Showing 51001 words to 54000 words out of 197468 words
and promise me zakisha maganin ki,nasan indai har na shigo ajin Nan ba lalle in samu magana dake ba shiyasa na tsaya na rubuta miki letter na shigo dashi""
"Kici abinci Kisha magani and kije clinic"
"See you tomorrow byeeeeee"
Hannnunta tasa ta rufe bakinta tana murmushi watoh abinda ya faru Nan daman Lahab ya riga ya tsara kenan kafun ya shigo,Jakarta ta bude a hankalin ta aje papern a cikin litattafanta, cire barrect nata tayi ta aje a gefe laidan ta bude tana maijin dadi Sam ta rasa meyasa indai Lahab ya Bata Abu har marmarin karba take,Koh Abraham dake dan uwanta bata karban abin hannunsa.
takeAway in ta fitar duka biyu budewa tayi ganin daya indomie ne dayan Kuma kwai hakan yasata aje kwai in ganin akwai bread ma,indomie ta bude ta zubawa Kiki a marfin roban ta aje Masa akasan binci ya sauka ya kamaci,flask in ta bude don tasan yanda ake budewa akwai irinsa a gidansu.
Tsiyaye coffee tayi a cup fork ta d'auka Shima na roba ne ta Soma cin indomie cikin happy tana hadawa da coffee inta hankali kwanci sosai taci indomin Harta rage don daman Saida ya cika roban dam,karshe rufe sauran tayi ta maida cikin laidan ta,Ana dawowa breakfast haka sukaci gaba da Zama babu malami har azahar musulman suka fita sallah itakam kwai da bread ta d'auka taci ta koshi.
Misalin karfe 3 na yamma aka tashi makaranta dayake yau ba extra lesson kasancewar abinda ya faru yasa su tun karfe ukun akace su tafi gida,duke take tana tattara litattafanta data fitar tana bitawa saboda ita dai abinda ya faru bai Mata dadi ba da asaran lesson nayau dabasu samu ba,Amma ta lura yan ajin Koh a jikinsu Basu wani damu ba.
Excuse me senior,taji muryar wata yarinya dake tsaye a kanta d'aga Ido tayi ta kalli yarinyar black beauty ce kyekkyewa sosai Yar doguwa bazata wuce 15 ba Koh kasa da haka"yes" shine abinda Nnenna tace tana kallonta don d'aga gani juniorn sune.
Am daman nace Koh jakan dake zaune a gaban des Nan naki ne?
Girgiza Mata Kai Nnenna tayi"no ba nawa bane na class mate nawa ne.
Murmushi zulaihat tayi,ok sister na uncle nawa ne Bari na d'auka.
"La ba kome Nnenna tace tana d'auka da kanta ta Mika ma zulaihat in don ganin yanda ta tsaya sai kallonta take Kuma tana magana idanunta akanta.
da Sauri zulaihat tasa hannu ta karbi boron tana kallon laidan abinci dake gefe Amma dai batace kome ba tama Nnenna sallama tabar ajin,Nnenna ma jakanta ta d'auka tare da laidan ta fita a ajin.
Zulaihat Kam tana fita ajin su Rahab ta nufa ta Kai Masa jakan Kamar yanda ya umurceta kafun ta wuce masallaci domin sallan la'asar suci abinci kafun su Fara hadda by 4 O'clock.
Harta nufi gate sai ta tuna Lahab yace taje clinic juyawa tayi ta nufi clinic in,tana Hawa block in ta samu wasu Yan coper guda biyu sun fitoh d'aga ciki suna yare, alamu dai ya nuna wajen uncle physics nasu Suka fitoh shiga clinic in tayi direct ta nufi office in likitan knocking tayi shuru ba'a Bata izinin Shiga ba,gajiya tayi da tsayuwa kawai saita yanke shawarar tafiya abinta, juyawa tayi saura kadan suci Karo da Dr daya kawo Kai,da Sauri tayi baya hade da dukawa, "good afternoon Dr"?
Afternoon Nnenna Koh?
gyada Masa Kai tayi, toh muje ciki sai muyi maganar,Yana karasa maganar ya bude kofar office in ya shiga,biyosa tayi a baya Zama yayi a kan kujerar sa tare da nuna nata kujeran kaban Des nasa,sit down Mana Nnenna?
gyada Masa Kai tayi hade da Zama akan kujeran dake gaidashi tayi Shima ya sake amsawa kafun ya daura da cewa,gaskiya Naga jikin yayi kyau sosai ashe shiyasa ban ganki da safe ba.
"Sorry Dr naji saukine sosai shiyasa"
Ok Amma ai zakizo mu cire kanula in Aiko,ya karasa maganar Yana kallon hannnunta.
"Dr Na zare Allurar ai"ta karasa maganar tana kallon sa
What???meyasa Zaki cire kina aikin asibitine ban hannun mu gani.
Mika Masa hannun tayi,da kansa ya warware tsumman zare Ido yayi Ganin yanda hannnun ya kubura alamu ma sun nuna jini ya zuba,Aiko take yahau masifa irin dai yanda Dr kema majinyata in suka jika musu aiki,take yadau waya yayi magana ba'ajima ba sai Suka ji knocking izinin Shiga ya bada,aka turo kofar wata kyakyawar budurwace sanye da kayan asibiti.
Cike da girmamawa tace,sir gani
Yauwa sister farida ga wannan kuje da ita pharmacy kusai Allurar Nan saiki Mata tare da dressing in hannun nan nata Kisa Mata plaster,yakarasa maganar da Mika Mata Dan paper daya rubuta Mata allurar.
da Sauri ta karba cikin girmamawa.
Am sannan ke Nnenna kina Shan magani akan Kari Kam Koh? karki kuskura kiyi Wasa da magani kinji Koh?
Gyada Kai Nnenna tayi tare da mikewa tabi nurse in a baya,fuskarta a hade don wallahi ta tsane Allura.
Haka ba yanda ta iya ana kammala Mata allurar aka wanke hannun nata aka manna Mata plaster ta fita a clinic in, lokacin kusan 3:30 yayi haka ta fita a makarantan Koh sisi Bata dashi haka ta ringa takawa da kafa har gida duk tabi ta gaji ta jirkita gabaki d'aya.
Ta bangaren su Lahab haka Suka ringa yawon su har rana yunwa data Kama Lahab abinci Suka saya dukansu Suka ci,d'aga Nan sai Kuma yamma Suka Kama hanyar gidan su Nabeel.
Da sallama dukansu suka shiga gidan Inna ce zaune tana kwaba lalle zata daura sai yayar Nabeel dake rataye da jakan makaranta a kafadar ta sanye take da dogon riga na atamfa Wanda yasha wanki da guga duk da yasha ruwa Amma tas yake sai gelenta fari medium rataye a kafadar ta,ta rataya hand bag nata maikyau a kafadarta fuskar ta ba kome sai powder data shafa,tunda Suka shigo Adewale ke binta da kallo itakam kallo daya ta musu ta kauda kanta tare da zura takalmin ta ta nufi kofar fita.
"Ah ah big Aunty sai Ina Lahab yace Yana kallonta"
Mtwss Inda ka aikeni, shine amsan da ta bashi tana fita a gidan Inna Kam Ido kawai ta zuba musu irin kallon Nan na tuhuma da haushi don haryanzun Bata bar Jin haushin abinda Lahab yama jikanta ba gashi Kuma yau ta gansu tare duk buga Masa gargadi datayi bashi ba Lahab d'aga yau.
Adewale Kam saurin juyawa yayi tare da zaro wayarsa yahau wayar karya Yana fita a gidan Lahab Kam da kallon tuhuma ya bisa Amma Nabeel bai kawo kome a ransa ba ya nufi dakin sa Lahab na binsa a baya harsun kusa Isa dakin da Sauri Inna ta Mike kaiii lahabu dakata Ina zakaje badai dakin jikana ba kamko???Mara mutunci.
Dakatawa dukansu sukayi suna kallonta da mamaki bare ma Lahab Inda sabo dai ya Saba da masifar ta Amma bata taba koransa ba,"oh Inna yanzun ni kike kora a gidan Nan"?
Eh na koreka lahab,shine amsar da ta basa tana Masa kallon uku saura kwata.
"Kaga Nabeel shiga ka dauko mini kayana na shanja"
Shiga dakin Nabeel yayi Kamar yanda Lahab yace Masa don baison shiga rigimar su da Inna,kayan ball in Lahab da yake bari a gidan su ya dauko Masa da takalma duk ya fitoh masa dashi,kallon Inna yayi dake tsaye ta rike kugu yayi kawai ya girgiza Kai tare ta mikawa Lahab kayan,gasunan Lahab.
Amsa Lahab yayi ya aje akan dogon igiya dake tsakiyar gidan ya makala kayan ya aje takalmin a gefe,rigan uniform dake jikinsa ya cire tare da vest ganin addan Nabeel Bata gida yasashi Kwabe wando ya rage dagashi sai gajeren wandon jikinsa salati Inna ta buga,innalilahi wa'inna'ilahu raji'un mezan ganin nan dan duniya tsirara kayi a gaban jama'a nashiga ukuna,tana maganar tana tafa hannaye.
Shikaran kansa Nabeel mamakin iskancin Lahab yake wallahi ace mutum baya shakkan kowa.
Bucket Lahab ya d'auka batare dayabi takan masifar Inna ba yaja ruwan sa ya wuce bayi bayan yadau kayan daya makala a igiyan, wanka yayi ya zura kayan ball in abinsa ya fitoh daidai lokacin Nabeel ya dauko musu kwanon alele da Inna tayi a kitchen aje musu yayi a tsakar gida ya shimfida musu taburma,Lahab ga abinci fa ka fara ci Bari nima nayi wanka.
gyada Masa Kai Lahab yayi ya zauna tare da tambayar sa"wai har yanzun Adewale bai shigo bane"?
Nabeel najan ruwan Yana basa amsa,wallahi bai dawo ba nayi tunanin Koh fa ya wuce gidane.
"Anya kuwa Nabeel kasan yaufa akwai show bazai koma gida ba"
Kai gaskiya hakane fa Bara nayi wanka kaci alelen ka rage Mana daidai na fito wanka maybe ya dawo.
Bandaki Nabeel ya Shiga yayinda Lahab ya bude kwanon yayi Bismillah ya Soma cin alelen da Miya Inna Kam sai hararansa take makokonta cike yake tam da haushi ita da gidan ta ta kasa koransa.
Ta bangaren Adewale Kam Yana fita ya hangeta a bakin titi da Sauri ya nufeta,Assalamu Alaikum Gimbiya mubeena sai Ina haka.
Kallon sa mubeena tayi, waalaikumu Salam lafiya Kam?
Lafiya mubeena nace Ina Zaki?
Cikin yanga tace school zani wani abun me?
No ba kome Kuma in ba damuwa Zan iyya rakaki?
Kallon sa tayi da kyau itafa lamarin dan yarobawan Nan ya Fara isarta,akan me zaka rakani cema akayi bansan hanyar bane Koh me?
No ba hakan bane mubeena me laifi dan na nuna Zan rakaki school Naga dai duk Inda kaga kyautatawa da kulawa alamune na.................sai Kuma yayi shuru Yana kallonta kamar yarda ita ma ta juyo gabaki daya tana mamakin mezai ce kenan.
Uhmm uhmm a gaskiya mubeena nagaji da boye abinda ke Raina na gaji da hakuri da abinda ke cutar dani,nagaji da lallashin kaina wallahi Ina cutuwa mubeena bazan iyya daurewa ba nayi iyya yina Amma nakasa juriyar hakan.
Zuciyar ta bugawa take sosai Wanda har Saida ta dafe kirjin ta kafun ta daga idanunta tazuba Masa a hankalin ta bude bakinta ta Kara tambayarsa a Karo na biyu,menene wannan abin Adewale??...........
*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*
Page 39&40
Ina sonki Ina kaunar ki Ina bukatar ki a rayuwata,dan Allah karkice ah ah zuciyata bazata jure hakan ba ki tausaya min, Adewale yakarasa maganar cikin wani yanayi na fargaba.
Wani irin gyara tsayuwa mubeena tayi cikin Al'ajabi da mamaki take bin yaron da kallo don Koh a cikin su ukun shine karami su Lahab da Nabeel sun Dan girmesa kusan da shekara daya ma Koh watannni,Amma Kai dai baka da hankali Koh ince baka da mutunci yanzun Kai Inba tsaurin Ido da samun wuri ba ka rasa wance zaka kalla kace kanaso sai ni? sa'ar kace Koh tsarar kace ni toh wallahi d'aga yau sai yau magana makamancin wannan ta sake shiga tsakanin mu sai nayi mummunan Saba ma aikin banza kawai da wufe,ta karasa maganar tare da juyawa tana tsaida Mai keken da zai wuce.
Adewale dayayi mutuwar tsaye a wajen ganin Mai keken ya tsaya har tana kokarin Shiga yasasa saurin Kama Mata hannu,pls Mubeena ki tsaya ki saurare ni don Allah zuciyata bazata juri wannan horon da kike Mata ba.
Tasss kakeji mubeena ta wanke Adewale da Mari tare da fizge hannunta ta shiga keken tare da cewa Mai keken,malami dan Allah ja muje.
Adewale na dafe da kumatunsa Yana bin keken da kallo Harta cila,dafe kansa yayi a take yaji Kan na Masa wani irin ciwo kirjinsa na mugun bugawa juyawa yayi zai tsallaka titin,Sukayi Ido biyu da Lahab dake tsaye a nesa ya zuba Masa Ido alamu ma ya Jima agun.
Lahab Kam tunda Nabeel ya Shiga bandakin haka kawai taji hankalin sa ya kasa kwanciya ta fitar Adewale Kuma ya tabbatar bin mubeena yayi,hakan yasasa kasa hakuri har Saida ya rufe kwanon alelen yasa silifas din mubeena dake waje duk da ya Masa kadan Amma haka yasa.
Inna sai masifa take,Kai lahabu cire takalmin Nan wannan kafa naka kamar doya manya manya zaka saka Mata a takalmin ta Mai number 10 da rabi so kake ka tsinka Mata ai kafarka sai number 11 da rabi.
Kin kulata yayi ya wuce ya fita don ya gaji dasa boot takalmin ball in Kuma so yake inyasa Kar ya cire saiya dawo ball,fita yayi a gidan sanye da kayan ball in jikinsa tun d'aga nesa ya hangesu tsaye Suna magana hakan yasa shi jingina da ginin kofar gidan su Nabeel in ya hade hannu a kirjin Yana kallon su Amma baijin abinda suke cewa,bai Gama Shan mamaki ba Saida yaga mubeena ta wanke fuskar Adewale da Mari.
takowa Lahab yayi har Inda Adewale ke tsaye hannunsa ya Kama suka ye bakin wani dakali Suka zauna dafa kafadar sa Lahab yayi,"Adewale Koh baka fadamin ba na fahimci meya faru tun farko abinda na Fara guje maka kenan nace maka ka maida abinda kake kokarin bayyana wa saboda babu alamun nasara a tare da hakan.
Haba Lahab yazakace haka sannan laifine dan na nuna Ina son mubeena dahar zata d'aga hannu ta mareni,saboda na Kama Mata hannu Koh don nace Mata Ina sonta zata gaggayamin magana Koh saboda ni kabila ne kuke kyamata?
Kaga Adewale maganar gaskiya Zan fada maka,ni bana kyamar ka bama Kai ba duk wani mutum Mai hali irin naka ba abin kyama bane Kuma maganar banbancin kabila babu shi Koh na addin dazan nuna maka,kowa da addinin sa da kabilar sa Amma nasan mu Yan kasa dayane,kaima shaida me da ace mun nuna maka da bamu kai warhaka tare ba, Amma fa ka sani Ade mu a addinin mu bai halatta mana mace musulma ta aure Christine ba sai dai an hallata ma namiji musulmi auren Ahlil kitab,kaga Kenan a addinin mu bai halatta Mana ba,kaga kenan babu amfanin Neman soyayar mubeena tunda babu aure a tsakanin ku,sannan bayan Nan ka dubi shekarunka ka dubi nata atleast ta Baka 3 years a yanzun ita take bukatar abokin rayuwa,Kai yanzun ka aureta Ina zaka kaita nasan zata iyya kula da hakkin ta na aure don namiji baya kadan muddin ya balaga,Amma fa ka tuna cinta Shanta sannan iyayen ka kana tsammanin hakan zaiyu aikin me kake da zaka riketa? All this well Addinin mu bai hallata Mata ba don haka maganar gaskiya ka janye maganan Nan kodon cigaban alakarka da Nabeel don kasan in yasan zancen Nan Abu bazai maka kyau ba na tabbatar mubeena bazata fada Masa ba Amma Inka cigaba da yada manufarka gareta wata rana zai gane"
Bude Baki Adewale yayi zai Yi magana Lahab ya girgiza Masa Kai tare da Masa alamun yayi shuru ganin Nabeel ya nufo su,guys ya haka dukan ku kun fitoh kunzo kun zauna a waje gulman wa kuke?
Murmushi Lahab yayi cikin basarwa yace"Kai Nabeel aimu munfi karfin gulmar mutum sai dai mu tinkaresa da zance"bai bawa Nabeel daman magana ba ya kalli Adewale tashi muje Ade ka chanja uniform Nan mu wuce ball yamma na karayi fa"?
Ade dake zaune dafe da Kaine yace,gaskiya kuje ni yau babu Inda zani tare da mikewa tsaye gaskiya ninama wuce gida sai goben ku,Yana karasa maganar ya ratsasu ya wuce,da Ido Suka bisa Harya tsallaka titin ya wuce layin su,Yana bace muzu Suka juya a tare Suka kalli juna cike da mamaki Nabeel yace,lafiyan Adewale kuwa meyake faruwa ne?
d'aga kafadar sa Lahab yayi irin Shima baisanin nan ba,shuru kawai Nabeel yayi bawai don ya yarda ba,Mikewa sukayi suka koma cikin gidan, alelen da Basu karasa ciba Kenan Suka fita filin ball.
ta bangaren mubeena Kam tana shiga keken napep kuka kawai ta kamayi tama rasa meke damun ta guda da'ya Wai ita Adewale keso wannan shine so maso wani.
Baiwar Allah nidai Zan Baki shawara a matsayina na babba karki sake d'aga hannu ki dake namiji irin haka baida kyau zuciya baida Kashi wani inkin maresa ya barki wallahi wani bazai barki ba,Mai keken yace Yana kallon ta ta madubi.
Toh baba na gode amsar da ta basa kenan tana share hawaye dake bin kumatunta.
Adewale na Isa kofar gidan su hannu yasa ya tura get in ya Shiga har cikin falon su ya Kama hanyar corridor dazai sadasa da dakin sa idanu jazir.
Ade Ade mamar sa data fitoh d'aga kitchen rike da plate d'auke da nama soyaye.
Tsayawa yayi Yana kallonta sai Kuma ya kauda fuska,good afternoon mama.
Uhmm,cikin yare tace,toh yau Kuma ni kake gaidawa toh ma tsaya inaka fitoh ne?
School ya Bata amsa har yanzun idonsa na kasa.
School??ok Ina schoolbag first,shi sai yanzun ma tuna da school bag nasu shi da Nabeel Amma ya tabbatar friends nasu zasu daukar musu,mama banjin dadine shiyasa nabarwa Nabeel ya wuce min dashi.
Ok Amma yaushe ka Fara wuni har 4:00 a school,bude kofar dakin nasa kawai yayi ya shiga ba tare daya Bata amsar taba,Zama yayi a bakin gadon sa ya buga tagumi abin duniya ya damesa.
Mama dake tsaye aje plate in tayi tabi bayan dan nata,turo kofar tayi ta shiga a yanayinda ta gansa ya mugun d'aga Mata hankali Ade ne ke kuka ya rufe fuskarsa da tafukan hannayen sa, Jesus Ade what happen??meyasa kake kuka?
Da Sauri ya goge hawayen sa, nothing mom kawai kaina ke ciwo.
Kanka na ciwo Adewale yauka Fara ciwo ne? da bansan kaba me zakace ciwo ne ya saka kuka.
Nace Miki nothing mama,girgiza Kai mama tayi sai Kuma tayii murmushi tace,wace ce?? Kuma tace Bata sonka Koh?
Da mamaki yake kallon maman nasa shikaran kansa wani lokacin Yana mamakin yanda take saurin karantansa,Kwabe fuska yayi mama...
Shiii ba wani mama,nace wacece?
Shuru yayi sai Kuma ya rufe fuska Yana dariya hawaye Nabin kumatunsa.
Ok tunda bazaka fadamin ba is ok bazan takura maka ba Amma nasan wata Rana da kanka zaka fada basai na tambaye kaba,yanzun dai ka tashi Maza kayi wanka ka cire uniform, tana maganar tana shafa Masa Kai.
Mikewa yayi ya nufi toilet in ta bisa da kallo Harya bude kofar sai Kuma ya juya ya kalleta mama ya akai kikasan na Fara sonta Kuma tace Bata Sona.??
Hhhh Adewale kenan nice fa na haifeka nafi kowa sanin son nawa nasan babu abinda zaisaka kuka haka da damuwa sai so saboda nasan yarona ba rago bane sai a soyayya.
Murmushi yayi cikin Jin dadi ya shiga bandakin,mikewa tayi ta fita a dakin Naman ta d'auka dake plate ta wuce kitchen abinci ta zuba Masa ta shigo dakin aje Masa tayi tare da ruwa,fita tayi a dakin ganin har lokacin bai fitoh ba.
Adewale na fitowa yasa night Wear nasa abincin ya d'auka yadan ci duk da babu testing Koh