Showing 42001 words to 45000 words out of 47989 words

Chapter 15 - NI DA GIDANA Complete Hausa Novel

15 Jul 2025

3104

Khairat, tana k'aunata sosai, tun da ta iya fad'amin sirrin mahaifiyarta.

Na tara bokiti bakin fanfo zan debi ruwa
zan Shiga band'aki nayi wanka, saboda wani zafi da ake surfawa, Muhibbat ta taho da sauri da nufin angijeni tayi saurin shigewa saboda neman fitina, bayan ta baro wani band'akin a bayanta. Batasan a yarda nake ji da tsiya ba, kowa ya tunkaroni a lokacin karawa za' muyi. Shi yasa banyi jinkirin angijeta ba,iya k'arfina, Sai gata a k'asa wanwar .

Ta kuwa Mik'e da masifa za'ta soma aunamin zagi, yarda ta saba. Nace cikin d'aga murya.

"Ahir. yarinya. Karki d'auki kawaicina a matsayin gazawa. Kuma karki d'auki hak'uri na a matsayin tsoro. Idan har ke kin cika d'iya ta halas, to ki kai ga jikina, domin fad'a na baki na matsorata ne."

Sautin murya ta da yayi Sama, a she Momi taji yo, Sai ta fito, haka Khairat, suka zubo Mana idanu daga saman bene.

Muhibbat tayi min wani matsiyacin kallo, cike da mamakin yarda na rikide tashi guda, don duk iskancin da take min sunkuyar da kai nake yi na wuce.

Tace cikin tafa hannu.

"Samun wuri, Wai d'an wake a hotel. ke bora, kuma 'yar tsaron k'ofa, har kina da bakin magana? har da fiffik'a?
to ba za ta kaimu da nisa ba, zakisan matsayin ki idan kin manta. Bari yaya ya dawo."

Na sake hada idanu da Momi sai kuwa na sake daga murya a fusace.

"Yazo din, me ya isa yayi min, datse min numfashi, ko duka na zai yi, don bazan daku ba wallahi, iko daya ne dai cal zai iyayi kololuwa, shine ya sakeni, kuma na shirya tsab, tun da ba autan maza ba ne. Gari da yawa ai maye baya cin kansa".


_wasa farin girki, har yanzu ba a shiga farfajiya na rigin gimu da manufofi da soyayya da dadin wannan littafi ba, duk maison ya kashe kwarkwatar idanun sa, to ya turo_500 kacal 👌🏻

Ta wannan a count no👇

8025527956, Opay.
Zainab ilyas

_Shaidar biya ta wannan number ta whattap_.
O9096409711





_Zainab ilyas mazwaje_



Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe


*NI DA GIDANA*



_Zainab ilyas mazawaje_


_Best brilliant interlligent writer_.... 🖋️





*Page 18*





Furutaina na fahimci sun tunzura Momi, saboda gabanta nake tijarar, kuma tasan na ganta. Kuma tasan idan 'yarta tayi sake muka dambata, Sai na lallasata sosai, saboda na fita siffar k'arfi ma a ido. Ita 'yar kyalan kyalan take. Bata da cikowar komai a jiki na cikar surar mace. Kyan iya fuska yake, Sai farar fatar abin alfahari, irin na 'yan uwanta, idan aka cire Khalifa.

Momi tace cikin daga murya da fusata.

"Karki kulata Muhibbat. Ai Kare baya yi Maka haushi ka rama, Sai Ku zama d'aya. Ko a usuli da nasaba kun bambamta, ba kya daka ta tata ba. Kinsan kuma harbi ga d'an kunama gado ne."

Na d'aga kai na kalli Momi a zuciye, na kau da kai, Kenan ta ramawa 'yar ta. Darajar haihuwa taci, da tazarar shekarun da ta bani, gashi na samu tarbiyyar girmama manya, da ta gane ita ma shayi ruwa ne. Domin sun kaini k'urewar bango.

"Momi, ni Mamaki take bani fa! wai bora kuma 'yar jiran k'ofa keda a bin cewa. A cewar Muhibbat.

Na Doka mata kallon k'ask'anci.

" Ke shashasha, ragowar yunwa, A littafin maganganun dake bakina wallahi , shafin farko ma ban bud'e ba. Zan kuma karance miki shi, in dai kika ci gaba da ja dani. Matsoraciyar Kawai, Wacce a fad'an baki tafi kauri".

" Ina kai nan, Sai muka had'a idanu da Khairat. Murmushi tayi, dake nunin taji dad'in 'yancina da na karb'a.Dole idan ba'a kiyaye ni ba, za'a sassauta kuwa.

Nan na wuce band'aki na bar Momi da Muhibbat suna ta yada maganganu. Na fahimci na had'a musu zafi, bayan mamakin da na basu. Basu tab'a zaton zan iya haka ba.

A na Kiran sallar Isha'I na jiyo sallamar Ancle Fa'iz ya shigo. Nasan Kiran'sa a Kayi a waya, domin baya dawowa dai dai wannan lokaci.

Nan ma saman Momi ya wuce kai tsaye.

Ina zaune rik'e da kofin flastic, Ina shan corn flake's, domin shine ire iren kalar a bincin da na komawa, mai ruwa ruwa. Sati biyu kenan da k'untatawa kai na da nayi na k'in yin girki. Saboda b'acin ran da nake ciki, bayan rashin a bincin kirki, duk na soma rama, k'asusuwan kwarin wuya na sun soma yi min mirjani. Ga bak'i da na soma yi.

Ancle ya shigo min da sallama a sanyaye jikin sa naga. Saye yake da rigar kakin jin's riga mai gajeran hannu da wandonta na jin's. Gaban rigar manyan mab'allaye ne, ya b'alle biyu na saman a na hango k'irjin sa kad'an.Kayan jajaye ne masu duhu, shi yasa sun k'ara haskaka kyawunsa da hasken fatarsa. Kyawun da suka yi masa bazai misaltuba. Tamkar d'an bak'on balarabe a k'asar Hausa. Bantab'a ganin yasa kayan ba. Ta yiyu, sababbine ko a jiyayyu.

Ranar ko sannu da zuwa na kasa yi masa,saboda nauyin damuwa da ya rik'emin Mak'oshi. Tun da muka samu Sab'ani da shi, dama gaisuwa Kawai ke had'ani da shi, ko sannu da zuwa, idan ya dawo ya shigo ya a jiyemin nawa a binda ya sayo na mak'ulashe. Ancle Mutum ne mai sakin hannu sosai na sayo wannan sayo wancan na wasa baki, in dai yana da shi. In yayi kud'i za'aci dad'i kam ba kad'an ba.

Ya zauna kusa dani kan kujera. Na basar na ci gaba da shan corn flakes d'ina kamar ban San da tsirar sa ba. K'iris Kawai nake jira, a yi b'atacciya.

Yace "Sumayya!. Na amsa da k'yar.

"Wai maye yake damunki ne? gaba d'a ya kin canza, kan d'an a binda bai kai ya kawo ba. Ban San ki Sam da halayyar fishi ba, ko rigima, ballantana fad'a. Ina kika a ro wad'an nan d'abi'u? "

Duk a sanyaye naji yana furutan ma.

Na fusata nace.

"Ba'arowa nayi ba ma, Karb'owa nayi kyauta, domin na ceci kaina Ancle."

Yayi d'an jinkirin magaba, domin jinjina furutaina.

"O k, naji. Yanzu fad'amin a binda ya faru a yau".

"Au, ba'a fad'a Maka ba?"

Yace. "Ko an fad'amin a dalcine naji kuma daga b'angarenki ko?".

Nayi yak'e na takaici.

"Duk a binda akace Maka nayi gaskiya ne Ancle. Bani da kirki. Duk d'abiar da kasani ta banza, toni gwanace. Matsalolin duk da suke faruwa a gidan nan, nice sila, tuntuni fad'a Maka ne ba'ayi. Saboda haka babu wani bincike da zaka kumayi, na kuna kuma yanzu babu wani kauri ko hayaki da zai tsoratani, kazartar min da hukunci Kawai, shine magana".

Kuka ne ya nunamin fin k'arfi, na aibata kaina da nayi, domin na yarda k'wallon mangwaro na huta da k'uda kawai.

Nayi k'ok'arin Mik'ewa na shige d'aki, Sai Ancle ya rik'e hannu na, domin dakatar dani. Iya k'arfina da bansan ina da shi ba, nasa kuwa na fizge, saboda a tunzure nake sosai nace.

"Ni ka rabu dani, Ancle ka zartar min kawai da hukunci, shi ya rage kawai".

Na fad'a d'akin ina sheshshekar kuka. Baki bud'e na bar Ancle Fa'iz, domin furutaina sun girgiza shi ainun.

Ina Shiga d'aki Sai gashi ya biyo ni. Na hau kan gado, Shima ya hawo. Ina ja da baya, yana biyoni.

"Wai ka rabu da ni Mana. Bana fad'a Maka gaskiya ba? Ka k'yale ni Ancle"

Cikin kuka nake fadi.

Nama rasa a binda ya hanashi yin zuciya a lokacin ya rabu dani, domin mai zuciyar ne.

Sai da na kai k'arshen gado, na hak'ure, saboda ya kureni yarda bazan iya zullewa ba kuma.

Ga Mamaki na, sai yayi dan murmushi ya d'ago fuskata, da hannayen'sa ya shiga sharemin hawayen fuskata da wani tisue da ya fito dashi daga aljihunsa.

A hankali kamar mai rada ya soma cemin.

"Ban yarda ke mutuniyar banza bace, mai kuma mummunan halaye, banyarda ba Wallahi, duk da kinyi ik'irari da bakinki. Duk in da kika je kika b'ata kanki, zanje na k'arya taki nace karya kike yi. Zan baki Kariya sosai, na kuma wankeki, nace Sumayya yarinyace me ladabi, mai kirki, mai hak'uri, mai addini, tayi zarra wurin yakanah da kamun kai.".

Furutan sa sun zo min a ba zata. Ban tab'a sanin shi d'in ya tsaya nazarin sanin halayena ba, har ya karance su tsab, a tsawon watanni Kusan biyar da auren mu.

Jikina yayi sanyi, kuma yayi laushi lub'us. Har lokacin hannun sa yana rik'e da hab'ata fuskata na fuskantar tasa dab yace.

"Bansan me ya hargitsaki ba, ya kuma tunzuraki, har kike k'agar halayyar banza kike danganta su, da kanki. Me zai sa kiyi haka? haba my Sumy."

Baki d'aya lakar jikina ta mace. Sunan da ya k'irk'iran min lokaci d'aya, yayi matuk'ar karb'uwar jin dad'in sa da tasiri a Zuciyata, wurin hab'aka k'aunar Ancle a zuciya ta, da da nake k'oK'arin ya kicewa da k'arfi, saboda wuya, da fitintinu, wani irin yanayi na samu kaina a ciki da bazai misaltu ba, game da irin yanayin da muke ciki a lokacin da Ancle, domin numfashinsa ma inajin saukarsa kamar ni nakeyi, bai kuma saki hannuna ba, da habata da ka kaita dab da fuskarsa ba yana magana.

Cikin sauk'i Ancle Fa'iz yajanyo ra'ayina na fad'a masa a binda ya faru, Amma banda na can baya. Ko sunan Momi ban kamaba,domin matsayinta gareshi, bazan iya cewa tayi min wani a bu ba.

Fushi sosai na gani kan fuskarsa, yace. "Banyi Mamaki ba, Muhibbat zata iya fiye da haka. Dadai Khairat ce, shine zanyi ko kwanto, domin shigen halayyarku d'aya.
Muhibbat kowa hak'uri yake yi da ita a gidan nan Sumayya. Ko iyayen mu, ni nake yi musu maganinta idan ta buwayesu, domin ni kad'ai take shakka. Nasan kuma ba iya a binda ta tab'a yi miki kenan ba, kin b'oye wasu. Kiyi hakuri domin, ni. Ki jure domin ni.ki kau da kai domin ni.Nasan kina Sona, domin a binda kike min, Wallahi soyayyace Kawai zata yi jagoranci ga haka.Don Allah komai ya wuce, kinji Sumy?".

Bansan Sanda murmushi ya sub'uce kan leb'ena ba.

"Wallahi komai ya wuce. Kuma zan k'ara d'amarar juriyar a binda zai sake biyo baya, my Ancle. Naji dad'i daka fahimceni, batare da tallafina ba.
Da sauri yace.

"Yauwa my daughter. Bazance da Momi ko Muhibbat komai ba, domin cewa za'ayi nabi bayanki. Sai kiga rigingimu sun kuma b'allewa. A Kwai wasu a bubuwa da nasani da kike zaton ni d'in bansa ni ba. Har jarrabaki nayi a wani a bu, amma Sai da kika lashe jarrabawata. Nayi miki jinjina Gaskiya."

Ya k'arashe cikin wani tattausan murmushi, ya Mik'e a hankali, jikin sa Sam babu kuzari ya Fice.

To ni d'in ma ya burgeni ainun, na yarda ya janyo hankalina, yasa nayi sanyi na hak'ure komai, sa'i d'aya. Ban tab'a zaton yana da taushi da sanyi na d'abiar iya tarairayar mace ba cikin salo na sace zuciya. Ni Kam ai sai na k'ara matowa a Soyayya.

Faruwar rikicin nan, da aka so Ancle ya d'au mummunan hukunci a kaina, kamar k'ara ingiza alak'ata da Ancle Fa'iz tayi da k'arin shak'uwa.

A binci tuni Ancle ya maido cin,sa falona. Ko Momi tayi masa girki, Sai ya d'auko ya shigo wurina. Dama ga nawa da ya zame masa k'ara'i, Sai yaci ko bayawa.

Yanzu kuma yakan d'an yaba, sab'anin da da Sai ya kushe, ko yace na kuskure wani a bu, ko kuma yayi shiru bazai yaba ba, ko da yayi dad'in. To yanzu, nima na k'ara zage damtse ne sosai wurin kyautata girkin da jikina da kud'ina. Na sayi littattafai na koyon girki da Shiga group group kuma na internet na koyon girki, har da na practical. Duk domin na k'wato 'yancina a matsiyina na matar Fa'iz ya damu da girkina, ya rink'aci fiye da na kowa.

Jiddin tare muke cin a binci da Ancle Fa'iz. Hira ma ya rage yawan yimin k'orafi, ko nuna damuwa irin da yace na dameshi. Amma dai duk da haka bai fiyason hira ba, Sai Sama Sama.

Ana jimawa sosai kafin ayi hira da shi mai tsayi. Sannan zafin zuciyar'sa yana nan daram, Sai dai idan ba'a b'ata masa ba. Shi yasa nasan irin takun Zaman da nake yi da shi.

Momi da Khalifa da Muhibbat ganin mun sake d'inkewa da Ancle fiye da da, ai Sai a ka sake yiyowa kaina da fitintinu iri iri, amma ba'a takani kamar da. Musamman Muhibbat da take zuwa gabana ta d'uramin ta maguzawa (zagi). Yanzu Sai baya baya, idan zata yi min tsiwa, saboda na nuna mata nima A' ce , tsab zan casa ta idan ta Shiga hannu na. Wannan yasa a kayi musaya, Khalifa ya karb'i ragamar, domin yasan bazan iya da shi ba. Sai yafi uzzuramin a tsukun. Zagi ta uwa ta uba. Lub! nayi , duk da nasan iya zagi zata tsaya, bai isa yace zai kai hannu jikina ba. Na mai da shi, tamkar Kare mai haushi, da Sai an kula zai samu tasiri. Saboda darajar Kawai Ancle da yace na jure domin shi."

Cikin hutu muke a tsukin. Saboda haka, Ina zaune na rasa a binyi, ga babu wuta, babu a bokin hira, na fito tsakar gida fitina ta afku. Na rabka ta gumi. Ancle Fa'iz ya shigo da sauri, ya tsaya kaina yace.

"Sumy zo Muje kiga motar da na Saya a k'ofar gida, Sati shida Kenan da na bada cigiyar a samomin irinta, Sai yanzu a kayi katarin samota."

Cike da farin ciki nayi a zamar Mik'ewa."Wow! Ina murna my Ancle. Muje na ganta. Nasa mayafi nabi bayan Ancle Fa'iz. Motar Kam tayi kyau sosai. Pomatic, sunan ta, kuma Automatic ce. Dark green. zata dace da mai ita Kam.

"Gobe tun da babu makaranta, Sai Muje na d'anaki Mu zaga gari ko?".

Cike da zumud'i na gyad'a kai. "Sosai ma, a she nice farkon d'ani "

Washe gari kuwa, a gaban Momi da Muhibbat muka Fice ni da Ancle. Mugun kallo Momi ta jefa min da nayi mata sallamar zamu fita da Ancle. Bata tsinka ba kuma. Amma nasan Ancle ya fad'a mata komai.

Tafiya muke cikin 'yar kyakykyawar motar zuciyoyin Mu duka cike da nishad'i. Hatta Ancle na ganshi cikin walwala sosai, duk da ba Wata hira muke sosai ba, Sai Jifa Jifa, Sai Jan motar da yake, sannu sannu, ya Saki slow music na R. Kelly, cikin wak'ar sa ta I blieve I can fly. I blieve I can touch the sky. Ancle yayi 'yar dariyar nan tasa ta burgewa da Sai tayi hali za'aga yayi.

Yace. "Sumayya kinji wani Mak'aryacin mawak'i a binda yake cewa kuwa?" Na saurara, naji nace "Ai da kansa yake Ancle. Tunda cewa yayi ya yarda zai iya tashi sama, kuma ya yarda zai iya tab'o saman gajimare, kaga mu 'yan jine da kunne, ba yarda muka yi ba."

Ancle ya gyad'a kai.

"That is true." Yace a Tak'aice.

Na maida kaina wurin taga ina ta faman kallace kallace ta tagar mota, har na k'yallaro wata mata tana tuk'a mota, gwanin Sha'awa.

Na waiwayo gefena nace wa Ancle Fa'iz.

"Ancle wai kuwa tuk'in mota da wuya?".

Yace "Babu wani wuya, nima nan da nan na koya. Kinga wannan Automatic tafi sauk'i sosai fiye da manual, domin Kinga Auto, ita take caccanza giya da kanta, kuma totur Kawai zaki taka, ki tafi, babu ruwanki da taka kuloci da caccanza giya."

Nace"To ai ni bazan fahimta ba Ancle Fa'iz tun da ba koyon nayi ba"

"Kina Sha'awar koyon tuk'in mota?" Yace bayan ya rage sautin music d'in da yake tashi da hannu guda, guda kuma yana kan sitiyari yana d'an jujjuyashi.

Nace "Wallahi Ina Sha'awar driving."

Yace "To kuwa kin samu. Bari Muje filin koyon tuk'i na soma nunamiki daga yau." . Nasha mamaki da nan da nan
Ya juya kan mota, ya canza hanya Sannan ya k'ara speed, Sai gamu a babban wani fili babba, har da wata mata ma da mijinta, Itama tana koyo.

Ancle ya nunamin komai a hankali, da yarda zan yi komai. Kamar wasa ya bani kan motar, ko tsoro bai jiba, yace na jarraba, amma yana kusa dani a gefena. Kafin na soma yace" Sai kin sa nutsuwa sosai fa, kuma ki cire tsoro, idan ba haka ba, zaki jima baki iya ba."

Tiryan Tiryan da na bi shawarar Ancle na kuma bi yarda ya nunamin komai, Sai gashi ina tuk'in motar sannu a hankali, saboda nima nutsatstsiyar ce ga saurin daukar karatu.

Sai da ya sani nayi round biyar na tafkeken filin wurin.

K'arshe yace.

"Sumayya, Stop the car."

Da na tsaya cak, yace.Na tsaida mota a hankali.

"Kin burgeni gaskiya. Nasan duk in da muka sake yin fita uku ko biyar zaki iya mota. Abinda ya rage Kawai zai rage miki, hawa titi da lunguna, kinsan Shima training d'insa, dabam yake da na filin wuri irin wannan.

Yanzu ki mai damu gida."

Na zaro idanu "Daga koyon farko? baka tsoron na tintsirar da kai a hanya. d'an Murmushi kawai yayi, bai tanka ba, ya karb'i kan motar.

Tun daga ranar kullum Sai mun fita a mota nida Ancle Fa'iz saboda koyamin mota. Mu kanyi yawace yawace kuma sosai a mota, bayan mun gama da komai. Bantab'a Samun farin ciki ba, zuciya ta ta rink'a haske tun da na auri Ancle, ba kamar na lokacin. Domin mun sake da juna da hira da annashuwa fiye da ko Yaushe. Amma dai har lokacin bansan matsayi na ba wurin Ancle Fa'iz. Ko da wasa banga alamun wai sona a tare da shi ba, duk da kulawar da yake bani fiye da baya, da kuma hira ta nishad'in da mukan yi.

A k'arshe dai nike Jan mota na fita damu na dawo da mu. Har takai ma yakan bani mukullin motar na fita, ni kad'ai a cewar sa, da haka zan k'warance. K'iyayya sosai kuma mai zafi, na ganta a wannan k'arni, tasu Momi da 'ya'yanta, amma nayi biris.

Da muka koma makaranta, Ancle ni ya bawa mukullin motar nake zuwa makaranta da ita. Shi ba kullum yake hawa, bai fi a Sati sau biyu ko d'aya ba. Domin idan ba wuri mai nisa bane, ya gwarace ya hau babur. Shi yasa motar kamar tawa. Idan Zai hau Sai dai ya karb'i mukullin a hannu na.

Nan ma, Ina wuta a jefani. K"iyayya ta ninka ta baya. To na lura Momi, kamar batason b'acin ran Ancle Fa'izu ma.Domin ran nan na gaji da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login