Showing 36001 words to 39000 words out of 103342 words

Chapter 13 - ALJANAR FATIMA Complete Hausa Novel

King Boy   

13 Jul 2025

7829

ta yi wurgi da magen. Magen na zuwa kasa sai kuma ta mike da kafa biyu ta fara tafiya irin
ta mutana. Murmushi magen ta nufo Ameera tana yi "Kawata ni zaki di ga yiwa iyen wannan?.
Ce kace dai baki shan ko ni wacece ba ni ce fa". Magen ke magana wa Ameera maganar irin ta
yara. Karkarwa Ameera ta fara. Mugun tsoro ne ya kamata nan take ta fara kuka domin tama
rasa abunda zatayi.




Durkushe wa tayi kasa tana bada hakuri hade da cewa magen tayi mata rai!. Wata 'yar siririyar
dariya magen tayi lokacin da ta zo tana zagaya Ameera da kafafunta biyu biyun kuwa tana
jujuya su kamar hannu. "Haba kawata ni fa ba abunda zan miki ko baki gani ni ba ni ce fa".
Aljanar ta fadi haka lokaci da ta tsaya a gaban ameera ta tsura mata idanu da suka juye suka
koma Ja Blue. Ameera kallo daya tayi mata ta kara tsoracewa. Domin ko a tarihi bata taba jin
mage mai (blue eyes) ba, wannan ya tabbatar mata da cewa aljana ce. "Dan Allah kiyi min rai!.
Me nayi miki dan Allah me na tsare miki idan naman kike so ki dauka Wallahi na yafe miki,
kuma Wallahi nayi alkawarin zan sayo miki rago dan Allah amma ki kyale ni". Murya na rawa
Ameera ke magana haka duk jikinta rawa yake. Magen hannu tasa a bayanta ta fiddo w wani
dan bakin glass (ko daga ina oho) makala shi tayi a fuska. "To shikenan tunda kin tsane ni na
tafi bazan kara kawo miki ziyara bama". Ameera cike da farin ciki tace "To Mama na Allah ya
tsare hanya". Magen ce ta juyo "Au! Na manta ban gaya miki ba na iya kitso ko za'ayi miki?".
Da sauri Ameera ta dago "A'a Wallahi na gode jiya aka min". Ta bude kai "kin gani ma". Ta bude
kai kafin ta dago taga ba magen sama ko kasa. Tashi tayi cike da tsoro tana waige-waige a
dakin. Fitsarin tsoro ne yazo. Da sauri ta nufi ban daki dan ta juye shi. Bude ban dakin tayi
hade da ihu!. Itama ta cikin ihu tayi. Ameera ce ba bambanci ko kadan har kayan jikin ta.
Baza ka iya banbanta su ba. Kanta ne ya shiga juyawa hannu na karkarwa ta nuna ta cikin da
dan yatsa "Ke wace ce ke mai kama dani. Ko Aljana ce?". Ta cikin ce itama ta mai do da shigen
tambayar "Wacece ke ko aljana ce?...............................................



Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee king boy

��

*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*

��

Page 45-46


NA. ✍KING BOY ISAH


✍ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍

*DEDICATED TO YOU QUEEN HAUSY*

Wannan page kyauta na baki, Ina taya ki murnar kammala littafin ki

����������
*ILLAR BASHI PART 1*
����������

Littafin ya fadakar kuma ya tunatar hade da Tsoratar wa ga masu cin bashi Suki biya. Ina fatan
wannan ya zama izina ga masu irin halin Cin bashi Su tuba su Daina In kuwa ba haka ba Suma
Zasu iya ciyo bashin Aljana kamar yanda Yake a littafin


Mun gode kwarai da gaske Allah ya saka da Alkhairi Allah kuma ya baki hakuri kici gaba
suburbudo mana Littafai. Muna jiran Next






*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Kanta ne ya shiga juyawa hannu na karkarwa ta nuna ta cikin da dan yatsa "Ke wace ce ke
mai kama dani. Ko Aljana ce?". Ta cikin ce itama ta mai do da shigen tambayar "Wacece ke ko

aljana ce?.~

»»Bangane me kike nufi ba. Ai nice Ameera dama akwai wata Ameera ne mai kama dani
komai-da-komai kamai ni?. "Aljanar ce ta kwada ihu! "Wayyo aljana" Ta nufi kofa a guje da
ganin haka itama Ameera ta da sauri. Mama asiya a tsaye sai fada take kirtawa Fiddausi ba
wanda ya kula ta ihu! Suka ringa ji har na mutum biyu ta cikin dakin. Hakan yasa suka tsare
kofa da kallo. Ameera Aljana ce ta fara fitowa a guje tana ihu ta rukunkume Mama asiya da
kadan ta kayar da ita. "Miye-miye?". Haka mama Asiya ta fara jero wa Ameera aljana tambaya
ita kuwa kofan daki take nuna wa tana fadin "Mama Aljana...". Kafin ta rufe baki sai ga Ameera
ta Asali ta fito daga daki sautin Muryar ta da kuma ganin ta da akayi shi ya firgita duk 'yan dakin
gaba daya akayo waje da gudu. Ameera kuka ta fashe da shi ta bisu a guje tana fadin "Mama ni
ce fa wannan ce aljanar". Mai gadi na dakinsa da jin ihun jama'ar gida da sauri ya dauko Adda
ya fito ya nufe su yana kiran "Mine ne-Mine ne?. Nasmat da Asmart sune gaba wajen gudu da
su ya fara cin karo basu tsagaita da gudun ba suka bashi amsa "Aljana ce". Da fadar haka ya
buga ta kobi a kasa tayi dan kara cike da kuri yace. "Kul!-Ubanta Aljanar". Ya nufi falo a guje Ya
kusan isa kofar falo kenan sai ga Ameera ta fito da ganinta yaja wani uban burki ya fadi kasa a
tsora ce domin yaga Ameera a cikin 'yan gudu



"Dan Allah Aljana kiyi hakuri ki rufa min asiri na tuba bazan kara ba. Duk abunda na fada
Wallahi cika baki ne ban dauka da gaske Aljanar bace". Da sauri Mai gadin ke fadar haka yana
jan kugu yana da baya-da baya, Hannu Ameera ta mika mishi "Mai gadi Wallahi nice Ameera.
waccan ce Aljanar Wallahi taba ni ka gani". Ai kafin hannuta ya karaso gare shi tuni yayi wani
irin juyi Ya tashi ya zabga a guje. Duk uban gudun da su Nasmat suke yi sai da mai gadi y tarar
da su har ya wuce su, Bai bi ta kan bude gate ba domin gani yake kamar bata lokaci ne Ta kan
Gate din ya haura su Nasmat lokacin suka karaso ganin sunja gate din a kulle yasa suka fara
kokarin hawa ta gate suma. Tuni Suka haye Su juwaira mama asiya da hauwa Duk sun tsure
Ga Nin Ameera ta nufo su Tana fadar "mama nice Wallahi ta kusa da ku ce Aljanar". Itama
kuma Aljanar abunda take fada kenan cikin tsiwa Kara rikita Su mama asiya take da fadin "Gata
nana aljana Aljana". Gaba dayan su rudewa suka yi kowa jikinsa rawa yake. Ganin wannan ba
mafita bace Juwaira da Hauwa suka fara kokarin Haurawa ta gate din suma. Mama asiya dake
tasan jikinta yayi nauyi ko gwada wa batayi ba. Sai bada hakuri wa Ameera take. Juyawa tayi
ta kalli su Juwaira da har sun kusa haye wa. Wani mugun bakin ciki ne ya ziyarci zuciyar ta.
Domin taga zasu gudu su barta. Kafafuwan su ta kama da nufin itama ta hau kan gate, Abunka
da mai jiki tana kamawa kuwa ta rinjayo su. Da nauyinta suka rikito kasa gaba daya. Ameera
Aljana ta faki idanunsu ta mayar da hannunta key ta bude gate din Da gudu ta fita tana "kufito
karta cinye ku". Tashi sukayi Kamar ba sune suka fado daga sama ba a million suka fito daga
gidan Ihu! Suke da karfi suna fadin jama'a Aljana Ita kuwa Ameera bata dai na binsu ba. Su
kuwa su asmart lokacin da suka diro daga gate tuni mai gadi har ya kusan fita daga layin ai
kuwa suma suka bishi tuni sun bar layin.

Tafe suke shida amaryarsa A tsakar gida sun nufo wajen mota da alamu fita zaiyi.Dam matashi
ne cikin shigar sa ta 'yan sanda ASP Abdul King Article kenan. Ba abunda yake zurarwa
amaryar nan sai karya. "Ai in gaya miki Zainab ba karami dace kikayi ba da kika same ni a
matsayin miji. Wallahi kin gama dace wa". "Allah mai gida". Amaryar ta fada cikin mamaki.
"Allah kuwa. Ke kinsan irin jarumta ta kuwa?. Duk garin nan magana ta ake duk inda kayi sai
dai kaji ana maganar Asp Abdul King Article, Irin barayin da nake kamawa da 'yan iska Allah
yayi yawa da su. Ke ni fa ko Aljani yayi sata in dai a yanki na ne ina tabbatar miki kafin Gobe sai
na shako shi". "Kai mai gida Aljani kuma?, Ni fa gaskiya tsoran Aljanu nake yi". Hahahaha 'yar
kuntuwar dariya ya yi "Kamar dai kin manta labarin da na baki ranar nace na kama barawo
Aljani kin dauka wasa nake ko?. To ai shekaran jiya ma na kama aljani barawo". Ya fada yana
wulwula yar feston din dake hannun sa. "Innalilahi, bani labari mai gida". "Wani dan iskan
barawo muka kama a Kasuwa ya saci waya ashe Alja...". Bai karasa maganar ba suka jiyo
ihun su mama asiya Ana Aljana-Aljana. Mai gida kamar fa Aljanar nake ji



Ana fada kuma kamar neman taimako suke". "Ai na gaya miki da na damki wuyan barawan
nan na fara jibga..." Asp ne yake wannan maganar dan a manta da Zancan. Zainab ta fahimce
sa hakan yasa ta takura mishi Sai da ta tursasa shi a kan sai yaje ya gano. Bai so ba cike da
tsoro ya nufi gate din tana biye da shi a baya. A hankali ya bude gate din ya dan leka lokacin
kuwa yaga su Juwaira a guje sun wuce suna faman ihu ciki har da Ameera ya gani. Juyawa
yayi baya dan ganin abunda ke binsu din. Yana ganin wannan ameerar sak! take da ta gaban.
Tsoro ne ya kamasa dan yagane alamun wannan ce aljanar. Da karfi ya juya ya banke Amaryar
tasa ta fadi kasa bai bi ta kanta ba ya Ruga daki a guje. Itama kuta tashi ta bishi da gudu. Yana
zuwa cikin wardrobe ya shike ya rufe duk da a mats........................


Alqur'an Na gaji Dama yau bajin type din nake ba.


Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee king boy




��

*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*

��

Page 47-48


NA. ✍KING BOY ISAH


✍ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍

*DEDICATED TO YOU* ♥♥
Mineert Jibir
Jiddah A Adam
Musa Umar Abdullahi
Bilkisu Yusuf
Ummu Muhsin
Sadiya Bala
Hauwa Agabi
Maryam M Gidado
YearRya Yr Abba
Rabiu Shehu Ps
Jamila Mahmud
Naseer Saleh Babaiye
Sunusi Yusuf Jammo
Yariman Masoya
Maman Kawu
Yusuf Jibril Umar
Aslamiyyat Islam

*HAKIKA KU MASOYA NE. ALLAH YA BAR ZUMUNCI NA KUMA GODE DA ADDU'O'IN KU.
HAR KU WANDA BAN AMBATA BA. KUMA RAI NA. A KWANA A TASHI WATA RAN ZAKU
GANKU.*

Nasha dariya ba laifi. Saura kuma yanzu zakuyi taku.



*KARSHEN PAGEN BAYA*

~Da karfi ya juya ya banke Amaryar tasa ta fadi kasa bai bi ta kanta ba ya Ruga daki a guje.
Itama kuta tashi ta bishi da gudu. Yana zuwa cikin wardrobe ya shike ya rufe duk da a matse
yake...~
_»»Haka itama Zainab haka Duk da wajen ya matse su Sai da ta kutsa ta shiga. Shiru suka yi
na 'yan mintuna. Zainab tace "Mai gida wai miy...". Kafin ta rufe baki yasa hannu ya toshe mata
baki. Yana cewa. "Kiyi shiru karta jimu". Ciki rada. Sun kai kusan mintuna 10 a cikin sunyi
mukwai. Tukun can Asp ya dan leko dakin ganin ba komai yasa ya karashe fitowa. Kai gado ya
fara yana wash! Wash!. "Mai gida gaya min wai me ya tsorata ka haka ne?. Nayi mamaki
abunda ya tsorata ka yanda kake jarumin dan sanda mai fada da Aljanu..." Zainab ce ke
maganar kafin ta karashe zancen da ta dako. Asp ya katse mata "Keee!. Rufa min asiri wane ni
fada da Aljani kinga karki jawo min". "Haba mai gida kamar ba kai ne yanzu ka gama fada ba.
Kace kana kama aljanu kana cin...". Nan ma bata karasa zancen ba ya dakatar da ita. "Zainab
nafa ce miki ki raba ni da zancen aljanun nan. Ke inda kinga Aljanun da suka biyu wadancan
muta nan da daga nan sai dai a dauko ki kinyi dogon suma. Kai!, Ban karashe tabbatar da
jarumta ta ba sai yau". Asp ya fada yana kallan Zainab dake tsaye bakin ta dauke yake da
uwayan tambayoyi. "Bani labari mai gida dama ba Aljana daya bace, ni ji nayi kamar suna fadar
Aljana-Aljana". Asp ya gyara zama tukun yace "Ai in gaya miki ba aljana daya bace. Aljanu ne
sunkai dari tun daga farkon layin nan in gaya miki aljanu ne har kofae gida.abunda yasa kuma
kika ji su suna fadar Aljana, Ai wata Narkekiyar Aljana ce a gaba. Kingata wata makekiya kamar
bishiyar kuka. Idanunta in gaya miki sun kai girman tulu. Ga wasu uwayen hakora Kai fin su da
gani sunfi Raiza. Hancin ta kuwa sai a tusa mu mu biyu. Gashi a wani tabe Bama wannan ba
wuta ce ke fita ta cikin sa. Kanta kuea wani makeke duk girmansa ba gashi sai wasu kwara uku
dogaye wanda suka zubo mata har kusan gwiwa. Gata baki kirin"._





_Karkarwa Zainab ta farayi domin tuni Tsoro ya kamata. "Innalillahi, Mai gida Wallahi har naji
mugun tsoro ya kama ni. Da gaskiyar ka da ni ce na ga wannan mugun abu Wallahi da suma
zanyi a gun. Na gode Allah ma da yasa ban gani ba". Tana fadar haka ta nufi kofar daki ta
garkame cike da tsoro ta dawo ta haye kan gado can ta dukun-kune wai ita da gaske tsoro ya
kamata. Dariya yayi, "Hahahhahah kai haba dai Xainab karfa ki bani kunyi. Ba'a san matar dan
sanda jarumi irina da tsoro ba, Ai ke baki ma san wani abu ba. In gaya miki lekawar da nayi Wai
Aljana nan tayi man nuni da hannu alamun in zo. Ni kuwa naga tama raina min wayo hakan
yasa na dalla mata wata muguwar harara irin wacce nake wa kananun aljanu suna zabgawa a
guje, nan take itama kannun aljanun da suke tare da ita wajen guda goma suka zube sume.To
wai ashe ita har ta ji haushi Nan fa ta fusata ta nufo ni gadan gadan. Abunda fa yasa na rugo
da gudu kenan._

_"Lalai mai gida kai sadauki ne kuma jarumi. Ai in da ni ce da sai dai a dauko ni a group". Wani
dan kara ne suka ji alamun an dan taba kyaure, Ai kuwa Zainab ta kwadda ihu! Kafin kace
kwabo Asp king Abdul tuni har ya haura gado ya Shige blanket. Jin shiru ba abunda ya shigo
dakin ne ya sa ya fito nan ya fara kokarin Cire kayan 'yan sanda dake jikinsa. "Yallabai ya naga
kana faman cire kaya kai da zaka p
Office?". Zainab ta tambaya, "Amma sai yau na gane bakya kauna ta. In fita wato aljana ta
wujijiga ni ko?. To in gaya miki ina nan ba inda zani yaseen yanzu bara in kira Dpo in sheda
mishi bani da lafiya"_.


_Asmart da Nasmat tare da mai gadi ashe da suka sha kwana wani waje suka samu suka boye.
A cewar mai gadi "Aljana ta fimu gudu duk gudun mu sai ta kamo mu gwara mu labe kawai ta
zo ta wuce". Ameera aljana ita ce a gaba wajen gudu sai Zuwaira da Hauwa suna biye da ita.
Can baya kuwa Mama asiya ce a tubur-tubur Gudun da take yau bata taba yin kalarsa ba.
Ameerar gaskiya tana ce mata "mama ki tsaya ni ce". Duk sanda Ameera ta fadi haka ita kuwa
sai taji kamar cewa tayi. Tsaya in yanka ki hakan ke sawa tana kara kaimi a gudun nata duk da
ta gaji. Ameera Aljana tsakanin kwana-da-kwana ta bace bat!. Su Zuwaira na shayo kwana
suka ga ba mutum. Tsayawa sukayi cik! Suna haki. Su asmart ne suka fito daga inda suke a
boye suka fara Wa su Juwaira tambayoyin "Ina Aljana". Juwaira tace "Bakugwa Ameera ta
shayo kwana ba?". "Ko daya mu bamu ga wata Ameera ba". Cikin daga murya Hauwa tace
"To alqur'an wannan itace Aljanar tunda kuka ga...". Bata karashe magana ba sai ji tayi anyi ciki
da ita. Dake bakin kwana take kuma lokacin su Mama asiya suka karaso a guje. Sanda suka
wuntsula domin da karfi mama Asiya ta bangaje ta. Ameera na shayo kwana gaba daya suka
yi shirin rugawa. "Ku tsaya- Ku tsaya wallahi ni ce Ameera ta gaban ce Aljana wacce ta fara
zuwa". Tsayawa suka yi a tsorace suna kare mata kallo. Kallan zargin da suke mata yasa ta
miko hannun "Ga hannuna wata ta taba ma taji Wallahi ni ce"._



_Kowa baya-baya ya farayi Hauwa ce ta kama Asmart tana kokarin Turo ta wai ta taba taji. Ita
kuwa Asamrt ba abunda take sa kakafe wa tana cijewa, Ihu! Ta fara da taga hauwa ta fara turo
ta da karfi ga Ameera na matsowa. "Wayyo Allah uwa ta, wayyo baba wayyo jama'a ku taimako
zasu kashe ni". Asamart ce mai fadar haka da karfi. Abun ne ya bawa Juwaira haushi Zuwa
tayi ta tunkuda Asmart da karfi. Ta fada jikin Ameera ta rungume ta. da ganin haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login