Showing 57001 words to 60000 words out of 66937 words

Chapter 20 - RANAR WANKA Complete Hausa Novel

14 Jul 2025

2167

ƙara maka wani, ka san dai ko lokacin da muke yara kuka nake saka ka."

"Ni kuma na saki birgima ba." Dariya suka kwashe dashi suna tuna yarintarsu.

Wajnah da take laɓe a windo tana kallonsa, suna wasa sai matuƙar baƙinciki ya kamata. A ranta take mamakin dariyar da yake yi.

Ganin Hilah ranta ya ɓace sosai, domin har ga Allah ta tsane ta, musamman jiya da ya sanya ta ba da tarihin rayuwarsa.

Sakin labulen ta yi, ta xauna a kan kujera tana gyara xaman guntun hijabinta.

Da sallama suka tura ƙofar suka shigo. Turus Sauwama ta yi tana ƙare mata kallo.

"Lafiya kike Wajnah? Kin ga yadda kika dawo kamar wacce ta yi ciwon shekara?"

Kuka ta fashe da shi, tare da faɗawa kan jikinta.

Shi kuwa tsaki ya yi, zai wuce ciki sai ya fasa yana kallon Hilah da take kallon Wajnah.

"Anty Ya Huwais ba ya ƙaunata! Duk yadda na so na faranta masa, amma kulle ɗakinsa ya yi ya bar ni na kwana a falo."


"Falo?" Ta faɗa da ƙarfi tana kallonsa da ya yi halin ko in kula da su yana kunna tibi.

"Kai Huwais, kana da sukuni kuwa? Amarya sukutun da guda xa ka bari ta kwana a falo?"

Ɗago idanunsa ya yi, ya kalle su sai kuma ya mayar gurin Hilah, da ta yi jugum tana kallon ƙasa.

"Fitina ta sanya wa ranta ai na gaya mata bana son..."

"Kul kar na ƙara ji ka faɗi haka musamman a gaban ƙanninka. Ke Wajnah mu shiga bangarensa."

Ta ce wanda babu musu ta riga su murɗa ƙofar.

Harara ya bita da shi sannan ya miƙe.

Zama ya yi a kusa da Sauwama, yana sauraren Wajnah da take gaya mata ƙarya da gaskiya.

"Ya gaya mini ya tsane ni ba ya ƙaunata, yana da wacce yake so. Jiya Anty na yi burin da ma mutuwa na yi, kan baƙar rana da na gani."

"Kar ki ƙara faɗin haka, kuma ki kasance mai biyayya da haƙuri za ki ci ribar hakan. Kai kuma Huwais abin da ka yi sam ba ka kyauta ba.."

"Laifin me na yi? Gaya mata na yi bana buƙatarta a rayuwata, kamar yadda tuntini na sanar mata, amma ta yi kunnen uwar shegum Ta shafa ma idanunta toka a dole sai ta aure ni."

"Mene ne laifina don na ce ina sonka? Ko ba ka soni don soyayya ba, ai ka soni saboda dangantakar da ke tsakaninmu. Ni na sam wannan tsinannanniyar da kake so ne take sanyawa kana mini wulaƙanci, kuma wallahi idona idanunta sai na yi ajalinta in ya so ka kashe ni nima, don matuƙar ina raye babu kai ba wata ƴa mace..."

"Anty kina jin abin da take cewa ko? In har za ta rinƙa zagin xaɓin raina, wallahi watarana sai dai ku zo ku ɗauki gawarta."

"Eh ka kashe ni zan fi buƙatar hakan da na yadda wata ta ƙwace mini kai. Na san wacce kake so ba wata bace face kilayar karuwa, saboda in ta gari ce ai ya kamata ka nuna ta."

Miƙewa ya yi cikin zafi zai ɗaura mata mari, wanda ganin hakan ya sanya Sauwama shiga tsakiyarsu.


"Kuna da hankali kuwa? A washegarin aurenku kuke wannan sa'insar? Kai Huwais, biye mata za ka rinƙa yi kuna cece kuce a gidanku?"

"Amma ki na jin abin da take cewa ko? Ba marinta ya kamata na yi ba farfasa mata jiki zan yi, don wallahi matuƙar ta ƙara xagin abar ƙaunata sai na zama ajalinta."

"Ka kashe ni ai ba kanka farau ba namiji ya kashe matarsa, amma ba zan fasa zaginta ba."

"Wawiya mara tunani! In har da zan kawo miki zaɓina wallahi sai kin raina kanki, domin ita ɗin mai tarbiya ce, na san duk abin da na yi mata ba za ta yi sa'insa da ni ba, saboda ta fiki hankali da natsuwa."


"To ka nuna ta mana in har mutuniyar kirmi ce."

"Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Ni kam na yi matuƙar dana sanin zuwa gidanku, domin da na san abin da zan tarar gara na tafi ban zo." Ta furta tare da fashewa da kuka.

"Ki yi haƙuri raina ne ya ɓace." Ya ce tare da zama kusa da ita yana huci.

Wajnah ita ma zama ta yi tana harararsa ta gefen ido. Matuƙar haushinsa take ji, saboda da ace ya yarda ya kwana da ita da yanzu yana nan yana rawar jiki a kanta, amma saboda wulaƙanci ya toxartata a ranar daren amarcinsu. Ga shi ko da ta faɗa a group, cewa ta fara al'ada sun ƙi yadda haka kawai ya zubar mata da mutunci.

"Ke Wajnah fita ina gama magana da shi xan kira ki." Ta faɗa mata haka domin ta lura ta tara su babu abin da zai ƙara sai rigima.

"Kai Huwais, irin tsarin da xa ka ɗauka a zaman gidanka kenan?"

"To ya kike so na yi Anty Sauwama? Kin san sam bana son raini. Tun daren jiya mara kunyar yarinyar nan take ta gaya mini maganganu marasa daɗi, kuma wallahi ba zan ɗauka ba don ƙasa-ƙasa zan yi da ita."

"Ai ko ina ba ka shawara ka canza, in ba haka ba maƙota za su jiyo ku kuma sa'insa.".

"Jikinta ne zai gaya mata sam ba zan ɗauki raini ba."

"Amma ka san ba daidai bane ka ƙi kwana da ita ko? saboda Allah ya ɗora maka haƙƙi a kanta dole ka sauke."

"Ni fa bana sonta ina da wacce nake so. Ba zan iya ɓoye miki komai ba, ba zan iya haɗa jiki da ita ba, kuma bayan haka na tsani mata masu shan kayen mata, saboda jiya abin da tasha kenan ta wahalar da kanta ta koma kamar mahaukaciya."

Kasancewar babu kunya a tsakaninsu ya sanya ta kalle shi ta ce.

Tun da muka mallaki hankalin kanmu kake gaya mini kana sonta, amma kaƙi sanar dani wace ce. Huwais a tunanina babu abin da xa ka iya ɓoye mini."

"Ba zan iya gaya miki ita ba."

"Don haka babu amfani wulaƙanta matarka kan wacce na za ka iya bayyana ta ba, in kuma aljana ta aureka sai na sanar wa Ummu ta yi maka ruƙiya."


Dariya ya saki tare da kai mata duka yana faɗin,"Eh ina ga hakan ki sanar mata, amma har da wannan ƙyamushshshen mijinki xa a haɗa ayi mana ruƙiya."

"Ba na son iskanci Huwais ni fa a matsayin mahaifiyarka na ke kake dukana."

"Kin manta sanda na ke zane ki a makaranta kenan? Ai ƙaramar uwa abokiyar wasa."


Dukan ta rama, sai kuma ta kalle shi tare da mai da hankalinta gare shi.

"Don Allah ka canxa tsarin gidanka ku, xauna lafiya karka barinta raina ka."

"Hmmmmh!" Ya ce tare da miƙewa ganin ta miƙe.

"Bari na je na yi mata magana."

"To," Ya ce sai ya miƙe, ya biyo bayanta don ya yi kiran su Hilah su shigo sashinsa.

Hilah wacce tun da ta shigo suka fara sa'insa ta tsure da lamarin Wajnah. Mamakin ƙarfin halinta take gani na rashin kunyar da take yi masa. Ta san cewa yana wasa da ita, kuma duk ya fi sakin mata, amma ba ta taɓa ko da gigin masa rashin kunya ba, domin ba halinta bane, kuma shi ma ba ya ba da fuskar da za a raina sa.

Tana cikin wannan tunanin, Wajnah ta buɗe ƙofar ta fito cikin ɓacin rai tana share hawaye ta yi ɗakinta.

Sororo ta yi tana tunanin irin zaman doyan da za su yi, domin matuƙar ta ce raina shi za ta yi, ba za ta ji daɗi a gurinsa ba.

Anty Sauwama ta tura ƙofar ta fito yana biye da ita. Bangaren Wajnah ta yi sh,i kuma ya kama hannun Umnah da Amnah yana faɗin,

"Ku zo muje sashina." Miƙewa suka yi zuwa ciki.

"Wow! Gaskiya gidanka ya yi matuƙar kyau Yaya." Hilah ta ce tana zama a gefensa. Azerh tana kallon falon admiringly.

"Allah ko?" Ya yi mata tambayar idanunsa cikin nata.

Yes Ya Huwais the house is fine." Hilah ta bashi amsa tana zama a gefen kujerar da yake.

"How about mace mai irin ki tsafta da iya decorating ɗin gida take a ciki. Na san the house would be finer than this?"


"Anty Wajnah ma za ta yi koƙarinta. Yar gayu ce itama."

Taɓe bakinsa ya yi, yana shafa kansa tare da kallonta har ta zauna.

"Hilah, akwai maganar da na ke son mu yi kan maganar mahaukacin masoyinki, amma ba anan ba ya kamata na zo makarantarku."


Jikinta ya kama ɓari jin abin da ya ce."

Kallon Azerh ta yi wacce sam hankalinta ba ya kansu.

"Yaya..."


"Ba yanzu za mu yi maganar ba. In kin samu lokaci ki kira ni."

"To," Ta ce amma ba don haka taso ba.


"Please Yaya tsakaninka da Anty Wajnah..."


"Ke yarinya ce ba ki san komai ba don haka kar ki interfering."

Kama bakinta ta yi, ba ta ƙara cewa komai ba kan lamarin, suka ci gaba da hira, amma hankalinta na can tana tunanin abin da xai gaya mata.

Anty Sauwama kuwa, ɗakin Wajnah ta tura ta sameta ta yi wanka tana shafa mai.

"Ashe ba ki da hankali? A haka za ki gina rayuwar auren na ki, kuna sa insa? Wallahi matuƙar ba ki canza ba zai iya illata ki, kin san shi da baƙin xuciya. Kin kwana da sanin baya sonki dole aka yi masa, amma kike gaya masa magana son ranki."

"Anty to ya kike son na yi? Inda kin ga rashin mutuncin da ya yi mini, sai kin tausaya mini. Ƙiri-ƙiri ya barni cikin mawuyacin hali jiya."

"Eh, ai gara ma da ya yi miki haka, saboda ki daina biyewa waɗannan sheɗanin ƙawayen na kina ɗirka wa kanki maganin matan da xai cutar dake. Kina sane da shan maganin da yawa babu alfanu kuma daga ƙarshe xaki yi nadama mara amfani.




Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423






*RANAR WANKA...*



NA



JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"



☀️ *First Class Writers Asso* ☀️

Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation


*GARGAGAƊI*

Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️

JAN HANKALI

Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.


SADAUKARWA

Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.



PAGE 22

BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
"Anty to ya kike son na yi? Inda kin ga rashin mutuncin da ya yi mini, sai kin tausaya mini. Ƙiri-ƙiri ya barni cikin mawuyaci hali jiya."

"Eh, ai gara ma da ya yi miki haka, saboda ki daina biyewa waɗannan sheɗanin ƙawayen na kina ɗirka wa kanki maganin matan da xai cutar dake, saboda shan shi da yawa babu alfanu, kuma daga ƙarshe xaki yi nadama. Ina Gobbe aka kira ni, aka sanar da ni cewar tun da aka sanya ranar kike bankan maganin bature. Kin kuwa san illar da kike yi wa kanki? In maganin matan za ki sha, ga ba ƴaƴan itatuwa nan ba da kuma na gargajiya wanda baya cutarwa."

Tura bakinta ta yi, ta ci gaba da kwalliya tana faɗin,"Ni na san Anty Hibba za ta gaya miki munafuka kawai."

Duka ta kai mata tana faɗin,"Don ubanki ƴaƴar ki kike zagi? Ai ita tafi ki hankali, ko da yake laifin Anty Fati ne, da ta barki kike abin da kika ga dama."

"Yanzu laifina duka za ki gani Anty?"

"Eh mana tun da kin zubar da mutuncin kanki kike roƙonsa ya taimaka miki."

"Ni ban ga abin kunya ba domin mijina ne."

"Shikenan, ki ci gaba da zubar ma kanki da mutunci."

Ƙara tura bakinta ta ƙara yi, ta ba ce komai ba ta ci gaba da kwalliayrta.

"In ɗauki shawarar da na ba ki, sai ki canza taku ta hanyar yi masa biyayya, in kuma ƙin ƙi sai ki xauna fitsara da rashin kunya ya ƙwatar miki darajar ki. Miji dai yana da babban matsayi da kima a gurin matarsa, kuma dole sai ta ƙarƙashin ƙafarsa za ki samu ya ɗaga ki shiga aljanna. A yanzu da aure ya zama a lallaɓa auren zamani, waɗanda suka yi auren soyayya ya suka ƙare? Ballantana ke da kin san yadda aka yi aure. In zawarci kike son yi Allah ya taimaka, kin san dai namiji na da dama sosai a rayuwarsa. In yau ya rabu dake xai iya auran mata huɗu duka ƴan mata. Don haka in kunni ya ji, gangar jiki ya tsira.

Miƙewa ta yi yayin da jikinta ya yi sanyi jin abin da ta ce.

Sashinsa suka shiga, inda suka same Hilah da su Azerh suna ta kallon hotunan biki. Shi kuma hankalinsa na kan wayarsa, yana duba chatts ɗin da suka yi a matsayin mahaukacin masoyi, yana murmushi sai kuma ya ɗago ya kalleta ya girgiza kansa.

"To ni zan wuce, don Allah ku rinƙa haƙuri kar ku ɓata zumunci." Ta ce tana kallonsu duka.

"In sha Allahu Anty Sauwama, Allah ya kiyaye hanya." Ta ce mata cikin sakin fuska kamar babu abin da ya faru.

"Hilah ku tashi muje."

"Ki barsu mana na kai ki, zuwa anjima sai su koma."

"Ƙafata kafarsu tun da ka ga Ummu ba ta so zuwan ba."

"Ni ma zan biku." Cewar Wajnah tana kallonsa da tun da ta shigo bai kalle ta ba.

"To ka ji Huwais ta raka ka sai ku dawo tare?"

"Ina da inda za ni." Ya faɗa fuska a ɗaure tare da hanyar waje.

"Ki yi haƙuri da kanshi zai kaiki kin ga duka jiya aka kawo ki, kuma mutane ma ba su gama watsewa ba, sannan ki xama mai biyyaya kin ji?"

"To,"Ta amsa fuskarta babu yabo babu fallasa ta bisu zuwa waje.

Abu da ya koma ɗakinsa wayarsa ya ɗauka ya yi kiran Ummu. Shi kansa lamarin ya rikirkita shi tare da tabbatar da zargin Ummu, wanda yake ƙoƙarin ƙawar da zargin da yake yi.

Ummu ce ta shigo fuskarta a ɗaure ta zauna a gefensa.

"Ni kaina na fara tunanin abin da kike zargi."

"Tun tuntuni na ke gaya maka a ɗauki mataki tun kafin ruwa ya ƙarewa ɗankada."

"Amma yaron nan ba shinda hankali. Wane hauka zai sa ya rinƙa kallon ƴar'uwarsa da kallon soyayya. Tuntuni na ke ganiin haka daga gare shi, amma sai na watsar da batun."

"Wataƙila dalilinsa na ban shayar da Hilah ba..."


"Kan me zai ɗauki wannan a matsayin hujja har ya fara sonta? Yana gani ko Umnah ciwon mama bai bari an shayar da ita ba. A gaban idanunsa aka yi cikinta kuma aka haife ta. Yaron nan ba shi da hankali. Tun kafin ya ja mana abin kunya, ayi mata aure kawai xan sanar da Hamad ya turo ayi auren in ya so ya kama mata haya in ta gama karatun su koma Kaduna."

"Hakan shi ya fi. Tuntini na ke gaya maka ka ɗauki mataki. In aka yi musu aure hankalinmu zai kwanta."

"In sha Allahu, zan kira mahaifinsa na yi masa magana, amma kafin nan ya kamata mu kira shi Huwais ɗin, sai mu sanar mishi da za a sanya mata rana, in ya so sai muga yadda zai yi."

"Wane hujja kake son ka tabbatar? Karka manta haukar da ya yi lokacin da Hamad ya nuna yana sonta kuma aka bashi damar ya rinƙa kiranta sau ɗaya suna gaisawa."


"Duk da haka mu ƙara kwatanta sa mu gani."

Bayan ya dawo da su gidan Najib ya wuce. Yana ganinsa ya kwashe da dariya suka tafa.


"Ango kasha ƙamshi."

Tsaki ya yi jin abin da ya ce sai ya zauna yana kallonsa.

"Ina madam? Ta kawo mini abinci yunwa na ke ji."



"Ikon Allah! Ango kamarka yana ɗauke da yunwa."


"Hmmmh! Ba za ka gane bane. Yau korar kare Ummu ta yi mini ni da gidammu."

"Dama ta haɗa maka da duka, saboda na tabbata ba yunwa ya kai ka ba."

"Kamar ka sani, amma ai a banxa nama na jan kare. Saboda ita wacce na je gani tare muka koma gidana."


"Hmmmmh! Iska na wahalar da mao kayan kara." Ya ce yana ƙoƙarin kunna tibi.

Banza ya yi da shi daidai lokacin da Samahatu ta fito daga kicin.

"Baby, kamar ango na ke gani."


"Shi ne ba gizo idanunki suke miki ba. Ki taimaka masa da abinci karya mutu."

"Haba! Mai amarya guda yake neman abinci. Ko da amarya na hutun girki, ai ya kamata a restourant za su yi oder.

"Ki taimaka masa, ƙila kuma amaryar ce ya yi mata laifi ta yi masa horar yunwa." Harararsa ya yi, ba tare da ya ce komai shi kuma yana dariya.

Abincin ta kawo masa sannan ta shiga cikin ɗakinta.

"Ina fatan jiya ka bai da kai bori ya hau? Saboda yadda na ga amaryarka jiya, na san cewa ba za ta yi wasa da wannan ranar ba."

Ƙaramin tsaki ya ƙara ja."Ni kuma da yake shashasha ne sai na biye mata ko? Kana ganin irin iskancin da ta fara yi mini. Kulle ƙofata na yi, domin mace mai arha ba ta birgeni."

Takaicin abin da ya faɗa ya kama shi."Arha fa ka ce Huwais? In kai ba ka kai kanka ba sai ta kawo matarka ce fa."


"Please, don Allah ni ban zo gidanka ba don ka dame ni da surutu. In kuma abincin ne ba ka son na ci sai ka gaya mini."

"Gaskiya ce dai ba ka so, amma kuma dole a matsayina na abokinka, na tuna mala da haƙƙin da ke kanka."

Ture abincin ya yi yana harararsa."Ga abincin ka nan sai ka cinye, ai na lura dama ba ka so a kawo mini ba." Ya faɗa tare da miƙewa zai fice.

Dariya ya yi tare da kama hannunsa bayan ya miƙe."Ka dai ƙoshi amma ai na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login