Showing 96001 words to 99000 words out of 124388 words
"Ka kula sosai dan Allah, idan har lokacin da ya kamata yayi, ban dawo ba zan fada maka sai
ka damka su a hannun Aji! Dan Allah kar kayi kuskure, ka kula sosai, kai kadai na yarda dakai
da wannan amanar."
"In Sha Allah." Yace yana rik'e envelope din sosai.
  Ciki ya koma, ya barshi a wajen ya tarar ta gama hada masa jakar sa waje daya, tana
gaban jakar ta zabga tagumi har ga Allah bata son tafiyar tasa, amma kuma dole zata hakura
saukin ta daya fitar da zatayi school, ga ma'aikata birjik an kara karo wasu ma, gate din ma
kuma cike yake da jami'an tsaro da ba dan haka ba, ba zata iya zama a wannan tafkeken gidan
ba.
  Tashi tayi ganin ya shigo,ya kalle ta ya kalli jakar sai kawai ya rungume ta
"Zanyi missing dinki sosai, take care of yourself for me dan Allah, idan kina bukatar wani abu,
reach out to me, idan baki sameni ba, Musaddik yana nan, nayi miki saving number dinshi kema
zan bashi naki."
" Ai babu ma abinda zan nema, akwai komai."
"In case dai."
" Owk tam, nagode. "
" Yawwa, muje ki rakani. " Ya rik'e hannun ta suka fito har wajen mota, ta tsaya daga gefe bayan
ya shiga ya zauna, yayi mata murmushin karfafa guiwa itama ta maida masa zuciyar ta na
rauni, daga mata hannu yayi har suka fice daga gidan gaba daya.
***Abinda ya faru lokacin da Bashir yazo daukar Zeenat bayan tafiyar Iman, suna barin kofar
gidan yana zuwa, adaidaita sahu yazo dan ya maida machine din wa maishi, aikawa yayi a
kirata, dan babu waya a hannun ta, Mama na jin sakon kiran ta zira mayafi taje wa Zeenat din
tana zuwa, ta je ta same shi a tsaye yana jira ta fito suna magana da me napep din. Be yi
mamakin ganin Maman ba, dan dama yasan ba za'a yi komai ta sauki ba, gaishe ta yayi taki
amsawa, sai ma cewa da tayi tana bud'e hannun ta
"Bani takardar yata."
"Ban gane ba Mama?"
"Eh ina nufin ka sauwake mata kaddareren auren ka dan ba zata koma ba ku karasa kashe ta
kai da tsohuwar matar ka."
" Amma Mama Zeenat tana so na, nima Ina son ta, kiyi hakuri dai ta fito mu tafi."
"Wanne so? Bayan yaudarar da kayi har kana tunanin tana son ka?"
"Toh ni dai nasan auren soyayya mukayi da ita, kiyi hakuri ki bimu da addu'a kawai."
"Ba zan hakurin ba, Malam takardar 'yata kawai nake so ba dogon surutu ba."
"Ba zan iya sakin ta ba gaskiya, kiyi hakuri kawai."
Sai ya juya ya haye napep din,da sauri ta bishi tana kiran sa, me napep yaja suka bar kofar
gidan. Tana juyowa da nufin komawa gida sai ga Abba a tsaye a bayanta, ya harde hannayen
sa yana kallon ta ransa a matukar bace, bacin rai da be taba yin irin sa ba tun da aka fara
hayaniyar auren Zeenatun, tsoro ne ya shige ta, dan yadda taga bacin rai a fuskar sa zai iya
aikata komai.
"Dan Girman Allah..."
Daga mata hannu yayi
"Babu abinda zaki ce min, bana son naji komai!
Jikin ta ne ya hau rawa, yayi ciki ta bishi tana son yi masa bayani, ba zai tsaya jin komai ba, ba
kuma zai dauki maganar da sauki ba wannan karon, tayi abinda ba zai mata uzuri ba. A zafafe
ya shiga falon yana k'wala kiran zeenatu, ta tashi jikin ta na rawa har tana yar da dan kwalin
kanta da yake hannun ta,
"Me kike yi har yanzu baki tafi ba."
"Uhm.. uhm.. dama..."
"Karya kike yi, munafuka!"
"Minti biyar kachal na baki, ki fice ki koma gidan mijin ki, na fad'a miki!"
Be jira ya sake jin ta bakin ta ba, ba kuma zai saurari magiyar da Mama take masa akan dalilin
da ya saka tayi abinda tayi ba, yayi gaba kawai ya shige dakin sa ya rufo.
  Kuka Zeenat ta fashe dashi, da gaske bata son komawa gidan Bashir, ya zatayi yanzu?
Gashi taga wani irin fushi a fuskar Abban da bata taba gani ba,dama mama so tayi bayan ta
kori Bashir din idan Abban yazo tace shi Bashir din ne yace Zeenat din ta zauna a gida zai yi
tafiya ya dawo, daga nan sai suyi ta matsa mata har ya sake ta, shikenan Abban ba zai zargi
komai ba, amma sai gashi komai ya lalace tun ba'a kai ko ina ba.
"Kina da number Bashir ko?"
Girgiza kai tayi
"Dan ubanki baki haddace number sa ba? Yanzu ya kike so muyi? Dole ya dawo ya dauki ki ku
tafi kafin nasan abinda zanyi akai."
"Mama ni ba zan koma ba."
"Aikuwa sai kin koma, baki ga fuskar babanku ba? So kike yace na tafi gida shikenan ki rasa
wanda zai tsaya miki? Tashi maza ki kira bashir ga wyata kice ya dawo, idan yaso sai mu san
abinda zamuyi."
Kuka ta cigaba da rerawa a hankali, ta karbi wayar ta saka number tasa ta kira, tayi ta ringing
amma be daga ba, ta cigaba da jera masa kira amma babu alamun zai dauka. Rasa yadda
zasuyi sukayi, har goma saura gashi bata san gidan ba balle idan tafiya zatayi da kanta ta gane.
Suna nan a falon ya fito, ya kalle su sannan ya fice gaba daya.
***Bayan tafiyar sa sai taji gidan yayi mata girma da fadi, ta kwanta a saman kujerar falon tayi
lamo tana jin cikin ta na juyawa sama-sama. Bacci ne ya dauke ta a wajen bata tashi farkawa
ba sai da rana tayi. Sallah ta fara yi taci abinci sannan ta zauna ta dauko littafan ta na islamiya
ta shiga duba su, tana muraji'ar na baya, tana so ta cigaba da karatun ta ko ita da kanta ne ta
dinga karawa kanta, zatayi amfani da damar duk da sun koma boko amma ba zata kyale na
islamiyya ba, akwai wasu littattafi da take son koya wanda dole sai dai ta samu manyan
malamai su koya mata, amma bata san yadda zatayi ba. Tana nan zaune yayi mata text
message, tayi masa reply sannan ta cigaba da abinda take har zuwa la'asar, gaba daya sai taji
ta rasa ma me zatayi, sai kawai ta zagaya baya wajen ma'aikatan gidan ta same su suna hira,
suka tashi da sauri suna tambayar ta abinda take so, murmushi kawai cike da mamakin yadda
suke girmama ta take ta zauna a wata kujerar roba, tace zuwa tayi zaman cikin ya ishe ta, nan
fa suka hau murna suka cigaba da hirar tana sauraren su, a kalla sun debe mata kewa dan bata
dawo ciki ba sai bayan da aka kira sallar magriba.
  Washegari ta tashi da murnar zuwa school bayan tsawon lokacin da sukayi a gida, jin ta
take tamkar sabuwar shiga dan wasu abubuwan ma ta mance su, tasan da yawa duk yau zasu
koma saboda dai kowa ya gaji da zaman gidan. A tsanake ta shirya tsaf, sannan tasaka
madaidaicin mayafi akan doguwar rigar atamfar da ta saka brown da touches din blue, ta dauki
jaka da takalmi da suka shiga sosai ta saka, tayi shigarta ta mutunci ta fito ta nufi kitchen in da
ta hanyar ne ake bi zuwa bq, a kitchen ta tarar da Ummimi, tana karasa hada breakfast dinta, ta
russuna har k'asa ta gaishe ta, ta amsa a sake tana dudduba aikin.
"Zan je school ba jimawa zan ba, idan an gama komai sai a jera a dining, zanyi bakuwa anjima
da rana."
"Allah ya dawo dake lafiya gimbiya, idan kina bukatar abu ba sai kin zo ba, kira kawai zakiyi
ranki ya dade."
"Babu komai karki damu."
"A dawo lafiya, Allah ya bada sa'a."
"Amin."
Tace ta juya ta fita, ta samu driver ya gyara motar, sai kawai ta fad'a baya tana tuna rayuwa
yadda take a shekarun baya, shekarun da basu gaza biyu ba. Tun da suka isa makarantar duk
in da suka wuce sai an kalle su, a department dinsu kuwa kamar an ga nama ko wata sabuwar
halitta, dama labari ya riga ya karad'e ko ina amma dama ance gani ya kori ji, wasu takanas
suke zuwa su tabbatar da gaskiyar abinda suka ji. Tayi ta zuba ido ko zata ga Zeenat amma ko
me kama da ita bata gani ba, har suka gama abinda zasuyi suka koma gida.
  Tun daga ranar kullum sai taje school din ta dawo, sai zaman gidan ya zama mata kad'an,
duk dare kuma suke shafewa suna magana da shi a waya, ba wani sosai take jin kadai ta ba,
sannan kuma duk sanda take free da rana ko ta dawo da wuri tana zama ta koya wa masu aikin
karantun al'qurani da ta lura kusan rabin su basu iya ba, kawai rayuwar su sun taso ne akan
hidimtawa gidan sarautar, tun iyaye da kakanni suke a haka har zuwa yanzu babu wani sauyi
da ya samu rayuwar su. Hakan ba karamin dadi yake mata ba, a kalla ita ma zata samu lada
me dinbin yawa.
  Wasa wasa sai gashi yayi sati uku cif da tafiya, duk sanda ta tambaye shi yaushe zai dawo
sai yace mata surprise zai mata kawai, haka take hakura ta kyale shi, kullum cikin shiri take dan
tasan zai iya zuwa mata bakatatan, wasu magunguna da momma ta bata wanda yawancin su
na fruits ne da madara su take ta faman sha, dan sosai suke mata dadi har ta kanyi mamakin
kanta a lokacin da Mamman ta bata , bata wani ji dadin su kamar yanzu ba.
  Wata rana a cikin ranakun da take zuwa school ta kai yamma, ta tashi duk jikin ta babu
dadi, ciwo take amma bata san takamainai me yake mata ciwo ba, kamar kar taje school din
amma sai ta daure dai, ta shirya ta kira Ummimi ta rakata, tunda dama sai da yace lallai ta
dinga tafiya da masu rakata amma bata tafiya dasu. Tare suka tafi yau haka nan taji bata son
tafiya ita kadai, suka jirata tayi lecture ta fito wajen biyar na yamma, a gajiye likis gashi ko ruwa
bata saka ma cikin ta ba, kaidar tace bata cin abu a school tun da ma, sai dai idan zata dade
irin haka taci ko snacks ne shima ba ko yaushe ba, dan mafiya yawancin lokuta rage kudin da
Abba yake bata Mama take ta bata kadan, shiyasa ta koyi yadda zata yi karatun haka,sai kawai
ya zame mata jiki ko yanzu da take da komai bata damu taci din ba
  Da sauri Ummimi ta karbi Jakarta da kayan hannun ta, ta tayata bud'e mata motar ta zauna
sannan ta zagaya ta shiga bangaren ta, bata lura da su biyu ne a gaba ba, har da wani sai da
ya gaishe ta
"Amarya barka da rana."
"Barka dai, ai ban ma lura ba, ina wuni?"
"Lafiya lou wallahi, dama wannan gajiya da kuka kwaso, dama munyi waya dashi ne yace na
biyo ta makarantar taku sai mu wuce, zasu sauka da karfi shida da rabi, sai mu dauko shi a
airport, amma fa yace kar na fad'a miki dan wai so yake yayi surprising dinki."
Dariya ta saka
"Lallai, ina ta tambayar sa yaushe zai dawo yaki fad'a min, so yayi kawai yanzu ma sai dai na
ganshi kenan."
" Ai irin wai surprise din masoya."
Dariya kawai tayi, bata kawo komai a ranta ba, ganin Musaddik ne, haka kuma sai taji wani
yanayi na dokin ganin mijinta, wanda yau ya cika sati uku da kwana biyar cif da tafiya. Hanyar
airport din suka dauka, ta kwantar da kanta a bayan da yake saramata sosai.
**A word of encouragement to All TTC mother's (Trying to conceive) do not lose hope, Allah
yana tare daku, ku cigaba da addu'a, Allah ya baku 'yaya masu albarka da mu baki daya. Baa
debe tsammani daga rahmar Allah.
_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D'aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
2/17/22, 09:45 - Buhainat: Halin Girma
36
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇�_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇�_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇�_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_con
tent=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator
=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLo
SKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇�_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
*******�
Cikin wani yanayi taji kamar bacci yana fuzgarta, ta sake gyarawa sosai Ummimi ta matsa mata
sosai ta kwanta a bayan, nan take kuwa bacci ya dauke ta. A tunanin Ummimi tsabar gajiya da
wahala ce ta saka ta baccin, dan tun safe suka fito kuma tana lura bata saka komai a cikin ta ba
sai ruwa, ita dai ta bata kudi taje cafeteria ta siya abinci taci, amma ita kuwa bata ci komai ba,
dole ne ko ba karatu kake ba, ka jigata balle. Tausayin ta taji, musamman da ta gama fuskantar
halin kirkin da, bama ita kadai ba duk ma'aikatan gidan na murna da samun ta a matsayin
uwargijiyar su, babu hantara balle tsangwama, gaba dayan su son ta suke da gaske.
  Tafiya suke tayi babu alamun zasu tsaya, har duhu ya fara mamaye sararin samaniya,
kallon ta Ummimi tayi taga har lokacin bacci take da gaske, shiru kake ji a motar babu wanda
yake magana a cikin su, a tunanin da za'a samu ko yar karamar hira ce tsakanin driver da na
gaban amma babu wani wanda yayi magana a ciki, jakar dake kusa da Iman din ce ta fadi kasa,
Ummimi ta sunkuya da nufin dauka, abinda ta hango a hannun shi ya saka hantar cikin ta
kadawa, a firgice ta dago tana dunkule jakar a hannun ta, juyowa yayi ya dube ta, ya sake dago
mata hannun nasa da kyau dan ta gani sosai, bindigar ce kuwa, tsoro ne ya kamata,
"Idan kika sake kika bud'e bakin ki a wajen nan, sai na fasa kanki da alburushi."
Da sauri ta rufe bakin ta da hannun ta, juyawa yayi kan driver yace
" Idan ka kai karshen titin zaka gangara haggu."
Da ka ya amsa, daga gani a tsoroce yake, rashin sani ya hanasu ganewa tun shigowar su
motar. Kallon Iman take ganin da gaske bacci take, bacci me nauyi da ya hanata jin duk abinda
ya faru, mamaki ne ya kama Ummimi, dama ta saba irin bacci haka ko kuma dai akwai matsala,
da sauri ta dan taba ta, sai taga ta motsa kad'an tamma kuma bata tashi ba, ajiyar zuciya ta
sauke, hawayen da take ta makale shi ya gangaro zuwa fuskarta, me yasa mutane suka lalace
haka? Labarin da suke ji a gidan radio yau shine ya faru dasu? Idan har masu sarauta da masu
hannu da shuni basu da tsaro toh waye kai kuwa talaka? Anya rayuwar zata tafi a haka?
  Cikin tsananin fargaba take har suka karaso wani gida, karami a cikin gungurmin jeji, babu
gida gaba babu baya, ba zaka taba tunanin halitta irin ta mutum zata rayu a wajen ba, tana jin
yadda suka dinga shiga kan tudu da kwari alamun sam hanyar bata mota bace, ko tace mota
bata taba bi ba. Murfin motar ya bud'e yana nunawa driver bindiga, suka fito a tare ya zagayo
wajen sa ya rik'e kugunsa. Fito yayi da bakin sa, sai ga wasu kartin maza su biyu sun fito, tare
da wata mace a bayan su, tafawa sukayi da daya daga ciki sannan yace
"Kayi babban aiki, aikin da zai firgita ilahirin k'asar har ma da ketare, tana ina?"
Bayan motar ya nuna masa, ya tafi zuwa wajen ya bud'e yana leka ciki
"Baccin ne be sake ta ba har yanzu?"
"Eh!"
"Tasha ruwan kenan!" Yayi murmushi yana rufe kofar
"Tasha sanda ta shigo motar."
"Kayi kokari sosai... Kudos!"
"Thank you sir."
"This is a shame to the Nigerian Armies, The royalties, government, gaba daya ma, duk sunyi
failing, ta yaya kake tunanin mutane zasu sake yarda dasu? Bayan sun damka hakkin kulawa
rayuwar su garesu, sai ya zama sun k'asa tsare kan su?"
Sai ya kwashe da dariya
" Yaron nan a bayan mu yazo, yaron nan ta dalilin sa na rasa komai, ciki harda aikin da na
kwallafa rai, saboda shine shafaffai da mai? Saboda shi din dan gata ne, shiyasa aka fifita shi
akan kowannen mu, me yafi mu? Mulki?"
"Oga!"
" Haka ne mana!" Ya fad'a da karfi
"Haka ne. Kullum cikin favoring dinsa ake, kullum cikin yabon sa ake, na kai mataki Babba
amma yaron nan, ta dalilin sa komai ya baci, ya kake tunanin zan iya hakura?"
"Kunsan shekarun da na dauka ina gina rayuwata har na kawo wannan lokacin?"
"A ah." Suka girgiza kai dukka
" Shekara goma sha daya, amma cikin sakan da be wuce goma ba, ya kwace komai, khaki na,
rank dina, mutunci na a idon duniya, na muzanta, na zama abin gudu da k'yama."
Duk sun yi shiru kowa na sauraren sa, shirun shima yayi dan bashi da abin fad'a kuma
" Ku shigar dasu ciki, idan princess ta tashi a fad'a min."
Sai ya juya ciki ransa fari tas, ya tabbatar saura kiris bomb ya tashi, bomb din da zai tarwatsa
duk wani farin cikin Muhammad Ahmad Santuraki da duk wani makusancin sa, shekara biyar
kenan yana bibiyar sa, ya kuma samu nasarar samun duk abinda ya samu a yanzu, wanda
yake