Showing 21001 words to 24000 words out of 26903 words
sane ba haufi
Mai martaba ya Dade yana kallon Yaron
Yatabbatar da wasu abubuwan na yarima ajikin Yaron saiyaga tamkar yarima yana Yaro
Wata kaunar yaronce taringa shigar Sarki yaji inama tahanyar sunna aka haifoshi
Koda yakebe shikadai kuka yaringayi waiyau shine da jikan dayazo bata hanyar Aureba yarima yacuceshi yabata masa suna
Yarima baidauko halinsa ba baiyi shashanci ba yana saurayi Komai nasa da nutsuwa da kamun kai yayishi harsaida yayi Aure yasan mace to amma gashi Allah yajarabceshi da abubuwan tir agidansa
Munjajanta maka Sarki Abdallah 😭
Abin arxiki FAATU da MAMAH suka hada sosai na kayan jariri aka kaiwa *KUYANGA*
Jakadiya tabazama ta gayowa UMMAH
Fulani tahau gyada kai tana fadin "munafukai nagama ganosu sunayine badan Allah ba saidon Neman suna da kuma Neman duniya agun Sarki
Kinaji ko Jakadiya nima zanhada kayan inbaki kikai badan Allah zanyiba saidan wadancan munafukan Dan aga banyiba sukayi tunda za.ace niya kamata nayi ko
To zan yi nima Wanda yafi nasuma yawa sannan ke zanbawa kikai harkudi zandora amma inaso kiyawaita kai kafa don hidimtawa mejego dakuma duba yaro inaso kinuna musu soyayya tayanda inkin kashe Yaron baza,a zargekiba
Jakadiya tahau gyada kai
" angama ranki Dade.
Jakadiya nafuta ta wuce sashen su FAATU dontakai musu tsegumin abinda UMMAH tace na kayan da zata hada itama
Amma dai wannan jakadiya duk randa aka karya miki kafar dama baxamuzo cetoba kuma ko jaje bamuzuwa🙄😆
Muje zuwa
[8/5, 11:13 AM] Ummi Tandama: 📿 *KUYANGA...* 📿
*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION_*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*Nabilancy Luv* 💘
(Auntyn S&S)
80-85
YAU jakadiya bata samu damar yin tsegumin ba tana shiga sashen nasu ta tararsu Da Baki ga LAMIDO yana nan
Dole tayi kwana takoma da baya
*KUYANGA* Tasa jaririn agaba tana kallo Abu biyu takeji akansa na farko Tsanarsa adalilin Haushin Ubansa da ta hanyar da akasameshi tunda takasa manta yanda YARIMA yaringa mata karfa karfa akan saiya Santa a "Ya mace Ashe duk rabone Ke kira tabbas Banda ba,a Tara Sani ga Allah da tanada masaniyar samun ciki dashi da saita bujire masa bazatayi masa biyayya ba koda zai kasheta ko yaumata korar kare
Awani bangaren kuma tanajin Tausayin Yaron ta irin hanyar da yazo
Yanzu da ace ta hanyar sunna yazo da tuni gidan yacika da yan zaryar yiwa mutan gidan barka na xuwan jikan fari garesu
Wani makokon bakin cikine yatsaye mata ganin Yaron yana kama da yarima futuk yanda tatsani yarima bataso zata ringa kallon photography dinsa akusa da itaba
Kafin rasuwar MAHBUB ta tsara idan ta haihu in namiji ta haifa tasakawa Yaron SAHABI ta dalilin taimakon da yayi mata arayuwa takasa mantawa dashi akullum saita tunoshi inama zata Ganshi
Amma yanzu data haihu babu MAHBUB aduniya saita canza tunani inhar za,a bata dama sunansa zatasaka
Tasan dakyar in yarima zaiyarda tunda tasan ba kaunar sa yakeba
Da SAHABIN nema ya iya bari tunda Abokin sane
Ta goge wasu hawaye masu zafi akuncinta Adaidai lokacin da Zulaihat tashigo dakinta da Leda ahannunta
Zulaihat tazauna kusa da ita kan katifar tareda ajiye ledar tana fadin
"Kintisa yaro agaba sai kallo kike ko kunya bakyaji na D'an fari
Yanzu idansu iya Sha,awa sukashigo suka ganki kina masa qurillar nan aikin kade da magana bayama inna Dije taji labari uwar karadi da gyani bakyalewa cewa zasuyi Ma kinata masa wasa
*KUYANGA* Tayi gajeran murmushi tace " hhmmm Zulaihat walh banajin kaunar Yaron nan araina ko kusa dakinsan tsanar Dana masa da bazakice komai akai ba adole nake bashi NoNo nasan inban bashiba baida abinda xaisha kuma hakkin ne akaina kuma madara ba dauwwama zatayi gunsaba ba za tayi masa amfani kamar nononba sannan Za,a tuhumeni ackn gidan nan
Zulaihat tace "hhhuuimm Zeenatu kenan kifa godewa Allah ma da kaddararki tazo da sauki gashi Allah yasa kinyi arxikin da yaro yasami gata ackn gidan kowafa sonsa yakeyi
Nifa ji nakeyi inama niceke inama nice na haihun nan...
" amma dai Zulaihat kina da son duniya shiyasa kike wannan tunanin meye abin so ga haihuwa irin wannan nifa bana kwadayin sarauta ballantana arxiki kenifa da ayanzu LAMIDO zaidawo yace yafasa Aurena ko ajikina tunda dama bansaka akaba
Kuma da kike cewa yaron nan Dan gatana ta INA yazama Dan gatana tunda har yanzu Wanda yake amatsayin mahaifinsa baileko shiba balle mahaifiyarsa da bata kaunar Yaron
Zulaihat tace "barfadin haka kadama suzo din aikowa dai yasan nasune kuma ko tasoshi ko kada tasoshi yarodai jinintane kowa yashaida tunda d'anta yadawo yafadi gaskiya anji
Sannan inbasu so shiba dubunsu agidan sunsoshi koina fa kikayi zancen kyan yaron nan akeyi da kamarsa da ubansa ni tunani ma ko kunyace ta hanashi zuwa suda uwar
HhhhmM " kawai *KUYANGA* Tace tana fadin "me kika kawo aledar ne ?
" magungunan da akasiyo mk ne gashinan hardana Karin jini aciki
Tahau budewa tana nunnuna mata
*********
Da daddare bayan Sallar ishsha 'i saiga sakon kiran *KUYANGA* daga fada sarki ya aika mata
Zulaihat ce "yar Rakiya tadauki jaririn ta goya abayanta
Koda sukaje bayan sungaida mai martaba yace mata " kiyi hakuri Zeenatu natasoki da dare ga jego
Kanta akasa tana murmusawa tace
"Bakomai "
Yaci gaba "To dalilin kiran dama akan sunan da za,a sakawa Yaron ne daga bakinki nakeso ba daga bakin yarima ba domin bai isa komai ba aguna kenafiso kixaba domin ranar suna arada masa
Sai taji inama ta hanyar sunna aka samoshi da kawai cewa xatayi SUNANKA ME MARTABA
To amma yata iya daidai ruwa daidai tsaki takada baki tace " sunan margayi MAHBUB nakeso asaka masa Ranka yadade
Ya gyada kai yagamsu yaga kuma kyautawar ta duk da baisan tsakanin suba amma dai yasan Dan UWA yake gareta kamar yadda yake matsayin bawa haka take itama
Sarki yace "to jeki abinki za,a saka masa akwai wani Abu da kike bukatane?
Ta girgiza kai tace " Babu.
Yabasu umarnin tafiya tunda babu
Suka mike suka futa ko Dan. Bai Tambaya ba (amma bawai Dan baya son saba shikansa yanajin ba dadi inya tuna yanada jikan da aka haifa ba Aure ack)
Bayan kwana biyu ana gobe Za,a rada masa sunan saiga kaya daga UMMAH akwati guda kayan jarirai manya masu tsada ga kudi ackin akwatin dubu hamsin (Dan ma mekawowar jakadiya ta dauke hamsin din kai yarima me yasako dama)
Iya Sha,awa da inna Dije da sauran tsaoffin gidan nasu *KUYANGA* Sukaita murna ana guda
Jakadiya ta dauki Dan tana yabashi azahiri azuci kuwa kiyasta yanda zata kasheshi takeyi
Tun daganan jakadiya take kawo musu kafa sashen nasu duk don su saki jiki da ita tana nuna soyyyarta ga jaririn
Aranar ma agunsu ta wuni harda tayasu yiwa yaro wanka
Da dare ana gobe suna saiga Yarima yazo shima ganin yaro domin yanada labarin yanda aketa fadin kyansa da kamar da sukayi shiyasa yazo dai yaganewa idonsa yakuma gaya mata sunan dayakeso yasakawa Yaron
😏😇ka makaro
Ajikin katangar dakin *KUYANGA* yaja yatsaya ta farfajiyar tsakar gidan bai shigaba
Ta aika aka kai masa farar kujera ta roba
Ta aika masa da Yaron duk Zulaihat CE yar Aiken
Yakurawa Yaron idon akwai hasken tsakar gida nafitilu
Yaji kaunar yaron tashigeshi tabbas ko bai Aure taba zai karbi kayansa inyayi Aure yarike kayansa
Tafito gurinsa tana taku ahankali
Ya amsa sallamar da tayi
Bayan tagaidashi tanemi ta juya takoma
Yace mata "Dakata tukunna daga zuwa saiki tafi banga kyakykyawar fuskar kiba sannan banyi miki godiyar Haifar me kama dani da kikai ba
Tayi masa banza
Yace " Zeenatu INA matuqar sonki nasan kingane hakan walh nakasa sakat araina INA so tunda kin haihu lfy inkinyi arba,in Adaura mana Aure...
Tadago da sauri takalleshi "anya yarima ba kwaya yashaba kuwa tunda tasan yana korawa
To ita kuwa me zatayi dashi ga LAMIDO mutumin Kirki Allah yai mata tsari aiko babu LAMIDO bazata Aureshiba
Yakatseta da cewa " kin amince ?
Ta girgiza kai tace "LAMIDO shine mijin da zan Aura ayanzu haka ina ganin Allah ne yadubi abinda kayimin shiyasa yabani shi amatsayin miji dan hakama kacire batun wai zamuyi Aure dakai
Yace mata " kina nufin bakya sona?
Tace "babu sonka araina kam! Waima kamanta wata rana daka so kwanciya dani naki kacimin zarafi kace mezakayi dani bawai sona kakeba me zakayi da BAIWA maqasqanciya...
Yadaga mata hannu don borin kunya yace " ya isa bance kiyimin tuniba yadade da wucewa yanzu dai gonb suna na zabi insaka masa SAFWAN
Tayi murmushi tace "to saikaje kasanar dame martaba yacanza Wanda zaisaka
Yace " me kike nufi? Yaxabi wanine bansaniba?
Tace "tun jiyama yakirani fada yabukaci zabina akai nagaya masa MAHBUB nakeso asaka
Yaxabura yakusa yarda Yaron don furgici
Tayi saurin taro D'an ta
Eyeeee😅🙄🙄😳😳Zeenatu Ashe dama kina sonsa
Yanunata da yatsa " Baki isaba wannan suna baiminba niya cancanta inzaba bake ba Nike da iko danhaka maza kikoma kice SAFWAN za,a saka masa ba Wani sunan BAWA ba
Tayi murmushi tace masa "aika makaro aikin gama yagama mai martaba yakarba tuni Dan haka banzamo meraina nagaba daniba da zanje masa da canxa magana
Tana gama fadin hakan ta juya ta tafi abinta
Yabita da kallo yana kwafa
Da bakin ciki yakwana Tirkeken ragon daya ware zaikai don ayankawa jaririn saiya fasa bayarwa domin ba sunan dayakeso za,a sakaba bazai iya xuwar wa sarki da canjin sunan ba domin kallon arxiki ma baya samu inyaje gaidashi
Yanajin wata irin kaunar jaririn domin sonta ma yafara raguwa yadawo kan Yaron kyan Yaron yatafi dashi tabbas zaiyi fashion dashi agun abokai
Da Sassafe gida yakacame da taron suna dama tun asuba a masallaci da suka idar da sallah aka radawa yaro suna da MAHBUB
Raguna biyu manya mai martaba ya aika fadawa suka kai bangaren Bayi aka yanka amatsayin Hakika
Tabbas kowa ya aminta agidan yaro dan gatan sarkine tunda gashi sunga abubuwa da dama na soyayya daga sarkin
Ita kanta *KUYANGA* taji Dadin hakan saikuma tasake akoina tunda da ace Dan bai karbuba agidan da tuni anata tsangwamarsu
Aranar kwana tayi rumgume da d'anta tanajin wata kaunarsa na shigarta ayau da yaron ya amsa sunan Masoyinta taji kaunarsa tashiga jikinta tabbas tana masa so sosai Albarkacin son da tayiwa margayi MAHBUB
A Bangaren UMMAH Jakadiya takawo mata tsegumin yanda Sarki yakai abin yanka manya manya na hakika
UMMAH ta quta cikin Takaici tace "Lallai Ashe har soyayya aka shiryi nunawa Dan shege kenan nifa har yanzun jakadiya banyarda da jaririn nan Jinina bane tabbas akwai meshi awaje
Jakadiya kamar ta furta " Duk kamar da sukai 🙄😆
Saitaja bakinta tayi tsit sbd tsaro kada UMMAH Taji haushinta
UMMAH tace mata "kinajina ko agobe nakeso aikinki yafara akowane lokaci kika sami dama ki shaqe min Yaron yamutu shine kadai burina da farin cikina mutuwarsa inhar kika aikata hakan Alkawarukanki sunanan zanbakisu
Jakadiya tace " angama uwar dakina yanzuma can zantafi inshiga cikinsu inzauna ayi komai dani kafin gobe in aikata aikinki........
Tofa muje zuwa fans
Auntyn Sayyada da Shahida ce 👌🏻
[8/8, 10:02 AM] Ummi Tandama: 📿 *KUYANGA...* 📿
*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION_*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*Nabilancy Luv* 💘
(Auntyn S&S)
85-90
*KUYANGA* takurawa junior MAHBUB idanu tana karewa irin kyan Da Allah yabashi sai ayau taji ta kara kaunar Yaron dayaci sunan MAHBUB
Ta rumgumeshi sosai ajikinta tamkar Wanda za,a kwace matashi tana Adduar Allah yasa yagado hali da ilimi na me sunan sa
Yanata baccinsa dama yarone me hakuri inyasha nonon dare baya farkawa saisafiya
Sallar ishsha,i akayi inba,aci sa'a ba shida tashima sai safiyar
Zulaihat bata dakin nata taje sashen Inna Dije takarbo abincinta
Kafin ta dawo bacci yafara daukanta tana rungume dashi akan kirjinta
Can ta motsa da sauri da taji motsi ana shigowa tayi tsammanin ko zulaihat CE
Saitaji sanda can kuma taji tsit
Da taji dai shiru ba,a shigo dakinba saita dire junior tafuto tana kiran zulaihat saitaga bakowa atsakar gidan
Ta dau buta tashige bandaki abinta dama fitsari takeji ga cikinta yana murdawa tunsafe dama take Dan shiga toilet din tana ba haya
Acan waje kofar gida Yarimane yazo gunta yanata Neman Wanda zai aika yaji shiru tsit babu gilmin mutane sbd whether ta sanyice da wuri ake shigewa akwanta
Yananan tsaye dai dayaga zai tsayu agun saiyayi kokarin yacusa kansa kawai domin dama sallama yazo yi mata yaga dansa kafin gobe yatafi Turai abinsa
Adaidai sadda yazo saka kai cikin gidan alokacin ne Yaga fitowar mace aguje tayo waje daga ciki afurgije ba gaskiya atare da ita ta bangajeshi tazura da gudu
Baiyi kasa aguiwaba yabi bayanta yazage karfinsa yacimmata acan nesa da gidan yadamqeta
Wa zai gani inba Jakadiya ba
Tana ganinsa tasan yaganta sai jikinta yayi sanyi tunda tasan asirinta yagama tonuwa ayau
Yace mata "jakadiya kece dama?meya kaiki bangaren bayi awannan Daren meyasaki uban gudunnan ?
Take tarasa ta cewa ta diririce tafara kuka tana fadin " karufamin asiri kamar yadda narufa maka
Yanuna kansa "kika rufa min kamar Yaya?
Tace " Eh Ai inada wani sirrinka da bakowa yasaniba sai ni da mutanenka dakasa aikin
Yarima ya mamakantu da maganar jakadiya ya nuna kansa yace "Sirri kuma?ni nasaka aiki ?to akan me nayi aikin dahar kika Sani?
Tayi wata dariya kana tace " kasani cewa akan kunne na naji kabada Umarnin aje akashe Bawa MAHBUN kawai don son rai da kishin da kake dashi nasan komai yarima ayanzuma daka ganni nima akan aiki nake
Yace "wanne aiki kikaje gidansu Zeenatu awannan Daren ?
Jakadiya tace " aikin kisan kai...
Dasauri yawatsa mata Tambaya "wa kika kashe ?kada dai Zeenatun?
Ta girgiza kai babu tsoro atare da ita don tasan me ta taka " Dan Zeenatu nakashe amma mahaifiyar kace tasani hakan
Yadafe kansa "wa,iyaxubillah D'an nawa kika kashe?
Tace " kayi hkr banida laifi
Yaharxuko kanta "Kinfi kowa laifi kuma saina hukuntaki bazan kyale kiba
Tace " idan har katonamin asiri tokamar mahaifiyarka katonawa sannan nima saina tona naka asirin nabaya
Tana gama fadin haka ta tawuce abinta tabarshi da tarin bakin ciki
Kai yadafe yana fidda hawaye
Jakadiya ta cuceshi yana matuqar son Yaron nan SBD shi yazo gidan tabbas mahaifiyarsa ce taja masa komai Ashe dama ba kaunar jininsa takeba
Ihu da hargowa yajiyo ta cikin gidan Su Zeenatu itada Zulaihat ne suke kuka da karfi da neman dauki ganin anzo ankashe yaro hargida
Dayake ta bayan gidan yake tuni yai saurin barin gurin kada wani yaganshi yashiga zargi
******
Kuka sosai sukeyi gidan yacika da mutane anata jajanta mata narasuwar jaririn ta Wanda akashigo hargida aka kasheshi
Kowa mamakin wannan Abu yakeyi anata fadin lallai duk yanda akai makashin yana ckn gidan kafin tashiga bandakin haka bayan makashin yafito zulaihat ta shigo gidan
Da filo akai amfani wajen danne shi harya mutu
Saida safe aka sallaceshi aka kaishi
Da yarima aka kashi aka binne yanaji yana gani dole yai shiru bai iya bayyana wacce takashe yaronsa abin sonsaba
Ranar dama fushi yayi da mahaifiyarsa bayan adaren yaje yai mata bore da kuka akan ta aika ankashe abin sonsa jinin jikin sa
Mai martaba ma yaji mutuwar Yaron dakansa yataka yaje yaiwa *KUYANGA* Ta,aziyya domin yana son Yarinyar aransa domin Nutsuwarta
Kwana tayi tana kuka tana tuno fuskar yaronta
Aranta kuwa tanajin bazata taba yafewa Wanda yai mata wannan abuba don ancuceta saida akaga tafara kaunar yaron aka rabata dashi
UMMAH kuwa ranta fes ta cikawa jakadiya alkawarinta na abubuwan datace zata bata
Ammafa agun yarima bata jin ta dadi shiga daya shiga biyu saiya gaya mata magana tamkar ba mahaifiyarsa ba
"Kinji dadi kinraba Dan tahaliki da duniya kunji Dadin hakan Kuda Allah kuncuceni kunrabani da farincikina.
😏kunjishifa kaika manta daka sa aka raba bawan Allah da duniya Ashe abun ba dadi
Kwana uku da faruwar hakan LAMIDO yazo yi mata gaisuwa
Tafito cikin hijab har kasa
Yakura mata ido harta iso gareshi tagaidashi ckn ladabi
Ya amsa yana kallon Dan karamin bakinta mekamada alawar lollipop
Yace " ZEENATU ya hakuri kuma?
Ckn sanyin muryarta tace "Da Godiya
Yace " Allah yajikansa yabaki hakurin rashinsa
Ahankali tace "Amin nagode"
Yaso yafurta mata wata kalma saikuma yafasa
Yaimata sallama yatafi
Yauma binshi tayi da kallo
Yanda yake takunsa na kasaita da iya tafiya ta sarakai abin birgewane kokusa Yarima baikamoshi akomai ba Tabbas LAMIDO na daban ne
Ayau tayiwa Allah godiya dayasa zata zamo mallakinsa donta farajin wani Abu akansa
Abin mamaki ma da dare kasa bacci tayi tayita juyi akatifa tana tuno irin yanda yake maganarsa da tsari da tausasawa ga iya kallo kodon idanunsa Sexy eyes ne gashi da kyau da tausayi
Tabbas Samun Namiji irin LAMIDO sai antona
Tooo🙄😳fans *KUYANGA* me kuka fuskanta ne a Heart din KUYANGA
To kodai ta kamu ne ???
Muje zuwa
[8/8, 8:11 PM] Ummi Tandama: 📿 *KUYANGA...* 📿
*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION_*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*Nabilancy Luv* 💘
(Auntyn S&S)
90-95
FAATU ce A zaune aturakar mai martaba bayan yagama cin abinci yadubeta yace "Kince kinada magana inajinki meke tafe dake akwai damuwane?
Ta gyara zama tace "Dama maganar LAMIDO ne Naga tunda har anyi sadakar arbain din jaririn Zeenatu nace to me zai hana atsaida ranar Auransu da LAMIDON ba tunda har ya amince kuma naga kamar yafara sonta
Murmushi Sarki yayi yace "To babu komai sai a tsaida Wata daya mai zuwa sai adaura Auran nasu bamusan me Allah ya ajiyeba kuma Inaso aranar da za,a daura Auran ayi bikin dorashi Kan karagar mulki natsufa yakamata nayi murabus nadorashi akai duk abinda nakeyi wanda yakamata yake kaina zai iya sannan ya cancanta don haka zansa ayi shela agari kowa yasanda wannan rana
FAATU tace "To amma Takawa kana ganin wannan abun dakayi bazai kawo rabuwar kai atsakaninsa da Dan,uwansa yarima ba mahaifiyar safa ta kudurci dantane zai zama sarki natabbata zataji ba dadi koma tayi