Showing 15001 words to 18000 words out of 25334 words

Chapter 6 - GUDUNA AKE

10 Sep 2025

2047

bita da kallo da jajayen idonsa. Saida ta saka Anees cikin mota ta zagaya zata shiga ta tsinkayi maganan.

"You just make thesame mistake da ki ka yi before. So watch out for me"

Sosai maganansa ya bata chill har cikin bargon jikinta, bata juyo ba ta fad'a cikin motar da sauri ta fisgeta a guje ta bada masa kura da sauran mutane da suka tsaya kallo. Yanzu wannan mutumin tsoro yake bata. Maganan gaskiya bazata iya cigaba da zama nan ba matsawar yana nan. Mutum kaman aljani. To wai taya yake iya shiga yake d'auke Anees da zarar ta ajiyeta? Kuma yake dawowa da ita ta d'auke ba tare da kowa ya lura ba?. Anya kuwa mutum ne?. Numfashi ta k'ara saukewa ta kalli Anees dake rungume da wata katuwar pink Teddy Bear. Yarinya tayi wani irin shiru kaman mara lafiya da alamun bataso rabuwa da Mutumin ba. Bazaiyiwu ba dole ma ta gaggauta nesanta Anees dashi. Tanaji tana gani bazai kwace mata yaba. To yanzu ina zataje?. GIDA . Zuciyar ta ta bata amsa. Hawaye suka wanke mata fuska ta k'ara maimaita GIDA kan leb'enta hankali .

Shikam ya jima a tsaye kafin ya buɗe motar ya zauna a baya. Jingina ya yi kujera ya maida idonsa ya lumshe yana wani irin numfashi a hankali.

'InshaAllahu yanda ka shiga rayuwarta ka hanani samun nutsuwar zuciya da kwanciyar hankali, sai Allah ya jarrabeka da kwatancin uk'ubar rayuwa daka jefani. Duk wani hali dana shiga kaine sanadi kuma bazan tab'a yafe maka ba. Ka fita daga rayuwata dana y'ata '

Maganganun ta suna tayi masa yawo a kunne. What did she mean by that?. Zain dake zaune wajen direba ya juyo sosai yana kallonsa. Yau daga shi sai Zain ne suka zo saboda ya sasu suna investigate na wasu da yake tunanin suna bibiyar Jaleelan da bata sani ba. Target d'in nasu kuma yaga kaman kan Anees ne. Abunda Jaleelan bata sani ba tun ranan dukkanin wani motsin ta a tafin hannunsa yake. Yasan dukkanin wani abu da ita kanta Jaleelan bata sani ba. Wasu mutane ya gani suna binta kullum zata kai Anees makaranta. Idan ta sauke ta zasu faka motar suna tunanin yanda zasu shiga su karbo Anees. Ranan daya tabbatar da zarginsa ya shirya Plan nashi perfectly. Da zarar ta sauke Anees kafin kowa ya ganta yaronsa da yake ciki yana jiranta zai fito masa da ita. So she kansa baisan why yake protect na yarinya daya tsani uwarta ba. But he can't help the feeling da strange connection da yake ji duk sanda yaga Anees ko ya yi kusanci da ita. Ya barwa kansa yana protect nata ne saboda yarince dake so innocent and pure koda kuwa bata hanyar Sunna aka same taba. Jan numfashi ya yi ya kai hannu a hankali ya shafa fegen fuskarsa data mara.

'But hannun ta is so soft '

'What?, dude no'

Murmushi ne ya kufce masa jin yanda yake fad'a da zuciyar sa shi kad'ai.

"King ka sani a duhu. What is going on ne ? Dama ka santa ne har ta iya daga hannu ta mareka and you did nothing?"

Idonsa dake lumshe ya ware su kan Zain dake kallonsa cikin rashin fahimta. Zubawa juna ido sukayi yana karantarsa sosai yake hango damuwa cikin kwayar Zain d'in. Kaman bazai bashi amsa saida ya maida idonsa ya lumshe sannan yace

"She's that girl 7years ago"

Sosai zain ya ware ido waje. Itace wannan yarinya data tab'a marinsa shekarun baya da suka wuce tasa ya yi abunda ba halinsa ba. This life is so scary wlh. A hankali ya sauke numfashi yanajin wanj irin nauyi a k'irjinsa. Yanzu daya k'ara ganin Jaleelan a fili he can't deny da sudden attraction da yake a kanta.

"Follow her"

Bai musa ba ya tada motar ya harbata kan titi. Jaleela na fakin motar ta harabar compound na gidan Zain ya danno da Prado tasu ciki. Saida k'irjinta ya buga ta fito da sauri ta suri Anees zata shige gida a guje. Saidai tana buɗe k'ofar shima ya kawo hannu jikinta. Bai jira ta juyo ba yace

"Ki same ni address dana baki yau By 7p.m. "

Bai jira tace komai ba ya juya ya koma mota. Numfashi ta sauke mai zafi ta k'ara matse Anees jikinta. Tana kallo suka fice ta buɗe gidan ta shiga. Tayi decide by seven suka fito da kayanta ta saka cikin booth na mota. Doguwar riga ce a jikinta k'irar Dubai maroon Colour. Anees kuma y'ar kanti ce pitch da tayi mata kyau sosai. Maigadi taba keys na gida suka fice. Address daya bata tayi kai tsaye. Wani tamfatsetsen gida ne Address d'in daya bata nan Maitama. K'ofar gidan cike yake da masu tsaron sa. Abun mamaki tun kafin ta k'arasa aka buɗe mata gate alamun sun san da zuwanta. Wajen fakin ta faka motar ta da already wani yake jiranta. Rik'o Anees tayi suka fito har zuwa bakin k'ofa da zai sadaka da ciki. Bugu d'aya ya yi ya wuce ya barsu a gurin. Saida sukayi sakan biyu a tsaye kafin taji an buɗe k'ofar. Ido suka had'a lokacin daya buɗe sanye da white shirt da black wando. Kansa a jiki yana digar ruwa da alama daga wanka ya fito. Fuska babu wani emotion yace

"Come in"

K'ofar ya buɗe sosai ta rab'a ta shiga riƙe da Anees . Bakin k'ofar taja tungs ta tsaya kai tsaye tace masa

"Gani nazo what did you want?"

A hankali ya juyo ya watsa mata tsumammun idonsa ,maimakon ya bata amsa yace

"Me zaki sha?"

Kaman ta haushi da duka a zafafe ta k'ara cewa

"Kana batamin lokaci. Ka gayamin dalilin da yasa ka ke son ganina anan"

Anees ya kalla dake kellonsa alamu ya nuna tana son zuwa gurinsa. Hannu ya mik'a mata da d'an murmushi yace

"Come here baby "

Ai a guje ta fisge hannun ta daga na Jaleela tayi wajen sa ta d'ane tana dariya. Matuƙar mamaki da aljabi ya saka Jaleela sakin baki tana kallon su. Sumbatar Anees ya yi goshi kafin ta ajiye ta a hankali yace

"Go and play OK. Zanyi magana da Mummy "

Kai Anees ta d'aga da sauri tana cewa to "uncle" sai kuma ta kwasaa guje tayi wata k'ofa kaman ta san inda zata. Baki Jaleela ta saki tana kallon ta harta b'ace. What? .

"Sit down"

Taji muryar sa data dawo da ita daga shock datayi. Tabbas dole ta guje masa as soon as possible.

"Ba zama ya kawo ni ba. Ka gayamin abunda yasa ka kawoni nan"

Ido ya zuba mata na y'an minti baicr komai ba sai kuma ya jinjina kai. Wasu takardu dake kan glass tebir ya d'auko ya yi inda take tsaye ya miƙa mata.

"Hold this"

Kaman bazata karb'a ba ta warce azafafe tanajan tsaki. Tana duba takardun ya k'ara da cewa.

"Ina so muyi aure "

Chak ta tsaya da duba takardun ta d'ago ta watsa masa manyan idonta. Can kuma ta fashe da wata irin dariya kaman mahaukaciya. Baice komai na sai ido daya zuba mata tana dariya harda hawaye. D'an murmushi ya yi dashi kad'ai yasan ma'anan sa. She thinks am playing. Yace a zuci yana murmushi.

"Wayyo Allah " tace tana goge hawaye tsaban dariya kafin ta nunashi da hannu ta nuna kanta.

"Amma dai wannan kan ba d'aya yake ba ko? Ka buga kan naka ne ko ciwon hauka ne ya kama ka? Dawa zakayi auren"

"Hmm"

Ya saki d'an murmushi kafin yace " Kinga wata ne a nan?. See, kar kiji nace muyi aure ki d'auka your something special. Kedin ba komai b'ace sai a desperate prostitute. After all babu wani namiji dazai aure ki in his right mind. So ki dauka favour ne nake miki badan ke ba saidan saboda y'ar ki."

Zafin maganganun sa ji take kaman mashi yasa yake sukanta dashi. Batasan hawaye sun zubo mata ba saida taji digar su. Mutumin daya jefata cikin wannan kaddarar shine yanzu ya yi sanadin da taji ta k'ara tsanan karuwanci da take. Murya na wani irin rawa ta nunashi da yatsa

"Kana ganin laifin waye?. Kaine sanadin dana fad'a cikin wannan halaka. Kai ka lalatamin rayuwa. Da ace ana maida hannun agogo baya dana mayar na goge ranan da zaka shiga rayuwata. Ni karuwance naji amma ina so ka sani ko zan mutu banyi aure ba, da dai na aure ka gwanda na gama rayuwata a titi"

Fuu ta wuce shi tana kuka sosai tayi k'ofar da Anees tayi. Ace katon play ground ne babu abunda baby aciki. Ranan da yafa kawo Anees washegari yasa aka had'ashi saboda ita. Can kan wata mota ta hangota tana yi masu tsoro tsaye lungu da tsako suna bata kariya. A guje ta yi wajen ta d'auko ta fito. Yarinya ta saki kuka dan ko kad'an batasan abunda zai katse mata wasan da take. Haushi ya kama Jaleela ta daka mata tsawa. Kiga daga had'uwa da mutum soyayya da shukuwa mai k'arfi na neman shiga tsakaninsu.? Wai a haka ma don bata san cewa shine ubanta ba?. To da sake. Yana nan tsaye inda ta barshi ta wuce bai motsa ba tayi bakin k'ofa ta buɗe. Saida ta tura Anees waje sannan ta juyo ta kalleshi da wani irin tsana ta sakar masa bomb

"Kuma ina so ka sani. Anees y'ar kace. Flesh and blood. But she's my daughter tun daga farkon haihuwar ta har zuwa yanzu. Nice ubanta nice kuma uwarta. Stay out of our lives."

A hanzarce ta fice ta barshi a tsaye cikin matsanancin mamaki. 'Anees y'ar kace. Flesh and blood' What?. Tsaban yands maganan ta dake shi ya kasa motsi sai k'ofar daya kafe da ido. Magana d'aya ce cikin ransa. But how? Bazai manta ba clear as a day ko a wancen ranan bai kusance ta ba so how is this possible? .sai a yanzu ya yi snap daga shock d'in daya Shiga a guje ya fito daga gidan amma tuni Jaleela ta fice da matsanancin gudu. Numfashi ya fesar mai zafi bazaiyi k'arya ba ya yi abubuwa da ita sosai ranan but he did not go all the way in.

Jaleela dai maimakon tayi gida sai tayi hanyar wajen Abuja kaman yanda tayi kuduri. Sosai take shek'a gudu kan titi don ta tsere masa. Tasan yanzu tunda yaji wannan bomb dole zai biyota gida, inshaAllahu ita kuma ta gama zaman Abuja. Koman dare a yau d'innan ba gobe ba zata koma Gida .zata koma wajen iyayenta.


UNKNOWN


Wani irin d'aki ne mai tsananin duhu da ko tafin hannun ka baka iya gani. Babu windo ko k'ofa a d'akin da wata iska ko haske zai shigo. Haske guda d'aya ka ke iya hangowa kaman dot. Wasu irin eerie red glowing eyes ne masu matuƙar ban tsoro da tsananin hasken su yake dan reflecting a d'akin. Blinking idon sukayi don su kad'ai ka ke iya gani saboda duhu. Direct suka kalli bango sai ga wani irin round mudubi ya nuna a jikinsa. Hasken idon ya yi reflecting mudubin a take wani irin hayaki ya fito daga cikin sa sai kuma ya koma ys rufe mirror d'in gaba d'aya. Wata irin murya mai amo da ban tsoro ta fara magana kaman mai chanting abu.

Abun mamaki saiga hoton Jaleela da Lameen tsaye jikin mudubin suna magana tsakiyar d'akin kaman mai kallon TV. Dukkanin wani abu daya faru tun daga inda Jaleela ke dariya na cewa suyi aure har zuwa sanda ta fice tana gaya masa Anees y'ar sace. Kaf ya yi playing a jikin mudubin. Wannan bakin hayakin dake zagaye da mudubin ya rikid'e lokaci guda ya yi shaping kaman mutum. Gaban wannan jan idon ya tsaya da har zuwa lokacin baka ganin mamallakinsu. Maganace ta fara fitowa daga cikin sa kaman iska

"The fairest of all ta kara dawowa shugaba. Idan mukayi sakaci zata zama mukulli da zata kawo k'arshen mu"

"A'a. "

Muryar tayi amo mai k'arfi saida d'akin ya jijjiga. Tana wani irin gurnani mai ban tsoro tace

"Wannan karon babu tantama idan ta kara shiga gonar daba tata ba zata mutu. Allahn ta da take bautawa shine yake bata kariya mun kasa samun nasara a kanta. Amma karfin ikona da magic nawa wannan karon zan samu nasara. Zamu fara da y'ar. Babu wani shamaki da zai shiga tsakanin da KING . Da nasan cewa tun wancan ranan tana d'auke da cikin sa dana hallaka shi tun baizo duniya ba. KING nawa ne ni kaɗai. A shirye nake na kashe duk wanda zai rabe shi."



WACECE JALEELA?

Shekara BAKWAI (7YRS) da suka wuce.

Seven years back.

......


Next page.





𝗚𝗨𝗗𝗨𝗡𝗔
𝗔𝗞𝗘 .





𝒜𝐬𝐡𝐚𝐧𝐭𝐲 𝐥♡︎𝐯𝐞.





A/N. Wannan page naku ne masoya littafin GUDUNA AKE. bazaiyiwu na kira suna ba don Allah kaɗai yasan yawan yaku. Ashanty tana godiya da kauna ❤.






36/40.





WACECE JALEELA?


Jaleela Mukhtar Bature ko nace ALEEYNA. Iyayenta Mukhtar Bature cikakken Kanuri ne ya yinda Ammi , Zulaikha Abdulaziz Bature sadaka yalla ce. Mutanen Niger ne sudin kuma y'an uwane. Sunyu aure ma zumunci da kuma kauna. Allah ya azurta Bature da ya'ya da jikoki. Sai ya kance suna aure tsakaninsu da wuya kaga sun auri bare. Bayan auren Mukhtar da Zulaikha suka bar cikin dangi da y'an uwa suka dawo nan Jihar ADAMAWA state Saboda aiki. Abhie yana da buri ganin ya buɗe makaranta ta yana yana koyar dasu ilimi na addini. Saboda haka suna dawo ya fara tara yara nan k'ofar gidan sa yana d'an koya musi hadithi da fikihu. Shekarar su biyu da auri Ammi ta haifi AL'MUSTAPHA. Almu dana Shekara guda cif Ammi ta fuskanci tana d'auke da wani cikin. Sosai ta shiga damuwa ga ciki ga kuma goyo. Haka tayi ta hak'uri da kukawar Abhie ta rani cikin da Almu da take shayarwa. Wata tara cif ta haifi Amnah. Almu da Amnah sun taso cikin gata da soyayya da kuma tarbiyar. Daga kansu Allah sa ikon sa Ammi bata sake ko b'ari ba. Saida Almu da Amnah suka shekara bakwai da y'an watanni saiga wani ciki. Wannan karan kam ciki mai matuƙar laulayine da saida ta kai Abhie ya aika can Niger aka turo kanwar Ammi ,Fareeda tazo tana taimaka mata. Sosai Ammi taci wuya wannan cikin kaman bazata kai ba. Yanda ta saba haihuwa wata tara cif wannan saida ya cika wata goma. Ranan da nakuda ta tashi kuwa wuni tayi tana fama. Makota da unguwar zoma sunyi k'ok'ari a kanta sosai. Cikin ikon Allah wajen asuba ta sankaco baby girl mai tsananin kyan gaske don tafi su Almu da Amnah kyau nesa ba kusa ba. A take Abhie ya yi mata hud'uba da rad'a mata sunan ALEEYNA wato ma'ana ( BEAUTY AS THE MOON). Babu wanda yakai Almu da Amnah farin cikib samun kanwa. Y'an uwa da abokan Arziƙi suna ta turuwa zuwa barka kace haihuwace ta farko. Duk wanda yazo yaga ALEEYNA saiya tanka ta. Saboda haka ne Abhie ke yawan sawa ana mata rubutu ana bata basu gaba d'aya saboda bakin mutane.

ALEEYNA ta taso cikin kauna gata da soyayyar iyaye da kuma yayye. Lokacin data shekara goma sha d'aya cif a duniya sukayi sauka gaba d'aya ita dasu Almu wajen Abhie. Ya dage sosai a kansu wajen karatu gasu yara ne masu matuƙar hazaka da kwakwala. Allah da ikon sa kuwa makarantar Abhie ta habbaka sosai almajirai ta ko ina suna tururawa wajen ganin sunzo sun samu ilimi mai kyau. Nan k'ofar gidansa Abhie yasa aka buge akayi siminti da kuma rufi na kwano. Kangon da yake jikinsa kuma ya siya aka gina masa makaranta da kuma dakuna na almajirai da suka kwana. Shekarar Almu ashirin cif lokacin ya yi sauka har bazata ta kirguga ba. A lokacin kuma ya gama secondary shida Amnah suna shirin wucewa Jami'a ta ABU dake can zaria. Aleeyna tana shekara goma sha uku. Idan kaji yanda take karanta maka hadithi da nahawu, sai ka riƙe baki. Abhie saboda ganin ta fara tasawa yasa ya sakata nan makaranta ta islamiya da take can gaba dasu. Tana fara zuwa makaranta saboda hazakar ta duk wani abu daya danganci musabaka ko taro da za'ayi itace a gaba. Wani lokacin haka zaka ganta y'ar mitsitsiya a aji tana koyarwa. Sosai Aleeyna tayi suna ga kyau ga ilimi. Qur'ani kuwa idan ta fara karatun sai kaji kaman karta daina. Tana shekara goma sha biyar kyawunta ya fara fitowa sosai da sosai. Don Aleeyna irin yarannan ce mai garin jiki saffa-saffa musamman daga kirji da kugunta. Komai nata irin na Ammi ne. Lokacin da girma ya fara zuwa zai ya kasance koda yaushe cikin hijabi take ko a gida. Kai ko barci zatayi bata cire Hijabi ,gata yarinya mai tsananin kunya da girmama mutum. Hakan ya jawo mata soyayya ta mutane lungu ta tsako. Ko baka santa ba kanajin labarinta sai ta shiga ranka.

Tana shekara goma sha shida akayi auren Aunty Amnah da Zubair. Yasha wuya sosai kafin ya sameta don Amnah da Zubair jirginsu ba d'aya ba. Zubair dan gidan attijaran mutum ne, maihaifin sa kansila ne a nan garin ADAMAWA. Acan ABU d'in ya ganta sanda yaje raka wani abokinsa. Tun daga lokacin ya haukace yana binta ita kuma sam taki bashi fuska. Saida ya had'a hannu da Almu ya shige jikinsa ya zame masa aboki na k'arfi da yaji. Cikin ikon Allah ya fara samu kan Amnah. Babu b'ata lokaci duka iyayen sukayi Na'am da batun. Lokaci kad'an akayi aure babu wata haniya sai yar walima da sukayi da y'an al'adu irin nasu na kanuri da sadaka yalla. A nan ne dan gidan wan Abhi , wato Lukman yaga Aleeyna ya rikice shifa yaga mata. Da yake ba wani zuwa Niger din take ba shi yasa dangi ba kowa ta sani ba. Saida kowa daya halacci bikin yasan Lukman na son Aleeyna. Sosai ya rikice ya zama abun dariya cikin y'an uwa. Kowa yana cikin murna da farin ciki saboda an jima ba'ayi auren zumunci ba. B'angaren

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login