Showing 90001 words to 93000 words out of 163149 words
inna meramu shiru bata dawo ba''
''eh.....wata qila itama baccin yayi awon gaba da ita ne,ai yau kam ta aikatu itama,meramu babu son jiki,harvta fiki son aiki''innan ta fada cikin halin ko in kula don bata kawo komai cikin ranta ba
''amma inna bacci da wuri haka,qarfe tara da rabi fa,yanzu ma wasu suke fita dandali''
''yo su mutan birni barci da wuri a gunau wani abu neοΌ,rayuwa suke gida a qulle,daga sallar isha idan suka shige gidajensu suka kulle sai kuma washegari''
''q'nn,bari na tashi nima na tafi''
''da wuri hakaοΌ''inna wuro ta fada tana binta da kallo
''eh''ta bata amsa gana zira sudaddun silifas dinta
''to kinga ga abincin nan kokus yake kome neοΌ,tafi da shi gida kwaci''duk yadda take kwadayin couse couse rin sanda ake dafashi take fata ya shigo farantinta amma a yanzu sai taji duk ya sure mata,a salube ta dauki kwanon tana fadin
''an gode sai da safe''
''Allah ya bamu alkahairi''inji inna wuron
bata haqura ba sai da ta je bakin qofar dakin tace
''abdullahi da meramu sai da safe''sau uku tana maimaitawa taji shiru,abdallah na jinta amma maryam batasan ma me ake ba don ta jima cikin daddadar duniyar barci ta musamman.
inna wuro ta dubeta
''na gaya miki sunyi bacci,kije kwa hadu da safen,ki gaida su hansai''jiki ba qwari ta fice daga gidan
ko a gida tana kallo qannanta na damben cin couse couse couse din amma ta kasa ci sai ido kawai data zuba musu tana kallonsu,sau uku babarta iya hansai na mata tayin taci bakinta cike da shi taqi cewa komai,qarshe ma tashi tayi ta shige dan takurarren dakinta wanda zakayi tsammanin duk ranar da aka samu ruwan sama mai yawa zai iya ruftowa mazauna ciki.
kasa bacci tayi,yau kam ta kai maqura,jin son Abdallan take kamar ta mutu kota haukace,ita kam ko a haka ma zata iya aurenshi,amma idan ta dubeshi ta dubi kanta sai jinta yayi sanyi qalau,tasan wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa,duk da batasan waye ainihin abdallah ba,amma kallo daya da ta masa ta san cewa ba qaramin mutum bane shi da maryam din ma baki daya
tunanin da ya isheta qarshe kuka ta fashe da shi a haka bacci yayi awon gaba da ita tana Allah Allah gari ya waye ta koma gidan inna wuro.
ππππππ
Kamar yadda suka amida shi al'adarsu bayan sallar la'asar su zauna hira har salllar magariba wani lokaci har isha'a yanzu ma hakane.
yana zaune kan whell chair wanda yau ita da mustafa suka dorashi don ya dawo daga gona da wuri,ta karbi dan qaramin alqur'anin da ya gama karatu da ahi daga hannunshi ta ajjiyeshi a muhallinsa,ta dauko roban da take ajjiye duwan ganyan magaryar,wanda ta karanta a yoyin dake cikin surutul A'araf aya ta 117 zuwa ta 122
sai ta cikin suratul yunus aya ta 79 zuwa ta 81
sai cikin suratu Daha aya ta 65 zuwa ta 70
ayatul kursiyyu falaq da nasi da iklas duka,tana shirin tsiyayowa taji sallamar mero wadda ta fita dazun tace zata je tayi wanka,idan da savbo maryam ta saba,da safe zata zo da kwalliyarta,idan ta gama wuninta qarfe uku zata koma gida ta sake wanka da kwalliyarsu irin ta mutan qauye.
a cup ta tsiyayo ta miqo masa,sai ya dan bata rai,saboda dandanon magaryar da baiso,itama kicin kicin tayi,musamman da ta jiyo tana tambayar inna wuro ina suke basu fito ba,tasan kadan daga aikinta ta fado musu,taji dadi da inna wuron ta ce mata
''zauna anan ki tsinke zogalen nan kada meramu ta fito ta hau aikin,sonke kwana biyu naga gun hira kika fi kauri,duka kin sakar mata ragamar aikin,kullum ita ke ruwon dare ta barki da lugudar lebe''.
Dariya ta bashi cikin ranshi ganin yadda tayi wani kicin kicin
''lallai ma yarinya,wuyanki ya isa yanka,ni zaki wani budewa ido kamar qaninki,Allah ya bani lafiya zaki gane shayi ruwa ne''hakanan ya karba yayi bismillah cikin ranshi yasha donshi kansa yana jin dadin sa,wani lokacin don ya tsokaneta yake qin karba,don ya lura indai yanason ganin fushi da bacin ranta yaqi karba yasha ya kuma zauna sauraren labaran mero
ta bude wata 'yar roba mai kama data naseline,saidai ba shi bane ciki,man zaitun ne da na habbatussaudah wanda ta karantawa ayoyin da suka wuce a baya ta qara da ayatushshifa ta tofa aciki ya zama na man shafawarsa ta miqa masa don tana jin kunyar shafa masa,nan ma sai da ya gama shan qamahinsa ya amsa ya shafa ta maidashi inda yake.
komawa tayi ta zauna kamar ba fitar zasuyi ba,ya zuba mata ido yana son ganin iya gudun ruwanta saidai qememe tayi taqi kallonshi ta fara karanta azkar dinta na maraice,ta kammal ata shiga wasu sabgogin abinta,don har cikin ranta bata jin fitar,sai data qara kusan awa guda sannan ta miqe ta iso inda yake,ido suka hada sai taga ya dan harareta,dariya ma yaso bata amma sai ta dake ta tura whellchair din a tausashe suka fito.
tana kan tabarmar kabar da suka saba zama qasan bishiyar dalbejiyar,tasha daobta daidai da irin nasu baki cike da kan ta kile,koriyar atamfa ce jikinta shar wadda hatta da zanan jikinta yanzun da zaka bawa maryam ta zana maka tsab zata zanashi saboda tsabar sawar da meron keyi yau da gobe don bata da kamarta duk cikin kayanta,gaba dayanta qofar dakin take kallo,gyaran zogalen da aka batan ma ko rabi bata yi ba,inna wuro batasan me ke gudana ba don yau tayi riga malam masallaci ta shiga ta hura wutar tuwon da kanta don kada maryam ta karba yadda ta saba su ta barsu da shan inuwar qasan bishiya,sai da ta kalli gidan ko ina tsaf ya sha shara sai qamshin qasa yake kamar kullum kana ta juya abdallah can bayan mero yadda ba zata iya ganin fuskarshi ba saidai idan juyowa zatayi,ai kam kamad an tsikareta ta juyo din tana fadin
''nayi zaton yau ba zaku fito ba ai,har na fidda tsammani Allah''.
kai kawai ya girgiza yana dan qaramin murmushi wanda idan yayi meron kejin duk duniya fa ita an gama biyanta,kallon murmushin take da matuqar qima don bata taba ganin wani cikin samarin garin da idan yayi murmushi yake qawatashi ya masa kyau kwatankwacin haka ba.
yau kam innan ta zaunar da ita cikinsu babu batun zuwa kitchen wato rumfar girki,taqi kallo kosa baki ko sau daya cikin hirarsu,ranta take ji yana mata suya,kamar ta kori mero amma sai taga meye nata a cik,bata da wannan hurumin,ita kanta batasan me yake jefata damuwa mai yawa kan lamadin meron ba da abdallah,ita da ya kamata ta zama 'yar abi yarima asha kida cikin sabgar.
Dakinsu ta koma ta dora doguwar riga kan dinkin atamfa riga da skert dake jikinta,cikin kitchen ta samu inna wuro
''inna naga kuna kusa da rafo,zan qarasa da abdallah can yaga garin naku''
''to Allah ya kiyaye sai kun dawo''
bata kalli mero ba bare tace mata wani abu ta fara tura whell chair din abdallah,ya waiwayo suka hada ido sai ta dauke idonta
''ina zaki meramuοΌ''mero ta fada tana miqewa da sauri tare da zura takalmanta ta biyo bayanta,inna dake kitchen ce ta amsa mata
''zasu rafin malam dogo na bayanmun nan''
''ai da ni za'a,dama ina son in gaya muku idan kuna son zuwa,girin na da kyau aradu''ta fada tana bin bayan maryam
''um hmmm''kawai tace da ita tana ci gaba da tura abdallah.
Tafe suke mero na nunnuna musu gurare,duk da wani gun ma maryam dauke kanta take ba kalla taake ba,saidai abdallah ya bada hankalinshi sosai bisa dukkana alamu hakan na masa dadi kuma yana fahimtar baya nanta,mero kan makar ta taka rawa don murna,yau gata ka larabawan birni,duk inda suka gifta sqi an bisu da kallo har wasu ma su tambayi meron
'''yan uwanmu ne,wannan yaya na ne''haka take fada cikin washe baki,wasu mazan har hannu suke bawa abdallah,ba qyama yake basu nashi hannun suyi musaba,kodama can shi cikin aqidunshi baya qyamar maras shi,duk wanda kuwa sukayi musabahar farinciki da murna kamar yayi me,musamman idan ya shinshina hannunahi yaji qamahin turaren abdallan,da yawa idan mero tace bashi da lafiya baya iya magana addu'a suke masa sosai Allah ya bashi lafiya.
sannu a hankali suka ci gaba da ratsa qauyen mai cike da ni'ima kamar yadda sunanshi yake,ko ina ka duba shuke shuke ne koraye shar,a yadda taji mero na gaya wa abdallah haka qauyen nasu yake ko ba cikin damina ba,cikin mintina goma suka iso bakin rafin,ruwa ne mai kyau yake guda na ciyayi baibaye da da bakinshi,wasu fararen dutsina da jajayene reras a zube a gun tamkar ana sane aka shiryasu,saidai ikon Allah yafi gaban haka ai.
Gab da bakin nan maryam ata ajjiyeshi,suna iya,hango shanu daga daya,bangaren sunata kai kawo,mafi yawancincinsu fararene qal sai kuma ruwan qasa jifa jifa,shegen surutun mero sai data gaya musu hatta da mai shanun,na wani dan garin ne saidai duk da dukiyar shanun da Alah ya bashi,matashine don bazai wuce shekara talatin ba,don ko auren fari baiyi ba,gefe ta matsa maryam ta zura qafafunta cikin ruwan tana kallon yadda yake gudana,tunanin mama da hindatunta ya fado mata,don kusan babu wanda suke waya da shi a yanzun ,hisham ne yace ta haqura din kada nene ta bayar da nim dinta ayi tracing nasu,da hakan ma saidai abinda take ji yana sukuwa azuciyarta da ranta tana jin kamar yafi haka,duk da zubar da meron keyi hankalinshi na kanta,ya fuskanci akwai abinda ya taba zuciyarta.
ji yayi kamar ya miqe da ya fuskanaci hawaye take sharewa a idanunta,mero ya yiwa nuni da 'yan qananen fararen dutsinan dake gun,ta dauko yan,madaidaita ta miqa masa ga zatonta zai dinga cillawa ne cikin ruwa har tana fadin
''ai ka danyi nesa kadan da ruwan ko na matsar dakai gaba kadanοΌ''kai ya girgiza mata alamun a'a.
ya dauki daya ya cillashi ga maryam,ya sauka abayanta,sai tayi sauri ta waiwayo take kuwa suka hada ido,idonshi daya ya kashe mata kana ya daga mata gira alamun tambaya,sai ta kawar da kan nata ta maida kan rafin,ganin haka ya sa ya sake ciro wani ya jefeta wannan karon ta sani shine sai tayi banza taqi juyowa,da daya da daya sai da ya qarar da su duka amma taqi koda motsawa bare ta waigo gareshi,mero na tsaye a bayanshi tana kallonsu tuni tayi nisa cikin duniyar tunani har ta manta da a inda suke.
Gabanta ya yanke ya fadi,da sauri ta waiwayo,abdallah ta gani a qasa ya fado daga kan wheel chair din idonshi na kanta,a sukwane ta miqe daga inda take zaune dan tahowa inda yake,take santsin,bakin rafin ya debeta tayi baya luuuu zata koma cikin ruwan
''maryamοΌ''
muryar abdallah da take a shaqe ta daki dodon kunnenta ba zato babu tsammani,cikin ikon Allah ta turje bata kai ga fadawar ba ta dawo gaba ta kwasa a guje ta dira a gabanshi cike da tsananin mamaki,ko ina na jikinta rawa yake,sai hawayen idonta da take ta yiwa waigi ya balle baki daya,ta rasa me ma zata yi,hawan mero tayi da bala'i ta inda take shiga bata nan take fita ba,dn me tana gani zata barshi ya fado akan meοΌ,duk masifar da take taqi kallonshi yayin da ahi kuma ya zuba mata ido yana karanta al'amura da dama daga gurinta
''shshshhhhh''din ta taji yace yasa ta rage masifar da take, a hankali a hankali,daga qarshe taja bakinta tayi shiru
''ki taimakamin na koma kan kujerar tukunna madam''
ya gaya mata karo na farko taji,muryarsa ta fita sosai,wani abu taji yana ratsa ta tako ina.
har yanzu jikinta bai bar rawa ba don haka qarfinta ya gaza kaiwa har sai data haqura mero ta taimaka mata suka maida shi,bata sake cewa komai ba ta soma turashi suka fara barin gurin tana goge qwallarta lokaci lokaci,ta kasa tantance yanayin da take ciki,gaske ne koko mafarki,yau abdallah ke magana da bakinshiοΌ.
Dab da zasu fara shiga cikin mutane taji yace
''bai kamata ki shiga cikin mutane kina kuka ba koοΌ,dakat kadan ki daidaita yanayinki''
bata qi shawararshi ba ta tsaida wheelchair din din ta ciro dankwalin atamfarta ta goge fuskarta kana ta maida dankwalinta,amma maimakon hawayen ya tsaya sai wasu sabbi,ma dake bulbulowa har mero ta iskosu
ya limshe ido ya maida bayansa sosai ya kare da kujerar yana fadin
''ya salam,to me aka yi mikiοΌ,idan don warkewar baki na ne ai godiya zaki ma Alah ko,tunda dama shine mai kowa mai komai,idan kuma don fdowar da nayi ne ai gani sumul,ba ba abinda ya gutsireni mijinki baiji ciwo ba''
batasan ta harareshi ba sai data ji yace
''maida idon kada kija min asara,don ba qaramar asara bace idan na rasa wadann nan golden oily eyes din ba''.
A nutse suka ci gaba da tafiya kamar yadda suka zo,saidai canjin yanayi da aka samu,a dazu mero keta faman zuba cike da farinciki abunta abdallah na kalle kalle babu bakin magan,wannan karon kuwa tasbihi hailala da salatin annabi ke fita a bakinshi zalla,yayin da maryam ke cikin wani irin yanayi,jin ta take kamar an rage mata wani nauyi daga cikin nauyin da aka azawa zuciyarta,mero kuwa amsa kuwwa muryar abdallah ke maya cikin kunnenta,dadin muryar ya kasa barin dodon kunnenta,tsabar kulawa da qauna da take iya hangowa daga dukkan kallo da ikin abdallah da kewa maryamu,da gaka suka qarasa gida ana qwala kiran sallar magariba.
*mrs muhammad ce*π
πππβπ½βπ½βπ½
[7:29pm, 9/25/2017] Hugumaπ: ππππππ
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
πΊ *ABADAN*πΊ
ππππππ
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
ππΊππΊ
ππΊπ
πΊπ
π
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
πΊππΊππΊπ
πΊππΊπ
πΊππΊ
ππΊ
π
Β© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*π‘
*_home of expert and perfect writers_*
4β£7β£
*_Manzan Allah S A W yace:shaidanu suna nisantar gidan da aka karanta suratul baqra a cikinsa har na tsawon kwana uku_*
*_mala'iku sukanyi duba izuwa sararin duniya,yayin da suka kalleta suna hangota ne baqiqqirin basa ganin komai face hasken gidaje ko guraren da ake karanta alqur'ani a cikinsa_*
A bakin murhu suka tadda inna wuro tana kwashe tuwo,sallamarasu ce ta janyo hankalinta bakin qofar shigowar
''kun dawo kenan mer.....'''sauran maganar ta maqale wa inna wuro ganin har da abdallah cikin masu sallamar,marar hannunta da take kwashe tuwon ta saki ta miqe tana fadin cikin dafe qirji
''Allah qaadiran ala mai yasha'u,bawan AllahοΌ''ta fada tana kallonsa tare da qarasowa gabansu.
murmushi yayi yana kallon innar ganin ta kasa magana
''babu mamaki cikin ikon Allah inna,nine da bakina nake magana,yau Allah ya amince min''
kiran sallar magariba ya katse su
''inna muyi sallah tukun''ya dubi maryam dake tsaye guri daya tana faman goge qwalla lokaci zuwa lokaci
''gimbiya a dauran alwala,inna ki mata magana tun dazun nace tabar kukan nan taqi''inna wuron dake daura da maryam din ta dafa kafadarta
''haba meramu,farincikin da zaki nunawa ubangiji shine ki masa godiya ba wai kika ba,share hawayenki ki daurawa mijinki alwala''
''to inna''ta fada cikin rawar murya
tuni har mero ta debo ruwa cikin buta tazo gaban abdallan ta ajjiye ta koma bakin rijiyar ta ja wani ta fara daura tata alwala,dukkansu nan bakin qofar dakin innar suka shimfida karauni biyu sukayi sallar magaribar,shiru ya ratsa tsakar gidan kowanne na tasbihi cikin zuciyarshi banda mero da moysa bakinta kawai takeyi duk motsin abdallah ta cikin hasken qwan solar na kan idonta,har maryam ta fuskanci haka,dauke kanta tayi don ji da tayi ranta na aon baci taci gaba da tasbihi da yatsunta.
Ranar har sha daya na dare suna zaune suna hira,hiransu suke sosai shida inna wuro da yake jinta kamar maminshi.
Yana jin kewar mamin nashi sosai har bazai iya fadar adadi ba,mero ma tsakiyarsu tana sanya musu baki yayin da maryam taja bakinta ta tsuke,lokaci lokaci abdallah yana satar kallonta,ji yake tamkar ya jawota jikinshi ya rungume ko ya shiga zuciyarta ya jiyo damuwarta,shirun nata bai masa dadi sam,don haka sha daya na cika yace da inna wuro yana jin bacci zai kwanta
''nikuwa kamar mu kwana nan hirar yau tayi min dadi abdullahi,gashi yau kaima da bakinka akeyi da kai''mero ta fada yana kallonshi baki a washe,murmjshi kawai yayi ya girgiza kai,bata bar gidan ba sai da taga sun shige dakin kana ta waiwayo ta yiwa inna wuro sallama ta fice cike da jin dadin jin daddadar muryar abdallah da yau ta morewa.
sanye yake da jallabiya milk mai gajeran hannu yana zaune saman katifar tasu hannunahi dauke da qaramin al'qur'ani,daya hannun kuma riqe yake da wayarshi ya kunna torch din yana haskawa,ya sake satar kallonta sha biyu har da kwata amma bata da niyyar kwanciya,hakanan kuma ta kashe musu qwan solar dakin saboda ta lura da yadda yake ta nacin kallonta,tana zaune dirshan bisa dadduma sanye da hijabi da carbi a hannunta tana ja,ya saka zare kan shafin da yake na karatun qur'ani ya shafa addu'anshi,ya tabbata koya kirata kam ba zuwa zata yi ba indai ba cewa yayi yana buqatar wani abu ba.
''madam,a ataimakawa bawan Allah da ruwa mana''ya fada murya qasa qasa kamar mai rada har yasa tsigar jikinta tashi,ta ajjiye carbin kana ta miqe ta isa inda catoon na ruwan gora ke ajjiye ta ciro daya tare da cup ta hawo gadon,ta tsiyayo ta sake matsowa gabanshi ta miqo masa,jadawa yayi harda hannun nata ya riqe gam yana son saka qwayar idonshi cikin nata,ta soma qoqarin qwace hannun nata saidai ta kasa garin hakan har fiye da rabin ruwan ya zube a katifar.
Ta dago da niyyar dubanshi idanunta cike da qwalla da ya rasa ta meye,take idanunsu suka hadu,da sauri ta janye nata idanun don bata iya dauke nauyin idanunshi cikin nata
''ka sakemin hannu kaga duk ka.....''
''bazan sakeki ba,sai kin gayan meke damunki,tunda bakina ya budu baki,barni nayi magana da ke ba sai wasu ke tayani hiraοΌ''
ta sake kau da kanta kana tace
''to me kake so muce ko ince maka neοΌ''
''bana tunanin baki san me zaki gayan ba maryam,nasha hango maganganu da dama boye cikin idanunki,kin hana bakinki ya furta kina cutar da zuciyarki hakanan babu gaira babu dalili ba tare da ta yi miki laifin komai ba''
kamar wadda ya doka sai ta soma hawaye,ita kanta batasan me yake saurin karya mata zuciya ba
''subhanallah,kuka...kuka kuma maryam me na miki''babu amsa don haka ya janyota ta fada jikinshi ragowar ruwan ya zube mata ya jiqa mata gaban dan yalolon hijabin jikinta wanda takansa duk dare idan zata kwanta,dama ba wani kauri gareahi ba,yauqi ne da shi da rashin kauri take kuwa ya manne mata a jiki.
''yi shiru