Showing 6001 words to 9000 words out of 32024 words

Chapter 3 - KIDA A RUWA

09 Apr 2026

1102

ƴar sa'a ce kam Sir. Abinda ma zai saka ka farin ciki shine, duk abinda muka nuna mata tayi na'am da shi, damma bata san waye ke aureta nata ba”.
      “Wannan ai shine babban makamin mu a kanta, shiyyasa nace kada ku faɗa mata waye mijin, taje ta bincika da kanta. Yaya batun yaran?”.
     “Duk sun bamu haɗin kai. Sannan da yawansu ta tuna fuskokinsu”.
       “Good. Sai mu je Batch B. A sanar da kowa akwai meeting gobe da safe.”
     “Okay Sir”...........✍️
[14/02, 7:48 am] null: KIƊA A RUWA 3

7

........★9:pm★
   
     Sai a wannan lokacin Dada da Faro suka sami damar ganin Imran. Duk da tun ɗazun ya farfaɗo allurar da sukai masa ta saka shi barci ya saka sai yanzu aka basu damar shiga inda suke. Duk da daga shi har Nimrah sun kawo su wani sirrintaccen asibiti ne.
          Kalma ta farko da ya fara furta musu shi ne, “Ina Nimrah?”.
       Murmushi Faro yayi da faɗin, “Relax Colonel. Ɗiyarka na nan lafiya lau Alhamdullah. Duk da itama muna jiran ji daga doctors ne akanta amma in sha ALLAHU komai mai sauƙi ne, bakaga mijinta na tsaye kan ƙafafunsa ba”.
      “Alhamdullahi”.
    Ya sake faɗa a hankali yana kallon Dada daya zuba masa juyayyun idanunsa. Murmushi kwantar da hankali ya sakar masa. Sai kuma ya motsa a hankali zai tashi. Fuska ya yamutse da saurin kai hannu saman kansa da yay masa nauyi. Riƙe san da yaji anyi ya sashi buɗe idanunsa daya lumshe. Akan Dada ya sauke su, dan shine ya riƙe san.
          Hararar da Dadan ya sakar masa ta saka shi yin murmushi. A hakanli ya furta, “Miye na hararata?”.
      “Gaggawar ta miye?”.
    Ya faɗa yana maida shi ya kwantar. Sai kawai Imran ya sake yin ɗan murmurshi. Koda ya sake jeho musu tambayar miya faru da batun tashin bomb?.
         Kaɗan Faro ya masa bayani dan ya samu nutsuwa. Sauran yace sai ya samu lafiya. Dada dai na tsaye yana saurarensu. Sai dai ya zubama Imran idanunsa cike da yanayi na damuwar halin da yake ciki, dan ji yake kamar ya ɗauke ciwon daga jikinsa ya maido nasa jikin. Motsin da wayarsa tayi alamar shigowar kira yasa ya ɗan ja numfashi ya fesar. Batare da yayi magana ba ya ciro ta a aljihu.
      Ficewa yay a ɗakin cikin muryarsa data koma ƙasa sosai alamar gajiya, dan rabonsa da abinci ma tun safe. Shima ba wani breakfast ɗin kirki bane ba. Normal black tea ne da dafaffen ƙwai uku.
Daga can Mammah tai ɗan tsai tana sauraren gaisuwar da yake mata, sai dai maimakon amsawa tambaya ta jeho masa.
       “Yana jika haka? Ko akwai wata matsalar ne?”.
      Sai da yay ƙaramin murmushi daya tsaya masa iya lips kafin ya ɗan sauke ajiyar zuciya. “A'a kawai gajiya ce Mammah....”
       “Da yunwa kuma ba. Tunda kai da abinci maƙiyan juna ne Muhammad. Yanzu dai ga su Bilal nan zasu kawo muku abinci. Dan naga alamar ba sallamoku zasuyi ba a yau ɗin nan. Kai kuma ka hanamu muzo, gashi kowa ya ƙagu yaganta”.
         Yanzu kam murmurshin sa har sai da ya bayyana akan fuskarsa. Ya ɗan zubama ɗakin da Nimrah ke kwance idanunsa. “Ba hanaku nai ba, kawai dai yanayin aikin ne a haka. Suma su Bilal ɗin su bari zan turo Dabo ya amsa abincin”.
     “Muhammad kodai wani abu ya samar min Nimrah ne kake ɓoye min?”.
           Yasan za'a rina. Dan tun bayan zuwansu asibitin yay kiranta ya sanar mata suna asibiti amma bawani damuwa firgita ce ta sakata suma amma basai sun zo ba saboda yanayin tsaro. Amma sai da yaji Mammah ta jinjina kamar dai bata so ace kar su zo ɗin ba....
      “Muhammad!”.
  Ta faɗa cikin sanyi dake bayyana damuwarta. Iska ya ɗan furzar da gyara muryarsa, cike da kulawa yace, “Mammah ki kwantar da hankalinki. Babu wata damuwa. Da acema ba barci take ba da tuni na haɗaki da ita. Amma in sha ALLAHU zuwa da safe zasu sallameta. Idan basuyi hakan ba zanzo na ɗaukeki da kaina na kawoki”.
         Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi. “Shi ke nan ALLAH ya ƙara musu lafiya. Yaya shi Baban nasu?”.
     “Shima Alhamdullah, dan daga wajensa na fito ma ya farka.”
             “Masha ALLAH. ALLAH ya kiyaye gaba to. Ka aiko to a amshi abincin. Zan haɗo da kaya kuma ko zaku buƙata dan nasan Nimrah da ƙyanƙyami, kayan jikin nan nata na tabbatar sun isheta”.
      A hankali ya ce, “Uhmm”.
Daga haka sukai sallama Mammah najin nutsuwa. Suma da daren nan suka koma gida dan tunda Ruky taji anga Nimrah ta sake watsakkewa. Lailah suka baro da Ammie da taje zata zauna da ita...

      ★★★    Dai-dai yana katse wayar aka buɗe ƙofar ɗakin da Nimrah take. Ta ƙasan ido ya ɗan duba wajen, sai kuma ya janye lokaci guda. Dan duk ƙwaf ɗinka zaka ɗauka hankalinsa akan wayarsa yake. Doctor da ke fitowa Nurse a tare da ita ta rage yanayin ɗan hanzarin data fito da shi. Dan gaba ɗaya kwarjininsa ya cika mata wajen. Itama ba yarinya bace, sannan da aurenta, sai dai Dada ya girmeta sosai gaskiya. Tun ɗazun yanayin tsare gidansa da gizago yasa ya cika musu idanu. Dan irinsu Dada ko babu alaƙa, ko baka taɓa saninsu ba a gani ɗaya kamalarsu da cikar haiba ke siya musu girma ga mai kallonsu.
       “Barka ranka ya daɗe, dama neman ku na fito”.
       Baiyi magana ba, bai kuma kalleta ba. Amma ya janye wayar daga idanunsa alamar yana sauraren ta. Itama fahimtar hakan ya sakata cigaba da bayaninta kawai. Itako Nurse a kaikaice ta zubama masa idanu tanata tasbihi ga UBANGIJI mahaliccin wannan nutsatstsiyar halitta...
      “Ta farka, sai dai jikinta akwai zafi sosai, dole ko yaya a goge mata shi da ruwa mai ɗan sauƙin sanyi. Sannan akwai yunwa a tare da ita. Ga Nurse zata goge mata jikin yanzu sai abinda zata cin muke buƙata”.
          “Uhmm”.
     Kawai yace a taƙaice. Doctor data fahimci amsar kenan sai itama ta ɗan sake risinawar girmamawa tana barin wajen. Nurse kam da taso ita kam dai taji yayi magana sai taji kamar ta fasa ihu. Dole tabi umarnin doctor data bata na zuwa ta samar da abin zuba ruwan. Fin minti guda da wucewar su ya taka zuwa kofar ɗakin. Hakan yasa Faro daya tunkaro shi komawa baya kawai yana ɗan murmurshi. Shi ko Dada da bai gansa ba har ya shige...
       Yanda ta duƙunƙune jikinta cikin blanket ya sashi zubama gadon ido sosai. Ta rufe har kanta, sannan a dunƙule take waje guda. Hakan na nufin a tsorace take har yanzu, ko tana jin sanyi. Shiru kamar bazai ƙarasa ba, sai da kunnensa ya fara ji masa kamar tana jan shashshekar kuka sannan. Matsowarsa gaban gadon da ƙyau ya tabbatar masa kukan take kuwa. Maimakon yin magana hannu ya kai zai janye blanket ɗin duk da bai ma san ina kanta yake ba saboda yanda take a cure.
       Firgigit Nimrah ta zabura. Dan tana cikin wani yanayi ne na wanda abu ke dawo ma a rai. Cikin zafin nama Dada ya tarota, saboda yanda ta zaburan sai ta tafi gaba ɗaya zata wantsalo ƙasa. Ita kuwa batare da tunanin waye ba kawai ta cukuykuye shi a yanda yake a tsayen. Dan kanta ta kwantar a saman shafaffen cikinsa ta zagayo da hannayenta a bayansa ta matse tsamm. Da ace ragon namiji ne babu abinda zai hanashi jin matsar nan har cikin ƙashi. Amma da yake mazan mazan fama ne ko gezau, sai dai abin yazo masa a bazata daya tilasta shi lumshe idanunsa kawai. Fin minti guda suna a haka, zafin zazzaɓinta ya fara shiga jikinsa. Sai ɗumin hawayenta dake sauka masa akan riga har danshin na taɓa jikinsa, ga jikinta na ɗan rawa-rawa kaɗan, sai dai bai sani ba na tsoro ne kona jin sanyi...
       Kai tsaye Nurse da bata san da shi a ciki ba ta buɗe ƙofar. Sai da ta juyo bayan ta rufe tai arangama da shi. Da gudun tsiya taja ta tsaya. Lips na rawa ta ce, “Ka...k....”
        Wani mugun watso mata idanu yay da mata alamar tai shiru. Aiko kamar wata sokuwa tasa hannu ta dafe bakin nata tana risinar da kanta. A haka ta ƙaraso gaban gadon ta ajiye ƙaramin botikin hannunta na roba. Sai towel ƙarami shima sabo a ledarsa. Ta gefen ido take satar kallonsu da yin gulma a zuciyarta. (Uhumm lallai wannan ƴa na son Babanta. Kaga ƴar shagwaɓa. Ai dake zan kama ƙafa na samu shiga wajen wannan Barden mazajen. Dan daga gani kam ke ƴar lelensa ce...)
         Da alama dai Nurse ita tasan ma tana yi. Dan shi dai Dada na tsayensa har yanzu. Ga Nimrah ta masa ɗaurin goro. Shi kuma ya ma gagara yin komai, sai da Nimrah ta ɗan zabura har tana neman sakashi yin baya sannan ya ɗora duk hannayensa biyu a jikinta batare daya shirya ba. Ɗaya a gadon bayanta ɗaya akanta da ɗan kwalin ya fita. Sai dai akwai kitso ƙanana da suka mata ƙyau cikku dan tana son cikku sosai. Itama Nurse ɗin zaburowa tai kamar zata tare Nimrah ɗin duk da taga a jikinsa take amma da yake neman uwawun zama take itama sai tazo nuna bajinta.
Received at 10:47 AM     Yanzun ma kallo irin na ɗazun yay mata, dole ta dakata da gudu tana kai hannu ta sosa ƙeya tana jan jikinta baya. Shima daya tabbatar wannan yanayin zai iya saka cutuwa, a karo na farko ya furzar da iska yana shafa kan nata, ƙasa-ƙasa ya furta, “It's okay Babie” sai kuma ya kamata slowly ya maida saman gadon ya zaunar. Taƙi sakin hannunta dake zagaye da ƙugunsa, dole ya kai nasa hannun da kansa ya janye natan. Kuka ta sake fashewa da shi tana ƙoƙarin sake cusa kanta a jikinsa. Bai bari tayi hakan ba ya kai zaune kusa da ita. Sai kawai ta sake faɗa masa a jiki tana cukuykuye kan nata dai..........✍️
     
[14/02, 7:48 am] null: KIƊA A RUWA 3

8

.........Nurse data fahimci yanayin Nimrah ɗin cike da son birge shi ta zabura tana faɗin, “Yallaɓai bari na sanar da Doctor, dan kam akwai matsala a firgice take. Dama Doctor tayi magana ɗazun data farka akan ALLAH yasa kada ta shiga yanayin...”
       Yanda bai tanka ba a ɗazun yanzu ma hakan ne. Itama bata jira amsar tashi ba ta fice a hanzarce. Ai ko babu jimawa sai gasu sun shigo. Har yanzu kuma Nimrah ta hanashi ko motsi tsabar yanda ta cukuykuye sa. Dan zuwa yanzu gaba ɗaya rabin jikinta akan nashi yake. Cikin lallashi Doctor tai magana tana kamo hannunta. Amma sai ta fisge tana fashewa da kuka da sambatu irin na tabbacin bata cikin hayyacinta...
        Doctor ta rasa yanda zatai aikinta saboda yanda take jikinsa. Gashi maganar duniya Nimrah taƙi ɗagowa....
         “Miye matsalar?”.
   Dada ya faɗa yana ɗan kallon likitar a karo na farko. Sai kuma ya janye idanun nasa duk a lokaci guda. Itama ba iya kallonsa take ba, dan haka ta fara masa bayani yanda zai fahimta...... Da ga ƙarshe ta ce, “Yanzu akwai allurar dazan mata, in sha ALLAHU ƴan mintuna ne nutsuwarta zata dawo, dan har yanzu abinda ya faru bai bar brain ɗinta bane gaba ɗaya. Rashin tabbacin zata tsinta kanta a hakan yasa ban mata allurar ba tun ɗazu.”
       Bai ce komai ba, sai dai ya gamsu da bayanin nata, dan haka ya kama Nimrah da kansa ya ɗagota sosai. Tana mutsu-mutsu da son ƙwacewa dai akai allurar. Kusan a tare shi da Doctor suka sauke ajiyar zuciya bayan wasu mintina ganin Nimrah ta fara nutsuwa. Sai dai shi a ciki yay tashi, doctor kuma a bayyane. Knocking ƙofar da akai ya saka Nurse da Doctor kallon wajen, sai kuma Nurse ɗin taje ta duba. Dabo ne ɗauke da kaya, bayan sun gaisa ya miƙa mata kayan, ya ɗauki sauran ya nufi ɗakin Imran.
      Itama bayan ta ajiye kayan inda ya dace doctor ta bata umarnin gogema Nimrah jikinta dake sake ɗaukar zafi. Miƙewa Dada yay abinsa, dan tun da akai allurar ya kwantar da Nimrah gefensa yanzu ba'a jikinsa take ba. Sai da ya maida ƙofar ya rufe Nurse ɗin dake binsa da kallo ta ƙasan ido ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi tana nufar Nimrah. Murmushi Doctor tayi, sai ma taji Nurse ɗin ta bata tausayi...

÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷

Wani wawan birki Malam Buba yaja yana waro idanun mamaki ganin wanda ke ƙoƙarin tsaida shi. Duk da ya rufe fuska da handkachiff ga p-cap hakan bai hana shi gane shi ba. Wuff Dagger ya buɗe motar kuwa ya shigo. Ya furzar da iska mai nauyi yana janye handkachiff ɗin daya rufe fuska da shi...
       “Amma Oga wannan gangancine da mu duka zai iya sakamu a haɗari. Mizai sa kazo har nan anguwar, gari da haske kuma irin haka?”.
       Harara Dagger ya jefama Malam Buba kafin ya janye handkachiff ɗin da yake goge fuska yana gyara zama. “To faɗa min ya kake so nayi Mole? Tun randa ka kirani an ɗauke Nimrah ka sake nemana? Tsabar rashin mutunci ma waya ka kashe min gaba ɗaya. Jiya da shekaran jiya duk naje gidanka ance baka dawo ba. Sai da na kira Ari akan ya bincika min tunda na tabbatar bazai rasa huɗɗa da wani a gidan ba ya tabbatar min kana nan anan ma kake kwana. Mole mi kake nufi? Mi kake shiryawa? Ko Nimrah na hannunka?”.
        “Amma Oga wannan wace irin magana ce? Kasan dai duk wuya bazan ci amanarka ba, duk abinda zakaga nayi ina da dalili na, ko bakazo ba zan zo na kawo maka dukkan bayanai. Na farko dai kwana a gidan nima a gareni tilas ne, dan yarinyar nan Ruƙayya ce babu lafiya, sai kuma wajen jiyyarta ɗayar matar waɗannan ƙannen nasa ta faɗi akan ciki sai ta akai mata tiyata aka riro jaririn. Hakan yasa inata kai kawo na jigilar kai abinci da abubuwa. Sannan wlhy hankalina ba'a kwance yake ba, ina nane da su ko zanji bayanin an sami Uwa dan har yanzu mutumin nan bai sake dawowa gidan ba daga shi har Imran....”
         “Amma ba waya ya kamata ka kashe min ba, tunda nima ina buƙatar son jin abinda ke faruwa ko.”
Received at 10:47 AM
3 people reacted with     “Itama fa wayar ba kashewa nai ba oga. Wannan wawan Sanda ɗin ne ya ara ya shiga bayi saboda fitilar bayin ta lalace shine ya tsumbulata a ruwa, yanzu haka inda zan kai gyara nake nema”.
           “Mtsowww!”.
      Dagger yaja tsaki. Sai kuma ya miƙa masa hannu da faɗin, “Bani wayar.”
    Ba musu Malam Buba ya cirota ya bashi, Dagger ya ɗan jujjuyata a hannunsa sai kuma ya saka a aljihu. Wata ƙarama ya ciro ya bashi. “Ga wannan, daga yanzu na dinga sanin halin da ake ciki”.
       “Amma Oga ya batun Nimrah? Wlhy abin ya fara bani tsoro.”
    “Nima a tsoracen nake, dan itace rayuwata. Amma ina kan bibiyar iyayen yaron can da suka daka a makaranta satin daya gabata”.
       “Tsohon shugaban ƙasa fa naji ance”.
    “Eh su. Dan ina zarginsu gaskiya. Musamman matarsa bata da mutunci daman.”
       “To amma ta yaya Oga?”.
Wata dariya Dagger ya kece da ita. Sannan ya ce, “Humm Mole har yanzu kanka a tukunya yake kai kam. Baka san waye Dagger ba a ƙasar nan. Kodan kai kana ganina arhar banza ne. To bara kaji, wannan damar ina baka ita ne saboda Nimrah. Za kuma ka iya samun fiye da hakan. Kai dai bari na aureta”.
      Harga ALLAH sai da ƙirjin Malam Buba ya jijjiga. Har ya kasa dannewa cikin suɓutar baki ya furta, “Aure Oga?”.
         “Eh mana, ko bazaka bani ba?”.
    Dagger ya faɗa cikin tsatstsareshi da idanu. Yawu mai kauri Malam Buba ya haɗiya, zuciyarsa kuwa wani irin dukan take yi. Cikin rawar baki ya ce, “Ba..b...ba haka nake nufi ba Oga. Kawai dai naga ita ƴa take a wajen ka”.
      “A'a a wajenka dai, dan kai ka haifa. Ni masoyiya ce, kuma uwar ƴaƴana. Sai dai idan baka son bani”
     Yawu mai ƙauri Malam Buba ya sake haɗewa. “Oga ai kaima mai aurama wani ce. Kawai dai kasan ance wannan mutumin yana au.....”
      Cikin katseshi Dagger ya ce, “Oh kai harma ka ɗauki wannan auren aure? Shi jakin wace ƙasa ce zai aure ta babu iyayenta. Sannan ma wannan tsohon da aƙalla ma zai iya girmarka ne bakinka ke iya jinginawa da ƴarka. Jibeshi mutum a murɗe kamar ɗan damben turawa, dan ni banga abinda ya rage ba a zaman prison ɗin shiyyasa bamma yarda a can yake shekara takwas ba......”
      Sam Malam Buba ba jin Dagger yake ba a yanzu. Dan tsakani da ALLAH hankalinsa ya tashi. Ai koda rayuwa ta maidashi haka baya fatan yarsa ɗaya tilo ta auri mutum irin Dagger da babu sbinda ya sani a rayuwarsa sai mugunta da kisan kai. Ga neman mata kamar ɗan bunsuru. Tabbas baya ƙaunar Zak-Shadow, kuma ko zai rasa ransa wannan auren bazai bari ya tabbata ba akan ƴarsa. Amma kuma bazai so Dagger ya maye gurbin Zak-Shadow ɗin ba a rayuwar Nimrah. Dole ne yayi wani motsi a wannan gaɓar, kuɗin nan da su Oga suka bashi gida zai nema ya saya a wata ƙasa cikin maƙwaftan ƙasashen nan, ya ɗauke ƴarsa ya maida can, ya sama mata ma'aikata masu kula da ita, ya biya mata ta cigaba da karatunta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login