Showing 15001 words to 18000 words out of 32880 words
kuma sam bai nuna ya damu "
" hmmmm , ki na ganin ke ma ba zai iya yi miki hakan ba watarana ? namiji fa abun yarda ba ne , cikin sauki zai bad'a kama ya sauya kamar ba ki taba sanin shi ba "
ta na gama rufe bakinta kawai ta jiyo Muryar wani dattijo tsaye bakin kofar parlourn ya na fadin " oho , kenan haka ki ke tunani dangane da ni ? "
a tare su ka zaro idanu ita da Rehan , da sauri ta mike zaune su ka juya su na kallon kofar
ya na tsaye sanye da wata farar jallabiya alamun da ga massalaci ya ke , ba kowa ba ne sai Barister Aabid
🥂 𝑮𝑰𝑫𝑨𝑵 𝑴𝑨𝒁𝑨🥂
💙💦 ( ᴛʜᴇ ᴍᴀғɪᴀ' s ʜᴏᴜsᴇ ) 💦💙
___FUNNY , DRAMATIC , REVENGE , ROMANCE & DESTINY ___
🔥👑 𝐌𝐀𝐋𝐋𝐀𝐊𝐈𝐍 ᴍᴇᴇʀᴀʜ 👑🔥
The writer of
Taurin zuciya
Exiled Prince ( love meets power )
Two lights ( Yar jarida )
Taurin Zuciya ( Return )
Fairat
Soyayyar gaskiya ( TRUE LOVE )
and now 𝐆𝐈𝐃𝐀𝐍 𝐌𝐀𝐙𝐀 ( 𝐓𝐇𝐄 𝐌𝐀𝐅𝐈𝐀'𝐒𝐇𝐎𝐔𝐒𝐄 )
FOR INFORMATION +22798999753 WHATSAPP ONLY
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
🅂🅃🄴🄿 ____ 6 ✍ ❤ 🔥
cikin nitsuwa ya karaso cikin parlourn ya zauna saman sofar da ke gefen ta su Rehan
cike da kula Hajiyah ta ce mishi " sannu da dawowa Dear "
wani kallon ya wurga mata ya na yamutse fuska ya ce " ba wani Dear , ai na ji abun da ki ka ce mata , wato haka ki tunani har a kaina ko ? "
da sauri ta girgiza mishi kai ta na marairaice mishi fuska ta ce " haba Dear ta ya ce za ke haka ? ni fa kawai na fada mata hakan ne dan ta kiyaye "
bushewa da dariya ya yi har da tapi ya na kallon ta ya ce " gaskiya kin cika matsoraciya , Rehan maganar me ku ke yi haka ne ? " ya fada ya na dawo da kallonsa kan Rehan
wasu yawu ta hadiye kafin ta kai hannu ta fara shafa kontacen sajenta ta na fadin " Ummm , dama Daddy , akwai wani dan Universityn mu da na roke shi ya yi min lectures kan abubuwan da ban gane ba a class , kuma ya amince , shi ne na ce mishi ya dinga zuwa nan gida ya na min in kun amince "
mikewa tsaye ya yi ya na fadin " shikenan , gobe in ya zo ki fara kawo shi na gan shi sannan "
" okay Daddy " ta fada ta na murmushi
kallon Hajiyah ya yi ya na fadin " ke kuma , zan kama ki gobe jira ki gani " ya kai karshen ya na fara takawa zai fita
da sauri Rehan ta ce mishi " Sai da safe Daddy , ku ce wa momy ni a nan zan kwana "
bai ce mata komai ba ya sa kafa ya ficewar shi
ya na fita Rehan ta mike tsaye ta na tsale kamar wata karamar yarinya ta na dariya
ita dai Hajiyah ta yi zaune ta zuba mata ido ta na murmushi , duk cikin yaran mijinta Rehan kadai ce ke iya bude baki ta kira ta da momy ko bayan idon Barister ne , sauran a bayan idonsa duk Aunty su ke ce mata , sai in sun gan shi su ke ce mata momy , kuma da wuya ta yi kwana guda ba ta zo wajen ta ba sun yi hira , ta dauke ta tamkar wata friend's din ta komai fada mata ta ke yi , ko lokacin da ta fara period maimakon ta je ta fadawa momynta , Hajiyah ta nufo ta fada mata , hakan ko ba karamin dadi ya ke yi mata ba ko ba komai ta samu d'iya ita ma
bangaran Barister bayan ya baro part din Hajiyah , kai tsaye part din Amarya ya nufa ya shigo parlourn ya na sallama
nan ya tardo ta zaune tare da Nasser , ya na Sanye da jallabiya shi ma , da alamun tare su ka fito mosque shi da Barister
a tare shi da Amarya su ka amsa mishi sallamar sannan ta yi mishi sannu da zuwa
sai da ya karaso gefenta ya zauna sannan ya amsa mata
ya na zama ta kalli Nasser ta ce mishi " please je ka kirawo Rehan ta na garden "
har ya mike Tsaye Barister ya taro shi da cewa " no ba ta garden , ta na part din Hajiyah , ta ce a cen za ta kwana , ka yi wa auta magana ta tarda ta su kwana a cen "
gyada mishi kai kawai Nasser ya yi kafin ya mike ya nufi stair ya haye
ita dai Amarya tun lokacin da ya ce ta na part din Hajiyah yanayin face din ta ya sauya alamun ba ta ji dadin hakan ba
" Lafiya na ga kin yi sanyi ? " fadin Barister ya na kallon ta dan sarai ya lura da sauyawar yanayin face din ta
" ba komai " ta fada a takaice ta na kallon Tv
" ni fa ba makaho ba ne , ki fada min me ya ke faruwa ? ko ba ki ji dadi dan na ce Rehan da auta su kwana wajen Hajiyah ? na ga dai ita ma yaranta ne , laifi ne in sun kwana a wajen ta ? na lura kamar ba ki son yaran nan su na sakin jiki da ita , ko wani abu ta yi miki ne ban sani ba ? "
" ba abun da ta yi min , kuma ba abun da ka ke tunani ba ne , kawai karyar da Rehan ne ta min ban ji dadi ba , ta ce min garden za ta je , in ta fada min wajen Hajiyah za ta je hana ta zan yi ne ? "
" wa ya sani , may be da ga garden ta wuce wajen Hajiyah ne , kin cika damun kanki dayawa , ni na tafi barci na ke ji " ya fada ya na mikewa tsaye ya nufi stair ya Haye
sai da ya bar wajen sannan Nasser ya sauko ya na fadin " Momy , Auta barci ta ke ta ce ba za ta tashi ba "
" don Allah tafiyarka kawai kyale ta " ta fada ta na yamutse fuska
da to kawai ya amsa mata kafin ya juya ya koma part din sa
☆ THE SIX BUTTERFLY 🦋 ☆
a zazzaune su ke cikin parlourn , kamar kullum su na sanye da bakaken kaya da face mask , Alexander na rike da laptop ya na latsawa
Cookie da Joker kuma su na rike Jump rope su na tsalle kamar kananan yara , sauran kuma su na kallon Tv
su na a haka na jiyo Muryar Alexander ya na fadin " Cookie , Joker , ku je ku bawa mutanan nan abinci "
da okay su ka amsa mishi a tare kafin su daina tsalen su ka bar rope din a nan su ka nufi hanyar kitchen
su na barin wajen Delta ya ce wa Alexander " me za mu yi da mutanan nan ? ya kamata mu san abun yi tun kafin hukuma ta fara bincike tsakani da Allah "
" don't worry , ku dai kawai ku fara nemo bayanan da na ce muku , da ga nan mu mika su gaban kotu ta yanke musu hukunci dai'dai abun da su ka aikata "
" okay but batun tafiyar mu UK fa ? " fadin Loven
Delta ne ya amsa mishi da cewa " nan da one month za ku tafi tare da Joker da Cookie , mu kuma za mu tafi China "
" Jami'an tsaron UK sun turo wata officer undercover cikin garin nan dan yin bincike a kan mu " Fadin Alexander
a tare duk su ka juyo su na kallon shi su na zaro idanu
bai ce musu komai ba ya mike tsaye da laptop din sa ya juya ya nufi kofar fita parlourn ya fice
ya na fita su ka jiyo Muryar Cookie ya na sakin kara da karfi
a tare duk su ka zabura su ka nufi hanyar corridor dan ganin in ya na lafiya
su na shiga su ka hango shi tsaye bakin kofar wani dakin ya na rike da damtsensa an caka mishi wani dan rodi na karfe jini na zuba
da sauri su ka nufe shi su na tambayar shi me ya faru
sai kuka ya ke kamar wani karamin yaro hawaye na zubo mishi bibiyu
sai a lokacin hankalinsu ya kawo kan abun da ke faruwa cikin dakin
Joker ya na danne wani mutum saman gadon dakin , ya matse hannayansa tsam a baya da hannu guda , ya shako bayan wuyansa da gudan
da sauri Delta ya shiga cikin dakin ya na fadin " Joker , what are you doing ? sake shi ! "
ba musu Joker ya sake shi ya ja da baya ya na fadin " Delta , ya yi kokarin guduwa har ya cakawa Cookie karfe a hannu "
wani dan karamin tsaki ya ja ya na fadin " let him , ko da ya bar gidan nan namun daji za su cinye shi cikin dajin , je ka ida ba sauran abinci , zan kula da shi "
da to kawai Joker ya amsa mishi kafin ya fito dakin , ya na fitowa ya ga sauran sun bar wajen , alamun sun tafi yi wa Cookie dress
ya na fita Delta ya meda kofar dakin ya rufe , ya fara takowa a hankali cikin dakin ya na nade hannayan rigarsa
a hankali mutumin nan ya fara ja da baya , kamar zai yi kuka ya ce " don Allah ku kyale ni na tafi wajen ahalina , tsawan wata guda kun ajiye ni a nan , in kudin ku ke so zan ba ku lambar yayana ya turo mu kudin "
bai ce mishi komai ba ya karaso bakin gadon ya zauna ya daura kafa guda saman guda , ya na kallon shi ya ce " kudin da na mallaka ko mutuwa za ka yi ba za ka ba ni ko 1/3 din su ba , kuma duk ta hanyar halal na same su ba da cuta ba kamar kai , ni ba kudinka na ke bukata ba , dan haka malam sai ka dawo ka zauna , babu in da za ka je sai na gama bincike na a kanka , kuma in ka ce za ka gudu wlh cikin daji mu ke , ka na fita namun daji za su cinye ka babu hannuna a ciki " ya na gama fadar ya mike ya nufi kofar fita
har ya riko handle din kofar ya sake ta ya juyo ya nufe shi ya kai mishi wani mugun naushi a face sai da ya fadi kassa ya na fadin " wannan kuma na Cookie ne da ka jiwa ciwo , next time ka yi kokarin taba wani da ga cikin mu sai na kashe ka "
ya na gama fadar haka ya juya ya fice ya janyo kofar ya rufe ya bar shi nan konce
( 🤔🤔 ni dai wadanan Six Butterfly ina son na san dalilin su na sace wadanan mutane , su sun ce ba kudi su ke so ba , kuma ba su kashe su ba , dole akwai wata manufa a bayan wannan aikin da su ke , to bari dai mu ci gaba da labarin mu , za mu ji ko ma minene da ga baya )
☆ TUDUN WADA ☆
Zaune Abeeram ya ke cikin parlournsu tare da Danish , su na sanye da kayan barci white color su na kallon cartoon cikin Tv su na dariya kamar wasu kananan yara
su na zaune a haka Captain ya fara sauko stair din gidan ya na sanye da kayan barcinsa shi ma amma nasa blue ne
kai tsaye ya nufi Tv ya kashe ta sannan ya juya ya ce musu " ba ku ganin dare ya yi ne ? Benji ka na da class fa gobe shi ne za ka zauna ku na kallon cartoon "
ya kai karshen ya na karasowa wajen su ya sa hannayansa biyu ya dauki Danish ya nufi stair da shi
a hankali Danish ya juya ya dagawa Abee hannu ya na fadin " Good night uncle "
" Good night my baby " Abi ya fada ya na mikewa tsaye
bangaran Captain kuma ko da ya hayo stair kai tsaye part din sa ya wuce ya shiga bedroom din sa kai tsaye ya kontar da shi saman gadonsa
da sauri Danish ya mike zaune ya na fadin " uncle , ina son magana da Daddyna , please " ya fada ya na shagwabe mishi fuska
wani dan karamin murmushi Captain ya yi kafin ya kai hannu saman kumatunsa ya ce " bari gobe zan kira maka shi yanzu dare ya yi , ka konta ka yi barci okay ? "
gyada mishi kai kawai Danish ya yi kafin ya konta
janyo duvet Captain ya yi ya rufe shi har zuwa kirji sannan ya matso ya manna mishi kiss a forehead kafin ya dauki laptop din sa ya ci gaba da aikinsa
☆ WASHE GARI ☆
A zaune duk mutanan gidan su ke a dining table su na breakfast ban da Captain , Danish da Ashur
ko wane ya shirya cikin kayansa alamun fita za su yi
cikin nitsuwa Ma ta ce musu " ina Captain ne ya yi ko ya fita ? da Danish da Ashur duk ba su fito ba "
a tare su ka amsa mata ba su sani ba su ma
su na a haka su ka fara jiyo takun mutum ya na shirin shigowa dining room din
a tare duk su ka juya su na jiran su ga wanene zai shigo
kawai sai su ka ga Ashur ya shigo dining room din ya na sanye da kakin Captain ta soja
a tare su ka zaro idanu su na fadin " Ashur ? me ka ke yi da kayan Captain ? "
wata yar karamar dariya ya yi kafin ya fiddo wata paper cikin aljihun wandonsa ya nuna musu ya na fadin " da ga yanzu na zama Captain Ashur har na sati guda , dan Captain ya ba ni matsayinsa kun ga shaidar a nan "
" kamar ya ya ba ka matsayinsa ? Ma , dama a ba da matsayi haka ba tare da ka yi training din soja ba ? " Fadin Abeeram ya na kallon Ma
daga mishi kafadu ta yi alamun ita ma ba ta sani ba
mikewa tsaye Talal ya yi ya kwace paper din hannun Ashur ya fara karantawa
sai da ya gama sannan ya bawa Ashur kayansa ya na fadin " gaskiya ya fada Ma , Captain ya ba shi matsayinsa na tsawan sati guda , kuma har da sa hannun General da Minister of defense , duk abun da Ashur zai aikata cikin kayan nan ba wanda zai dakatar da shi "
" How it can be possible ? " fadin Ramadan
kamar da ga sama su ka jiyo Muryar Captain ya na fadin " kamar dai yadda Talal ya fada , cewa ya yi zai iya yin aikina fiye da ni , shi ya sa na ba shi wannan damar na ga abun da zai aikata " ya fada ya na shigowa dining room din rike da hannun Danish su na sanye da Jeans da T-shirt kai ka ce wasu Twins , su ka karaso Captain ya janyo chair gefen Abeeram ya zauna ya daura Danish saman laps din sa
ya na Zama Ashur ya ce " ni dai na tafi kar na yi late , sai na dawo " ya kai karshen ya na juyawa zai fita
ya na fita Chef ya fito da ga kitchen rike da tray din breakfast na Captain ya ajiye mishi gabansa
godiya Captain ya yi mishi kafin ya dauki Mug din coffeen ya fara sha ya na ce wa Danish " Baby , ci ko , sai mu ka fada min idan ka ke so mu tafi , yau hutu na ke ba in da zan je sai in da ka ke so "
cike da shagwaba Danish ya ce mishi " Uncle , mu fara tafiya shan ice cream " ya fada ya na daukar sandwich din da ya gani saman plate ya fara ci
haka dai su ka yi breakfast din su cikin konciyar hankali , duk sai da su ka watse su ka bar Captain da Danish nan zaune har Ma sai da ta fita ta tafi wajen aikinta
sai da su ka kammala breakfast din , sannan Captain ya dauki Danish su ka fito gidan
kai tsaye parking space ya nufa ya shiga motarsa da shi su ka baro gidan
yau dai shi kansa Captain ya san ya samu hutu , sai da su ka tafi restaurant har kala uku kawai shan ice cream
da ga nan su ka tafi Mall , ya yi wa Danish shopping shi ma ya yi , da ga nan su ka wuce wajen wassan yara , a takaice dai sai wajen karfe 11 na rana su ka koma gida
a lokacin ba wanda ya dawo gidan , kawai ya ja Danish part din sa ya wuce da shi bedroom din sa , ya yi mishi wanka ya fito ya shirya cikin wasu kananan kaya da ya sayo mishi yanzu , wandon short ne da wata yar T-shirt , ya shafa mishi lotion da turare
sannan ya kontar da shi saman gadonsa ya dauki wayarsa ya saka mishi game ya ba shi ya ce