Showing 3001 words to 6000 words out of 25334 words

Chapter 2 - GUDUNA AKE

10 Sep 2025

1970

cika tsayawa ba sai in Anees ta buk'aci yin fitsari. Wajen azahar suka isa Kaduna. Saida suka tsaya sukayi sallah ta k'ara cika musu mota da kayan abinci ,su tsire da y'an snacks da lemoka ,sannan suka d'auki hanya. K'arfe uku daidai suka shiga birnin tarayya. Kaman yanda kawarta Kainat tayi mata bayanin unguwar da take. Kai tsaye tayi Gwarunpha phase 2. Unguwar ce gwanin sha'awa ta manyan mutane harma da masu matsakicin rufin asiri. K'ofar wani k'aramin gate gida na bene tayi horn d'in motar ta. Maigadi ya buɗe ta danna kai cikin gidan. Tun kafin tayi fakin motar ta hango Kainat data fito a guje daga gidan sanye cikin riga da wando na jeans da t-shirt fara. Kannan nata yasha gashin doki har hips nata. Kainat irin black beauty d'in nan ce mai yar kiba. Bata da tsayi sam shi yasa koda yaushe cikin heels takarmi take ko a cikin gida. Kainat idon Naira kenan akwaita da san kuɗi da son jindaɗi na rayuwa.

Murmushi Jaleela tayi hango Kainat d'in da tayi. A guje ta k'araso tana ihu ta kama murfin motar ta buɗe.

"Wayyo Beauty wai kece yau a gida na da gaske?, wlh da ki ka yimin waya na d'auka wasa ki ke. Wayyo jama'a yau ga Beauty a gidana "

Y'ar dariya Jaleela tayi tana girgiza kai ta juya tana kallon Anees data fara motsin farkawa daga barcin da take saboda ihun Kainat. A hankali yarinya ta buɗe manyan Blue eye's nata ta watsa su kan Kainat dake kallonta kaman ta had'iye. Da sauri ta matsa bayan motar ta d'auko Anees dake yunƙurin zama.

"Kai gaskiya MashaAllah Jaleela. Wlh komai naki mai kyau ne. Yanzu dubi yarinya nan don Allah kaman ba mutum ba saboda kyau. MashaAllah "

Da taimakon Kainat suka shigar da kayan su ciki. Gaba d'aya bakin Kainat yaki rufuwa duk ta rikice sai zuzuta kyan Anees take, gashi yarinya ita kuma tak'i sake mata sam. Duk da sunci abinci saida Kainat ta k'arayi musu order na take away. Ranan sam ta hana dukkanin wani aboki nata zuwa gidan. Itama Kainat kaman Jaleela zaman kanta take. Gidan da take ciki yanzu ma wani sugar Daddy nata ne ya bata. Dukkanin wani abu da take dasu daga mota har wayoyi dake hannun ta,abokan harkar ta ne suka bata. D'aki guda Kainat ta bawa Jaleela da Anees. Duk da cewa gidan k'aramine, an kashe masa dukiya ta kece raini. Babu abunda babu a ciki. Wanka Jaleela ta farayi kafin tayiwa Anees ta shirya ta cikin doguwar riga pink mara nauyi. Saida ta kwantar da ita tayi mata Addu'a ta kwanta nan gefen ta har tayi barci sannan ta miƙe ta jera musu kayansu cikin kwaba. Lokacin data gama an fara kiraye-kirayen sallan isha. Saboda haka ta koma ta d'auro alwala ta saka doguwar riga mara nauyi da katon hijabi daya kai mata har k'asa tayi sallah. Kaman yanda ta saba bayan ta idar zama tayi tana tilawa karatun Qur'ani. A haka Kainat ta shigo ta sameta. Mamaki ya rufe Kainat jin yanda Jaleela ke rera karatun Qur'anin. Ita dama tun ba yauba sun san Jaleela akwai ibada. To amma tana da wannan ilimin take irin wannan harkar?. Ko da yake ko wane bawa da sanadin kaddarar sa. Har yanzu basu san dalilin daya jefa Jaleela cikin wannan rayuwa da suke ba, don har yau tak'i sanar dasu komai. Guri ta samu gefen gadon ta zauna tana sauraran yanda Jaleela ke rere karatu. Tunawa tayi ita yaushe rabon da ma ta d'auki Qur'ani ta karanta?. Kai ko sallah idan zatayi Falak'i da Nas kawai take karantawa don tasan idan tace zata d'auko doguwar surata to tabbas zatayi kwaba, saboda babu karatun. Dama shi Qur'ani idan ka barshi ne da kwana d'aya ya barka da shekara guda. Tana jin Jaleela ta kai aya ta k'arshe tana 'Subhanakallahumma ashhadu an la'ilah illa'ant. Ashtagfurullahi wa'a tubu ilai'. Tace

"Yauwa kin idar?. Ke nake ta jira tun d'azu. Na samo miki babbar harka...."

Saurin katseta Jaleela tayi ta hanyar girgiza mata kai. Shiru Kainat tayi tana kallon Jaleela data nuna mata Qur'anin dake hannun ta. Miƙewa tayi ta fara ajiye Qur'anin a gefa cikin nutsuwa, ta cire dogon hijabin dake jikinta ta ninke shi ta ajiye cikin kwaba, sannan ta juyo inda Kainat ke zaune tana kallonta cike da mamaki. Saida ta nannade daddumar da tayi sallan a kai, sannan ta sami guri kusa da Kainat ta juyo tana kallonta tace

"Yanzu ya dace kiyimin wannan maganan amma muje falo ,Anees tana barci"

Baki Kainat ta buɗe amma babu abunda ya fito. Tsananin mamaki ya saka ta saki bakin tana kallon Jaleela. Wai Jaleela nada irin wannan addini take wannan mummunan dabi'u?. Ita kuwa wane irin mummunan iftila'i ne ya sameta haka take irin wannan rayuwar?. Duk abunda take haka, baisa ta manta da ibada ba. Falo suka fito Kainat ta wuce kitchen ta deb'o musu drinks da gashin kaza . Bayan sun nutsu take gaya mata kamun da tayi mata.



DUBAI /ABU DHABI.


THE PALACE.


Katuwar masarautace da aka zuba mata dukiya kace baza'a mutu ba. Komai na masarautar tun daga wajen sa har cikin sa anyi sa da zenare da crystal stones. B'arin KING LK kuwa da daimons aka kerashi kace ruwan su ake. Kowa yasan Abu Dhabi shine b'angaren da dukkanin wani hamshakin mai kuɗi na duniya ke yada zango a Dubai ,wasu ma suna da gidaje na kansu a can, saboda Abhu Dhabi shine k'arshen gari na masu kuɗi. Kyakkyawar macece da bazata haura shekara 40 ba cikin wani tankamememen falo da aka k'awata da abubuwan more rayuwa. Tana zaune ne cikin wata lallausar kujerar mai tsananin taushi da akayi wa ado da zinare. Gefenta a tsaye,kuyangi ne wasu na mata firfita duk da cewa akwai Ac ta ko wane lungu da tsako na falon da girman sa ya yi wani k'aramin flat house d'in. Falon cike yake da bayi da suke tayi mata bauta. Gefenta yarinyace da bata wuce shekara 20 ba zaune k'asan lallausar kafet wajen kafar ta. Kaman yanda wannan babbar mata ke sanye cikin alkyabba ta sarauta data sha ado da zinare, haka itama yarinya. Daga gefen matar wasu manyan dattijai ne guda biyu zaune cikin kujeru dake fuskantar ta.

Numfashi ta sauke mai k'arfi tana k'ara bin dattijan da kallo, kafin ta mayar da ido kan yarinyar dake zaune wajen gefen k'afar ta. Numfasawa ta k'arayi ta buɗe baki tana magana da muryar ta mai sanyi da dad'in sauraro da harcen larabci.

"Anya kuwa wannan abu mai yiwu wane?. Kar ku manta irin kalubale da muke fuskata cikin wannan masarautar duk lokacin da wannan abu ya faru. Mata da yawa, rayuwar su ta salwata saboda wani sirri da mun kasa gane masa. Kuna ganin babu cutarwa cikin wannan LAMARI idan aka sake tafka wannan kuskure a karo na hud'u?"




To fa wane sirrine wannan? Wannan tafiyar ta dabance. Kudai ku cigaba da bibiyar alkalamim Ashantylove. Kafin muyi nisa wannan littafin PAID BOOK ne. Zaki iya fara biya tun tafiyar bata fara zafi ba @ 500N kacal. Domin neman k'arin bayani ko tuntu'beni a wannan number

👇

08140754777







𝗚𝗨𝗗𝗨 𝗡𝗔
𝒜𝓀ℯ 𝓎𝒾.





𝓐𝓼𝓱𝓪𝓷𝓽𝔂 𝓵♡︎𝓿𝓮







11/15.





Balaraben dattijan daya fi kusa da ita, wanda ke sanye cikin bak'ar alkyabba da rawani kaman yanda malamai suke. Hannun sa carbi ne kato mai d'auke da sunayen Allah. Saida yaja dogon salati da yin istigfari sannan yace da harcen larabci.

"Hak'ika kin kasance Malika, sarauniya mai adalci da kuma tausayin talakawan ta. Kin kasance sarauniya dake sauke nauyi da Ubangijin sammai da kassai ya baku, bawai don kunfi sauran bayin sa ba, sai dan hakan yana daga cikin hikima irin tasa. Hak'ika Ubangiji bai hallici ko wane bawa ba ,saida ya rubuta masa kaddarar sa. Wannan kuma na daga cikin jarabawar ku"

Shiru ya yi yana d'an jan fasali. Wani bafade dake gefen sa, ya yi maza ya zuba masa ruwa cikin wani irin glass cup mai kyan gaske ya miƙa masa cikin girmawawa. Karb'an ruwan ya yi ya d'an jik'a makogaro sa. Malika dake zaune tana sauraran sa, ta sauke numfashi. Allah kaɗai yasan abunda ke ranta. Juyowa mutumin ya yi sosai yana fuskantar ya cigaba da cewa

"Tabbas Abu Sufyan da y'ar sa Aafiya sunsan kalubale da ake fuskanta cikin wannan masarauta. Ba suzo nan ba saida suka tabbatar da dukkanin wani jita-jita da ake yad'awa , walau gaskiya ne ko k'arya . A shirye suke wajen ganin sun tayamu yak'i da wannan b'oyyeyyen sirri da muka kasa gane masa. Sun kasance d'aya daga cikin dubbunnan Al'umma dake da burin ganin wannan masarauta mai Albarka ta had'a zuri'a dasu, du da sanin su na cewa rayuwar ya'yan su, ko su kansu ya'yan na iya salwanta.

Yareema mai jiran gado dole yana buk'atar mace da zata taimaka masa kan wannan karaga ta MULKI. Lokaci na ja, lokaci na tafiya. Yanzu ne lokaci daya dace Yareema ya hau Mulki. Shine kad'ai ya cancanta domin shine ya kai wannan munzali ba kannen sa ba. Ya kamata Malika ta huta da dawainiya da dubbunnan Al'umma dake wuyanta. Ta sauka ta bawa Yareema mai jiran gado. Haka zamuyi hak'uri mu cigaba da kawaiwa Allah kukan mu har zuwa lokacin da zai yaye mana wannan musifa. Aafiya a shirye take don zama dashi da jure dukkanin wani kalubale da zata fuskata. InshaAllahu zamu samu nasara nan bada jimawa ba. Mu dage dayi masa Addu'a da yawanta sadaka har Allah ya kawo mana mafita"

Shiru falon ya d'auka baka jin komai sai k'arar Ac da saukar numfashin sa. Manyan idanuwanta dake b'oye cikin farin glass Malika ta lumshe. Saida ta d'auki sama da minti biyu a haka tana tunanin da Allah kaɗai ya sani. Cikin nutsuwa ta k'ara gyara maza ta buɗe idan nata a hankali ta watsa su kan Aafiya dake zaune gefen ta. Magana tayi da murya mai taushi. Kai kanajin yanda tayi maganan kasan sarauta an gaje ta ciki da waje.

"Aafiya "

Ta kira sunanta. A hankali Aafiya ta d'ago kai da girmawawa har tana d'an yunƙurawa. Ido Malika ta zuba mata. Tabbas Aafiya yarinyace kyakkyawa san kowa kin wanda ya rasa. Bazata so ace yarinya k'arama kaman wannan ta had'u da wannan cruel fate ba da saura mtan da suka zo cikin masarautar nan, kaman dai yanda Aafiya sukayi da mahaifin ta.

"Kina san ibni?"(D'a na?)

Kai Aafiya ta k'ara d'agawa a kunyace.

"Zaki iya zama dashi duk da sanin ki na abunda ke faruwa matsawar ki ka aureshi?. Duda da kinsa cewa zaki iya rasa rayuwar ki?"

Nan ma dai kai Aafiya ta k'ara d'agawa. Ido Malika ta zuba mata cike da nazari. Hak'ika tana cikin mamakin yanda mata ke sadaukar da rayukan su a kan d'an nata shi kuma sam basa gaban sa. Tana burin d'an nata ya yi aure ya hayayyafa don cigaba da gina wannan masarauta data taso tun kakanni daga zuri'ar su. Kai ta d'an jinjina ta juyo da kanta wajen Abu Sufyan.

"Abu Sufyan "

"Na'am ya Malika"

"Kaji ka aminci kuma kayi Na'am da wannan abu?, idan har kana da ja zaka iya magana. Aafiya y'ar kace babu wanda ya isa da ita kaman kai. Ka yarda ta kasance matsayin matar d'ana LAMEEN KHALELULLAH?. Sarauniya a wannan masarauta?"

Da girmawawa sosai yace " Na'am ya Malika "

Numfashi ta k'ara saukewa ta mayar da idonya kan Wazir dake gefenta.

"Ayi shela da sanarwa cikin satin nan Yareema zai sake aure. Ayi sadaka ta Shanu da rakuma na dubu hamsin, da kuma sauka sau hamsin don samun nasara da kuma kariyar ubangiji"

Murmushi ne kwance kan fuskar Wazir da Abu Sufyan har Malika ta miƙe don barin fadar. Kallon Wazir tayi da Abu Sufyan da suka rungume juna bayan sunyi musa baha na taya juna murna kaman yanda Larabawa ke yi. Kai ta d'aga musu ta wuce bayin ta da fadawan ta suka rufa mata baya. Wata had'addiyar lifter dake cikin falon ta glass da aka kawata da gwal ta shiga ita kad'ai sai wata baiwa dake binta duk inda tayi. Sauran suka shiga wata dake jikin wannan. Hannu ta kai a hankali ta dafe goshinta da take ji kaman zai rabe biyu ,sosai take cikin damuwa da tunanin kaman sun k'ara tafka wani kuskuren babba. Tana fargabar abunda ya faru da sauran matan da Yareema ya aura, ya faru ga Aafiya . Duk cikin yaran dake rububin zuwa ,bata san me yasa ba Aafiya tafi kwanta mata a rai. Ko dan hakan yana da nasaba da hankali da kuma tarbiyar da take tunanin yarinya na tare da ita ne?. A hankali ta furta a fili

"Ya rabbil samawati, ya ubangijin sammai da kasai. Ya ubangijin dukkanin wata halitta. Mutum ko Aljan. Ya wanda ya halicci ruwa, ya halicci iska, ya halicci wuta da Aljanna. Ya Zuljalalu wal Ikram. Allah ka kawo mana mafita cikin wannan sark'arkiya da bamu da amsar ta. Allah ka kawo mana k'arshen wannan musiba. "

Baiwar dake kusa da ita ta amsa da Amin cike da tausayin uwar d'akin nata. Hak'ika tun tasowar ta cikin masarautar nan taga irin gwaggwarmaya da SARKI KHALELULLAH ya yi da matarsa MALIKA, ARWA . Tasan dukkanin wani kalubale da jarumta da sukayi wajen ganin sun gina wannan masarauta mai Albarka. Taga irin jarumta da Malika tayi bayan k'asa ta rufewa SARKI KHALELULLAH ido. Irin dawainiya da take da ya'yan ta da mutane wajen basu kulawa da kariya daga dukkanin wani sharri da kalubale na rayuwa. Na ciki dana waje. To amma Yareema yana tare da wani sark'arken abu da an kasa gano masa. Anyi maganin sammu, anyi na aljanu. Amma an kasa samun nasara. A yanzu kam Addu'a ce kawai ake yi da yawan sadaka Allah ya warware koma menene. Ita kanta tana tausayin Aafiya.



ABUJA.



To Jaleela dai kam an zama mutanen Abuja. Duda dama Abujan ba bakon ta bane. Sai dai zuwanta yanzu ,Kainat tayi yawo da ita sosai cikin garin Abuja musamman clubs dake ci sosai na manyan yara. Tunda suka zo take ta fad'i tashi wajen ganin ta mayar da Anees makaranta. Yarinya har sukayi kwana biyu ta kasa daina kunci ,sam taki walwala. Abun tun baya damun Jaleela har ya fara damunta. Don haka yau ta d'auke ta suka dinga yawo Park,Parks da mall don ganin tayi walwala. Ai kuwa Anees tafi kowa farin ciki. Rabon da Jaleela taga farin ciki kan fuskar yarinya kaman haka harta manta. Sannu a hankali ta fara warwarewa musamman yanzu data fara zuwa makaranta tayi kawaye sosai. Kowa yana son ganin ya zama abokinta saboda kyau da Allah ya bata ga masifar k'ok'ari.

A b'angaren Jaleela itama abun haka ne. Don yanzu dukkanin wani clubs da suke zuwa ita da Kainat tayi suna. Sunanta na clubbing shina LA REINA ,the cold Beauty. Ba ko wane namiji ne yake cire tuta a kanta ba sai ta zaba ta dirje kafin kace me,kuɗi sun fara zamarwa Jaleela tana wadaka dasu sai abunda taga dama. Nanny guda ta d'aukowa Anees dake kulawa da ita idan basa nan, duk da cewa basa fita sai ta tabbatar Anees tayi barci haka nan duk inda take, duk inda hud'u na asuba tayi zata dawo kafin Anees ta farka. Ciki kwana biyun nan ma basu cika had'uwa da Kainat ba saboda tayi busy sosai da wasu alhazawa da suka zo Nigeria.
Ita dai Jaleela nata harkan bata bada kanta. Zatayi maka dukkanin abunda ka ke so amma baza ka tab'a ba tare da kasa ko yatsa a jikin ta ba. Wannan shine sharad'in ta. Abunka da mai kyau a guje mazan ke k'arban wannan offer, sudai indai zasu huta ai basu da matsala. Can k'asan zuciyarta tana kyamar wannan abu da take. Kai su mazan ma gaba d'aya ta tsane su , don namiji shine SILAH na fad'awarta cikin wannan halaka. A ganinta wannan abu da take shine kad'ai zai bata damar da zata bawa Anees rayuwa mai kyau. Dukkanin wani abu da zatayi gani take baza ta samu ba kaman yanda take samu haka ,bare har ta gina musu rayuwa mai kyau. (To amma kin manta kuɗi irin wannan basu da Albarka tunda ba ta hanyar mai kyau aka same su ba).

Yau asabar daga ita har Kainat suna gida. Gaba d'ayan su suna falo ne. Jaleela na kwace cikin katuwar kujera sanye da riga da wando pink color. Anees na sanye cikin wata y'ar k'arama gown silver mai hoton unicorn a jiki. Kanta an rabashi biyu an kamshi gefe da gefe. Kainat kuwa n kwance kasan kafet tana mafa da waya daga ita sai y'ar doguwar riga mara nauyi. Ihu tasa ta miƙe tana zare ido a waje. A kasalance Jaleela ta kalleta ganin yanda duk ta rude riƙe da waya baki a hangame. Anees tace

"Aunty Kainat, menene? Ko kinga dodo ne a wayar?"

Dariya Kainat ta saki a hanzarce tace da Anees.

"Baby jeki d'aki ki d'aukomin laptop d'ina kinji y'ar Albarka "

A guje Anees ta ajiye Teddy da take wasa dashi tayi d'akin a guje. Da azama Kainat ta taso ta zauna kusa da Jaleela dake kallonta. Saida ta nuna mata wayar hannun ta tace

"Gaskiya ke ko, ta dabance wlh. Labarin ki kawai yaji yake nemanki ruwa a jallo. Kinsa waye yake nemanki kuwa? Yanzu nan Khairat ta turo min. Kin san waye? ZAIN"

Ta fad'i sunan da k'arfi. Tsaki mai k'arfi Jaleela ta yi tace

"Waye kuma haka?"

Ido Kainat ta waro harda d'aka mata duka

"Zain ne baki sani ba?, d'an minister babban likita dake zama a turai. Ance yazo gari yaji labarin ki shine yace yana son had'uwa dake. Ko kinsan irin sa'ar da zaki taka idan ki ka kasance dashi?. Mata da yawa suna mafarki a kansa da burin kasancewa dashi kona rana d'aya ne. To ganin sa ma wahala yakewa mutane bare ka same shi. Kaman yanda ki ke juya mutane shima haka yake dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login