Showing 18001 words to 21000 words out of 47989 words

Chapter 7 - NI DA GIDANA Complete Hausa Novel

15 Jul 2025

3101

ba har zuci yanzu, saboda kallon wasu halaye na zahiri da kike yi masa. Amma a Kwai na bad'ini da bakisan da su ba. Shi yasa kike gani baza ki iya da shi ba. Tabbas zaki iya zama da Yarima, matuk'ar kika fahimceshi, kuma kika kiyaye a binda ya keso da wan"da baya so.

Nasan ko baki gwanance ba, zaki iya koyawa zuciyarki, ki jure kiyi, Saboda kina da hak'uri da biyayya.

Kuma ki sani, idan ma kink'i auren'sa ba damuwa zai yi ba, ba kuma hak'ura zai yi ba da auren cimma wata manufa ba. Wata zai samu ya aura. To ita Watan kina zaton irinki ce mai kyawun zuciya da zata ceto shi daga yin kuskuren da yake son aikatawa, nayin auren wucin gadi? Ke kuwa nasan ko baki taimakeshi da komai ba, zaki taimakeshi, da nasiha da addu'a. Sanin kan'kine yin aure da niyyar Saki daga baya saboda wata manufa, haramun ne. Kika yi kandagarkin hana afkuwar hakan bakiyi babban aikin Lada ba Sumayya? .

Naji jikina yayi sanyi Lis, da furutan Kawu.

Tabbas Gaskiya ya fad'i , a binda nake shakkar
yiyuwar, na yarda Ancle Fa'izu zai karb'i nasiha daga gareni, ko shawara. A yarda yake ji da kan'sa, ni kuma yake ganina a raine.

Kawu yace.

"Kuma ki rink'a nuna kulawarki wurin mahaifiyar'sa, domin yana tsananin son'ta. Zan iya ce miki nan ne sirrin farin cikin'sa. Ki soma d'ana tarkon'ki tanan. Ki kula.

_Nan farin cikin sa yake_


ni na sake jaddada wannan a raina, har sau uku ma.

Da wad'an nan kalamai Kawu Sulaiman ya sake farauto Zuciyata ta a minta da auren Ancle Fa'izu. Amma fa ban daina farga ba ba, da zullumin auren. Tabbas ba domin na yarda da irin K'aunar da kawuna kemin ba, cewa zanyi farin cikin rayuwata ne baya so, shi yasa yace na auri Ancle Fa'izu.

Amma duk da haka ni fatana ke dai kar ya dawo, fushin da tafi da shi na nayi masa kaiyanci ya hanashi dawowa. Amma idan kaddara ta sa ya dawo bazan bujire ba, ba dai haka na so ba.
Babbar fargaba ta kar na kamu da son sa ma, nafi shan wahalarsa, saboda siradi ne mai wuyar gaske mace mai sunan mace ta dora idanu a kansa ta dauke ba tare da ya zabaro zuciyarta ta kamu da soyayyarsa ba. Shi yasa ban fiye son na hada idanu da shi ba, domin a kwai sakonnin da kallon ke aikewa zuciya ta da ni kadai na sani, in da shi kuma yake jin haushin hakan, ya kuma daukeshi a matsayin kauyanci na ko kallonsa ba na iyawa.

Allah gani gareka, baiwarka marainiya, ka kawo mata dauki.

Na fadi a hakan a zuciya ta ni kadai ina zaune cikin tagumi.









_Taku har kullum_





_Zainab mazawaje_



Alkalami yafi takobi... 🖋️


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe



*NI DA GIDANA*



*NA*




_Zainab mazawaje_



_Best brilliant interlligent writer...... 🖋️






*Page* *9*





Nayi sauri na fito daga d'aki, na karb'e tsintsiyar da Baba talatu, ta soma Shara da ita. Bata Musa ba, ta sakar min. Sai da na share ko Ina na cikin gidan tas!. Na had'o Kayan wanke wanke zan'yi Sannan tace.

"Ke dai Sumayya bakison kiga nayi komai, in dai kina gidan nan."

Nace.

"To, Baba Talatu, kina da kamata kiyi aiki? aiko tsari babu. Kiyi kwanciyarki, nayi aiki nayi kuma girki, Sai dai Kawai na kawo miki kici. In dai ina gidan nan baza kiyi aiki ba."

Tace

"Koda a Kwai d'iya irin'ki mai kyawun hali, gaskiya k'alline. Kina da kyawun d'abi,a Sumayya, ga biyayya, ga tausayi. Ta Yaya kuwa bakina zai gajiya da sa miki albarka? da Fata na gari. In Sha'Allah Sai kin haifi masu binki, kuma Sai kin gwangwaje Miji na alfahari. Saboda kowa ya bud'i baki a kan'ki fata na gari ne. Addu'ar iyaye da 'yan uwa kullum bibiyarki za tayi tayi."

Tuni na saba da lafazan Baba Talatu da d'ad'a, kullum ne bata gajiya.

Tsawon kwana tara, ban sake ganin ko inuwar Ancle Fa'izu ba, ga wawtata farin ciki na Shiga sosai, a zatona ai ba zai iya dani d'in ba ne, kamar yarda yace, shi yasa ya janye.

A tsukin aka sake gayyatar k'ungiyar su Kawu sulaiman Kaduna united zuwa ga buga boll, cikin k'asar Enugu, za'su kara da club din
Ranger's.

Nan ma su Kawu na ne suka cinye. Ya bugo min waya, cike da farin ciki yana mai shaidamin, dama sau biyu muna waya da shi, bayan tafiyar'su. Nasan da Ancle Fa'izu suka tafi, amma ko zancen'sa bai yi ba, nima banyi ba.
Na fiddaran hakan, Sai ji nayi Ancle d'ina yace.o

"Ga Ancle Fa'izu zan kai masa ku gaisa, kuma kiyi masa murna, domin shi yaci mana k'wallon nasarar guda biyu. Yana dakin hutu amma na barshi yana shan mutuniyar tasa multina, bari na kai masa.

Da sauri nace.

"Don Allah Kawu ka rabu da shi, basai munyi magana ba, kace Ina yi masa murna Kawai".

Yace.

"Zai fi kyau ki kira wayar'sa ki fad'i masa. Idan baki da ita zan turo miki. Nayi d'an Jim, daga bisani nace.

"Ina jin nauyin hakan, Ancle. Naga shi ya kamata a ce yama nemi sanin lambata, ya kirani, amma bai yi ba. Shi yasa nake ganin kamar zan karyar da kaina idan na fara. Amma idan kace na kirashi, zan kirashin".

Yace.

"A'a. Rabu da shi kawai, na fad'a masa. Kinsan dai komai a kan'sa. Kinga kuwa komai ba zai shige miki duhun menene dalili ba. Kinsan dole zaki rink'a had'uwa da irin haka, amma kiyi hak'uri wataran Sai labari kinji shalelen. Ni da shi mukayi 'yar dariya.

"Gaskiya Ina son Kawu Sulaiman, har bansan adadi ba, ko misali.

Kwanan'su d'aya tal da dawowa kawuna yace min.

"Sumayya, yau Yarima zai zo. Don Allah, ki kula a komai, kar ki bani kunya kuma. Ki canza".

Nace.

"To, Kawu zan yi bakin iyawa ta"

yaji dadi.

Na samu kaina da tsala kwalliya da ado fiye da farkon zuwan'sa sosai. Less nasa kalar marun mai adon duwatsu da filawoyi ,mai kyau, da nasan sunai mini kyau, saboda kawaye na ma ko dani suke idan nayi ado dashi. Mayafi da takalmi to mach, daurin nan ya kafu a kaina kamar nike koyar da dauri ga 'yammata, bansa sarka ba tun da ba gani zai yi ba, sai fasion da bangles. Sai turare mai sanyin kamshi da humra da nasa. Nasan dai duk a banza wai talaka ya girmi sarki a wurinsa, nayi ne kawai domin jin hakan ya dace, kamar yarda na cewa kawuna zan yi a binda ya dace da duk zan iya.

Har bakin k'ofar waje da yake tsaye na isa na tarboshi, saboda Kawu Sulaiman Baba ya aikeshi ya tafi, kafin fitowata wurin Yarima.

Saboda haka kujeru na roba na Kawu na fito dasu harabar cikin wajen gidan kusa da dakin Kawu dake kusa da k'ofar fita waje, da yake a katange yake ba'a hangen na ciki.

Kamar had'in baki, Yarima Shima Man less yasa na maza, kalar pink mai cizawa. Sun yi masa wani irin kyau Kam.

Duk da naje har bakin k'ofa na tarboshi cikin sakin fuska sosai, da sakin jiki da girmamawa, Sam banga ya sakarmin fuska ba. Ya dai dubeni, a dak'ile ya kau da kai.

Abin a hali ne. Nace a hankali cikin dan tabe baki, duk da nasan ba sona yake ba, amma na dan ji ciwon kallon saurin da yayi min yayi saurin dauke kai kamar yaga abin kazanta.

Tare muka jeru zuwa mazaunin Zaman, hannun'sa cikin aljihu, yana tafiyar nan tasa ta isa da jin kai. Naga Sai wani shan k'amshi ma yake, kamar wanda aka tilasta Sai yazo wurina.

Kujerun da zamu zauna, suna fuskantar juna, kuma ni na a jiyesu ina sane a hakan. Zuciyata ce naji ta soma k'ek'ashewa, daga fargabar da nake ciki ma na auran Ancle Fa'izu, saboda na hanga gabas da kudu da arewa, ban hango matsera ba, na tserewa auran. Shi yasa Kawai na mik'a wuya, tare da nemo hanyoyin da zanbi, na k'ubuta daga tozarcin'sa da ya zama lazim.

Nasan idan na ci gaba da nuna d'ari d'ari da shi, da Jan jiki, da alkunyar nan, to kullum gumamin takaici zai ci gaba da yi, shi ko a jikin'sa, ni zai bari da ciwon zuciya.

Tare ma muka zauna. Bayan na gaishe shi nace.

"Yaya momi, da fatan tana lafiya "

Sai da ya fara da yi min wani irin salon kallo da Idanuwan nan nasa masu farauce zuciya. Amma na tabbata, babu manufar komai cikin'su.
Baki d'aya Sai naji yanayin komai nawa ya canza tashi guda. Wani irin feeling naji, da bantab'aji ba kan wani namiji ba. Gashi na jawa kaina, muna fuskantar juna bare na kub'uce, gaskiya macen da za ta iya kubuta daga tarkon shauki ko kaunar Ancle faiz ba ace babu ba, amma zai wahalar, sai dai wacce ba a halitta da shaawar son da namiji ba.

"She is doing fine. Yace cikin dan sakin fuska.

Na barota lafiya Lau. Amma yaya kikasan Momi?".

Nace.

"Tun da nasan'ka ai dole na San'ta"

Yace"A'a ni kad'ai kika sani. Ita dai kinji sunan'ta wurin Sulaiman. Any way, naji dadi da kulawar ki a gareta." Sai naga ya dan kara sakin fuska kadan.

Karo na farko kenan da na tab'aji ya nuna jin dad'i a a binda a kayi masa a sanina.

Gudun kar na kuma laifi, nayi saurin cika cup da lemon maltina mai sanyi na mik'a masa.

Kafin ya karb'a yace.

"Lady Kinyi karatun ta nutsu Kenan!. Ban tanka ba.

Ya Mik'a hannu ya karb'a, Amma bai shaba, ya Shiga juya d'aya kwalbar lemon da ban bud'e ba.

"Yaya a kayi, kika San Ina son lemon malt?.

aikin Sulaiman ne dai na sani".

Idanun'sa na kan lemon yake surutan.

Ya shanye, ya sake cika cup ya shanye. Ya bud'e d'aya kwalbar ya cika cup ya Sha, ya a jiye ragowar a gefe.


"Da k'ishirwa na iso, Sai kika samu ladana kika yi a binda ya dace. Ina son maltina sosai a rayuwata. Na kansha kwalba uku ko hudu wurin training ko gasar boll."

Nace.

"Lallai kana son"ta da yawa."

"Ke baki son'ta?" .

Yace.

Nace.

"Kadai d'arsa min son'ta, ga yarda ka damu da ita."

Yace cikin wani lumshe idanu kan kwalbar lemon.

"Look, ki fad'i opinion d'inki Kawai, ba ruwan'ki da zab'ina ok? ".

Naji rashin jin dad'in gwaliyar da yayi min,
amma Sai na danne.

"Domin na tayaka son a binda kake so laifine.?"

Yace.

"Kuskure ne dai, saboda ra a yina da bam naki dabam, banga dalilin da zai sa ki tayani son wani a bu ba, don ni bazan tayaki ba anan zance na fisabilillah, iya nawa zan tsaya, kinga kuwa bai kyautu kiyi min kara ba, gaskiya ni kullum ba na boyanta bayyana ta nake, ko da kuwa kowa zai tsane ni, i don't care".

Kafin na wartsake daga wannan ya jefomin wani.

"Sumayya wai addu'a kika yi min ne?".

Na waro idanu waje.

"Wace addu'a zan yi maka ni kuwa Ancle Fa'iz?".

Yayi harr da idanu ya sake kafeni da irin kallon d'azu, jin furucina

"Wallahi da da na tafi, naci alwashin bazaki sake gani na ba, saboda gidadancin da kika nunamin. Amma bayan few days, Kawai Sai samun kaina naji Ina son waiwayarki kuma, kuma zuciyata ta nuna min fin karfin sani sai da nazo ba domin na niyyaci zuwan ba, naga kin canza yau, kina d'an tab'uka abu. Kenan komai da kika yimin rannan kina sane Kenan.?".

Bani da amsa, idan ma a Kwai bazai jiba. shi yasa na zab'i yin shiru.

"Kin a mince zaki jure irin Zaman aure N'a? ".

Samun kaina nayi da juya idanu na rausayar

"Zan jure man, tun da na iya jure zafafan bulalanka goma, masu ratsa k'ashi da tsoka."

Sai ya d'an d'aga idanun'sa Sama, mai nuna a lamun ya tuno komai. Sai yayi dan murmushi da banyi zato ba.

"A shefa kin tab'a fad'owa tarko na ko? amma wannan shafar mai ne, idan kika yi saken da kika sake fad'owa tarko na. Kinsan yanzu matsayi uku zan had'a a wurinki da an shafa fatiha.
Malaminki nake, Sannan Ancle,Sai na gaba mijinki.".

Da hannun'sa yake nuni, ta hanyar lank'wasasu.

"Haka ne?".

'Yar dariya na saka.
Yace.

"Zakiyi ta gasken ne"

Ya tattaro, Nutsuwar'sa.

"Ina so ki fad'amin nawa zaki buk'ata na shirin auren'mu na biki, domin na tanadeki , banason auren nan ya wuce Wata guda fa. "

Da hanzari, na dubeshi. Duk nasan saboda manufar sa ne,da yake so ya cimma. Wani zafi, naji a k'irjina.

Eh, ga 'yar tsana ka samu, dole ka gaggauta.

A raina na fadi, saboda nasan ban isa na fadi a fili ba mu kwashe lafiya.

"Barshi, na yafe. Ni babu shagalin da zan'yi."

Ya jefa min kallon hadarin kaji.

"Kija Mani zargi ko? to bazai yiyu ba. Bazaki tozarta min aure ba, ko ba kya Sona , kuma ko banason'ki za'ayi shagali irin Wanda ya dace. Kije kiyi nazarin adadin kud'in da zakiyi amfani da shi. Idan na dawo naji. Dole ne , kima saddak'ar."

Shiru nayi, jin zai soma hawa dokin zuciyar'sa da nake tsoro.

Bayan sa'oi kamar mai wani tunani sai kuma ya dago kai gareni da nayi shiru cikin kafeni da idanun'nan nasa masu narkar da zuciya.

"Kiyi min magana ko?"

Nace.

"Zan fad'awa Kawu Sulaiman, idan na lissafa."

Ya kwaikwayi salon yarda na furta.

"Zan fad'awa Kawu Sulaiman idan na lissafa. To Wai meyasa zaki nuna bam bamci tsakanin ni dashi? Nima ba kawun bane?".

Da nayi shiru, ya tafa hannun'sa a hankali, ya kuma dunk'ule.

Shikenan 'yar gidan Kawu Sulaiman, Sai naji daga gareki."

Ya ci gaba da lissafomin irin shirin da ya soma na auren. Lefema da Sadaki, da kud'in aure yace rana guda zai kawo. Kenan Ranar d'aurin aure Kawai za'asa . Yarda yake nuna a fuwa da komai, Sai a zaci, wani auren soyayya za muyi da shi, na an matsu da juna. Bayan nan bana gaban'sa na Sani, ko na sakan na a gogo. Manufar'sa ya d'anawa k'ahon zuk'a.

Fargaba d'aya nidai ta ragemin, shine kar a zal ta fad'amin Ancle Fa'iz ya samu damar yi min cuta ta k'arshe. Shine burin'sa Yana cika ya sakenj, nazo na bud'e faifan Zaman zawarci. A binda nafi tsana Kenan a rayuwata, zawarci..

Jinake yi, har gabana na yankewa ya fad'i idan na tuno.

Nina shirya had'uwata da Nuriyya domin taji labarin da zai kid'imata. Wato na aure na da Ancle Fa'izu. Mutumin da ta k'wallafarai a kan'sa kamar ta zautu, wai yau shi yake shirin aure na. Inda a ke neman'sa yayi b'atan dabo..

Ko da yake batasan waye Ancle Faiz ba dangane da halayya, da ko daura mata a kayi sai ta kwance, duk son da take masa ba za ta iya da halayen sa ba, saboda ita ba ta da hakuri, ga tsiwa. Ai a guje za ta raina kanta, ta ce ba da ni ba.






_Taku a kullum_





_Zainab ilyas mawaje_

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe



*NI DA GIDANA*




_Zainab mazawaje_


_Best brilliant interlligent writer_...... 🖋️





*Page 10*




Nuriyya kuwa ta girgiza da jin komai. Nasan baza taji dad'iba, tun da ta nunamin irin son da take yi masa a baya. Sai dai bani da zab'i face dole na fad'a mata, tun da babbar a miniyata ce dole taji. Ban sanar da ita sirrin komai ba, na dai ce Kawu Sulaiman ya had'a auran, amma ni a fargaba nake.idanunta naga yayi rau rau.

Tace"Sumayya al'amarin ubangiji ya shallake tunanin bayi. Tsakanina dake a wannan lamari addu'a Kawai, to yaya zanyi? bani da yarda zanyi Sumayya."

To nima d'in dabara ta kubce, bani da yarda zanyin da na barmata, toma idan zan iya barmatan uban gayyar karba zai yi?

Dani da itan da take azabar son sa
duk rukuni guda muke. Babu Wacce ta rabauta da Soyayyar'sa, Sai ni da k'addarar auran'sa ta sauka a kaina.

"Ni haushi kike bani da kike Kiran wai kina zullumin auren'sa.

Kamar wannan zuk'ek'en saurayin za'a nok'ewa auran'sa?

Wallahi da motsi a cikin kan'ki, ba kalau kike ba koma ba na gari bane, ke dai ko baki tashi da ribar komai ba, kika tashi da ribar kyawawan fararen yara, ai kin gama da shi. Kasuwa ta tashima ai d'an koli yaci riba".

Ni kam haushi furucin'ta ya bani. Ana ga yak'i tana ga k'ura.

"Inaji ganin jarabarki ta son kyau da fari, Sai kin auri maye, nasan ko kinsan mayen nema auren'sa za ki yi ".

Tayi 'Yar dariya.

"Tabbas!. Ko zai rink'a lasar kurwata kullum Ina suma na farfad'o zan aureshi in dai irin Ancle Fa'izu ne."

Na jinjina furutanta.

"Al'amarinki Sai dai neman sauk'i Nuriyya, amma ba waraka ba."

"Bani buk'atar warakar Dama".

Tace, ni kuwa binta nayi da kallon mamaki kawai.

Akwatu Shida set da kit d'aya Ancle Fa'iz ya had'o min na lefe. Ya zuba abubuwa kuma gaskiya masu tsada fiye da zaton kowa.

A tamfofi Holand manya guda goma ne. Bayan masu matsakaitan kud'i goma. Lesuna masu daraja guda goma ne. Shaddodi da material ma sunyi . Hakanan Takalma da jakunkuna babu masu rangwamen kud'i. Sai a jakar Kayan sarkoki' za'a sha kallo. Duk da babu gold, Sai da aka zab'a a ka darje wurin zab'o k'ayatattun sark'oki na cinyewa, launi launi. Tilas a ce isashshiyar mace da tasan kan sirrin iya ado da kwalliya ta zab'o.

Ni dai Abin yayi matuk'ar d'auremin kai, na yarda ya narkar da kud'i irin haka a auren da yafi kowa sanin manufar'sa da makomar'sa a gaba.

Hajiya Mariya tafi kowa, murnar zuwan aure na, inda tayi ta kod"a lefen tana labartawa ga wad'anda basu gani ba, tamkar kaina farau, kuma k'arau. Haka ma 'yan uwan uwa da ubana kowa Sai Sam barka da Fatan alkhairi.

Sati hud'u a kasa d'aurin auren. An tasheni tsaye an kuma tashi Kawu Sulaiman tsaye da kakana. Domin duk basu shirya ba suma, saboda basu zaci zuwan aurena a tsukin ba. Amma Kawu Sulaiman naga ko a jikin'sa. Murna yake sosai da zumud'in zuwan auren . Kuma dama komai Ancle Fa'izu yace ga yarda yake so a yi a kan aurena da shi, to ta zauna. Shi yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login