Showing 42001 words to 45000 words out of 48601 words

Chapter 15 - CINIKIN RAI BOOK 1

12 Jul 2025

1765

gani nan tawowa!"
"Mayyar kudi! Ko kunya baki ji ba."
"Ki gaya min inda bolar kudi yake, na je na tsinta dan kaniyarki " ta kashe wayar, Hafsy kwalliya take yi, tana zuwa har gida tayiwa mutane, duk da kusan kayan kwalliyar Zeenobia take saya mata ko ta bata kudi, duk da jagaliyarcinta, tana kwalliya kawai bata damu da saka kaya ba ne, amma yarinyar ta san darajar ado da saka sutura.
Can Hafsy ta iso bakin kofar, ta buga kofar. Bude mata tayi, kallon wata hadaddiyar doguwar riga blue-black, har sa hat dinsa. "Wow ko nace sexy!" Zama tayi ta fara Ciro kayan, tana faWin. "Dinner zaki ne?" "Lunch za ni" d'ago kai tayi kafin ta ce mata. "Wai ke meye matsalarki da bakar magana." Dauke kai tayi tana latsa wayarta kamar bata san me take tambayar ba. "Kutumar Uba!" Ganin hotonta an manna a wani shafin yanar gizo an rubuta.
*BA IYA DABANCIN NE SANA'ARTA BA, HATTA KARUWANCI DA MANYAN MUTANE TANA YI DOMIN SAMUN DAMAR HADUWA DA MALIK MENK JORDAN!*
aka saka hotonta a gefen wani blank pic da babu hoton kowa sai alamar tambaya. Lekawa Hafsy tayi, ta amshe wayar. "Kiyi hakuri abin da nazo gaya miki kenan, amma da nasan baki san da zancen ba da." "Yi min kwalliyar, na rigada nayi al?awarin sai nayi aikin nan!" "Amma Zeenobia! Ki daina shiga duk wata kazamar harka, domin da ita za.."

"Ki min kwalliyar kawai!" Haka ta shiga mata kwalliyar, har aka gama cizon bakinta take, tana gamawa ta ce mata .
"Done!" Murmushi tayi ya ce mata. "Yayi kyau, bude wancan drower din akwai abin da kike so, ki sauka kawai!". Ta zauna tana kokarin zoge rigarta. "Zeenobia!" Bata juya ba ya cigaba da kokarin saka rigar. "Kiyi hakuri!" "Da aka yi me?" "Da abin da ya faru!" "Kai manta kawai!" Da taimakon Hafsy ta gama shirinta tsaf, sannan ta ciro Christian Dior bag and shoe, ta saka hill ne sosai. Sannan ta gyara zaman takalmin.

"Zeenobia ya baki saka turarenki ba!" Murmushi tayi ta ce . "Ban manta da shi ba, duba can akwai Tom Ford cafe rose." Ciro mata tayi ta fesa kadan, take dakin ya dauki wani sassanyar kamshi. Kama gashinta kanta tayi, ta daure shi. Sannan ta daura hat din kanta, "Don Allah zan iya daukarki hoto zan daukar a IG na ne, zan yi magana ne!"
"Yaushe kika koyo takife?" "Zaman da Yar kunama!" Gyada kai tayi tana fad'in. "You're welcome!" Daukarta hoto tayi sosai, a wurin ta daura a IG.
*SHI KARUWANCI IYA CE, DUK WANDA YA IYA YA KWASHE, DUK WACCE TA JI HAUSHI GOBE TA SHIRYA GANIN MAYOR MALIK MENK JORDAN...... UP-UP-UP SARAUNIYAR VOGUE MAGAZINE COVER*

Dama bata da wasu followers, amma tana sakawa ta yi amfani da Hashtag tare da gidan gwamnati dake Waterfall island, take aka fara bibiyar pagenta. A cikin abin da bai haura minti Talatin ba, sai ga Followers sama da dubu biyu sun bi ta, amsar wayar Zeenobia bata ta gyara pagen din tare da saka hotonta, ta kuma rubuta cewa.
*The dreams can be true!* Kafin ta saka yar ?aramar hoton
"Bura Uba! Dama haduwa da Malik ne wannan adon? A tow dole mu gayawa duniya mu haWu da Malik!"
"A'a bana bu?atar haka, ina son sirri a rayuwata, domin sirri na da dadi, DABANCIN dai da aka sani a bar shi a haka, ban da personal life, wannan nawa ne ni daya na, koda kika ga na bude account ba yana nufin kowani shirme zan daura a kai ba, ina son rayuwata da take binne yafi armashi."

"Kin sa jikina ya mutu, me yasa kike boye kanki?" Murmushi tayi sannan ta ce mata.
"Hafsy a gare ku, ni ba kowa bace face wacce kuke tare kuke haya gida daya. Amma a gare ni, kune duniyata idan wani abu ya same ni, ba zaku yi kuka sosai ba. Amma idan wani abu ya same ku zan mutu ina kukan abin. Rayuwar mu ta zahiri tafi dadi sama da ta social media! Ina son kowa ya za sani a zahiri ba ta media badili ba, kin ga ajiye wannan Posting din saura minti goma kacal na isa inda zamu haWu."

"Ok ranki shi dade, a dawo lafiya!" Daga haka ta dauki key motarta da jakarta da files din, ko da ta sauka kasa, cillawa Dundurosu key tayi yana cewa. "Kai katon banza muje ka raka ni!" Haka ya cabe, sannan ya shiga gabar motar tana baya. "Uwar Wakina, ina zaki haka kika tashi kan gidan nan da kamshi?" "Meeting!" Ta fada tana kallon agogon chopard, tab'e baki tayi tana faWin. "Bakin Waterfall island zaka kai ni!" "What?" "Ka kalli titi ka da ka watsar da ni a rami" daga haka bata kuma magana ba, har suka isa bakin ruwan tara saura minti biyu.

Sai dai abin mamaki, tunda tazo babu alamar akwai me jiranta, ko za azo dauke ta, tun tara saura minti biyu har tara da rabi. Idan ranta yayi dubu sai da ya Saci, kallon agogon hannunta tayi tana kwafa. "Muje Man" tasar da motar yayi suka bar wurin.
Da Sacin rai ta isa gida, tana isa ko magana bata yiwu kowa ba, dama kuma haka take idan ranta ya b'aci bata magana. Har ta isa Wakinta ta kwanta bata cire kayan ba, sai fuskarta da ta gyara ta cire makeup din ta kwanta, wurin karfe biyu na dare, tana zaune akan abin sallah, wayarta tayi kara. Bakuwar number ce don haka ta dauka tana me sakawa a kunnenta. "Me ya hanaki barci?" Shiru tayi tana son tuno muryan. "baki gane ni ba ne? Ai na yi following din ki a IG!"
"Shatima rite?" " Yes Baby!" Murmushi tayi sannan ta ce mishi. "Ai ko a duniyar mafarki bana jin kalmar baby ta dace da bakinka. Ai kai Babana ne!"
"A'a naki wayon. Baby Ina sonki da aure!" Ajiyar zuciya tayi tana faWin. "Don Allah kayi hakuri ni bana son wanda bai kai ka ba ma, Ni har ga Allah ka min tsofa!"
"What! Shekaru na basu wuce hamsin da takwas ba fa!"
"Allah na tuba, ai ko talatin da tara ya tsufar min balle me arba'in! Ni bana son me shekaru irin naka, kada ya wuce talatin da biyar. Yawwa muci kuruciyarmu tare ba wanda xan aura ya cinye min kuruciyata ba."
"Zainabia kin san me kika faWa?" Ya tambaye ta, in serious tone. "Yes na! Ni bana son namiji da ya tsufa. Ba a san waye gawan fari ba, idan ka mutu ka bar ni kafin na samu daidai dani ya aure ni, zan sha wuya so kawai hang out!" Ta kashe wayar.
Sake kiranta yayi yana faWin. "Ni ba irin wadannan tsofin ba ne, ina da lafiyar da zan baki kulawa, ki amince da ni." Dariya tayi sannan ya ce mishi.
"Kaga kuwa bana son tsoho, har ga Allah idan nace maka ina sonka nayi karya, kawai zan ta bata maka lokaci ne, idan na samu wani nayi aure ba ni da dogon buri. Iya abinda ba samu ya ishe ni, na fahimci maganata."
"Young lady! Ina son na gaya miki wani abu daya, zan cigaba bibiyar lamarinki!"
"Hmmm! Ina baka shawaran ka da ka tsaya ka tafi akwai yan mata dayawa!"
"Ni ke idanuna ya gani, ki haifa kin Yara kyawawa irinki!"
"Sai da safe!" Ta kashe wayar baki daya, a wurin ta kwana, wurin karfe shida ta farka, ta shiga ban daki tayi alola ta gabatar da sallah asuba, karfe tara ta nufi wurin aikinsu, taso ta tafi ta titsye Elbashir, amma kada ya ce akwai wani abu da take nima yasa ta share shi.

Office din chairman ta shiga domin, tun a block one ta fahimci, akwai matsala musamman yadda ake kara kallonta ana kallon wayarsu. Fuska tayi tana me shiga Office din. "Wacce irin abin kunya kika aikata haka?" Ya cilla mata jaridar. Daga bangon shafin ta hango an rubuta.
*BAN SAN IYA MANYAN MUTANEN DA SUKE BINA ZAKU KWANTA DA NI BA!* bata kuma marmarin karanta sauran bayanin ba. "VOGUE MAGAZINE sun cire hotonki a jikin mujallarsu.
"Dama ai ban aike su, su saka hotona ba! Sannan da ake ihu kamar kare ni na bukace ka ko kai ne ka bukace Ni? Kamfaninka kake niman cigabanta, kai me yasa baka fuskanci Malik ba? Kasan hadarin da mutuwar da na fuskanta? Amma ka bude wawwaran bakinka kana min ihu. Kaci arzikin halaccin da kai min da sai na zane maka mazaunanka wallahi!"
Daga haka ya juya ta fita, bata tsaya ba sai a wurin motarta, tana shiga wayarta yana kara. ?auka tayi aka ce mata. "Ki tow daga kamfanin, akwai wata sharon ki ajiye motarki ki shiga."

"Waye kai?"
"Kiyi yadda nace!" Da farko ta dan rude, amma kuma daga baya sai tayi kamar yadda ya ce, har inda motar take ta ajiye. Sannan ta shiga sharon Win, sai da aka kaita gindin gada, aka bude mata bayan an zazzage jakarta da takalminta, sannan aka nuna mata wata Audi,. Shima suka fara tafiya sai da suka bar cikin gari, sannan suna isa wurin da aka ajiye wata mota Rr, ta fita sannan aka bude mata shi, ta shiga a hankali. "Wai ina zaku kai ni?"
Wayarta tayi kara tana dauka aka ce mata. "Saurin me kike?" Aka kashe wayar, ana fara tukin, aka saka mata wani abu tare da rufe mata fuskarta.
Sannan suka fara tafiya, sai da aka yi tafiyar minti Talatin kafin aka fito da ita, tana jin lokacin da aka tadda injin kamar jirgin ruwa. Haka aka yi ta gudu da ita, ba halin ta bude fuskartar. Suna isa ana fito da ita, jin ta taka kasa sosai yasata sauke ajiyar zuciya. A hankali suka shiga mata jagora har ta shiga motar da zai katai Mansion Win, duk wani abin da ake sai da aaka mata bayan ya cire bakin abin da aka rufe fuskarta.
Kallon kome tayi na gidan Black and whiter. A hankali take gyara zamap n hular kanta, da ya zame. "Ina ne nan?" Murmushi aka yi bayanta.
"Mayor Malik Menk Jordan Mansion!" Juyawa tayi ta ga Elbashir, "zamu iya shiga!" Kallon hanyar tayi tana takawa a kasaitacce, domin shi destroy all over record na kowa ta kuma kafa nata da kanta. Har cikin gidan ya rakata, aka bude kofar shiga gidan ya shiga tana bin bayanshi.
"Me yasa jiya kayi breaking promise dinka, bayan ba haka muka yi da kai ba?"
"Shiiiiiiii! Keep quiet ba a cika surutu anan ba!"
Gyada kai tai, har suka shiga cikin gidan a ranta ta ce. "ko makabarta ana magana balle nan!" A tsakiyar Main falo suka tsaya, karar inji yasa suka juya bayansu.
"Kan bura uban can.................
Hhhhhh kome ta gani ga Zeenobia ga Malik.....
*Assalamu alaikum......! Guys wannan littafin na kudi ne! 500? normal 1k VIP. 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga GTBank. Ko katin Mtn, a tura shaidan biya ta wannan number +2347035133148 yan Nijar zasu tuntubi Nana A'ishah. +227 84 50 64 76 500*
*Idan na samu lokaci zan karo page 1 zuwa dare! In sha Allah*
[01/09, 1:17 pm] usmanlauratu71: CINIKIN RAI....20
Beauty an??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????d the beast.
Mai_Dambu *Wannan shafin na ku ne, Aunty Halima da Habibay ku more!*
<<<<<<<|=|>>>>>>>>>
Wato dukkan hankalinta ta daura akan shi, har ya fito falon baki Waya. *Wheelchair!* Ta furta a kasar zuciyarta. Dauke kai tayi tana dariya ?asa ?asa, d'ago idanu yayi ya zuba mata. Sake kallonshi tayi ta kunshe dariyarta, baki daya sai yaji ya muzanta. Jikinshi ya wani irin sanyi. "Ke meye haka?" Dake bata iya boye abin da yake ranta ba ta ce mishi.
"Malik Menk Jordan! Ya kare akan keken guragu. Wai dama wannan shi ne dalilin da yasa shi nisanta kanshi da Al'umma?" Ta kuma kwashewa da dariya, sannan ta dan durkusa akan gwiwarta kamshin turaren Imperial Majesty ya daki hancinta. Sau daya ta tab'a jin kamshin nan, a rayuwarta sai yaui. "Ko a yaya nake bana kunyar haduwa da mutane, sannan maganar pmutane bata gabana. Ni mutum ce me ra'ayin kaina. Ban zo nan domin Kasuwancinmu ba, nazo na ga waye ya firgita mutane da Gwamnatin kasa ba?i daya.
Ka ji da kyau, bana tsoron tunkarar kowacce matsala, amma a karon farko na rayuwata da na ga makirkirin matsala ya koma gefe yana gudun matsala, shi yasa na mishi dariya. Da nasan cewa Malik Menk Jordan ya gudu daga cikin al'umma saboda nakasarshi da ban tako nan ba!"
A karon farko da yaga macen da ta saka shi ya ji ashe, shi in matsoraci h ne. Ashe tsoro ne ya saka shi boye kanshi. Kasa magana yayi ya kalli Elbashir. "Coffee take bukata ko Tea?" Wani dariyar takaici ne ya kamata, wato shi a haka har wani izza ce da shi. Haka kawai zuciya ta ingizata ta kai mishi naushi. Kafin ta idda nufinta, ya ja kekenshi. Sai da ta fadi can.
"Ke baki da hankali ne?" Elbashir ya fisgota zai kifa mata mari.
"Kyaleta mana, bakuwar mu ce tana bu?atar karramawa ko wacce iri ne!" Gyada kai yayi. Fita yayi kallon Malik tayi yana tafiya a keken shi har gaban wani table. Zaman shi ya gyara yana kallonta. Nuna mata kujeran da yake facing Winshi yayi.
Hadiye yawu tayi tana me zama dakyau ta ce mishi. "Da gurgunta kake niman maza?" D'ago kai yayi ya kalleta, kasa tayi da kanta tana wasa da file din hannunta. Kwarjini ya mata lokaci guda, yadda ya kura mata idanu, tana jin ba dadi domin tsakani da Allah idanunshi na da kaifi. "Me kake so?" Ta tambaye shi muryanta a shake. Murmushi yayi yana me juya kekenshi. Shigowa aka yi da tiren tea. Elbashir yana biye dasu, duk maza ne kuma matasa.
Ajiye a gabanta suka yi, Elbashir ya koma gefenshi ya tsaya a gefenshi. "Sha!" Ya fada a sassanyayye. "Ba na shan ruwa ko wani abu a inda ban yarda dasu ba!" Murmushi yayi ya ce mata. " "Sugar nawa kike so.?" "Guda bakwai!" "Bakya tsoron ciwon sugar ne?"
"Waye ya damu idan na mutu? Don haka zanji dadina kafin na mutu." Duk da tarin yarintar da ya hango a tattare da ita, amma kuma ya fahimci tana fadar duk abin da ya fito daga zuciyarta ne. Sai da ya zuba mata sugar hudu, ya juya kafin ya d'an diba a cokali ya sha kaWan, ya tura mata. Da wutsiyar ido ta kalle shi ta ce mishi. "Duk da haka ba zai saka na sha ba ""Ok" ya kai spoon zai diba Elbashir ya ce mishi. "Malik ka manta baka shan sugar!". Juyawa yayi ya kalli Elbashir ya ce mishi. "Kai haba dole mu karrama bakuwar mu"
Sai da ya sha sau uku kafin ya tura mata har da cookie Win. A hankali ta dauka tana kallon coffee Win. Kurba tayi a hankali, "Idan kuma da mun saka, guba fa?" "Tunda ya sha ai zamu mutu tare ne!"

Murmushi Malik yayi yana kallon Wan bakinta yayi, yana girmama maganar da yake fitowa sam babu mara ma'ana sai dai rashin da'a. Ajiye kofin tayi tana faWin. "Ya ishe ni" "Muje ji ga gidan!" "Tab! Ba ji ya kawo ni ba." Ta mika shi file Win. "Da dai kin tashi kunje!" A fusace ta kalli Elbashir.
"Ban zuwa wani abu ne?" Ta tambaye shi, "ko daya"
"Ok Ina file Win!" Mika mishi tayi ya dauki medical glass ya saka sannan ta ce mata. "Su mutanen da suka baki aikin me yasa basu, bawa Yaransu ko su kansu ba?"

Shiru tayi tana kallon shi, sam bai yi kama da wanda yake dogon magana ba, amma yadda yake magana. Yana kara saka mata mamakinshi.
"A Kasuwancinmu, cinikin rai yafi kome armashi da me zaki biya asarar da aka min?"
Kallon shi tayi, sannan ta ce mishi, "Na sani rayuwa ita ce fansar, tsinannen dukiyarka"
"Ke ki iya kalamanki!" D'aga hannu yayi alamar Elbashir yayi shiru. "Hmm! Ina jinki." Ganin babu Sacin rai ko muzanci a kan fuskarshi yasa ta sake wani lalacin murmushi ta ce. "Ba fa ni ce ba fada ba, abin da naji mutane na fada ne, me yasa ba acin dukiyarka?"
"Saboda gumina ne, babu gumin kowa a cikinshi."
"Kana cire hakkin Allah kuwa a cikin gumin naka?" Rintsa idanu yayi ya ce mata. "Bana cirewa ko zaki cire min ne?". Kallon shi tayi sannan ta ce mishi. "me yasa kake jin haushi?" Nuna kanshi yayi sannan ya ce mata. "Bana jin haushin!" "Kana jin haushi mana, kokarin boye fushin zuciyarka kake, amma kafi wancan sikagon fusata!" Ta kalli Elbashir.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login