Showing 6001 words to 9000 words out of 25334 words
yaga yana da kyau. Ga kuɗi, ga kyau, ga aji, ga class. Haba wlh kedai kina da sa'a, manyan yarane kawai ke binki, ko da yake kin cancanci hakan ne don duk yanda mutum zai kiyasti ki kin wuce haka"
Baki Jaleela ta tab'e cikin ko in kula tace
"Bani da lokacin sa"
Kainat ta buɗe baki zatace wani abu Anees ta fito a guje da laptop d'in datace ta d'auko mata. Dole ta taune harshe tayi shiru da maganan, amma ta kudurta a ranta dole nema ta had'asu. Itama ta yagi abunda zata yaga Jaleela baza tayi mata bak'in ciki ba.
𝗚𝗨𝗗𝗨𝗡𝗔
𝒜𝓀ℯ.
𝓐𝓼𝓱𝓪𝓷𝓽𝔂 𝓵♡︎𝓿𝓮
16/20.
Tsawan kwana biyu Kainat nayin dukkanin iya bakin k'ok'ari wajen ganin ta shawo kan Jaleela sunje club d'in da take tunanin Zain na zuwa, fafur Jaleela tak'i kwana biyu ma babu inda taje ta mak'ale a gida wajen Anees. Duk hanyar da Kainat ta biyo Jaleela zata toshe dole tayi shiru ta zuba mata, amma k'asan ranta tana had'a plan. Saida tasan yanda zatayi ta samu number Zain. Da farko tayi masa kiran duniya yak'i d'agawa saboda isa. Haushi kaman ya kashe Kainat. Batayi k'asa a gwiwaba ta tura masa sak'o cewar ita tasan yarinya da yake nema La REINA, the cold Beauty. Zata had'ashi da ita amma sai ya bata kaso mai tsoka.
Lokacin da sak'on ta ya shigo wayarsa yana kwance ne cikin tamfatsetsen d'akin sa da aka kashewa dukiya. Gajeren wando ne a jikinsa da single. Zain kyakkyawan mutum ne irin handsome black beauty d'in nan. Yana da manyan lumsheshshun idanuwa da dogon hanci ,bakin sa irin full d'innan ne dake nan jazur dashi ,kuma very oily kaman wanda ke shafa masa man leb'e. Zain yana daga cikin irin mazannan da za'a kira tsaka-tsaki a fannin tsayi. Yana da murdadden jiki burin ko wace mace. K'irjinsa kuwa cike yake da gashi yala-yala daya kwanta tsam gwanin sha'awa. Haka fuskar sa kewaye take da dan siririn gashi daya zagayo har zuwa bakinsa. Ana kiran irin wannan gyaran fuska da kwata million. Zain kan abun MashaAllah don ya gama had'ewa ta ko wanne fanni. Bak'ar fatarsa da taji hutu da kuɗi sai shek'i take irin ta aje butters. Ga fatar tasa da mugun laushi kaman mace. Bashi da gashi sosai a kansa don gashinsa irin namu ne na malam bahaushe, amma saboda gyara da mai da kan kesha gashin ya kwanta lum kansa, ya nannade kace hula ya d'ura.
Hankalin sa da nutsuwar sa gaba d'aya yana kan laptop nashi ne yana duba wani file da aka masa transfer na wata mata da tayi mummunan had'ari a can CALIFORNIA. had'arin ya yi muni da dole ake buk'atar manyan likitoci surgeon's don su dukafa a kanta, wajen hatsarin da tayi ne wani irin rodi mai tsananin k'arfi ya huda ta kasan habarta ya bullu ta saman kanta. Kana ganin kwakwalwarta dake motsi ga jini dake fita ta kan nata yana tsartuwa kaman fanfano. Likitoci sun had'u sosai a kanta wajen ganin an bata taimakon gaggawa, duk da cewa da yawa suna tunanin bazata kai ko ina ba. Sai akayi rashin sa'a Zain baya k'asa lokacin da abun ya faru. Da za'ayi mata aikin sai Zoom call akayi dashi yana ganin yanda abun ke gudana yana bada taimakon da yake ganin ya dace. Cikin ikon Allah kuwa aka cire k'arfen amma saida aka kwana aka wuni sunayin. Yanzu matar tana kan bed rest ne don ta shiga coma.
Bayan samun nasara na wannan babban aiki da akayi. Tun dawowar sa bai fita ba sai ranan ya shirya don samun fresh air. Bayan zuwansa club d'in ne yaji maza na magana kan Jaleela, da yanda suke buri ganin sun samu lokacin ta kona awa d'aya ne. Amma ita d'in wuyar samu take sai ka ajiye kwalitis da take so. Yanda yaga mazan na hauka a kanta duk inda ya wuce maganan The Cold Beauty suke. Hakan yaji shima yana da interest a kan wannan yarinya. Baiyi zaton zataki amsar tayinsa ba duba da matsayin sa da yanda mata ke hauka a kansa. Saboda wannan ja masa class da take yaji interest nashi a kanta ya kara picking.
Murmushin gefen baki ya yi bayan ya gama karanta sakon Kainat. A take ya bata amsa yace ta turo account nata zai saka mata kuɗi. Yana ajiye wayar aka buga k'ofar d'akin nasa aka shigo. Yarinya ce ta shigo da bata wuce shekara 18 ba. Kyakkyawace ta gaske Black beauty. Kallo d'aya zakayi mata kasan sun had'a alaka da Zain. Manyan idanuwansa ya d'ago ya watsama mata ta shigo rik'e da tray dake d'auke da wani bowl na fruits da shawarma sai zuba kamshi take. A kunyace ta ajiye kayan kan tebir saboda irin kallon da Zain ke jefanta da shi. Kusa da gadon ta samu guri ta zauna tana murmushi tace
"Barka da rana Ya Zain. Ga fruits na kawo maka nasan kayi aiki ka gaji"
Wani irin killer look ya bata yana murmushin gefen baki ya ajiye laptop din dake cinyarsa. Murya so sexy yace
"Thank you my dearest, yaushe ki ka zo?"
D'an far tayi da ido a dan shagwaɓe tace " ba tunda ka dawo ka ki zuwa mu gaisa ba?, to ni na biyoka har gida"
"Sorry tunda nazo ban zauna bane. How is Uncle?"
Tana wasa da yatsun hannun ta tace
"Yana nan lfy. Tare muka zo"
Kai ya jinjina ya d'auko abincin yana ci . Sosai suke jefin juna da wani shirtaccen kallo kai kana gani kasan ko wanne da matsayin daya ajiye d'an uwansa. Ayush y'ar k'anin babansa ce. Kaf family na mai tangaran. Wato minister an san yanda Ayush da Zain suka shaku da juna tun suna yara. Saboda wannan dalili yasa iyayen suke yanke had'asu aure. To amma daga Zain har Ayush babu wanda yasan da wannan batun. Dukkanin su ,su biyun babu wanda ya furtawa d'an uwansa kalman so.
B'angaren Kainat tana ganin sak'on ta daka wani tsalle da ihu. A gaggauce ta tura masa account number nata da kuma ranan da zata kawo masa Jaleelan har inda yake. Kaman yanda Kainat d'in ta shirya Plan nata. Yau rana ta juma'a da safe misalin k'arfe takwas ta fito cikin shiri. Falo ta sami Jaleela da Anees na karyawa. Anees shirye cikin kaya na makaranta. Kaman yanda Jaleela ta koyar da ita yarinya da ladabi ta gaisar da Kainat. Murmushi Kainat tayi ta shafa kanta tana tambayar yanda ta tashi. Zama itama tayi suka karya tare suna gamawa suka fito gaba d'aya don kaita makaranta. Bayan sun sauketa Kainat ta juyo ta kalli Jaleela data maida hankali kan tuki tace
"Yau fa ina da wani babban event."
"Na me?"
Jaleela tace ba tare data juyo ba. Kainat ta cigaba da cewa
"Ina wata kwata Cele?. Yau birthday nata za'ayi party a nan club da muke zuwa. Don Allah badan niba ki daure kizo kinga musamman ta gayyace ki"
Shiru Jaleela tayi tana tunani. Itama dai tana san ta d'an fita tasha iska. Kwana biyu babu inda ta leke. Ko wayarta kashewa tayi don bata san damuwa. Saida ta d'an tura harshen ta wajen kuncinta kaman wanda ke hura iska tace
"Zanje"
Ihu Kainat tayi harda d'an rungume ta ta gefe. Tace
"Kai amma na gode. Ga Vip card naki idan kinzo kai tsaye zaki shiga "
D'an k'aramin card ta mik'awa Jaleela . Karb'a kawai tayi ta ajiye bata duba ba. Ran Kainat fari tas ta ajiye ta hanya inda zata had'u da wani sugar Daddy nata. Itama Jaleela wani had'edd'en restaurant tayi ta kebe guri d'aya tana cigaba da tunanin rayuwarta da iyayen ta. Misalin k'arfe goma na dare ta gama shiryawa cikin wata arniyar doguwar riga mai hannu d'aya. Rigar kaman net take tabi dukkanin wani sassan jikinta ta ta kwanta. Gashin kanta ta sake shi ya zubo gadon bayanta. Dogon takarmi ne a k'afarta mai igiya. Kan rigar ta d'ura wata y'ar jacket mai hula dake da gashi. Sosai tayi bala'in kyau ta fito sak baturiya. D'an k'aramin bak'in daya sa janbaki ta motsa tana k'ara kallon kanta cikin mudubi. Kai ta jinjina kanta ta matsa gadon da Anees ke kwance ta k'ara tofeta da Addu'a kafin ta fito daga d'akin. Zaune falon ta sami LAMI dake kula da Anees idan bata nan. Dattijowar mata ce . Mata tana da kulawa sosai ga tsabta. Bacin haka akwaita da ibada. Murmushi Jaleela tayi ta ciro y'ar k'aramar waya ta mik'a mata kaman yacce take duk ranan da zata fita.
"Gashi Mama. Idan kuna buk'atar abu sai ki gaggauta yimin waya koda Anees zata farka"
Kai Lami ta d'aga ta karb'i wayar cikin girmawawa. Sallama Jaleela tayi mata ta wuce Lami ta bita da kallo ciki da mamaki da Allah wadai irin wannan rayuwa. Tana mamakin rayuwar da Jaleela ke yi. A haka kana kallonta kallon salihar mace zakayi mata. Don tana da hankali ga nutsuwa da tausayi, bayan haka kuma ga tsananin ibada. Dazu tana jin yanda take rera karatun Qur'ani kaman wata Sudais. Amma yanzu ji irin shirgar da tayi ta fice da wannan tsohon daren. Ita kuwa wane iftila'i ne ya sameta haka harta jefa kanta cikin wannan halaka?
Kai ta girgiza ta miƙe ta shige d'aki da Anees ke kwance. Saida ta k'ara gyara mata kwanciya tayi shimfiɗa nan kasan kafet ta kwanta cike da tausayin yarinya da irin rayuwar da uwarta take. Don ma taga Jaleelan na sauke dukkanin wani nauyi da Allah ya d'ura mata na uwa .itace uwa itace kuma uban. Tana kuma yin bak'in k'ok'arin ta wajen ganin ta ginata bisa tarbiya mai kyau. Har yau bata tab'a kawowa ranta cewa Anees bata hanyar sunna aka same ta ba.
Sha d'aya daidai tayi fakin motar ta harabar club din. Tun daga wajen sa mutane keta kai da kawo kace safiya ce. Club din yau a cike yake tam da manyan yara,maza da mata. Kota ina fitilune kaman rana. Guri ta samu wajen su dank'ara-dankaran motoci da ganin irin su a nan sai a kashashen waje. Haka nan kawai taji k'irjinta ya d'an buga tana k'arewa motocin kallo. Juyawa tayi yaga yanda da yawa duk ji da kuɗin su motocin suke kallo suna musu hoto, babu wanda ya iya matsawa jikin su saboda wasu shegun Bodyguards dake jikin motocin da suit a jikinsu fuskar su rufe da mask ,baka gani komai sai idanuwansu. Harta hannunsa bakaken safe ne. Kana ganinsu kasan ba hausawa bane don yanda suke a murde. Idanuwan su kad'ai ya isa ya saka fitsari a wando saboda yanda suke jefan mutane da wani deadly glare. Kana gani kasan wannan Bodyguards abun tsoro ne.
Ji tayi kaman ta juya,amma ita tana daga cikin mutanen nan da suka d'auki alkwari da muhammaci. Numfashi ta fesar a hankali ta buɗe murfin motar ta fito. Ai kuwa ido ya yi caa a kanta bata bari kallon ya dameta ba ta taka a hankali ta shige club d'in. Saida ta fara zuwa gurin Bartender ta nuna masa katin. Da d'an mamaki ya nuna mata hanyar da zatabi ta wuce mutane dake kallonta. Wasu na rawa ,wasu na zaune suna shaye-shaye. Y'ar corridor tabi mai dan tsayi sai gata ta bullo wata k'ofa da samanta aka rubuta VIP LOUNGE. Babu tunanin komai ta kama k'ofar ta kutsai ciki. Abu na farko daya fara dukan fuskata shine wani irin kamshi da tsananin sanyi daya ratsa ta. D'akine hadadden gaske da aka kwata da kayan more rayuwa. Kana ganin d'akin kasan ba kowa ke iya book nashi ba sai d'an wane da wane shima sai ya kai ya wuce. Da d'an mamaki take bin d'akin da kallo sam bata kula da wasu tsumammun deep black eyes kaman midnight da suka kafeta ba. Baki ta d'an buɗe da mamakin ina mutanen kuma nan babu kowa. Sannu a hankali ta fara yin k'asa da idonta har suka sauka kan wannan black eyes d'in daya d'aga gira cikin matuƙar confusion yana kallon ta.
Dukkanin wani noti dake kanta kuncewa ya yi numfashi ta ya tsaya cak lokacin da idanuwan su suka sarke da juna. Idonta ya yi wani irin buɗewa so wide da sai ka tsorota. Kace mutuwa ta gani.Shima nashi b'angaren matsanancin mamaki ya rufesa yana kallonta. Da wani irin mugun slow gefen bak'in sa ya yi wani irin coiling da wani irin creepiest way ya saki Smirk. Cikakkayar girar sa ya d'aga guda d'aya murya so ,so deep and husky yace
"You"
......
😁finally ooo.
Kina so a tallata miki Hajar ki @ affordable price?.
Chat me up
👇
08140754777
𝗚𝗨𝗗𝗨 𝗡𝗔
𝒜𝓀ℯ .
𝓐𝓼𝓱𝓪𝓷𝓽𝔂 𝓵♡︎𝓿𝓮
21/25.
Yanda ya kira ke d'in sai tsigar jikin ka ta tashi kaji kaman ka buga kai jikin baango tsaban creepiness. Jaleela bata san sanda ta juya da wani bala'in gudu ba har tana yarda wayarta da jakarta dake hannun ta. A guje ta fice wani irin kuka ya kwace mata. Yanda ta fito kaman mahaukaciya ya bawa mutane mamaki suka bita da kallo. A guje ta fice daga club d'in ko takan motar ta bata bi ba. Haka tayi ta shek'a gudu kan titi tana kuka kaman hauka sabon kamu. Duk wanda ya tsaya don taimakon ta idan yaga yanda duk ta firgice sai ya tsorata ya kasa mata magana. A guje zasuja motar su. Da yawa ma suna tunanin ko gamo sukayi. Gabas kawai ta saka a gaba bata tsaya ba saida ta ganta k'ofar gida.
B'angaren wannan mysterious mutum wani irin miƙewa ya yi majestically ya tako inda ta tsaya. A hankali ya sunkuya ya d'auki jakarta data yasar yana juyata cikin tafin hannun sa dake sanye da safa. Sunkuyun da ya yi lallausan gashin kansa ya zubo ya rufe masa ido. Mugun smirk ya saki murya so husky yace
"So..... finally after all those year, we meet?. Who could have thought The world is too small" ya k'arasa yana wani irin chuckling.
K'ofar banɗakin da aka buɗe yasa ya d'aga ido a kasalance ya watsawa Zain daya fito yana goge hannu da d'an k'aramin tawol. Gira ya d'aga yana kallon Zain ta gefen ido.
"What?"
Zain yace yana k'ok'arin zama. Wani irin chuckling ya yi ya miƙe rike da pose d'in ya dawo ya zauna kusa da Zain yana kallon sa.
"Your Babe. She just left"
"What?"
Zain yace yana zare ido ya yi saurin warce jakar daga hannun sa. A hanzarce ya fice daga d'akin ya bishi da manyan black eyes nashi yana mugun murmushi. Da saurin Zain ya fito har harabar gurin amma ko kurar ta bai gani ba. Baki ya cije rai a b'ace ya koma lounge nasu. Yanda ya barshi haka ya same shi zaune lazy kan kujera ya d'ura hannuwansa kan kujerar ya kafe k'ofar da sexy eyes nashi. Mugun kallo Zaid ya watsa masa
"Me kayi mata?"
Y'ar gira ya d'aga kafin ya saki y'ar deep dariya da dimples nashi suka lotsa. Oooh wannan mutum is a very sight to see. Baza kasan sanda ka ke dilalar yawu ba idon kana kallonsa. Da deep voice nashi yace da hausar da bata fita sosai
"Ni kuma? Ask her mana. Me yasa daga ganina ta tsorota ta gudu, kaman wacce taga wani mugun abu? "
Smirk d'in daya saki zaka san akwai meaning bayan maganan da ya yi. Numfashi kawai Zain ya sauke. Duk lokacin daya d'auka yana jiran wannan rana in the blink of an eye komai ya wargaje. Zama ya yi gefen sa yana kallon yanda ya koma ya kwanta ido a lumshe, har zuwa lokacin da murmushi kan fuskar sa. Tunanin abunda ya kawo shi Nigeria ma yau d'in nan yake.
2 DAYS BACK .
kwana biyu da suka wuce.
ABU DHABI.
Kaman yanda Malika tasa ayi shela, hakan ne ta kasance. Cikin d'an k'ank'anin lokaci labarin auren LK da Aafiya ya baza Abu Dhabi. Da yawa suna cikin jimami da tunanin yanda makomar Aafiya ita ma zata koma. Kaman sauran matan da Lk ke aura, itama Aafiya gagarumin biki Malika ta fara shiryawa. Dukkanin wasu dangi na b'angaren Aafiya da Lk sun hallara cikin wannan katuwar masarauta. An fara shagali bikin irin nasu na larabawa ta ko wanne fanni. To amma shi wanda ake abun domin sa yana can MALIBU baisan abunda aka be. Sai bayan an d'aura aure Malika ta tura kannan sa da suke twins. Aizak da Aryan suka je suka tisoshi a gaba. Bai san da zancen bikin ba sai da daddare ya kebe cikin d'akin sa.
Had'addiyar black suit dake jikinsa yake cirewa a hankali cike da kasala. Wani irin ingarman namiji ne majiyi karfi. Koya ya motsa jiki sai kaga damtsen nan sun motsa. Dogon gashin sa dake tufke a tsakiya kansa ya kai dogayen yatsun sa ya cire band d'in. Kaman ruwa gashin ya biyo ya kwanta wuyansa luf mai tsananin laushi da tsantsi gashi bak'i sid'ik. K'ofar d'akin sa da yaji an buɗe alamun an shigo baisa ya juyo ba saida ya kama farar rigar dake cikin suit d'in ya fara cirewa. Jin shirun ya yi yawa ya wani irin juyowa a hankali yana balle ragowar botirin rigar da ya yi saura. Numfashin Aafiya ya wani irin tsarkewa lokacin da kwayar idonta ta fad'a cikin midnight Black nashi. Kut ta had'iye yawu. Hak'ika waya da labarai basa masa adalci sam. Don yanda ta gansa haka a zahiri , Sam ba'a kwatanta irin matsanancin kyau da Allah ya bashi. Mutum kaman shi ya yi kansa. Jan wani irin numfashi tayi sanda kwayar idonta ta sauka fatar cikinsa dake uban shining ga wasu uban 8packs kace zanasu a kayi. Kut ta k'ara had'iye wani yawun. Sannu a