Showing 54001 words to 54627 words out of 54627 words
kara haihuwa nuratu ta haihuwa sannan kuma maryam ma ta kuma haihuwa.
Zaune nake a babban falona ina taiwa islam faɗa sabida tai latting fita school sabida suna placement ne ta shiga ss1 sallama mai aikina tai tare da cemin hajiya kinyi baki suna karamin falo.
Fita nai na tarar da wata tsohuwar mace baka da wani gurgu suna zaune a kasan carfet.
Zama nai muka gaisa batare danai ƙyamarsu ba,"Mammah sena dawo" islam yarinya mai shekaru goma sha biyu take gayamin.
"To adawo lafiya bakiga baki ba".
Gaisarsu tai ta wuce naga wannan tsohuwar tana bin islam da kallo.
"Islam zo baki gane nine bako?".
Dawowa tai tana ɗan ɗage hancinta gani.
"Islam ina kaninki?".
"Yana madina daddy ya kaisa makarantar haddar kur'an"
Tafaɗa a gajarce.
"Islam nice antynku ku yafen yaran nan dan Allah cutar danai tai muku abaya ita Allah ya nunan domin nai auren mai mata da wata ɗaya ya sakoni harda karayar da ƴaƴansa sukai min wadda ita ta nakasan rayuwa kinga hannun baya sarrafuwa ta sauki inko ya kama min ciwo kamar zan mutu".
Kamar islam zatai kuka tace.
"Na yafe miki mommy mammah ki bata magani na tafi school"
Tafita ta barmu tunda ta soma magana nake mamakin yadda Allah yake ikonsa daman sakinace wannan?
Sautin kukanta ya dawo dani daga tunanina tana kuka tana bani hakuri tare da gabatar min da nazeer atake anan tsoron Allah ya kamani tabbas bazakai sharri kaji daɗi ba haka bazakai alkairi kaji rashin daɗiba yanzu tun aduniya ake sakayya wallahi ba'a bari aje can.
"Nazeer sakina na yafe muku kuma Allah yasa wannan ya zama darasi akaina dama sauran alummah sabida haka kuje na yafe muku".
Na faɗa ina tashi naje ɗaki inata mamaki kayana na hado mata harda na islam dayake tace tana da yarinya sannan na basu kudi kimanin dubu hamsin mukai sallama sunata godiya kamar zasu ari baki
Dawowa nai na zauna aini sakina ta koyan hankali shiyasa tunda na dawo nan ban yarda sabga ta haɗani da kowa ba face mutuncin gaisuwa babban abokina mijina ƴaƴana kawayena.
Koda ya dawo na tareshi da maganar bai wani damu ba haka ya shantakar da abin yana cewa daman ai karshen alewa ƙasa.
Islam kwa data dawo tana basa labari harda kuka rarrashinta yay yana tsokanarta wai mai irin zuciyata.
Kafin ya dawo kaina ya ribacen muyi master room tun a bakin kofa yake faman kissing ɗina tare da ɗagani cakk yay saman bed dani ya shiga ya mutsamin jikina.
"I love you wfy"
Yafaɗa yana kafa bakinsa a na shanuna.
"I love you hubby"
Nima na faɗa ina ɗora a hannuna a lantarkinsa kafin mu lula duniyar ma'aurata
*TAMMAT BIHAMDIHI*
Anan na kawo karshen littafin zuma a baki.
Jigon labarina:
Yarda da ƙaddarah mai kyau da marar kyau sannan kuma sadaukarwa da cin amana wanda yay girma acikin alummarmu.
Uwa uba soyayyar gaskiya wadda tai aiki acikin labarin.
Kuskuren danai ya Allah ka yafen abin da nai dai dai kuma kabani ladan
My fans abinda kuka gani na dai dai ku ɗauka amman abunda kuka gani na rashin dai dai ku watsar!
Allah ka ƙarawa mahaifiyata lafiya ina godiya sosai gareku da jimirin bina daki daki.
Godiya ga wahidin ahadun daya bani ikon rubutun ya kuma haskan tunanin ya kuma bani karfin gwiwa ya kuma buden ƙwaƙwalwa yakuma haɗani da masoya ta hanyarsa nagode maka ubangijina ina rokon ka daka ƙarawa annabin(s.a.w) daraja da wasila da fadila fil jannatul firdausi amin.
End of zuma a baki on sat/25/december 2022.
*AUTAR MANYA*
Marubuciyar.
*MURADIN ZUCIYA*
*TAURARO*
*HASKE*
*RABON WANI*
*KOBA SO*
*ƊAN MAJALISSA*
*DA IZZATA*
*AUREN BARE*
*ZUMA A BAKI*
Sekuma........
*BAƘAR FATA*
Love and romantic story 2022 da yardar Allah ze faso.
BAƘAR FATA
Kalar fatar jikina!
BAƘAR FATA!
Daga fitattu huɗu🔥
BAƘAR FATA!
Launi daga cikin halittta
BAƘAR FATA!
Takun na musammane
BAƘAR FATA!
Hmmm bazance komai ba amman zance wannan karon sekun wanke hannu kun tanadi ruwan ɗumi kusa sabida😜..........
More information akan BAƘAR FATA DAMA SAURAN CHART ME UP! 08142105218
Autarku ce😘