Showing 1 words to 3000 words out of 77938 words

Chapter 1 - KURUCIYAR MINAL COMPLETE

11 Jul 2025

3564

🏆KURUCIYAR MINAL🏆

1 - CHAPTER 1-10
🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by miss untichlobanty🌹

*🍀CHAPTER 1🍀*

Amina ce zaune a kan wani lotsatstsen katifanta Kamar an taka bredi,basai nayi magana akan
gadonta ba . Gefe wani kwano ne with a remained smelly stinky tuwo miyan kuka Wanda da
alama tunna jiyane bata fitar da kwanon ba.

kuka take rizga Kamar ranta zai fita
innace ta shigo dakin domin ganin Lafiya yau yar lelenta shiru bata fito ta kama aiki ba? Turus
tayi tana ganin ikon maleeku

Wani Abu na yar lele sai ita idan Ba haka Ba ya za'ayi mutum shi daya ya zauna yana kuka
babu dalili.

innarce ta rafka uban salati Kamar an kama malam da karuwa tace me zangani haka aminatu
Lapiya ? wa yatabo min tuwalle? me ya saki kuka?

Sai alokacin Amina ta dago ta soma magana cikin shessheka Kamar haka inna Dan Allah ki
yafe min,ki roki kanwata deejeh ma tayafemin,awararta Dana karba tayi hakuri,dukan da nake
mata ma na daina,kuma...kuma bazan kara zubar mata da abinci Ba kuma Wlh bazan sake
kwace mata rakenta Ba Nayi alkawari har naira 50 din tama zan biyata 😭 duk rashin mutincin
danakeyi Allah na dena Wlh na dena ta kara fashewa da kuka.

Galala inna tayi tana kallonta Wai yau aminatuwa ke Neman yafiya harda kiran deejeh
kanwarta, lallai za'ayi ruwa da kankara
Inna tace toh yar lelen inna yi shiru kisanar dani ya akayi?me ya faru?
Minal tace inna aradu mafarki Nayi Wai cutar laser fever ta kamani Wai na mutuuu!
Inna tace kinga irinta ai mutum ace sai shegiyar kazanta yaushe Rabon da Kiyi wanka Yanzu?
Kina ganin kin kyautawa kanki kenan ?
Kuka ta fashe dashi tace kwana biyar ne kacal fa.

Inna tace ko kunyar fada bakyaji? wannan Ba laser Ba har ebola ma zata kamaki ai.
Kuka ta kara fashewa dashi tana shure-shure tace haba inna dama Ba sona kike Ba ?
Kuma ai dukda bana wanka ina canja pant fah.😭

Inna tace ni rufe wannan bakin naki karki taramun makwabta gashi duk kin cikani da warin baki.
Tashi dallah kije ki wanke baki Kiyi wanka.

Kurma ihu tayi tahau shure-shure da burbuwa.

Nan inna ta lallabata tace mata ai mafarki Ba Gaskiya bane.... haka dai ta hakura nan inna tace
taje tayi wanka taci abinci Dan yau zata rubutar jarabawar karshe a makaranta daga shi next
term zasuyi WAEC haka dai ta hakura ta shirya.

Ta fito zata tafi tace inna kin Tina wannan 100 Dana taba aramiki?
inna tace yaushe? tace lokacin nan sanda muka fara jarabawa
inna tace na Tina tace ki Dan banishi,inna tace haba yar inna nawa na baki atsakanin wannan
lokacin?

Tuwalle tace ehheeeen wato dama badan Allah kika bani Ba inna ?!cabdi wallahi Nide sai kin
bani kudin nan.

Inna tace sarkin jaraba, kin fita naci Kamar me, ta since bakin zaninta ta miko mata wata
kodaddiyar Dari biyu tace ingo kuma kikawo mini canji domin shi kadaine gareni. Inna ta fadi
dukda ko tasan da wuya ta kawo chanjin.
Yamutsa fuska minal tayi kamin ta karba tare da Cewa dande ina bukatar kudin ne da yasin
bazan karba tsohuwar kudinnan Ba.

Nan ta rungumi inna Kamar da gaske sannan ta fita tare da Cewa sai na dawo sannan ta biya
ta gidan su kawarta zaliha domin tafiya makaranta.

Koda aka tashi Tara(break) tsallaka katangan makaranta tayi taje tasiyo gurasa a kasuwa na
duka kudin tayi sadaka dashi wa almajirai akan Allah ya kara rufawa iyayenta asiri

(dukda Cewa Amina akwai tsiwa da rashin mutunci ga Wanda ya nema amma akwaita da
tausayin iyayenta sosai domin kazantarta Nada nasaba da haka acewarta Idan sabulu da
turarenta basu Kare Ba ai iyayenta bazasu kashe kudi wajen siyan wani Ba shiyasa sau biyu
take wanka a sati su inna har sun gaji da mata magana)
Amina Yusuf yarinya ce er shekara 18-19 farace sosai ga hanci shima daidai misali 8 figure ce
ga tsayi daida gwargwado idonta ko sexy eyes ne gashin kanta kuwa ba'a magana.

Babanta wato malam Yusuf Wanda akafi sani da baban kowa carpenter ne bashida karfi amma
yanada rufin asiri sannan duk anguwar ana ganin girmansa sosai manya da yara.

Asalin sa fulanin taraba ne wadda yarasa kowa NASA sanadiyyar gobara tun yana shekara 18
haka yarike Kansa har yakai 25 ananne ya dawo kano da zama inda ya hadu da falmata wanda
ake kira da inna wacce take kanuriyar barno ce gyaran miki da turaren wuta take a kanon har
sukayi aure dagabaya suka Koma Kaduna da zama Inda suke can cikin malali ahaka har inna
ta haifi danta na fari wato Abubakar Wanda yanzu yake project a ABU amma shi yake rike
kansa domin ya ragewa iyayenshi nauyi sannan yakanyi musu aike idan ya samu hali tunda Ba

zaman banza yake Ba.

Daganan inna bata kuma haihuwa Ba sai bayan shekara takwas Inda ta Haifi Amina wacce take
yarr jagwal ce ga neman magana,ga tsiwa, saide matsoraciya ce na masifa amma ta rike
addininta dukda ko Ba ganewa ake Ba.

Sai daga baya inna ta Haifi khadijah wacce take auta kuma shekaranta 12.

Wannan kenan

Kubiyoni domin jin cigaban kuruciyar minal

26th April 2019

Love you all

Mzz untichlobanty💕
[1/11, 1:06 AM] Mzz_Untichlobanty💞:
*🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆*

🌹by miss untichlobanty🌹

*🍀CHAPTER 2🍀*

*BAYAN WANI LOKACI DA RUBUTA JARABAWAR MINAL*

*Morning*

Minal rike da sakamakonta a Hannu miftahu (kanin hannatu zamu ganta a gaba #chapter 8 )
yace manya manyan Yan boko har an karbo sakamakon kenan da fatan wannan karan ma ba'a
dauko ajinba. Cukumosa minal tayi ta naushi bakinsa tace aiko Ba Komai ni nane makarantar
wasu a yawon banza za'a kare. Daidai lokacin sani (yayan bilkisu itama zamu gantaa gaba
#chapter 8) ya wankawa minal mari juyowa tayi tace buhun bala'i bai ankareba yaga an nunashi
wa sama an nana da kasa suka minal tamai jina-jina sannan tasa yara sukabuleshi da kasa.

*Evening*

A guje yara suka rugo Suna oyoyo baban kowa oyoyo baban mu! dama ya saba Dan haka yasa
kullum baya rabuwa da tsaraba, hanjin ligidi mai yawa acikin bakin laida ya ciro ya basu suka
karba Suna godiya kamin suka raba, wata yarinyace tace baba yau wani tatsuniya zaka mana
yace tatsuniyar gizo bakin barawo zan muku. Lado ne ya shinfida masa buhu Kamar yadda suka saba sannan Suma yaran suka zazzauna
nan dattijonnan ya soma musu ta tsuniya......

🌹.............

Wasu samarine zaune Suna busa sigari wayan dayansu ta soma kara daukowa yayi yaga karfe
alarm dinsa na large hudu ne take ya kashe sigarinsa yace kai yau fa alarm NASA mana aradu
lokacin dawowan tsohonnan yayi,dariya suka fashe dashi wani yace Ba mamaki ya tsaya yiwa
yara tatsuniyane. Sukace Ba shakka amma fa tsohonnan yana yiwa mutane cikas ka duba
abinda yar b*ra ub*an yarnan tasa tayi dazu.
Daidai lokacin baban kowa ya karyo kwana,a take suka karkade jikinsu tare da wulla alewa a
baki Dan kar yaji warin sigarin tasu.

Nufosa suka farayi Kamar abin arziki shima da murmushinsa yaje nufosu domin yaune karo
nafarko dabai kamasu Suna busa sigari Ba.

Saide kash suna motsowa kusa dashi ya jiyota aiko take annurin fuskarsa ta dauke sukace
babanmu sannu da zuwa Suna masu durkusawa

bata rai yayi yace Duba su Kamar da haske Kamar mutanen arziki, Wai Ku fi sabillilahi bazakuyi
wa kanku fada ba, Kamar da gaske nadau kunyi hankali Ashe da sauran Rina a kaba,

Bakusan cewa wannan shaye shayen naku yana janyowa iyayenku Bacin sunaba?ko kunaso
duniya tazagesu ne?girgiza kai sukayi sukace ayi hakuri baban mu Insha Allah zamu daina.

murmushi takaici yayi domin Indai wannan alkawarinne to an karyasa tun kafin adaukesa yace
Allah ya bada ikon dainawan,kuna batawa kanku rayuwa ko bakusan Cewa duk abinda mutum
yayi yana kuruciyar shi zai bishi har girma ba ko kunaso idan kun hayayyafa acewa yaranku kun
taba busa wiwi ?girgiza kai sukayi yace Idan yaranku suka sha Ku ya zakuji hada baki sukayi
wajen Cewa bazamuji dadi ba yace Idan Baku sani bama Ku sani wannan shaye shayen yana
haifar da tabin hankalin,lalacewar koda da zuciya kuma tsaf zai kashe mutum. Ku a haka zaku
hadu da Allah? Kuma kuna tunanin Idan an tafi a haka ba matsala?Ba Arabic Ba bokon?Allah
ya Shirya....

Tafiyarsa ya cigaba dayi yana mai fada akan yadda matasa ke bata rayuwarsu.

Majalisar su malam yakubu zai wuce sukace salamu alaikum baban kowa barka da war haka
murmushi ya soma musu sannan ya mika musu hannu sukayi musabaha.
Malam isa mai wankin hula ne yace ya naganka haka ne ? baban kowa yace kaide bari yaran
yanzu basu rabuwa da kayan bakin ciki yanzu na.....

Malam saminu ne yazo yana girgiza kai alamun alajabi jikinsa a sanyaye ya zauna
Baban kowa yace haba malam saminu ya haka zakazo ka zauna bako sallama? inkai kayi haka
'yan'yan mu kuma yaya zasuyi ?

Malam saminu ne ya cire hularsa ya ajiye kana yace wato wani abune yayi mugun jijjigani, Wai
yar gidan malam ado salma akayiwa fyade saboda sakacin maihaifiyarta. fita tayi bayan
magariba ba'a saniba uwar kuma da bata ganta Ba bata nemeta Ba sai da taga kusan goma ya
wuce shine ta Sanar da malam adon. neman duniya an mata ba'a ganta Ba yau da asuba aka
yadda ita koda aka kaita asubiti likitoci nata kokarinsu amma ina. yanxu yanzunnan rai yayi
halinsa,Allah ya mata rasuwa!

Shiru wajen ya dauka kamin caaan malam sambo Wanda tun dazu baiyi magana ba yace Wai
salma dai guda Dana sani yar shekara 6?itafa wannan salmar dai inji malam saminu
Salati suka rafka jikin kowa yayi mugun sanyi kamar an musu duka.
Allah sarki salma yarinya mai hankali da Shiga rai. Allah yaji kanta bari anjima sai mu hadu
muje muyi masa ta'aziya nan dai suka Dan tad'a kamin malam Yusuf yayi gidansa.

Koda yake tafiya a hanya sai surfo masa gaisuwa ake ta ko'ina manya da yara. Atakaice de
baban kowa mai jama'a ne.

Yana isowa kofar gidan sa, basheer mai shago yace baban kowa ina wuni,Lpy klau basheeru ya
shagon?basheer yace Alhamdullah baban kowa yace masha dafatan dai yauma minal bata
taba kowa Ba Dan yau da safe tace Mani Wai tun jiya akace suje su karbo sakamakonsu.
Basheer yace Gaskiya baban kowa yau minal bata yi hayaniya da kowa Ba hasalima ko
fitowanta bangani wadda nima abin ya bani mamaki da alamu dai kawattamu ta natsu(haka
basheer din ke kiranta domin ya kasance abokin ya abubakar ne tun yarinta shiyasa ma yayiwa
baban kowan karya Dan kar yasa wa ransa damuwa sosai)
Baban kowa yace to Masha Allah haka akeso ai ni bara in Shiga Daga ciki ko? Allah yayi
albarka basheer yace amin.

Minal na zaune tana yanka kubewa taji sallamar mahaifinta hantar cikinta ne ya kada da gudu
ta mike har tana tuntube a 360 ta fada daki,garin sauri ta barar da yakuwar da take yankawa
innace ta haba er lele lafiyarki kuwa zaki barar mani da......

Bata ida maganar ba baban kowa ya shigo yana cewa inata sallamma Baku amsa ba Kamar ba
kowa a gidan inna tace yi hakuri malam sannu da dawowa Wlh wannan yarinyarnance ta fada
daki da gudu har tayi Mani bari banjika ba yi hakuri bara na kawo ma ruwa
Takalmin sa ya cire ya zauna a tabarmar dake shinfide a tsakar gidan yana Cewa halan
wayanta aka kira take wannan gudu , inna dake shirin bude randa domin sachet watern su ya
kare tace anya kuwa?hira fa muke daga jin sallamarka ta rusa da gudu Kamar taga aljani,baban
kowa najin haka jikin sa yayi sanyi bayason irin faduwsrnan da yarda keyi a makaranta domin
Hanson tayi karatu ta inganta rayuwarta

Yace takarbo sakamakon jarabawar tasu kuwa inna tace eh ta karbo dazu gasucan yana kan
yana kan taaga(window),tashi yayi jiki babu kwari ya dauko ya Duba aiko Kamar yadda yace ne
ankuma na 48 tazo acikin su 52 a Dan fusace yaje kofar dakin yace aminatu me kikeyi acikin
dakin nan,minal tace Riga make canjawa yace inba so kike na Shiga Ba maza ki fito tace baba

aradu Babu Riga ajikina wanka make shirin yi yace Kamar da haske rabon da Kiyi wanka keda
kanji Ba tare da dance Kiyi Ba yanzu shekaru 6 kenan amma shikenan ni bara in dubo sakona
waje.


Oya show some love
By voting,
liking,
sharing
and
commenting

Tnxs for reading

26th April, 2019

Mzz untichlobanty💕
[1/11, 1:09 AM] Mzz_Untichlobanty💞:

*🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆*

🌹by mzz_untichlobanty🌹

*🍀CHAPTER 3🍀*

Sanda ta kara kusan 5min sannan ta leko da kanta duk ta hada gumi saboda rashin gaskiya

Saukan rankwashin da tajine yasa ta sankare a wurin na wani sakanni.

Durkushewa tayi a wurin tana tutturo baki kamar zai taba kofa.
Baba ne yace rufi min baki kamin in kara miki,maza tashi.

Mikewa yayi tana zuzzunburewa tace haba baba ko Dan wannan rankwashin da kake samani
kamar abinci Ba dole na KASA kokari Ba kana taba min CPU na bakasan Cewa itace
masarrafin Dan Adam ba?

yace yimin shiru kamin in da'da maki wani yar kaniya kawai,me kwakwalwar kifi Allah dai ya
bude maki wannan toshesshiyar kwakwalwar taki.

kuka ta fara yi tana buga kafa ni Gaskiya baba kwakwalwata ba a toshetake baaa😭 inna tace
ni yimin shiru karki taramin makwabta ehe.

Murya ta kara baba yace bari kiga ikon Allah mikewa yayi ya dauko sanda.

yanda Kasan Anyi ruwan sama an dauke tsit ta shanye kukan da takeyi tana tsitstsilla idanu
tare da sheshsheka baba yace banson jin sheshekar nan. Ki natsu bari inga tsiyar da kika
shukowa mutane wannan karan.

Mutum bashida aiki sai fada ni Nayi mamaki ma yau kusan sati 2 ba'a kawo kararki Ba.
Turo baki tayi duk yasha mai sai yalki take tace yo ai dannayi mafarkin na mutu ne kuma ko
yanxu ma Ba fasawa nayi Ba.

Kallonta baba yake har ta ida maganan ta already ya Ciro takalmi Dan haka ya lafta mata.

papers din ya fara dubawa yaga  subjects 2 ne takeda A amma saura Wai sai a slow saide
rubutun nan war inka gani zaka dauka wata Dr ce tayishi sai ka karantawane kaji Kamar kayi
kuka.

takaicin rashin kokari na diyartasa abar kaunarsa ne ya taso mai.

Kansa  kawai yake girgizawa saboda takaici bazai musaba Idan akace masa Dan primary five
ma yafi yar tasa kokari.

Tsawa ya daka mata ke zonan !
Simi simi taje ya kalleta sannan yace yanxu ke ahakan zaki tafi makarantar gaba?ki Duba fa
gododuwar banza da wofi. Murmushi tayi
inna tace Allah zanci mutuncinki ana miki fada kina dariya saboda kin daina mutane ko? Tace
Toh Toh Toh ni inna me Nayi ? Dakuwa inna ta mata tace kaniyarki kikayi

tace to yi hakuri bazan kara Ba shikenan aiko?yauwa inata Dan Allah ki siyan awara?harara
inna ta banks mata tace ba'a siya dinba
Baba dake jinsu  ya tattare takardun yana cewa ace mutum anmai repeat har sau biyu amma
bai gyara ba nasan duk ajin keda zaliha kun fisu girma amma kanku Kamar kifi har gara ita
akanke.
antara dakikai biyu a aji daya bakuda aiki sai ciye ciye kuma da kunada kokarinku tunda kuka
fara Hulda da wannan fatiman shikenan lamuranku ya tabarbare.

tace toh Ba kai kake Bani kuddin Ba? Kuma ai fatimamma sun Koma kano.

Yace au haka zakice?

Inna tace kaga malam rabu da ita kar hawan jininka ya tashi
Mika ma innatakardun yayi yace jeki ajiye min adakin ki Dan in ina ganinsu takaici ne zai
kasheni

ni inanan ina fafitikar biya miki WAEC kan arufe amma naga alama asara zanyi

Zama kusa dashi tayi ta Washe baki tace baba kawai ka barni in fara aiki a gidan abinci Dan
Gaskiya ni karatun bokonnan sai a hakali bazan maka karya in batama lokaci da dukiya ba
yasin dakyar in zan hada ko credit 4 me kyau a wannan WAYES din
Yasin Gaskiya kake fadi kwakwalwartawa a to she take nakifinne maganarka Ba karya.

Abin yaso bashi dariya amma sai ya Girgiza kai

yace ai ga irintanan ana WAEC kina WAYES dubaki ko ajikinki Yan ajinku zasu makarantar
gaba amma ke oho ko ?kinacewa inbarki Kiyi aiki a gidan abinci

Bakiji abinda ya faru da salma Ba ko 'yar gidan malam ado ?tana gidan ubanta ma ba'abarta Ba
balleke budurwa kin tallata kanki a gidan abinci
Nan ya labarta musu abinda ya samu salma sannan yace Suma suje suyi ta'aziya.
Inna kam salati take harda kwalla tace kai duniyar nan Ba imani.

Minal ko mikewa tayi tana bubbuga kafa tace Toni baba idan ma bazaka iya barina inyo aikin Ba
kawai kamin aure ka huta
Ai da gudu sukayo kanta ba shiri tayi waje tare da Jan mayafi akan igiya.
Baba yace da shegiyar kazanta ma wa zai soki?ja'ira yar kwal uba
Inna tace abita da addu'a da fata na gari kawai.

🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀

Wakarta takeyi tana tafiya ta hango murtala da wani abokinsa mai kawo masa ziyara babba
yake kowa?waishi a dole Santa yaje. Zukar sigari suke Suna busa abarsu.

Tsayuwa tayi a wajensu tace anya murtala kanada hankali kuwa kullum kayita busawa 'ya'yan
hanjin ka hayaki Kana biyewa wannan sha katafin?

Dariya ya bushe dashi kamin yace minal kenan ai na Fiki  hankali ma. Babba yace ke yar shila
karki kawao mana raini Anan fa ko kinga sa'anki ananne?

Bata kulashiba taci gaba da yiwa murtala magana da tayi:
Dalla tafi can wallahi baka isa ba kayi kadan.

Kaikuma ta nuna babba da yarda kama daina nuna ka sanniwata kila ma sanadinka ne samari
basa kulani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login