Showing 123001 words to 126000 words out of 156457 words
mutumin da be ta6a kiranta ba sai texts din dayake mata kawai.
Tayaya ma zata gayamashi? Me zata cemashi? Zani saloon?
Daukar wayarta tayi tana kallo not knowing what to do, yanzu idan bata kiraba mamy fushi xatayi tace taqi bin umarninta.
Shiga wajen rubuta sms tayi tayi shiru tana tunanin me yakamata ta rubuta mashi don bata tunanin zata iya kiranshi.
Ta dade tana daurawa da kwancewa daga qarshe ta sadaqat tayi typing din.
*Good afternoon, zanje saloon, permitted?*
Tsayawa tayi tana kallon abinda ta rubuta tanaji kamar tagoge but she has no choice haka ta danna send botton ta senda mashi.
Zama tayi wayar ahannunta tana kallonta tana jiran jin shigowar reply amma shiru.
Haka tazauna kusan 30mins amma ba reply.
Ranta ya 6aci sosai jitake me ma yakaita yimishi text at the first place? Jitake kamar ta dora hannu aka.
Qin fitowa tayi don haushi har saida taji hayaniyansu abdul alamun sun dawo.
Dagowa tayi ta kalli wayar dake can gefen gado ta jawota ta kunna taga babu reply. Kwafa tayi rai 6ace ta ajiye wayar tafita dakin ranta na suya.
Aqasa ta tadda su abdul wanda dawowarsu kenan zasu hau sama su chanza uniform.
Sannu da gida duk sukayi mata ta amsa ba yabo ba fallasa sannan suka haye sama don chanza kayan.
Zama tayi tana kallon t.vn dake kunne fuskarta ba walwala.
Mamy dake zaune falon ta kalleta sannan tace
"Yanzu saudart banida ikon gayamaki gaskiya sai ki tsiri kumbure kumbure? Wacce uwar arziqi zata bar diyarta tafita yawo da aurenta batareda izinin mijinta ba? Nabaki shawara as a good mother shine kike fushi kika ma fasa tafiyar? Dakyau" taqarashe zancen tana jinjina kai.
Saudart da dama kamar a wuya take sai kawai tafashe da kuka.
Sakin baki mamy tayi tana kallonta a mammakince don bataga abinda tayimataba da zata samata kuka.
Kuka saudart take sosai kamar wanda aka daka don harda shesheka.
"Ikon Allah, me akamiki kike kuka?" Inji mamy tana kallon yadda take kukan bilhaqi
"Mamy nifa baqin bin umarninki nayiba, na gayamashi yayi banza dani, ya zanyi?" Takuma fashe dawani kukan, dama me neman kukane akaima dariya.
"To shine saiki 6are baki kamar yar 5yrs kina kuka? Lallai wannan sangarta tayi yawa, allah ya shiryaki" inji mamy tana girgiza kai.
Itadai batace komaiba sai hade kanta datayi da gwiwa tana cigaba da kukanta qasa qasa.
"To nidai kimin shiru, kuma yanzu su abdul zasu sauko suganki kina kuka godai godai dake, kitashi kishiga dakinki kije kiyitayi hankali kwance babu mai takuraki"
Shiru tayi ta kyaleta batace komaiba tana sniffing ahankali.
Jin saukowarsu abdul yasata share hawayen a6oye tayi fuska tacigaba da kallonta saidai haryanzu ranta a6ace yake sosai.
Zama su abdul sukayi suna bata labarin abinda yafaru a school yau.
Sama sama take amsamasu don batajin yin magana ma kwata kwata, suna haka sukaji knocking a kofa.
Dagudu abdul yanufi kofar dagudu don duba wanene.
Ba'a dadeba yadawo falon yana dan tsallen murna.
"Aunty, uncle is here!" Yafada cikin murna.
Juyowa tayi tana kallonshi kawai not saying a word.
"Wane uncle?" Inji mamy
"Uncle A'A wai inkirata" inji abdul
Kallon saudart din mamy tayi tayi saurin kauda kai.
"Saiki tashi ko?" Inji mamy
Turo baki tayi sannan ta tashi tayi sama cikin jin haushi.
Ba'a dauki lokaci ba ta sauko sanye da doguwar hijab akan kayan jikinta.
Bata tadda mamy ba a falon hakan yasa tafice kawai.
Koda tafita bataga motarshi ba a inda yasaba parking ba hakan yasata nufar falon baqin tana tunanin yau bezo da mota bane.
Maigadi ya nufota yana gaisheta, amsawa tayi cikin fara'a kamar yadda tasaba tanufi bangarwn bakin.
"Hajiya ai yana waje" inji maigadin.
Hakan yasata chanza akalar tafiyar tata zuwa waje tanajin haushi dikya cika mata zuciya.
A gaban gidansu gefen hanya taga wata dalleliyar baqar mota parke wanda ko ba tambaya tasan tashi ce.
Ahankali kamar mai tausayin qasa tanufo motar kanta a sunkuye.
Tunda tafito yaketa kallonta, yarasa dalilin da kullum take chanza mashi, gani yake kamar kullum chanzata ake, she looks soo adorable.
Ja tayi ta tsaya bakin motar batareda ta dagoba.
Gani tayi anbude kofar 6angaren datake tsayen.
Dagowa tayi ta kalleshi suka hada idanu tayi saurin kauda kai tana sake tamke fuska.
"Get in please" yafada ahankali.
Shiru tayi kamar bazata shigaba saikuma ta qaraso ta shiga ta zauna batareda ta maido kafafun cikiba ta sadda kanta jin idanunshu na yawo akanta, ga qamshin turarenshi dasuka fara addabar kofofin hancinta.
"Good evening?" Yafada ahankali yana kallonta
"Uhmm evening" tafada kamar wanda aka tilastamawa
"Zaki saloon right?" Ya tambaya yana kallonta
"No, that was then" ta amsa tana kauda kai
"Yanzu fa?" Yasake tambayarta still yana kallonta
"Nafasa" ta amsa mashi a taqaice.
"Why?" Yasake tambaya
Cikin qosawa da maganar tace "kawai" tana kauda kai
Ajiyar zuciya ya sauke sannan yayi starting din motarshi yace "get your legs in muje"
Kallonshi tayi taga ita yake kallo saita dauke kai tace "nifa nafasa"
Shiru taji yayi hakan yasata sake juyowa ta kalleshi
Gani tayi ya kafeta da idanu wanda yasata jin wani iri cikin jikinta hakan yasata janye idanu ta sannan ahankali tace
"Ok bari nadauko purse dina"
"Ok" ya amsa yana kallonta
Sauka tayi daga motar tanufi hanyar shiga gidan yabita da kallo harta shiga. Ajiyar zuciya yayi yakoma ya jingina da kujerar motar yana jiranta.
Tadan jima da shiga cen saigata tasake fitowa wannan karon sanyeda maroon abaya tayafa madaidaicin gyalenta.
Iskeshi tayi kamar yadda tabarshi don ki kashe motar beyiba.
Babu yadda ta iya haka ta shiga motar tanajin dama tun farko bata tattagi fitarba, ita a tunaninta ma idan takoma ta gayawa mamy yadda sukayi dashi zata hana fitar saitaga akasin haka don addu'ar allah ya kiyaye kawai tamata.
Maida kofar tayi tarufe tana gyara zamanta, saida yayi making sure tashirya sannan yaja motar sukabar kofar gidan.
Tafe suke babu maicewa kowa uffan, saudart dama tunda tashigo tajuya kanta tana kallon waje ta window kamar yadda tasaba while shi hankalinshi rabi na kan tuqi rabi akanta.
Jinshi yake so happy having her next to him. Dama yana gidansu sadeeq saqonta yashigo wayarshi.
Da farko kasa believing idanunshi yayi dayaga message from *other half* saida ya murza idanunshi yaqara kallo yaga dagaske ita dince.
Cikeda zumudi ya bude saqon ya karanta.
It's just three words amma yajisu har cikin ranshi most especially na qarshen nan wato *permitted?*
Yaji dadin ganin tana neman izininshi ne, hakan yasashi jin kamar ta nuna yanada matsayi awajenta.
Babu shiri ya miqe yadauki car keys dinshi ya nufi kofa.
Yanajin sadeeq nata tambayarshi ina zaya yai banza dashi yafice, this is a chance of being with her nawani lokaci and he dont want to lose it.
Saida yakoma gida yayi wanka ya dauki wanka sannan yanufo gidan nasu don kaita dakanshi.
Jin motar tadauki shiru sosai yasashi miqa hannunshi nadama ya kunna disc din motar yasa waqar *sorry* na justin biebier
Ahankali waqar tafara tashi acikin motar in a very emotional mode.
Cigaba yayi da tuqin yanabin waqar acikin zuciyarshi yanajin waqar tayi daidai da yanayin dayake ciki kuma yanajin kamar waqar na isar da saqonshine gareta.
Itama a 6angarenta tunda waqar tafara ta nutsu tana sauraronta, tarasa dalili amma saijitayi waqar na tasiri a zuciyarta, tanasa jin wani sense of emotion a tattare daita.
Haka duk sukayi shiru suna sauraron waqar kowa da abinda yake saqawa azuciyarshi harsuka qaraso saloon din...✍
Ummin fasihu🧚🏻♀️🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)
Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)
086
Tsayuwar mota yasata sanin sun qaraso saloon din.
Bin harabar tayi da kallo tacikin motar tana wondering inane nan ya kawota.
Jin an bude murfin 6angarenta yasata dagowa suka hada idanu dashi tsaye riqeda murfin motar daya bude mata.
Sauke idanunta tayi sannan ta ziro kafarta ahankali ta sauko tana qara qarewa harabar kallo.
Dukda duhun magrib yakawo kai hakan be hanata ganin qawatuwar wajen ba.
Idanunta ne suka sauka akan logo din wajen wanda ke walainiya cikin kaloli daban daban ansa *EXCLUSIVE BEAUTY SALOON*
Dan wara idanunta tayi ganin inda yakawota don wajen bana qananun mutane bane don tasan dakyar kudin hannunta su isheta ko sun isheta bazata rage ko sisi ba na shopping datayi niyyar yi.
Ganin yayi gaba zai shiga yasata saurin tsaidashi da
"Ehmm.. ba..ba anan nake saloon dina ba" tafada tana janye idanunta ganin ya juya ya zubamata ido.
"Ina kikeyi?" Ya tambayeta yana saka hannayenshi a aljihu
"Mhiz zee saloon" ta amsa ataqaice
"Nan ma sunayin mai kyau, nan baby keyi ma" yafada idanunshi kyar kanta.
"No nafi son can" tayi saurin fada don she's not ready to embarass herself
"Why?" Ya tambaya.
Haushi yacikata, wai ina ruwanshi daita ne? Meye ruwanshi da inda zatayi?
"Just" ta amsa ataqaice tana tamke fuska
"Then let's go, i bet you'll like it here too" yana fadin haka yajuya yanufi cikin wurin cikin tafiyarshi ta qasaita data riga tabimashi jiki.
Binshi tayi da kallon taqaici ranta na mugun 6aci, wai wacce qaddara ma tasata tarkar fitar tun farko? Yazo ya kawota saloon din masu kudi cemashi akayi nan takeyi? Koko wani kilbibi ne wannan?
Jin kamar ba'a biyoshi ba yasashi juyowa yana kallonta.
Sake hade rai tayi sannan tafara takowa wajenshi tanajin kamar tayi bindiga.
Binta yake da kallo harta qaraso wajenshi ta giftashi tawuce batareda ta kalleshi ba.
Dan murmushi yasaki sannan yabi bayanta shima yashiga.
Saloon din ya amsa sunanshi na manyan mutane don kallo daya zakamashi kasan bana irin namu na yaku bayi bane.
Koina naciki is glass, gawani sanyin A.C dake chakude da qamshin freshener dake iya samutun ya 6ingire da gyangyadi batareda yayi aune ba.
Gaba yayi tana binshi har suka wajen wata waiter.
Itadai tana daga baya bataji abinda suke cewa ba saigani tayi waitress din tamiqa mashi dan kati ya amsa sannan yajuyo yayimata alama da tabiyoshi.
Babu yadda ta iya haka tabishi suka haye sama tana kallon yadda aka qawata wajen kamar ba saloon ba.
Kofofi tagani asaman jere duk anyi numbering dinsu, haka sukaita tafiya har suka isa wata kofa mai number 22.
Murda handle din kofar yayi ya bude yakoma gefe yana kallonta alamun tashiga.
Babu musu tazo tashige tanajin kamar taita ihu, ta tabbata yanzu magrub tayi don anan ciki ba ganewaba ake kasancewar koina tarr yake da haske.
Ahankali ta tako ta qaraso ciki tana kallon yadda aka qawata dakin, ga mayyukan mai kala kala kan wani mirror mai qatoton madubi, ga naurorin wankin kai kala kala, su dangin wigs, weavon babu wanda babu ga kalandodi na hair styles da henna manne a bangayen dakin bayaga magazines dinsu dake ajiye akan kowanne stool dake gefen kujera.
Qarasawa tayi ga wata kujerar ta zauna tanajin kamar tayi kuka, ita datasan haka abun zai zama da ta wanke kanta dakanta cikin kwanciyan hankali, yanzu yaushe akafara wankin kan bare ayi maganar tafiya gida? Ga shopping din da takeson tayi, that's idan kudin hannunta sun rage.
Tsaki tayi cikin zuciyarta tanajin mugun haushi.
Bude kofar da akayi yasata dagowa, wata budurwa ce tashigo sanye da irin uniform din jikin waitress din qasa.
Cikin fara'a duk ta gaidasu tana masu maraba dazuwa exclusive saloon.
Saudart kadai ta amsa while ashraf kanshi kawai ya dagamata.
Kallon tsadadden wristwatch din hannunshi yayi sannan ya kalli budurwar yace
"Zan shiga sallah, idan kun gama let me know"
"Yes sir" ta amsa a girmame.
Juyowa yayi ya kalleta tayi saurin kauda kai tana hade gira, murmushin gefen baki yayi sannan yafita.
"Ok ma'am please have your seat" inji yarinyar tana murmushi.
"Zanyi sallah nima, ina zanyi ablution?"
Leading dinta tayi inda akeyi ta dauro alwallar sannan tadawo dakin taga har an shimfida mata sallaya.
Hawa tayi ta kabbarta sallarta tafarayi.
Saida tagama tashafa addu'a sannan tadago tana kallon yarinyar wanda da alama christian ce don ga yanayinta ma zaka gane.
"Kin gama ma'am?" Ta tambayeta cikin murmushi
Gyada mata kai tayi tana miqewa tsaye tana linke sallayar.
Amsa yarinyar tayi taje ta adana sannan tadawo ta nunamata wata turning chair tana cewa
"Please have your seat ma'am"
Ba musu tazo ta zauna, hankalinta duk yakoma gida ta qagara agama sutafi.
Miqomata magazine tayi tana cewa
"Pick your choice ma'am"
"Look kawai retouching zakiyimin shikenan" tafada batareda ta amshi magazine dinba.
"Hennah fa? Ko manicure da pedicure? Munayin foot bath ma"
Rolling din idanunta saudart tayi cikin qosawa tace
"Yes duk nasan kunayi, retouching kawai nike so"
"Ok ma'am"
Nan da nan aka fara wankin kan.
Itadai saudart tana zaune tana kallonsu ta mirrorn gabanta, ta matsa wannan ta shafa wannan ta diga wannan kamar baza'ayi wankin kanba.
Saida tagama hade hadenta sannan ta kwantar mata kan tabaya inda za'a tara a wanke tafara wankemata gently da ruwan dumi tana dan cuccuda mata gashin ahankali.
Sosai saudart kejin dadin wankin kan don jitake kamar ana messaging din kan, har wani gyangyadi gyangadi ke son dauketa.
Ba'a dadeba aka gama aka nade kan da qaramin towel yarinyar tafita don discharging din ruwan wankin.
Ba dadewa tadawo tafara tsane mata kan ahankali da towel din sannan ta warwareshi ta kauda, ta dauko hair dryer tafara busarmata dakan.
Cikin dan qanqanin lokacin tagama sannan ta dauko maya mayai na kai masu qamshin gaske tafara mulkemata gashin dasu, nan take gashin yadauki extra sheqi da qamshi saida tagama sannan ta dauko hair straighter tafara straighting din gashin dashi.
Sai gashin duk wanda tariqe da straighter din taja sai su zubo luff harkan kafadarta suna daukan ido.
Haka tayita straighting din gashin harta gama sannan tayimata bonding dinshi a tsakiyar kai in a stylish way ta saki jelar data fado mata har qarshen wuya.
Bayan haka tabi da hair perfume ta feffesa mata akan.
Juyo daita tayi tana fuskantar madubi tana cewa "how was that?"
Shiru saudart tayi tana kallon kanta a mirror, tunda take ba'a ta6a mata irin wannan gyaran gashin ba, it look soo muah!
Murmushi tasaki tana sake kallon kanta a mirrorn tace "great! Yayi kyau sosai"
Washe baki yarinyar tayi cikin jindadin an yabi aikinta tace
"Awnn thanks ma'am, ayimiki hennan? Please just yatsu kawai" tafada cikin marairaicewa
"No gaskiya, yanzu dai nawa ne wankin kan?" Tafada tana addu'ar allah yasa karsu zuqamata kudin da batadasu yanzu ga ATM dinta ta baroshi gida.
"Bari dai agama ma'am, bari kiga you'll like it"
Kafin tasamu zarafin amsawa harta dauko abubuwan qunshin.
Amsar hannunta tayi ta zauna kusada ita tana cewa "wlh harna hango wanda zaiyi fitting din hannunki, bari kiga"
Itadai saudart shiru tayi tana kallonta.
Wanke mata akaifu tafarayi tayi filling sannan ta dauko jan lalle nacikin kwarkwaro takama hannun tafara zanamata simple but breathtaking style a yatsu.
Tsayawa saudart tayi tana kallon yadda take henna din cikin qwarewa, ita kanta henna ba qaramin birgeta ba yayi dukda bada son rantaba akeyi.
Cikin qanqanin lokaci tagama mata, haka ta zauna tanata kallon qunshin harya bushe sannan ta tashi da jagorancin yarinyar taje ta wanke ta dauro alwalla daga nan don har isha'i tayi.
Saida tagama sallar sannan yarinyar tazo tana duba qunshin datayi mata din tana washe baki don tasan baqaramin kyau yayiba, hotuna taita daukar qunshin don sawa ajerin hotunan dasuke talla dasu.
Saida tagama sannan saudart ta sauke ajiyar zuciya ta dau purse dinta tace
"Yanzu nawane bill din?"
Dan bude idanu yarinyar tayi tace "bill? Your husband has settled it ai"
*Husband* ta nanata a zuciyarta jin sunan wani banbarakwai.
"Ok thanks" tafada cikin basarwa ta gyara yafin gyallenta.
"Thanks ma'am, do come back another time" tafada cikin fara'a
"Insha allah" tafada itama tana murmushi.
Tare suka fita daga dakin suka sauka qasa.
Har harabar wajen ta rakota sannan tajuya.
Tundaga nesa ta hangoshi zaune cikin motar kasancewar harabar pauu yake da gaske gashi kuma glass din motar duk a qasa suke, sauke kanta tayi aqasa ta nufi motar kamar mai tausayin taka qasa.
Tunda ta taho yake kallonta babu ko kyaftawa, yarasa dalilin dayasa duk sadda ya kalleta saiyaga kamar anchanzata, yarasa abinda yasa yakejin nishadi azuciyarshi idan yana kallonta.
Jin qarar bude kofar yasashi blinking din idanunshi wanda beyiba tunda yafara kallonta.
Shigowa tayi motar da bismillah kasa kasa sannan tajawo murfin motar tarufe.
Sauke kanta tayi qasa tana wasa da yatsunta jin idanunshi akanta, ita ta tsani kallon nan wlh, bata sonshi kwata kwata.
Ahankali yamaida kallonshi kan yatsun datake wasa dashi ya kafesu da idanu suma don sun mugun tafiya dashi.
Jin shirun yayi yawa yasata dan dagowa ta kalleshi.
Ganin yatsunta yake kallo yasata saurin maidasu cikin gyalenta tana tamke fuska.
Kallonta yayi yadanyi murmushi sannan ya kunna motar yaja suka fice daga wajen.
Tafe suke in silent don wannan karon be kunna komaiba.
Satan kallonta yayi yakuma maida kanshi ga tuqi.
"It's soo cute" taji yafada cikin cool voice
Juyowa tadanyi ta kalleshi shima daidai yajuyo ya kalleta.
Kashemata ido daya yayi yana murmushi yace "qunshin"
Janye idanunta tayi ta kauda kai.
"Please mugani" yafada yana shan wani round about.
Juyowa tayi tasake kallonshi.
Marairaice fuska yayi dayayi mugun yimashi kyau yace "please?"
Saurin dauke kai tasakeyi tana qara qudundune hannun cikin gyalenta.
Murmushi yayi yace "shikenan, zan rama nima, zanyi new low cut bazan bari ki ganiba" yafada kamar dan yaro
Itadai bata juyoba saima qara kallon waje datayi yayinda zuciyarta ke chanxa beat.
Agaban wani qaton supermarket taga yayi parker.
Dan waro idanu tayi don ita duk atunaninta gida sukayi batama lurada sun dauke hanyar gida ba.
Saurin juyowa tayi ganin yana neman sauka.
"I... i thought gida zamu" tafada tana kallonshi.
"No, zan danyi shopping ne" yafada yana fasa fitan
"No please ka maidani gida this is almost 9" tafada tana dan ware manyan idanunta.
"Bazamu dadeb.."
"No nidai mutafi please, mamy tafara kirana, it's late" tafada tanajin kamar tafasa ihu.
"Ok let's do this, mushiga muyi shopping cikin 5mins mu fito bazamuyi taking time ba" yafada persaudingly, shi wannan ma maganar dasuke dadinta yakeji har beson maganar ta yanke
"No ni i dont need anything, idan kuma kai kana buqata kindly take me home idan kakaini kadawo or better still in hau adaidaita" tafada cikin son danne 6acin ranta.
Ganin kamar ranta ya 6aci yasashi sauke ajiyar zuciya yace "Alright then" ya maido kaffafunshi ciki ya maido murfin kofar ya rufe.
Furzar da iska tayi ahankali tana komawa ta jungina da kujerar motar.
Babu yadda ya iya haka ta tada motar suka bar harabar wajen.
Shi da so samune da ba yanzu zasu koma ba, bayan shopping dinnan ma har restaurant yaso suje suyi having dinner tare, jiyake beson abinda zaisa surabu daidaida second daya, soyake su dawwama ahaka har abada.
Jin motar ta dauki shiru yasashi kunna disc din motar, wani cool love music mai antaya mutum cikin shauqi yafara tashi ahankali amotar.
Wani uban zagaye yayi dasu da gangan don kwata kwata beson su isa gidan dawuri, saigashi tafiyar dabata wuce ta minti 15 ba ta daukesu 40mins.
Wani ajiyar zuciya saudart ta sauke ganin sun shigo layinsu atlast don harta fara tantamar anya yasan inda zaikaisu kuwa.
A bakin gate din gidan yatsaya yana sauke ajiyar zuciya.
Dan jimm tayi kamar bazata motsaba saikuma ta sa hannu zata bude murfin kofar tajita gamm.
Juyowa tayi ta kalleshi taga shima ita yake kallo.
Murmushinshi ya sakarmata mai kyau yana dagamata gira daya.
Daure fuska tayi tareda kauda kai gefe wanda hakan yasashi sakin wani murmushin.
"Ka budemin kofar" tafada batareda tajuyoba
"A