Showing 75001 words to 78000 words out of 115153 words
na Iya,Nace Ruwa ya Danyi sauki duk da cewar motar Tasha Tint, Kayan jikinmu da suka jike muka gyara sannan muka fita tare da Shiga gidan Bayan ya kulle motar,Iya tana kitchen Tace Aiken ku bacin Rai ne gaba daya,aikenku Babu huce zuciya,Ina kuka tsaya haka? Fu'ad ya shafa Gashinsa yace Me kantin ne baya Nan sai da ruwa ya Dan tsagaita ya zo ya Bamu,sai kuje ku cire kayanku ku shanya ku canja wasu ko mura ta kamaku sai dai naji Kuna tari ba ruwana,ke Kuma Rumaila sai ki karbi dankunnen naki ki maida kunnen naki ko? Sai lokacin na shafa kunne na naji ba dankunne a kunne daya, Fu'ad na kalla sai na hango Dankunnen a jikin rigarsa ya makale a kirjinsa shima Bai sani ba,Kunya ce ta kamani sosai,Dakin Iya na fada na dukunkune fuskata da pillow na Iya,shima Fu'ad sai da yaje cire kayansa yaga dankunnen,Kunya ta kamashi yaki fitowa daga daki ya kwanta yayi baccin karya,shi wlh ya Matsu Iya ta koma gidan Yayanta Haruna,Shi dai Yana Jin kunyar Iya Amma Kuma gidan akwai Dadi,ga Aljani baya zuwa sosai.
Umma kuwa tunda Fu'ad yace ya tafi wajen Rumaila suka Yi waya yace ai bazai kwana ba,Karo na biyu yace Mata ya wuce Kano Meeting sai Nan da kwana biyu zai dawo,Umma Bata San karya yayi Mata ba sabo da dole sai ta hanashi kwana shi yasa yace ai shi Yana Kano ma,Abbi kuwa Wani malami abokinsa ya hadashi da shi yace zai Iya yiwa Fadila magani,Abbi yace Malam to ya aikin yake? Malamin yace ai cikin dare Zan na kwana Ina Yi har na kwana bakwai Amma sai an kashe kudi,sabo da akwai wani turare Aljani za a tura can kasar Chech Republic a can za a siyo turaren Kuma gaskiya sai an kashe Dubu dari biyar,Abbi Yana ji ya Gane Dan damfara ne,sai yace to Bari zanyi shawara sai na dawo da kudin,malamin karya sai murna yakeyi banza ta Fadi,Abbi tunda ya fece ba a sake ganinsa ba.
Wani malami kuwa Nan ma Abbi aka tura can wani Kauye a kano,Shima yace Babban Aiki ne Alhaji Bakin Aljani ne a jikin Yarinyar Nan,dole sai kun dauki mataki idan ba Haka ba daf yake da nakasa Danku Mijin yarinyar,shi yanzu Aiki da kuke gani sai da kudi Matukar Ana son biyan bukata,sabo da maganin a makabarta za a binne,tunda Abbi yaji Haka Nan ma yace a bashi lokaci zai dawo, ya gudu abinsa.
Na Uku Kuma da Umma suka je Bayan sunyi bayanin komai,sai malamin ya kalli Umma yace Amma kina da kishiyoyi ko? Umma Tace ae,yace Ashsha duniya Ina Zaki damu ai wannan kishiyar a cikinsu Guda daya ce tayi mata asiri,Kuma ta jikin danki aka tura Aljanin ya sauka a Kan Yarinyar,Umma ta gallawa Malam Harara Tace to tun yarinya Bata San gidanmu ba take da aljanunta,Amma ai Basu tashi ba sai da tazo gidanku,Umma Tace gaskiya baza ka sa min zargin kowa a Raina ba,mu dai Kawai maganin Aljanu muka zo Nema ba neman ya akayi suka shige ta ba,Abbi yace Zaka hada min rigima a gidana dama ance irinku ke hada makwafta,Mata da Miji,Dangin miji,Yan Uwa duk kune kuke hada fada a tsakanin Alumma,Wanda Basu da hankali sai su yarda da Karyarku,Malam ya rike Baki yace nine makaryacin? Abbi yace to da mene?Umma Tace tashi mu tafi wannan ba malamin Allah bane,Malam ya nuna Umma da yatsa yace Zaki gani sai na sa Mijin naki ya sakeki,Ai ba Kaine Allah ba cewar Umma,Abbi yace karya kake Malam ya nuna Umma yace wannan Rayuwata ce gaba daya,Aurenta ma me tsada ne,Har Sudan na tsallaka na zabo ta aka dakko Amarya a jirgi me tsada ce me daraja,Ba irin matakar bace ta ladan noma auren Hadi,na tabbata Sanda ka auri matarka baka San ma kalarta ba aka daura maka aure da ita,Ni kuwa sai Dana zaba na darje,Malam sai yaji Abbi kamar yasan Sanda aka Masa aure,lokacin Yana karatun Allo a Sokoto sai kiransa akayi a gida Yana zuwa akace an Masa aure Kuma dole Haka ya hakura gashi har sun Tara Yara,Malam ya nuna Abbi da yatsa yace kaima boka ne na gano ka,idan ba boka ba ya akayi kasan ta yanda aka min aure? Abbi ya rike Hannun Umma yace muje,suka bar Malam Yana ta masifa,Har yanzu ba son matarsa yake ba Kawai Yana Zama da ita sabo da Iyayensa da Kuma Yaran da suka Tara,Nan take Malam yace wallahi Nima sai nayi auren so na zabo dalleliya.
Da kyar Su Abbi suka samu wani malami ba Dan tsubbu ba Addua Kawai yakeyi a man Zaitun Ana bawa mutum Yana lasa Yana shafe jikinsa har ya Kare sannan yace kudin aikinsa Dubu saba'in ne idan mutum Yana so ya biya a sa Masa Rana yazo ya karbi maganin,Nan take Abbi ya biya kudin,Yace wani satin a dawo a karba ya rubuta Sunan Rumaila a takarda sabo da gudun mantuwa,Kuma shi baida Almajirai Dan Ahlul Sunna ne Islamiyya ce da shi a Nan yake koyarwa,babu shirka babu Bidi'a,Abbi ya dawo ya bawa Umma labari yace yanzu Naga Malam na kirki Har wa'azi yake Yi Kuma Yana koyarwa a makaranta ta Sunna,Wancen mutanen duk ba malamai bane,Malam me wa'azantarwa da koyarwa shine malamin gaskiya Wanda zai ce Allah da manzo ba Malam na soro ba Wanda aikinsa damfara da shirka ga hadin fada a tsakanin Alumma,Umma Tace ai yafi Amma duk me yarda da Maganar malami Dan tsubbu to zuciyarsa rufaffiya ce bazai Gane ba Kuma bashi da rabo.
Momy Da Mama zaune suke suna cewa wannan munafukar Ina suke zuwa ne da Abbin su Fadila?Mama Tace su suka sani Idan tayi tsami zamuji,Amma su Khaleesat sunce zuwansu gidan Fu'ad sau biyu Amma gidan a kulle sai Mai gadi da me kula da Compound,Amma da suka tambayi me Gadi Ina masu gidan Suma munafukan sai cewa sukayi Wai sun tafi Lagos Honey Moon,Momy Tace Wai su masu Aiki na Amana baza su tonawa Ogan su asiri ba,duk sai sunci Ubansu da kaina zanje gidan Anjima,Mama Tace muje Kai tare,5pm suka shirya Mama itace ke Driving har gidan Fu'ad suka je ko motar Basu shigar ciki ba a waje suka Yi parking ,suna kwankwasawa me Gadi ya taso tare da lekowa ta Yar wata kafa a jikin gate din Wanda dama anyi ta Dan ganin waye yazo,Ta ciki Yace basa Nan sun tafi Lagos,Momy ta galla Masa Harara Tace Kai karka Raina Mana hankali idan ma zaka fada Mana gaskiya ka fada kudi zamu biyaka,Me gadi yace Hajiya baza ki Iya biyana kudin da Oga ke bani ba,Kuma sunce sun tafi Lagos sai nayi Miki karya,gwara ku tafi sabo da Ina da bindiga ta sai na dakko ta na fasa muku kafafu,Momy Tace da kuwa ka Kare rayuwarka a fursuna,to sai ki hauro katanga ki bude gidan mu gani,Mama Tace muje zamu dawo Next time sai kaci Ubanka,Me gadi ya rufe Yar kafarsa ya koma ciki abinsa ya barsu Nan suka gaji tare da tafiya.
Sai da Iya ta Gama Yi Mana Tuwon shinkafa miyar taushe Tasha nama sannan na daukar Mana,dama tunda yazo har Iya ruwan Roba muke Sha,Iya tana Sha Tace Typhoid Karyarki ta kare,sai dai na dauka a Salat Amma ta hanyar ruwa kuwa na Gama da ke,Iya taji Dadi suna ta cin dadinsu tunda Fu'ad yazo shi yasa Bata so ya tafi,shima wani dadin garin yake ji,Muna cin Abinci Wayarsa tayi Kara,Umma ce ke kiransa ,kin dagawa yayi har ta Kira sau biyu Bai daga ba,Nace ka daga Mana yace sai Mun Gama ci sannan Zan kirata,Da Hunnu muka ci Tuwon mu yace tsotse min yatsu na,Daya Bayan daya na tsotse yatsunsa tas,Nima ya tsotse min Nawa tas,Fitowa Mukayi tare da wanke Hannu da baki,Mukayi Alwala yaje masallaci,Ni kuwa da Iya munyi Sallah a gida na gyara dakinmu Dana Iya har tsakar Gidan,Ina wanke wanke Fu'ad ya dawo ya tayani Yana min dauraya,Sai da muka Gama sannan ya Kira Umma,Bayan sun gaisa yace Iya...da Sauri yace au Umma,Umma Tace Iya kuma? Nice Iya yau Kuma? Sai kace Wanda ka Dade a gidan Su Rumaila ka rike sunan Iya sosai har mantawa kakeyi kana kirana da Iya Kai ga me suruka ko,Dariya Fu'ad yayi yace ba Haka bane Umma, kinji shuru ko Meeting ne ya rike Ni sai yanzu na fito,Umma Tace ai nayi tunanin Haka,gobe zaka dawo ko? Fu'ad yace Aikin ne Umma yayi yawa da kyar ne Idan Zan dawo goben ma sai dai ko jibi ko Kuma Nan da kwana Uku Ma,Umma Tace ai kafin ka dawo an karbo maganin Rumaila idan ka dawo sai kaje ka Kai Mata tayi amfani da shi mu gani ko za a Dace, Fu'ad Yana Murna yace to Inshaallah za a Dace Iya...Au sorry Umma zance,Umma ta girgiza Kai Tace zaka zo ka sameni.
Yamma na Yi yace zai tafi Iya Tace Sam bazai tafi ba sai gobe dama shi ba Niyyar tafiya yayi ba shi yasa yace to Allah ya kaimu goben,Iya Tace goben ma sai yamma yace Inshaallah,sai murna yakeyi,Yau ma Haka Mukayi bacci makale da juna Aljani Bai zo ba,Lokacin tafiyar Fu'ad yayi Amma sai ya kwanta yace Kansa ne ke ciwo,Iya duk ta gigice tana Sannu kaji, tafiyar Nan ka fasa ta sai kaji sauki, Fu'ad ya kwanta yayi wani ranga ranga kace mutuwa zaiyi har da kuka na,Iya Tace Bari a samo maka Yar Fura kasha naga tun safe ka kasa cin komai,dama Fu'ad Yunwa yake ji Dan kar ace cutar ba me zafi bace sai yaki cin komai,Iya tana jikin Kofa Tace furar za a kawo maka ko ayi maka kunun gyada,Ko Kuma Taliya da Miya za a kawo maka? Fu'ad yayi wani Ranga Ranga da kyar yake magana kasa Kasa yace a hada duka Ukun,ba Iya ba har Ni Rumaila sai da Mukayi mamaki,maralafiya Amma duk zaici Abu Haka,Iya tunaninta Bata ji dai dai ba Tace me kace? Ya sake cewa a hada duka Ukun a hankali Yana nishi.
Masu Sharhi a ci gaba Dan Allah
Ina godiya Kuma.
AsmaBaffa
[7/13, 8:42 AM] Sis Asma: 🎈🎈🎈🎈
DANGIN RABI
🎈🎈🎈🎈
NA KUDI NE
DUK WACCE TA CI AMANA TA FITAR DA NOVEL DIN NAN MUSAMMAN MASU TURAWA A GPS DAN A BIRGE FANS BAZAN YAFE BA.
DANGIN RABI IS DEDICATED TO AIDA MAMAN TASNIM
76-80
Official
By
AsmaBaffa
Page naku ne
Mmn Saddeeq
Nafee
Iya tace gaskiya yau babu tafiya jiki yayi zafi da yawa, Dan Nan ko ruwan garin Nan da kake wanka Bai karbeka ba?Fu'ad yace ae Ina Jin da shi dinma,Iya Tace Bari to a samo maka magani,Fu'ad yace nasha dazu ai zaiyi sauki Iya,Iya Tace to Bari na hada maka Furar sai a kawo ke Rumaila ki taimaka Masa ya canja kayan jikinsa sunyi nauyi wannan uban Jus (Jean) dake jikinsa kafin mutum ya cire ai yayi fitsari a wandonsa,Kinga Idan Sallah zaiyi kafin ma yayi Alwala an Idar da Sallah da wannan wandon nasa, Yana ji Yana ta Dariya a ransa,Iya tana tafiya na karasa saman katifar Ina tattaba wuyansa da Bayan Hannu na nace naji ba zafi? Yana numfarfashi yace ai...aini Haka nake zazzabi na jikina baya zafi Watarana ma sanyi Zaki ji,Doctor Dina yace zaman da nayi ne a turai shi yasa,Kuma abinci ma Ina Iya ci sabo da Albarkacin turai na samota a cikin jinina,Ni ban taba Shiga ko jirgi ba nace Allah ya taimakeka,Kayan na Taya shi cirewa yasa jallabiya fara,Harda cewa na Miko Masa turarensa,na dakko Masa tare da fesa Masa wani dadin kamshi abinka da Abu me tsada,Rufe Kofar ya Furta,naje na rufe ta yace sa key,na saka Key na dawo yace to kwanta haka na kwanta a gabansa,Kansa ya daura a dogin wuyana Yana sinsinar kamshi na,gashi na ya shafa yace yau an wanke min gashin Nan kuwa? Nace ae ban sharce shi sosai bane baka da lafiya shi yasa,yace min cumb,Mamaki ya kamani wannan wacce rashin lafiya ce Haka,Na Miko Masa Cumb ,ya wani Mike da kyar kamar zai Fadi har Ina rikeshi Ina cewa Karfa ka Fadi a hakura da taje gashin Nan zanyi da kaina,No Ni Namiji ne ya kamata na dinga yin kokari a Abu Zan Iya,Can muka matsa jikin Miro ya zage tare da taje min gashin kaina Shar,ya shafa min Mai me kamshi,jana yayi muka sake Kwanciya ya juyo Dani Muna kallon juna,Nace harka Dan Rame kuwa na Furta a hankali,a ransa yace kaji karyar Mata,dama Mata Haka sukeyi Haka Kawai sai ma idan suka ga Dan uwanka sai suce ya fika kyau,ko kana cewa baka da lfy sai suce shi yasa naga ka rame aikin su kenan kakale kakale da sa Ido.
Hancinsa na Danja kadan nace Hancin naka Ina sonshi da yawa ko Kai ka zanawa kanka baza kayi kamar wannan ba,yace ke kuma naki fa?fari nayi da Ido,yace Dan Kara Yi na gani,Dariya nayi Ina Jin kunya na sake Yi yace kin ci kyautar sarkar Gold nayi tunanin Wasa yake yi nayi Dariya kawai tare da yin Wani Wal Wal da idanuwa na yace kin cinye harda dankunnenta,gashin girarsa na shafa me yawa,Ina ta Masa tabe tabe a fuska yace na fara Jin Dan sauki, Alhmdllh na furta,Rungumeni yayi sosai a jikinsa bacci ya fara kwashe Ni Iya ta Kira Ni,Zan tashi ya sake makalkaleni Yana wani Shagwaba harda cewa karki tashi jikinki Dadi,Nace Iya ce fa ke Kira kasan Halinta ba ruwana,da sauri yace tashi ki tafi kar Iya tace sai na bar gidan Nan,Kofa na Bude na fito naje kitchen Tace gashi Nan ki Kai masa,Ni banga kina chasa kwalliya ba Rumaila Haka akeyi? Iya Bata San Fu'ad ko nayi kwalliyar ba Indai zamu kwanta sai ya cire min kayan idan Zan fito ne Kawai nake maida kayan jikina,nace Iya ko banyi kwalliya ba ai Ina da kyau,ke ki kiyayi maza wallahi ba ruwansu da kyanwunki Kawai ki Zama Me Maggi da gishiri har da Onga,Ashe Iya ba kwalliyar Kaya take nufi ba gyara jiki na matan aure,Nace to Iya ai Ina Sha,Ni dai Ina gaya Miki karki Bari ki warke bakya cikin shiri,Abincin na dauka na tafi Dakinmu,Ko da na ajiye a katon Tire nace ga Abincin yace sai dai ki bani bana Jin karfi,Sai da na fara bashi taliyarsa Yana ta ci muka ji sallamar su Saude,Iya ce ta tare su Tace a Miko ishirin ishirin su Uku ne Suka bawa Iya Naira Sittin,Iya Tace ki zauna can gefe sai sun fito sai ku kalle su,Kamar Wanda suka je gidan lalle da Sallah Haka Suka zauna Saude Ana ta tauna chewgum Ana kas kas,Hajara Itama Haka Ashe Har da Rabi ta dawo daga birni jiya Kuma Gulma tazo daukarwa Su Momy sune Suka turo ta tazo ta gani Ina gida ko an Kore ni,sai akace ai Angon ma yau kwanansa Uku a kauyen shine tazo ganin Zahiri.
Iya kuwa Shiryawa tayi Tace na tafi gidan Suna daga can Zan wuce taron siyasa sai dare Zan dawo Amma daga can gidan Kawunki Haruna Zan wuce na kwana sai Kuma gobe idan Allah ya kaimu, Fu'ad harda cewa Iya a dawo lafiya ki gaida kawun Yana ta murna a ransa,Iya tana tafiya yace je ki kulle Mana gidan Nan,Ina fitowa naga su Rabi a zaune suna ta surutu,nace au kune dama kuka zo? Saude Tace muka biya kudi dai gida idan za a shugo Dan son abin duniya sai an biya Ishirin, Fu'ad ne ya fito yaga su Rabi Kamar yaga Kashi ko kallon su baiyi ba yazo ya daukeni cak tare da Saba Ni a kafadarsa,nace Sweety ga mutane fa yace matata ce fa Ni Nace su zo,Su Rabi ya kalla tunda yazo garin ko Kofar gidan su Rabi Bai taka ba,Suka gaida shi,lfy Kawai yace sannan yace idan kun Gama zamu rufe gida,Tsoron Fu'ad da kwarjininsa yasa su Saude suka Mike tare da ficewa sum sum,suna fita Saude Tace a Dirka mata ciki,a shekara biyu ta Haifo Yara Uku suka gudu, Fu'ad yace lallai Yaran Nan Allah ya kawo su Gidanmu tun daga gate Zan sa a maido su Kauye zasu ci ubansu,Allah yasa naga Rabi a gidan Abbi zata ga yanda Zan koreta,kamar Ni su fada min magana wannan Sauden me kafa Kamar tsinken Tsintsiya sai naci Ubanta tunda Bata da kunya,Ni tafiya ma zanyi wannan Yan kauyen naku jahilai wlh.
Dariya ya dinga bani yanda yake ta faman masifa yace Iya ce Kawai wayayya,Iya tafi Yan Birni ma wayewa,Affa Kuma fa? Yace ai yanzu Affa baya layin mutane bare ayi lissafin.....bakinsa na rufe masa da sauri nace Kai Affan nawa? Shine fa ya Haife ni,Ni Ina son Abina,akansa zamu Bata wallahi,Hakuri ya bani ya Gane yayi subutar Baki,Fushi nayi na kwace jikina Zan tafi ya riko Ni da Sauri yace I'm sorry, Hawaye ne ya shararo min,Yace cikin sigar lallashi kiyi Hakuri kuskure nayi bazan sake ba, Hawaye na ya dinga lashewa Daya Bayan daya,Yana ta lallashi na,nace na hakura ai ya wuce,Yace to Smile for me,nayi murmushi yace Dan kadan kika Yi ai na sake bangale Baki yace to na yarda kin hakura,nace sai munje ka gaishe shi yau ma, Fu'ad yace ba komai ko Baki fada ba ai Affa ya cancanci gaisuwata kullum,ai Affa shima wayayye ne ga fara'a ya fara Yabon Affa Dan naji dadi,yace ai duk kauyen Nan Bamu da kamar Affa,nace to waye ma ya Isa ya Kai Affa matsayi a garin Nan,Yana ta min wayo Dan na hakura Ni ban Gane ba sai murna nakeyi Ina Kara zuzuta Affana.
Kallo na yayi yace Baby Ina tausayinki kin shiga jarabawa