Showing 72001 words to 75000 words out of 124388 words

Chapter 25 - HALIN GIRMA

12 Jul 2025

3464

din sakin ransa, ya dinga
satar kallon Iman din cikin so da kauna.
  Gyaran murya Bubu yayi, ya shiga bayani da harshen da yake tunanin duk zasu fuskanta,
muryar sa na fitar da amo me tsoratarwa, babu wasa ko digo a cikin maganar sa, ta in da yake
shiga bata nan yake fita ba, yayi wa Lailan tas, ya kuma tabbatar mata da sai ta karbi hukunci
daidai da abinda ta aikata, gaba babu wanda zai yi sha'awar aikata irin abinda ta aikata, karshe
kuma yace y haramta mata karatun nata baki daya, ta dawo gida kenan ba zata koma ba, tunda
babu abinda ta sake daukowa sai mugun hali.
  Ko gezau batayi ba, dama kuma babu wanda ya saka ran zata girgiza ko ta tsorata, kanta dai
yana k'asa dan bata isa ta hada ido da Bubun ba, amma tana zaune kekam har ya gama ya
kuma juya kan Muhammad da Iman ya sake basu hakuri musamman Iman da ta shigo gidan ta
kuma fara da karo da irin wannan abun, kachokam ya dora laifin Lailan a akansa, ya sallame su
ya zama daga shi sai Kilishi.
  Gaba Ammi tayi zuwa bangaren ta, tare da Iman dan bata bukatar sake jin komai hakan ma
ya isa, Allah ya kawo komai cikin sauki, ba zata kuma bata lokaci a abinda ya riga ya wuce ba,
shi dama sharri dan aike ne, duk in da yaje sai ya dawo.
   Sauri-sauri yake ya isa gida a tunanin sa Iman chan tayi, ya matso yaji yadda akayi ta
samu evidence din, a lokacin da ya riga ya cire rai, tsaida shi Laila tayi, ya tsaya yana juyowa,

"Ni ka wulakanta ko cap..."

Ai bata kai karshen maganar ta ba, ya dauke ta da wani gigitaccen mari, marin da ya dauke
mata ji da gani na wani lokaci

"Ni ka mara?"

"Shine kawai abinda nake ganin zan miki na huce, duk da addinin musulunci ya hane mu da
dukan mace, musamman ma a fuska, amma bani da zabi, nayi duk kokarin da zanyi nayi
avoiding dinki, amma saboda ke jaka ce sai da kika saka ni aikata abinda nake gudu, idan kika
cigaba da shiga rayuwata ko? Wallahi sai na miki abinda baki taba tunani ba."
Hannun ta dafe da fuskar ta, ta kasa cewa komai har ya juya da nufin barin wajen, cikin daga
murya yadda zai ji tace

"Sai dai idan kashe ni zakayi, amma nayi maka alkawarin sai ka aure ni, ko kana so ko baka
so!"

Be tsaya ba, dan bashi da lokacin batawa, yana kyautata zaton Laila ta haukace, ko kuma tana
shaye-shayen kayan maye, idan ya biye ta zai iya mata illa, dan yadda yake ji kamar ya saka
hannu ya shake mata wuya har sai ta bar numfashi.

  Sababbin masu kula da kofar ya tarar, suka gaishe shi ya amsa musu da kai, har ya wuce ya
dawo ya nuna su da yatsa

"Idan har na samu wani abu daga gareku, wallahi tallahi sai kun yabawa aya zakinta."

Ya wuce su yana juyo su suna bashi hakuri da alkawarin ba zasuyi komai ba, kofar ya buga da
karfi, ba zai cigaba da zama a cikin gidan nan ba, idan ma ya zauna toh fa ba zai iya da tsarin
su ba, tafiyar sa zai wata k'asar ya huta sosai, ko da zai dawo amma sai ya tabbatar da ya
samu enough time da matar shi, ba zai yiwu wasu banzaye su nemi hana shi morewa ba,daga
yin auren sa.
  Abincin dake saman dinning ya kalla, ya wuce ya hau bubuda dakunan yana neman ta, bata
cikin ko daya, ya dudduba toilets nan ma bata nan, ya zata nan zata wuto be yi tunanin Ammi
zata bi ba.
  Dawowa yayi falon ya kwanta rigingine ya rage volume din tv ya rufe idon sa. Bacci ne ya
soma daukar sa, yaji kamar ana taba shi, bud'e idon yayi ya ganta a tsaye a wajen kafar sa,
kallon kayan jikinta yayi daga sama har kasa, doguwar rigar material ce me budadden hannu,
sai kanta dake rufe da inner cap, murmushi tayi masa ya mayar mata yana mika mata hannu ta
daga shi, make kafada tayi alamun a ah, ya sake mika mata ta noke, marairaice mata yayi yana
sake mika mata hannun, karba tayi da nufin dagashi amma sai ya saka karfi ya jawo ta, ta fado
kansa ya saka hannu ya zagayeta a jikinsa.

"Dama na san haka zakayi, shiyasa naki."

"Toh laifi nayi? Mutum da iyalin sa halaliyar sa."

"Zuhr ake kira toh ai."

"Don't tell me azahar tayi."

"Tayi, har ma nayi sallah ta."

"Ohh... Ya Salam rayuwar nan tana gudu."

"Wallahi, tashi toh kayi sallah." Tace tana kokarin daga shi, maida ita yayi yace

"Zan tashi, amma sai kin min tausa, I'm weak kwana biyu ban fita exercise ba."

Gefen kadarsa ta danna masa, zuwa saman chest dinshi

"Gashi nan na gama."

"Ojoro, wannan ai ba tausa bane, danna ne."

Dariya ta saka

"Menene banbancin?"

"Tausa daban danna daban, ji fa yadda kika danna min kafada kamar wani katako."

Dariya ta kwashe da ita sosai, irin wacce be taba ganin tayi ba, tsayawa yayi yana kallon ta
yana admiring dinta, komai idan tayi burgeshi yake sosai, sai da ta lafa sannan ta ga irin kallon
da yake mata sai kuma taji kunya, ta dora fuskar ta a saman kirjinshi tana dannawa.

"Sarkin kunya." Ya mike yana dagata, zama sukayi akan kujerar ya rik'e hannun ta cikin nashi

"Thank you so much, kin taimaki mijinki a lokacin da yake cikin tsananin bukatar taimako, dama
mace ta gari itace me taimakon mijinta idan ya shiga matsala, I'm very proud of you, bari nayi
sallah nazo ki bani labarin yadda akayi, I hope baki saka kanki a matsala ba ko?"

Girgiza masa kai tayi

" Ko daya, kayi sallah ga abinci na shirya mana da kaina"

"Really? Kece kika girka?"

" Nice." Tayi folding hannunwanta a kirjinta tana murmushi

"well-done, hakan yayi min dadi, bari na zo naci girkin amarya ta."

Dariya tayi ya shige ciki ita kuma ta zauna tana jin dadi sosai.

***Cikin dare ya tashi, ya kalli Hajiya Layuza dake shirge kamar kayan wanki, bayan ta hanashi
sakat da zalamar sa ya samu ya bata maganin bacci shine tayi bacci, sadaf-sadaf ya sulale ya
fice yana kallon hanya sai dakin da Zeenat take. Tura kofar yayi yaji ta a rufe, ya shiga
kwankwasawa a hankali kamar barawo, cikin baccin wahala Zeenat din ta farka taji kamar ana
taba kofar, tsoro ne ya kamata ta, ta makale a wajen daya tana zaro ido,

" Zeenat kina ji? Bashir ne dan Allah bud'e min. "

" Ba.. bazan bude ba." Tace tana sake makalewa a jikin ginin dakin

" Dan Allah ki cece ni, ki bud'e muyi magana akan tafiyar ki gida, na samo hanyar da zaki koma

gida cikin ruwan sanyi, dama naji an ce an janye yajin aikin da jami'oi suke, bud'e kiji."

" Da gaske kake? "

" Da gaske nake, bud'e dan Allah kafin ta gane bana nan ta biyo ni tazo ta tafi dani. "

Tashi tayi ta bud'e kofar, tana gama budewa ya fado daga shi sai gajeren wando, wani iri taji tayi
saurin dauke kanta, kamar wanda yasha wani abu kawai taga mutum yayo kanta, ya dakume ta
yana kokarin rabata da kayan jikin ta, dukan sa ta shiga yi amma kamar ingiza shi take, toshe
mata baki yayi sosai ta hanyar saka abu ya daure bakin yadda ihun da zatayi ba zai fito ba. Duk
yadda tayi kokarin ganin ta hana shi amma sam be hanu ba, sai da ya karbi sadakin sa, ya
kyaleta yana maida numfashi, kamar wanda yayi tsere da zaki. Bayan kamar minti goma ya
tashi da sauri ya fice daga dakin ba tare da ya kalli in da take ba.
   Tun tana kuka har ta daina ta galabaita sosai, ko hannun ta bata iya dagawa balle tayi wani
kwakkwaran motsi ko ina na jikinta ciwo yake balle uwa uba chan kasanta da take jin kamar
zata mutu dan tsabar azabar da take ji

_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)  s_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107
2/2/22, 18:35 - Buhainat: Halin Girma
      26

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇�_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇�_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇�_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_con
tent=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator
=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLo
SKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇�_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

******* �

Sai da ya gama komai sannan ya biyo ta dakin ya yaye abinda ta rufan yana shigewa jikinta
"Kinyi bacci?" Yace yana leka ta kin motsi tayi a dole tayi bacci, fuskar sa ya matsar jikin ta ta,
ya taba saman idon ta, motsi yaji idon nayi yayi dariya yana cewa

"Stop pretending ki tashi, nasan ba bacci kike ba."

"Uhum..."

"Yawwa, hira zamuyi, zaki iya tambaya ta koma menene akai na, zan sanar dake."

_"Farko  dai sunana Muhammad Ahmad Santuraki, kamar yadda kika gani, mahaifi na shine
sarkin Adamawa, sannan Mahaifin Ammi shine sarkin Kano, na taso tsakanin Kano da

adamawa in da zama na yafi yawa a Kano saboda yadda Maimartaba ya kwallafa rai a akai na.
Nayi karatu na both na addini dana boko har na kai matakin captain a yanzu a bangaren aikin
soja. Ni kadai Ammi da Bubu suka haifa,bani ne dansu na farko ba, kuma bani ne na karshe ba
amma ni kadai ne Allah ya raya musu. Aji shine Mahaifin Bubu da sauran yan uwansa su hudu,
shine na biyu akwai babban wansa wanda Allah yayi masa rasuwa, shine Mahaifin Laila da
Kamal, bayan rasuwar sa ne Bubu ya auri matar wan nasa wadda ake kira da Kilishi,a lokacin
kuma rikon su ya dawo hannun Bubu tunda dama chan gida daya muke baki daya. Daga nan
ne kuma Aji ya sauka ya nada Bubu domin ya huta shima. Tun farkon dawowar Kilishi gidan
mu, daidai da sakan daya bata taba kauna ta ba, infact idan za'a bata wuka ace wa zata kashe
toh tabbas ni zata kashe, bata kaunata ko kad'an duk akan sarautar da take ganin Kamal dinta
ne yafi dacewa ya karbi kujerar tunda Mahaifin su shine gaba da Bubu. Tun da na taso bani da
ra'ayin sarauta ko kad'an, mutane da yawa na min kallon wanda be san abinda yake ba,.
abubuwa da yawa sun faru wanda ni kadai na san su, wanda suka kara taimakawa sosai wajen
ganin ban karbi tayin bubu ba, tsawon lokaci ya dauka yana bibiyata da maganar amma sam
ban taba nuna masa zan iya ba, illa iyaka sai ma na nisanta kaina da duk wani abu da ya shafi
gidan da sarautar baki daya. Wannan dalilin shine ya saka ni zama lafiya har wannan lokacin.
Akwai abubuwa da yawa na ban mamaki a gida irin na sarauta, wanda sai wanda yake cikin ta
ne kawai zai iya ganewa, babban kalubale shine tsantsar makirci da nake kyautata zaton dashi
ake haifar da yawa yawan yayan sarauta. Amma duk da haka akwai mutane na gari a ciki
wanda basu da matsala ko kad'an sai abinda ba za'a rasa ba."

Shiru yayi kamar me nazari, kafin daga bisani yace

" Laila ta jima tana so na, tun bayan da ta taso ta san menene soyayya ta kwallafa rai akaina,
sai dai nayi ma kaina alkawarin ba zan auri jinin saurata ba, sannan ba zan iya auren mace me
irin halin Laila na rashin sanin darajar hatta mahaifiyar da ta kawo ta duniya, a sangarce ta tashi
ganin duk wani abu na duniya ta same shi, kyau kudi mulki sannan uwa uba gata, sai ya zama
na bata san komai ba sai kanta, bata son talaka da duk wani da zai rabe ta, she's very selfish,
mutum ce ita da zata iya komai dan ganin ta samu muradin ranta. Mafiya yawan lokuta takan
aika min da sakonni, na kyaututtuka ko wani abu, amma ban taba nuna na gane me take nufi
ba, har tazo ta tarkata ta bar k'asar don karatun ta na Masters, hakan ya saka ni samun sauki,
sai gashi ta dawo a lokacin da maganar auren na ta kai mata, bansan da wanne shiri ta dawo
ba, amma nasan ba zata hakura ba."

" Humm..."

Taja numfashi tana jin shi, kanta a saman chest dinshi yana wasa da gashin kanta, dagota yayi,
suka kalli juna,

"Nayi alkawari zan kula dake da dukkan karfina, gatan da kika rasa zaki same shi yanzu har sai
kin ce na gaji Muhammad dina."

Ya karashe cikin kwaikwayon muryarta, dariya tayi tana dora fuskar ta a saman tasa.

"Baka fad'a min dalilin da ya saka ka boye identity dinka ba."

"Saboda step mom dinki ne, na samu labarin komai ta wajen Sadeeq abokin yayanki Habib,
shiyasa na zo a haka dan na tabbata ba zata taba hutawa ba har sai ta tabbatar da auren mu,
wanda na tabbata da nazo a ainihin identity dina da ba lallai ta bari ba."

" Haka ne." Tace a sanyaye cikin son kauda tunanin Maman da zaman da sukayi.

" Na tambaye ki..."

" Ummm." Ta daga mishi Kai

" Did you love me?"

Da sauri ta kalle shi

" I'm serious, inaso na sani, ko tausayi na baki kika taimaka min kika aure ni!"

" Inji wa?"

" In jini, haka nake gani, tunda ni banga wata alama ba, baki taba furta min ba, ni kadai nake
kida na nake rawata."

Sauka tayi daga jikin shi, ta kwanta tana juya bayanta.

" Ni dai goodnight bacci yazo."

Da sauri ya jiyota

" Ai baki isa ba, sai kin fad'a min."

Sake juyawa tayi tana jan duvet ta rufe kanta, ya shiga ja tana ja, ganin zata bashi wahala ya
saka shi dagata gaba daya, ya mike da ita a jikin shi zuwa doguwar sofa din dake chan gefe a
dakin, zaunar da ita yayi akan cinyar sa ya warware duvet din daga jikin ta, yunkurawa tayi zata
gudu ya riko waist dinta ya dawo da ita.
"Sai kin fad'a min, ko kuma na miki irin abun jiya."

"Na shiga uku."

Danne dariyar sa yayi ganin yadda ta firgice

"Allah kuwa da gaske, tell me you love me or else..." Ya rad'a mata a kunne

"Me zance toh?"

"Abinda nayi ta ce miki, I love you Zahraah, Iman, Fatima, Baby, sweetheart duk dai."

"Ni dai... Ni bansan me.zance na."

"Kice I love you baby, ki hada da hot kiss a nan." Ya turo bakin sa gaba, hannun ta tasa akan
bakin ya dan cije ta, tayi saurin janye hannun ya maida shi baya.

"Oya ina jinki, say it, inaso naji muryar ki tana fad'a "

Shiru tayi kunya na kamata, kunyar sa take ji sosai ta yaya zata fara furta masa wani I love you
right in front of him, ai da kunya tunda ba sabawa tayi ba, gashi har da wani hot kiss shi ko
kunyar nan ma babu. Rufe idonsa yayi ya sake turo mata fuskar tasa

" I'm all ears."

Minti kad'an yaji shiru ya bud'e idon, lokacin har sun sauya zuwa wani abu daban, saurin dauke
kanta tayi tana turo baki. Kamar daga sama taji hannun sa a cikin rigarta, ta juyo da sauri tana
rik'e hannun

" Dan Allah tsaya zan fada, wallahi zan fad'a."

" Oya ina ji, don't waste my time."

" I lo...ve... You." Tace a rarrabe

" Ban yarda ba, ki fad'a kai tsaye daga chan k'asan zuciyar ki, in a romantic way., Kice I love
you Muhammad. "

" I love you Muhammad. "

Tace da sauri kamar wadda tayi gudu ko tsere.  Murmushi yayi mata ganin yadda ta fitar da
maganar, yana son komai nata, har kunyar ma, ya san in dai suna tare toh har wanka ma sai ta
yi masa wataran, zai koya mata komai, yadda yasan yana so rayuwar auren su ta kasance.
  Zaka rantse wani babban laifin ta aikata ganin yadda take jujjuyar da fuskar ta gefe, zaunar
da ita yayi ya fita, tashi tayi da sauri ta haye gadon ta kwanta, shigowa yayi dauke da cups akan
tray da vacuum flasks dake dauke da black tea, dorawa yayi akan table ya zuba ya mika mata,
sannan ya zauna a gaban table din ya shiga kurbar nasa da zafin sa. First time na shan black
tea dinta kenan amma sai taji yayi mata dadi sosai, sai dai bata shanye ba ta ajiye a gefen nasa
ta dawo ta sake zama, sai kuma ta tashi ta nufi toilet din ta daurayo bakin ta, ta fito ta haye

gadon ta kwanta. Kallon ta yake har ta gama ta rufe idon ta, sai da ya gama shan tea din tas, ya
wanko bakin sa sannan ya kashe hasken dakin ya barshi k'asa k'asa, ya kwanta rigingine yana
kallon sama, yana tunanin yadda zai bulowa al'amarin Lailah don baya son a samu matsala,
gashi har lokacin bashi da wata hujja da zai kare kansa. Ganin zai cigaba da bata lokaci wajen
tunanin abinda bashi da iko akai yaga gwanda kawai yayi abinda zai karu ya kuma samu
dumbin lada, duk da yasan duk gudun sa take amma ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login