Showing 9001 words to 10546 words out of 10546 words

Chapter 4 - WA YAFI K'AUNATA

12 Jul 2025

793

na tafi kawai".

Tashi nayi jikina a sanyaye ina hangen Ya Hafiz dake sujjada ta godiya ga Allah ina hangen fuskarsa cike take da tsananin farin ciki, ji yake kamar ya goya ni dan murna sai jifa na yake da wani shu'umin kallo harna b'acewa ganinsa.



Bayan kwana biyu Inna Rabi da taji irin had'in da akai da yaranta inda Hajara ita da saurayinta, ita ko Zeena da Hashim d'an abokin Kawu Iro sai kuma Sa'ida da Hamza d'an gidan Hakimi ni ko tare da Ya Hafiz duk muna murna da hakan, bare ni bazan ce bana so ba, ba kuma zance bana ra'ayi ba, duk dai Sa'ida taso Ya Abbas amma ba yadda ta iya ta hak'ura.



Inda Inna Rabi ta tasa Kawu Iro gaba da masifa danmi za'ayi irin wannan had'in masifa take tana cewa "ni gaskiya an cuce ni ba'a kyauta min ba danmi za'a had'a Hafiz da waccar yarinyar mai bak'in jini" tashi yayi kanta rantsa ya d'an fara b'ace ya ce "koke keda ikon aurar dasu, idan kin isa sai ki suke auran na gani" tashi tayi itama a zuciye tana banbamin masifa tana cewa "ai dole ka ce haka mana saboda an tab'a y'ar so, kuma wallahi indai na isa da Hafiz bazai aure wannan yarinyar ba bazata sab'o ba wallahi bazan yarda ba a maida min yaro yadda aka ga dama ba a maida min shi kamar wani lusari, waye bai san uwar wannan yarinyar ba sadda take aure a nan gidan, sai da ta maida Yayan naku kamar wani bawanta", wata irin tsawa ya buga mata idonsa ya kad'a yayi jawur, ita kanta sai da ta firgita ganin yadda mijin nata ransa yayi mugun b'ace ba shiri ta rufe bakinta cike da b'acin ran dake taso mai ya ce "wallahi Rabi kika sake kika tada zancan nan wajan Hafiz ko kikai mai maganar ya fasa auran nan to kema a bakin auranki.............






*KADUNA* POV





Zaune Munnira take tun jiya gabanta yake wata irin mahaukaciyar bugawa tun tana daurewa har wasu irin hawaye suka sami nasarar zubo mata wadda bata shirya zubowarsu ba, tashi tayi ta shiga d'aki, domin Ramdan ya fita zuwa wajan aiki d'akko wayar tayi ta dawo ta zauna Yayarta ta kira mai suna Hafsa wadda suke uwa d'aya uba d'aya su kad'ai suka rage ma junan su, iyayansu sun rasu tun suna y'an yara, itama Hafsar tana aure ne a Kadunar amma ita tana auran wani d'an siyasa ne mai kud'i, suna matuk'ar son junansu.



Bayan ta d'au wayar jin an d'auka ta sauke ajiyar zuciya can cikin wayar Hafsa jin kamar y'ar uwar tata tana cikin damuwa yasa ta ce "Munnira lafiya kuwa?, na jiki kamar ma kuka kike miye yake faruwa ne?" Munnira kam bata san sadda ta fashe da kuka ba, dama damuwar ta mata yawa, ta rasa wadda zata fad'awa ta samu sauk'i a zuciyarta abinda yasa bata yawan kai kukanta wajan y'ar uwarta indai tana cikin damuwa to itama ba k'aramar damuwa take shiga ba, cike da tashin hankali Hafsa ta ce "wai miye yake faruwa ne?, Munnira karki sa na wanko k'afata yanzu nazo gidan naki minene yake faruwa ne dan Allah?", share hawayen tayi tana girgiza kai kamar tana gabanta tana cewa "a'a ba sai kinzo ba amma Hafsa zuciyata ta kasa samun natsuwa akan wannan auran da Ramadan danginsa suke so yayi, wallahi Hafsa zuciyata bugawa take" cike da tausayin y'ar uwar tata tasan kishiya a yi maka ita da ciwo bare ita danginsa basa sonta wacce suke so ita za'a auro, cike da sanyin murya da son kwantar mata da hankali ta ce "ki kwantar da hankalinki dan Allah ki daina sa damuwa a ranki idan kika ji irin haka ki rink'a mai-maita Innalillahi wa'inna ilarhir raju'un, sana Munnira ki rink'a karanta Alqur'ani mai girma ki yawaita yin azzakar, insha Allahu koda da niyyar cutar dake ta shigo Allah bazai tab'a bata ikon hakan ba", sosai Munnira taji zuciyarta tayi sanyi.


Inda Hafsa ta ce zata shigo gidan zuwa gobe su k'ara tattaunawa, da haka sukai sallama.


Tana nan zaune kawai taji tsayuwar motoci a cikin harabar gidan nata ba shiri yadda zuciyarta ta buga ta tashi ta lek'a ta wundo, ganin masu fitowa a cikin motocin yasa ta d'an zare ido, da sauri ta zawo hijabinta ta sa tana cewa "to mi ya kawo Hajiyar Ramadan da Yayarsa guda d'aya Nawwara?," ta tabbayi kanta, can kuma saita tuno ai dama sunce zasu zo, addu'a take Allah yasa su gama abinda suke su tafi karma su shigo cikin sashinta dan taga sun shiga d'ayan sashin wadda tasan nanne amaryar zata tare bayan anyi auran.



Tana cikin tunani taji an banko k'ofar parlon, da sauri ta waiga tana kallon su yadda suke bin parlon da kallo yasa cike da fara'a ta ce "Hajiya ku shigo ina wuni" ta idasa maganar tana kaiwa har k'asa tana gaishe da Hajiya dake binta da hararara da kallon wulak'anci, Halima ce dake cin chingum tana bin ko ina na parlon da kallo tana jefama Munnira wani matsiyacin kallo ta juyo wajan Hajiya tana cewa "dama Hajiya wannan kucakar ce matar My Man ai na zata zanzo na tadda wata uwar mata a yadda kuke ikirarin wai ta mallake sa a hakan", ta idasa maganar tana nuna Munnira, tafawa sukai ita da Nawwara ta ce "hmm kema kin gani dai ya rasa uban mi yake ci tare da wannan tsohowar guzumar matar tasa kullum suna mak'ale da juna" wani irin taku Halima tayi tana matsowa kusa da Munnira tada dake tana kallonsu bak'in ciki ya cika zuciyarta amma ta dake tana son kawar da fushinta, ko kad'an idan ka kalli fuskarta baza ka ce abinda suke fad'a game da ita ya bata haushi ba, Halima dake kallonta cike da tsana da hassada saboda taga ta fita ta ko ina kyanne kyan jiki da diri da komai kawai ta fad'i hakan ne danta bak'anta mata rai sai dai tana kalli fuskarta sai taga sab'anin haka dan kuwa fuskar Munnira wani kalar annuri ma ke fita da kwarjini, ta bud'e baki ta ce "ai daga yanzu a shirya dan ba mutum shi kad'ai keda shi ba, kuma idan banda jaraba ta d'a namiji ina wani abun so da abun mak'alewa a nan", shuru Munnira tayi dan tasan shine alkhairi baza ta so tayi cece kuce a gaban sirikarta ba kuma tun kamin ma ta shigo tsayawa fad'a tana fad'a kamar zubar da mutumci ne da kima.




Shurun da tayi kuwa ba k'aramar shak'a sukai ba ta maida su mahaukata kenan cike da isa Hajiya ta zauna kujera tana d'ora k'afa d'aya kan d'aya tana nunama Halima gidan ta ce "fatan dai wancan sashin yayi miki idan ma baiyi miki ba, wannan ne yayi miki zata iya kwashe kwamutsanta ta baki waje mai gurin yazo mai tabarma ai dole ya nad'e" wata dariya Halima ta saki ta jin dad'i ta ce "ai Hajiya nafi k'arfin na zauna a inda ta zauna sabon waje yayi min ina ni ina zaunawa inda ta tashi ai nafi k'arfin haka Hajiya tayi zamanta dama bakiga wajan ba duk an maida shi wani iri" Hajiya data gyara zama ta kai dubanta wajan Munnira dake tsaye ko ci kanku bata ce ba, wani banzan kallo ta watsa mata tana cewa "da alama gidanku basu iya tarbar bak'i ba ko?, kinga mutane bazaki basu abin tab'awa ba kin wani tsaya kin tsare mutane da idonki irin na munafukan farko, nazo gidan d'ana amma ko arzik'in ruwa bazan samu nasha ba, saboda baki da mutumci dama marar tarbiyya ce ke", sosai taji maganar Hajiya ta b'ata mata rai amma saita d'an k'ak'aro murmushin k'arfin hali ta ce "a'a Hajiya ba haka bane baku zauna bane na gani, kunata wasu maganganu ne wadda bai shafe ni ba, bari nayi wai ku gama idan kuka zauna saina gabatar muku da abun motsa baki" cike da mamaki suke dubanta au yanzu duk maganar nan da suka yab'a mata bata dameta ba, kam uban nan kayyasa kai rik'e baki Nawwara tayi, Halima kuwa sakin baki tayi tana duban Munnira dake shigewa kitchen, harta kawo masu ruwa da lemo suna tsaye cike da mamakinta.


Hajiya dake zaune ta cika tayi fam ai gani take kamar gayamata magana Munnira tayi, ai kuwa Halima data harbo jirgin Hajiya ta bud'e baki domin k'ara zuga tana d'aukar robar ruwa ta zuk'a tana watsa ma Munnira shi a fuska, ta ce "ai wannan maganar da tayi Hajiya gaya miki magana kawai tayi wallahi" runtse idonta Munnira tayi tana jin ciwon watsa mata ruwa da Halima tayi, Halima dake kallonta ta sake cewa "ke har kina da abunda zaki bamu mu ci?, saura muma a gama damu komi kike nufi?", Munnira dake shirrin yin magana suka ji wani irin k'arar mari tasssss tassss mai azabar k'arfe k'arar mari ta mamaye parlon su duka har rige-rigen dubawa suke waye aka zafga ma mari haka..........✍️






*To laifin dad'i aka ce k'arewa, Jama'a nima zanso inji waye aka zafga ma mari haka, mu had'u a PAID BOOK akwai k'ura fa, shin yaya rayuwar Maryam zata kasance a gidan Ya Hafiz ne?' shi kuma Ya Abbas wai miye yake nufi ne da Maryam?, akwai cakwakiya a wanga littafi, ta b'angaran su Munnira ma fa yanzu wasan zai fara yanzu aka soma tafiyar*......




ZAHRA ROYAL STAR CE



SHARE FISABILILLAHI🥰🙏

2
3
4

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login