamu samu ganinsa ba, kiyi ƙoƙari kisan ƙaryar da zaki masa mu tafi 5:30am."
Shuru Momy tayi kafin tace.
" Shikenan zan gwada Allah yasa ya barni, wallahi haushin tsohuwar nan nake ji, ta tsaneni tun ina budurwa har kawo yanzu girma ya fara kamani amma bata barni na huta ba, ni a wannan karon so nake a raba tsakanin su da Alhaji Buba kowa yaji ya tsani