Showing 3001 words to 6000 words out of 59418 words

Chapter 2 - Farhat Complete Hausa Novel

14 Jul 2025

4127

lokaci daya kaman ita ba yana ganin ta shige ciki shima cikin sauri ya Mara mata baya.koda ya shigo rarraba ido yake ina zai ganta?can ya hangota wajan kayan kwalam tana ta kwaso ice cream murmushi ya saki yana kara godewa Allah da yafito yau gashi yayi gam day katar.

Saurayi ne kakkyawa fari kal dashi ga quality kana ganin shi kasan ya gama hadewa.yana biye da ita Tana gama Kazan ice cream ta wuce arean su chocolates nan ma tayi ta kwasa,pizza da shawarma suma baya manta dasu ba.

tazo wuce ta arean kayan maza Nan ma yaga ta tsaya ta kallon wani wrist watch na zallan azurfa mai Dan karan kyau sai kyalli yake hannu tasa ta dauko tana kallo da kyau can kuma tayi murmushi ta jefa a cikn kayanta ta nufi wajan biya.bayan an zuba mata kayan a ledoji ta fito da pos dinta tana jiran a fada mata bill ta biya,maimakon a fada mata sai ma wasu ledodin aka karo mata shake da kaya akace wani ya biya mata kuma shi yace abata sauran kayan.

Idanu ta kwakwalo tana kallon Wanda ya dage yake mata bayani take.wai kaman ita har wani kazamin zai Iya biya msta kudi ?yau wai ita farhat yar gatan abbanta aka mayar poor bagger.kankance ido tayi alamun masifa kana tace"waye shi kuma ina yake ?nuna mata yayi ya juya cikin sauri ya bar wajan dan kar and hada da shi sbd sarai sun Santa gaba da baya

Inda aka nuna mata ta kalla yana tsaye rungume ds hannuwansa a kirji yana jifanta da murmushi,a hankali ta fara har zuwa inda yake tsaye kallon wulakanci +na tsana take aika masa Dan a rayuwa ta tsani namiji fari wai bleaching suke(nace su farhat kodai anawa mutane hassada sbd ke blacky ce)

Tana karasowa gaban shi ba tayi watawata ta dauke shi da lafiyayen mari tare da watsa masa kayan gaba daya a jiki.jikunta har wani rawa yake tsaban masifa ta nuna shi da yatsa tace"kai jakin inane ko ince mai fish brain if not ka dubi kaman ni kace zaka biyawa kudin shopping? Do u know who i m"tace tana nuna kanta wai yau ita za a mayar poor bagger? shi kam kuri ya mata da ido yana kallonta Dan bai taba tsamanin akwai mutane irin wannan ba a duniya masu mai da alkhairi ya zama sharri.kamin ya Ankara sai ji yayi ta watso masa bounds na dubu dubu guda 2 suka watse a jikin shi ta juya a zuciye ta fice a mall din.ba tare da tabi kan kayan da ta saya ba.

Kunya takaici duk suka yi masa dirar mikiya tare da wani irin tsananta da ya darsu a zuciyarsa wai waye ubanta a garin da har take da guts din yi masa irin wannan wulakancin ?shima haka ya fice kaman zai tashi sama ba tare da yayi abinda ya kawo shi tare da kisinsina abubuwa dayawa aranshi.
[11/15, 8:13 PM] Ummee Yusuf: 💥🔥💥🔥🌹🌹


FARHAT


💥💥🔥🔥🌹🌹
Written by Ummee Yusuf (maman Yusuf)


Page 9


Horn take ta dannawa tun kamin ta karaso,ba madu mai gadi da gudu yazo ya bude mata wagegen gate din danna hancin motan ciki tayi tare da nufan parking lot.fitowa tayi a fusace ba tare da ta gyara parking din motan ba,hanyan parlour ta nufa tana zuwa baking kofan parlourn ta dai daita natsuwarta dan bata son ammin ta ta gane halin da take ciki.

Sallama tayi amma ba kowa a parlour sai kamshin girke girke dake ta tashi.direct kitchen ta wuce inda ta tarar da ammi tare da sauran yan aikin gidan suna ta aiki ."farhat har kin dawo"?ammi take tambayanta bayan sun amsa sallamar da tayi musu"na dawo ammi but naga har kunyi nisa da aiki"tace tana karasa shigowa kitchen din "eh mun kusa kammalawa just go nd freshen Up"Dafa kitchen cabinet na gefenta tayi tana cewa kai kamshin abincin nan ya cika gidan nan,wai me da me kuka girka ne ammi?"farhat tace tana kokarin bude warmers da ta gani jere a kan table din kutchen din."kar ki bude min warmers his favorite me a ciki"ammi tace tana wanke hannuwan ta a sink"kema kin san abban ki yafi son abincin gargajiya,toh shi nayi"yatsina fuska tayi tace "oh no! I dont knw y abba ke son irin wannan abubuwan gaskiya i cant eat this ammi",kallonta ammi ta tsayayi na wasu sec sannan ta girgiza kai tace"kina da aiki farhat kar allah sa ki iya cin mana cikin ki ko nawa?kwabe fuska tayi kaman zatayi kuka tace "pls ammina...."toh naji nayi fried rice wit peped chicken ko shimaba kya ci?"washe fuskan tayi tana dariya tace "zanci wannan bari inyi wanka b/f jirgin su ya sauko.

Ladi ta kwalawa kira ta same ta tana kokarin cire kaya" ke meye haka ban hana ki shigo min daki ba sallama ba "baya ladi tayi dan tasa ba karamin aikin ta bane kai mata bugu"kiyi hkr hjy nayi sallama baki ji bane"tsaki farhat taja tana mata wani mugun Kallo"Dallah ni zo ki min abinda yasa na kira ki"jiki na bari ladi tazo ta bayan ta ta zuge mata zip din riga sannan ta fice ita kuma ta shiga wanka.

Atampa tasa na super sharaton dikin dogon riga blue da touch din white jiki,light make up tayi amma abinka da kyakkyawa tayi kyau sosai.white veil ta yafa a kanta ba tare da tasa dan kwali ba.perfumes designers ta feshe jikin ta dasu,Tana dada gyara veil din kanta taji ammi tana kwala mata kira a palourn kasa.amsawa tayi ta dauki phones dinta ta zira wani hadadden white high hill shoe kaman yanda ta saba sannan ta fito da sauri tana cewa "gani ammi na shirya"kallon yanda take sauri ammi tayi tace "sauko a hankali mana ko kin manta irin takalmin da yake kafan kine?no! Ammi ai kema kisan na saba da hill shoe tun ina yarinya"tace tana wani shagwabe fuska"uhum toh naji wuce muje time is running.gaba tayi itama cikin shiganta na alfarma yayin da farhat ta mar mata baya.driver na ganin haj kaltuma ya taso cikin ladabi ya iso gabanta ,tace "bala yi sauri airpot zamu jentaran ALh kar mubb makara ko?toh hjy",yace ya juya cikin sauri ya dauko wata fitananniyar mota suka shiga suka kama hanyan airpot

Lokacin da suka iso airpot sun tarar har jirgi ya sauka
dan tsakanin new g r a da airpot akwai nisa.wuri suka samu suka zauna suna jiran fitowan su ,basu fi minti 10 da zama ba passingers suka fara fitowa.farhat sai baza ido take taga abban ta ,aiko can ta hango shi da gudunta ta isa wajan shi ta rungume shi,ahima cikim tsananin farin ciki yasa hannu ya rike ta yana dariya yace "mamana yaushe zaki girma ne uhum?"itama cikin daryan tace "ni kullum a wajan abba na baby ce"dariya abba ya kara yi kamin yace wani abu har ammi ta karaso wajansu,itama cikin farin ciki take ma mijin nata sannu da zuwa.wani kyakkyawan saurayi ta gani wanda a kalla bazaifi 25years ba fari kal dashi ga gashin kansa baki tsidik ya kwanta lub lub dashi.karasowa yayi tare sa cewa "ammi mun same Ku lafiya"fuskan ta dauke da mamki take kallon sa ,da yatsa ta nuna shi tace "FARHAN"?da alaman tambaya.murmushi yayi ya sunkuyar da kansa kasa,abba ne yayi dariya yace "ashe zaki gane shi"itama cikin dariyan tace "haba alh taya zan manta dashi?kawai ku zo mu karasa mota"a tare suka kama hanya yayin da farhat har ta tsufa a wajan mota ita da driver yana saka kaya a boot.shiga motan sukayi abba da ammi.ita kuma farhat tana kokarin bude seat din gaba taji abban ta na cewa"zo nan mamana ki barwa yayan ki can din.sai a sannan ta lura da wannan kyakkyawan guy din ,suna hada ido a sai da zuciyar su ta buga a tare.
[11/16, 8:37 PM] Ummee Yusuf: 💥🔥💥🔥🌹🌹

FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹


Written by Ummee Yusuf(Maman Yusuf)

Wannan shafin naki ne Hafsat SHEHU,INA gdy da kaunar ki gare in da yanda kika karfafam min guiwa.ina yin ki sosai Allah ya bar kauna.

Page 10

Kasa dauke idon ta a kansa tayi,shine ya janye nashi idon tare da karasowa inda take.tsaki taja a ranta tana mai jin haushin kanta ko menene nata na zuba mishi ido har yana wani dauke kai.wani tsiriri tsakin ta kuma ja ta bashi hanya,tana me cigaba da mita a ranta halin iyayen ta na jan talakawa a jiki.duk inda zai je ba zaka raba shi dasu ba,ba wayan da take jin haushi kaman wayan da suke zuwa abroad karatu da alama shima daga can yake.sai wani ji da kai yake kaman dau kudin uban sa yayi karatun.sauran talakawan in sun dawo har wani girma suke bata na musamman amma shi wannan har wani dauke kai yake.hararan keyar sa tayi ta madubi tare da yi kwafa wanda har ya fito fili "lafiya dai mama na"?abban ta ya bukata,ba komai abba"tace tana juya kai.

Ko parking bala bai gama ba,ta fiti da saurinta ta sgige ciki dan bata son kara kallon wannan mai kama da sadaka yallan.ammi ce tabi ta da ido tana cewa"bansan ranan da yarinyan nan zatayi hankali ba"abba ya hada rai yace "ah ah kar ki takura min uwa baki san uzurin ta ba"ammi gani yanda ya hada rai yasa tayi shiru,tasan tunda ya dawo kuma shagwaba sai abinda ya karu.farhan yana jin su baice komai ba sai murmushi da yake "muje ciki mana son"abba yace tare da riko hannnun sa,suka yi cikin palour suka zazzauna cikin manyan kujeru na alfarma.nan aka kara gaisawa"ku fara watsa ruwa ga abinci na jiran ku"ammi tace.mikewa suka yi abba yayi sama,ita kuma ammi ta kai farhan wani hadden daki anan cikin palourn.tana masa murmushi tace "ga dakin ka nan son,go nd freshen up muna jiran ka dinning ko?"godiya ya mata sannan ya shiga cikin dakin.kallon dakin ya tsaya yi komai neat kuma ya hadu komai na dakin brown nd milk colour.sosai dakin ya birge shi saiu kamshin turaren wuta ke tashi.murmushi yayi yana jinjina karamci irin na abba da ammi ba ruwan su kowa nasu ne tsabanin yar su da ya gani alamun kanta na hayaki.tabe bakin sa yayi tarebda cewa"ina ruwa na ma da ita.kayan jikin sa ya rage sannan ya shiga bathroom,nan ma komai neat.wanka yayicikin minti 10 ya fito daure da towel daya kuma yana goge gashin kansa mai matukar laushi da tsanti.trollyn kayan sa ya bude ya fito da kayan da zai sa,bayi amfani da kayan da ya gani a gaban mirrow ba.nashi yayi amfani dasu,shiryawa yayi cijin dark blue t-shirt da black jeans ya feshe jikin sa da perfumes sannan ya fito parlour.

Dukkan su uku ya tarar akan dining suna jiran sa,cikin sauri ya karaso yana basu hakuri.murmushu kwance akan fukan su ammi tace "haba son ba komai ai"farhat kuwa ta cika tayi fam saura kiris ta fashe,an hana ta cin abinci akan wani banza can ,ya shanya mutane shine har ake wani ce mai ba komai?dago kai tayi aiko karaf suka hada ido wata muguwar harara ta balla mai.shi kuwa dariya ma abin ya bashi dan haka sai da ya murmusa."me za a zuba maka son"?ammi ta bukata bayan ta zubawa kowa saura shine kadai bata zubama ba.plate din abba ya kalla ya gani shake da tuwon ndalayi da miyar danyen kubewa yasha man shanu ga naman danderu shima tururi.na ammi kuma kisire ne shima da miyan danyan kubewa"ammi a zubs min tuwon ndalyin dan nafi son abincin gargajiya"yace yana murmyshi "toh"tace ta fara zuba masa,kowa yana cin abincin sa hankali kwance banda fsrhat da take ta juya spoon tana zancen zuci,"dama dan qauye dai dan qauye ne in ba haka ba duk zaman da yayi a abroad ya dawo ya bige da cin tuwo?ita wlh haushi ma yake bata wai ammi ko wani jill nd jerk take kira da son.tsaki taja ammi tace"lfy kike ma mutane tsaki?baki na ne ba taste" tace dan tasan in ammin ta tasan abinda take ma tsaki toh in ranta in yayi dubu sai ta bata mata"ke dai kice abincin ne ba kya son ci dama"ammi tace tana hararan ta.abba ne ta katse ammi da cewa "kyale min uwa ta,me kike son ci mama na?"cike da shagwaba tace "abba ni ice cream zan sha amma kullum ammi sai ta hana ni kuma......yau abban ki ya dawo tashi kije ki sha na kawo miki favorite choculates dinki.

Ko Yaya zaman farhat da farhan zai kasance a gida daya
[11/17, 8:06 PM] Ummee Yusuf: 🔥💥🔥💥🌹🌹

FARHAT

🔥🔥💥💥🌹🌹


Written by ummee yusuf(maman yusuf)

Wannan shafin sadaukarwa ne gare ki,Godiya da jinjina gare ki UMMi GARKUWA marubuciyar ummi allah ya kara basira.


Page 11


Mikewa tayi cike da happy har da Dan tsallen murna"u re d best dad in d word"tace tana karasawa wajan fridge Dan daukan ice cream,palour ta wuce cikin jin dadi ta zauna sha.

Parlour n suka dawo suma bayan sun kammala suka samu waje suka zazzauna,farhat kuwa had yanzu ice cream dinta take sha cikin kwanciyan hankali tana kallon wani film a MBC 2.gyaran murya Abba yayi alamun zaiyi mgn mai mahimmanci,duk suka maida hankali gare shi.kallon farhat yayi yace"mama na Ga Dan uwan ki nan Baku gaisa ba kuma zai zauna damu na kwana 2"taji haushi zama da aka ce zaiyi a gidan su,amma ta kudirta a ran ta da kafar Sa zai bar musu gida cos she promised herself to make his life miserable.

Zamewa tayi kadan daga kan kujera cike da ladabi tace"Yaya sannu da zuwa ya hanya"?kusan daskarewa farhan yayi a wajan cos karara yaga tsantsan kiyayar Sa a idon ta but Ga yanda take yi masa mgn harda ladabi?da kyar ya saita natsuwar shi ya amsa mata da "lafiya lau kanwata ya karatu"?dariya tayi cikin zuciyan ta na ganin mamaki karara a fuskan shi,a ran ta tace baka Ga komai ba in dai nice."lafiyau alhmdllh" ta amsa tana gyra zamanta a kan kujera.

Abba ne yacigaba yace "yanzu ka huta na kwana 2 sai muje kaga company ko"?"toh abba duk yanda kace haka za ayi,nagode sosai Allah ya saka da alkhairi"Ameen"abba da Ammi suka amsa cikin jin dadi."zan shiga in Dan huta abba"yace yana mikewa "toh son a fito lafiya"Ammi ta amsa mishi.

Takaici kaman ya kashe farhat,tana bakin cikin abban ta ya tura shi abroad karatu kuma kasan da tafi so,yanzu kuma harda wani wai za a bashi aiki a company.tsaki taja"I hate poors,they all baggers"tace tana tashi a palour dama ita kadai ta rage.

Koda ya Shiga dakin kwanciya yayi akan bed Dan ya huta amma sai tune tune da kuma yanda zaman Sa zai kasance a gidan,har aka kira la asar.alwala yayi ya fito palour amma ba kowa,direct masallaci da ya gani a kofar gidan
ya fito sukayi sallah.tare suka shigo da abba cikin gida.

Farhat ce kadai a parlourn tana zaune akan 2 seaters ta daura kafafun ta akan handle din,tana chat dash ramlat tana lbrn abban ta ya kawo Sabon poor bagger mai jiji da kai.d worst part kuma wai a gidan zai zauna for 2days."just teach him a lesson"suka ce mata."sai kace ba starn Mu ba har akwai Wanda zai Iya Sa mini headache?"kuma kunsan hali na I don't tolarate nonsense, I know how to deal wit him"Sallama da sukayi ne ya katse mata charting da suke,amsawa tayi tare da dago kanta tana yiwa abban ta murmushi.zama suka dukan su,ganin harda farhan ya sata mikewa tare da yin hanyan sama"mama na ina zuwa ne, ba zaki zauna muyi hira ba?"abba yace mata .juyowa tayi ba tare da ta dawo ba tace"abba sallah zanje inyi"abba yace assha ba kiyi sallah ba,kika zauna latse latse a waya?yi maza ki je kiyi kar lokaci ya wuce".toh Abba" ta amsa ta karasa haurawa.a zahirin gaskiya tayi sallahn kawai zama da poor bagger ne bata son yi.


Har dare basu kara haduwa Dan ko cin abinci kin saukowa tayi,kwanciya tayi tana charting da frnds din ta har tayi bacci.

Koda washe gari,kwanciyar ta ta karayi bayan tayi sallahn asuba.

Sai kusan 7:30am ta tashi,tasa kayan sports din ta.Karamain Riga pink colour da wando 3quater fari kal da facing cap shima fari.tayi parkng din gashin kan ta a tsakiya in a pony style jelan gashin ya fito ta bulin hulan yana reto a bayan ta.wannan al adar tace every weekend sai tayi wasan basketball cos tana bala'in son game din ,dalilin haka abban ta yasa aka fitar mata da katon fili a gefen garden din gidan.

Fitowa tayi parlourn kasa,bakowa kaman yanda ta zata sai ladi kadai da ta tarar hannun ta rike da wani karamin tray ta daura lemon
juice da table water masu sanyi da cup din glass.sai wani karamin farin towel a gefe.

Wucewa tayi abin ta ba tare da tabi ta kan ladi da take Haida ta ba.

Filling basket ball din isa ,ba bata lokaci ta fara wasan ladi kuma tana gate tana kallo.

Farhan duk kadaici ya ishe shi,abba da Ammi suna kokarin su na Jan shi a jiki amma ya kasa sakin jiki dasu.

Fitowan shi daga wanka kenan,shafe jikin sa yayi da lotion masu kamshi sannan ya shirya cikin polo shirt brown da ratsin fari.jeans yasaka shima fari kal, gaban Mirror ya tsaya yana combing gashin kan sa bayan ya shafe su da mayukan gashi. Turare kusan kala 4 naga fesa bayan body spray da yayi amfani.wow gaskiya farhan ya yadu.

Wajan windo yazo ya yaye curtains din ya juya,waiwayowa yayi da sauri ganin yanda farhat take ta wasan basketball duk ta hada gumi.

Baisan minti nawa ya dauka nan tsaye ya kallon taba Dan ya shagala sosai.

Knocking kofan dakin Sa da akayi ne ya dawo dashi hayyacin Sa,murmushi yayi yana shafa gashin kan Sa yace"crazy gal"kofan yaje ya bude,mai aiki ya gani tsaye.

Tana ganin ya bude tayi saurn dukawa ta gaishe shi tare da sanar dashi Ammi na kiran shi."toh"yace kawai yabi bayan ta.

Yana tafiya hankalin shi na kan agogon sa da yake Daurawa a wrist din shi.farhat kuma shigowan ta kenan ,hannun ta rike da farin towel tana goge gumin fuskan ta.ji tayi,tayi karo da mutum,dagowa tayi cike da bacin rai taga wani mai tsautsayin ne da wannan gangancin Dan ta dauka cikin Yan aikin gidan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login