Showing 126001 words to 129000 words out of 156457 words
nawa?" Yafada yana kallon qeyar data juyamashi
Shiru tayi batace komaiba kuma bata juyoba.
Shima shirun yayi yana aikin kallonta.
Ganin batada niyyar juyowa ko tasake magana yasashi sakin murmushi mai sauti yace
"Alright sorry angry bird, i don't mean to annoy you, just want to say... being with you is the sweetest thing ever, thank you for today" yaqarasa ahankali kamar mai rada
Shiru tayi tana sauraronshi still bata juyoba
"Idan zaki sake fita, alert me, zanzo if kuma am busy zan aiko driver, kinji?" Yafada cikin murya mai kamada ta rarrashi.
Kada mashi kai tayi ahankali batareda ta dagoba.
Shiru motar taqara dauka sai cool music din dake tashi qasa qasa a motar.
Qara kai hannun tayi a handle din motar ta murda dukda tasan be budeba.
Ahankali shima yakai hannu anashi gefen idanunshi akanta yayi unlocking din kofar.
Ganin haka yasata bude motar tazira kafarta daya zata sauka.
Cak ta tsaya jin an riqomata hannu.
Tsayawa tayi daga yunkurin saukar baterada ta juyoba gabanta na faduwa.
"I'll miss you" yafada ahankali
Shiru tayi kuma bata juyoba.
"Please find a place in your heart and squeeze me in, i'll be grateful no matter how tiny the space it... don't let me keep wandering about helplessly in your love" yafada emotionally.
Shiru tayi bugun zuciyarta na qaruwa sosai, she's feeling somehow, tanajin wani iri sosai.
"Please give me another chance.... the chance to show you how i really feel about you" yasake fada still riqeda soft hannunta.
"I... i want to go, dare... yayi" tafada muryarta nadan cracking
Shiru yayi yana kallonta na wasu mintuna sannan ahankali taji yana dago hannunta dake cikin nashi.
Saurin runtse idanu tayi don tasan abinda zai biyo baya.
"Muah!" Yaba hannun light kiss wanda saida tajishi har cikin ranta.
"I love you" yafada ahankali sannan ya saki hannun.
Kamar jira take yasaki sai tayi saurin sauka daga motar tayi gaba batareda ta juyoba don ko rufe murfin kofar batayi ba.
Binta yayi da kallo cikin wani yanayi harta shige sannan ya sauke ajiyar xuciya ahankali.
Yadan dade anan sannan yafito ya zagayo yarufe kofar sannan yakoma mazauninshi ya rufo kofar ya tada motar yabar kofar gidan feeling so empty again...✍
Ummin fasihu🧚🏻♀️[9/12, 5:41 PM] Makera: 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)
Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)
087
Itakau dakyar tasamu tashige gidan tana tafiya tanajin kafaffuwanta na dan harhardewa.
Wani irin abu takeji wanda batasan taqamaimen menene ba, sosai magangganun ashraf suka shigeta ga dumin da hannunta keyi haryanzu kamar yana cikin nashi.
Tsayawa tayi bakin kofar falo tana qoqarin daidaita nutsuwanta, danna power botton din wayarta tayi takawo haske.
Wara manyan idanunta tayi ganin har 9:27 yayi.
Yanxu me zata cema mamy ya tsaidata har wannan lokacin?
Ganin qara 6ata lokaci take yasa tayi taking din deep breath sannan ta danna doorbell ahankali.
Ba'a wani dau lokaci ba aka bude kofar
Ido hudun dasukayi da mamy yasa qirjinta bugawa tayi saurin sunkuyar dakai cikin diriricewa.
Wucewa ciki mamy tayi batareda ta kulata ba hakan yasa itama tabiyota ciki kamar kazar da kwai yafashemawa aciki
Saida ta ida qarasowa ciki taga ashe harda Abba a falon.
Gabadaya taji ta daburce don tafiyarma saida ta nemi gagararta.
Abdul ne yarugo dagudu ya rungumeta yana tsalle yana mata oyoyo.
Saurin riqeshi tayi itama ganin yana neman kayar daita tana murmushin yaqe sannan suka qarasa cikin falon gabadaya.
Zama tayi qasan carpet tana murmushi ta gaida abba.
Amsawa yayi cikin fara'a yana tsokanar abdul wai ya tadata yafiye son jiki kamar mage.
Turo baki abdul yayi yana qara matsawa jikin saudart yana cewa
"Aunty kinji Abba ko?"
Dan murmushi tayi tana shafa kanshi kawai.
"Aunty what took you and uncle so long? Tundazu naketa jiranki kidawo in gwadamaki wani abu amma kikaqi dawowa" yaqarashe maganar yana turo baki.
Wata iriyar kunya ce ta kamata tadan sadda kai tana dan rintse idanu.
"Kinji aunty? Ina ke da uncle kukaje kuka dade" ya sake tambaya yana dan leqa fuskarta.
Kasa dagowa tayi don sosai taqara nutsewa cikin kunya musanmman datasan Abba na wajen kuma yana jinsu jitayi kamar ta zubamashi rankwashi akai don takaici.
Abba yayi gyaran murya yace
"To yafa kamata kowa yaje ya kwanta, dare yayi akashe t.vn hakanan"
Babu musu aka kashe kallon duk sukaima juna saida safe sannan suka wuce sama su Abba suka bisu da kallo har suka kule.
Ajiyar Zuciya mamy ta sauke ta kalli Abba tace
"Yanzu Alhaji aganinka yakamata azubama yarinyarnan ido haka? Da aurenta tana zaune gida? Bama wannan ba, baku ganin anshiga haqqin yaronnan? Sai inga kamar hakan be daceba" tafada atausashe damuwa a fuskarta.
"Hakane khadija, yauma daga wajen alhaji shamsu nayonan, insha allah zata koma dakinta very soon"
Dadi sosai mamy taji tace
"To allah ya amince"
Amsawa yayi da amin yana tashi shima yayi part dinshi.
Saida mamy ta kashe komai na falon sannan tashiga dakinta ta shirya tafito.
Saida ta leqa dakunan yaran don tabbatarda kowa ya kwanta kamar yadda tasaba sannan ta fito tanufi part din Abba.
Tanajin alamun ta tafi ta bude idanunta don dama tanajin takunta tayi saurin kwanciya tayi pretending barci takeyi.
Tashi tayi xaune ta jingina da kan gado ta dora tunaninda take daga inda ta tsaya.
Ita tama rasa taqamaimen meke damunta, kawai dai jinta take wani iri badadi ga tunanin magangganun ashraf dayaqi barin brain dinta.
Takusan raba dare ahakan kafin barci ya sadado ya saceta.
Tun daga ranar bata sake bari sun qara haduwa ba, duk randa tasan zaizo saita qirqiri ciwon kan qarya ko tace batajin dadi, zuwanshi uku tana haka.
Be ta6a damuwaba saima sayayyar dayakeyi mata yaba su abdul sukai mata donshi baqaramin kunyar shiga ciki yakeba.
Duk zuwanshi sau uku ya ta6a shiga suka gaisa da mamy shima a darare, kunyar matar yakeji sosai kamar ya nitse dukda sakin fuskar dayake samu awajenta.
Abba ma sun hadu dashi sau daya, wani zuwan daya ta6a yi shima daidai abba yadawo daga aiki.
Shima a kunyacen yabishi falonshi suka gaisa sannan yafito.
Kunyarsu yakeji sosai gani yake suna kallonshi da abinda ya aikata shiyasa duk yadda sukaso yasaki jiki dasu yakasa don duk lokacin dayake tareda su yanajin sense of guilt a jikinshi musanmman daddy don ko hada ido be yarda suyi don sosai yakejin nauyinshi.
Shikau daddy yadda kasan d'a haka ya daukeshi, yana qoqarin janshi jiki don ganin ya sake dashi amma yaqiya don the more yake janshi jiki the more yakejin nauyinshi.
***
Yau laraba, tunda ya dawo daga office yake shiri don zuwa ganin tauraruwar tashi dukda beda tabbacin yauma zai ganta.
Wanka sosai ya dauka cikin manyan kaya kalar milk wanda akaima aikin brown colour, kanshi sanyeda hula brown mai ratsi ratsin milk colour.
Hannunshi daure da agogon fata brown sai kaffafuwanshi dake sanye da brown half cover shoes.
Sosai yayi kyau kuma kamalarshi taqara bayyana, saida yafeshe jikinshi da turarrukanshi sannan ya dauki car keys dinshi da waya yafita.
A falo ya tadda ummy zaune baby tayi matashin kai da cinyarta tana mata tsifa.
Saurin tashi zaune baby tayi hangoshi datayi yana saukowa qasa.
Duk binshi sukayi da kallo harya qaraso falon don ba qaramin haduwa yayiba kuma ko basu tambayaba sunsan inda zashi.
Hararar gefen ido ya jefama baby ganin tawani kafeshi da ido, hakan yasata kauda kai tana qumshe dariyarta.
Zuwa yayi ya zauna dayan gefen ummy sai ya kasance sun sata tsakiya ya dora kanshi bisa kafadarta.
Ta6e baki tadanyi tace
"Sai ina kuma daga dawowanka?"
Turo baki yadanyi sannan yace
"Unguwa"
"To Allah ya tsare ni tadamin kafada ajebo kawai" tafada tana ture kanshi.
Tashi yayi zaune yana kallonta fuska adan kwa6e.
"Yaya in rakaka unguwar?" Inji baby cikin neman magana
Wata uwar harara ya gallamata sannan yace
"Eh rakani din tunda ni sa'anki ne"
"Sorry" tafada tana toshe bakinta don dariya keson kufce mata
Kwafa yayi sannan ya tashi tsaye ya kalli ummy
"Ummy saina dawo"
"To adawo lfy" inji ummy
"Yaya allah ya kiyaye agaidasu"
Juyowa yayi ya kalleta tayi saurin sadda kai qasa tana shigewa jikin ummy.
Kwafa yayi sannan yafice daga dakin.
Tureta ummy tayi tana cewa
"Ni dagani ga tsoro ga jan fada"
Dariya baby ta kyalkyale dashi tace
"Wlh ummy wajen aunty zaya, oh su yaya manya! Kinji yadda yaketa qamshi kuwa?"
"Mtcheew saiya kamaki sannan ido ya raina fata kizo ki dameni da raki ko? Cigaba"
Dariya tasakeyi tace
"Ai yanzu naga yayi sanyi, yabarmin wannan muguntar ko saboda aunty ne oho? Ni ummy yaushe zata koma ne? Kullum shikenan yaita zaryar xance kamar saurayi?"
"Ni tadani kiga magrib takusa, kikuma qulle kan nan hakanan kin ida tsefeshi gobe idan munada rabon ganinta, kuma kema kitashi kiyi haramar sallar"
"Toh ummy" inji baby tana daukar hularta zata rufe kan itakuma ummy tayi gaba.
Saida yatsaya ahanya yasiyama su abdul chocolates da kayan malaqi kamar yadda yasaba sannan yanufi gidan.
Lokacin daya isa har anfara kiraye kirayen sallar magrib.
Parking yayi inda yasaba parkawa yayi saurin fitowa sanadin g
hango Abba dayayi.
Qarasawa wajenshi yayi yana dan murmushi kanshi qasa, shima abba fara'a fall fuskarshi yake kallonshi.
Koda ya qaraso, hannu abba yabashi suyi musabaha, amsar hannun yayi a kunyace ya duqa still hannunshi ana abban ya gaidashi cikin girmamawa.
Amsamashi shima yayi cikin fara'a yana tambayarshi ya mutan gida shikuma yana amsamashi da duk suna lfy.
Haka suka jera tare suka fita don dama massalaci abba yanufa don har ankusa kabbara sallar.
Koda aka gama ma tare suka fito suna tafe suna fira dikda ashraf bawani sakin jikinshiba yayi sosai.
Tare suka wuce part din abba sakamakon cemashi da abba yayi yanason magana dashi.
Haka kawai yaji gabanshi na faduwa yana addu'ar allah yasadai lafiya cikin zuciyarshi.
Zama abba yayi kan daya daga cikin kujerun dakin ashraf ya xauna kan centre carpet ta tankwashe kaffafunshi dake sanye da baqaqqen safa don yariga yacire takalminshi abakin kofa ya sadda kai yana sauraron abinda abba zaice.
Gyaran murya abba yadanyi sannan yace
"To alhamdulillah, dama ba komai yasa nace kazoba saidan na sanar dakai idan ka shirya kana iya zuwa ka dauki matarka kutafi jibi idan allah yakaimu, fatanmu akanku shine allah yabaku xaman lafiya ya kuma albarkaci zaman daku baki daya"
Wani farinciki nan take ya lullu6e ashraf, jiyake kamar yatashi ya taka rawa don murna.
Godiya yashiga zubama abba kamar wani maroqi kallo daya zakamashi kasan he's soo happy.
Shima abba yaji dadin reaction dinshi don haka yashiga yimishi nasihohi masu shiga xuciya sosai.
Saida suka kusan rabin awa ahaka sannan abba ya sallameshi.
Fitowa yayi feeling soo happy, jiyake babu wanda yakaishi farinciki yau a duniyan nan. He can't wait yaganshi da ita agida su kadai just like before.
Koda yafito harsu abdul sunfito don tuni maigadi ya sanar dasu zuwanshi.
Dagudu suka nufoshi suka rungume kaffafunshi suna murna.
Nan suka shiga gaidashi yana amsawa cikin murmushi, yacema habeeb yaje yacewa mamy zaishigo su gaisa.
Can saiga habeeb yafito yana cewa sutaho.
Kama hannayensu yayi suka nufi main door din suna tafe abdul na xubamashi surutu.
Da sallama suka shiga falon mamy dake zaune sanye da hijab ta amsa fuskarta asake.
Qarasowa dakin yayi akunyace ya zauna inda yasaba zama qasa yashiga gaidata kanshi kasa tana amsawa cikin fara'a.
Tashi tayi ta haye sama don kiran saudart da tunda taji labarin yaxo ta ruga sama.
Shima ashraf fita yayi tareda su habeeb don jiran fitowarta yana masu habeeb tambayoyi gameda karatunsu.
Qudundune ta isketa cikin bargo don har kai ta lullu6e.
Girgiza kai mamy tayi ta qaraso cikin dakin fuska daure tace
"Zaki tashi ne ko saina zubamiki dundu abaya?"
Jin haka yasata saurin tashi bashiri don tasan halin mamy
"Saiki shirya kije ki sameshi, allah dai ya shiryaki kekam don abin naki naga sai ana hadawa da addu'a"
Turo baki tadanyi tace
"Ummy am not feeling well fa"
Harara mamy ta aikamata sannan tafita batareda tasake cemata komaiba.
Sake turo baki take tana gunguni don ita allah yasani batason fitarnan dazatayi, yanzu data fita zai maidata mirror yana kallonta da mayun idanun nan dasuke sata jin wani iri.
Haka ta tashi tana kumburi ta canza kayanta daga doguwar armless gown zuwa doguwar rigar atamfa mai kalar baqi da jaa ta dora jan three quater hijab tadan fesa turare tafita tanajin an takurawa rayuwarta.
Tun daga nesa ta hangosu gefen parking space shi dasu habeeb zazzaune kan plastic chair sun sashi a tsakiya sunata zubamashi surutu.
Sauke idanunta tayi ganin shima ya dago yana kallonta ta cigaba da nufosu kanta qasa tana jujjuya phone din hannunta.
Da sallama ta qaraso wajen duk suka kalleta suna amsawa.
Jan wata kujera tayi ta zauna tana bada dan tazara a tsakaninsu sannan ta gaidashi ahankali.
Ansawa yayi yana kallonta kamar zai hadiyeta don sosai tayimashi kyau kuma daya tuna cewa jibi warhaka tana gidanshi sai yaji ranshi yaqarayin fess.
Habeeb yazo tafiya don ba laifi yana hankali sosai ashraf ya riqo hannunshi yana cewa ina zashi?
Murmushi yayi yace ciki ashraf yace A'a su tsaya ai basu gama firarba don yasan kosun tafi bawani hira zasuyiba da saudart saidai suyita zaman kuramen dasuka saba don koyayi niyyar janta da fira bata bashi hadin kai sai taita amsamashi a taqaice ko tamayi shiru.
Haka sukaita firarsu tana jinsu ko dagowa batayiba shikau ashraf suna fira yana kallonta qasa qasa don sosai take qara chanza mashi gawani kyau datake qarawa kullum.
Haka akayi firar ranar tsakaninshi dasu habeeb while saudart tun maganarsu tafarko ko tari bata qaraba burinta kawai yatafi don atakure take sosai.
Saida akafara kiraye kirayen isha'i sannan yatashi da nufin tafiya.
Sallama sukayi sama sama tajuya tashige ciki kamar dama akan qaya take, binta yayi da kallo har saida ta shige sannan ya girgiza kai yana dan murmushi ya tafi dasu habeeb wajen motarshi yaciro kayan daya siyomusu suka amsa suna godiya sannan yashiga motarshi ya tadda yafita suna dagamashi hannu.
Tuqi yake amma sai sakin murmushi yake from time to time.
Jiyake babu wanda yakaishi farinciki yau aduniya, he can't wait jibi tayi yaxo yatafi da abinshi.
Da daddare bayan kowa ya kwanta Abba ke sanar daita yadda sukayi da Ashraf.
Sosai taji dadi don har saida hakan ya bayyana sosai a fuskarta.
Dariya abba yayi yace
"Dole ai kiyi murna tunda wanda ta tsaremiki wuri zata tafi, ai ina lura daku kwanan nan bakida abun hantara kamar ita"
Murmushi mamy tayi tace
"Wlh ba haka bane, saudart din ce sai ahankali gashi banajin dadin ganunta tana zaune haka da aure kanta"
"Ai hakan shine daidai don yanzu shi kanshi ashraf din bazai wahala ba kamar yadda zaiyi da tun farkon faruwar abun takoma, yanzu nasan zuciyarta tayi sanyi sosai kuma bazai sha wahala wajen shawo kanta ba don naga alamun ke tabiyo wajen taurin kai, kinga da ana gaba abin takoma ba qaramin wahala zaishaba wajenta amma kinga yanzu lokacin yadanja kuma yana yawan zuwa suna ganawa so sai inga yanzu it will be more easier for him"
"To allah yasa alhaji, kuma wlh kunyi dubara don saudart halinta sai ita idan ta nacewa abu ta nacemashi kenan, allah ya basu zaman lfy yakuma hada kansu"
Amsawa abba yayi da amin cikin jindadi da qaunar matar tashi dayakejinta daya tamkar dubu...✍
Sorry for jina shiru kwana 2.
Kusamu a addu'a anyi kidnapping din wani brother namu😭
Allah ya ku6uto dasu cikin qoshin lfy🤲
Ummin fasihu🧚🏻♀️
[9/12, 5:42 PM] Aeesha umar aliyu: 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)
088
Yana komawa gida yafadawa ummy yadda sukayi da abba cikin farinciki.
Itama ummy tayi farinciki sosai nan ta shiga yimashi fada da nasihohi masu matuqar amfani, bashi yakoma dakinshiba har sai wajajen shadayan dare.
Shima barcin qin daukarshi yayi dawuri haka yaita juyi yana ta saqe saqe har barcin ya sadado ya daukeshi.
Washegari tunda yatashi yashiga busy, be nan be can kamar jigida.
Shirye shirye yake sosai na tarar saudart wanda bemayi wannan doqin ba lokacin daurin aurensu, shi sai yanzu yake jin irin doqin nan na angwaye, jiyake kamar yajawo ranar taxo don beda burin daya wuce ace gashi ga saudart a muhalli daya amatsayin tashi halak malak.
Itakau saudart batasan wainar da ake toyawaba don babu wanda yace mata komai.
Ranar mamy da kanta tacemata ta shirya ta rakata unguwa.
Dadi taji sosai don tunda taxo gidan sau daya ta ta6a fita wanda tayi da A.A, sosai take cikin kewa da kadaici musanmman idansu habeeb basanan gashi batason tambayar fita wajen mamy don tasan tana iya sawa kuma ta gayawa ashraf.
Da harta ma fara shawarar komawa gidan daddy ganin batajin dadin zaman nan sosai amma kwata kwata mamy taqima bata fuska bare tayi yunqurin tunkararta da zancen.
Cikeda doqi ta shirya cikin wata milk colour roll silk gown mai adon flowers brown ta sanya brown madaidaiciyar hijabi dayai mugun mata kyau ta dan yi simple makeup sannan tafesa cool turarenta.
Koda tafito itama mamy tafito ashirye itama don haka batareda 6ata lokaci ba suka garzaya parking space saudart tashiga mazaunin driver kasancewar ita zata tuqasu itakuma mamy tazauna dayan gefen suka fice daga gidan.
Sosai saudart taji dadin fitarsu ta yau don yawo sukayi sosai gashi mamy is so free today babu fadan nan nata haka sukaita labari gwanin sha'awa.
Saloon suka fara biyawa aka wankemasu kai aka kitsesu, sosai shukku din saudart yayi kyau yazubo har wuyanta gasu qananu ne sosai.
Bayan haka aka mata qunshi mai shegen kyau na baqi da jaa kamar ba hannu ya zanaba.
Bayan haka suka biya supermarket sukayi shopping kala kala don ranar saida saudart ta jidi duk abinda take buqata bata samu damar fita siye ba.
Itadai mamy batace mata komaiba itama tashiga daukar mata english wears na nightie masu kyan gaske.
Haka suka gama shopping din suka fito sannan direct suka yi gidan wata qawar mamy.
Sundan dade gidan sannan suka taho bayan ta amshi turarrukan wuta dana jiki da su humra data bada sautun akawomata sannan suka baro gidan sukayo gida.
Koda suka dawo mamy bata zaunaba tayi kitchen ta hada mata wani shegen farfesun kayan ciki dasuka ji kayan hade hade kala kala da kunun aya dayaji madara da kwakwa sosai ta kawomata ta tisata gaba ta shanyesu tass.
Sannan ta hada mata kujerar garwashi yazuba turare aciki tasata tsugunno akai.
Itadai saudart yin abinda mamy tasata kawai take tana wondering meke faruwa, dukda tunda tazo gidan takemata wannan abin amma na yanzu yafi nada. Sharewa tayi kawai ta shashantar da zancen don gani tayi it doesn't worth 6ata lokaci wajen tunani akanshi.
Washegari tinda su abdul suka tafi makaranta takoma daki ta kwanta tana hutawa kafin lokacin girkin rana yayi.
Tana tsaka da waya da P.A dinta na bakery mamy tashigo dakin da sallama.
Murmushi tayima mamyn sannan tayima maryam din sallama akan zata kirata later.
Dagowa tayi ta kalli mamy da itama ita tazuba ma idanu tana kallo.
Murmushi tayi tace "mamy na?"
Ajiyar zuciya mamy tayi sannan ta qaraso ta zauna gefenta tana kallon yadda cikin yan kwanakin nan taqara wani kyau da cika.
"Angel?" Inji mamy cikin tattausar murya
Kallonta saudart keyi cikin jin dadin sunan data kirata wanda rabon da takirata dashi hartama manta.
"na'am sweet mamy na" tafada tana kwantowa kafadar mamyn a shagwa6e.
Hannu mamy tasa tana shafamata kanta dayaji qananun kitso sai daukar ido