Showing 9001 words to 12000 words out of 15803 words
kece haka da ranar nan Ohh keda Anwar ne can, ai Anwar ba ruwansa wallahi, yana da kirki ga son jama'a gashi da k'ok'ari yana k'ara koyar damu idan Malamai sun fita yana k'ara ganar damu bashi da matsala wallahi", da sauri Khairat ta ce "to fad'i ba'a tabbaye ki ba, na ce ki fad'a min ya halinsa yake ne daga ganin mutum kawai saina saki jiki dashi nidai wuce muje", dariya Teemah tayi ta ce "hmm kinfa sakko da kanki dan kuwa Anwar na fad'a na k'ara fad'a bashi da matsala Allah sarki bawan Allah bashi da kowa d'an talakawa ne a cikin garin katsina yake kinsan zakiyi mamakin idan ya koma katsina adai-daita saho yake ja domin rufawa kai asiri duk iyayansa sun raso shi ke d'au nauyin karantunsa da kansa wallahi mugun tausayi yake bani, dan Allah Khairat idan ma cewa yayi yana sonki karkiyi mai wulak'anci baki san nan gaba mi zai zama ba please na rok'eki", ta idasa maganar tana had'a hannuwanta waje d'aya alamar rok'o Khairat kuwa tuni hawaye sun wanke mata fuska da sauri ta juya inda ta barshi bata gansa ba sai dai bayansa data hanga yayi nisa dasu kamar ya sani ya waigo daga inda yake hana faman mata murmushi, itama murmushin ta mayar mai lokaci guda taji bala'in tausayin Anwar ya shiga zuciyarta.
Fita sukai wajan school d'in kad'an da yake nan aka kama masu gida da yake Federal University Dutsanma bata da hostel a cikinta.
Washe gari ita da Teemah suka shigo school d'in suna cikin tafiya suka hango su Goga suna nufo inda suke tafiya da sauri Teemah ta ce "kinga Khairat zomu koma in suka wuce sai mu wuce dan wannan mutanan suna da had'ari", "had'ari kuma Teemah to mi yasa aka barso suna shigowa school d'in?", cewar Khairat girgiza kai Teemah tayi ta ce "kamar baki san a cikin Najeria kike ba to shima mai kud'i ne yana da kud'i sosai kud'in sa basu anfane sa da komai ba sai shaye-shaye da tara y'an iska yana k'ara lalatasu, ubansa ya mutu yabar mai mak'udan kud'ad'e sana d'an siyasa ne yasan mutune da yawa koda yayi laifi ba'a gani sai a boye kinga zo mu wuce dan Allah karma su ganmu", ai kami ta rufe baki Goga da bud'ad'd'iyar muryarsa ya ce "ku dakata daga nan idan kuma kuka matsa na rantse da Allah sai na keta mutumcinku", jikin Teemah ne ya kama rawa gabanta yayi wata irin mummunar fad'uwa jin abinda Goga ya ce.
Goga na k'arasowa ya tsaya akan Khairat data rungume hannu duk da itama taji shakkarsa dakewa kawai tayi, kallonta yake har yana wani karkace baki yana fiddo harsha irin na y'an iska kawai basuyi tsammanin maganar da zata fito bakinsa kenan ba ya ce "ina sonki", ya fad'a yana kallon Khairat wani kallon banza tayi masa wani murmushi tayi ganin Anwar na nufo wajansu da sauri bawan Allah har yana had'awa da gudu yana isowa yaji Khairat ta ce "ni ga wadda nake so nan ya k'ara so", ta idasa maganar tana matsawa inda Anwar yake tsaye yayi mutuwar tsaye wata irin shegiyar dariya Goga ya saki ya ce "tabbas ina sonki kuma sha'awarki nake duk wadda ya ce zai shiga gonata to sai nayi SILAR MUTUWAR SA kima sa wannan a ranki shi kuma sakaran da keki so kece zaki ceceshi daga halaka", yana idasa maganar yaja y'an koransa suka bar wajan kuka Khairat ta saki ita da Teemah da sauri Anwar ya ce dan Allah ku daina kuka haka nan Insha Allah ba abinda zai iyayi inba abinda Allah ya rubuta a cikin littafin K'ADDARAR MU ba", share hawaye Teemah tayi ta ce "hakane amma har yanzu baku san waye Goga ba ina tsoron abinda zaije ya dawo wallahi", da sauri Anwar ya ce "babu abinda zamu gani sai alkhairi kunga kuzo mu wuce class kubar wannan maganar ma please", badan maganar zata iya fita a ransu ba suka shiga aji haka dai aka gama lecture's har uku ba abinda suka gane daga su har Anwar d'in dan kuwa damuwa ce dank'are akan fuskarsu dan yau Anwar ko tsayawa koyar da d'alibai bai ba suma kansu sunga yana cikin damuwa.
Har tsawon sati uku basu k'ara ganin Goga ba har hankalinsu ya d'an kwanta har soyayyar Anwar tayi tasiri a zuciyar Khairat soyayya suke mai cike da nutsuwa abinda basu sani ba shine Goga bawai kyale su yayi ba zuba musu ido yayi kuma yana sa y'an baradansa suna sa mai ido akan Anwar da kuma Khairat zuciyar Goga a bushe take kamar tsohon arne kwata-kwata ba Allah a cikinta bare imani shed'an yana nan yana kitsamai mugun abun daya shirya musu dan har cewa yake "indai bazau d'an d'ana zumar Khairat ba ya rantse da sarkin dake bosa mai lumfashi sai dai kowa ya rasa zai iya hallaka kowa akanta kai harma da ita inta k'i basa had'in kai............✍️
*ZAHRA ROYAL STAR CE*
share fisabilillahi🥰🙏
*💔🧟♀️☠️SILAR MUTUWA🧟♀️☠️*💔
(Horror Story)
ZAHRA ROYAL STAR CE.......✍️
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI*
PAGE 1️⃣3️⃣➡️1️⃣4️⃣
Bak'ar rana ita ce ranar da Federal University Dutsanma da yawa wadda suke cikinta kai harma da cikin gari baza su manta da ita ba.
Washe gari cike da nutsuwa Khairat da Anwar suke tafiya dan Teemah bata samu shigowa school d'in ba dan kwata-kwata bata jin dad'i.
Kamar an jefoshi ya shiga gaban su yana zazzare idonsa irin na y'an shaye-shaye cike da muryarsa irin ta y'an iska ya ce "Khairat bazaki rabu da wannan malohon ba dai ko na rantse da wadda raina ke hannunsa idan baki rabu dashi ba nine zan zama SILAR MUTUWARSA indai a kanki ne kai kuma", ya idasa maganar yana kai dubansa kan Anwar yana tsaye ko gezar bai ba sai ma ya b'ude baki cike da rainin wayo ya ce "kai harka isa ka raba ni da RAYUWATA inba Allah ba koda yake kufa ba sanin Allan kukai ba ban tab'a ganin dabba...... Kamin ya idasa maganar Goga ya kai mai wani shegin naushi yana cikumo wuyan rigar sa, cike da tsananin tashin hankali da tsananin tsoro Khairat ta rushe da kuka tabbas babu abinda Goga bazai iyayi ba a kanta da sauri ta nufi inda suke da sauri Goga ya waiga yana ware mata jajayen idonsa ya ce "tabbas kin jamai mutuwa dan ba abinda zai hana ban hallaka sa ba ke indai ban same ki ba sai dai kowa ya rasa harke zan iya d'aukar RAYUWARKI", wani irin ras taji gabanta yayi wata mummunar fad'uwa har tana yin baya ta fad'i k'asa hawaye na k'ara b'alle mata wannan wacce irin k'addara ce haka take shirin faruwa da ita.
Da kyar mutane suka b'anb'are Anwar jikin Goga da kyar ya samu wunyansa ya dawo dai-dai dan ba k'aramar shak'a yayi mai ba, da sauri Khairat ta ce "dan darajar Allah Anwar kabar makarantar nan yau-yau d'in nan ina gudun abinda zaije ya dawo bazan tab'a yafe ma kaina ba idan wani abu ya same ka", "karma kice haka babu inda zani", yana idasa maganar ya tashi ya fice daga school dan kwata-kwata baya ma jin dad'in abinda ke faru dan dai ba yadda zaiyi ne har k'arar Goga yasha kaiwa amma babu abinda akeyi sai kaga kamar da gaske za'a d'au mataki amma sai dai kaji shuru.
Khairat kuwa ganin dare ya fara yi dan da k'arfe shadda tayi rana ke fad'uwa duhun dare ke mamaye ilahirin garin cike da tsananin tsoro take tafiya har tana hard'ewa dai-dai zata sha wata kwana wata bak'ar mota ta zo da gudu kamin tayi wani yink'uri suka jata da tsiya suka tusata cikin motar tana niyar ihu duk da school d'in sai mutune dai-dai ku kuma dai-dai kwanar ba'a cika binta ba saboda school akwai girma, suka sa tsunma suka d'aure mata baki hawaye ne kawai ke zuba ta idon Khairat kamar fanfo.
A wajan Anwar yana zaune a shi kad'ai domin d'ebe kad'ai ci ga gabansa dake fad'uwa kawai yaga dan-dazon maza a kansa rik'e da wuk'ak'e da sandina kamin ya ce tak suka rufesa da Uban duka kota ina baji ba gani baka jin k'arar komai sai na dukan da suke mai sai na ihunsa tun yana motsi har ya daina sai da suka duba ganin baya motsi da sauri wani cikin su ya ce "kai gayis kamar fa ya mutu muyi maza mubar gun nan ku tabbatar baku bar wata shaidar da za'a gane mune ba", sai da suka tabbatar sun kwashe duk wani k'arfe nashi sana suka ajiye shi tsakiyar titi dan ayi zargin mota ce ta bank'e sa dan irin bugun da zuka mai yadda kasan tirera ce tabi ta kansa Anwar kuwa dama rai tuni yayi halinsa tun farkon bugun da suka kaima dama ransa na gaf da fita sai ya zama sune sanadi.
A wajan Khairat kuwa bata tsinci kanta a ko ina ba sai a gaban Goga, zaune yake kan kuje wata irin dariya yayi yana cewa "yanzu akwai wadda zai iya cecanki wadda kike tak'ama kina so tuni yanzu na sani yayi bankwana da duniya kuma yaune zan cika buri na a kanki", wata irin zabura Khairat tayi tana zubewa k'asa wani irin kuka ta saki tana cewa "Wai kai wani irin bawa ne marar imani badai sawa kayi a kashe Anwar ba to wallahi dana bari ka keta mutumci na gara na mutu nima nabi masoyina na rantse bazaka tab'a cika burinka a kaina ba", Goga tashi yayi a zuciye yana kai mata wani bahagon mari ji kake tassss har saida Khairat ta kifa a k'asa tashi tayi tana dafe kumatunta iyanzu zuciyarta ta bushe bata ma tsoronsa k'ugunta ya kamo da sauri tasa hannunta domin hankad'e sa sai dai ina yayi mata mugun ruk'o, miyau ta tattaro ta tofa mai a fuska, runtse idonsa yayi cike jin haushinta ya k'ara kai mata wani marin har guda biyu tassss tassss tassss kake ji kamo gashin kanta yayi dake cikin hijab da k'arfi wata y'ar k'ara ta saki tana kallonsa da idonta da sukai jawur sai da ta dai-dai ci wajan mafitsarar sa tasa k'afarta da k'arfi ta daddage tana kaima wajan wani shegen naushi ba shiri Goga ya saketa yana sakin k'ara ai kamin kace mi ta d'auki wani k'aton k'arfe ta bibbigi duk wadda yasha gabanta da sauri ta b'alle K'ofar gidan tana fice da gudu hawaye take tana wani abun gudu gasu Goga dake binta a baya yana cewa "ku tabbatar bata shaba inba haka ba wallahi dukanku saina yanke muku mummunan hukunci", jin abinda ya ce suka k'ara k'aimi dan sunsan Goga kamar mai zuciyar fir'auna bashi da imani ko kad'an, gudu take tana waige harta hau babban titi bata sani ba wata babbar mota ce ta taho gadan-gadan kanta ga mai motar nata so ya kawuce mata amma ina sunzo gaf da juna Goga ne ya fasa wata irin k'ara yana faman cewa "keee Khairat baki da hankali mota ce fa gabanki", wata irin dariya ta saki tana cewa "ai dana bari ka kassara rayuwata gara mutuwa ta cinmini a yanzu kayi SILAR MUTUWAR masoyi na ka rubuta ka aje zaka girbi abinda ka shuka nan bada dad'ewa ba in...... Kamin ta idasa maganar ma motar tayi gaba da ita ba k'aramar banka ce akai ma Khairat ba dan sadda zata dawo k'asan titin kanta ne ya fashe dan har kana iya hangen tsakiyar kanta, shi kansa Goga ya girgiza da sauri suka bar wajan mai motar shima bai tsaya ba guduwa yayi (kai Allah ka kasa mufi k'arfin zuciyarmu Najeria kenan).
Wayewar gari ba k'ara min tashin hankali garin Dutsanma da kewaye aka tashi dashi ba Teemah kuwa kasa d'aukar maganar kanta da tunaninta yayi suma ta rink'a yi har saida akayi asibiti da ita sadda dangin Khairat zasu k'araso nanma sabon tashin hankali ya k'ara b'arkewa kuka kam ba'a magana duk wadda ke cikin school d'in nan indai mai tausayi ne sai da yayi kuka imani ya k'ara shigarsa har mutuwar Anwar an danganta tane da had'ari yayi makarantar kanta ta girgiza har saida aka daka ta da komai na kwana biyu.
A sadda Teemah zata farka kuka take tana cewa "wallahi Allah ba mutuwar Allah da Annabi ce sukayi ba kashe su akai" ba wadda ya d'au maganar da mahimmaci saima aka dankanta da hakan da cewa mutuwar ce ta zautata ba k'aramar jinya Teemah tayi ba k'arshe ma karatun katseshi tayi ta ce ta hakura da karatun, sai dai abinda ya dakatar da Teemah daga barin school d'in duk sadda nayi niyar barin school d'in nan ina yawan wasu irin mafarkai masu rikita min tunaninta a cikin mafarkin ina yawan ganin Khairat tana cewa "in daina sa damuwa a raina kuma kar nabar karatu na akan wannan abun k'arshen Goga bazai kyau ba in zauna a cikin makarantar nan zanga yadda Allah zaiyi ikonsa akan Goga".
Teemah ta idasa maganar tana kallon su Surayya yadda kowa daga cikinsu tunkan aje k'arshen labarin suke kuka harda shashsheka ita kanta kuka take Surayya ta share hawayen tana tashi tsaye kamar wani abu ya shiga jikinta muryarta ta koma wata iri ta ce "tabbas saina sa su Goga cikin uk'uba da kansu zasu kai kansu koto kuma dole a yanke musu hukunci dai-dai da laifinsu", cike da mamaki suke kallonta har Teemah kamin suyi magana suka nemi Surayya suka rasa sama ko k'asa babu ita kamar ba'ayi wanzuwarta a wajanba sosai suka shiga tashin hankali anya Surayya ita d'aya ce kuwa.......✍️
*ZAHRA ROYAL STAR CE*
Share fisabilillahi🥰🙏
*💔🧟♀️☠️SILAR MUTUWA🧟♀️☠️*💔
(Horror Story)
ZAHRA ROYAL STAR CE.......✍️
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI*
PAGE 1️⃣5️⃣➡️1️⃣6️⃣
Wani irin daji ne mai duhun gaske su Goga suna tashi suka tsinci kansu a ciki ga wasu irin koke-koke ba dad'in ji, wata irin dariya suka ji daga bayansu dariyar na wata irin tashi gaba d'aya kogunan dake dajin da bishiyoyi har wani amsawa suke suna wata irin girgiza waigawar da zasuyi suka ga wata mace sanye da take da wasu bak'ak'en kaya fuskarta rabi a k'one idonta ko d'igon baki babu gashin kanta na tashi sama kamar iska na hurasa sosai suka tsoron ta suka fara ja baya Goga ne mai k'arfin halin bud'e baki ya ce "bawar Allah shin wai ke wacece da kiketa azaftar damu haka?", wata dariyar ta sake yi wata irin murya bud'ad'd'iyar muryar ba dad'in sauraro ta cika musu kunne har saida suka runtse ido muryar na fitowa a rarrabe ta ce "harka manta da abinda kayi duniya to shine yanzu kuke girbar abinda ka shuka kaida mutanan ka wallahi Goga kamin in bari kaje wajan shari'a su yanke ma hukunci saika d'and'ana kud'arka", zubewa Goga yayi a k'asa ya fashe da kuka kamar yaron goye yana cewa "kayiwa Allah kabar mu haka wallahi munyi laushi kuma nida kaina zanje kotu domin yanke min hukuncin abinda nayiwa Khairat ne nasan cewa shine yake biya-biyata", wata dariyar ta sake kecewa da ita mai ban tsoro ta buga mai wata irin tsawa ta ce "kai har kasan Allah sadda zaka cuci mutane ai sun had'a ka da Allan ka kyale su ne dan haka yanzu ma sai kunyi muguwar nadamar da har abada bazakuyi marmarin cutar wani ba har abadan kuwaaaaa", ta idasa maganar tana buga wata sadda dan danan wasu irin namun daji masu had'arin gaske suka wanzu a wajan.
Kamin kace mi su Goga sun arce da mugun gudu cikin jejin umarni taba namun daji ai kuwa kamin ta rufe baki sun bisu da mugun gudu su Goga ganin yadda suke gudu namun dajin gudun nasu kamar walk'iya haka suke gudun.
Gudu suke suna k'ara nausawa cikin jejin ko kallon gabansu basa yi ga namun dajin dake binsu masu had'arin gaske da yawa cikin mutanan Goga sun fara gajiya da gudun kuma ba damar tsayawa shi kansa Gogan numfashinsa har d'aukewa yake mak'oshin sa ya bushe k'amas wata irin k'ishir ruwa yake ji kamar zai mutu tuntub'e yayi da wani mugun icce ya buge kansa yana fad'uwa k'asa wata irin juyawa kansa yayi yana sarawa kamar zai rabe gida biyu zubewa yayi a wajan numfashinsa na barazanar d'aukewa su kansu mutanan Gogan zubewa sukai suna faman sauk'e numfashi sun riga sun sadak'ar namun dajin na k'arasowa zasu cinye su.
Sai dai namun dajin na k'arasowa suka b'ace b'at kamar babu kowa cikin jejin dajin ne yayi cit baka jin ko tari wata irin ajiyar zuciya suka sauke.
Wata irin k'ara daga cikinsu wani ya saki da sauri su Goga suka matsa kusa dashi hankalinsu yayi mugun tashi ganin wata shirgegiyar mage bak'a wulik girmanta ya wuce misali sai tayi girman wani jaririn ta kama k'afarsa da wasu irin farce zak'o-zak'o ta karceshi da k'arfin tsiya shi kuwa sai birgima yake dan wani irin azaba yake ji kamar ana yankan naman jikinsa, kallonsu take da jajayen idonta masu firgitarwa kamin suyi wani yink'uri ta b'ace b'at wani irin tsoro ne ya dirar masu ganin babu magen babu alamarta sukam sun shiga uku wannan waccce irin masifa ce haka.
Basu k'ara tsurewa ba sai da suka ga d'an uwansu wadda magen ta yakusa yana wata irin girgiza da wani irin gurnani kamar mage ta samu nama matsawa sukai kusa dashi domin basa taimako sai dai mi. Wata irin zabura sukai ganin idonsa ya koma fari fat tsakiyar bak'in ya koma wata irin kala hakuran bakinsa sun koma irin na masu shan jini masu tsinin gaske jikinsa na wata irin babbank'arewa kamar ana kakkarya k'asusuwan jikinsa wata irin mik'ewa yayi kamar an basa umarni yana wani irin gurnani.
A wajan su Zuby kuwa k'awayanta na komawa gida sukaita zuga Zuby akan cewa akwai wani boka mai aiki kamar yankan wuk'a, sha yanzu magani yanzu aikinsa ba k'arya yana yi k'anwarta ta ce "ai Aunty wallahi idan baki shiga gidan Ahmed Sadeeg Garkuwa ba sai na ce kinyi asara babba kuwa, koni na samu