Showing 18001 words to 21000 words out of 32024 words

Chapter 7 - KIDA A RUWA

09 Apr 2026

1104

sakamakon abinda zuciyarta ta ayyana mata akan matar. Amma sai ta danne shi ya tsaya cikin ƙirjinta. Dada dake ƙoƙarin kai waya kunnensa ya ɗago ya kallesu, shi sai ma suka nema sakashi yin dariya. Ya dai gimtse baiyi ba, dan saima ƙara ɗaure fuska da yay cikin bada umarni ya furta, “Kiddo zoki bani abinci”.
Duk da wani haushinsa da take ji saboda rungumar da Nabeeha tai masa sai ta jinjina kai tana nufarsa, dan kurama ai tasan gidan mai babbar sanda. A kusa da shi gab takai duƙe gaban table ɗin, ta bubbuɗe kwanikan abincin sannan ta kalleshi, duk da waya yake da Imran dan taji ya ambaci sunansa bata fasa faɗin, “Dada mi za'a zuba?”.
Yanda tai maganar cikin raɗa da masa nuni da hannu tana wara masa idanunta manya ya sashi ɗan zuba mata nasa idanun. Sai da ta sake waro natan sosai ta ce, “Dadaaaah”. Sannan ya farga da abinda yake ya janye yana nuna mata da hannu. Ta jinjina kai ta fara zubawa, sai dai ta raba hankalinta a kallon Nabeeha da har yanzu ke tsaye inda suka barta tabbacin ta shaƙa da abinda yay mata. A cikin zuciya Nimrah tace (Tun banyi komai ba aunty masu miji) a zahiri kuwa sai da ta kammala zuba abincin tsaff kawai ta saka murfin kwanon tangaran ɗin da aka zuba salad ciki baki-bakin table ɗin da gangan ta kaɓoshi ya wantsalo ƙasa sai kuwa akan ƙafarta. Duk da dai tayi dabarar saka hannu sai da ya taɓa bisa tsautsayi. Zabura tayi cikin gigita sai kuma hannunta ya tsumbula cikin kular farfesu. Aiko ta fasa ƙarar data saka Dada sakin waya ya juyo kanta...
Itako tuni ta miƙe a zabure ƙafar damƙe a hannunta ɗaya tana tsalle da ɗaya, hannun daya shiga miya kuma tana yarfa shi har tana neman faɗawa kan abincin nasa. Ba arziƙi ya tarota gaba ɗaya sai kawai ta faɗa saman cinyarsa. Anan kam harga ALLAH bata san kansa take ba, dan da gaske zafin ya ratsata har cikin kai, gashi bibbiyu hannu da ƙafa, dama ga Nimrah da shegen ragwantaka.
Rasa ina Dada zai kama mata yayi, dan ita kanta Nabeeha sai da ta zaburo, sai kuma taja ta tsaya tuna wacece da kuma yanda ya riƙota jikinsa. Tai bala'in waro idanunta waje ganin ya kama hannun Nimrah kawai ya saka yatsun data saka a farfesu cikin bakinsa. Ɗayan hannun kuma ya riƙo ƙafar tata.
Itama kanta uwar haɗa wajen tsittt tayi a karo na farko, dan abune da yazo mata a matuƙar bazata, bazatar ma mai gigitar da zuciya. Dan yanzu kam ta fahimci an sauka daga layin abinda tai niyyar aikatawa an tafi wani layin sabo data gagara bama suna ko kalma. Dada da shima sai yanzu ya fahimci halin da suke ciki sai ya runtse idanu, kafin ya buɗesu a hankali kan fuskar Nimrah data zuba masa nata idanun cikin yanayin ruɗani. Sai kawai suka sarƙe cikin juna, kamar kuma waɗan da aka hana motsi kowanne ya kasa janyewa suka shagaltu. Shagala a kallon juna irin yanda basu taɓa yi ba cikin idanu dai kamar haka.....

=============

“Baƙo kuma?”.
Hajiya Hasiba ta faɗa da mamaki tana kallon maigadi. Kansa ya jinjina mata. “Eh Hajiya. Kuma kamar ma baɗan ƙas.....”
Ya kasa ƙarasawa sakamakon shigowar Adeel falon. Miƙewa Hajiya Hasiba tayi, dan ita kaɗaice a gidan su Amima na gidan Nabeeha. Cikin in-ina maigadi ya ce, “Ya....ya..yauwa Hajiya ai gama shi nan ya shig.....”
Hannu ta ɗaga masa. Sai kuma tai masa nunin ya fita. Babu musu ya nufi hanyar ƙofa yana waigen Adeel. A ransa faɗi yake (Yau gani ga Balarabe ikon ALLAH) sai da ya kusa cin tuntuɓe ya dawo hayyacinsa...
Received at 12:22 PM
Adeel dake kallon Hajiya Hasiba fuska a ɗaure hannayensa duk a cikin aljihun wandonsa ya kai zaune cikin kujera cike da isa da gadara. Sai wani bin falon yake da kallo a yatsine. Duk da kuwa ba laifi falon ya haɗu, kuma a gyare yake tsaff ga ƙamshin air freshener na tashi. Sake maida idanun nashi yay a kanta. Da sauri ta fara gaishe shi murya na rawa.
Maimakon amsa mata sai yaja siririn tsaki. Cike da wulaƙanci ya furta, “K! Nine zakima ƙaryar kinyi tafiya?”.
“Wlhy ba ƙarya nake maka ba. A cikin satin nan na dawo. Kuma na nemeka amma ban samu ba. Ban san ka dawo ƙasar nan ba shiyyasa nake neman layin Abu-dabi.”
“Mtsoww!” ya sake jan tsaki. Sai kuma ya sake watsa mata kallon banza. “Nayi alƙawari dake kin saɓa. Kince mijinta na prison na bincika ance ya fita. Baki zo kin min bayani ba saboda kina ɗaukata wawa....”
“Wlhy ba haka bane Sir! Idan baka manta ba nata ƙoƙarin mu haɗu kafin kayi tafiyar farko. Amma hakan bai samu ba. Lokacin daka dawo nan ma naso hakan amma baka ɗaga kirana ba, sai daga baya nake jin ka wuce a wajen First Lady”.
“Wannan kuma damuwarki ce. Na baki kwana bakwai ku koma Dubai da ita. Idan ba haka ba zan yi abinda naga dama. Sannan duk abinda na baki komin ƙankantarsa ne babu sai kin cika. One week”.
Daga haka ya miƙe abinsa ya nufi ƙofar fita. Cikin rawar jiki Hajiya Hasiba ta yunƙuro zatai masa magana. Hannu ya ɗaga mata tare da watsa mata kallon daya sakata dakatawa da sauri. Sai da ya fice ta bugo musu ƙofar ta zabura gefe.....

(Idan kwaɗayi.....🥱🏃🏼‍♀️)


>>>>>>%<<<<<<

A ɓangaren Daddy Imran da ƙarar Nimrah ta tayarma hankali tun yana kiran hello! Hello! Har ya haƙura ya yanke kiran. Vibration ɗin kiran daya sake yi da yanda Nabeeha da ke jin kanta na juyawa kamar zata sume a wajen ta nufo inda suke a matuƙar fusace jikinta har yana rawa ya dawo da Dada da Nimrah hayyacinsu. Hannu Nabeeha ta kawo a zafafe zata cakumi Nimrah. Amma sai aka riƙe hannun nata caraf a bazata. Ido cikin ido suka kalla juna ita da Dada. Da wani kalar kallon dake tabbatar da gargaɗinsa da barazanar da bata taɓa gani ba ya furta,
“Kada ki taɓa koda mafarkin tsallaka wannan layin a karo na biyu. Dan tabbas bazaki ajiye ƙafarki kan ƙasa tana tare da gangar jikinki ba. Ni mai RIKICI ne akan wannan ANANAR. Ba lallai na iya kauda idanun TAƁATA ba koda akan kaina ne.”
Sosai zuciyar Nabeeha ke bugawa da sauri-sauri a cikin ƙarjinta. Lips ɗinta na rawa ta buɗe zatai magana.....
“Shiiii!!!” ya faɗa cikin ƙatseta yanama bakinsa alamar zipping da nuna mata hanyar ƙofar fita.
Nabeeha dai tasan halin kayanta, ta kuma san mi zai iya. Ta kuma san fassarar gargaɗinsa da umarni musamman idan har ya buɗe baki yay magana akan abinda ke ransa. Ita ko tsuntsuwar tasa bama ta fahimci inda kalaman nasa suka dosa ba. Hasalima ba maida murtani ga Nabeeha datai niyya bane a wannan gaɓar damuwarta, kasancewarta akan cinyarsa ne tashin hankalin ta. Gashi ya riƙeta ta yanda ta gagara koda motsi. Sai da Nabeeha ta buga ƙofar da ƙarfi Nimrah ta zabura, tsalle ɗaya tai ta wantsalo ƙasan lallausan carpet ɗin wajen jikinta na tsuma, ga zuciyarta na wani kalar bugawa diff-diff-difff. Dada ma idanu ya runtse da ƙarfi, sai wani motsa yatsunsa yake kamar mai kiɗa akan hannun kujerar. Sai da ya tabbatar ya samu nutsuwar da yake buƙata sannan ya buɗe idanun tare da yin gyaran murya yana sake tsuke fuska tamau.
Cikin dakewa a ainahin Dadan sa ya furta, “Naga hannun”.
Nimrah dake jin kamar tayita kwarara ihu saboda kunya, har idanunta sunyi jawur ta ɗan kallesa. Sosai taji shakkarsa da kwarjinin sa na sake mamayeta. Dan duk da ba dariya yake mata ko surutu ba ƴar sakewar da yake da ita na sakata jin sauƙi. Amma yanda yay ɗin yanzu ita tasan wargi ma waje yaka samu. Sai da ya ƙarema yatsun kallo, ya kamo ƙafarta itama ya duba, duka farcinan sunyi ja daga na ƙafar harna hannun. Baiyi magana ba ya miƙe zuwa fright ɗin ɗakin, ice ya ciro babba ya dawo inda take ya zauna.
Received at 12:22 PMIta dai binsa take da kallon mamaki, handkachiff ɗinsa dake ajiye a saman kujerar ya ɗauka ya saka ƙanƙarar a ciki. Kai tsaye ya kamo hannun nata ya ɗora a wajen data ƙone ɗin duk da baiyi alamar tashi ba. Tako sauke ajiyar zuciya da har sai da ya lumshe idanu ya buɗe. Sai da ya saka mata kusan na minti uku sannan ya miƙa mata alamar ta cigaba da sakawa. Shi kuma ya ɗauki wayarsa.
Bata san waya kira ba, kawai jitai cikin umarni ya furta, “Turo min Ruƙayya”. Daga haka ya yanke kiran.........✍️

Hajja Ninah Ai wanda bai ji bari ba yaji hoi🥱🏃🏼‍♀️.
Received at 12:22 PM
[16/02, 10:58 pm] null: KIƊA A RUWA 3

14

........Anan falo Ammar na ajiye wayar su Aunty Ummi suka shiga masa alamar yaya dai. Dariya yayi, dama kuma ita suke yi tun fitowar Nabeeha da gudu tana kuka da basu san abinda ya korota ba. Tun wucewar Nimrah sama Mammah ta bar falon. Hakan yasa Gwaggo Khadijah da Gwaggo Alawiyya binta, dan sun san dai bai wuce lamarin Nabeeha ne ke damunta ba duk da tana ƙoƙarin ganin ta danne. Amma dai abinda Nabeehan tayi yau rashin kunyar tayi yawa ai.
Wucewar iyayen nasu ciki daɗi yay ma su Ja'afar, dan a take suka shiga amaye abinda ke bakinsu game da Nabeehan suma, kowa cin alwashi yake akan koyama Nimrah abubuwan da zata ƙona Nabeeha da ruwan jikinta. Sai kuma gata ta sakko a kiɗime harma tana kuka. Tsabar wulaƙanci sai suka fashe da dariya a tare har wasu na tafawa. Aiko kamar sun izata, sai ta ƙara gudu tana danne bakinta saboda tahowar wani sabon kuka mai ƙarfi. Suna cikin dariyar ne kiran Dada ya shiga wayar Ammar. Da sauri ya ce, “Kuyi shiru Dada ne”.
Tsitt sukayi ya gama amsa wayar, shine yana yankewa suke tambayar mike faruwa. Abinda Dadan ya faɗa ya sanar musu. Biebah ta ƙwalama Ruky dake kitchen tare da Mu'azz wai suna ma Nimrah special girki kira. Amsawa tai tana fitowa. Saƙon Dada ta gaya mata, da yake bata san wainar da ake toyawa ba ta nufi saman cikin farin cikinta..
Rikicewa Ruky tai da ganin Nimrah kamar tayi kuka. Ta shiga tattaɓata tana tambayar mike damunta. Har sai da Dada daya shagala a kallon su yay gyaran murya. Cikin shagwaɓa Ruƙayya ta kalleshi, kamar zatai kuka ta ce, “Dada Aunty Nabeeha ce ta dake ta?”.
Idanu ya waro waje dan mamaki. Wato dai halin iri ɗaya ne ita da aminiyar tata. Ji wani sharri kuma. Bashi da zaɓin daya wuce girgizama Ruƙayyan kansa, kafin cikin umarni ya ce, “Kamata kuje ta kwanta”.
Kamata Ruky tai, har suka fita yana binsu da kallo, a ransa kam yana jinjina wannan ƙaunar juna. Bayan soyayyar jini, da soyayyar ma'aurata soyayya mafi muhimmanci da ban mamaki ga ƴaƴan adamu itace ta abokantaka da babu alaƙar jini a ciki, lallai duk abokan da sukai tarayya akan soyayya ta gaskiya zasu shiga aljanna suna masu farin ciki da juna. Idan riya ko cin dunduniya ta shigo sai su ƙare da zage-zage da aibanta juna a ranar rarrabe ayyuka. (Ya Rabbi kasa mu rayu da masoya na gaskiya, mu kuma kasance a aljanna tare muna masu farin ciki da juna. Duk wanda zai zo garemu da fuska biyu, ya rabbi kasa shartinsa ya zamewa rayuwarsa bargo akan kansa can ya ƙarata shi kaɗai🙏).
Cahh iyayen nasu suka yo musu da tambayoyi a falo. Sai da Nimrah ta sanar musu abu ne ya faɗo mata a ƙafa sai kuma ta ƙone sannan suka nutsu. Amma da kowa ya hau da tunanin Nabeeha ce. Har sun fara ɗaukar alwashi a zukata. Dariya ce ta nema suɓuce ma Mammah dake ƙoƙarin fitowa. Ta girgiza kai tana gimtsewa. A ranta kam ta fahimci dole tai wani abu kafin waɗan nan iyayen banzar su ɗora Nimrah kan wani layin daban, a haka ma yaya lafiyar kura tunda itama ba ƙyalen bace ƙyallece ita da aminiyar tata Ruƙayya da basa ɓoyema juna sirri....

^^^^^^^^^^^^^^
A ɓangaren Nabeeha kam yanda ta shigo sashen nata ya saka Amima da Rayhana dake cin abinci kallon juna. Sai kuma suka taɓe baki a tare. Amima ta ce, “Lafiya kuwa?”.
“Ƙya tambayeni bayan muna tare”.
Cewar Rayhana fuska a yamutse.
Amimah ta ce “Hummm maybe korota sukai ko”.
“Mtsowww matsalarta ce. Banda zubar da kai ka dawo miji baizo inda kake ba kai ka ɗauki ƙafa ka tafi nemansa. Itafa wannan da cikin aljihun baya aka haifeta muguwar kidahuma za'ayi. Bata gane komai sai son miji.”
“Ikon ALLAH to miye dan taso mijinta Rayhana. Wani kike so taso to ne?”.
Hararar Amima mai maganar Rayhana tayi, cike da takaici ta ce, “Kema fa wawuya ce wani lokacin. Inba hauka ba son miji ne kawai rayuwar aure?. Mijin ma irin Haysam daya san martabar kansa, wlhy sam bata dace da shi ba.”
Received at 12:22 PM Galala Amima tai tana kallonta yanzu kam. Sai kuma tace, “Tofa wata sabuwa. Sai yanzu duk kika san wannan? Toke auren kikai da kika san mima mijin ke buƙata? Anya Rayhana babu wani abu a ranki?”.
“Ubanki ne a raina. Shegiya munafuka”.
Cike da son tura haushi Amima ta kwashe da dariya tana miƙewa da faɗin, “Oh to lallai abin ya girma. Ubana kam ai ubanki ne kema dole ya zauna miki a rai. Adai bi a hankali. Kar wajen tone-tone kaza ta tono wuƙar yankanta. Shi wannan NAMIJIN ZAKI ne ba Mazan club ba. Baya ɗaukar wargi balle shashanci. Itama data samu bata kasance ballagaza bane kuma tana cin darajar Abbanta. Amma kinga matsayarta, balle ke da aka saba leƙe-leƙ...”
Jifan da Rayhana ta wurgo mata da saving spoon ya sata barin wajen da gudu tana dariyar iskanci data sake shaƙe wuyan Rayhana...

••••••••••••••••••••

9:pm na dare Dada daya fita a gidan shi da su Ma'aruff tun bayan sallar magriba suka dawo. Asibiti suka rakashi ya duba Lailah da Baby, daga can suka je duba Daddy Imran gida. Zuwa lokacin su Aunty Ummi duk sun wuce gida. Falon ma babu kowa alamar duk sun shige barci. Baiyi mamaki ba dan yasan masu ƙiriniyar gidan na fama da kansu. Mammah kuwa dama akwai barcin wuri. Su Bilal kuma office gobe. Har ya nufi upstairs sai kuma ya dawo da baya, ƙofar Mammah ya nufa, yay knocking a hankali. A mamakinsa sai yaji tana bada umarnin shigowa.
Koda ya shigo a zaune ya sameta bakin gado tana duba wani littafin addu'oi. Ta ɗago tana kallonsa da amsa sallamarsa. Dai-dai yana kaiwa zaune take faɗin, “Ai har na fara tunanin kiran wayarka. Dan zaman jiranka nake daman”.
Ƙaramin murmushi yay da faɗin, “To Mammah lafiya dai ko?”.
“Lafiya lau. Yaya jikin Imran ɗin?”.
“Alhamdullah ai ba a jigace yake ba. Kawai dai harda razani”.
“Alhamdullah ALLAH ya kiyaye gaba. In sha ALLAHU zan je na duba shi gobe nima.”
“ALLAH ya kaimu”.
“Amin ya rabbi. Shaiɗancin mutanen nan ya fara bani tsoro Muhammad. Tunda har tunaninsu ya fara basu yin amfani da makusantanka domin samun biyan buƙatarsu. Abin akwai haɗari sosai a ciki, idan na farko an tsallake rijiya da baya nan gaba kuma fa?”.
Ajiyar zuciya ya ɗan sauke, dan shi da farko ma yayi tunanin maganar Nabeeha zatai masa. “Kar ki damu Mammah in sha ALLAHU hakan bazai sake faruwa ba. Wannan ma da suka aikata zasu biya bashinsa harda riba da hannayensu. Akwai shirin da nake yi musamman akan su ƙananun nan. A cigaba da mana addu'a dai. Dan in sha ALLAHU nasara ce ke tunkaro mu. Ko ba komai abinda sukayi yanzu ɗin ya ƙara buɗe min tunani na akan sanin su waye su.”
“Addu'a har mu koma ga UBANGIJI bazamu daina yi muku ita ba, ALLAH ya cigaba da baku kariya. Ya ɗora nasararku akan maƙiyanku. Suma ALLAH ya shirye su su gane gaskiya kafin lokaci ya ƙure musu idan masu shiryuwa ne.”
“Hummm Mammah kenan, to Amin. Amma waɗan nan mutanen basa buƙatar shiriya.”
“A'a ba'a yankema UBANGIJI hukunci akan ikonsa ai.”
“Haka ne kam, ALLAH yasa mu dace. Ranar asabar iyayen Haydar zasu zo a tsaida magana.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login