Showing 30001 words to 32880 words out of 32880 words
إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
🅂🅃🄴🄿 ____ 11 ✍ ❤ 🔥
da sauri Sana ta mike ta nufi Danish ta zube saman guyiwowinta ta rungume shi , ta dan bubuga bayansa cikin sigar rarrashi
rungume ta Danish ya yi ya na fadin " momy , Daddy ba ya so na , he hate me "
Dam Fahd ya ji zuciyarsa ta buga jin Danish ya ce mata momy , shi tun lokacin da su ka fara call din bai lura da ita ba sai yanzu
nan take ya ji jikinsa ya yi wani mugun sanyi , ya tsare ta da ido , a hankali ya sauke ajiyar zuciya , kafin ya ce " I'm sorry Ma " da ga haka ya kashe kiran
Danish na jin kiran ya mutu ya kara sautin kukansa
da sauri Sana ta dago shi da ga jikinta ta na fadin " Baby , please yi hakuri ka daina kukan nan , Daddynka ya na son ka , sosai , fiye da rayuwarsa ma , ka ga ba hannunsa ka tasso ba , shi ya sa bai san ka ba , bai san abun da ka ke so ba , amma bari ka ga idan ya dawo zai dinga daukar ka ku tafi shan ice cream shi da kansa zai dinga kai ka school , ko ba ka so ? "
" ina so " ya fada ya na turo dan karamin bakinsa , hawaye na zubo mishi
hannu ta kai ta goge hawayensa ta na fadin " shikenan , yanzu ka daina kukan nan , mu tafi na yi maka wanka mu konta mu yi barci ko ? "
gyada mishi kai ta yi ta saki wani dan karamin murmushi
murmushi ita ma ta yi kafin ta mike tsaye ta sa hannayanta biyu ta dauke shi , sannan ta juya ta kalli Ma ta ce mata " Aunty , zan je na kontar da shi "
gyada mata kai Ma kawai ta yi , da ga nan Sana ta nufi bedroom din ta ta shiga da shi
sai da ta bar wajen Captain ya ce " Ma , wai ba ki lura da yarinyar nan Danish ya makale mata sosai ba ? like kamar ya san ta sosai , in ita ta na iya boyewa , shi yaro ne ba za iya controling abun da zai yi , kun ga tun da ta zo ya ke makale da ita , har ya na ce mata momy , kuma lokacin da ya gan ta dazu har ya fada jikinta , na ji ta kira sunansa Danish , bayan tun lokacin da ta ke zaune da mu ba wanda ya fadi sunan Danish , duk Baby mu ka ce mishi "
nan fa ya ja hankulansu dan abun da ya fada duk gaskiya ne , tabbas akwai wani abu tsakanin Sana da Danish
cikin nitsuwa Ma ta ce " gaskiya ba na tunanin haka , kamar yadda ka ce Danish yaro ne , bai san abun da ya ke ba , may be a cen gidan mahaifiyarsa akwai wadda ke kula da shi , ya yi tunanin ko ita ce "
da okay kawai Captain ya amsa mata kafin ya tashi ya nufi stair ya Haye , amma cikin ransa ya na da tabbacin abun da ya ke tunani haka ne , tabbas akwai wani abu a kassa dole ya samo ko minene
daya bayan daya su ka fara tashi su na yi wa Ma sai da safe , su ka koma bedroom din su dan su yi barci
☆ SANA 🧸 ☆
Bayan ta shiga bedroom din ta da Danish , kai tsaye saman gadonta ta kontar da shi , ta Haye ita ma ta na kallon shi ta ce " My Baby , kukan ya isa haka , na yi maka irin wassan da mu ke yi a gida ? "
da sauri ya mike tsaye ya na fadin " Eh , Eh , ina so "
murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta zauna bakin gadon , ya karaso ya konta saman bayanta ya zagayo da hannayansa a wuyanta
mikewa tsaye ta yi da shi ta nufi tsakiyar bedroom din ta fara juyawa da shi
dariya sosai Danish ya yi , su na ta juyi , ita ma ta na dariya
sai da ta gaji sannan ta sa hannu ta zagayo da shi gabanta , ta tilla shi saman gadon sannan ta Haye saman gadon ta konta ta na dariya
sai da ya tsagaita dariyarsa sannan ya ce " momy , me ki ke yi cikin gidan nan ? ba Kaduna na baro ki ba ? "
" Uhm , biyo bayanka na yi , ta ya za a raba ni da babyna haka kawai ? na tafi school ina dawowa wai Gwoggo ta ce min ka tafi gidan Daddynka , ba zan iya jure rashin ka ba My baby , shi ya sa na taho ni ma na zauna tare da kai " ta fada ta na daura hannu saman face din sa
( 🤔🤔 Kenan Captain ya tanka dai-dai , Sana ta na da hadi da Danish , sun san juna Sosai , hakan na nufin ba ta yi amnesia ba ? , to minene asalin sunanta ? wacece ita ? me ta zo yi cikin gidan ? ni fa har yanzu ban ga kan labarin ba 😪😪😪 )
cike da shagwaba Danish ya ce mata " that's why i love you so much Momy , dama na san ba za ki taba kyale ni ba "
hannu ta kai ta ja mishi hanci ta na fadin " ni ma ina son ka sosai my angel "
marairaice fuska ya yi ya na fadin " amma kin ga Daddy ba ya so na "
" kar ka damu , ba ina nan ba ? bari ya dawo , za mu shawo kansa , ya ji ya na son ka fiye da rayuwarsa , saboda kai ne rayuwarsa , Daddynka ne kuma dole ya so ka , in kuma ya ki na fasa mishi baki "
dariya sosai Danish ya yi har kananan hakwaren su ka bayyana
ita dai ta zuba mishi ido ta na murmushi , sai da ya gama dariyarsa sannan ta kai hannu ta janyo duvet ta rufe su har zuwa kugu sannan ta kashe lamps din dakin ta kunna bedside lamps ta ce mishi " now close your eyes mu yi barci "
" Good night momy " ya fada ya na lumshe idanunsa
a hankali ta kai lips din ta ta manna mishi kiss , sannan ta konta ta kai hannu saman kansa ta na shafawa a hankali har barci ya yi gaba da su
☆ UNITED STATES OF AMERICA ☆
*WASHINGTON DC*
- FAHD 🧸 -
konce ya ke tsakiyar lafiyayen gadonsa , ya na sanye da kayan barcinsa white color
ya zubawa laptop din sa da ke ajiye saman bedside drawer ido
ba komai ba ne ya ke kallo sai dan uwansa , kowane cikin bedroom din sa , duk bedroom din gidan da camera a ciki har bedroom din Sana , kuma duk ya na ganin abun da ke faruwa saboda cameras din na kunne
hakan na nufin duk abun da Sana ta yi ko ta fada tare da Danish duk ya ji su , amma bai yi wani yunkurin ba , asali ma ko motsi bai yi ba da ga konciyarsa
sai su Ashur kuma
shi dai Ashur ya na konce rike da waya a kunne alamun kira ya ke , ga face din sa dauke da murmushi , har da rungume pillow
Abeeram kuma ya na sharar barci , da ga shi sai short , ko lamps din dakin bai kashe ba
Captain ya na zaune bakin gadonsa rike da wayarsa ya na latsawa da alamun aiki ya ke
Talal da Ramadan duk su na barci , su na sanye da kayan barcinsu
Abdoul-Aleem kuma ya na konce tsakiyar gadonsa ya na kallon film cikin laptop d'insa , da alamun irin comics ne dan sai dariya ya ke har da dafe ciki
bangaran Ma , ita ma ta yi barci sai dai ba ya iya ganin ta sosai dan ta kashe lamps din dakin baki daya
ya na a haka kawai na ga magensa ta hayo saman gadon ta na kuka a marairaice
wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya ce " ke sauka min da ga nan , ba na ce kar ki sake hayo min gado ba ? "
wani dan kuka ta yi mai karfi kafin ta sauko da ga saman gadon ta nufi kofar fita dama kofar na bude
a hankali ya dago kai ya na fadin " Snow , ba dai fushi ki ka yi ba ? " ya fada kamar za ta iya jin sa , asali ma ita ta ficewarta
sai da ta fita ya koma ya konta ya ci gaba da kallon yan uwansa
ya yi wajen two minutes a haka kafin ya kai hannu saman bedside drawer ya dauki wayarsa ya kira lambar Captain
ya na kallon shi ta cikin laptop har ya dauki ya dauki kiran ya kai wayar a kunne
cikin nitsuwa ya ce mishi " Ina so ka yi bincike a kan Yarinyar da Ma ta kawo cikin gidan "
dan jinkirtawa ya yi kafin ya ce " Ni kaina hankalina bai konta da ita ba gaskiya , ko ba ta da niyar cutar da mu akwai abun da ya kawo ta cikin gidan nan "
" shi ya sa na ce ka yi bincike a kanta "
" Okay , amma Big bro zan so na yi maka wata tambaya please "
" Uhm " ya fada
sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " me ya sa ba ka son Danish ? na ga babynka ne , jininka ne , why ba ka son shi ? "
wani dan karamin tsaki Fahd ya ja ya lumshe idanunsa a hankali
a haka ya sake jiyo Muryar Captain ya na fadin " Please ka fada min , ko ma minene matsalar ka fada min , ba na jin dadin abun da ka ke , Fahd wlh in ka rasa soyayyar Danish a wannan shekarun nasa ka rasa ta har abada kenan , duk irin soyayyar da za ka nuna mishi da ga baya kullum zai dinga tuno wannan kiyayar da ka nuna mishi lokacin da ya ke karami "
ko sannu Fahd bai ce mishi ba ya sauko wayarsa ya katse kiran , ya rufe laptop din sa , ya daura wayar sama sannan ya kashe lamps din dakin baki daya , ya janyo duvet ya rufe jikinsa baki daya
▪UNITED KINGDOM ( LONDON )
▪The Mayor's Office for Policing And Crime (MOPAC)
Zaune Jimy ya ke cikin office din sa , ya na kallon laptop din sa
ya na zaune a haka Eliot ya shigo rike da wata yar karamar laptop ya na fadin " ka ji abun da ya faru a China ? ni fa ina tunanin gang din nan akwai abun da su ka shirya aikatawa "
wata yar karamar ajiyar zuciya Jimy ya sauke kafin ya rufe laptop din sa ya ce " no ba tunanin gang din Six Butterfly ne , su na sata su na garguwa da mutane amma ban taba ji an ce sun tashi Bomb , kuma har da gawar mutum guda , bayan su har yanzu mutanan da su ka sace su na a raye a hannunsa , akwai wani abu da ya bace mana tabbas "
" Tabbas akwai abun da ya bace mana , wai ina officer din da ka tura yin investigation ? har yanzu shiru ? "
" ka san wani ? "
girgiza mishi kai Eliot ya yi ya na fadin " no sai ka fada "
" Get out ! " ya fada ya na matse gera
" no , babu in da zan je sai ka fada min , kowa ya San abun da ke faruwa ban da ni kun bar ni cikin duhu "
mikewa tsaye Jimy ya yi ya dauki wayarsa ya nufi kofar fita ya fice ya bar Eliot nan tsaye
da sauri ya bi bayansa ya na rokon shi ya fada mishi amma ya share shi
▪ NIGERIA ( JOS STATE )
yau dai ta kama week-end duk samarin gidan su na gida , ba wanda ya farka da ga barcinsa karfe 8 , duk karfe 10 su ka tashi , Ashur sai da ya kai har karfe 12 dan jiya ya share dare ya na hira da masoyiyyarsa
Sana kuma ta na tare da Danish , ta na kula da shi , shi kansa Danish sai wajen karfe 10 ya tashi ,
bayan ya tashi ta yi mishi wanka ta shirya shi sannan su ka fito a tare ta na rike da hannunsa su ka yi breakfast tare da sauran mutanan gidan
- 05 PM -
wassan ball su ke yi cikin harabar gidan , sun yi Team biyu , har da Tracksuit din su color guda na team din su , da Ashur , Abeeram , & Talal , Team din su red color ne , Captain , Abdoul da Ramadan Team din su kuma ash color ne , Danish shi ne arbiter , Sana da Ma da Chef su na zazzaune saman chair su na kallon su , yanzu dai Team din Red ke wining 2 da 1
gaskiya abun ya yi matukar kawatar wa , duk da ni ba wani wassan ball na ke kallo ba sai da su ka burge ni , har sauran sojojin Captain sun yi tsatsaye su na kallon su
su na tsaka da wassansu kawai su ka ga wata budurwa ta bangad'o karamar kofar gidan ta fado da gudu ta na kuka ta na waiwaye
cak kowanan su ya tsaya ya zuba mata ido har ta karaso wajensu
idonta a rufe ta nufe Captain ba tare da ta sani ba , kawai sai ji ta yi ta bugi mutum da karfi har ta yi baya za ta fadi
da sauri Captain ya kai hannu a kugunta ya taro ta kar ta fadi
ta na jin an taro ta ta ware idanunta a dubu dari
kai tsaye ko cikin nashi su ka sauka ,
nan take ya tsargu da kallon ta , specially kananan sexy eyes din ta farare kal , kwayarsu blue kamar tashi , ba karamin burge shi su ka yi , har wata bugawa ya ji zuciyarsa ta yi
ya na a haka ya jiyo Muryar Talal ya na fadin " Captain me ya faru ? "
sai a lokacin ya dawo hayacinsa , ya gyara mata tsayuwarta sannan ya janye hannunta da ga bayan kugunta
ya fara kallon ta da ga sama har kassa , budurwar kyakyawa ce gaskiya , at least za ta kai 22 years , ta na da tsayi , dan ta kusa kai wa shoulder din Captain , skin din ta fara kal amma Su Abeeram sun fi ta haske , a gefensu wannan sai a ce mata black amma fara ce , gashin kanta duk ya na tirje brown color smooth da shi , ta na sanye da wata Gown ta atanfa amma duk ta yage , musaman wajen hannu kamar an sa hannu an yage ta da karfi dan har gabanta ya yage kadan ya yi saura a ga breast din ta , fuskarta duk ta yi red kamar an dake ta
da sauri Ma ta mike ta karaso wajen ta na fadin " Captain me ya faru ? wacece ? "
har ya bude baki zai yi magana su ka ga wasu samari hudu sun fado gidan da gudu da alamun yarinyar nan ce su ka biyo
ta na ganin su ta saki kara da kuka a tare , ta boye bayan Captain ta na fadin " don Allah ku taimake ni , wlh cutar da ni su ke son yi , don Allah "
kallon sojojinsa Captain ya yi , kafin ya musu alamun su kamo samarin da kai
ai ko samarin na ganin sojoji sun nufo su su ka juya da gudu za su tsere , amma sojojin nan su ka bi bayansu su ka fice gidan da mugun gudu
sai da su ka fita sannan Ma ta riko hannun Yarinyar , cikin sanyin murya ta ce mata " ki kontar da hankalinki ba abun da zai faru da ke "
sai a lokacin ta sauke wata nanauyar ajiyar zuciya ta fito da ga bayan Captain ta fara bin wajen da kallo
ta na ganin Maza ne a wajen , ta yi sauri ta sunkuyar da kai ta na sa hannu ta ja rigarta ta rufe kirjinta
wani dan karamin murmushi Ma ta saki kafin ta ce " Sana , zo ki tafi da ita bedroom din ki , ta yi wanka , cikin kayanki sai ki ba ta guda ta saka "
da To Sana ta amsa mata kafin ta karaso wajen ta riko hannunta su ka nufi cikin gidan , ba ta yi mata musu ba ta bi bayanta su ka shiga cikin gidan