Showing 138001 words to 141000 words out of 156457 words

Chapter 47 - AUREN KWANGILA COMPLETE HAUSA NOVEL

14 Jul 2025

5839

gajiya ba.

Binta da kallo yafarayi daga kafaffunta dake sanye da takalmin soso baqaqe wanda suka matuqar qawata yan qannanun shaped feets dinta zuwa dogayen kaffafunta sake glowing zuwa round pecking shaped hips dinta zuwa tiny waist dinta zuwa straight bayanta zuwa straight wuyanta zuwa kanta dake daukeda headphones.

Nan take yaji wata iriyar kasala ta saukarmashi yakoma ya jingina da kofa yana lumshe idanunshi yana sake budesu akanta.

She's just perfect! Gaskiya dolene ya godema Allah yakuma cigaba da godemashi daya mallaka mashi ita a matsayin matarshi halak malak, gaskiya da ya rasata da yayi babban rashi a rayuwarshi.

Cigaba yayi da binta da ido duk motsin dazatayi, yanajin wani abu na tasomashi sanadin yadda take dan motsawa wanda kesa hips dinta moving in a sexy way.

Saudart kau batasan wainar da ake toyawa ba, she's super happy yau ummy tabari tashiga kitchen, tun washegarin ranar da tadawo gidan take nacin zata shiga kitchen ummy na hanawa acewarta tayi zamanta ta huta batason ta huta, itakau aduniya babu abinda ke burgeta kuma kebata nishadi idan tanayi kamar girki shiyasa kullum saita tisata gaba kamar zatayi kuka akan tabari tashiga, to yau dai allah ya daurata kanta tasamu ta yarda amma da sharadin baby zata tayata, dagudu ta amince don she missed cooking dan kwana biyun nan dabatayi ba.

Koda taje tasamu baby ta tadda barci take hakan yasa ta lalla6a tafito don dama tafison tayi ita kadai don baby bawani abun kirki zata iya tayata dashi ba inbanda cikata da surutun dazatayi.

Ta dan dauki lokaci tana tunanin me yakamata ta dafa musu sannan ta yanke shawaran yimusu fried rice da pepper chicken sai tayi baking din cup cakes sai ta hada banana smoothie.

Saboda aikin yayimata dadi yasata dodewa da headphones tana sauraron cool music ta hau aiki.


Tun dazu take jinta somehow tanajin kamar ana kallonta ga wani sabon qamshi wanda bazata iya cewa na menene ba datakeji amma dayake hankalinta be wajen bata kawo komai aranta ba, ita burinta kafin ummy tasauko tagama komai don saida ummy ta kashemata warning kan cewa ta girka light simple food wai karta wahalar dakanta kuma tasan tana saukowa taga abinda take tofa saita sata bari don haka hankalinta gabadaya naga abinda take tana gudanar da aikinta cikin qwarewa da kuzari.

Ahankali tahau bin waqar datake ji acikin headphones dinta na mawaqiyar nan *simi* mai taken *chemistry* cikin melodious muryarta

"But i don't even know if am your spec oh

I don't even know if i'll take you grantful ehh

You don't even know my widest dream

Maybe it will just be chemistry

But i knoww ooo

Kind of maybe you really do like me

Maybe me and you we can try to

Do this love something

Maybe there's something there.

And i know ohhh

Kind of maybe you really do like me

Maybe i can be your baby

We should start fronting

Maybe there's something else"


Shidewa ne kawai ashraf beyiba alokacin

Sosai zuciyarshi ta kumburo don shauki, jiyake kamar ya ruga dagudu ya chakumota yashiga bata the hot kiss ever.

Ahankali yake sauke numfashi yana kallonta yanajin kanshi na qara girma don shauqi.

Sosai waqar tayi affecting dinshi don jiyake kamar yana narkewa ne ahankali.

Ahankali ya dago daga jikin kofar dayake jingine daita yanufota ahankali yana kallonta yana sauraron yadda take bin waqar.


Zuba bananas din data yanyanka tayi a blender ta zuba cubes din qanqara sai madarar ruwa datasa bada yawaba ta rufe da marfin blender din tana waqarta cikeda nishadi tayi plugging din waqar blender din jikin socket ta kunna tasa hannu ta danne murfin don kar ya bude.

Jinta take very uncomfortable jikinta harwani tsima yake hakan yasa tadan saci kallon bayanta ahankali.

Ganin kamar inuwar mutum abayanta yasata saurin sakin murfin blender din atsorace ta juyo.

Ganin mutum daff daita yasata ware manyan idanunta ta bude baki don sakin ihu tana ja da baya

Saurin janyota yayi yasa hannu yayi saurin toshemata baki don kar ihunta yafito.

Jikinta ne ya dauki rawa nan take tanajin kamar ta sume don firgici amma suman yaqi zuwa, ashe idan ma aka suma to firgicin bekai firgici bane.

Jiki na rawa take qoqarin kwacewa daga riqon dayayimata, idanunta sun rufe don ko ganeshi batayi ba ma saboda tsabar yadda ta tsorata.

Ganin haka yasashi qara riqota batareda ya saki bakinba yace

"Shiiish it's me, nine... calm down... look at me"

Ganin kamar taki nutsuwa yasashi sake cewa
"Nine.. A.A.. mijinki, open your eyes" yafada wannan karon cikin dan daga murya hakan yasa ta shiga bin fuskarshi da kallo kamar meson gano eh shi din ne?

Kada mata kai yayi cikin tabbatarwa yace
"Eh nine... am sorry i scared you, bansan zaki tsorata bane"

Ahankali take sauke numfashi tana kallonshi nutsuwarta na dawomata ahankali.

Shima kallonta yake batareda ya saketa ba ko ya budemata baki ba yana jin yadda zuciyarta haryanzu ke bugawa abnormally.

Haka sukaita kallon juna har ta ida dawowa nutsuwarta, mitsiniya tafarayi alamun ya saketa.

"No please don't, it's me... nine" yafada don shi duk atunaninshi har lokacin firgicin ne alhalin ba haka bane kawai sotake yasaketa saboda yadda takeji.

Kada mashi kai tayi alamun eh ta ganeshi.

"Nine..Ashraf.. A.A?" Yafada yana kallonta sosai

Janye idanunta tayi jin yadda nashi suka haskemata nata ta kada kai ahankali

"Am sorry.. na tsorataki, i don't mean to" yasake fada yana kallonta

Batareda ta kalleshi ba tasake kadamashi kai

Ganin yacigaba da kallonta bataresa niyyar sakintaba tasata qara yin motsi uncomfortably

"Ok...ok zan sakeki amma promise bazakiyi ihu ba, pleease" yaja please din a shagwa6e.

Saurin sauke idanunta tayi jin yadda taji shagwa6ar tashi a cikin zuciyarta ta kada kai ahankali

"Promise?" Yafada yana kallonta

Nanma kada mashi kai tayi idanunta aqasa.

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya saketa tareda janye hannunshi daga bakinta.

Wani nannauyan ajiyar zuciya ta sauke tana hadiye miyaun dasuka tararmata abaki.

Dan jada baya tayi don matsawa daga kusadashi.

Jin bayan kafanta iska yadan bugeshi yasata dan waro idanu don shaff ita tama manta da kalar shigar dake jikinta.

Saurin sake jada baya tayi cikin tsananin kunya da nauyi tanajin kamar ta nitse ta huta.

Shikau bema luraba saima wucewa dayayi wajen blender da haryanzu tanayi amma duk kusan rabi ya watse don tuni murfin yayi tsalle yayi nashi wajen.

Kashe blender yayi sannan yajuyo ya kalleta inda take tsaye sai faman mitsiniya take cikin rashin sanin abunyi jitake kamar ta arta dagudu tafice daga kitchen din.

Hade rai yadanyi yana kallonta yace
"What is this?"

Jin yanayin dayayi maganar yasata dan dagowa ta kalleshi taga yawani hada rai yana nuna abubuwan datakeyi na girki.

"Dama ummy ta riqemin mata ne don tasata aikin bauta?" Yafada yana huro hanci

Tsayawa tayi tana kallonshi kawai batareda tace komaiba.

Bubbude pots din wajen yake yana dudduba abubuwan datakeyi, binshi da ido kawai take tana kallon ikon allah.

"Ca6! Lallaima, so dama dalilin kwaceki datayi kenan? Tazo taita saki aikin bauta? Salan kiyi fading ki tottoye? No wonder, wato ga yar aiki tasamu a bulus ko? Harda wani saki girki fin daya wato ga cooking engine" yafada yana rurrufe tukannen

Itadai kallon ikon allah kawai take tama rasa abin cewa.

Kallonta yayi yana qara tamke fuska yadawo sak A.A dinshi yace
"Yanzu fisabillilah hakan ya dace? Kema why not ki kirani ki fadamin? Allah kadai yasan abubuwan datake saki kinayi, amtsayinki na mrs A.A, mrs A.A a kitchen? Ina maid din gidan nan tukunna? Ba aikinta bane? Uban me take zata barmin ke a kitchen? Ina wannan picking stick din itama? Duk sun nade sun barminke anan kina wahala don basusan ciwonki ba ko?"

Itadai sakin baki tayi kawai tana kallonshi don tama rasa me zatace mashi ganin yadda ya haqiqance yanata fada.

"To wlh baxai yiwuba, muje yau sainaji dalilin mayarmin mata baiwa agidannan.. muje" yafada yana kamo tsintsiyar hannunta yayi gaba

Ganin dagaske yake yasata saurin kwacewa tana dan komawa baya.

Juyowa yayi ya kalleta yace
"Come mana, babu abinda zasu miki, ba ganiba?"

Janye idanunta tayi daga kanshi ta kauda kai tana turo baki

Dawowa yayi kusada ita yace
"Menene? Are you scared?"

Dan kallonshi tayi taqara janye idanunta sannan kamar mai ciwon baki tace
"Ni babu wanda yayi forcing dina, it's my choice, ni nace zanyi" taqarashe zancen tana kauda kai tana murguda baki

"then why? Sokike ki qone?" Yafada yana kallonta

Sake kallonshi tayi sannan ta kauda kai tana sake turo baki, duk ya 6atamata aikinta, mema yakawoshi gidan a daidai wannab lokacin.

Wucewa tayi wajen smoothie dinta da duk rabi sun zube blender tayi faca faca tana kallonshi kamar zatayi kuka.

"Kizo mutafi, let someone finish it, ina baby ma tukunna"

Banza tayi dashi tafara qoqarin juye kingin smoothie din

Kamar daga sama taji muryar ummy a falo tana cewa
"Daughter! Daughter!! Wai haryanzu girkin ne?"

Ware idanu tayi tayi saurin juyowa.

"Yauwa gatanan tama sauko, bari inje inji dalilin sa matata aiki" inji ashraf yana nufar kofa.

Batasan ya akayiba sai gani tayi tasha gabanshi gabanta na mugun faduwa, cak ya tsaya yana kallonta kawai

Girgiza mashi kai tashigayi tana waiwayen kofa.

"Please ka rufamini asiri karta ganka anan, na bani" tafada tana zare idanunta a tsorace

Tsayawa yayi yana kallonta kawai ganin yadda tawani tare hanya tana leqen baya

"Wannan trolleyn fa? Daughter! Daughter!!" Suka sakejin muryarta tana nufo kitchen din.

Qara ware manyan eyes dinta tayi tayi saurin kamo hannunshi batareda tasan tayiba tana cewa
"Innalillahi, wayyo banso tazo taganka, please hide"

Tafada tana riqeshi sosai.

Wutar ashraf ne ta dauke diff jin yadda ta kama mashi hannu sosai kamar her life depend on it.

Bude baki yayi zaiyi magana tayi saurin saka dayan hannunta ta dode mashi baki tana girgixa mashi kai a mugun tsorave tana jin takun ummy daff da kofa...✍

Ummin fasihu🧚🏻‍♀️[12/1, 8:33 PM]

Ummin fasihu🧚🏻‍♀️
[12/2, 1:42 PM] Aeesha umar aliyu: 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)

Alhamdullilah am back after almost two Months of vacations, fatan duk nasameku lfy, thank you all for your concern, wani sa'in tsoronma hawa whatsapp nake saboda jaje, amma that's all signs of love you guys got for me, nagode da qauna, Allah ya dorar da zumuncinmu har a aljannatul firddaus (Amin)


Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)




093


Bude baki yayi zaiyi magana tayi saurin saka dayan hannunta ta dode mashi baki tana girgiza mashi kai a mugun tsorace tana jin takun ummy daff da kofa.

Ganin yadda take a tsorace don hannunta dake a bakinshi har rawa rawa yake yasashi janye hannun yace
"Look, I'll hide but on one condition"

Saurin kada mashi kai tayi idanunta na kawo ruwa, idan ummy ta taddashi anan Ai ta banu, Ina zata sa kanta don kunya?

"Zakimin coffee anjima kikawo apartment dina, promise?" Yafada yana dago qaramin yatsar hannunshi alamun su qula

"Yes, promise... Please go" tafada tana turashi a kidime.

Wuff kamar iska haka ya ruga ya la6e a bayan kofar kitchen din yayinda saudart tayi saurin juyawa tana tatta6a abinda ke kan wuta batareda tasan abinda takeyiba.

"Daughter?" Inji ummy data shigo kitchen din

Saurin juyowa tayi tana washe baki cikin yaqe tana fadin
"Na'am ummy" yayinda take yawo da idanunta cikin kitchen din a fake tana son gano inda ya 6uya.

Ganin shi bayan kofa yana dagamata hannu yasa gabanta faduwa tayi saurin janye idanunta ta maida kan ummy dake bubbude pots din

"What?" Inji ummy ganin abinda take girkawa.

Qara Satan kallon kofar saudart tayi a tsorace don tasan da ummy ta juyo dolene ta ganshi.

Ganinshi tayi yafita sai leqo kai dayake kamar kusu mai shirin sata.

Narke fuska tayi tana kallonshi pleadingly alamun please ya fita.

Kashe mata ido yayi sannan yayimata alamun karki manta da deal dinmu

Ganin ummy na niyyar juyowa yasashi saurin ficewa

Saida Ummy tabi kofar da kallo jin kamar taji motsi awajen sannan ta maido kallonta kan saudart daketa raba idanu kamar marar gaskiya.

"Dole kiyita zare idanu Ai, I told you kiyi light food shine kika tarki wannan uban girkin ko? Besides Ina baby danace ta tayaki?"

Shagwa6e fiska saudart tayi tana cewa
"Ummy barci fa take and na tadata taqi tashi shiyasa na kyaleta"

"Ai kinyi daidai, zanga Wanda zai sake bari gobe ki shiga kitchen, yanzu kwashe naga duk sunyi Bari naje ni na tadata narasa wane lalaci ke damun Baby kwanan, mutum kullum ba abinda ya iya sai kwanciya kamar mai?" Tafada tana nufar hanyar fita

Ajiyar zuciya saudart ta sauke da qarfi bayan fitarta sannan ta juya tana kashe gas din tana hamdala a zuciyarta


Jin takun ummy na tunkaro falon yasashi saurin gyara zama ya maida hankalinshi kan wayar hannunshi yana dannawa.

Sosai ummy tayi mammakin ganinshi amma sai ta basar tanufo cikin falon tana tsuke fuska

Dagowa ashraf yayi daga wayarshi ya kalli saitin ummy dake tahowa ya Dan sakarmata murmushi yana maida wayar a aljihu.

Zama ummy tayi tana kallonshi tana qara nazarinshi ganin yadda fuskarshi ke fayau bawani alamun damuwa unlike jiya ranan dayabar gidan rai 6ace.

Zamewa yayi qasa ya gaidata cikin girmamawa kamar yadda yasaba.

Amsawa tayi ba yabo ba fallasa tana dauke kai don tayi tunanin maganar ranan zai sake dauko Mata


Ganin yakoma ya zauna batareda yace komaiba saima maida hankalinshi dayayi a t.v yasata cewa
"Yaushe kashigo?"

"Ban dadeba" ya amsa a gajarce

"Wannan fa? Na wanene?" Tafada tana nuna trolley din dake tsakar falon

"Oh.. Nawane, yanzu zan wuce dashi ciki" yafada batareda yanuna yaga kallon datake Mashi ba.

"Naka? Tafiya zakayi?"

Dan murmushi yasaki ya girgiza kai yace
"A'a kayana anjima zan kaisu apartment dina"

Sai yanzu tagane inda ya dosa.

Lallai kenen shima yadawo nan da zama yake nufi ko me?

Aikau in yasan wata besan wata ba.

Bata qara cemashi komaiba itama ta maida kallonta kan t.v don Tama fasa zuwa tado baby din tinda saudart na kitchen


Haka suka cigaba da zaman kurame har saida sukaji motsin saudart ta fito daga kitchen din hannunta dauke da warmers.

Caraff suka hada ido tayi saurin dauke kai tanufi dining tana doddorawa akai

Binta da kallo yake harta gama doddorawa takoma kitchen din

Janye idanunshi yayi daga binta da kallon dayayi ya maida kan ummy, cikin taushin murya yace
"Ummy ina maid dinmu ne?"

Batareda ta kalleshi ba tace
"Ta tafi kasuwa"

"Baby fa?"

"Tana sama" ta amsa a taqaice

"Doing what ummy?"

Dagowa tayi ta gallamashi harara tace
"Bansàniba"

Dauke kai yayi yana dan turo baki sannan qasa qasa yadda yasan zataji yace
"Kowa nata hutawa sai matata akabari da aiki"

Dan dagowa tayi ta kalleshi saikuma ta janye idanunta ta cigaba da kallonta


Haka saudart taita fitowa tana jera dishes din dukda duk acikin qarfin hali takeyi saboda yadda take junta very uncomfortable saboda kallon dayake binta dashi

Saida tagama komai sannan ta qaraso falon adarare

Dagowa ummy tayi ta kalleta cikin fara'a tace
"Yauwa Yar albarka, kin gama ko?"

Murmushi tadan Saki tana sinne kai

"Sannu to, kije kiyi haramar zuhr naji anata Kira"

Kada kai tayi kawai, kamar zata wuce saikuma tadan juyo saitin ashraf daya maidata mirror tundazu.

Janye idanu tayi sanaddiyar hada idon da sukayi, cikin calm voice dinta tace "ina yini" tana dan russunawa

Wani farinciki ya ziyarci zuciyarshi nan take hakan yasakashi sakarmata murmushi yana cewa
"Lfy.. Sannu da aiki"

Bata amsa ba sai wucewa datayi tana jinta so uncomfortable saboda shigar dake jikinta dukda yanzu ta yafa gyalle Wanda dama aiki yasata cireshi a kitchen.

Saida ta haye sama sannan ummy ma ta tashi itama ta haura saman batareda tace mashi komaiba

Murmushi yayi sannan shima ya tashi ya nufi trolley dinshi yaja yafice yanufi apartment dinshi yana tafe yana cilla keys dinshi sama yana cafewa zuciyarshi fess.

Da sallama yashiga dakin jaye da trolley dinshi

Dakin bawani datti don ana gyarashi koda bayanan bare dama yan kwanaki yayi rabonshi da dakin.

Ajiye trolley din yayi kawai yanufi bathroom ya dauro alwalla a gurguje yafito don har Ana shirin kabbara sallar

Koda aka gama sallar yadan jima be dawoba.

Lokacin daya dawo duk suna dinning da alamu abinci sukeci.

Qarasowa yayi cikin takunshi na qasaita idanunshi kafe da saudart da kanta ke qasa tana jujjuya spoon dinta a abinci

Zuwa yanzu ta chanza shigarta zuwa deep blue Arabian gown buba wadda hannun yadan tsuke a daidai gwiyagun hannayenta, sai adon fararen tutar flowers da aka jera round din wuyan rigan, sai veil din rigar data yafa simply akanta.

Tayi kyau sosai dukda bawani kwalliya tayiba amma glowing din fatarta kadai abin kallone da sha'awa.

Saida ya qaraso sannan ya janye idanunshi akanta yana jan kujerar dake facing din saudart baya sannan ya zauna.

Dagowa yayi suka hada ido da baby dake shirin kai spoon abaki, wata uwar harara ya gallamata yana kada kai

Sadda kai tayi tana kumburo fuska

"Anan kikafi afki ai, a girka kici" yafada yana ziran plate at the same time yana cigaba da hararanta.

Qara turo baki tayi tadan saci kallon ummy taga abincinta kawai takeci hakama saudart dako dagowa bataiba

Hakan yasa itama maida kanta ga abincin tanaci a sanyaye don saitaji duk ya ficemata akai duk dadinshi.

Itadai saudart tin shigowarshi bata yarda taqara dagowa ba don tanajin yadda idanunshi ke yawo akanta abin har mammaki yake bata, kodai ya manta ummy na a dinning din ne.

Bata ida tsinkewa da al'almarinshi saida yaji yace
"dear serve me mana, yunwa"

Shiru dining din ya dauka don they're all confused sun rasa dawa yake

Gaban saudart yafadi jin yasake cewa
"Kinji wifey? Am hungry" ya qarashe maganar a shagwa6e kamar yadda yakema ummy

Daburcewa saudart tayi yayinda wata matsananciyar kunya ta lullu6eta.

Dagowa tayi ta saci kallon ummy taga kamar ma batasan dasuba don abincinta kawai takeci.

Hakan yasata maida kallon akanshi, kashe mata ido daya yayi sannan yace "kinji?"

Rasa inda zata sa kanta don kunya tayi, tashi tayi kamar wanda aka zarewa lakka tana Satan kallon baby Wanda ta sadda kai tana qumshe dariya da wutsiyar ido sannan ta bude warmern fried rice din kamar zatayi kuka

Turo mata plate din daya zara yayi yana qoqarin danne dariyarshi ganin yadda tayi da fuska da yadda take zuba abincin a daburce

"Yauwa ya Isa hakan" yafada yana janyo plate din sannan ya turamata glass cup daya yana cewa
"Saura drink"

Bata kalleshi ba ta dauki glass din ta bulbula smoothie din dayayi gwanin kyau aciki sannan ta zari wani glass din ta zubamaahi ruwan gora masu sanyi.

Duk tanayin wadannan ne a nonnoqe don wani irin kunyar ummy takeji wanda bata ta6a jiba.

Komawa tayi ta zauna tanajin kamar ta nitse don kunya

Shikau ko ajikinshi saima spoon daya saka a plate din ya debi spoon guda yakai baki.

Lumshe idanu yayi sakamakon karon da abincin yakaimashi harcikin qwalwa, abincin is so delicious kamar yadda look dinshi is so salivating.

"Hummm" yafada yana chewing din abincin ahankali ido a lumshe irin yakaimashi Karo dinnan.

Kasa qumshe dariyarta baby tayi wannan karon saida tafito tayi saurin dafe baki tanayi

Atare suka wurga mata harara ta gefen ido, fuskar saudart kamar mai shirin kuka, jitake kamar taita ihu don takaici

Itakau ummy ko alamun tasan abinda ke faruwa bata nunaba saidai can qasan ranta mammakin rashin kunyarshi take.

Cigaba da cin abincin shi yake hankali kwance yana wani lumlumshe idanu yana humming alamun yana enjoying

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login