Showing 42001 words to 45000 words out of 115153 words

Chapter 15 - DANGIN RABI COMPLETE

13 Jul 2025

4340

Amma Ni sabo da bana jure yunwa kamar yaki Haka nake ci,in cinye wannan in shanye wancen,duk abinda Fu'ad yaci ya Kara ragewa Haka Zan dauke na Kara dannawa ciki na,Su Hakeem suyi ta min dariya,Islam yace shi yasa kullum buleliya kike Zama kina ta cika gaki har kin Zama Yan Mata sai Aure Wanda ya aureki ya Dace,kalarki bakwa tsufa, Fu'ad ya Harari Islam,Islam yace sorry Babban Yaya na manta na Yaba maka Mata,Ai sai Fu'ad ya dinga bala'i shi ba matarsa bace,Ni dai Ina cin Dankali na nace Kai kudi sunyi a rayuwa dole Iya taso kudi Ashe Iya ta Gama gano kan kudi,Yanzu Fadila ma tana can tana soye soyenta,Iyata Allah ya Baki halin yin soye soye kema,aka dinga dariya har su Khaleesat naji girki harda tuno da Fadila,na Bude farfesun kaji nace to jama'a su Fadila ko Ana can Ana soye soye ko Kuma Ana ta fada da Miji Bata iya girki ba,nasan ma tana can tana ta shirga Masa kwaba a gidansa,wlh ayi Sauri a Kai Mata me Aiki kar ya sako ta da wuri akan girki kadai ya Isa a koro Fadila bare sauran munanan Halayenta,wa ya sani ma ko yanzu Mari ta Sha Guda Uku oho,Momy ta jefe Ni da takalmi karya kike Munafuka,Abbi Basu San me akeyi ba, Fu'ad Yace dazu da Rana a kasan tiles kika kwanta kina ta birgima Akan kina Azumi ko magana bakya Yi,Makarantar safe data Yamma duk Baki je ba Akan Azumi Amma yanzu an Sha ruwa kinfi kowa surutun masifa.

Nace Ina ma da Iyata yanzu Muna mutunci da sai na Kira ta naji wacce wainar take toyawa ita da Ali Shagali me shayi,au bakwa ma mutunci kika ce?Muna magana su Momy suna gulma mama Tace kinga suna Hira shegu,Momy Tace Ina kallonsa Yana ta wani kashe Mata Ido daya da alama yau tare zasu kwana Dan Kira yake mata.
Ni kuwa ban sani ba naci gaba da surutu na nace da gidan talakawa ne da yanzu Mata Ana ta kishi Ana masifa da bala'i har makwafta Ashe kishi ma an fi Yi a gidan talaka,Kai tsiya tana gidan talaka,Amma Nan kowa da kudinsa Ina ruwan wani da wani,Habaici na fara yiwa su Momy Ina Waka nace Alhmdllhi naci na Sha yanzu ko me za ai ayi,gida Ana Zaune lfy akan Yar yarinya an hargitse Ana ta yaki Ana kashe Kudade Ana tashin hankali,Allah ya Zabeni, Waliyiya Rumaila,na zama Waliyiya,Mikewa Fu'ad yayi yace ke kin dameni wlh bana son surutu dazu bakya iya cewa komai an Sha ruwa kin Dame mu,Nima binsa nayi nace ai har Kai a Sel fa ka kwana sabo Dani,ka Mari su Fadila ka murdewa Khaleesat hannu sabo dani,ka bini Sel lailahaillallahu Kamar Fu'ad a Sel sabo da Rumaila,kuma ka bada kudi, wayyo Ni... Na kyalkyale da Dariya nace ka bani abinci a Baki Ashe kana da tausayi Kai mashaallah,Ahhh Baki Ahh bakin Subhannallahi,Allah so na kake Yi Kawai gwara ma ka fada min ka huta,ko sai Watarana idan ba kowa sai ka rada min kace Kawai Ina sonki , Fu'ad Yana tafiya Ina ta Shan gabansa Ina surutu.

Yanzu Ya Fu'ad cinya ta da laushi Sanda ka kwanta? Dariya ce ta kamashi na takura Masa gaba daya,Yana Dariya yace kamar dutse Ni Azumi nakeyi Ramadan ban San wani laushin cinyarki ba,Zan sake magana ya fisgo hannu na zai min mugunta na kwace da kyar na gudu na barshi Nan Yana ta Dariya.
Yace Allah ya kawo wani abu ya sameta bazan sake ceton ta ba tunda yanzu na zama abin tsokanarta har tana ji da kanta Wai Ina sonta,har ya koma bangarensa idan ya tuno sai ya kama dariya shi kadai.

Haka tare muke Shan ruwa,Tarawi ma duk Muna zuwa,tahajjud tazo idan Muka tafi sau da dama ba a gamawa Dani bacci zai sa na gudu gida,sai yaga Ana fitowa Dani baya ganin Ana komawa Dani yasan guduwa nakeyi,kullum Ina karatun Boko Dana Addini na goge sosai na waye haduwa da kawaye duk na canja Nima na rage wani Haukar Kauye.

Ranar da za ayi azumin karshe zobo na hada lafiyayye me kauri yasha pineapple da Banana a ciki yayi dadi matuka,Muna Shan ruwa yau ma Ina shimfidar Fu'ad na zuba Masa a glass cup ya dauka banyi zaton zai Sha ba ya kurba ya dago da fuskarsa Muka hada Ido ya Bata Rai ya balla min Harara yace da tun farko kin San kin iya wannan Dan mugunta sai da kika Bari an Kai last Ramadan an Gama Zaki fara hada wannan,Dariya nayi da farko nayi zaton Bai Masa dadi bane,Abbi na kaiwa a juck ya dinga Santi,Su Islam ma na Basu Amma su Momy da yaransu suna kallo Ana ta Sha Ana dadi nace ku kuyi Hakuri bakwa kaunata Nima bana kaunarku baza kuji dadi na ba Sam,Safna Tace zobon banza wa zai Sha kazantarki,nace Nima bazan baku ba,baza ma Ku Gane kurenku ba sai na zama Antynku Nan gaba zaku sani,Kuna kallo dangina zasu zo suyi ta wadaka da kayan Dan uwanku ku kuwa sai dai ku zauna a palon Baki ko kitchen Dina baza ku samu matsayin shiga ba,sai dai ku hango su Rukayyatu Yaya ta da kannena su Basira da Basiru a kitchen suna ta dafa Indomie da kwai ku kuwa sai dai mu gaisa na koma daki na barku a Palo ku bushe anan ko ruwa baza ku samu daga wajena ba,Kuma Yan uwana su dinga saka super super ku kuwa sai dankwali irin na tsofaffi me Asabari,
Dariya aka dinga Yi Banda su Momy da su Safna,Abbi yace Rumaila kema tsokanar fada ne da ke kullum sai kin kulasu ki kyalesu Haka nace magana ta wuce Amma kinfi so kullum ki tsokane su,Dariya Umma tayi tace ai Wasa takeyi itama ba aikatawa zata Yi ba...Inji uban waye wannan muguwar aikatawa zatayi Mama ta bada Amsa Kai tsaye.

Duk an Mana dinkunan Sallah sai abinda ka gani Kawai kala biyar na samu, Fu'ad ya min kala biyu,Abbi ya Mana da Yan gida kala biyu na samu Umma ta Kara min wata Arabian gown ta zuwa Idi,kala biyar takalma na kala Uku da jaka kala Uku da mayafai kalar kayan Guda biyar,Inner wears sababbi kala kala,harda kana Nan Kaya wata na yo Order daga Dubai masu shegen kyau Umma tasa na zabi kala hudu ta siya min,na makalewa Fu'ad sai da ya bani kudin kayan kwalliya dubu goma da kaina naje na siyo har da wasu rigunan Yan kanti na Karo abina.

Washe gari Idi masu Aiki tuni gida ya dau kamshi yasha gyara na musamman, kowa yaci wanka Muka tafi masallacin Idi Allah yasa Bamu da nisa, Fu'ad da abokansa Suka shigo wajen su bakwai palon Umma a Nan zasu ci abincin Sallah,fitowa nayi na shiga kitchen na fito da nama a plate Ina Kiran Yar Aiki Tasalluwa Ni tuwo zanci ki kawo min Ina fada na zauna a palon Mazan sai kallo na suke yi,na gaishe su suka amsa, Tasalluwa ta kawo min tuwon shinkafa miyar Egusi na karbi tuwon nace ke Tasalluwa me Zan gani Haka Sallah guda wannan dan tuwon kamar tsaiwar wata shi Zaki kawo min,kin San fa bani kadai bace mu biyu ne ya kike Haka ne sai kace wata bakar kadara Baba Jummai,ai a Yan aikin gidan Nan ba kamarki ko Sarkin Izzar gidan Nan Dole sai ya iya cin girkin ki,Haba Tasalluwa Uwar tuwo,tuwo da Miya sai Tasalluwa.,Tasalluwa tana washe baki ta Karo min tuwo Leda Uku na karba na tafi dakina Ina cewa ki sa Abula ta kawo min ruwa da lemo da Red Apple Guda biyar.
Fu'ad a ransa yace Bari Baki su tafi tunda Habaici kike min Zaki sani,su kuwa abokan sai Dariya sukeyi Wai Dan tuwo Kamar tsaiwar wata.










Masu Sharhi Kuna birgeni Ina Jin dadi Kuma Ina godiya.







AsmaBaffa
🎈🎈🎈🎈
DANGIN RABI
🎈🎈🎈🎈






FREE PAGE








DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM






NA KUDI NE

GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE.


ACCOUNT NUMBER
0175487861,ASMAU GARBA MUHAMMAD GTBANK

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER
08033933642

'YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39










31-35








Official









By
AsmaBaffa









PAGE NAKU NE

Ummy Manga
Momyn Sultan
Rukayyatu
Maryam














Bayan Na shiga Bedroom Dina cikin abokan Sayyeed yace gaskiya ta hadu tunda na taba ganinta a gidan Nan nake sonta Dan Allah Friend kayi min hanyarta ko na samu na fita a gwaurantaka, Tsaki Fu'ad Yaja yana Danna wayarsa,na fito na fito na Manta Umma tace karbo Mata wasu flasks a kitchen,na fito a kitchen Na tsinci Muryar Fu'ad yace Ke Ina Ummata? Nace banji me kace ba na karaso kusa da shi na duka Ina tambaya me kace,Tsaki Yaja yace Umma ta nace,Oh tana can taje karbo dinkunanta da Suka rage,a hankali nace kayi kyau,Bai kula Ni ba.

Masu aiki ne Suka cika musu gabansu da kayan Alatu suna ta hira,kunya ta kamani Ni kadai tashi nayi tsam na shige bedroom da kwanon Abinci na,Ina tafiya Hakeem da Adam suka shiga yabon kyau na da hankali na,Hakeem yace Ina sonta idan Zaku bani Dan Momy da gaske nakeyi irin kalata ce,Sayyeed yace ai na Riga ku, Adam yace Nima Haka Ina ciki, Fu'ad ya kalle su yace to tana da aure matar wani ce ciki ma gareta mayun Mata sai a ajiye Zalama gefe,Hakeem yace waye wannan yayi min shigar sauri ya Gama Dani wlh,Tsaki Fu'ad yaja yace Allah ya shirye ku da son Yara irin wannan in Banda shirme da hauka me irin wannan zata maka ta birge ka,ai ka nemi babba wacce da kadan ka girme ta wacce tasan ya kamata me Ilimi,tasan jiya ta San yau kaga love,Amma irin wannan yaran in Banda hauka me zasu Yi maka,kana magana tana cewa sai ka rantse zata yarda komai sai ka koya Mata Amma idan ta mallaki hankalinta to Ka Gama dacewa kawai.

Suna jinsa sun San Halinsa suce ba daidai ba ayi fada sai Suka barshi,Hakeem ne kadai yace Kai Dalla baka San Mata ba bazan tsaya jayayya da Kai ba,Umma ce ta shigo cikin Wata arniyar Shadda tana kwala min Kira na fito Ina tsotse miyar Dake yatsu na,Je ki shirya aikenki zanyi gidan kawata Hajiya Haule,to nace na koma bedroom,Wanka na sake sallawa nasa Atamfa ta Golden and black,dinkin Riga da skert sun kamani Surata ta fito,kayan Sallah kenan nayi Daurin Yan birni me kyau,na shafa powder tare da zizara tozali kadan na shafa jambaki maroon,Na daura agogo da sarka ta na fito Shar kamar rainon birni,Takalmi na Half cover na saka Golden da mayafi da Jakata Golden na fito Ina kwambo,Umma ta kalle Ni tayi Murmushi tare da Furta kinyi kyau nace na gode,Mazan Nan Suka bini da kallo yuuu Banda gogan waya yake latsawa,Kaya ta bani a Leda Tace gashi idan kinje kawai ki Bata munyi waya tasan Zancen,to nace ta bani kudin Taxi na tafi Zan fita kenan na tsinci Muryar Fu'ad me shegen Dadi yace

Ana ta kidnapping a Gari Gashi yanzu na karanta a News an sace mutane Saba'in a kusa da layin unguwar Nan Bayan anyi batakashi da musayar wuta da Yan Sanda,Umma tayi tunanin gaske ne sabo da yanda kullum bashi da abin ji sai Labarai,Tace Innalillahi Kai Dan Allah? Fu'ad yace sosai ma yanzu Haka Sojoji ne ko Ina,Nan take Umma Tace ke Rumaila dawo na fasa Aiken hanyar lafiya a bita da Shekara Bari na bawa Driver ya Kai,Nace Umma Ni dai zanje Allah ya kiyaye,Umma Tace to jeki Allah ya tsare.

Fu'ad yace an dakatar da masu taxi ance yau Kar a ga me Taxi a hanya,Kai wannan Bala'i na kasar Nan da me yayi Kama Wai da me zamu ji ne haka,Dagewa nayi Ni sai naje sabo da yawo nake so Naga Gari nima,da sauri na tafi abina tunda na fita normal naga Gari ba abinda ya faru,Address din da Umma ta bani a takarda shi na mikawa Drivern taxi ya karanta,har kofar gida ya kaini wani katafaren gida shima ya gaji da Haduwa,Masu gadi Basu tare Ni ba Suka Bude min,Mutum Daya na roka ya rakani har Palon Hajiya Haule, wani matashi ne wankan tarwada Kyakyawa zai Kai sa'an Fu'ad Yana kwance a kujera kannensa sun zagaye shi suna hira.

A mutunce Suka amsa min sallama Muka gaisa,tunda na Shiga Matashin ke kallo na Kamar Maye,Hajiya Haule tace sakon Umman Fu'ad ce ko?nace ae tare da Mika mata ledar,lemo aka kawo min da snacks ga fruits a gefe,Matashin ya kalle Ni yace ki ci Mana bakuwa,Haka na Dan tsakura na mike Zan tafi Hajiya Haule tace Anwar je ka Mika ta gida ba sai ta shiga taxi ba,murna ta kamashi ya mike da sauri tare da cewa taso muje,Lafiyayyar motarsa baka na shiga gaba,Duk kunyarsa ta kamani sabo da yanda yake Bina da mayen Kallo.

A bakin gate din gidan ya tsaya tare da Danna Horn Nan take gate man ya Bude gate har ciki ya Shiga tare da yin parking,Na balle murfin Mota Zan fita yace Ban San sunanki ba? Rumaila na furta,wayarsa me tsada ya Mika min tare da Furta sunana Anwar please sa min number dinki,Ban karbi wayar ba nace saka Bari na fada maka,Yana wani murmushi ya shigar da number wayarsa mukayi sallama ya wuce Ni Kuma na wuce part din Umma,Da sallama na Shiga na Iske ba kowa ciki sai Naila tana kwalliya Fu'ad Yana kwance Yana kallon News,Naila ta kalle Ni ta sake Kallo na tare da Furta Lallai kauye ta Fara gogewa,Mayafi na Dana rike a Hannu na ajiye a saman kujera tare da Zama nace Ina Umma? Sun fita yarinya sai dare zasu dawo mu gidan Nan manya da Yara bama Sallah a gida yawon shakatawa muke fita kullum har a gama Sallah,Wayyo Dana sani nace Anwar ya kaini yawo yanzu ya kawo Ni gida Kuma sai da yace na rakashi naki Amma ai nasan zai kirani a waya.

Baki Naila ta tabe Tace shi Kam Anwar ya cuci kansa dan Bai San Yar kauye bace ke shi yasa har ya dauko ki a motarsa, Anwar yaro ne me tashe me zaiyi da ke yaudarar ki zaiyi kawai ya barki ba abinda zai ci da ke,Murmushi nayi nace Wanda yafi Anwar ma Wlh nasan sai ya kula Ni bare wani Anwar Mikewa tsaye nayi nace Ni na San nafi duk Yan Matan gidan Nan komai kalla Kutiri yarinya a palon na shiga Taku dai dai tare da shanye Hannu Daya nace ke nasan idan Kika sa skert dina fadowa zaiyi sabo da kugun sauro gareki,Dariya Naila tayi tare da Furta ya Fu'ad kaga abinda takeyi a gabanka kayi maganinta Wai Kutiri ne Duwawu fa, Munafuki ya kalli komai Amma sai yace me aka Yi? Baka gani yanda take murgude deniya a gabanka wayarsa ya ci gaba da latsawa ko kula ta Bai Yi ba,Dariya nayi na juya Ina murguda Mazaunai na nayi kitchen a Haka, Fu'ad ya girgiza Kai yace Dole ayi Mata ciki fitsararra ko kunya ta Bata ji,
Ina Fitowa lokacin Naila ta Gama Cakarewa ba karya ta Sha kyau ta Gama tsukewa Kamar a sace ta,Kallo Daya ta min tana wani yatsina Tace ayi a Haifo Mana Dan shege mu Sha kallo,A zuciyata nace Zaki ga me Kama da Yayanki a fili kuwa nace Allah ya kawo shi lafiya sunansa Fu'ad idan Namiji ne,ai da Sauri Ya Fu'ad dake kwance ya juyo yace Zan balla ki Dan shegen naki Zaki sa Masa sunana? Nace yo Kai kadai ne Fu'ad a duniya Wanda yayi Cikin ma ai sunanku Daya Kuma Ni Allah Fu'ad Zan sa masa,To ki sa ki gani yanda Zan tatsile jaririn ya mutu,idan mace ce Kuma Sunan Khaleesat Zan saka Mata ko Fadila na sake furtawa Ina Murmushi me tafiya da Imanin me kallo na,Umma ce ta shigo ta Sha kyau Tace yawwa dama Ina wajen Nene ke nake Jira Rumaila Zo mu tafi kema ki kalli Gari,murna Ina washe Baki nace to Umma, Fu'ad yace Umma wlh bakwa kiyaye lafiyarku kasar Nan Babu lafiya ba tsaro Amma ku ba ruwanku so kuke Dole sai Kun jawo Mana Maraici da kukan rashi,Harara Umma ta watsa Masa tace Kai nifa ka ishe Ni yanzu kullum ka tare min a part Dina sai Iyayi kala kala kake zuba min,Ni ban San yaushe ka nacewa Zama a Nan ba ka koma part dinka ka ishe ni,ka Hana Yara sakewa gaba Daya haba.

A dawo lfy Umma Shawara na Baku...Bama so Umma ta furta,Lace Dina me kyau yasha dinkin Riga da skert na shirya na fito ko Dankwali ban daura ba Yana a Hannu na saman kaina Kuma na yafa mayafi na Karami na fito Ina yanga Ni a Dole na waye tare da Umma muka fita Ina ta Santi Ina kalle kalle, da ka kalle Ni kasan ban waye ba sutura ce kawai irin ta Yan birni ta Dan rufa min asiri,Amma sai zare idanuwa nakeyi Ina waige waige,Umma da Naila suna ta min dariya,Umma ta kalleni taga na zurawa wani waje Daya ina ta faman kallo Tace kiyi dai a hankali karki karya wuyanki irin wannan juye juye da kallo Dan Allah ki dinga rage idanuwanki jiba duk sun Kara girma akan kallo kawai,Ni dai Ina ta kallo na ko kulasu banyi ba hankali na yayi gaba,wata budurwa na hango ta gaji da Haduwa ga wani saurayinta Dan charas suna tafiya cike da Nishadi da gani kasan masoya ne, Nan take Fu'ad ya Fado min

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login