Showing 6001 words to 9000 words out of 32880 words
fita ya yi hannun dama
Eliot kuma ya nufi hannun Hagu su ka yi hannun riga
( duk maganar nan da su ka yi da turanci su ka yi , kar ku manta kassar UK da turanci su ke magana , yawwa )
🥂 GIDAN MAZA 🥂
👻 ( THE MAFIA'S HOUSE ) 👻
____FUNNY , DRAMATIC , REVENGE , ROMANCE & DESTINY ____
🔥👑 MALLAKIN MEERAH 👑🔥
FOR INFORMATION +22798999753 WHATSAPP ONLY
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP
https://chat.whatsapp.com/LWmuu0yv6C9DAhpdepDb4i
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
STEP ____ 3 ✍ ❤ 🔥
▪NIGERIA ( JOS STATE )
▪TUDUN WADA
wani kyawatencen parlour ne ya kyawatu da kayan more rayuwa na ji da gani , da ga gani mutanan gidan ba ma su kananan hali ba , ba zan bata lokaci wajen yi muku description ba yawwa kowa ya yi tunani da nashi brain
cen na hango wata kyakyawar mace zaune cikin dining room , ta na Sanye da wata Abaya white color me mugun kyau , ta yi Rowling veil din ta a kai , macen cikakiyar bahausa ce gaba da baya , launin skin din ta chocolate ne , da ga ganin yanayin jikin ta ka san mace ce mai mugun son gyaren jiki , akkila za ta kai shekara 50 , amma sam jikinta bai nuna hakan ba
ta na zaune ta na breakfast cikin konciyar hankali
ta na a haka wani kyawawen saurayi fari kal , ya shigo dining room din ya na sallama cen kassan makoshi cike da shagwaba
saurayin Fari ne kal , sam ba ya kama da matar nan , ya so ya yi kama da korean , ya na da dara daren idanun farare kal kamar madara kwayar cikin su kuma blue ce , ga dogon hanci sai dan karamin bakin shi , lips din shi pink color ma su mugun laushi , ya na da darck black smooth hair , ya zubo mishi har bayan keya duk a tirje ya zubo mishi har gaban goshi kadan ya rufe mishi idanu , a shekaru ba zai wuce 19 to 20 years ba , amma yanayin jikin shi bai nuna hakan ba , dan jikin shi a murde ya ke da ga gani ya na yawan motsa jiki
da ga shi sai short da singlet , dukka farare , sai yamutse fuska ya ke da allamun yanzu ya tashi da ga barci
matar nan na ganin shi ta saki wani cool murmushi ta ce " Good morning my Abee "
a hankali ya karaso wajen matar nan , ya kai bakin shi saitin kumatun ta ya manna mata kiss , cikin wata yar siririyar Muryar shi cike da shagwaba ya ce " Good morning Ma "
ya fada ya na janyo chair a geffen ta ya zauna , kawai ya kontar da kan shi saman table din ya lumshe idanunshi
murmushi mai dan sauti matar nan da ya kira da Ma ta yi ta kai hannu ta fara janye mishi gashin gaban goshin shi ta na fadin " Abeeram , yau ma ka cika dare ka na kallon film ko ? "
a hankali ya ware idanunshi murya cen kassan makoshi ya ce " Ma , wani assigment ne da a ka ba mu na kammala , shi ya sa na cika dare , dadin abun ma yau ba mu da class sai monday "
" da gaske ka ke ? " ta fada ta na janye hannunta
a hankali Abeeram ya gyada mata kai allamun Eh
ta na shirin magana wani mutum ya fito da ga cikin Kitchen , ya na sanye da wasu suit bakake da allamun Chef din su ne , amma bai yi kama da mutanan Nigeria ba , da ga gani cikaken korean ne gaba da baya shi ma
da murmushi a face din shi ya karaso cikin dining room din ya na kallon Abiram ya ce " Abee , na hada maka smoothie din ka ? "
" No , bari har a jima , yanzu ka kawo min fruits , Thanks "
gyada mishi kai Chef ya yi kafin ya koma cikin kitchen
ya na komawa matar nan ta cewa Abiram " where is your brothers ? "
wani dogon nunfashi ya ja kafin ya lumshe idanunshi ya ce mata " Captain tun karfe 7 ya fita tare da Talal , Ashur kuma ya na Gym , Ramadan & Abdul-Aleem har yanzu su na barci "
a hankali Ma ta gyada kai kafin ta mike tsaye , ta matso kussan Abeeram , ta manna mishi kiss saman kumatu ta na fadin " Okay , na tafi , sai na dawo "
" see you later " ya fada cikin sanyin murya , da ga haka matar nan ta sa kafa ta fice dining room ta bar parlourn
ta na fita ko chef ya fito da ga kitchen rike da tray cike da fruits ya karaso wajen dining table din ya ajiye tray din gaban Abiram ya na fadin " Abee , ka na bukatar wani abu "
" ba ka da maganin barci , barci na ke ji sosai wlh " ya fada a sanyaye
wani dan karamin murmushi chef ya yi ya na fadin " Sorry Abee , tashi ka koma ka yi barcin ka , ka ce yau ba ka da class "
a hankali ya dago kan shi ya na wani dan lumshe idanu , har ya bude baki zai yi magana wani dan saurayi ya shigo dining room din ya na sallama
kamanin shi daya tak da Abeeram kamar Twins , sai dai shi kananan idanu ne da shi amma kwayar cikin su blue ce irin ta Abiram
ya na sanye da wandon Tracksuit white color sai singlet ita ma white color , wannan murdaden jikin nashi duk a waje , har wata yar zufa ya ke yi da allamun da ga Gym ya ke
a hankali ya karaso wajen Abeeram ya manna mishi kiss saman kumatu ya na fadin :" Benjamin , har ka tashi ? yau ai ba ku da class "
wani dan karamin murmushi Abiram ya saki kafin ya ce mishi " Ashur , ni ma ban san yadda a ka yi na tashi ba , ga shi yanzu barci na ke ji "
a hankali ya kai hannu saman kan shi , ya tirje mishi gashi ya na fadin " All right , Chef ka shirya min breakfast yanzu ina zuwa " ya na gama fadar haka ya janye hannun shi ya fice dining room din
a hankali shi ma Abeeram ya mike tsaye
da sauri Chef ya ce mishi " ba za ka sha fruits din ka ba ? "
" no , ka shirya min smoothie kawai , ina parlour " ya fada ya na fara takawa ya fice dining room din
kai tsaye parlour ya dawo ,
parlourn irin wannan Sofar doguwar guda daya ce a kawata shi da ita , sai wasu one seaters guda biyu kusan juna dukkan su Sky blue color , da ga tsakiya kuma wata kyakyawar table ce ta glass fara kal
kai tsaye doguwar sofar nan ya nufa ya haye ya konta , ya daga kafa ya daura ta saman forehead din sofar , ya kai hannu ya janyo wani pillow da ke ajiye wajen chock din sofar , ya tada kai da shi ya lumshe idanunshi
ko five minutes bai yi ba da konci Chef ya shigo parlourn ya na rike da wani dan karamin tray , dauke ta wani glass a sama chake da smoothie pink color da allamun na strawberry ne , an saka wata straw a ciki
kai tsaye saman table din tsakiya ya ajiye tray kafin ya kalli Abiram ya ce " Abee , ga smoothie din nan "
ba tare da ya bude idanun shi ba ya ce mishi " okay , na gode chef "
gyada mishi kai kawai chef ya yi kafin ya bar wajen ya koma kitchen
ya na shiga ko Abeeram ya bude idanun shi , ya sauko da kafafun shi sannan ya mike zaune , a hankali ya kai hannu ya dauki glass din saman tray , sai ya ga har da wani dan karamin plate na cookies , wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya kai hannu ya dauki cookie guda ya kai a baki sannan ya kai bakin straw din cikin glass a bakin ya dan ja , har wani dan lumshe idanu ya ke da ga gani ya na jin dadin Abun
ya na zaune a haka wasu samari biyu su ka fara sauko stair a tare , guda na sanye da Jeans Black color da t-shirt Red color , gudan kuma ya na sanye da Trouser purple sai shirt white color mai dogayen hannu ya soke ta a cikin trouser din shi kuma gashin kan shi brown sabanin dayan black curly ne , amma dukkan su gashin ya dan taru ya zubo musu har bayan keya
mai Black curly hair din ba zai wuce 25 years ba , dayan kuma 27
kamanin su daya tak tak kamar an tsaga kara , ga shi kuma su na kama sosai da Abeeram kallo guda za ka yi musu ka san brothers ne , har blue eyes din su duk iri daya ne , da yanayin jikin su , da allamun fa su na gym dan su na da murdaden jiki gaskiya
a haka har su ka sauko stair su ka nufi Abiram , a jere su ka manna mishi kiss saman kumatu sannan mai black curly hair ya ce " Benjamin , har ka tashi ? yau ba ku da class ai , ko dai Ashur ne ya je ya tashe ka ? "
a hankali Abiram ya girgiza mishi kai ya na fadin " no , kawai dai na tashi ne , za ka sha smoothie ? " ya kai karshen ya na mika mishi Glass din hannun shi
a tare su ka girgiza mishi kai sannan dayan ya ce " Ramadan mu tafi , Abee sai mun dawo , ka kula da kanka ka ji ko ? " kenan wannan shi ne Abdoul-Aleem to
" sai kun dawo , but ku biyo min da ice cream yau ba zan fita ba " ya kai karshen ya na kai cookie a baki
da to kawai su ka amsa mishi kafin su nufi kofar fita parlourn su fice
cikin nitsuwa Abeeram ya ci gaba da shan smoothie din shi ,
sai da ya share wajen ten minutes a haka kafin Ya jiyo takun Ashur ya na sauko stair
ya na sanye da wani Trouser brown color da wata Polo red color mai dogayen hannu da sneakers farare a kafafun shi ya na taku cikin nitsuwa
a haka har ya karaso cikin parlourn ya zauna geffen Abeeram ya kai hannu ya dauki cookie guda ya kai a baki kafin ya ce mishi " Abee , please cewa Chef ya kawo min breakfast "
turo dan bakin nan nashi Abeeram ya yi ya na fadin " ni gaskiya babu inda zan je , ka kira shi mana "
" ka ga abun da ke gama ni da kai , please je ka amso min "
wani dan karamin gunguni Abeeram ya yi kafin ya mike tsaye a hankali ya fara takawa ya nufi kitchen ya na turo dan bakin nan nashi
da kallo Ashur ya raka shi har sai da ya shiga sannan ya yi wata yar karamar dariya
Ko one minute bai yi ba da shiga ya fito ya na faman turo baki ya dawo saman sofar ya zauna
ya na zama ko Chef ya fito da ga cikin kitchen din rike da tray , dama ya riga da ya shirya komai kawai jira ha ke Ashur ya fito
kai tsaye saman center table ya ajiye kafin ya juyawar shi ya koma kitchen
ya na barin wajen Ashur ya fara yin breakfast din shi cikin konciyar hankali
a hankali Abeeram ya konta mishi a saman shoulder
wani dan karamin murmushi Ashur ya saki kafin ya ce " what happened ? "
a sanyaye Abeeram ya ce mishi " Ashu , akwai wata yarinya a university din mu , kullum in na je na yi mata magana sai ta kyale ni , ko gaishe ta na yi ba ta amsawa ni kuma gaskiya ba na jin dadin hakan saboda duk makarantar ita kadai na ke bude baki na gaishe ta amma ta share ni "
murmushi mai dan sauti Ashur ya yi kafin ya ce " na tambaye ka mana ? me ya sa ka ke gaishe ta , tun da ba ta amsawa ka kyale ta kawai "
cike da shagwaba Abeeram ya ce mishi " Ashu , ba zan iya ba , ko na ce ba zan yi mata magana ba sai na yi mata , ban san me ya sa duk lokacin da na gan ta sai na ji wani bakon yanayi cikin zuciyata , jiya har mafarkin ta na yi ta na min magana "
wani dan karamin murmushi Ashur ya saki ya na ga fa autan nasu ya fada tarkon soyayya , to wacece wanan yarinyar ?
ya yi nisa duniyar tunanin shi kawai ya jiyo Muryar Abeeram ya na yi mishi kukan shagwaba ya na fadin " Ashu , please tell me ya zan yi na daina kula ta , ni ba na ma son na sake ganin ta , please ka yi wa captain magana a sauya min university ni ba na son wannan , in kuma ba a sauya min ba ba zan sake zuwa makarantar ba "
wata yar karamar dariya Ashur ya yi kafin ya juyo ya kalli dan uwan nashi ya ce " ka na ji ko Benji ? gobe idan ka koma school ka je ka fada mata wannan abun da ka fada min , amma in ka tashi fada mata ka yi kamar ka na cikin bacin rai , ka yi maganar da dan karfi yadda za ta ji tsoro , ita da kanta za ta yi maka magana nan gaba "
wani kyawatencen murmushi Abeeram ya saki ya na fadin " Ashu da gaske ka ke za ta min magana ? "
a hankali Ashur ya gyada mishi kai ya na murmushi ya ce " Eh , in kuma bayan haka ba ta yi maka magana ba , ka dawo ka fada min zan yi maka maganin ta "
wata yar karamar dariya Abeeram ya yi kafin ya ce " shikenan , yanzu tashi ka je ko ? kar fa ka yi late "
da to kawai ya amsa mishi kafin ya kammala breakfast din sa , ya sha ruwa , sannan ya mike tsaye , ya dan sunkuyo ya mannawa Abeeram kiss saman forehead , da kumatu , sannan ya yi mishi kiss saman lips din sa kafin ya ce " sai na dawo "
wata yar karamar dariya ya yi kafin ya ce " ni ka daina yi min kiss saman lips , ba na so " ya fada cikin yar shagwaba
murmushi mai dan sauti Ashur ya yi ba tare da ya ce komai ba , ya fice gidan
🥂 GIDAN MAZA 🥂
👻 ( THE MAFIA'S HOUSE ) 👻
____FUNNY , DRAMATIC , REVENGE , ROMANCE & DESTINY ____
🔥👑 MALLAKIN MEERAH 👑🔥
FOR INFORMATION +22798999753 WHATSAPP ONLY
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP
https://chat.whatsapp.com/LWmuu0yv6C9DAhpdepDb4i
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ،