Showing 3001 words to 6000 words out of 197468 words
a jikinta da sauri ta kwala kara ta matsa gefe, don ta tsorata ainun zuciya mai sake-sake harta saka mata wani abin cutarwa ne.
jin abin bai motsa ba yasata lalubar jakar ta ta bude kulenta dataji yana kuka, aiko tana budesa da gudu ya nufi inda Abin nan yake d'aukowa yayi da bakinsa ya matso kusa da ita ya aje mata a jiki, hannu tasa ta tattaba jin ayabane yasa ta murmushi, duk da ita a d'abiyarta sam batacin abinda ba'a bata ba koh yayane, Amma yunwar da takeji bazai saurara mata ba rabonta da abinci tun jiya.
barewa tayi a hankali tana kai dubanta zuwa ga kulenta mika masa tayi Amma taji bai karba ba alamu dai bazaici ba, daman tasan Bayacin Ayaba, cin Abinta ta shigayi dayake bari guda ya fadi kusan k'walli 15 ne a manne waje d'aya.
bayan ta gama cin ayabar ta, zuwa lokacin ruwa ya d'auke mikewa tayi da jikekken uniform nata a yage, jakanta ta bude ta saka kulenta a ciki shima duk ya jike, tafiya ta cigaba dayi tana kallon dishi-dishi dayake hanyar ba bakonta bane koh babu ido garanti zata gane kauyen su.
tunda ta shigo kauyen jikinta ya fad'a mata ba lafiya, sanin da tamusu war yanzun suna bakin bishiya wasu na caca wasu nashan giya, Amma yau sit kakeji, duk inda ta wuce binta ake da ido wasu yaran kam gudu suke suna bata hanya.
a haka ta iso kofar wani yamusheshen d'akin falange wanda akayishi ciki da falo, sai tsunmokaran su a rarrateye a jikin kwanukan gidan kome nasu a waje yake kama daga bandaki wajen girki kamar dai gidajen inyamurai babu katanga koh makewayi daga an fita a daki toh kamar an fita a kofar gidane.
tura kofar d'akin tayi kamar yanda ta tsammani hakance watoh a bude kamar kullum, da takalmi a kafarta ta shige ciki.
falone d'an kankani sai kujera da katifa mai masifar datti a gefe da tufafi a rarrateye sai risho da takalma da kwalaban giya, wucewa tayi kofar dake tsakar falon, tana shiga dakine karami babu kome sai taburman ta karami da kullin kayanta data d'aure mai datti tamai dashi filo.
aje jakan kulen tayi a gefe ta bude sa a ciki da sauri ya fice a dakin yayi falo, itakam kaya ta cire ta d'aura zani a kirji uniform jikekken ta fitar ta aje a gefe, takardun ta duka ta ciresu ta d'au jakan ta rataya akan igiyar kayanta dake dakin, hannu tasa a gefen katifarta ta fitoh da wani karamin akwatin karfe budewa tayi hannu tasa ta d'auko wani glass in, jujuyasa tayi a hannunta tana tunanin shine kadai ya rage mata in tsautsayi ya rafkawa glass in shikenan bata da wani, sakawa tayi a idanunta, kayan makaranta ta d'auka a hannu tayi waje dashi.
boket nasu dake falo ta d'auka ta fita waje dayake basa shan ruwan sama, sai Amfani dashi kawai suke Amma yau koh tarewa basu samu sunyi ba, ruwan jarka data ibo jiya ta tsiyaye kasancewar tasan tabbas bata da omo bata da kudin su, yasata wanke kayan haka da ruwa zallah ta shanya su.
Ruwa ta ibo takai bandaki duk irin sanyi da ake haka ta kwara ruwan ta fito, dakin ta shiga ganin kulenta rakube yanajin sanyi zani ta d'auka ta lulluba masa, kwanciya tayi akan taburman ta,har bacci ya d'auketa ga kulenta a gefenta shima a kwance.
Nnenna!!!Nnenna! Papane ke kwala mata kira da karfi tun kafun ya shigo falon.
Bude idanunta tayi da sauri jin kiran mahaifin nata, glass nata dake gefe ta dauka ta saka, sanye take da Jess da t-shirt, kod'andu da sauri tafito a d'akin jin ya shigo falon.
"Yes papa barka da dawowa" tace cikin yaren Egbo hade da karban laidan dake hannunsa.
"Yauwa Nnenna ga Abinci saiki ci saya miki nayi a kasuwa yau na d'an samu kudi na sai miki Abinci saikici ai karki mutu da yunwa?
Shuru tayi batayi magana ba ganin yau papa da mutunci ya dawo, harda sai mata abinci zama tayi a falon bayan ta dauko plate, ta bude laidan tuwon Amala ne ta fitar ta juye a plate, bude laidan miyan tayi zata juye sai kuma tasa a hancinta ta tsuntsuna.
Da sauri ta aje laidan tana kakarin amai jin miyar Akwai naman kare a ciki.
Papa dake kallon ta cikin jin haushi yace,kee Nnenna bazakici abincin nan ba kenan again koh dai da gaske ke mayyar ce, naga dai miyace babu nama a ciki koh Alamun nama?
"amma ai miyar naman ce?kuma naman ma na kare ni banzanci nama ba"
Keee mu Egbo ne munacin aladu da kare ke waye da bazakici ba?
"Ni namane kwai banaci koh miyar nama"tace tana Aje miyar a gefe ta kama cin tuwon zallah yayin da papa ke zaune a kan kujera, kallonta yayi sai kuma yace Nnenna?
Yes ta amsa masa
Koh kinsan meya faru da onye da chukwudi kuwa?
Gabanta ne ya fadi Amma ta maze cikin basarwa tace, "no pappa"
Thank god daya kasance babu ruwan ki a maganar nan, babu wanda yace akwai hannunki, kinsan kuwa d'azun da rana onye da chukwudi babban roka tabi kan onye ta markad'a masa kai atake ya mutu, chukwudi kam ya samu karaya uku yana asibiti har yanzun baisan wake kansa ba.
"Mai motar ya tsayane"?
No bai tsayaba gudu yayi, akwai wasu mutane a bakin titin sune suka gaggauta kaisu asibitin cikin Enugu.
"Toh god ya basu Lafiya"
Emeen daughter god bless u yarinyata bata da rike kowa a zuciya duk abinda suke miki a kauyen nan kina musu Addu'an samun sauki?
Shuru kawai tayi tacigaba dacin tuwonta yayinda kulenta ke lashe miyar.
*********************
Ta bangaren Lahab da gudu ya haye Addayiya data ruga gefe ta zauna Amma tsabar masifa saida yabi ta kanta ya haye, Rahab kam gefe yabi.
Da gudu ya bude kofar falon ya b'anb'ara bakin get tun daga nesa yake kwalawa mai gadin get akan ya bude masa kofa.
Jin hakan yasa Rahab shima yiwa mai gadin warning akan karya bude kofar, Amma ina mai gadi kam duk ya rikice, driver dake tsaye yana jiran yan makaranta da ido ya bisu ganin yanda sukazo suka wucesa kamar walkiya da gudu lahab ya bankade kofar get in ya fice a tamanin.
Turus Rahab ya tsaya rai a bace yana maijin bakin cikin abinda lahab ya masa, gashi yasan tunda lahab yafita a gidan shikenan badai ya iyya kamasa ba.
Kamar zai fashe da kuka haka ya koma cikin gidan cikin bacin Rai,Abbu ne ya kallesa Rahab waton rashin hakuri koh? Rahab kiranka muke Amma ina zuciyarka ta kasa hakuri koh?ai da wannan zuciyar kullum lahab ke galaba akan ka.
Shuru yayi fuskar nan tayi kirim Kamar zaiyi aman wuta, Addayiya dake gefe har yanzun tana salati akan hayo mata kai da Lahab yayi tace, wallahi Allah ya isa tsakanina da uwar yaran nan ta cuceni data aure mini miji.
Cikim haushi RAHAB ya juya gareta,kinga wallahi kimin shuru Addayiya karki sake zagar mini uwa banaso wallahi bala'inku ya tsaya iyya kan Lahab ba mamata ba.
Baki suka sake gabaki d'ayan su suna kallonsa da mamaki, sau dubu lahab zai masa abu in aka zagesa sai kuma ya nuna bacin ransa.
Babu wanda ya sake magana sai tashi da sukayi daga kan daining Area in, shareef ne ya mikawa Rahab 10k, gashi uncle ka sai littafin?
Karba Rahab yayi yana sabar jakarsa ya fita a falon, su munira sukabi bayansa dayake duk school d'aya suke dasu lahab.
Motar school da Ake kaisu suka shiga, Rahab ya shiga gaba munira da zulai suka shiga baya, driver yaja suka bar gidan, shareef da Anwar mototin su suka hau, haka ma umaimah da dan uwanta duk suka wuce school.
Lahab kam da gudu ya fita a gidan haka bai tsaya ba saida ya dangana da karshen layinsu, kafun yaja birki yana numfashi, sai kuma ya sake dariya tunawa da yanda yanzun Zuciyar Rahab ke tafarfasa.
Boom yaci ya kama tafiyarsa kamar bashi ba tun daga nesa ya hango Adewale tsaye sanye yake da uniform, wando da riga, wandon pencil ya d'amesa sosai sai rigan uniform in koh botur bai rufe ba wuyansa sanye da sarkan cross mai sheki sai hannunsa dake sanye da abin hannu na maza.
Yana kallon Lahab daga nesa ya kama baki cikin tarin mamaki, jesus nashiga uku me zan gani haka Lahab ina kayan makarantar yake dan iska?duk cikin hausar sa dabai nuna ba ya tambaye lahab.
"Kallon banza lahab ya masa kai na fasa zuwa school in"
Wannan wani irin iskancine lahab kace mana jiya zaka school kasa yau na buga uniform zaka wanice baxaka ba?
"Eh bazani bane kawai yau in ma"
Amma baka da mutunci yanzun so kake nayita yawo da uniform ai danasan bazaka ba bazan saka ba.
"Basai ka koma ka cire ba"
Aikin banza momy na gida zakace na koma na cire uniform?
"Sorry ina Nabeel yake wai bai fito bane har yanzun, nifa na samo kudin jesen nan"
Kallonsa Adewale yayi, nima ai na fito dasu yace yana zaro kudi a Aljuhunsa ka gansu nan 10k ne cip.
"Kai anya ba satosu kayi ba daga magana jiya harka samo"
Kowa barawo ne irin ka, an gaya maka ni dady ne ya bani dana ce masa a school aka bukace kudin kaga kuma uniform na saka ga kekena ma, shiyasa ya yarda makaranta zani, yace yana nunawa lahab kekensa dake gefe a fake, kekene mai masifar kyau da tsada.
Murmushi kawai lahab yayi yace"aiko kudin Rahab na rarumo"
Toh kaikam Allah ya shiryeka?
"Ameen shige Ade muje mu dubo nabeel koh tsohowar nan ce ta tsayar dashi"
Kekensa Adewale ya hau Da sauri lahab ya rike bayan keken ganin Adawale na kokarin jan abinsa"wallahi Ade baka isa ba ka wuce a sama ka barni a kasa"
Turesa ade yayi yaja kekensa da karfi ya bule lahab da kura ya kara gaba.
Cikin jin haushi lahab yake bin kuran bayan keken ade har kofar gidan su Nabeel, irin gidan nan ne na block da block sai d'an karamin kofar falange ga ade a tsaye a kofar gidan yana jiran isowar Lahab.
Koh kallon ade baiyi ba ya tura kofar gidan, da sauri Adewale yabi bayansa.
Da sallama suka shigo tsakar gidan, amsa musu mubeena dake zaune a tsakar gidan tana wanke wanke, sanye take da xani na Atamfa riga daban zani daban, sai hulan bacci data soka gashin kanta a ciki, amma hakan bai hana ganin gashinta dake kwance a gaba goshinta ba.
Sai kakar Nabeel inna dake zaune a taburma tana tsefe kanta, Kallon Su lahab inna tayi sai kuma Adewale, dake gaidata Amsawa tayi ciki ciki ganin lahab bai sanya uniform ba, tasan daker ne yau su leka makarata.
Jin yanda ta wani Amsa ma Ade gaisuwarsa yasa lahab kin gaidata, d'akin ya nufa Adewale na binsa a baya.
Ku dawo nan karku kuskura ku shiga d'akin nan yan iskan yara fitinannu Addan Nabeel dake wanke wanke tace.
Koh kulata lahab baiyi ba ya wuce d'akin, yayin da Ade ya tsaya kamar yanda Mubeena tace, jingina yayi da jikin ginin dake gefen wajen wanke wanken nata.
Mikewa Inna tayi ta sabe bokatin wankan ta ta shiga ban dakin, batace musu uffan ba.
Ganin ba kowa yasa Adewale fisgo Mubeena dake tsaye tana kokarin d'aukar kwandon kwanukan ta, had'ata da bango yayi ya rufa mata jiki da nasa, ya kasance tana jikin bango yana gabanta, yasa hannu akan ginin dake bayanta.
Da sauri ta kallesa sai kuma cikin bacin rai tasa hannu ta ture sa amma koh gezau baiyi ba, yana mai duban cikin kwayar idanunta, a hankali ya bude baki yace, Akan ki na koyi sallama a gidan koma waye in zan shiga mundin musulmine,Amma na fahimci ke baki ganewa koh?kin matsamin.
Cikin jin haushi tace karka kuskura banason wasan banza don Allah sakeni?ni sa'arkace nifa Aunty kuce?
Hhh dariyanya sake tare da cemata, auntin nabeel da lahab dai, badai niba kuma shekara nawa kika bawa nabeel in? Amma sai son girma.
Hannunta tasa ta make masa kumatu da mari amma irin mara zafin nan.
Da sauri ya riko hannayen ta cikin zafin nama ya murd'a mata su.
Ihu tasa da karfi
Kamar daga sama sukaji ance mezan ganin nan haka
Da sauri ya saketa yana kallon mai maganar................
pls Subscribe!!!!
๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐
๐คน๐ฟโโ๏ธ *ALKAWARIN MASOYA* ๐คน๐ปโโ๏ธ
~ Na ~
๐ *Rukayya Ibrahim*๐
Free page๐คง
*EXQUISITE WRITER'S FARUM*
Page5โฃ&6โฃ
Lahab ne tsaye yana kallonsu cikin mamakin Abinda Ade yake ma Mubeena, fuska ba walwala ya tako wajen da suke tsaye, Itakam jikinta sai rawa yake don ta tsorata bata d'auka lahab bane.
Karasowa yayi kusa da Adewale a daidai lokacin wani farin matashi bazai wuce sa'ar su lahab ba, sanye da kayan gida a jikinsa wando 3queter da riga duk da kayan da gani sun d'an sha ruwa, kallonsu lahab yayi cikin tuhuma ganin su a tsatsaye harda Addansa ma, kai lafiyarku?
Har suna had'a baki wajen basa Amsa ba kome, da sauri mubeena ta sabi kwandon wanke-wanken ta har lokacin jikinta na bari ta shiga kitchen nasu dake gefe.
Kofar gidan suka nufa har sun iso bakin kofa sukaji muryar inna data fito daga bandaki, kai nabeel!!
Da sauri dukansu suka juyo gareta suna kallonta.
Ina zaka??banaji kace makaranta zaka da safen nan ba? yana ganka a haka sannan dumamen dana aje maka bazaka d'auka bane kaci sai ulcer ya kamaka.
gaskiya Inna ki basar kawai ni bazani makarantan nan ba.
akan me bazaka ba?koh don uban gidanka(lahab) baxaije bane? ai tunda na gansa ba uniform nasan za'a rina, toh ka tsaya na fad'a maka gaskiya, tun duniya bai fad'a maka ba, kaga wannan yaro lahabu da wannan d'an yorobawan?su suna da gata iyayen su nada hali koh basuje makaranta ba, rayuwa bazata musu tsami irin naka ba, Amatsayin ka na maraya ka rike maraicin ka kayi karatu ka samu na tallafawa rayuwar ka damu duka, in bakayi karatuba ka samu madogara wazai zamo gatan mu nida yar uwarka nabeel?
jin kalar fad'arda akema nabeel yasa Su fita a sulale suka bar gidan, suna fita kallon Ade lahab yayi"Adewale menene tsakaninka da mubeena Addar Nabeel"?
shuru ade yayi sai kuma ya ce ba kome.
cin serious lahab yayi, karka fara karka kuskura duk rashin jin mu baikai nan ba, koh zamuyi iskanci banda Ahlin mu a ciki, dangin nabeel tamkar nawa nake ganinsu kuma bazanso wani abin ya samesu ba, haka naka dangin bazan yarda a tuzartasu ba, don haka karka kuskura ka bari nabeel yaga irin abinda kayin nan, don Wallahi nasan karshen relationship naku yazo karshe kenan, kadaisan halinsa"?
Promise u hakan bazai kara faruwa ba, amma fa bada niya nayi ba kawai abinda tamin ne banji dadi ba?
"sai kuma aka.......shuru lahab yayi bai karasa ba ganin nabeel ya fitoh daga gidan fuska a hade.
Ade ne ya kallesa toh ina dumemen(dumame)yake koh bazaka fito mana dashi bane?
daga lahab har Ade dariya suka sake tuno Yanda abokin nasu ya tsane dumamen tuwo.
kallon banza ya musu ya kama tafiyar sa, da sauri sukabi bayansa ganin ya nufi gangaren layinsu, " kai nabeel ina zakane"?
kamar bazai amsa ba sai kuma yace, shago
"wani shagon"?
shagon dinki mana
da mamaki lahab da Ade sukace shagon dinki?har suna had'a baki, don rabon nabeel da shago ai an kwana biyu duk da ya iyya dinki, Amma fa banda had'a kura babu abinda ya iyya inya kakkarba kayan mutane sai ya daina zuwa shago" Amma dai yau mafarki kayi wata zata karka akan kudinta koh"?
kallon Lahab yayi sai kuma yayi murmushi kawai hade dacewa, kun manta kudin jesen jiya da mukayi daku zamu saya.
"eh mun tuna"
toh shiyasa yau zanje shago tunda mun fasa shiga school in naga koh Allah zaisa na samu kafun yamma.
amma Nabeel taya zaka samu 10k a rana d'aya kuma a d'inki gaskiya da wuya.
lahab kam baice kome ba jin Amsar da Ade ya bawa nabeel yasa sa ciro 11k innan a Aljuhunsa mikawa Abokin nasa kudin yayi, "gashi 11k ne ka d'auki dubu goma kuje da Ade kusai jese shima kudinsa na hannunsa 1k in ku hau transport"
da mamaki Ade ke kallon lahab daman haka kullum yake mundin D'ayansu baida abu tsakanin shi da Nabeel haka lahab zai d'au nasa ya basu, toh yanzun kai ina zaka?
da sauri Nabeel ma ya jefo masa tambayar sa shima, toh lahab inna karbi kudin nan kai kuma ka saya dame?
"kallonsu yayi toh tambayar wa zan fara amsawa a cikin ku"?
dukan mu suka basa amsa.
" toh gidan mamina zanje koh zaku rakani ne"?
da sauri sukce Ah ah
ok toh sai kuma maganar kudi, ina da wasu kuje kawai da wannan in, kai kuma Ade bani keken nan naka naje dashi a cikin 1k innan Nabeel ya saya abinci tunda bai karya ba.
godiya nabeel ya masa, bai amsa ba sai harara ya dallara masa, cikin wasa yace"babu godiya a tsakanin mu Abokai ai yiwa kaine, ya karasa maganar da hawa kan keken yaja ya kara gaba, suma da ido suka bisa sai kuma suka wuce bakin titi suka tare keke napep zuwa kasuwa.
lahab kam unguwan da maminsa ke aure ya nufa, unguwane mai kyaun gaske packing yayi a kofar wani tangamemen get, gidane mai kyau Amma baikai gidan su kyau ba, hannu yasa ya bubbuga get in hade da danna hon na kekensa.
maigadi dake zaune a d'akinsa jin bugu ba gaggautawa yasa da sauri ya mike takalminsa ya saka cikin sassarfa ya nufi kofar, kokarin bude kofar yake hade da tambayar wanene.
shuru lahab yayi baiyi magana ba, mai gadin nad'an bude kofar zai leka yaga waye ne da gudu lahab yaja keken yayi cikin gidan saura kad'an ya kade maiganin, da sauri ya basa hanya tsayawa kawai yayi yana bin lahab da ido hade da mamakin ganinsa yau don duk da baya ganesu da d'an uwansa, Amma mundin lahab yazo saiya ganesu a d'abi'a da d'an uwansa ne yana zuwa gaidashi zaifara ba kokarin kad'esa ba, komawa kawai yayi ya rufe kofar ya zaune a benchin dake gefen d'akinsa.
lahab bai tsaya da keken saba har ya wuce compound na gidan sai da ya