Showing 6001 words to 9000 words out of 26903 words

Chapter 3 - KUYANGA COMPLETE HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

3491

binda ba.a rasaba takeyi daman tunda ana musu daraci da islamiyya da bangaren koyarda harshen turancin duk ackn gidan Sarkin


Ta juyar da kanta

Aiko dai wannan bature yai gangancin kama hannunta yana mata fara.a

Yarima na zuwa ya fuske hannun nata sannan ya wanke baturen da mari

A furgice baturen ya ranta ana kare domin yai tunanin ko mijin tane yadawo gunta

Tashige motar da sauri gabanta na dukan uku .uku

Saida suka fara tafiya sannan yace mata "ke bakida hankali zaki kulashi dahar zai rike miki hannu.

Tace ahankali "bansan yaxo gunba walh kuma kafin inyi masa magana yarikoni.

Yaja tsaki kawai ransa na msa quna baisan daliliba

Amaimaikon yawuce gida saiya nufi wani makeken hotel da ita

Saida yakama daki sannan yace ta biyoshi

Yabude dakin da key wanda ke a saman hawa na biyu

Dakin babbane daya jal amma ahakan VIP ne domin yakawatu yaji kayan alatu ga komai nan daka danna wata tarho ma,aikata zasu iso maka da gaggawa

Gadone makeke da mayan kujeru adakin duk sunciye ga furji da toilet ack


Ya kwanta akan gadon yana nishi waishinan yagama gajiya

Ta zauna akan kujera tana kallonsa

Yakalleta da ido guda yace

Zoki daddanna min jikina

Ta mike ahankali ta tsaya akansa

Yacire kayan jikinsa dagashi sai gajeran wando da bes

Hankalinta yadaga ganinsa ahaka tunda take bata taba ganin halittar namiji abayyane ba saiyau domin yar bes dinma cireta yayi

Tayi kas da kanta gabanta na faduwa domin jikin yarima na dabanne akwai gargasa ga kwanji ga cikar halitta

Ya janyota kan gadon yana fadin

Matso sosai kiyi min tausa bacci xanyi

Batace komaiba tahau yi masa cikin biyayya ba musu

Yalumshe idonsa wani magana disu na shigarsa

Tabbas abubuwa sun gama motsa masa babu abinda zai hanashi jin dadi ayau dama tun dawowarsa Kasar sau daya yayi da wata baby Rihanna tayi tafiya karuwar tasa

Tuni yabirkitota jikinsa yana neman zille mata rigar jikinta

Gabantane yaci gaba da bugawa tana addu.a ckn ranta domin dai tasan tashiga hannu babu me kwatarta sai Allah sannan bata isa tayi masa musun komai ba ayau sai alokacin ta tuno kalamansa na ckn mota wato nufinsa zaisha mintinta amma ba soyayya zaiyi da ita ba

To ai ita gara suyi soyayyar yabar mata mutuncinta

Hawaye taji zai taho mata tayi saurin mayar dasu don kada yagani yazaci zata bujire masane

Itako kanta take tausayi ayau tasan batada mafita sai Allah....……



πŸ€” tabdijan Fans akawo mata taimako
[7/24, 8:16 PM] Ummi Tandama: πŸ“Ώ *KUYANGA* πŸ“Ώ




*_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



*Wannan Page Sadaukarwane kyauta sukutum ga Takwara takaina wato NABILA DIKKO* marubuciyar *DANGIN MIJI* _ina jinjina miki inayinki irin Sosai dinnan Alherin Allah yakai inda kike yakuma kawo mana Daukaka da tsari mu 4 Stars Writers_




*Nabilancy Luv* πŸ’˜
(Auntyn S&S)




25-30
Tanajinsa ya hau sille mata kaya tareda shafata ahankali salo salo Yahau shinshinarta kamar wani kare ko mage

Itako tayi lakwas ranta baya so amma takasa motsawa don gudun bata masa

Yaringa wasa da sassasan jikinta axuciyarta addu,a kawai takeyi akan Allah yakawo mata dauki

Harya cire wandan jikinsa kuma sai yaji wata Izza tashigeshi yaji aikwata kwata bai dace yakusanci baiwarsaba domin hakan zai iya kawo masa ragin Aji

Ya turarta gefe tareda tashi da sauri yahau zira kaya yana fadin "maza tashi kisaka kayanki mutafi

Ckn Sanyin jiki ta mike ta fara maida kayanta ajiki tana godiy ga Allah daya kubutarta

Koda suka baro hotel dinnan kai tsaye gida yamayarta

Da dare saida yadawo Club yasami mata yazaba ciki tareda diddikar giya son ransa yasha yayi tatil sannan yakebe da mata

Bai dawo gidanba saida tasakeshi giyar Wajen 4 na asuba yadawo

Duk bidirin da yakeyi nafutar dare da yawon dare bata ramfo abinda yake fita yiba Duk azatonta ko wani aikin yake futayi tunda bata sanin lokacin dawowarsa

*******
Da Safiyar wata juma,a Yarisketa akicin tana kokarin dora masa abin kari

Yayi gyaran murya tayi saurin juyowa

Ta durkusa ta gaidashi ya amsa fuskarsa ba fara,a

Yace mata "kishiga kigayara min dakina Kitabbatar kingyara minshi tsaf domin yayi kura goge koina Domin Bakuwa zanyi

Ta gyada kai tana fadin "angama Ranka yadade.

Yafuce yabarta tana ci gaba da abinda takeyi

Aranar ta wuni aikin gyaran dakin nasa bata taba shiga ba sai ranar

Duk yanda yake kwalliya da kwalisa da izza da d'agawa irin na Jinin Sarauta amma dakinsa cikin datti yake gado kawai yake hayewa yakwanta tun xuwansu duk da satinsu biyu baisa ta shareba saiyau


Damasu maza aisai a slow sungaji hakan πŸ˜…

Saita hau tunanin ko wacece hakan da zatazo lallai tanada babban matsayi agunsa tunda har asbd ita akeyin gyaran dakin

Ta goge koina ta gyara dakin tsaf tafeshi da Air freshner me dadin kamshin Splash

Harta juya zata futa kuma saitayi tunanin mezaisa bazata bude d'an furjin data gani adakinba ko shima cknsa zaibukaci gyara

Tadawo da baya ta budeshi

Aiko wani wari yabugi hancinta

Tayi saurin toshe hanci

Kwalabe tagani wanda bata fahimci kona meye ba

Saida tahau fito dasu tana dubawa tafara gano kona meye

A iya fahimtarta kwalaben giyane taga anrubuta

*WISKY* da manyan harufa sai wasu datagani sunfi yawa agun anrubuta *ORIGINAL ALCOHOL*

Tahau gyada kai tabbas giyace!

Ta maidasu inda suke ashiryensu

Takama baki tana mamaki da zancen xuci

"Yanzu dama giyar da aketa cewa yana sha da gaskene? Lallai wannan ya iya takunsa Allah yashiryaka.

Ta mike tsam tafuta abinta

Sai dare yadawo gidan amma bashi kadai tajiyoshiba

Ta fito da sanda tarabe a wata siririyar hanyar dazata sadaka da falo ta hanyar dakinta tana hangensa yashigo shida wata siririyar baturiya da kananun kaya ajikinta sunshige dakinsa



Ta tsaya kem agun tana Allah wadaransa Aranta domin yarima dai ba hali ga bin mata ga shan giya tabbas Duk wacce ta Aureshi batayi dace da uban "ya"yaba Sarkinsu adali me kyan hali Allah yajarabcesu da D'a mara kyakykawar zuciya

Takoma daki abinta tana tuno masoyinta MAHBUB ko yaushe Allah zaiyi komawarsu gida taganshi!?

******
Da safe tagama abin kari takai musu daining table Dankalin turawa ta soya da kwai sai shayi dayasha kayan hadi data dafa taxuba a flask

Takoma daki abinta

Basu fitoba sai karfe 11 daya suka fito tana rike dashi ajikinta

Tare suka ciyar da juna tana bashi abaki yana bata

Rihannah kyakykyawar baturiyace wacce itace mace kadai dayafi so tafi kuma gamsar dashi

Tasan salo salo da luggar gamsar da namiji

Macece me tsananin kishin tsiya saita kashe mutum akan kishi

Tunda suka fuce basu dawo ba sai dare daga yawon su

Yatarta da *KUYANGA* adakinta tana bacci

Yabubbuga mata kafa ta farka afurgice ta tashizaune tana mitstsika idanu

Yace mata "nazone don inja miki kunne akan kada ki sake kiringa futowa alokacin da kikasan bakuwata na nan banason taganki zamu iya samun matsala da ita.

Tayi saurin gyada masa kai

Yajuya yafuta yana waiwayenta domin tayi masa kyau ga surarta tar wacce yake tsananin kwadayi ckn wasu kananan kaya

******
Duk yadda yake gudun RIHANNAH kada taga kuyanga saida aka sami akasi taganta domin kwananta uku agidan akai kicibus a falo

Tafito tabaroshi adakin xatayi kallo ita kuma *KUYANGA* Tafito Zata dauki Abinta akicin kuma dole saita sada kanta ta falon tunda dakinta atsakiyar falon yake yana kallon nashi

Kallon kallo aka hauyi

Ita *KUYANGA* Ba damar yin magana gashi gabanta na dukan uku uku tana ganin tasab'a doka gashi Ba turanci take jiba balle tagaidata ckn harshen turancin

RIHANNAH Tayo kanta tana fadin " _hey girl what Are you Doing here_

*KUYANGA* Tasadda kanta kasa jikinta na kyarma

RIHANNAH takarewa kuyanga kallo taga yanda yarinyar tahadu ga kayan jikinta ya amsheta wandone pensil da riga b'igil me siririm hannu ajikinta kanta ba kallabi gashinta yakwanto agadan bayanta


RIHANNAH Ta fuxgota Tana ihu kamar zata cinyeta don kishi " _When are you coming This house_?

*KUYANGA* takara furgita ta kankame jikinta takasa magana tunda bata fuskanci mema takece mataba balle tabata amsa

RIHANNAH ta gaura mata mari tana fadin " _are you mad_? _If you talk me Rubbish i will kill you now_ ganin *KUYANGA* Batada niyyar magana yasa taga kamar raina mata hankali takeyi

Tashakota ta hadata da bango

Ihu da kakarin da *KUYANGA* Keyi yasa YARIMA dake can dakinsa kwance yasa yafito aguje

Yana ganin abinda ke faruwa yayo kansu aguje yakwaci *KUYANGA* Ahannun RIHANNAH yatura *KUYANGA* Gefe yana fadin taje maza dakinta

RIHANNAH ta cakumeshi tana masa ihu akan saiya gaya mata wacece tagani agidansa

Yazabga mata mari saida taga taurari

Agigice ta sakeshi tana rike da gurin taji marin har kwanyarta tahau kuka tana tumami agurin

Yawuce ta afusace yayi dakinsa

Ta tashi tabishi tana cewa saiya kori yarinyar kokuma ita tabar masa gidan

Tasan yana sonta sosai shiyasa take fadin hakan


Amma agun yarima wannan ba abune dazai yiyuba yama xa.ai yakori *KUYANGA* To inya ma koreta ina zataje itada batasan kowa akasar ba shine dalilin xuwanta ai inhar yabiyewa son zcyr yabi zabinta tabbas zai aikata kure domin sai ya fuskanci bacin rai gun mahaifinsa inyaji toko mahaifiyarsa da bata son bacin ransa itanma ai baxata barshi ba

Dayagaji da hargowar tata saiya zare belt yaringa dukanta ko ta kyaleshi

Ranta yabaci da irin hukuncin da yayi mata wanda bata xataba

Kwana tayi tana faranta masa rai domin sau biyar yahauta kafin wayewar gari domin ita din jurauce itace tayi masa sabo da ZAZU πŸ˜…


"Oh!SU Rihanna yau ga karshenki sai akara gaba πŸ˜›


Itadai *KUYANGA* tana jiyo ihunta ana dukanta saita kara cika da tsoro taji kuma baiburgeta ba domin shine yajawa kansa dabaya dauko mata da bazasuzo suyi masa hauka agidaba.


RIHANNAH bata kwana agidanba tuni ta fuce da ita da komatsanta tayi fushi dashi sukayi baran baran aranar ………

*Hhhhh muje zuwa*

Auntyn Sayyada da Shahida ceπŸ‘ŒπŸΌ
[7/25, 3:33 PM] Ummi Tandama: πŸ“Ώ *KUYANGA* πŸ“Ώ




*_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



*SHARHI*....

*ZUWA GAREKU MAKARANTAN LITTAFIN KUYANGA INASO INYI MUKU WANI DAN TSOKACI MUSAMMAN MASU YAWAN KAWO NASU RA,AYIN AKAN KUYANGA TOKU SANI BAWAI INA KUSHE GA BATUNKU BA INASO KUBARNI DA NAWA RA,AYIN NAYANDA NA DAUKO ABUNA, AKWAI MASU CEWA KIYI KAZA GURI KAZA!KADA KIBARI YAYI MATA KAZA!KYANTA DAMA KISAKA TAYI KAZA KO YAZAMO MEYIN KAZA!!! TO DUK INASO KUZUBA IDO KUGA KARSHENSA WANDA YAGA ABIN HAUSHI MA YACE ABIN BAI MASA BA ZAIDAINA KARANTAWA INBAN YI KAZABA DON BAI DACE BA TO FALILLAHI HAMDI NI DAMA BANYI DAN INMUKU DOLE BA DOMIN INHAR NABI TA BAKIN WASU TO LITTAFINA ZAIYI KWANA NE YATAFI LABARIN WATA MARUBUCIYAR TONIKUMA BANA FATAN INYI SATAR FASAHA YANDA NA DAUKO LABARINA ABARMIN AHAKA DOMIN DIRECTOCIN INDIA DANA KASAR MU NIGERIA DA SUKE HAUSA FILM BA DAYA SUKE DANA INDIYA BA AKWAI BAMBANCIN FASAHA KARYAR MUTUM YAGANO YANDA FILM DIN INDIYA ZAI KASANCE AKARSHE TO NIMA KADA ACANXAN RA,AYI INA KARA FADA WACCE TAGA NOVEL DINA YABATA HAUSHI AKAN STAR MACE KO NAMIJI ANYI ABINDA RANTA BAISOBA TABAR ABIN ARANTA BASAITA FURTA MARA DAD'IBA INA K'ARA JADDADA MUKU BABU FA DOLE.DOMIN KUYANGA YASAMI DAUKAKAR DA BAZAI FADUBA, KALAS*!!!! _tank you fans inayinku yanda kuke yina Allah yabar kauna_πŸ’‹πŸ’˜



*Nabilancy Luv*πŸ’˜
(Auntyn S&S)



30-35
Da daddare *KUYANGA* Tana kwance taji shigowarsa dakin nata

Tayi saurin tashi tana masa Barka da dawowa

Ya xauna bakin gadon nata yana mata murmushi tare da Amsawa

Tayi mamaki domin bata xaci zataga fara,arsa ba ma tunda tasan ta karya masa doka tafuta alokacin dayace kada tasake tafuto in RIHANNAR tana nana gashi harsun sami sabani adalilinta tsorone ma yadarsu aranta tana tsammanin ko fada yazo yi mata

Ta takure jikinta agefen gadon

Daya fahimci atsorace take dashi sai yasha mur yace "meye kike wani matse jikinki wato kina ganin ko wani abu nazo miki ne? Ko a hotel kyaleki nayi bawai hkr nayiba yanzu kuma ba zuwa nayi na taba kiba tunda kinyi sanadin barin me debe min kewa gidan dole yazamo kece zakici gaba da deben kewar tunda dama dan hakan nataho dake bawai donki dafan girki koki gyaramin daki nake zaune dakeba don inji dadin rayuwa ta dakene dan haka kizama cikin shiri zuwa daren gobe yau ba,a gidan xan kwana ba inada Dinner din wani abokina till down kwana zamuyi acan.

Yana gama fadar hakan ya mike yafuce yabarta da fargaba aranta

Zancensa ke mata yawo akwanya tome yake nufi?

Nufinsa kenan zai maidata farkarsa innalillahi wainnailaihirrajiin Allah kayimin tsari da aikata zina.

Tarintse idonta wasu zafafan hawaye suka hau mata xarya akuncinta

MAHBUB ne yafado mata aranta domin akullum insun zauna a inda suka saba zama aikinsa ne yi mata Nasiha da wa,azi akan kamun kai ga mace dakuma tsare mutuncinta

Yanzu kenan yana nufin agoben zai santa a "ya mace ? Batada tsumi bata da dabara domin ita baiwace agareshi dolene tayi masa biyayya fatanta dai Allah yatseratar mata da mutuncinta kawai kada yayi sa.ar abinda yake da kuduri akanta

Da safiyar Allah Ta tashi da Zazzabi fargaba ce da tsoron abinda xai faru da ita yasanya mata zazzabin

Bata iya futowaba sai shadaya na safe ta mike dakyar ta nufi kicin don neman abinda zatasaka abakinta

Dafe take da kanta bari guda na mata ciwo ga jikinta zafi rau kashinta kamar ana kwankwatsarsu

Wani jiri ne yakwasheta ya yarda ita afalon bata san inda kanta yakeba ashe suma tayi ma πŸ˜³πŸ™„

Allah cikin ikonsa sai ga SAHABI abokin Yarima yazo nemansa gidan

Yana shigowa falon yai kicibus da ita ayashe ba nunmfashi

Ya isa gareta da sauri

Yana tabata yana fadin "ke lafiya kuwa? Meya sameki

Yataba kirjinta yaji bata numfashi ga jikinta zafi rau

Ai ba shiri ya kinkimeta yai waje da ita yasata amota sai asibiti

Shidai megadi yaga shigowarsa kuma yaga futarsa batareda SAHABIN yagaya masa dalilinsa na futa da *KUYANGAR* magashiyan yafito da ita ahannunsa yasata amotar

Me gadi yacika da mamaki don dai yawayi SAHABIne sosai yasan matsayinsa ga Yariman da Bazai barshi yafuta da itaba Amma kuma awani barin na zcyrsa yana zaton ko batada lafiya ne zaitaimaka mata tunda yasan dai yarima Baikwana gidanba

******
Dayake Babban Asibitine na kwararru akasar ma sai wane da wane

anbata taimakon Gaggawa tasamu kanta tafarko nan akai mata allurar bacci dontasami hutun ko ciwon kan yaragar mata

Saida tayi awa uku sannan tafarka ckn ikon Allah kuma bata farka da ciwon kan ba normal tajita

Zazzabinma yarage mata amma still dai jikin da zafi kwankwatsar kashin ma yarage

SAHABI yasiyo magunguna anbata tasha

Yakawo mata abinci

Dakyar takeci don yatakura matane

Ita tambayar kanta ma tahau yi ya akai wannan mutumin yakawota asibiti?taya suka hadun?bata manta fuskar saba Tagane abokin yarima ne duk da gani daya tayi masa agidan

Amma taji yaburgeta yana da kirki matuqa yakuma ceci rayuwarta bazata manta Alkairinsa ba

Yakura mata idanu yana hango tsantsar kyan da Allah yabata

Tabbas ayau yaji zogin sonta yakara addabarsa

Bazai bar wannan damar da Allah yabashiba zai bayyana mata Soyayyarsa gareta tunda dama wancan karan Yarimane yakawo masa tsaiko da dalilinsa mara amfani


Tana gama cin abincin yakawo mata ruwa takarba tana godiya

Yace "Niya kamata ingode miki.

Tayi murmushi tace "ana me zaka goden kaifa kataimakeni ahalin da nake rai ko mutuwa bazan manta da wannan Alherin nakaba nagode sosai.

Yayi murmushi yace "ai yiwa kaine yaya sunanki?

Ahankali tace " *ZEENATU*! Amma amatsayina na baiwa zaka iya kirana da *KUYANGA*


Ya hau girgiza kansa yana fadin "Zeenatu yadace nakiraki domin sunanki me dadine me kuma amfani yanada matuqar ma,ana a musulunci kinganni nan Allah yajarabceni da sonki tyn aranar da Allah yasa naganki agidan yarima yakuma gayamin ke baiwace agareshi shiyasa yahanani inbaiyama miki domin acewarsa matsayina yawuce naso baiwa tunda nidin Dan sarkin Garin Daurane


Tayi murmushi tace "Dacewar hakan dayagani yasa yai saurin yi maka Togaciya don kada asalinka ya da ajinka yaragwanta Nima kuma ina me baka shawara akan kacire sona Don bazai maka amfani ba tunda bamu dace ba kaidin da "yar sarki ka dace

Yayi murmushi tareda zama agefen gadon yace "ZEENATU nine D'a na uku agun mahaifina SARKI ADAMU wanda kaf cikin "yayansa nine Namiji yafi sona ackn su Ankuma bani mata Amma nace bana so "yar sarkice tana sona banida Ra,ayin in Auri yar mulki ko Sarauta Nafi son in Auri "Yar marasa shi atsarina ma yar talakawa nake so in Aura...

Tagyara zama don hira dashi yamata dadi yakuma kara burgeta

Tawatso masa tambaya akaro nabiyu "kaiko meyasa hakan?

Yace "Zaki sani anan gaba inna Aureki.

😳 tazare ido aranta tace "tab kayi nisa lallai ashe dagasle yake abin naka babbane badaniba.

Tace "Dan Allah kacire wannan maganar ma tun wuri kafin yarima yafuskanta zanmayarka yaya agareni abokin shawara inka yarda

Yace "To zandau hakan abayyane don kada yarima yagane tunda naga bazai bani goyon bayaba amma azahiri azcy kinanan awacce nakeso nima inaso kidaukeni amasoyinki nagaske azcy kada kinuna amma azahiri mununa mu Abokaine kinji.


Ta daga kanta kawai ta gamsu da hakan

Wayar sace tahau ruri

Yana dubawa yaga Yarima ne

Yai picking yana fadin "abokina kana ina haka?

Yarima yahau masa fada "Meya kawoka gidana alokacin da kasan bananan wato shiyasa kaki zuwa Dinner din dankazo kadauki Zeenatu kuje yawo ko?bansan zaka nuna halinka ga baiwata ba to walh kasani baxan xuba ido inga kana aikata...

"Dakata mallam angaya maka ni irin kane?

Yarima yadaga murya kamar zai cinye SAHABIN ta waya "Bazan dakataba harsaika dawo da ita gida nan da minti biyar inba hakaba....

SAHABI Yace" Zan dawo da ita amma harsai likita yasallameta... "What! Meya sameta mekayi mata?

Cewar yarima agigice yake tambayar sahabin dan axaune yake sai gashi baisan yamikeba

SAHABI Yace "Kai zancewa me kayi mata domin asume nazo nasameta afalon gidanka bata hayyacinta Ni taimakonta nayi nakawota asibiti inzakazo kadauketa saika taho asibitin da muke da file acan wanda familyn mu kezuwa nasan kasanshi tunda kataba xuwa kaima. SAHABI yana kaiwa nan amaganarsa yakatse wayar Yariman yana tsaki

Itadai sakato tayi tana jinsu tana kuma mamaki aranta Duk yanda suke amma Yarima saida ya zargeshi toko dai halinsu daya ne?

Hhhmmm Allah dai yasa ba kalmar Abokin Barawo barawone ne zaiyi tasiri akan suba...πŸ™„


Sallama SAHABI yayi mata yabar Asibitin domin Yarima yabata masa rai bazaima bari yazo yatarar saba don haushin kalamansa daya gaya masa

Koda yariman yazo yanemi Dakin da aka kwantarta

Yana ganinta yahau tambayarta meya faru da ita?

Ta gaya masa abinda tasani tareda nuna masa SAHABI ne yataimaketa alokacin da take ahalin neman taimakon


Yarima yace "toke meya haddasa miki shiga wannan halin.?

Tayi shiru

Yasake mata tambayar again

Tace "babu komai Daga Allah ne.

Yace "to yanzun yajikin naki?

Tace "naji sauki Alhamdulillah.

Yace "Ok zanje su sallameki ban iya xaman Asibitiba.

Yafuce zuwa mintina yadawo yace "Anbasu sallama yanzu likita zaizo yaganta su wuce.


*******
Koda suka dawo gida Taga canji agunsa don wani tattalinta yakeyi yana nuna mata kulawa ga cima kala kala dayake kawo mata

Har manta matsayinsa gareta yakeyi

Bawai zama yake yayi hira da itaba kawai dai kulawa yake bata saikuma aikin dazatayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login