Showing 3001 words to 6000 words out of 36321 words

Chapter 2 - Ribar Biyayya Complete Hausa Novel

14 Jul 2025

5362

juya ya tafi kallonshi take kaman wacce aka hanata binshi har ya fita a gidan. Bayan fitanshi baba yayi wani tunani lek'owa yayi daga d'akinshi yace fatima maza kira min yayanku kafin yayi nisa da sauri ta tashi har d'ankwalinta na fad'uwa amma bata tsaya d'auka ba, fita a gidan tayi da gudu can ta hange shi yana tafiya da gudu ta bishi tana kiran uhmmmm bah k'arami uhmmm kai kai uhmmmm yah sagir juyowa yayi da sauri ta k'arasa gabanshi tana haki. Kallon k'aramin figure d'inta dake gabanshi sai kanta ba d'ankwali sai dogon shukunta da yake nuna alamun warewa ko kuma rashin kamuwa jujjuyawa yayi yaga ba wanda hankalinshi ke kansu kasancewar anguwar ba musulmai sosai yace" k'awas ya dai kin biyoni rakiyar ne ko d'ankwali babu?"

Shafa kanta tayi tace " wallahi fad'uwa yayi ni kuma ina sauri kar ka b'ace min baba yace in kiraka inace ma a mota kazo kar kayi nisa" kai ya kad'a yace ai na bar motar a bakin hanya ana wanke min" haka suka k"arasa suna hirarsu. Baba ne ya kalleshi bayan ya shiga d'akin ya zauna yace" babana dama wata shawaran na yanke me zai hana ka komo kan fatima tunda ita bata da wani damuwa asalima bata san meye soyayya ba. Gabanshi ne ya fad'i jin batun kawun nashi a kasalance yace " kawu baka ganin za a shiga hakkin yarinyan da da karatunta? Baka ganin tayi k'ank'anta da aure?" Murmushinsu na manya yayi yace " ko d'aya fatima dai rashin jikin girma gareta amma ai ta isa aure shekara goma sha biyar aiko ta kai aure watan d'aya zata cika shekaru goma sha biyar mamakine ya k'ara cika sagir jin wai y'ar shekara sha biyar ce ta kai aure ai ko a karkara sai haka shifa ko da yace yana son khadeeja ba wai yana nufin suyi aure nan take bane shima d'in ai yaro ne gaba d'aya shekarunsa 26 kuma so yake yaje ya karo karatunsa zuwa phd.

"Kayi shiru babana ko baka son fatiman ne daman nayi k'wad'ayin had'in zumuncin ne kar kaji komi in baka sonta ka gaya min" ah ah baba Allah yayi zab'in alheri zan sami hajiya da maganan kafin kazo.

Haka ya musu sallama fateeman ta fito raka shi taga duk jikinshi a sanyaye hannunshi ta kamo kallon cute face d'inta yayi yace " ya dai mai suffan y'an korea?" Zaro idanu tayi tace" au na tashi daga mai kama da 'yan china na dawo 'yar korea?" Murmushi yayi kawai duk da k'arancin shekarunta ta san da ciwo ace ba a sonka marairaice fuska tayi ta kirashi da sunan da ta san yafi son a kirashi da shi wato sunansa na gaskiya "yah sagir kayi hak'uri k'ilan ba alkhairi tsakaninku ne shi yasa abin bai working ba kayi hakuri Allah zai kawo maka wacce ta fita hali da komai wacce zata kawo farin ciki rayuwarka, ka daina damuwa kaji ta k'arasa maganan kaman zata yi kuka.

'Dan dogon hancinta yaja yace wa yace miki na damu ni ai har na sami matata" alhamdulillah" shine abinda tace. Sai yaso yaji cikinta dan yaran yanzu baka shaidansu mussaman akan soyayya " ke kuma waye saurayinki" ya tambayeta a dai dai lokacin da suka iso wajen motarsa dafe k'irji tayi tace "ni shegiya inji d'an daudu ina ni ina wani saurayi" dariya yayi sosai ya d'an jujjuya ya duba yanayin anguwan yace ke dai gaki baki girma cikin hausawa ba amma ya aka yi kika iya hausa haka" itama dariya tayi ta rufe idonta tace "ai ina zuwa islamiya a kwana shagari kuma ai kaga anguwan hausawa ne kuma akwai wata yarinyan ajinmu in malam bai shigo ba tayi ta karanta mana littafin hausa. Had'e rai yayi yace ashe ma ba karatu kike zuwa jin karatun littafin soyayya ke kai ki da sauri t girgiza kai tace ah ah ah ba littafin soyayya bane irin su iliya d'an mai k'arfi da magana jari ne fa kuma ma sai in ba malam a ajin" "duk da haka ai gwara kuyi muraja'a"

Haka suka yi sallama ya kama hanya yana me dana sanin fara furta kalman so akan khadeeja da yanzu bai shiga tsaka mai wuyan nan ba
💖RIBAR BIYAYYA💖







By Sawwama A.







Page 4.







A zaune ya sami hajiyar cikin shiga ta alfarma kyakyawar macece wace tsufarta ya b'uya cikin jin dad'i da kyan jiki fuskanta na d'auke da manyan idanuwa da dogon hamcim da take yawan hurashi hakan yasa hancin ya zauna haka a bud'e saboda sabon da akayiwa hancin saboda masifa.


K'arasawa yayi ya zauna a k'asan kujerar da take ya d'ora kansa a bisa cinyanta ita kuma tajiye jaridar da tun da ya shigo ta daina karantawa ta d'ora hannunta a kanshi tare da fad'in ya "akayine babana me kawun naka ya fad'a maka ina fatan ba matsalar wancan shed'aniyar yarinyan can da uwarsu ta gama zugeta bane?" Turo baki yayi cike da shagwab'a irin na tabb'arrun yaran nan yace "kai hajiyata ni wanne toh zan ansa sai jero min tambayoyi kike?" Shafa kanshi tayi tace toh yi min bayani a nutse" d'ago kanshi yayi ya sake turo baki yana wani shagwabewa yace " toh ba tace wai ni nayi mata yaro ba kuma ni d'an k'auyene kum...." A harzuk'e ta katseshi da fad'in a haifeka a turai ka taso a turai sannan ta kalleka tace maka d'an k'auye kuma ina batun yaranta yake a nan tunda ka mallaki hankalinka gaka da iliminka da sana'arka banda ka dagewa koyarwan nan daka sa kanka ga kamfaninka da mahaifinka ya bar maka amma a dubeka ace maka yaro d'an k'auye saboda tab'ewa da rashin rabo?" Ajiyar zuciya ya sauke yana murmushi dan shi d'in me yawan murmushi ne yace kin san 'yan Jos d'in nan in kana Bauchi ko wani gari na Hausa fulani d'aukanka suke d'an k'auye bagidaje saboda mu bamu d'auki d'abi'ar yahudawa ta sanya tufafi me nuna tsaraici da rashin sanin hakkin gabb'an jikin d'an adam kuma maganan yaranta tabbas ni d'in yaro ne shi ya sa kawu nema min mata k'aramar yarinya daidai ni...." Cikin k'araji ta kuma fad'in " me kake shirin gaya min in na fahimceka so kake kace min wancan k'abilar taci nasara a kanmu a karo na biyu kenan ta samu ta auri d'an uwana a b'agas sannan yanzu ta nemi hanamu had'a zumunci shi kuma wancan sallamamen sai biye mata yake yi har da wai ya samo maka mata a wani wajen" fuskantanta ya kuma yi da kyau yace " bafa a wani wajen ya sama min mata ba 'yar wajen sa d'ayar fatima ya bani." Hmm ta sauke ajiyar zuciya ba tare da tace komi ba dan ita gani kawai take an raina musu wayo ganin tayi shiru yasa ya cigaba da fad'in " shi yasa nake so kije ki sameshi a bar maganan nan da zuwa wasu 'yan shekaru dan ni ganin k'ak'antar yarinyan nake a bari zuwa ta gama secondary nima kafin nan na d'ora karatuna sai a ga abinda Allah yayi" yayi shiru ya zuba mata idanu yana me addu'ar Allah yasa ta yarda da hakan hikimarsa tayi hakan shine watak'ila in aka bar maganan zuwa wasu shekarun la Allah su daidaita ko kuma kowa ya had'u da abokin rayuwarsa a gaba danshi sam son da yake yiwa yarinyan na 'yan uwantaka ne toh ya ma zai iya mata wani so bayan nan yarinyan da take 'yar mitstsiya baya tunanin ko nono ta ajiye a k'irjinta, sai dai ina adu'arsa bata ci ba dan bud'en bakin hajiyar tasa sai cewa tayi " lallai kuwa Hauwa taci riba akaina ai haka take so uwar tasu dabarar ta kenan ai kaga itama wancan d'in in ta k'ara girma sai a hure mata kunne watak'ila ma ta nemi had'ata da wani birom d'in ko wani k'abilan nan cikin jos d'in ba dai aurene bata so y'ay'anta suyi a zuriyarmu ba ai kaman anyi an gama dan bazan yarda a wani d'au lokaci ba za ayi abinnan duk da ba wani son wancan yarinyan mai kama da zuriyar masu k'ananan ido nake ba dan yarinyan akwai falli in tace zata zo ta min halin uwarsu ni casa shegiya zanyi."

Rintse idanu yayi ya mik'e ya fice a palon ba tare da yace mata komi shi bai san ranan da hajiyarsa zata daina masifar ba gaira ba dalili ba ko me mamansu fatee tayi mata oho to ita fatin me ta tab'a mata dan dai kawai itace shugaban masifafun Bauchi tsaki yaja yana since kayan shi dan shiga ya watsa ruwa.


💖💖💖💖💖💖💖💖

Zaune suke a gaban mahaifansu inda baba yake magana da adeeja ya fara " ki gayawa shi manemin naki kwanaki 14 na bashi ya turo magabatanshi in ba haka ba kar in k'ara ganin ya kiraki a waya dan ni ban son harkar yaudara nayi bincike a kansa duk abinda kika fad'awa mamar taku a kanshi gaske ne saboda haka yanzu shi mike jira a tsai da magana nayi waya da hajiya zata zo ke kuma" ya juya kan fatima " na san ke kam d'iyace me biyayya na san komi na yanke a kanki ba za ki ban kunya ba shi yasa na yanke shawara akanki ba tare da ko mamanki nayi shawara ba saboda na san na isa dake" gabanta ne yake lugude yayin da ita adeejan duk ta muzanta dan ta san gugar zana yake mata duk da bata san me yake shiri faruwa da y'ar uwarta ba.

A cikin tsakiyar kanta taji yana cewa " na ba da auranki ga d'an uwanki sagiru" a firgice ta d'ago da kai sai kuma ta mayar da kanta k'asa tuno irin yabon da mahaifinsu ya mata kafin ya furta musu zance adeeja kam jin zancen tayi banbarakwai sai abin ma yaso bata dariya har sai da ta murmusa wai dole ne sai ya auri 'yar gidansu" baba ne ya cigaba da yiwa fatima nasiha ita kam sai hawaye take wanda ta rasa dalilin zubar hawayen dan ita baza tace tana k'in yayansun ba amma ita sam bata mishi soyayyan aure kukanta ba zai rasa nasaba da ya makomar karatunta yake ba wai shin ita dukka dukka shekarunta nawa da za a kinkimo mata magana aure anya baba na lissafin shekarunsu kuwa? Haka tayi ta sak'e saj'e har baban ya gama maganarsa ya sa musu albarka ya fice.

Mama ce ta matso kusa da ita tare da dafa ta d'ago kanta tayi wasu hawayen na zubo mata hannu maman ta sa tana goge mata hawayen tare da furta " Saahyu ra pfenda daramo( kiyi shiru kiyi abinda babanki yace) kinga in kika k'i y'an uwanku ni zasu zarga suce na hanaku aure a zuriyarsu a gabanki ranan hajiya ta kirani a waya tace ko nak'i ko na so ku yaransu ne kuma dole suyi iko daku dan basa yiwa yaransu auran dolene da ba abinda zai hana baba karami ya auri adeeja sai kace nice na hana adeeja ta aureshi kece yanzu zaki wankeni ki daure ki auri zab'in su zaki ji dad'i wata rana kinji" fad'awa jikinta tayi tana kuka tana fad'in ni ba wai bana so bane is just too early kaman kuna manta shekaruna i am just 15 years for goodness sake mah ko ina fulani i am not living like one is high time a daina wannan auran wurin(shekaruna 15 fa dan Allah ko da nake fulani ai bana rayuwa kamar bafulatana lokaci yayi da za a daina auran wuri)" gyad'a kai maman tayi tace " dagani har ke bamu da choice a gabanki yace baiyi shawara dani ba ya zartar da hukunci sai mu zuba musu ido Allah yayj zab'i ke dai ki daure ki bisu zaki ji dad'i ni na tabbatar miki da haka duk wanda yaji maganan iyayenshi ba ya tab'ewa zaki ci *ribar biyayya"* kad'a kai tayi tace" na miki alk'awarin ni kuma zan muku biyayya ko dan in wankeki a wajensu" murmushi mama tayi tace na gode 'yata Dagwi an nonwo wen homa neimo niraho (Allah ya miki albarka ya sa kema yaranki su biki) ameeen.


















SAWWAMA QAWWAMA😘
💖RIBAR BIYAYYA💖







By Sawwama A.







Page 5.







Hajiya tazo tare da baffannin su da kuma yayyun sageer da suke gari maneman auran adeeja sun zo an tsai da aure wata biyu dan baba ya rantse ba zata kuma yi mishi shekara a gida ba tunda ita bata jin magana taje can ta k'arata in mijin yaso ya mai da ita makaranta. Sageer da fatima kuma an tsai da magana da zarar ta gama jss3 bayan sallan azumi kenan hakan ya kawo cecekuce a cikin anguwa da dangin mama inda ake ganin an shiga hakkkin yaran har wani wan maman ke barazanan maka su a kotu sai da mama da ngo suka yi jan ido tukun wanda hakan bai tsirar da maman daga shan zagin hajiya ba tattas ta wanketa wankin babban bargo.

Bayan tafiyarsu hajiyar adeeja ta shigo d'akin inda ta tarar da teema na ninke kayan da ta wanke musu ( dan tunda taji su hajiyar zasu zo ta gudu daga gidan kar ta sauke mata kwandan bala'in tak'i d'anta) dariya ta kwashe dashi tace "su amarya manya tare da angon aka zo ne banga kina farin ciki ba 'ya mai biyayya ki zauna a kashe miki rayuwa wai ke zaki faranta ran iyayyenki toh bari in gaya miki ki shirya kamuwa da yoyon fitsari tunda kika zab'i aure a wannan shekarun kina samun cuta ya sakoki dan halin 'yan Bauchi kenan in bai sakeki ba ya k'aro aure another halinsu kenan ke kuma kin zama rajab ya tsufar da ke saboda nuk'urk'usa a daidai lokacin da nake shan love da hameed d'ina."

Bata kulata ba sai da tagama adana kayanta har da na adeejan tace " adda adeeja ni yanzu kin daina ban mamaki sai tsoro kin koma kamar ba musulma ba kin kasa yiwa iyayenki biyayya ni da nake k'ok'arin yi musu kina neman ki hure min kunne ta hanyan tsoratar dani wai kam kina tunawa da cewa mama kike sawa a matsala duk wani hali da kike yi? Ba abinda masifafiyar matar nan ke cewa da ya wuce kin zuqa kafirci a nonon uwarmu wanda ita mahaifiyar tamu ba a haifeta a kafirci ba sai dan kawai tana ansa suna yaren birom shikenan ake dangantata da kafirci kema kuma kina taimaka musu wajen b'llo da wasu halaye baki tsaya a iyakan k'in musu biyayya da tsoratani ba har mugun baki kike bina da shi a matsayinki na 'yar uwata wallahi ki kama girmanki tun kafin ya fad'i dan in ya fad'i ba abinda zai hanani hawa in tattakashi har da tsalle."

Shak'ota tayi tana nufin jibgarta mamansu ta shigo ta fizgeta a hannunta tace " kar ki yarda ki tab'a min yarinya ke in ba kya tausayina ita tana sona tana tausayina ace kece babba sannan kuma kece ba ki da hankali Allah ya wadaran halinki hadija" ta ja hannun fatima suka barwa adeeja d'akin.

💖💖💖💖💖💖💖💖

Asalinsu mutanen Bauchi ne malam salisu shine mahaifinsu yayinda inna sala itace mahaifiyarsu su biyu tak ne a wajen mahaifansu Hadiza itace babba ratan shekaru biyar ne tsakaninta da k'aninta mustapha suna k'anana iyayensu suka rasu sakamokan gini da ya fad'o musu sanadiyar ruwan sama da aka tsuga a lokacin yaran sunje gidan k'anin babansu baffa umaru.


Dole rik'onsu ya koma wajen baffan nasu da fari matar baffan ta so gwada musu mugun rik'o kasancewar hadiza yarinya ce me shegen tsiwa da masifa yasa ta shafawa kanta lafiya hadiza na gama primary aka hankad'ata GGC kafin madaki inda ta bar k'aninta wajen matar baffa tana azabtar dashi shima yana wayo ya k'arbarwa kanshi 'yanci.

Ranan da hadiza ta gama aji uku ana speech and price ta lashe mafi yawan kyautuka cikin manyan bak'in da suka zo alhaji musa ya nuna yana sonta bada jimawa ba aka sha biki ta tare a gidanta inda take rik'e mishi da yaransa maza biyu da matarsa ta mutu ta bari.

Haihuwarta biyu duk maza salis da mustapha alhaji musa ya sami aiki a america suka tattara suka koma can ba yanda bata yi ta tafi da k'aninta ba baffansu yak'i yace baza a d'aurawa bawan Allah nauyin da ba nashi ba can ta haifi salamatu da sagir mai sunan baban mijinta.

Shi kuma mustapha bayan gama secondary d'inshi ya sami gurbin karatu a university of jos inda yake karantan mechanical engineering yana shekara ta uku aka kama wani da satan ansa aka mishi cune aka koreshi. Bai gayawa kowa ba ya kama kanikanci a gada biyu nan ya had'u da hauwa yarinya birom cikakkiyar musulma ce gaba da baya sai dai zuriyarsu na cakud'e da marasa sallah baffa ya shige mishi gaba aka yi aure yayarsa cr ta had'o mishi lefe daga can ta aiko baffa shi ya hana a gayawa hadiza k'abilar da mustapha ya jajub'o kasancewarta mai kishin yare da addini.

Dawowarsu nigeria kuwa ba k'aramin artabu akayi ba dan fushi tayi da k'anin nata sosai wai k'aninta ne da aure wata k'abila har da rabon y'ay'a biyu lokacin shekarun fatima bakwai lokacin ne tazo da dukka ya'yanta gidan mustapha zuwa sagir na farko kenan yana d'an yaronshi ba k'ara zuwa ba dan shekarar ya shiga jami'a b'angaren k'iyayyar da hadiza ke yiwa hawwa kuwa sai abinda ya yi gaba.
Wannan kenan.





SAWWAMA QAWWAMA😘
💖RIBAR BIYAYYA💖






By Sawwama A.







Page 6.








*Alhamdulillahi Ina mai mutukar nuna farin cikina hakika baka sanin masoyanka sai abu ya sameka na gode muku masoyana Ana mugun tare irin sosai din nan*




_Na manta a dalilin mutuwar alh musa ne yasa haj hadiza_ baro us






***** ******* *****

An tsai da ranan auran adeeja watanni biyu kacal Dan baba ya dage bazata karasa makaranta ba tunda ita bata ji.

Fatima da sagir kuma an yanke bayan sallan azumi dai dai da ta gama jss3 kenan watanni shida nan gaba kenan.

Adeeja da hameed sunfi kowa farin ciki cikar burinsu duk da adeejan na tausayawa yar uwarta halin da ake shirin jefata na aure da wuri sannan ga masifaffiyar uwar miji ga neman iliminta da ake shirin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login