Showing 54001 words to 57000 words out of 197468 words
kadan a bakin da Amma saboda Kar hankalin mama ya tashi yasa sa d'an Sakura yaci ya kwanta Yana ta tunane tunane abinsa.
ta bangaren Nnenna tana Isa gidan nasu dakinta ta shiga tayi wanka ta chanja kayan ta ta sanya wando fari da rigan t-shirt sauran indomie Mai sanyi ta baiwa Kiki yaci laidan ta d'auka ta nufi kitchen,falo ba kowa wanke Robobin tayi ta zubar da coffee dake flask ya Soma baci tayi ta dauko takai dakin ta ta aje, zata fita kenan saiga mom ta Shigo,keee Yar iska saiki fitoh ai Koh? peace taje kauyen su don haka ki fitoh ki daura Mana dinner tunda ba hutu kikaxoyi gidan Nan ba ai.
Gyada Kai Nnenna tayi tare dabin bayan mom data fita,tana binta a baya har kitchen,cikin store mom ta shiga,keee ki shigo store in Mana kin tsaya a kitchen Kamar na ubanki.
Shiga Nnenna tayi ta tsaya tana sauraron lissafin da mom ke Mata,
ga yam ki Mana sokora da miyan Stew kisa tsokar kaza a ciki sannan miyan Mai zakiyi karki kuskura Naga Mai yayi kadan Koh yawa hakama Magi Koh pepper,wallahi in abincin Nan bayi Dadi ba nida ke.
Gyada Kai Nnenna tayi again ta tsunguna tana daukar doyan,ke magana zakiyi min ba gyada Kai ba,ok mom kawai tace tana fita a store in itama mom fita tayi ta wuce falo ta zauna tana girgiza kafa.
Nnenna Kam doyan ta fere ta wanke ta kunna gas ta zuba a bujuwa ta daura tare da sa ruwa ta rufe,tattasai da tumatur sai tarugu da Albasa Mai ganye(lawashi) ta had'a ta gyara ta zuba a blander ta markad'a a take lawashin ya rinjaye colour tattasan ya zama green,bude fridge tayi ta dau kaza ta wanke ta yayyanka ta zuba a bujuwa Albasa da attarugu ta yanka a ciki ta zuba kori kadan da tafarnuwa kadan tasa Magi da gishiri tare dad'an shitta da masoro ta daura a huta ta rufe daidai lokacin Kuma doyan ta ya nuna saukewa tayi ta dauko wani bujuwan ta d'auka ta zuba Mai a ciki ta yanka Albasa Yana soyuwa ta zuba nikekken kayan miyanta ta fitoh da turmi tana zuba doyan a ciki tana dakawa gabaki d'aya ta hada gumi gashi daman ba isheshen lafiya bane da ita kanta ma wani ciwo yake Mata da hannunta gurinda aka da Mata ruwa.
ta daka doyan ta rage kadan Wanda zata ci sakwaran ta mulmulasu a laidan ta zuba a kula kayan miyan ta ringa juyawa Yana Shan wuta ta ibi kadan ta zuba a kwanon Miya ta aje a gefe ta zuba Naman Kazan ta Kara soyawa kafun tasa ruwan zafi a ciki Magi ta Kara kadan ta rufe miyar.
Doyan da ta ragen tasa a plate tadau miyar data zuba a kwano tasa a Kai tare da Barbara Magi ta Kama cin kayan ta Saida tacinye doyan duka tass kafun ta wanke hannunta ta duba miyar ya nuna saukewa tayi ta juye a kula yayi kyau sosai gashi ganyen albasar ya kawata miyar,tare da daukar daya bayan daya tana fitarwa a kitchen in tana jerawa a dinning Harta gama ta jera su plate da cups spoon ta goge kitchen in ta share, lokacin ma kusan 6:30 na yamma a gajiya ta wuce dakinta ba tare data wanke kanukan ba don wallahi ta gaji tana shiga ruwa ta d'auka tasha maganin ta ta kwanta sai baccin gajiya.
Ta bangaren Lahab Kam d'aga filin balls Basu dawo gida ba sai kusan mangari ba wucewa gidan su Nabeel yayi yayi wanka yadau jallabiyar Nabeel ya sanya lokacin mubeena na alwalan mangariba fuskar ta tamke Koh kallon arziki basu samu ba masallaci Suka nufa sukayi sallah mangari ba d'aga Nan Nabeel yace su koma gidan su suci abincin dare Amma Lahab yaki yace shi zai wuce gida.
Ok yanzun Kai Lahab gida ka nufa kenan?
"No Nabeel yau dai gidan Yaya jafar zani nida gidan mu Kuma sai muzammil ya Barta"
Au laifi kayine kake tsoron zuwa gida?
"Kutt Kai harka manta abinda yafaru kenan Nabeel toh nidai ban manta ba kasan maganar dole xai dawo gida don haka bani ba komawa gida"
Kai Kuma fa hakane Lahab, toh shikenan sai da safe Amma dai gobe ba Shiga school kenan Koh?
"tam Nabeel kenan in kaga zaka jeka nidai nayi Nan"
Dariya Nabeel yayi yabi Lahab da kallo Harya share kwana.
******************
Adewale Kam Yana kwance har 7 na dare Yana dakin sa a zaune Kamar d'aga Sama yaji papan sa na kwala Masa kira Adewale Adewale.....
Mama dake zaune a falon da Sauri ta Mike ah ah papan Ade ya haka d'aga dawowar ka Koh hutawa bakayi ba koh daki baka shiga ba ka Fara kwalawa yaro Kira.
Kinga tsaya nifa na Fara gajiya da halin kin Nan duk abinda yaron Nan yake aikatawa harda daurin gindin ki Nasha fadamiki banason Ina kallon Adewale da yaran hausawan Nan na tsane su banason ganinsa tare dake Amma ke nafahimci Koh a jikin ki ma Koh??
Kai papan Ade yanzun me nawa a cikin maganan Nan Kuma?Naga dai yaran Nan tun Suna yara suke abota duk abinda zakayi ka rabasu kayi Amma Basu rabuba sai yanzun da Suka Fara girma,Kuma a irin wannan age yara irin su basa bukatar fada Koh duka Koh tsawa Nasiya da lallashi daja a jiki sukafi bukata a yanzun.
Do Allah rufemin Baki nonsenses wance batasan ciwon kanta ba Taya zakice bazan ma yarona fada ba who I u??
Am ur wife Kuma uwar Ade Amma tunda kace hakan shikenan Allah baka hakuri yanzun dai meya faru???
Ina yake na tambaye ki ya dawo ne Koh bai dawo ba?
Ya dawo Yana bedroom,ai da Sauri ya nufi dakin yana surfa masifa binshi tayi a baya har cikin dakin.
Adewale tun Kiran farko ya Mike ya zauna Yana Jin duk cacar bakin da suke har nufo dakin Nashi,Yana jiran isowar papan Nashi,turo kofar tayi da karfi ya shigo tsayawa yayi akan Adewale Kai who I u da zanna kiranka kana jina ka kasa fitowa Kai wanene?
Kauda fuska kawai Adewale yayi donshi bai taba ganin baba masifaffe irin nasa ba ace mutum baida sassauci Kuma Wai a hakan shi pastor ne guda Amma baisan ya sassautawa iyalansa ba.
Ina magana ka manna mini hauka?
Am sorry papa
Sorry for ur self,me ka aikata a school principle naku ya kirani dazun da rana akan gobe yanason ganina Kuma na tabbatar tare da Kai zanzo.
Haba papa yazaka zo kana tambaya ta ai shugaban makarantan zaka tambaya bani ba?
Kai Ade kul karka sake gayawa baban ka magana like this,mama tace tana kallon sa.
gyada Mata Kai yayi,papa Kam cewa yayi keee barshi bayana ji da tashen balaga ba dole ya fadamin abinda ya fitoh a bakin sa.
Mikewa Ade yayi domin ransa ya Fara bace,kaga papa pls a hate noise tunda dai kazo ka tambaye nace ban sani ba pls u can leave now na gaji da surutun Nan ka barni naji da abinda ke damuna.
Kaiii Ni da gidana kake cemin na fita a dakin dana gida da kudina?
Bude kofar toilet in kawai Ade yayi ya Shiga hade da banko door in da karfi ya rufe Wanda Saida mama ta dafe kirjinta alun sanun tabar daki Bata Kara magana ba sai papa dake ta surfa masifa Yana zagin Ade..........
*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*
Page 41&42
Masifa papa yayita surfawa,Ade na toilet kin fitowa yayi Kuma yaki tanka Masa Harya gaji ya fita a dakin don kansa.
Jin ya fita yasa Ade ya fitoh yazo ya rufe kofar dakin sa ya kwanta.
************
Lahab Kam Keke napep yahau har unguwan su Yaya jafar"a kofar wancan gidan zaka tsaya Mai Keke"
Kallon gate in Mai keken yayi gate ne tankameme Mai shegen kyau da daukar hankali gaskiya kudi yayi kuka a gidan sauka Lahab yayi ya zaro lalitar sa ya Ciro dari biyu ya mikawa Mai keken,nufar kofar gate in yayi yasa hannu ya kwakwasa da karfi,ba'a Jima ba security yazo ya bude kofar Yana sanye da bakaken Kaya Kuma d'aga ganin sa madakin katttine,Yana ganin Lahab ya fadada fuskarsa,ah ah Rahab sannu da zuwa shigo Bismillah.
Shiga Lahab yayi ba tare daya mabi takan maganar Saba ya Soma ratsa tsakiyar gidan rufe gate in security yayi yabi bayan Lahab Yana Masa magana Amma Lahab Koh takan sa baibi ba yayi kofar falo dake manne a flat babba Wanda yafi Koh wanne kyau a gidan tura kofar yayi bakin sa d'auke da sallama, "Assalamu Alaikum"shuru babu amsa bin Koh Ina na falon yayi da Ido ganin ba kowa yasashi nufar upstairs dake falon ya Haura sama,Harya Isa babban falo dake saman binin bai hadu da kowa ba dan tsiririn corridor dake falon yabi direct ya bullar dashi wani kayatacen falo madaidaici Mai d'auke da kayan alatu na mure rayuwa.
"Assalamu Alaikum"ya Kara sallama a Karo na biyu Jin motsi a dinning area dake falon, waalaikumu Salam yaji an had'a Baki aka amsa Masa don ba kallon mutanen yake sosai ba,saboda labule daya karesu da falon Amma ana ganin alamun mutane a zaune,muryar wa nakeji kamar ta Rahab ka karaso Mana ka tsaya a falo kaman Bako?
takawa yayi a hankali zuwa dinning in hannu yasa bayan ya haura dan steps dake wajin ya yaye labulen,Yaya jafar ne sai matarsa nenne da yaran sa guda hudu Fatima da Hashim sai Aisha sai autan su Abdulmajid(gagararre),laa Uncle Rahab sannu da zuwa, shine abinda Fatima tace tana jawo Masa kujeran dake gefen ta, ba musu Lahab ya matsa wajen kujeran ya zauna,"Ina kwana Yaya Ina kwana nanne"?
Lafiya Rahab ya gida yasu Addayiya da Hamma Umar(Abbu)?
"Lafiya Yaya sun ma ce a gaida Kai"?
Rahab ya gida ya kwana biyu shuru Koh lekamu bakwayi harma gwara Kai da dan uwan ka Kam rabona dashi ai harna manta Koh gidan naku naje bancika samunsa ba.
"Alhamdulilah nenne kowa Lafiya"kawai Rahab yace don baison maganar tayi Nisa hannu ya baiwa Hashim sukayi musaba'ha sai Abdulmajid daya Mike yazo ya rungumesa"Kai man kwana biyu bama haduwa Koh wajen ka nazo uncle bai Bari na ganka ranan naje school naku ma Mai gadi ya hanani shiga, Wai Ina labarin Rahab ne mun kwana biyu da shegen wallahi?
"Kai da Allah sakeni karka karyamin kafadu ka bar Addayiya da wahala"Lahab yace Yana banbare Abdulmajid daka kafadar sa sake sa Majid yayi ya koma ya zauna Yana dariya gaisawa yayi dasu Aisha,kafun Fatima ta Mike tazo ta zuba Masa abinci ba musu yayi joining nasu Suka Soma cin tare.
Suna tsaka da cin abincin suka jiyo takalmi na kwaras kwaras alamu dai wani na taka tiles na falo kaf nasu babu Wanda ya dago Kai ya dubi Mai tahowan kowa cin abincin sa yake sabanin Lahab daya dago Kai ya kalleta, budurwace zatakai shekara 17 Amma kallo daya zaka Mata kasan akwai rawan Kai bana Wasa ba Koh d'aga yanayin tafiyarta ma kadai zai nuna Mata stubborn ce.
Shima sauke kansa yayi yaci gaba dacin tuwon dake gaban sa yayin da hankalisa ya Soma tafiya tunanin Nnenna Koh yanzun me take warhaka,wani hali ya tafi ya Barta a school ya jikin nata Kai Amma gaskiya ya Zama dole gobe da safe yaje ya ganta,Jin mutum a kansa yasa sa saurin kallon Kan nasa, yarinyar d'azun ce tazo ta tsaya Masa akai tana sanye da wasu matsatsun Kaya dinkine na riga da zani.
"Kee da Allah lafiya zakizo ki tsayamin akai in Zaki zauna akaina Zaki xaunane Koh Yaya"?
gabaki d'ayan su kallon Lahab sukayi Suna mamakin masifar sa don Sunsan Rahab na zuwa Amma babu ruwan sa da CeCe kuce asalima shi bai kaiwa mangariba a gidan d'aga yamma yayi yake tafiya gashi yau yazo da mangariba Kuma a fusace.
Amrat Kam kallon sama da kasa tayi Masa Amma dai batace kome ba taja kujeran ta zauna tadau plate ta zuba abinci ta kamaci gabaki d'aya wajen yayi shuru sai Karan shukula dake tashi wajen masu cin shinkafa Lahab Kam tuwo yake ci shida ya jafar.
Ringing wayan Ya jafar shine ya katse musu shurun nasu kallon Aisha yayi,ke dauko min wayata akan kujera,mikewa tayi da Sauri ta nufi falon daidai ta isama har wayar ta tsinke d'auka tayi ta kawo Masa,ganin Mai Kiran nasa yasa sa d'auka da Sauri ya Kara a kunne, waalaikumu Salam muzammil.
Jin an abbace muzammil sai da gaban Lahab ya Fadi Amma dai haka ya dake abinsa Yana sauraron abinda yayan nasa ke cewa.
Lafiya Alhamdulilah sai Kuma yayi shuru Yana sauraron muzammil in,eh Naga Rahab dai yazo dazun Nan yanzun ma Muna tare dashi akan dinning,shuru ya sakeyi sai Kuma yace oh Lahab ne Aiko gashinan nima saida na tuna nace lafiya da mangariban Nan ok ok ka dai Bari gobe da safen sai kazo Amma yanzun dai ka barshi ya kwanan,shuru ya sake sannan ya cigaba,ok Allah ya kaimu lafiya babu damuwa shikenan Zan kula.
Sauke wayar yayi a kunnen sa yakai duban sa ga Lahab Amma baiyi magana ba Shima Lahab abinci ya cigaba daci bai wani damu kansa ba,sai da Suka kammala ci nanne ne ta Fara tashi sai Lahab ma ya Mike,koma ka zauna,shine abinda yayan nasa yace Masa tare da kallon sauran yaran,ku bamu waje gabaki dayan su Suka Mike harda Amrat itama mikewa tayi da plate nata a hannu tabar dinning in don Yaya bai yarda Yama kannensa fada a gaban matan sa Koh yayan Saba,kallon Lahab yayi, Lahab?
Dago Kai yayi a hankali ya kalli yayan ya amsa "na'am"
Meya faru Koh ince Meka sake ma yayan naka Wanda yasa ka kasa komawa gida?
girgiza Kai yayi Kamar mutumin kirki"babu abinda na Masa Yaya"
Ah ah Lahab nasan ka nasan halinka nasan abinda zaka iyya da abinda bazaka iyya ba kadai San zaman ka a gidan Nan bamai yuwa bane Koh? Addayiya bazata yarda ba sannan muzammil bayason kana had'a inuwa daya da Abdulmajid saboda gani yake Kamar xai Kara Bata Kane Kuma Koh Ni Dana haifi Abdulmajid Yana matsayin d'ana nasan baijin magana,don haka gobe da safe muzammil zaizo ku wuce na nemi Alfarmar ya barka ka kwana.
"Shikenan Yaya nagode Amma Ni gaskiya bazan koma ba ai Nan ma gidan mune"
Eh gidan kune Amma nasan tabbas zaman ka a ciki bazai yuba ban hanaka zuwa ba Amma gaskiya Banda ikon ja da maganar da Hamma zaice Kuma nasan Koh yace ka zauna muzammil bazai amince ba don haka bazance kome ba.
Shuru Lahab yayi yana tunanin abinyi don shi harga Allah baison Zama a gidan yafison sai muzammil in sun koma kafun Shima ya koma,mikewa kawai yayi ya fita a dinning in,bangaren su Hashim ya wuce direct ya bude kofar dakin ya shiga zaune ya samu Majid a Kan kujera Yana waya ga dukkan alamu da mace yake wayar sai wani make murya yake kamar kwarto,kwanciya Lahab yayi akan gadon Yana wani irin jinsa incomplete Yama rasa tunanin me xaiyi na damuwar abokin sa Ade Koh na Nnenna dake son samun waje a zuciyar sa.
Ok baby Zan kiraki anjima ok Love you too,Majid yace Yana yanke wayar in kallon Lahab yayi,Kai mutumina kwana biyu baka lekomu ga Uncle ya samin Karan zuga shiyasa na daina zuwa gidan ku kwata kwata.
tsaki kawai Lahab yayi sai Kuma yace"mtwssss kaga aramin wayan Nan naka kabarni da abinda ya dameni"
Mika Masa wayar Majid yayi,a gaskiya Lahab kana ganin takura wannan uncle muzammil Nan anyi mugu wallahi shiyasa bana ma yarda na hadu dashi last dana hadu dashi ma a kofar school namu na gansa lokacin Muna level100 kaga an Jima Kuma ba zuwa gidan Nan nake ba.
"Taya zaizo Majid bayan basa shiri da nannen ka kasan shifa duk Wanda xai taka Masa birki akan hukunci toh fa sun Kulla tsama kenan"
gaskiya Kam don nanne ta dade da manta rikicin Nan Amma shi har gobe Yana Kan bakansa na gaba.
dariya kawai Lahab yayi Yana Kara wayar a kunnen sa bayan ya loda number Adewale a ciki, ringing uku yayi ba'a d'auka ba karshe ma rubuta Masa messagei yayi ya tura Masa.
*************
Adewale dake kwance abin duniya ya damesa ya rasa ma da wanne zaiji da masifar papa Koh da matsalan mubeena don shidai bai wani d'aga hankalin sa ba Akan Case in school Sam,yaji ringing in wayan sa Amma ya kasa tashi ya d'auka gani yake duk Mai kiransan Nan baida damuwa ne,Amma Jin shigowar sako yasa sa mikewa zaune a hankali tare da dafe Kan nasa Jin yanda yake azaban ciwo sosai hannu ya Mika ya kunna wutan dakin wayar nasa ya d'auka ganin an turo Masa sako da Sabon number,"Ade Lahab ne pls pick the call kaji"
tsaki kawai yaja don harga Allah haushin Lahab yakeji ganin harda Shima baiyi supporting na soyayyar sa ga mubeena ba.
Komawa yayi ya kashe wutan dakin ya kwanta tare da aje wayan a gefen sa wasu kiranne Suka ringa shigowar Yana basarwa gajiya yayi Kuma ya kasa hakuri sanin da yayi in dai har Lahab nama mutum nacin Kira haka toh da biyu me, daukar wayar yayi ya Kara a kunne,Hello..
Ta bangaren Lahab Kam sai Kira yake duk da Ade bai d'auka ba Amma haka bai hakura ba bai Kuma kula Majid dake masifa ba Wai dole ne sai babyn nasa tadau call in ya Kira so daya bai Isa ba.
Jin Adewale yayi picking Yana cewa hello"Ade fushi kake dani"?shine tambayar da Lahab ya Fara Masa.
Eh Lahab fushi nake dakai.
"Akan. Me toh"?
Au tambayana ma kake Lahab bakasan me kamin ba?
"Indai maganar dazun ne kayi hakuri Amma gaskiya na fada maka"
Jin abinda Lahab yace yasa Ade uhmm kawai baiyi magana ba.
Shuru Lahab yayi Jin bai basa amsa ba a hankali yace"baka da lafiya ne friend"?
Babu abinda ya shafe ka da rashin lafiya ta Koh lafiya na yanzun dai ka Fadi abinda yasa ka kirani in Kuma baka da abin fada na kashe wayata?
rike Baki Lahab yayi cikin mamaki don shifa bai d'auka Ade zai dau maganar daya fada Masa da zafi ba,a ganinsa me amfanin zaman tare in baza'a fadawa juna gaskiya ba"shikenan Ade Allah ya baka hakuri Amma wallahi kaf duniya Mai sonka ne kadai zai fada maka gaskiya Amma tunda ka nuna baka so is ok,daman maganan da Zan fada ma shine daman zance maka akan Case na makaranta gobe Kar