Showing 18001 words to 21000 words out of 32880 words
ya jira yanzu ya dawo
da to kawai Danish ya amsa mishi ya karbi wayar ya fara game
shi kuma Captain ya shiga toilet ya yi wanka , ya fito ya shirya cikin kananan kaya shi ma , Wando Three cuter da T-shirt ,
ya haye saman gadon ya konta ya lumshe idanunsa ji ya ke yau duk ya gaji duk da ba wani aiki ya yi ba
MY BOOK IS ONLY N300
VIA
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank
Dm +22798999753 for evidence
🥂 𝑮𝑰𝑫𝑨𝑵 𝑴𝑨𝒁𝑨🥂
💙💦 ( ᴛʜᴇ ᴍᴀғɪᴀ' s ʜᴏᴜsᴇ ) 💦💙
___FUNNY , DRAMATIC , REVENGE , ROMANCE & DESTINY ___
🔥👑 𝐌𝐀𝐋𝐋𝐀𝐊𝐈𝐍 ᴍᴇᴇʀᴀʜ 👑🔥
The writer of
Taurin zuciya
Exiled Prince ( love meets power )
Two lights ( Yar jarida )
Taurin Zuciya ( Return )
Fairat
Soyayyar gaskiya ( TRUE LOVE )
and now 𝐆𝐈𝐃𝐀𝐍 𝐌𝐀𝐙𝐀 ( 𝐓𝐇𝐄 𝐌𝐀𝐅𝐈𝐀'𝐒𝐇𝐎𝐔𝐒𝐄 )
FOR INFORMATION +22798999753 WHATSAPP ONLY
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
🅂🅃🄴🄿 ____ 7 ✍ ❤ 🔥
*REPUBLIC OF CHINA*
HONG KONG ( 12:54:09 PM )
wata dankareriar bakar mota ce ke tafiya saman titi ta na shawara wani uban gudu , glass din ta baki daya black ne ba ka iya ganin komai , ga shi ko titin babu kowa sai lamps da ke kunne
ya yi wajen two minutes ya na sharara wannan uban gudun kafin na ga ta tsaya gaban wani dankareren building na a zo a gani
a hankali na ga an bude gefen driver , wani kyakyawan saurayi ya fito ya na sanye da wasu kaya black color baki daya , wandon jeans da t-shirt da jacket da sneakers duk black , amma gashin kansa white ne , ya na Sanye da face mask white color , idanunsa kadai na ke iya gani black color da du , ma su jan hankali , ga shi ko da murdaden jiki dai'dai
cike da izza ya fara takawa ya nufi hall din shiga building din , hannayansa na cikin aljihun jacket din sa
ya na shigo wa wajen na ga wata kyakyawar chinese zaune a reception da alamun Hotel ne wajen , ta na sanye da Uniform din ta
da sauri ta nufe shi , cikin harshen chinese ta ce mishi " Sir , ba a visit a wannan lokacin , please ku fita ko na kira security "
ko ta kanta bai bi ba ya nufi wata door ya na fadin " na sani ba a visit a wannan lokacin " ya fada da turanci shi kuma da wata zazzakar murya cike da nitsuwa da kwarjini
da sauri ta ce mishi " Sir , please ku fita ko na kira sec....... "
ba ta karashe maganarta ya fiddo gun da ga cikin aljihunsa , ya saita kanta kawai ya harbe ya ci gaba da tafiyarsa , nan take ta fadi gawa a wajen , sai zubar da jini ta ke
shi kuwa ko a jikinsa , ya sa hannu ya tura kofar ya shiga
nan na ga wajen wani dogon corridor ne mai mugun tsayi , cen da ga karshe na ga wata kofar an rubuta EXIT ya na fitar da wata Red light
cikin corridor din na hango wasu doors shidda , uku gefen dama uku gefen hagu
bai wani tsaya duba me bayan kofofin ba kawai ya nufi kofar da ke cen karshen corridor din
ya yi wajen two minutes ya na tafiyar nan kafin ya iso wajen kofar , kawai ya sa hannu ya tura ya fice
ko da ya fito wajen na ga wajen kamar wani kwango ne , da wasu manyan trush guda uku , da alamun bayan hotel din ne
ko da ya fito ya nufi hanyar barin wajen , in da wata mota kirar BMW ke parked dan nesa kadan
kai tsaye motar ya nufa , ya bude gefen mai zaman banza ya shiga
ya na shiga driver din ya tada motar su ka bar wajen da mugun gudu kamar za su tashi sama
Driver din ka na ganin shi ka ga cikaken Chinese , har kananan idanunsu amma kamar 1 ya ke tsananin rama , ya na sanye da wasu suit , jacket din suit din ma ta yi mishi yawa
sai da su ka yi nisa na ga ya fiddo wata yar karamar waya da ga cikin aljihunsa ya danna button din tsakiya
ya na danna shi ko na ji wani razanannan sauti ya tashi kamar fashewar Bomb
bushewa da dariya Driver din ya yi ya na fadin " Boss , plan din ku ya tafi dai'dai , kamar yadda ku ka tsara "
shiru wanda ya kira da Boss ya yi , ya fara zuge glass din gefensa ya tilla wayar karama
sannan ya meda glass din , sai a lokacin ya amsa mishi da cewa " Yanzu plan din zai fara , mu koma HQ "
da okay kawai ya amsa mishi , da ga haka ba wanda ya ce ufan har su ka karaso wata tsohuwar unguwa da ga gani ta talakawa ce
sai da su ka iso bakin kofar wani gida sannan ya tsayar da motarsu ya kashe ta
a tare su ka sauka da ga cikin motar , da sauri driver din ya nufi kofar gidan ya bude kofar ya matsa gefe
cike da izza ya ci gaba da takowa ya shiga cikin gidan sannan driver din ya shiga ya meda kofar ya rufe
ko da ya shiga kai tsaye sai saman wani madaidaicin parlour , babu komai ciki sai sofa guda , da wata katuwar table tsakiyar parlourn , da wata yar karamar Tv ta na fuskantar sofar
cen na hango wasu samari guda hudu , biyu zaune saman sofa biyu saman table din duk chinese , su na hira da dariya
su na ganin Boss din ya shigo su ka mike tsatsaye su na fadin " Barka da dawowa Boss "
ko ta kan su bai bi ba ya nufi wata yar karamar kofa da alamun ta bedroom ce dan yanayin da da wuya a ce corridor ne ko makamancin haka
sai da ya bude kofar sannan ya tsaya ba tare da ya juyo ba ya ce " Money , Lee , Sniper , Doctor , Yung , kar wanda ya takura min har zuwa safiya ! "
a tare duk su ka amsa mishi da " Yes , Good night Boss "
da ga haka ya shiga bedroom din ya medo kofar ya rufe
bedroom din karama ce sosai dai'dai mutum guda , sai gado na mutum guda da closet din kaya , da wata board rufe da farin tissu gefenta kuma wani dan karamin office ne da tarin takardu a sama kamar jarida da , laptop guda a sama , shikenan abun da ke cikin bedroom din , sai toilet
bakin gadon ya karaso ya zauna ya cire sneakers din sa , da jacket din sa , ya cire jeans da t-shirt din baki daya ya bar short da singlet kadai a jikinsa ya ajiye kayan saman gadonsa , sannan ya nufi toilet ya shiga
wanka ya yi ya fito da ga shi sai short da singlet din da ya shiga da su , ya cire face mask din sa , nan ne na samu ganin face din sa , fari ne sosai kamar ka taba jini ya fito , amma ka na gani ka san ba Chinese ba ne , ya fi kama da Bature haka , Ya na da dogon hanci kamar pencil da karamin bakinsa , lips din sa pink color
gadon ya nufa ya zauna ya na sauke wata doguwar ajiyar zuciya ya kai hannu cikin gashinsa ya fara shafar sa ya na meda shi baya
ya yi wajen two minutes zaune a haka kafin idanunsa su sauka kan board din wajen
zugum ya yi ya zubawa Board din ido babu ko kiftawa
a hankali ya mike tsaye ya nufi board din , ya kai hannu ya riko tissu din ya janye shi ya fadi kassa
nan na ga board din cike da pic , da guntayan jarida
abun da ya kara jan hankalina shi ne pic din Captain da na hango har wajen biyar , daya ya na sanye da wasu uniform irin na school haka , ba zai wuce 15 years ba , na biyu zai kai 25 years ya na sanye da Kayan American Army , na uku kuma ya na tare da Fahd sanye da suit white dukkan su ko wane da murmushi a face din sa , Captain ya zagayo da hannunsa a bayan wuyan Fahd , na hudun kuma shi da Boss , su na sanye da Kayan American Army duk za su kai 25 years su na rike da gun Captain ya daga kai sama ya na dariya Boss na kallon shi shi ma ya na murmushi , na biyar kuma da ke makale a tsakiyar board din , shi da Boss ne , su na sanye da Uniform tun su na 15 years , zaune cikin wani garden da books a gabansu su na karatu , ba su ma san an yi pic din ba , sai kananan Pic na su Ashur , Abdoul-Aleem , Ramadan , Talal , Abiram duk akwai , sai wani Pic na Fahd ya na rike da hannun wata mace ta na jinin Danish sosai , amma kallo daya za ka yi mata ka san jinin hausa ce , su na kallon juna cikin ido ita da shi su na murmushi
( To fa , duk yadda a ka yi wannan Boss ya na da hadi da Familyn Captain Fayd , abun da na lura kamar a tare su ka yi karatu saboda pic din su da na gani a tare sanye da uniform din makaranta , amma cikin pic Captain kayan American Army ne a jikinsa 🤔🤔 to minene tushen labarin ? mu je dai zuwa )
a hankali ya kai hannu ya shafa pic din tsakiya , cikin wata cool voice ya ce " na yi nadamar sanin ka a rayuwata Fayd , amma ba komai , da a ce yanzu hanyar mu ba su hadu ba ba zan taba sanin abota ba ta da wurin zama a rayuwata , da a ce hanyarmu ba su hadu ba ba zan taba sani abota ba ta taba yin rana ba , duk kai ne silar zama na wannan mutum da na ke a yanzu , ka jira ka gani , daya bayan daya sai na raba ka da yan uwanka abun farincikinka , kamar yadda ka raba ni da nawa farincikin sannan na raba da rayuwarka baki daya , sannu a sannu za ka gane bakin rijiya ba wajen wassan makaho ba ne , za ka yi nadamar hada hanyar ka da tawa shekaru 25 baya "
ya karashe maganarsa ya na janye hannunsa ya kai wa board din naushi , sannan ya juya ya nufi gadonsa ya Haye ya konta ya lumshe idanunsa amma ba barci ya ke ba
☆ *WASHE GARI* ☆
ya na tsaka da wani wahalalen barci da ya sace shi ya jiyo a na yi mishi knocking
slowly ya fara motsi ya na yamutse fuska kafin ya ware idanunsa a hankali ya na jan tsaki
murya a disashe ya bude baki ya ce " wai waye ke buga min kofa ? ba na ce kar a takura min ba ? "
" Boss , Lee ne , ya kamata ku zo ku ga abun da ke faruwa "
wani dogon tsaki ya ja kafin ya sauko da kafafunsa kassa , ya mike tsaye ya dauki wandonsa ya mayar sannan ya nufi kofar dakin
nan ya ga Lee tsaye ya na jiransa
tun kafin ya yi magana Lee ya riga shi cewa " Boss , ya kamata ku zo ku gani "
gyada mishi kai Boss ya yi kafin ya juya su ka karaso cikin parlourn , nan ya ga sauran tsatsaye gaban Table din nan ta tsakiya su na kallon Tv
gaban su ya karaso ya tsaya ya na fadin " me ya faru ? "
Money ya dago hannu ya na rike remote ya kunna mishi Tv
a hankali ya juya ya kalli Tv din , dai'dai lokacin ko ta kunnu , a na shirin labarai wata yar jarida zaune a kan chair rike da wasu takardu ta fara magana da harshen Chinese ta na fadin " a safiyar yau ne mu ka samu labarin tashin Bomb a bakin kofar Kowloon Harbourfront Hotel , a bisa binciken jami'an tsaro bomb din ya tashi ne tsakanin karfe 12 na dare da mintina 59 , happily Bomb din ba wani mai girma ba ne , explosion din ba ta yi wani babban tasiri ba , sai dai sun samu gawar wata ma'aikaciyar hotel din , duk yadda a ka yi wanda ya ajiye Bomb din ta cikin hotel din ya ratsa ya wuce , departement of defense ya na son kowa ya kontar da hankalinsa , ko wanene ya tada Bomb din za su kamo shi su ba shi hukuncin da ya dace , sai magana ta gaba ........ " tsit kawai na ga Tv din ta mutu
wani dan karamin murmushi Boss ya saki ya na tapi da hannunsa
cike da izza ya ce " Yesss , Step one finished "
" Boss , yanzu minene shirin mu na gaba " fadin Yung
dan jinkirtawa ya yi kafin ya ce " Marshal Fayd Yeonjun , ina investigation din da na ce ku yi a kansa ? "
Lee ne ya matso ya nufi sofa ya tsugunna , ya kai hannu kassan sofar ya fiddo dasu takardu ya karaso gefen Boss ya tsaya , ya ajiye takardun saman table
ya ce mishi " Boss , kamar yadda ku ka ba da Umarni na yin bincike a kansa , a binciken da na yi Marshal Fayd Yeonjun ya bar American Army shekara uku baya , bayan ya bar Army ya koma kassar Nigeria da ke cikin Africa a jahar Jos , a cen ya na aiki a matsayin Captain cikin Nigerian Army , a yanzu dai shi ne kadai abun da na sani a kai "
" Sauran yan uwansa fa ? "
" Boss , ban san ya da yan uwa ba , amma zan koma na sake bincike a kai "
" Talal , Abdoul-Aleem , Ramadan , Ashur , Abeeram shi ne sunan yan uwansa , su na da Big bro mai sunan Fahd , shi da Fayd tare su ka yi karatu a US , bayan Fahd ya samu master din sa a marketing ya dawo Nigeria in da sauran yan uwansa su ke zaune hannun kanwar mahaifiyarsu bayan rasuwar iyayensu , Fayd kuma ya tsaya a US , ko ni da ke zaune na fi ka masaniya a kai Stupid kawai " ya fada ya na wurga wa Lee wani mugun kallo
da sauri Lee ya sunkuyar da kansa ya na fadin " I'm sorry Boss "
tsaki Boss ya ja kafin ya kalli sauran ya ce " ku yi a hankali dan a yanzu wassan zai fara , ba na son a samu mistake ko da guda ne , Money , Yung , Sniper , ku shirya tafiya UK kamar yadda mu ka tsara nan da one month "
" Amma Boss kudin da mu ka sato fa last months ? " Fadin Doctor
wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya juya ya nufi bedroom din sa ya shiga ba tare da ya ce komai ba
jim kadan ya fito rike da wata bag ya tilla tsakiyar table din , nan take kudin da ke ciki su ka fito su ka bazu tsakiyar table din
" ku yi a hankali wajen kashe kudin nan , in ku ka yi abun da zai janyo hankalin jami'an tsaro kanku , daya bayan daya zan iya kashe ku " ya kai karshen maganarsa ya na juyawa ya koma cikin bedroom din sa ya turo kofar ya rufe
a tare su ka saki wani kyawatacen murmushi su ka nufi table din
su ka fara tattare kudin su ka mayar cikin jakar su na tunanin wace irin masha'a yau za su yi , kowane dai na fadin ra'ayinsa , wani ya ce nightclub , wani ya ce restaurant su fara cin abinci , wani ya ce shopping
haka dai su ka tsaya bata lokaci , Boss kuma ya koma ya konta
Ni kuma na dauki takarduna na nufi Nigeria
MY BOOK IS ONLY N300
VIA
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank
Dm +22798999753 for evidence
🥂 𝑮𝑰𝑫𝑨𝑵 𝑴𝑨𝒁𝑨🥂
💙💦 ( ᴛʜᴇ ᴍᴀғɪᴀ' s ʜᴏᴜsᴇ ) 💦💙
___FUNNY , DRAMATIC , REVENGE , ROMANCE & DESTINY ___
🔥👑 𝐌𝐀𝐋𝐋𝐀𝐊𝐈𝐍ᴍᴇᴇʀᴀʜ 👑🔥
The writer of
Taurin zuciya
Exiled Prince ( love meets power )
Two lights ( Yar jarida )
Taurin Zuciya ( Return )
Fairat
Soyayyar gaskiya ( TRUE LOVE )
and now 𝐆𝐈𝐃𝐀𝐍 𝐌𝐀𝐙𝐀 ( 𝐓𝐇𝐄 𝐌𝐀𝐅𝐈𝐀'𝐒𝐇𝐎𝐔𝐒𝐄 )
FOR INFORMATION +22798999753 WHATSAPP ONLY
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
🅂🅃🄴🄿 ____ 8 ✍ ❤ 🔥
☆ *NIGERIA ( JOS STATE )* ☆
- 09 PM -
*CAPTAIN FAYD*
a hankali ya ke sauko stair din gidan ya na sanye da kayan barcinsa white color
a nan parlourn ya tardo duk sauran yan uwansa zaune , Talal , Ramadan , da Abdoul-Aleem su na rike da laptop su na aikinsu , Abeeram da Ashur kuma su na game da Danish
Danish na ganin Captain ya mike da gudu ya nufe shi ya na dariya
wani dan karamin murmushi Captain ya saki , sai da Danish ya karaso gabansa ya sa hannayansa biyu ya dauke shi ,