Showing 9001 words to 12000 words out of 47989 words

Chapter 4 - NI DA GIDANA Complete Hausa Novel

15 Jul 2025

3102

Malam Fa'iz ke tausasa harshe yana fad'amin wad'annan kalaman? Dama ya iya tausasan kalamai a she?

Kawu Sulaiman ya duba yana mai cewa.

"Farko ta yarda wayar'ta na tsinta, ta kira layin mu kayi magana ta kwatan'ta min gidan nan na kawo mata. Kasan ban tab'a zuwa gidan nan ba Sai yau ai da tun a ranar na d'au haske, domin Sai yanzu komai ya dawo min,nan gidan nazo na kawo mata waya. Bayan watanni mun sake had'uwa da Sumayya a makaranta nayi teaching d'inta, Kenan a malamin ta nazo. Yanzu kuma Bayan shekaru biyu mun sake had'uwa da ita ta dalilin ka. Me hakan ke nufi Sulaiman, da sanadi ke ta had'ani da 'yarka?".

Murmushi Ancle d'ina yayi yace.

"Da walakin goro a miya. Kuma ruwa baya tsami banza. Idan kaji gudu kuma to da magana.

Fa'izu baice wa kawuna komai ba, game da furucin da yayi, don wasa ma naga ya dau zancen. Ya sake dubana cikin dan jin kan nan nasa kamar bazaice komai ba ya dan juyar da kai sannan ya dawo da shi kaina yace.

" Karatu kike yi ne Sumayya?".

Nace"Eh".

"Da kyau, kin birgeni. Ki daure ki zurfafa karatu, kici moriyar sa tun da kIna da k'wak'walwar fahimta. Ina yi miki fatan alkhairi da nasara."

"Na gode Ancle."

Na fad'a cikin wani nishad'i da naji ya bak'unci zuciya tashi guda. Gani nake tamkar ba Fa'izun da na Sani bane. Wannan yafi wancan kyawun Siffa ma da ake ta kwaroroto, da dan jiki kadan da ya kara, duk sanadin dan hutu da na fahimci ya samu, kuma sai naga yafi kyau a hakan, kuma halinsa ya canza wurin sanyi da sauk'in kai, amma nasan da dalili.

Amma dai tabbas shine, tun da gashi mun tuna baya ma. Sai dai nasan komai yanayine sanadin kawu Sulaiman ne wanda ya nuna yana da muhimmanci a gareshi.










_Ku biyo ni dai labari ba a soma ba ma tukun_.




_Taku Zainab mazawaje_


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe




*NI DA GIDANA*

*By*


*Zainab Mazawaje*


_Best brilliant interlligent writer_........🖋️





*Page 5*





Nasan albarkacin kawu sulaiman naci na daga fuskar da na samu wurin malam Faiz.

Zuciyata ce ta fad'amin.

Fa'izu ya dubi kawu yace da Kawu na.

"Zan tafi Sulaiman dare ya soma, don Allah goben ka fito da wuri, a yi training, kasan wannan wasan na farko ne sai mun nuna k'wazo fa."

Cikin 'yar dariya Kawu na yace. " Babu ji Yarima. ai bamu da fargaba, tun da muna da champion irin'ka."

"Kaji ka da wani zance. ni kad'ai ne zanji da komai? wato dani kuka dogara a nasarar ku ko?to kuwa wallahi zan kayar daku Ina sane."

"Tuba muke Yarima, mun tuba mun bika, ayi afuwa".

Yarda Kawu Sulaiman ke kwantar da kai, shi kuma Fa'izu ya sha mur serious babu kafar zai sauko, Sai dariya taso ta subcemin na kanne.

Yana nan dai bai canza ba. Nace a raina. Nan dai na bar'su ni na koma wurin Usman.

"Dan fodiyo, na jima ko? A yi hak'uri."

Nace.

Yace. "Gimbiya ai bata laifi. Yaya kuka yi da Yaya Sulaiman don Allah. Ina cikin fargaba."

Nace"Karka damu, yace nan da Jibi zai yi magana da kakanni na zai yi maka magana"
.
Dad'i ya kasheshi a ranar, gani yake kamar yayi nasara. Ni kuwa tuni na fahimci Kawu na kamar bayason magana ta da Usman. Kai ban ma fahimci alk'iblar sa ba ma. Kamar bayason nayi aure a kusa ma, Sai nayi ilimi mai zurfi, amma fa zato nane.

Koma hakan ne, nima burina ne dai. Amma Usman ne yake ban tausayi haka nan.

Da daddare an kawo wuta, na d'auko caza ta zan saka wayata a caji, inda kawai Sai Ancle Fa'izu ya fad'omin a rai. Saboda shi ya had'omin da cazar, Sanda ya kawo min wayata da ya tsinta. gashi kuma a ranar yazo gidan namu.

Zuciyata keta haskomin duk wasu a bubuwa na Fa'izu da suka wanzu tsakanina da shi. Na rasa kuma dalilin da hakan ya zauna min kuma a rai. Murmushin da yayi min da muka had'a idanu a bisa tsautsayi
, yak'i sharewa daga cikin k'wak'walwa ta, duk da na tabbatar babu Wata manufa a zuciyar'sa game da hakan.

Nayi kwance al'amarin farkon had'uwata da shi ya dawomin a hankali.

Ga yarda a bin ya faru a tak'aice.

Gidan k'anwar kakata naje wata Hajiya mariya, Wacce ita ta fara rainona bayan mutuwar mahaifiyata, kafin baba na ya rasu Shima.

Bansan na yarda wayata bama, Sai da nazo gida, Ina kici kicin zaro canjin kud'ina zan yi aike, ga yaron aiken kuwa tsaye a gabana. To babu kud'I kuma babu wayar a babban zip d'in jakar, da bansan lokacin da suka zube bama. Dama jakar ta d'an farke Sai gani nayi ta yage ma sosai a she ban Sani ba. Nan nasan na rasa wayata a karo na biyu, domin ko wata biyu batayi da saye ba da kawuna ya sayamun Sabuwa bayan an sace waccan. Kuma mai tsada ce a kan waccan. Damuwa ta tayi nisa, a raina a ranar, saboda kar Kawu Sulaiman yace Ina da sakaci da rashin kulawa a kan abinda yasa k'ud'i ya saimin. Waccan an sace, wannan kuma nayar? ai bazai ji mutuwar sarki a bakina ba kuma. Ba kina naja na tsuke. Amma fa kullum a farga ba nake, kar ya ne mini a waya ya fahimci komai. Kwanaki hud'u tsakani Sai ga wata a miniyata mai suna Nuriyya.Muna hira nake fad'a mata b'atan wayata. Ta jajanta min.

Nace. "Bani a ron wayarki ma na kira layin, duk da ban saka rai bama. Duniyar yanzu ba gaskiya. Masu tsoron cin haram ko rik'e haram, sun yi K'aranci. Da kud'i a wayar taki?".

Tace. "Kinfi kowa sanin waya ta kullum cikin credit take, bata zama fanko, saboda Ina da masu yi mata hidima."

Na warce wayar Ina cewa.

"Allah ya shiryeki Nuriyya. Kullum baki da aiki Sai tatse samari, kuma ba auran su zakiyi ba, Wallahi kiyi hattara".

"Na nawa kuma, wai ance da kuturu ka gama lafiya. Namiji ai yaso yaudarata, amma na nuna masa ni 'yar zamanice ai ni naci dubu Sai ceto, nafi gaban a washeni, domin murucin ni kan dutse ce ban fito ba Sai dana shirya. Ke dai ki jarraba Kiran ko kya dace, idan kina da rabo. A kwai na kirki a duniya."

A ringin na uku, a ka d'auki wayar kuwa, bayan na k'agu da a d'aga.

Muryar namiji a hankali naji tayi min sallama. Muryar bata da d'agawa irin ta maza.

"Dawa nake magana?".

Nace.

"Sunana Sumayya.....
Bai bari na k'arasa ba yace. "Ko zaki taimakeni Sumayya ki had'ani da mai layin wannan wayar da kika kira? Tsintar ta nayi a hanya zan wuce kwana ki hudu da suka wuce. Naji sanyin dad'i a raina nace"Wayar tawa ce wallahi yanzu ma kira nayi ko zan dace. Yace

"Kin kuwa dace 'yammata. Zaman wayar ma a hannu na duk ya dameni, so nake na mik'ata ga mai ita Kawai. Don da na tsinta caji ma babu, Sai da na Sai mata caza Sabuwa na caza ko mai ita zai bugo, sai yau a kayi dace a ka bugo.

Yaya za'ayi ki karb'a?".

Nace. "Fad'amin in da zan sameka Sai nazo na amsa."

Yace" Ba haka za'ayi ba, ke zaki kwatanta min in da kike nazo na kawo miki, dama fita zan yi. A wace unguwa kike?".

Nace" Ina unguwar Doka".

Yace. "Anya na tab'a Shiga unguwar nan?".

"Kai ba d'an garin zariya bane?". Nace da shi.

"Haifaffe ma kuwa.

Yace da hanzari. Domin kana d'an gari ai baza'ace ko'ina kaje ba. Amma dai zan zo, idan na shigo unguwar Sai na tab'aki a layin da kika kira kiyi min jagora, kar na manta. Tare da a bokina suhail zamu zo, tun da shi idon gari ne. Amma ki tanadi ladan tsuntuwafa. Kinsan yanzu ba'ayin aikin da babu in come".

"Ga zatona da gaske yake.

Nace"Babu damuwa, zan bada idan babu yawa."

Yace"Babu yawa ai. 'yar dubu goma ce kawai'.

Fa'izu yace da Kawu na."Zan tafi Sulaiman dare ya soma, don Allah goben ka fito da wuri, a yi training, kasan wannan wasan na farko ne sai mun nuna k'wazo fa."
Cikin 'yar dariya Kawu na yace" Babu ji Yarima. ai bamu da fargaba, tun da muna da champion irin'ka."

"Kaji ka da wani zance. Ni kad'ai ne zanji da komai? Wato dani kuka dogara a nasarar Ku ko?to kuwa Wallahi zan kayar daku Ina sane."

"Tuba muke Yarima, mun tuba mun bika, ayi afuwa. Yarda Kawu Sulaiman ke kwantar da kai, shi kuma Fa'izu ya Sha mur serious babu kafar Zai sauko, Sai dariya taso ta subcemin na kanne. Yana nan dai bai canza ba. Nace a raina. Nan dai na bar'su ni na koma wurin Usman.

"Dan fodiyo, na jima ko? A yi hak'uri." Nace
Yace"Gimbiya ai bata laifi. Yaya kuka yi da Yaya Sulaiman don Allah. Ina cikin fargaba."
Nace"Karka damu, yace nan zai yi magana da kakanni na a sa lokacin da zaka turo, sai na fada maka.

Dad'i ya kasheshi a ranar, gani yake kamar yayi nasara. Ni kuwa tuni na fahimci Kawu na kamar bayason magana ta da Usman. Kai ban ma fahimci alk'iblar sa ba ma. Kamar bayason nayi aure a kusa ma, Sai nayi ilimi mai zurfi, amma fa zato nane. Koma hakan ne, nima burina ne dai. Amma Usman ne yake ban tausayi haka nan.



Da daddare an kawo wuta, na d'auko caza ta zan saka wayata a caji, inda Kawai Sai Ancle Fa'izu ya fad'omin a rai. Saboda shi ya had'omin da cazar, Sanda ya kawo min wayata da ya tsinta. gashi kuma a ranar yazo gidan namu.
Zuciyata keta haskomin duk wasu a bubuwa na Fa'izu da suka wanzu tsakanina da shi. Na rasa kuma dalilin da hakan ya zauna min kuma a rai. Murmushin da yayi min da muka had'a idanu, yak'i sharewa daga cikin k'wak'walwa ta, duk da na tabbatar babu Wata manufa a zuciyar'sa game da hakan.

Nayi kwance al'amarin farkon had'uwata da shi ya dawomin a hankali.


Unguwa naje na yarda wayata bansani ba, a she kasan jakar ya yage.

Na kasa fadawa kowa musamman kawuna da ya sai min kuma bata dade ba, nasan bazai ji dadi ba.

Rannan kamar wasa Nuriyya kawata tazo nake fada mata, sai tace na kira a wayarta ko za a dace, tun da tana da lambata.

Na kira babu musu amma bansa ka rai ba gaskiya, domin takai sati biyu da yarwa.

A kira na farko a ka daga. Nayi sallama muryar namiji ce ta daga kiran, muryar ba ta da dagawa irin ta maza, ga dadin saurare.

"Sunana Sumayya, ....

Da sauri ya katseni.

Ko zaki taimakeni Sumayya ki hadani da mai wayar nan, ta jima a wurina tsinta nayi z hanya".

Nace " Ai tawa ce wayar, bugowa nayi ma ko zan dace na samu".


Yace "Kin kuwa dace 'yammata, yaya zaayi ki karba".

Nace " Ka kwatanta min in da kake sai nazo na karba".

Yace "Ba haka ya dace ba, ni ya kamata nazo na kawo miki, a wace unguwa kike".

Nace " Unguwar Doka".

Yace "Anya na taba shiga unguwar nan".

" kai ba dan garin zariya ba ne".

Yace da sauri. "Haifaffe ma kuwa, domin kana dan gari ai ba dole bane a ce koina ka shiga, amma zanzo tare da abokina Suhail, dama zamu unguwa a babur din sa, shi idon garine nasan yasan unguwar, idan na shigo sai na kiraki a layin da kika kirani ki kwatanta min gidan, amma ki tanadi ladan tsuntuwa, domin ba a aikin da babu income yanzu".

Nace"idan babu yawa baifi karfina ba zan bayar".

"Ba yawa dubu goma sha biyarce kacal".

Da sauri cikin mamaki nace " Dubu sha biyar? to daga nan na bar maka wayar mana, tunda ko sai da ita zaayi ba zatafi haka ba yanzu, tun da anyi amfani da ita".


Ya sake yin wata 'yar gajeriyar dariya da ta k'ayatar da ni, banganshi ba, amma dai zuciyata sai haskomin hoton sa take, saboda tsadaddiyar muryace mai wani irin amon sanyi da dadi, da take kamancece niya da irin cikar surar mai ita.

Kawai Ina jin a lokacin a cikin salo na raha yake sosai, domin barkwanci da raha basa cikin halayyar Fa'izu a sanina.

"Bari nazo dai sai mu kashe maganar".Abinda yace kenan ya datse kiran kafin ma nayi.

Nuriyya da tayi sararo
tana jin mu ni da fa'izu, saboda hand's free nasa .

Bayan na kashe wayar tace. " Kiji mu da Mutum. da har ina yabon'sa a zuci, ina kaga na Allah mutanen arziki,
ta fad'a hannun Mutumin kirki,a she duk gayyar tsiyar ce .

A bashi dubu goma kamar tasa ce zai bamu mu Saya?".

Nace.

"Ke dai rabu da shi, yazo tukun, muga gudun ruwan'sa. Nace a hankali domin tausarta.

Cikin a binda baiga gaza a wa guda ba, Sai gasu sun kafe babur a kusa da k'ofar gidan mu da taimakon kwatancen da nayi musu a waya da suka shigo unguwar.

Muna tsaye dama a k'ofar gida ni da Nuriyya. Samarin d'aya fari ne sosai, d'aya bak'i. Bak'in yafi sakin fuska da fara'a a garemu shima black beauty ne gaskiya.

Bayan musayar gaisuwa, farin saurayin ya zura hannu cikin aljihu ya zaro waya gami da sabuwar caza ya mik'o mana. Ni na karb"a cike da godiya.

Yace.

"Sai ki kula, karki sake yarwa, domin ba lallaine ta dawo ba."
Nayi mamakin canzawar sa kamar ba shine mai barkwanci a waya ba.

Nuriyya tace da sauri.

"Gaskiyane kam, domin ba domin mun yi dace da mutanen kirki irin ku ba, ai da tarasa kenan. Kuna da kirki da karimci gaskiya, don Allah yaya Sunayen Ku?" .

Ni Kam naga Zak'ewarta, shi yasa nayi kasak'e ina kallon'ta.

Wannan saurayin bak'in ,shi ya bata amsa.

"Sunana Suhail labaran. Shi kuma sunan sa Fa'izu Bukar".

"Kai Amma Sunayenku suna da dad'i, kamar na larabawa? a wace unguwa kuke ne? ".

Nan naga mai suna Fa'iz d'in ya jefeta da wani irin kallo a sakarce, dake nunin ta isheshi da Surutu. Ni kuwa dama tuni ta k'ular dani na irin wannan shishshigi. Su ya dace su nememu da hakan, ba suyi ba, Sai mu mata? domin kawai ta zubar mana da daraja?.

Tuni dama na fuskanci wannan Fa'izun d'an ji da kaine da fad'in rai. Tun daga Maganar farko bai sake cewa komai ba. Ko kallon mu bai sake yi ba, Sai da Nuriyya ta Shiga k'wak'ulen tambaya ga a bokin'sa ya waigeta sau d'aya, kallo ma na raini.

"Zo nu tafi Suhail, kasan sauri muke yi, kuma ba jiran mu zasu yi ba".

Inji Fa'izun. Inda ya ce masa "To" .

Amma bai motsaba, saboda Nuriyya da ya soma yiwa kwatancen in da suke dalla, dalla. Bai yi nisan ma da zata gane sosai ba Fa'izun ya sake cewa.

"Idan ba zaka zo mu tafi ba, ni kaga tafiyata. Bazan jiraka ba wallahi idan ka tsaya, ka taho daga baya."

Faiz Ya dubeni yace.

"Sai anjima."

Nace. "Na gode, Allah ya saka da khairan."

"Amin.".

Yace bayan ya soma tafiya.

Ganin haka Shima Suhail d'in yayi gaggawar binsa
saboda ya fuskanci tafiya zai yi ya barshi, bayan babur guda suka zo kuma. Bai k'arasa yiwa Nuriyya kwatance ba dai ya tafi.

"Gayun nan sunyi a rayuwa. Musamman ma farin, Fa"iz.Sai dai naga d'an girman kaine da nuna isa , d'an hana ruwa kuma gudu, abokin'sa ya fishi kirki. Yanason a k'ulla zumunci ya hana.Ya bani haushi fa!".

Nace".Naji dad'in a binda yayi Miki, haka Kawai daga had'uwar k'addara Sai ki Zak'alk'ale? Wannan halin zub da ajine Nuriyya. Nayi mata tatas, tayi lub. Amma fa an d'auki lokaci in dai mun had'u Sai tatada Zancen wai taji ciwon rabuwar mu da su babu a direshi.

Rannan kuma muna hira tacemin.

"Kinsan me Zuciyata ta ayyanomin yanzu?"

"Ta ina zan Sani,baki fad'iba.".

Nace da ita.

Tace"Zuciyata ke sak'amin, Ina ma ina cikin tafiya, na had'u da miskilin gayen nan, ai ko bai kulani ba naci riba."

Nace.

"Kin Shiga uku Nuriyya."

Tace"A wani dalilin zaki kiramin musifa".

Nace "Ai kuwa kin shiga cikin ta yanzu, tayaya za ki kwallafa rai da mutumin da ko kallo baki ishe shiba? dama daya hand some din guy bakin kike so, sai ince dan dama dama, don zai iya sauraronki ko baya sonki, saboda naga yana da saukin kai shi gaskiya. Ke ruwa ma ba saan kwando bane gaskiya daga yanayin ganin samarin nan kinsan ma ba saan nin yi ki ba ne, sun kuma kama dahir, kawai kisa hakuri".

Ta harareni kawai taja tsaki. Nayi zaton za ta kuma tankawa na kare mata tanadi, sai tayi shiru. Domin gaskiya haushin yarda take zubar da aji nake, gashi sun nuna mata a aikace na ba ma gabansu, amma ta rufe ido ta kulle tunani, wai bata dau haske ba, saboda son zuciya kawai.

Kunji wannan.




Daga bakin alkalamin....🖋️ Zainab mazawaje muje zuwa


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe




*NI DA GIDANA*

*By*



_Zainab mazawaje_

_Best brilliant interlligent writer_..... 🖋️






*page 6*




Tun daga lokacin na fahimci Nuriyya kamar tayi fushi da furucin da nayi, don naga bata kuma dauko min zancen ba, a raina nace ya dai fiye miki hakan, kisan ciwon kan ki da mutuncin kan ki gaskiya.

Daga lokacin, na samu lafiya ta dai na yi min Zancen, amma bansan cikin Zuciyarta ba ko tana sak'awa.

A daren ranar dai Alhaji Rabi'u yazo ya matsamin lamba na sai na bashi dama ya turo iyayen'sa Yasan matsayin'sa. Sayayya fal yayi min kuma. Yace ya kuma gaji, ko yin ko bari yana son sani. Nace ya bari, zanyi magana da kawuna.

Kafin ma na fad'awa Kawu Sulaiman, da Nuriyya k'awata tazo, ta rikirkita min lissafi.

"Wallahi ni nafi miki Sha'awar Alhaji Rabi'u domin yafi Usman kud'i . Alhaji Rabi'u yafi Usman shekaru da gwagwarmayar sanin wahalar aure da juriya da sanin darajar iyali. Kefa kika ce zaune yake da matarsa lafiya, gashi kince yana yabon matar Sama. Mai wannan ai Sai namiji na gari. Shi kuwa Usman baki da misali a kansa da zaki samu tabbas, Sai kin Shiga zaki gani. Kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login