Showing 78001 words to 81000 words out of 115153 words

Chapter 27 - DANGIN RABI COMPLETE

13 Jul 2025

4333

kala kala Amma Baki da zuciyar fushi da wata ce yanda take Laulayin Nan da kika Yi da bakin ciki bazai Bari ma ta iya komai ba a duniya,nace ai Ni ba komai ke shiga zuciyata ba ya dameni,Yace kice Kawai Idan Zan Kara aure bani da matsala? Dukansa nayi a kirji cikin Wasa nace Wai Ina cutarka ne? Yace dauriya Kawai nake Yi Amma Ina jinta a jikina kadan kadan,Tsabar samun sake yau a tsakar gida Mukayi wanka, Fu'ad yace wannan gidan akwai Albarka Salahu tsoron Iya yake ji,da acan ne ko Hannunki ban Isa na taba ba, nice na shafa Masa Mai sama sama na saka Masa wata arniyar shaddarsa Sky blue yayi kyau dinkin dai dai shi,hularsa Kalar kayan ya saka irin na matasan zamani an wani coka ta,sumarsa me uban yawa ta baya,Kai ba karamin kyau yayi ba,Nima na shirya na sa wata doguwar rigar material me tsada cikin na Lefe na,zanyi kwalliya ya kwace kayan yace powder ma ta Isa,Nace lipgloss din fa? Da Kansa yace kawo na shafa Miki kadan,Haka ya Dan zizara min kadan Wai kar maza su gani su yaba.

Yawon mu Muka fice ta cikin gonakin Mutane muke bi gaba daya garin Kore Shar gwanin birgewa,Ta Kan Yar hanyar da mutane ke wucewa muka bi muna tafiya dake Yamma ce ba mutane a gonakin,Hannu na ya rike muna tafiya muna hira,Rikeni yayi Muna tafiya muka tsaya,Hannayensa ya ware tare da furta Ayi Mana muma,Mu Kashi muka Miki a gado da baza ki Mana ba,Dariya na kyalkyale da ita sabo da na tuna farkon zuwan mu gidansu,Nace Ashe kaji me nace Amma ka share mu Kamar baka San Ina Yi ba,yace har tarihin pics dinki ne Dani sabo da kinfi kowa chaske gayu,Dariya nakeyi kamar ba gobe sabo da nasan irin Haukar da Mukayi,Yace gayun Habuja,Abujar ma sai dai kuce Habuja,Tunda kika zo gidan Nan kin fiye takura min sai da na soki ta dole,Dariya nayi na rike kugu Ina kallonsa,Ina ta fama da zuciya ta Akan lallai karta so ki Amma Ina,Sanda nace ban shirya aurenki Abbi yace ya Bawa Islam ke a lokacin Hada Kaya na nayi na koma Lagos,ciwon so yasa ko kwana daya banyi ba na dawo,nace mu muka San kayi wani yaji ma ka bar gida,yace ko Umma Bata sani ba,kar kuma mu koma gida ki fadawa Umma Watarana na San Halinki da shegen surutu,Hoto na ya nuna kwalliyar mu ta Fulani har da Radio a rataye ga Dan glass Dina irin na yara Baki na kwama a fuskata, Tsalle nakeyi sai ya goge yace ai Baki Isa ba Yaran mu Zan ajiyewa suga mamansu ranar da muka taba fara haduwa,Har pics Dina Ina zaune a palon Nene na saki Baki da Ido Ina kallon TV,Duk ban San ya dauka ba,Wai yaushe ka dauka?yace Islam ne yake ta daukanki Dana gani a wayarsa na tura a wayata na goge na wayarsa Baki daya,Wani Hoto na ya nuna min Ina Exercise shima na famfara da gudu,Kukan Shagwaba na saki nace Allah sai ka goge,Hannun sa ya daga sama nayi nayi na kwace Amma na kasa,nace muje to tunda baza ka goge ba,Tafiya muka ci gaba da Yi sai Hotuna yake daukan mu,Harda bani Wayar na Masa shi daya,Nima yayi min kala kala,nace Ni hoton Yan karya zaka min a motarka Ina tukawa Ina bin waka yanda Naga anayi Ana sawa a Instagram,Yace Amma da Mayafi Zaki Yi nace na hajiyoyi zaka min.

Komawa muka Yi muka Shiga motar nice ke Dan tukawa a tsorace sabo da ban wani Iya ba,Kida ya kunna na zabi ta Hausa wacce nasan na Iya, a wajen yayi Downloading wakar ya kunna min ita ta Garzali Miko (So Halitta ne)

Nayi daurin manyan Hajiyoyi ture kaga tsiya harda saka Glass din Fu'ad me tsada yayi min masifar kyau Yana ta Dariya nace ka daina dariyar Nan kayi min Video Kuma ka tabbata nayi kyau,Yace Kin shirya,Yes na Furta,Yace action...na wani fuske Ina ta tuka mota da kyar Ina bin wakar har wani nunawa nakeyi da Hannu Ina gwadawa kamar ana shooting film,Yayi aka gama,yace saura mu biyu ,ya canja wakar turanci Yana bi Ni Kuma Ina Driving Yana Mana har wani Yar rawa nakeyi Ina tuki,Muka sake pics,Ya tura min Nima a wayata,Sannan yace muje garin Yan uwanki duk Inda Iya tayi aure na San Yan Uwanki,Nace ka Bari sai gobe,ai gobe Zan tafi,no idan muka je sai mu koma Jigawa mu kwana a Hotel da safe sai ka ajiyeni a gida ka wuce abinka ko? Fu'ad yaji za a sake kwana a Hotel yace Masha'Allah harda wani kalkala yayi,Dariya nayi nace Lallai shayi ya ratsa ka wannan Irin fidda tajweed Haka,Hannu ya Mika min muka tafa.

Iya kuwa Tana gidan Suna Yamma tana Yi Tace ke mejego Zan tafi taron Siyasa Allah ya raya,Wata cikin Yan suna Iya ta taba auren mijinta har an rabu ma Mata basa hakura da kishi,gulmar Iya tayi ita da wata Baki ta tabe Tace a Haka dai za a Kare a neman kudi son abin duniya, Dan Abin kunya surukinta yazo ta bar musu gidanta sabo da Yana da kudi ko kunya Babu Yara suna ta tambadewa a gabanta,Ni Wallahi na tsani matar Nan gaba daya haushi take bani yanzu kaga Iyayi yarta ta auri me kudi sai yashe shi sukeyi komai shi yake musu,Karaf a kunnen Iya.
Iya Tace to Algunguma Ina jinki,Mene abin Jin haushi na idan kudin Dadi ne ke kiyi Mana ko kema yarki Mariya ta auri me kudin mana,Ni ban Hana ki Zama Mista miliniya ba a garin nan (Mrs Millionaire),ko na Hana kiyi kudi? duk bakin cikin tanda sai munci waina,Kuma kune jahilai bani da lokacin ku,kwarto yar tawa ta kawo ko dadironta ne? Halak malak mijinta ne babu Wani tantama,tsarkakarken Aure ne, yaro me tsarki Rumsilata me tsarki aka daura Aure tsarkakarke.

Matar tayi mukus tasan Halin Iya, Iya Tace ke auren yarki da akayi ba ingantacce bane sabo da lilamin Kauye ne yayi hudubar Auren bakinsa dagajaja da goro ko fatiharsa Bata Inganta ba,ita kuwa 'yata tsarkakakkun malamai ne Suka Daura shi,kace Balarabe ne sabo da Ilimin Addini, ke kuwa Auren Yar Taki Haka muka ji Ana daura Aure,Kun Bamu mun karba,Kun Bamu mun karba ita ake ta maimaitawa har sau Uku sannan Ana cewa Fatiha da Kursiyyu,An bada Sadaki dubu Bakwai da dari biyar Kamar kudin Yar budurwar Akuya ta kiwo,Hassada a kanku zata Kare,kuma Surikina shima Dana ne su sakata su Wala,kema idan kin koma gidan mijinki Dan Iska fakirin banza ki baje ku kwashi soyayya,ko na hanaki kiyiwa mijinki kema? Wannan jaririn da yake Hannunki uban me kikayi kika haife shi Algunguma ke Kuma a bokiyar gulmar kema a gidanki Mijinki baya murkushe ki? Kinibabba an kwantar da Yara a Palo suna yin bacci Zaki zare jiki ki fada dakin Miji aje Ana fyarfyadiyar Dadi shegiya me suffar Yan bori,Iya ta dinga masifa da kyar aka Bata Hakuri ta tafi matan Suka Yi mukus sabo da akwai kunya a kamaka kana gulmar mutum
Mejego Tace gaskiya baku kyauta ba kune baku da gaskiya Kuma kun San Halin Iya ba kyaleku zata Yi ba,Ina ruwanku da harkarsu,kishiyar Iya a da Tace jarababba ai ban San zata ji ba,na manta kunnenta kamar na miciji Haka yake.

Mu kuwa sai dare Muka je wajen Affa a wajen suyarsa Yana ta Yi,Gaida shi Mukayi yace to Yan bana bakwai daga Ina Haka fatan dai ba kyauta kuka zo na baku suya ta ba,Affa Tarwadar zaka bani,Daurin zaninsa ya gyara a kirjinsa saman Riga t-shirt,tsohuwar Rigata ce Dana taba mantata a gidan Affa sai gata yau a jikinsa duk ta jeme,Ni tausayin Abbi ma nake ji wannan sai Addua,yace ke uban me kike gani a jikina? Cire min shi ya Furta Yana gyara daurin zaninsa tare da bankaro min kirjinsa,Nace Affa Wai mu kuwa me muka yiwa Allah na laifi Haka ya jarrabce mu,Dan Ubanki Yi sabo a daina Yi Mana ruwan sama,maza kici gaba da sabo Dan Iskanci maimakon ki godewa Allah yayi Mana Baiwa gani Ina sana'a ta ci gaba kudi nake Tarawa Amma kina wani cewa kaddara,Abin farin ciki ya samu kice kaddara Dan Gyatimar Taki Iya ko bakin ciki kike min ne,Baki na turo nace Ni Wallahi ka daina abin Nan abin kunya ne,Affa ya rike Haba sannan yace Ayyiriri nanaye Ashe kina da Aiki,nace Affa Kawayena da surikinka a gabansu fa Affa kake Haka yace ki fadawa Surikin Nawa da kawayen naki anjima da dare suzo muyi gada da Wasan Buya buya,Nace Affa Surikin naka? Yace ae ya kalli Fu'ad yace kai taho muyi Tafa tafa,Allah baza mu sake zuwa gaishe ka ba na Furta,yace har Mahdi ya bayyana kar kuzo ko ance Neman ku nakeyi, Fu'ad ya kalla yace Kai mene kayi min wani kerere Haka a kaina ku tafi ku bani waje, Fu'ad ya juya shi Dariya ma Affan ke bashi,a ransa yace maybe ciwon hauka ne zai shige shi ta Haka.

Ko da muka koma gida Fu'ad yaga na Dan Shiga damuwa,Sai ya hada Mana game wayarsa da wayata yayi joining,Tabarma ya shimfida Mana a gindin Bishiyar gidanmu katuwa,Fresh Air tana ratsa mu nayi matashi da cinyarsa Yana Zaune Ni Ina kwance muna ta game sai na ware Muna ta nishadi,sai cinye Ni yake Yi ban Iya ba,Shagwaba na saki Ina bubbuga kafafu daga kwance nace Allah wayo kake min na daina,Kwanciya yayi Yana dariya na haye saman cikinsa Ina tsalle,Yace Zaki karasa Ni kin fiye Wasa Kamar wani Yar biri,Tashi ki dafa min Indomie Yunwa nake ji,Sharp sharp na dafa Masa Indomie da kwai dafaffe Guda biyar mu biyu Muka ci tayi dadi sosai.
Bayan ya dawo daga masallaci yayi Sallar Isha yace Zan fita majalisa nayi Abokai a garin Nan,ban so ya fita ba sabo da Ni nafi so Muna tare,Yana fita na kulle gidan nace idan ka dawo Ka Kwankwasa,Yace to ya tafi.

Fu'ad Bai San Su Jauro bane tsofaffin samarin Rumaila ne gaba daya a majalisar,Jauro anzo daga Lagos an Zama Dan Sanda,dabara yayi kudin da yake samu a can ya shiga makaranta yayi Yar Diploma dinsa Allah ya taimake shi ya samu Aiki.
Sauran Kuma duk cirani suke zuwa sun Dan waye sunfi Wanda basa fita a garin,wannan majalisar itace ta manyan Yaran garin samari masu tashe, Fu'ad ya zauna a cikinsu bayan ya Basu Hannu sun gaisa,wani aciki Iro yace Oga kafa jefa ka cafke,Rumaila Sarkin kyau da Yanga Kaine ka same ta,Jauro yace Kai Kamar saukar Aradu Haka naji Dana ji an Mata aure har na fara Tara kudin lefe,Sai da nayi sati Ina kuka, Allah na tuba Iya ta Sha zagi a wajena nayi tunanin Iya ce ta Mata aure da me kudi Ashe sai Naga Handsome ne Irinka,Iro yace samari da dama sunga Iftila'i a garin nan,Gashi tayi aure ta bar kawayenta Basu Yi ba,Jauro yace ai na tsani Rabin Nan Bata da hankali ko kadan da Yar Iskar Sauden Nan me Kama da Agwagwa, Fu'ad yaji wani kishi ya soke shi Ana ta Yabon matarsa,su Kuma mutan Kauye ba hankali,Wani Sabo yace Gaskiya Oga ka Dace Murmushin Rumaila Kawai ya Isa kaji kanka Yana wani juyawa,Ibrahim yace tafiyarta Kawai Jauro tafi birgeni,da Sauri Fu'ad ya kalli Jauro ransa a bace ya karewa Jauro kallo Dan matashi kyakyawa Caras dashi duk da Bai Kama ko kafar Fu'ad a kyau ba Amma shi Fu'ad yaga Jauro fa yayi shima Dan matashin Fulani,Yace Kaine Jauro me Zama a Lagos,Jauro ya washe Baki yace Ashe ka San labari na nine Wanda Muka taba zuba soyayya da Rumaila a da,Kai Rumaila ta so ni da yawa Amma ba Rabo na bace,Allah baiyi ba,mun tsula soyayya,ga iya kalamai zafafa ga abin Dariya Man kafa Dace cewar Jauro har da dafa kafadar Fu'ad.
Fu'ad yaji kamar ana zuba Masa garwashin wuta a zuciyarsa,a hasale yace to Ina ruwanku da matar wani yanzu da zaku yabe ta? Iro yace abin kaji Dadi ne ai mu a garin Nan idan aka ji a majalisar Nan tamu mun yabi matar wani to fa ta Kai mace, Fu'ad yace wannan majalisar tsinanniya ce Allah ya tsine Mata ya tsinewa masu yaban matan wasu,majalisar Yan Wutar Jahannama ce,Kuma Allah ya Isa kallon matata da kukayi har kuka yabe ta, jahilai marasa Ilimi Fuck you all ya Furta ya tashi a fusace ya tafi,Jauro yace Kai kazo har garinmu ka zage mu,Ku dauki mataki a kaina idan zaku Iya Nonsense cewar Fu'ad.

Ji nayi Ana buga gida Kamar za a jijjige Kofar,Da tsoro nace waye? Naji Muryarsa a fusace yace Dalla malama ki Bude kofa,Tsoro ya bani na Bude a hankali ya hada Dani yayi tafiyar ruwa dani saura kadan na Fadi ya rike Ni da Sauri,Yace gobe ki shirya tafiya zamuyi gida,nace Akan me Umma Tace a Bari sai na warke,yace Umma ce take aurenki? Wannan jahilan kauyen naku suna ta kallonki harda wannan Dan Iskan Jauro,Sai yanzu na fahimta Ashe kishi ne ya Koro shi,Nace kace abokanka ne to ma Ina ruwanka da su,tunda nazo garin Nan Iya Bata Bari na fita,da ake ta zuwa kallo na Iya kudi ta sa musu Amma Basu Iya biya ba,Kayi Hakuri Ni wlh ba Wanda na gani a cikinsu ko Jauron ma ban gani ba,Are you sure? Nace Yeah,Kai ya daga yace to idan na tafi ban bada dama ko Kofar gida ki fita ba,Kuma ba ke ba Jauro ko a Hanya nace to,karfa ya Miki magana ki amsa,nace to,You promise? Nace Yeah,idan kika fita daga gidan Nan ban bada Izni ba ban yafe ba,Nace to,Yace oya wanka zanyi ki kaimin Ruwa.
Zuwa nayi na hada masa ruwan wanka yayi,Nima nayi muka Yi Shirin bacci na kwanta a gefe can,Jikina ya matso ya makale Ni a jikinsa,Kuka na sake Masa,yace Mene Kuma ya faru? Shuru nayi naci gaba da kuka na,yace nine? Kai na daga Wai ae,yace nayi Miki masifa,na Kuma daga Kai Wai ae,yace To na daina,nace to cikin kuka Ni a dole na samu waje,kowa ya samu Rana sai yayi shanya da uban wa Zan yiwa sai dai naci ubana Kawai,Sabo da gobe zai tafi Wani Dirty Romance muka Sha wannan Yama fi xxx Dadi Ni dai Haka naji tunda ban San komai akan Xxx din ba,Yau ya gwangwaje na Sha wahala yanda ya dinga sarrafani ta ko Ina,Sai da muka samu nutsuwa yace Kai Baby Zaki Yi kwari a Harkar Nan kuwa daga yin Dan wannan har kin gaji Haka,Dariya nayi nace dadinka ne ya kashe min jiki,You are so sweet,Kin fini Sweet ai bakya Jin yanda kike susuta Ni.
Muna hirarmu ta masoya har bacci ya kwashe mu.
Washe gari Muna karyawa ya shirya tare da Yiwa Iya kyautar kudade masu nauyi,Iya ta dinga zuba Masa Addua,Allah ya kaika gida lafiya,Allah ya kareka da sharrin mahassada,Sharrin dare da Rana da Aljan musamman Salahu Allah ya watsa aniyarsu,Sharrin Karfe Allah ya rabaka da shi....Fu'ad ne yace Iya na gode ya Isa Haka kin cancanci fim wannan ma a wajena Kuma a Sannu Zan share Miki hawayenki,Iya tace Allah ya nuna min wannan Rana Dan Nan Dan Albarka.
Fita Mukayi tare Zan rakashi gidan Yan Uwana sannan ya wuce,Haka Affa da dukkan dangina na garin ya musu Alheri harda Kai kudi masallaci tallafi a siyi Generator da Speaker a sa a masallaci da Dan Abinda babu a masallatan garin kaf sai da ya bada kudin aikin.

Mota na shiga Muka tafi Gidan Babbar Yaya Rukayya Muka fara zuwa,Nice na Shiga Rukayya ta rike Baki yanda taga na canja,Tace kudi ba karya Rumaila kece Haka Kan Uba da kyar na Gane ki kin Zama wata baturiya ke Rumaila Anya kuwa kece? Dariya nayi nace nice Mana Sanda akace nayi cikin shege naji sakon gulmarki Yaya Rukayya Wai kar nazo gidanki baza ki rike Ni ba,Rukayya taga kudi Tace wallahi sharrin shedan ne Rumaila Iya duk ta taramu ta fada Mana Ashe Aljanine ya shafe ki,kiyi hakuri,waye ya fada Miki? Nace Basiru ne kaninmu,Rukayya Tace shege munafuki sai naci Ubansa, nace Ni da Mijina ne yazo gaishe ki,Da sauri Rukayya ta gyara harda sa Hijab,naje na shigo da Fu'ad suka gaisa yace Aunty Rukayya ya yara, Rukayya tana mamaki wannan bature Haka da Hausa radau,Mun Danyi Hira duk ya gaisa da mijinta da Yaran sannan ya min Rada a kunne tashi mu tafi,Rukayya Tace baza ku tsaya a siyo muku ko ruwa ba, Fu'ad yace sauri nakeyi sai Watarana idan mun dawo,Rukayya da mijinta sun Sha kyauta,na dawo zamu Danyi magana ta dangi,Rukayya Tace Rumaila bikin yarki fa ya kusa,nace Wannan Yar tayin Yar zaku yiwa aure,ke Rukayya har kin haifi Yar da ta Isa Aure? Zaki jawo Mana tsufa da wuri wanne Irin Aure Dan Allah a Bari tayi ko Secondary ce,Rukayya Tace to Haka ma babanta yace baya son Auren Nan,nace da Allah ku Kori Saurayin Nan gaba idan tayi karatu ayi mata auren Yan iskan Yara Basu tafasa ba zasu kone ita har tasan ma tayi wani saurayi Ina Haleesar take naci Ubanta,Saleeha ta shigo da Dan Uniform dinta nace ke Haleesa Dan Uwarki har kin San kula samari Yar yarinya dake to ba shegen da zai Miki aure yanzu a garin mahaukata ake,Dalla daukar min handbag dita muje mota,Haleesa Tace to Umma Rumaila Wai da shekara Nawa kika girme Ni ne? Kema fa auren wuri aka Miki ko Secondary Baki Gama ba,Rukayya Tace tsakaninku shekara daya tal da shekara daya Rumaila ta girmeki,Nace kina daurewa Yarinya gindi ta min fitsara wallahi Zan zare Hannu na a kanta,Duniya ba gaskiya Sanda nake talaka Rukayya ko shawara bakya Yi Dani idan nazo ma Zagina kike Yi Amma yanzu anga na Zama mutum auren yarinya ma Sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login