Showing 162001 words to 165000 words out of 197468 words

Chapter 55 - ALKAWARIN MASOYA COMPLETE

13 Jul 2025

6551

Sam tsawon sati d'aya kenan isheshen bacci Lahab baya samu sosai,zaune yake a kusa da ita hannunsa d'auke da kwaryar no-no Wanda aka dama da magani,iba take a ludayi Yana sanya Mata a baki a hankali in Kuma ya gangaro sai ya dau tsumman gefensa ya goge mata Inda ya gangaran a haka ya samu tadan sha kad'an,sai Kuma yaga ta Soma tari sosai tana kwarewa mikewa yayi ya dagata zaune ya jinginar da ita take ta Soma kwarara amai sosai take aman bakikkirin, kaman bakin Mai sosai tayi aman duk ta bata jikinta ta bata Masa jiki babu kyankyami ya Kamata harta gama kafun a hankali ya maidata kwance ya mike yadau babban tsumma ya goge wajen ruwa ya ibo ya wanke abinda ta batan ya Shanya ya had'a da kayan jikinsa ya wanke kayan jikinta matar malam ne tazo ta canja Mata don malam yace haka zatayi tayi ta aman har sai ta dawo aman abinda tasha wato in tasha no-no tayi aman nono.






A kallah Lahab yakai wata yanzun a kauyen Suna jinyar Nnenna Kamar kullum Yana zaune kusa da ita Qur'an ne a hannun sa Yana karanta mata,Kamar a mafarki yaga tana dan motsa hannunta Bai wani yi mamaki ba tunda dai ta Saba motse kawai dai Bata hayyacinta ne,sai Kuma yaga tana d'an bubbude idanunta harta budesu tar a hankali ta Soma magana Wanda yasa Lahab rufe Qur'an in ya matso kusa da kunnen ta Yana sauraron abinda take cewa Jin yanda take Kiran sunansa yasa sa damko hannunta jikinsa har rawa yake yake ce Mata"Nnenna ki kalleni ganinan kusa dake kinji Labiba"?





Hawaye ne ya Soma bin kumatunta da Sauri tasa hannu ta daura a jikinsa tare da jingina a kafadunsa tana kuka take cewa Lahab bata gani ya Bata glass nata da Sauri ya mike tsaye Jin tace bata gani kuka ta fashe dashi itama ta Mike tsaye tana lulubar hannnun sa kamo hannun nata yayi da Sauri ta damke hannun har tana kokarin faduwa na rashin kuzari,kamota yayi Yana cewa ta koma ta zauna amma Ina tace karya tafi ya Barta Dan Allah karya sake barinta"shigowa malam yayi sai Kuma ya tsaya Yana kallon su kauda fuska yayi yace Lahab ya zauna,Zama Lahab yayi itama ta zauna tana rike Masa hannu sai Kuma tambayar da ta jefo Masa"Lahab inane muke waya shigo dakin Nan? bana kallo Lahab bana kallo fa?Ina goggoji ta Miki min glass nawa.




Ki natsu shine amsar da malam ya Bata natsuwar tayi Lahab yadau wulan Fulani dake gefe ya aza Mata akai don gabaki d'aya gashin nata duk sun wargaje sunyi datti,kallon ta malamin yayi babu Wasa a fuskar sa yace"Zan tambaye ki Kuma Ina so ki ban amsa babu karya a ciki abinda Zaki cemin"jikinta har wani rawa take tasa hannu ta rike rigan Lahab da karfi ta gyada Masa Kai"ganin yanda ta rikice yasa Lahab sa hannu ya riko hannunta Yana dan Mata magana a hankali"ki natsu Mana babu abinda zai Miki kawai tambayar ki zaiyi fa"shuru tayi tana Jin abinda malam yake fada Mata.




Koh Zaki sanar dani sunan ki"Sunana Nnenna obinna"ke wace kabila ce"a hankali tace Igbo"toh tambayar da Zan Miki yanzun shine menene halakarki da Mafi'a(secret code)"zaro Ido Lahab yayi sai Kuma yace"haba malam ya zaka..........d'aga Masa hannu malam yayi yace"karka kuskura na sake Jin bakinka a cikin tambayar da Zan Mata karka kuskura"shuru kawai Lahab yayi Nnenna Kam jikintane ya tsoma rawa a hankali ta Soma hawaye sai Kuma ta fashe da wani irin kuka ta koma da baya timmm kakeji ta yanke jiki ta Fadi tayi wani irin sandarewa"salati Lahab ya sake yayi Sauri ya matso gareta ya tallafo kanta Yana Kiran sunan ta amma shuru bata amsa masa ba.





Mikewa malam yayi ya dauko wani magani yazo ya Shaka Mata a hanci saiga jini ya Fara bulbulowa Kamar bakin fanfo Kara Lahab ya sake Yana kuka yana cewa a taimaka Masa karta mutu"Kai ka kwantar da hankalin ka wannan jinin dake fita a jikinta warakane a gunta ka natsu sosai,natsuwa yayi aka maidata Kan shinfidar da ta tashi ,fita malam yayi yace Lahab ya biyo bayan sa bayan sunfita Zama yayi a kasan bishiyar tsakar gidan Zama yayi a gefen sa,magana malam ya Soma Masa Kamar haka"Lahab a gaskiya yarinyar Nan tana cikin gagarumin hatsari bana Wasa ba wanda in aka cigaba da hakan zata iya rasa ranta gabaki daya Dan soyayya ya Fara tasiri a zuciyarta.



Waro Ido Lahab yayi yace"mutuwa fa kace malam dan Allah ka taimakamin kada ta mutu don Allah fa"tabbas Lahab zata iya mutuwa in ba dai wani ikon Allah ba muddin ba'a samu ta dawo hayyacinta ba hakan Kuma bazaiyu ba harsai ta samu wani muharraminta kusa da ita wato miji muddin aka d'aura Mata aure karfinta a kungiyar su zai raunana rauninta zaisa ta samu sassaucin ciwon da take ciki in ba haka ba naman daya wuce cikin tannan zai iya Zama ajalinta......................







*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki*


🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀



da mamaki Dr tace yes she is pregnant bakace wife nakace ba"?komawa Lahab yayi ragob akan kujera gabaki d'aya yanayin sa sun sauya sabanin Nnenna da tayi shuru tana dai zaune a Bakin gado ba yabo ba fallasa ta sanya hannayenta ta cikin rigan tana shafa cikin,da Sauri Lahab yace"how many months ne Dr,Mika Masa result na hannunta tayi jikinsa a mace ya karba yayi Sai Kuma ya rumtsa idanunsa da karfi cikine na wata uku da sati uku,kallon Nnenna yayi sai yanzun yaga irin chanjawar da tayi amma dai ckinta Na nan a shafe Kamar babu halitta a cikinta.





Shuru yayi Bai Kara magana ba haka zalika itama Nnenna batace kome ba har ruwan ya Kare aka sallame su tare da bude Mata file na zuwa Ayo a wajen su,haka suka Kama hanyar silently Suka koma gidan yayi parking budewa yayi ya fita ba tare da yajirata ba itama binsa tayi a baya hannu yasa ya bude kofar flat nasu, Adewale dake zaune a falon tun safe mikewa yayi Yana tambayar Lahab Ina Mai jikin,bai rufe Baki ba sai gata ta shigo,wucewa dakin sa Lahab yayi ya maida kofar ya rufe ba tare daya baiwa Ade amsa ba sai Nnenna data tsaya Suka gaisa ya tambaye ta jikin nata kana itama ta wuce dakin ta.




Tura kofar dakin Lahab yayi ya Shiga zaune ya gansa yayi tagumi,tsayawa yayi a bakin kofar ya harde hannu don har lokacin Lahab baisan ya shigo ba,matsowa yayi ya dafa shi sai a lokacin ya dawo hayyacin sa ya kalli Ade sai Kuma ya sake tsaki"Wai Lahab lafiya meke faruwa ne wai me akace Yana damunta donni Karan kaina Naga Rama a tattare da ita Kuma kace tanacin abinci sosai"?Mika Masa paper kawai Lahab yayi Baiyi magana ba"amsa Ade yayi ya duba sai Kuma ya sake murmushi yace"daman irin wannan Rana nake guje maka Lahab shiyasa tun farko na nuna maka illan wannnan sure da zakayi"





"Wallahi Ade nayi auren Nan bada niyar a waye gari tayi ciki ba"oh kana nufin ka aure tane don ka ringa sex da ita karta haifi Y'ay'a Kamar kowace mace"?bazaka gane ba Ade taya Zan dau ciki Koda nakai nageria a matsayin nawa kasan Abune Mai girman gaske"




Cikin mamaki Ade yace daman tunda ka Fara kwanciya da ita baka tanadi abinda zaka fadawa gidan ku ba akanta nufinka Randa zaka koma gida rabuwa zakuyi Koh yaya"Koh saboda yanzun ka zama celebrate shiyasa bazaka iya Zama da ita da ciki ba"?da Sauri Lahab yace Ade bazaka gane abinda nake nufi ba wallahi Koh sau daya ban taba tunanin rabuwa da Labiba ba Amma Ina Jin tsoron kada mu tafka kuskuren da bunayya da muwaddat(Aisha bagudu)sukayi"Aiko ku kunma fiso tunda su Koh banza iyayen su Sunsan da auren jama'an garine Basu sani ba dasu kansu ma'aurantan Saida Suka tafka aika aika Amma daga karshe duk da haka an Kira cikin ta da shege bare kaida babu Wanda yasan zance.





Yanzun Ade menene mafita"mafita dayane Lahab ta haihu ka tattarata ku koma nageria Kama danginka bayani insun amince ai shikenan"wani kallo Lahab ya Masa kana yace karfa ka manta bari na tuna maka Nnenna suspect ce a naija komawarta yanzun bazaiyu ba haka zalika tinkaran iyayena yanzun matsala ne babba kawai Ni na yanke shawara za'a zubar da cikin kawai muyi planning sai lokacin da Zan koma nageria Inna kammala karatu saimu koma daidai lokacin case nata ya mutu"





Kai Lahab kana da hankali kuwa an gaya maka Nan nageria ne da zubar da ciki ya Zama abin sauki cikin ma na wata uku Yana kokarin shiga na hudu Koh kunyar halinda yarinyar mutane zata shiga bakayi toh wallahi karka kuskura karka Fara abinda zaija maka matsala a kasan Nan kaji na gaya maka"



"Koh baka fada Masa ba Ni bazan amince ba"juyawa dukan su sukayi wa zasu gani Nnenna ce Wance ke tsaye rike da kofa ga dukkan alamu ta Jima a wajen,sai hawaye kebin kumatunta bata taba tsammanin hakan daga wajen Lahab ba Wai zubda ciki"mikewa yayi yace"ciki Kam tunda Ni nayi nace a zubar Koh y'ay'a d'ari kike so daga baya mu Haifa Amma Banda yanzun kwata kwata shekaruna nawa da Zan kakkabawa kaina yaya"?




"Lahab bazan taba zubar da cikin Nan ba,domin shikadai ne ya ragemun Wanda Zan daga hannu na nuna nace ga dangina nan Banda kowa nawa sai shi Taya Zan zubar in Kuma Banda rabon wasu cikin a duniya fa sai wannan fa Kai kana da daman aure amma Ni har abada ka cuceni"Zan rike duk abinda na Haifa Koda kuwa baka so ni Mai iya cewa ba d'anka bane,Ni Zan zamo Masa uwa da uba bazanji kunya ba,amma wallahi banda zancen zubarwa Ina son jinina Ina son cikina Koda kuwa kowa zai gujeni"mikewa Lahab yayi Yana nuna kansa kana yace"Ni kike gayawa haka"an gaya maka Lahab na gaya maka indai akan cikin Nan ne"toh nace bana bukatar cikin"Ni ina ruwana Kuma daga yau Ina so ka manta cewa akwai sure a tsakanin mu da Kai haka zalika bazan Kara cin abinda ya zamo naka ba muddin dai zanci yaron cikina ya rayu"






Juyawa tayi tabar dakin tana kuka,kallon sa Ade yayi cikin tausayin su duka don wallahi sun basa tausayi yace"Lahab karka kuskura ka sake zancen zubda cikin Nan itace uwa ita keda ra'ayin haihuwa Koh ah ah don haka ka zamo Mai adalci,karfa ka manta Koh a addinin ku haramun ne abortion ka kula da ita Lahab ka tausaya Mata,daga haka shima yasa Kai yabar dakin,har yamma Lahab na dakin sa,mangariba nayi yayi sallah mikewa yayi ya shiga toilet,wanka yayi ya fito ya sanya Kaya fita yayi a dakin ya leka kitchen yaga kome net babu alamun ma Nnenna ta dau wani Abu a ciki.




Fita yayi ya sayo musu abinci laida biyu bude kofar dakin nata yayi ya shiga zaune take da kayan da Suka dawo asibiti Koh chanjawa batayi ba idanunta jawor da gani tun kukan safe da tayine Suka rine,shigowarsa baisa ta motsa daga inda take ba aje laidan yayi ba tare da yayi magana ba ya fita a dakin,washe gari da safe Kamar yanda ya aje Mata laidan haka yazo ya gani da mamaki yake kallon ta sai Kuma ya kasa hakuri yasa hannu ya dago blanket in, kwance take amma Bata dago ba"meya hanaki cin abinci"?ba abinda ya shafeka bane"abinda ya shafeni ne Mana kina ikiraren kinason abinda ke cikin shine kikeson kasheshe da yunwa"




Wani kalllo ta Masa sai Kuma tace"babu ruwan ka daya mutu Koh yayi Rai aikai farin ciki ya Kamata kayi sai Kuma ta Mike ta shiga toilet tare da banko Masa door,fita yayi a dakin ya wuce flat na Adewale zaune ya samesa Yana karyawa abincin gaban nasa Lahab ya Iba da yawa kana ya koma dakin Nnenna ya aje Mata yabar gidan,haka Suka cigaba da rayuwa kwata kwata Nnenna ta d'auke wuta fadan Mai ciki Bata shiga harkan Lahab abinci ma badon karta mutu da yunwa ba da bazataci ba gashi inta dafa da kanta baya Mata Dadi a Baki amma dataga uwar Bari ci take shi Kuma Bai fasa kawo Mata ba,tun tana dari dari karya sa Mata maganin zubda ciki harta cire tunanin abin a ranta amma Sam Bata yarda sun sake kwana daki d'aya ba ta tatttarasa ta watsar duk lokacin da taji sha'awa na taso Mata saidai ta shiga ruwan dumi shima Bai wani shega harkan nata iyakansa bata abinci akan kari yazo ya duba yanda ta waye gari.




*************
Wasan Lahab ya Fara gaba gaba don yanzun Yana iya barin kasan America ya tafi har wata kasa ball sai dai duk lokacin da zai tafi zai barwa Ade nauyin kula dacin Nnenna Kuma ba laifi shima Yana iya bakin kokarin sa,yau Monday Nnenna ce ta fito daga dakin ta sanye da siker da riga ta dau jakanta ta rataya a kafada sai takalmin ta flat gashinta a sake har gadon baya fitowa tayi daga part nasun ta fito compound na gidan,Lahab dake zaune a waje Yana Shan iska mikewa yayi ganinta tsaye a bakin titi.





Ina Zaki"?kauda fuska tayi ba tare da tayi magana ba,"ba magana nake Miki ba"?Nan ma shuru ta Masa ta tare taxi zata Shiga hannu yasa ya fizgota saura kad'an ta buge da marfin data bude janta yayi Suka koma ciki cikin bacin Rai yace"har zanna tambayar ki kina rainamin wayo Ina Zaki a hakan babu lullubi"kaga Lahab baison surutu da ranan Nan akan me Zan fada maka Inda zani,maganan lullubi Kuma Ni ba musulma bace"dagata yayi sama Suka koma ciki hijab karami ya d'auka ya saka Mata tare da kwace jakan budewa yayi ganin takardun asibiti ne hannunta kawai ya Kama ya rike jakan a daya hannun sa Suka fita daga gidan.




Asibiti Lahab ya wuce da ita aka Mata awo ba karamin shauki ya shiga ba lokacin da likita ke sanar dasu tagwayene a cikin Nnenna amma Bai wani nuna murna a fili ba,wayarsa ya d'auka ya d'auki hoton na'ura daya nuna yaran baro baro Suna kwance gasunan mitsitsi dasu yan 6 month's,kana ya dauketa tana zaune akan gado lokacin likita na Mata bayani ya had'a harda likitan dashi ya d'auki hoto likita sai dariya take don wallahi ita abin ma dariya ya Bata don kwata kwata Basu wuce 19year's ba a lokacin,Suna fitowa Suka samu wata Mata da miji zaune Suna jiran su fita Suma su shiga cikin matan ya girma don zaikai wata 8 sai kallonsu Mata da mijin Suke shidai Lahab baice kome ba ya Kama hannunta Suka fita, saloon ya kaita aka wanke Mata Kai da kafa ya biya duka,don lokacin cikin nata har ya fito ras dashi kowa ya ganta yaga Mai ciki ga jiki data juga Kamar me wuyanta har wani guru guru yayi na jiki ga haske Wanda Bai sani ba zai tsammaci bata had'a dangi da bakaken fata ba.







*********************
Su Lahab an kammala exam na karshen shekara Kuma na chanja aje sun samu dogon hutu na karshen shekara tunda Yan nageria sukaji kammala exam nasu suke sauraron ranan da uban gayyan zaice zasu kamo hanya,Lahab yayi kudi iya kudi yanzun Harya mallake gidan kansa a turai da mototi,sai dai har gobe Basu dawo normal da Nnenna ba lokacin da yaji bukatar matarshi ya tasashi a gaba yaje neman hakkinsa tace batasan zancen ba,shikenan shima ya ajeta a gefe yasa karatu a ga Kuma Alhamdulilah abinda ake tsammani shiya samu yau sati guda da kammala jarabawan,zaune yake a falo shida Ade Suna hiran wasan da Lahab a buga anan Ade ke kawo Masa zancen komawar su gida"gaskiya Ade kayi tafiyarka kawai wallahi Ni bazan iya zuwa Koh Ina ba"




da mamaki Ade yace saboda me"saboda bazan iya tafiya nabar Labiba da cikin 8 month's a jikinta fa,karfa ka manta dogon hutu Muka samu akallah mukai 2 to 3 months a chan nasan halinda zata Shiga bayan babu mu Ina wallahi ah ah"kaga Lahab Bai Kamata ka musu haka ba nasan kana da uzuri a gaban ka amma fa ka sani Suma Suna da hakkin akan ka,Mamu shekara guda Bata saka ka a idanunta ba haka ma Rahab tuni sun koma nageria Kai ake jira"Wai Ade da wani yare Zan maka bayani ka fahimta ne nace maka bazan iya tafiya nabar Nnenna ba"





Amma Lahab tunda Allah ya hore maka why not ka samu wata dattijuwan baturiya ta zauna ta kula maka da ita ko haihuwarce ya tashi ai akwai wata a kusa"wani banzan kallo Lahab ya Masa irin na baka da hankalin Nan"Ade taya Zan bar matata a hannu bayahudiya salon a haifamin yara biyu ta sabe daya ta gudu Koh ace sun mutu saboda da Bata da tsayaye gwara Ina Nan"shuru Ade yayi h?ar Lahab ya gama surutun sa kafun yace"toh nidai Ina kewar kasata Kuma zanje Naga iyayena"Allah ya bada sa'a babu Inda zani harsai Naga gudan jinina a doron kasa"yanzun me zakace musu a matsayin excuse naka"




Cewa zanyi Muna da wasa a France kawai"uhmmmm shine abinda Ade yace Suka cigaba da Hira Nnenna dake cikin kitchen tanajin duk abinda ke faruwa sosai taji zuciyarta tayi sanyi Jin Lahab har yanzun ya damu da lafiyar ta Koda yake ai ya damu da lafiyar ta ya bai damu da lafiyarta ba ai da ta Jima bata gidan sa,ta yarda Lahab na sonta baba Wasa ba.






Allah sarki Lahab bai sanar da gida bazai dawo ba har Saida Adewale ya koma nageria kafun ya sanar dasu sosai ran Mami ya baci tayita fada Akan wasan banza zaiki dawowa hakuri kawai ya Bata,yau tun safe lahab Suka shirya dashi da Nnenna zasu hospital cikin Nan gashinan tirim a gaba sanye take da polon wando sai riga bankacece har gwuwa Mai dogon hannu cikin Nan a gaba gyale tayi rafen nasa a kanta,ta sanya boot a kafarta,Lahab ma sanye yake da kananu kaya,motar ya bude Mata ta shiga Suka wuce hospital,Suna Isa facemask ya d'auka ya sa gudun kada mutane su Soma daukarsu hoto a watsa a duniya ya shiga uku tunda yanzun shima ya Zama popular Koh Ina ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login