Showing 30001 words to 33000 words out of 59418 words

Chapter 11 - Farhat Complete Hausa Novel

14 Jul 2025

4217

ba ya tashi ya fice daga dakin ya sauko kasa wajan ladi dan karba mata abinci dan mantawa yayi bata son drugs.ya tarar still dan mugunta ladi tuwon ta karayi da miyan kubewa.

Tambayan ta yayi ba wani abincin ne sai wannan tace masa akwai peppe soup din kayan ciki.nan yace ta zubo shi din kuma daga yau kar ta dafa tuwo tunda farhat bata so.toh kawai tace ta zubo musu a wani warmer mai dan girma ta daura a tray.plates da spoons ta saka masa sannan ta miko mai,fridge ya nufa ya daukojuice da ruwa ya kara akai sannan ya nufi dakin ta da kayan.

Tana zaune a inda ya barta sai dai ta daina kukan,ajiyr trayn yayi agaban ta sannan ya zuba mata a plate ya tura mata gaban ta.ba musu ta karba ta fara ci a hankali,ta ci dayawa cos dama yuwan take ji.

Ruwan zafi da towel ya dauko a bathroom yazo dan gasa mata kafan dan da gani bata gasa ba dazun.towel din ya tsoma a ruwan zafin tare da matse dan ruwan sannan ya fara gasa mata.kuka ta fara tana rike masa hannu,ganin zata bata mishi lokaci yasa ya cire jallabiyan jikin shi a ajiye sannan matse ta a kirjin shi da hannu daya sannan ya samu daman gasa mata sosai.


Sake ta yayi ya dauko maganin shafawa,shima saida ya matse ta sannan ya shafa mata.

Dariya ne ya kwace masa yana yi yana nuna fuskan ta da yatsa da yayi daga daga da hawaye da majina.sai da yayi mai isar sa sannan ya tsagaita.ita kuwa har yanzu bata daina kukan ba tanayi tana hararan sa.drugs na sha ya miko mata,girgiza kai tayi maimakon ta karba."zaki karba ki sha ko kuma yanzu in danne ki kuma in kara matse kafan"jin haka yasa ta karba ta sha tana yamutsa fuska.

Dariya ya kara yi yana kallon ta,zuciya ne yazo mata wuya bayan matse ta da yayi ya mata mugunta kuma ya sata agaba yana mata dariya kaman yaga mahaukaciya?


"Wani kalan salon wulakanci ne zaka wani sani a gaba kana min dariya?"tace tana hararan shi.bai amsa mata ba ya mike ya dauko mata karamin madubi ya kawo dai dai fuskan ta.bata san lokacin da dariyan itama ya kwace mata ba ganin yanda majina da hawaye suka bata mata fuska.

Yana taya ta dariyan ya dauko tisue ya miko mata,karba tayi tana goge fuskan ta har yanzu murmushi bai bar fuskan ta ba.

Kallon ta yake cikin wani yanayi dan bai taba ganin ta tana dariya haka ba sai yau,dan haka ba karamin kyau tayi mishi ba.

Sukuyar da kan ta kasa tayi ganin irin kallon da yake mata kuma yana zaune ne daga shi sai vest da short neaker.ba zata iya misalta yanayin da take ciki ba amma she feel so comfortable being wit him.

Wall clock dake manne a bagon dakin ya kalla yaga har 10:20pm,dawo da kan sa kasa yayi yana ayyana ina ma su dawwama haka.


"Ermmm kinga time ya tafi bari in taimaka miki kiyi brush ki kwanta ko?"yace yana kallon ta.kan ta akasa tace"to"a hankali.

Tashi yayi ya dauke ta in a bride style ya fara tafiya a hankali kaman baya so.idon ta a rufe ruf tana shakan kamshin jikin sa da take matukar so.wara ido tayi da sauri jin sun shigo bathroom din dan bata manta yanda dazu ya dugurar da ita ba. dan dariya yayi yace mata"relax baby"cikin murya kaman mai rada. ajiye ta yayi hankali" kar kiyi abinda kikayi dazu kimin magana in kin gama"yace bayan ya miko mata duk abinda yasan zata bukata sannan ya fita tare da rufe mata kofa.

Jingina yayi da jikin bango yana jiran ta.can yaji tace"farhan na gama".murmushi yayi ya shiga ba tare da ya amsa ba.


Kwantar da ita yayi akan gado a hankali,kara mata karfin ac yayi tare da kashe wutan dakin ya bar mata side lamp sannan yaja mata bargo ya rufe mata rabin jiki.har ya juya zai fita ya dawo ya manna mata peck a goshi ya fit da sauri yaja mata kofa.

Idon ta a lumshe tana maida numafashi da sauri da sauri,hannun ta ta dora a goshi inda yayi pecking din ta,bargon taja ta rufe har fuskan ta,tana murmushi.
[12/9, 6:19 PM] Ummee Yusuf: 💥🔥💥🔥🌹🌹

.FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹


Written by Ummee yusuf
(Maman yusuf).


Page 39~40

Jingina yayi da jikin kofan dakin ya lumshe ido,ya kasa koda daga kafa balle tafiya. inama zata yarda su kwana daki daya?.da kyar ya daure ya kai kansa part din sa,

Wanka ya karayi waiko zai samu sassaucin abinda yake ji.shirin kwanciya yayi cikin white pyjamer sannan yabi lafiyar gado.

Bacci ya kauracewa idon shi dan da zaran ya rufe ido yanayin su na dazu yake gani.ya dade yana ta juyi amma baccin yaki zuwa.shima mamakin kan sa yake dan tunda akayi auren su bai taba jin son kasancewa da ita ba irin yau.

Alwala ya dauro ya fara nafila dan samun sauki.bai hakura ba sai da yaji idon shi suna rufswa saboda bacci sannan ya bi lafiyar gado.mikewa daga kwqncen kaman an mitsine shi yayi hanyan part din farhat dan ya kara duba ta kamin yayi bacci.

Farhat kuwa tunda tasa kanta cikin bargo ta kasa fitarwa sai murmushi take.can ta daure ta fito da kan ta ta lumshe ido da niyan bacci,sai ganin farhan tayi zai kara pecking din ta.bude ido tayi taga bakowa dakin sai ita kadai.tsaki taja tana jin haushin kan ta,cos tun ranan da ta dora ido a kan farhan bata taba kwanciya bacci ba tare da tayi tunanin shi ba.a lokacin dai tasan tunanin yanda zata kuntata mai ne ko kuma tanda zata kore shi a gidan su.amma yau ta rasa wani tunani take yi a kan shi yau.

Kallon agogo tayi taga biyu saura,cike da jin haushin kan ta tayi wani irin juyi wanda sam ta manta da rashin lafiyan kafafun ta.gum taji ta buge kafan da bango,wani irin radadi ciwon ya fara kuka ta saki tana jan allah ya isa ma farhan gashi ko tunanin shi tayi itace a wahala.

Tun daga parlourn ta yake jin kukan ta,da sassarfa ya karaso cikin dakin sannan ya kunna wuta haske ya gauraye dakin.

Hango ta yayi can karshen gado tana ta kuka,karasowa yayi yana tambayan ta ko kafan ne ya hana ta bacci,ko kala bata ce masa saima dauke kanta da tayi.

A mamakin ce ya tsaya kallon ta,yarinya sai kace mai aljanu kama ba dazu dazun nan suka rabu lafiya ba?.yaye bargon yayi dan yaga kafan amma abinda ya gani yasa yayi sauri rufe ta.gani yayi rigan jikin ta ya tattare yayi sama wajan juye juyen ta cinyoyin ta gaba daya a waje suke.nadaman zuwa dakin ya fara dan da kyar dazu yayi jinyan kansa ya samu sauki sai gashi yanzu yazo ya kalli abinda ya dagula mishi lissafi.

Cikin drugs din ta ya nemo mata pain releaver ya hada da ruwa sannan ya hauro kan gadon yace mata"tashi ki sha magani zaki ji sauka yanzu"

"Ni ka rabu dani bana sha duk kabi ka takura ni".

Fizogo ta yayi da karfi ya zaunar da yana zaro mata ido yace"kin san allah in baki sha maganin nan ba wallahi zan baki mamaki".ganin yanda ya harzuko yasa jiki na bari ta karba ta shanye.

Shima ganin yanda ta tsorata da yanda ya mata,yasa yayi murmushin nasara cos yaga hanyan rage zafi cikin ruwan sanyi.cikin hade rai yace" kwanta kuma in kara ji kina ma mutane kuka akan abu kalilan ki gani kar kiga ina kyale ki".

Kwanciya shima yayi a bayan ta,a razane ta tashi daga kwancen jin mutum a bayan ta,kara murtuke face yayi yace"me haka koma ki kwanta dan ba abinda kike tsamani ne ya kawo ni nan ba cos banida wannan time din,just behave urself".haka ta kwanta a daddare.tana ji ya jawo ta jikin shi ya rungume tare da sauke ajiyan zuciya mai karfi na samun relief.

Ko motsi batayi ba,illa shiru da tayi tana jin dumin jikin shi da kamshin turaren shi da ya saukar mata da wani irin natsuwa.farhan shima ta wajan shi haka sai ajiyan zuciya yake.

Zuwa can yaji tana fidda numfashi a hankali alamun tayi bacci,a hankali ya fara shafa mata jiki tare da dan mammatse mata kaman mai mata tausa.gyara kwanciya tayi a jikin shi sbd jin dadin abinda take ji cikin bacci.a haka har ya dan samu saukkn abinda ke damun shi.

6:40am farhat ta bude ido sanadiyan hasken rana da ya dan huda ta window.

Ganin tayi a makale jikin farhan da yake baccin sa hankali kwance,kurawa face din shi ido tayi tana kallo,for d first time take ganin wani kyau na musamman a tare da shi.fuskan nashi yana baccin ma kaman mai murmushi ga eye lashes dinsa kaman anyi masa kari nd dogon hancin sa kuwa kaman na salman khan ga lips din sa pink kaman ya shafa lip stick.sajen fuskan shi daya kwanta ta kai hannu zata taba kuma sai ta janye.lip din ta kai hannu a hankali ta dangwala a hankali wai a zaton ta lip stick ya shafa amma ga mamakin ta taga yatsan ta empty.murmushi tayi tana kare masa kallo,dan ba karya farhan ya hadu over.


A hankali ta tashi zaune kuma da ikon allah yau taji jikin nata da sauki sosai.

Bude ido farhan yayi ya tashi zaune yana salati ganin yanda suka makara sallahn asuba.

Bai kalli inda take ba ya nufi bathroom yayi alwala ya fito tare da shimfida abin sallah.tana nan zaune ya idar da sallah.zuwa yayi bakin gadon yasa hannu ya dauke ta ya nufi bathroom da ita.

Ajiye ta yayi sannan ya hada mata ruwan wanka mai dumon gaske.tana nan zaune tana jira ya gama hada mata ya fita amma sai gani tayi ya nufo ta gadan gadan fuska a hade wai zai cire mata kaya,rike rigan tayi gam idon ta taf da hawaye take kallon shi amma bai dago ba balle su hada ido nd tsoran yi masa magana take ganin yanda ya hada rai."kar ki bata min lokaci dan na gaya miki i dont have time a kan abinda yake zuciyan ki just tryin to help u".

Ba yanda ta iya tana ji tana gani ya cire mata riga ya sata a cikin bath tub,ssi kakkare kirjin ta da hannayen ta.bowl din ruwan zafi da towel ta dauko yazo gaban bath tub din.tsoma towel din yayi a cikin ruwan zafin ya matso da zai dora kan kafan ta,ai ko nan da nan ta rude ta rike hannun sa mai towel din tana hawaye dan bata manta wuyan da tasha ba jiya.

"Dan allah kayi hakuri ka bari wallahi da zafi" tace still tana hawaye.

Dariyan jin dadi farhan yayi a cikin ran sa ganin tarkon sa ya kama tsuntsu cikin sauki.amma a zahiri kuma murtuke fuska ya karayi yace"karma ki bata bakin ki cos dole in gasa miki dan haka ki bar ma roko na".

Pyjama jikin shi ya cire,ya zama daga shi sai boxer,shiga yayi cikin bathtub din tare da kamo ta ya matse a kirji sannan ya fara gasa mata da kyar cos yanda jikin sa yake manne da nata ga ba kaya a jikin su.wani irin kasala ce ta rufe sauko masa,cikin dabara ya rinka wasa da duk inda yasan zai samu natsuwa a jikin ta da sunan gashin kafa.bata lura da abinda yake ba sosai saboda zaban da ya ishe ta.

Bai bar ta ba saida ya musu wanka tare ,farhat ta rasa wani sabon iskanci farhan ya samu gata ba bakin magana sai nannokewa take tana kare kirjin ta.alwala ya sata tayi sannan suka fito.lotion ya dauko zai shafa mata,kallon shi tayi da idon ta duk hawaye tace"na roke ka ka bari zanyi da kaina".

Ganin yanda ta zama kalan tausayi yasa ya kyale ta ya wuce part din shi bayan ya miko mata kayan sawa da hijab din sallah yau harda inner wear ya dauko mata.ita dai yau kunya kaman ya kashe ta.

Manyan kaya ya saka yau,blue shadda dikin half jampa da hula shima blue .cover shoe baki ya saka da da ratsin blue a kan takalmin sai kamshi yake.

Kayan break fast ladi ta dora mishi a katon tray ya shigo da shi dakin ta,ya same ta ta saka rigan da ya ciro mata wani dam karamin gown pink colour.ajiye trayn a tsakiyan rug capet dake tsakiyan dakin,a plate daya ya zuba musu komai sannan ya dauko ta itama ya ajiye ta a gaban abincin sannan yace mata "eat now kisha magani".spoon ta dauka ta fara cin abincin a hankali kaman bata so.ita dai ta banu bata sa wani add uan ya mata ba take shakkan sa yanzu dan ko ido bata iya hadawa dashi tsabanin da da take kallon cikin idon shi ta fada masa magana sin ran ta.

Maganin ya dauko bata shima ba musu ta karba ta sha.hankalin tane ya tashi ganin ya dauko na shafawa.hannu ta fara yarfewa tana hawaye,wani kallo ya bita da shi wanda yasa a take ta natsu.wannan karan a hankali ya shafa mata dan haka bata ji wani zafin kirki ba.

Mikewa yayi yace"zan dan leka office,ba zan dade ba kema ki kwanta ki huta"da kai ta amsa mishi.har ya kai bakin kofa kuma ya dawo cikin,sai da yazo dab da ita sannan ya tsaya.

Zuciyar tane ya fara bugawa da sauri sauri ganin shi a kusa da ita.

Numfashin ta ne ya dauke jin bakin shi kan nata,ya bata light kiss sanna ya fice yana murmushi ba tare da ya juyo ba.

Wani abu taji yana mata yawo a jiki,ji tayi kaman tana yawo a gajmarai.bata taba jin wannan feeling din dan yayi kissing din ta ba kodan da na mugunta yake mata oho.

Ta baya ta fada kan gadon tana murmushi ita kadai kaman sabuwar kamu.
💥🔥💥🔥🌹🌹

FARHAT

💥💥🔥🔥🌹🌹


Written by Ummee yusuf
(Maman yusuf).


Page 41~42

Baifi awa daya da rabi ba ya dawo gida ya same ta tana bacci,rage kayan jikin sa yayi shima ya hau gadon ya kwanta tare da jawo ta jikin sa ya rungume.ba dadewa bacci yayi awon gaba dashi saboda jiya basu samu isasshen bacci ba.

Karfe daya da minti biyar ya farka but ya kasa tashi daga kwancen da yake'kallon farhat yake wacce ta baje a kan kirjin sa tana bacci hankali kwance gaba daya ta saka shi a wani hali.

Yana ganin alamun zata farka yayi saurin rufe idon shi kaman mai bacci.koda ta bude ido akan fuskan farhan ta sauke su,kallon shi take cike da mamakin yaushe dawo har yayi bacci?


Shagala tayi sosai wajan kallon kyakkyawan fuskan shi,a hankali cikin tsoron kar ya tashi ta kai tana shafa lips din shi da yake matukar burge ta.hakan ma bai ishe ta ba,ta kawo nata lips din tayi brushing kan lips din shi a hankali.kaman dama jira yake taji ya capke ya fara bata hot kiss mai tafiya da zuciya.ko kadan ba tayi yunkuri hana shi ba saima biye shi da tayi,sosai suka shagala farhan sai jujjuya ta ke.

Kiran sallahn azahar ne ya dawo da su hayyacin su,mirginawa gefe yayi yana maida numfashi yayin da farhat kuma a kunya ce ta juya masa baya tana gyara rigan ta da ya zame.

Farhan sai da ya saita breath din shi sannan ya mike ya shiga bathroom ya hada musu ruwan wanka sannan ya dawo ya dauke ta zuwa bathroom din.koda suka shiga wanka ma wajan gasa kafa sai da ya kara dan jagwalgwala ta.alwala tayi sannan ya fito da ita .shi kuma komawa yayi ya kara dana sarki sannan ya fito sukayi sallah.

Yau satin farhat daya da yan kwanaki farhan yana jinyar ta kuma alhmdllh kafafun sunyi sauki har tana takawa da kanta zuwa bathroom ko zuwa palourn ta.a satin nan da sukayi tare yake jin ta a ran shi fiye da tunanin shi.

A bangaren farhat kuma tama manta da duk wani abu da ya faru tsakanin ta da farhan a baya,dan yanzu kullum suna manne da juna wajan bacci,cin abinci ko wanka kuma koda ya fita office ma suna manne a waya dan haka ba kasafai ma yake dadewa a wajan aikin ba burin shi ya dawo gare ta duk da har yanzu basu gama taka matakala na karshe ba a matsayin su na ma aurata.

Yau da wuri farhan ya fita office sakamakon aiki da suka taru mai.

Fitowa tayi palourn sama ta zauna kallo duk kadaici ya ishe ta tana lissafin yaushe farhan zai tashi ya dawo gare ta.tun yanzu she missed him.dan hayaniya ta fara ji a palourn kasa,ynkura tayi dan tashi ta duba ko su waye?sai ganin ladi tayi ta hauro saman,sake baki tayi tana bin ladi da mamaki sannan tace"ke kuma saukan yaushe"ladi da dama haushin ta take ji kuma ta ayyana ta daina daukan cin kashin farhat tunda yanzu ba a karkashin ta take ba.tace"tun ranan da kikaji ciwo farhan ya kawo ni gidan nan amma yace inyi zama na a can kasa,kar in bari kisan ina gidan.yanzu ma shigowa nayi in fada miki kinyi baki".

Daga haka ta juya ta koma inda ta fito ta bar farhat da mamaku ya kusan kashe ta.anya wannan ladi ce,in itace yaushe har raini ya shiga tsakanin su haka,kuma meye ma anan farhan na dauko ladi bada sanin ta ba,kodai da wani abune tsakanin su?a take taji zuciyar ta na mata wsni irin daci da kuna.dayan zuciyar ne ta kwabe ta me farhan zai da mace kaman ladi?a yanda ta fahimta yanzu yayi amfani da hakan ne wajan raina mata hankali.mayb ammi ta turo tane dan kula ita amma ya hana,yake yanda yaga dama da ita da sunan taimako.

Sallaman su ruky ne ya dawo da ita daga duniyar tunani da ra lula,ganin su yasa ta saki ihun murna suka rumgume juna dan rabon ta dasu tun bayan bikin ta.

Tsokanan ta suka fara wai ta canza tayi fresh ana ganin ta anga wacce take jin dadin rayuwar aure

Cike da shakiyanci ruky ta"hmmm da alamu poor bagger yayi winning game din nan dan naga alamun har ya kwashi gara".shewa suka sa ita da ramlat har suna tafawa.

Tunani ta fara anya kuwa itce? in itace toh me ya same tane?ashe fa da poor bagger take kwana gado daya,wanka tare komai tare,ina alkawarin ta na sai ta kuntata mishi,ko na rama kusan karya ta da yaso yayi?"oh god wat has got into my

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login