Showing 96001 words to 99000 words out of 103342 words

Chapter 33 - ALJANAR FATIMA Complete Hausa Novel

King Boy   

13 Jul 2025

7819

safiyar nan?". Washe baki su Asiya sukayi "Eh wllh
Nafisa daga ina haka". Asiya ta fada. Matar tace Wallahi naje sayo abu ne. Ina zaku je haka".
Asiya ta kwashe duk abunda ke faruwa ta fada mata. Rike baki nafisar tayi hade da cewa
"Aljana fa kika ce?. Tabb! To yanzu ina zaku sama malami". Mama asiya tace "Aa gamu dai

mun fito da wajen limamin masallacin jama'a zamuje watakil a dace". Nafisa ta roke baki "ah!
Liman to bari kuji in gaya liman ba abunda zai muku. Sai dai yace kuje kuci gaba da addu'a.
Amma akwai wani malami da na sani ya kware wajen fitar da aljanu, In kun amince na hutar
daku ni zanje in kawo muku shi har gida"................................._


DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA.
SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN
KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee King Boy Isah





��

*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*

��

Page 107-108


© *KING BOY ISAH* ✍


. ‍‍ .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​
. ✍ *®Z.W.A* .

. .
_*Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร*_

​ _*Zaku iya samun littafan mu a Facebook*_

Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

_*Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu*_
Zamaniwriterassociation@gmail.com




​SAI NA AURE TA​





ωяιттєи ву:
​shamsia salis​


​Eloquence Writers Association
____________________________________
Na tayaki murnar Autar Eloquence. Allah ya kara basira. Allah yasa mu amfana da darrusan
cikin littafin amin
____________________________________

*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Amma akwai wani malami da na sani ya kware wajen fitar da aljanu, In kun amince na hutar
daku ni zanje in kawo muku shi har gida".~
_Su Zuwaira sukace "ba dai boka ne ba ko?". Nafisat tace "Aa ko daya wannan shahararren
malami ne. In kun amince yanzu ma daga nan bazan karasa gida ba sai in juya in daukko muku
shi". Mama Asiya tace "To shikenan je sanar wa mai gidan ki to sai kizo ki karba kudin mota, ko
kusa ne?". "Aa Wallahi can wani kauye ne kudin motar mutum biyu Dubu daya ne. Dubu biyu
zuwa da dawowo. Batun mai gida kuma da kike. Dallah rabu dashi miye na sai naje na gaya
mishi". Hauwa da Zuwaira tabe baki sukayi suna kallan Nafisa din. Asiya bata ce komai ba ta
fiddo dubu uku a handbag dinta ta bawa Nafisa "Gashi kije ki daukko shi muna jiranshi. Mu in
dai zai cire mana wannan Aljanar to ko nawa ne zamu iya bashi". Ta juya ta kalle su Zuwaira
"Ko ya kukace yan uwa". Da sauri suka ce "Kwarai kuwa ko nawa ne zamu iya badawa mu dai
gurin mu ta bar gidan". Nafisa tace "Karku damu aikin wannan malamin sha yanzu magani
yanzu ne". Su Asiya suka juyo suka koma gida inda ita kuma Nafisa ta tsayar da napep ta hau
tace a kai ta Sabon layi, Daga anguwar su nan naira saba'in ne. Tana sauka ta nufi wata kofar
gida wanda kofar gidan wasu samari ne ke zaune ba abunda suke sai busa sigari da gulmar
masu wucewa kan hanya. "Sannun ku dai dan Allah Aliyu ko ta bare yana gida". Gudan ya
kalle ta yace "wani abu yayi mike ne?. Ko dai yayi tsiyar ne". Nafisat tace "Ba abunda ya min ni
dai kawai ina neman shi ne in yana nan". Dayan yace mata "Yaje can sama wajen wata

cuwa-cuwar sa amma yanzu zakigan shi ya dawo". "To na gode". Nafisat tace ta koma gife
tana jiran Ko ta bare. (Sunan da ake kiran aliyu kenan). Bata jima a wajen ba ta hange shi ya
taho, Duk da kasancewar shi dattijo hakan bazai hana ka gane cewa dan duniya bane. Yana
hango nafisat ya fara wasa ta yana mata kirari. "Kaga shegiyar uwa mai saka 'ya'ya biyayyar dole, Kaga kaska rabi mai jini wanda ke da dan
kadan ma abishi a tsotse. Ke ba maciji ba kinfi macijin dafi. Da ganin nasan bakin ki a kwai
batu. Dan banza bata kai zomo kasuwa._





_Kuma Wallahi da kaga kura ta ba nama ka tabbata ba dan Allah ta barshi ba. Yanzu dai miye
labari ne". Nafisa kam kallo kawai take binshi da shi tana murmushi domin ita da shi kar ta san
kar ne. Daya baya neman daya sai za'a aikata wani mugun abun wanda za'a dan fizgi wani abu
a ciki. Tana yar dariya tace "Shege Ko ta bare, Wato ka san dai in ka ganni gidan ka ba banza
ba". Yace "Eh mana ai nasan bazaki taba wanke kafafun ki takasan ki kawo min ziyara ba. Da
gani nasan akwai wata harkar ne". "Tabbas kuwa akwai babbar harkar. Wacce in dai ka yarda
zakayi nake gaya ma zamu sma kudi sosai". Aliyun yace "Gaya min mana kinsan fa ni dan
kasada ne bakiji suna na bama. Ai kawai ko miye na zanyi in dai za'a sama yan karafa". Nafisat
tace "Yauwa mutumina. To dama can wasu makwabtan mu ne suka neman za'a fitar musu da
aljanu, kuma gidan masu kudi ne. Watakil ma ba wani Aljani kawai firgitane suke. Shine wai na
hadi da su a hanya zasu je neman malami mai fidda Aljanu to kawqi ganin za'a sama wani abu
shiyasa ma wannan shawarar ta zo mun". Tsuru ya tsare ta da ido yana mata kallan yan iska.
Lura da hakan yasa tace "Kai malam bana san wulakanci ya zaka wani zura mun na mujiya. Ko
naci ban biya bane".
A fusace yace,"Ina fa kika biya, ai bansan dan banza kika dauke ni ba sai yau". Cikin rashin
fahimat da neman karin haske tace, "Ban gane na dauke ka dan iska ba?". "Kwarai kin dauke
ni dan iska tunda. Har wai ni zaki ce naje na cire Aljanu. Yo na cire Aljani ko kuma Aljani ya cire
ni". Kwashewa da dariya Nafisa tayi, Zuwa can kuma ta dan tsakaita hade da cewa,"Ko ta bare,
wallahi ban taba sanin kai mugun matsoraci ne ba sai yau". "Aa ba tsoro bane, ai gaskiya ne.
Duk iskancina ai bazanyi wa Aljani ba.kinsan ance aikin guguwa ta dau kara da karmami, bata
shiga rumbu ta dauko dammunan hatsi". Nafisat tace, "To kwantar da hankalin ka. Wannan kar
ya dame ka, dan bana tunanin aljanun gaske ne. Ni ina tunanin ma kag'e ne sukeyi mata". Aliyu
ko ta bare yace,"Au! Kina tunanin ba aljanun bane". Nafisa tace,"Kwarai ba Aljanu bane
iskancin sune kawo irin na masu kudi". Ko ta bare yace, "To in dai haka ne na amince". "Yauwa
ko kai fa. To yanzu abunda za ayi shine, ka shiga gida ka sako fararen kaya sababbi, masu
babbar riga da katan charbi sannan ka fito muga ko kayi kama da malami. Dan in bakayi kama
da malami ba wallahi wani zan nema in sashi wannan aikin". Gemun shi yaja hade da
cewa,"Haba ai ni din nan da kike gani in nasha manyan kaya bazaki iya banbanta mu da
limamin anguwar ku ba. Yanzu bari in sako kayan sallah na". Ciki ya shiga ya sako shadda ce
fara kal har dauka ido take, yasha malum-malum ga hula zannah. Matsalar daya baya da
charbi. Nafisat na ganin shi tace komai yayi. Nan yake gaya mata cewa bashi da charbi. Nafisat

tace ba komai suje kasuwA._„




_Nan take suka nufi kasuwa ta sayo mai katan charbi hade da wasu turaruka. Ya fashe jikin sa
sai kanshi yake kamar sabon ango. Sun taho a hanya Nafisa ke tsara mishi yanda zaiyi take
fada mai sunce Yarinya ce karama mai aljanun dan haka abunda zaiyi shine yace a saka su
daki daya su kwana idan yaga asuba ta kusa kawai sai ya shake yarinyar ta suma. In yaso da
asuba sai yace ya gama fitar da aljanun a sallame shi sai ya gudu. Fashewa yayi da dariya
yace ya fahimta. Bayan sun kamalla duk shirin su suka nufi gidan. Nafisa ta fara shiga ta sanar
musu gashi ta zo da malamin, Su mama Asiya suka ce ta shigo da shi ciki. Makeken carbi ne a
hannun shi yana ja bakin shi na motsi ka rantse da Allah kace tasbihi yake, Alhalin shi kanshi
bai san abunda yake fada ba kawai motsa bakin ne. Da shigowar shi falon ya kwashi kamshi.
Su Asiya na ganin shi suka zube kasa cikin ladabi da girmamawa. Nafisa a ladabce ta nuna
mishi 1star tace ya zauna. Da bismillah ya zauna nan take su Mama Asiya suka fara kwasar
gaisuwa. bayan ya gama gaisawa yayi hamdala tukun ya fara daga kai yana kare wa falon kallo
sama da kasa yana jijiga kai alamun a kwai magana. Cikin ladabi Nafisat tace "Malam me ke
faruwa?. ko aljanun ne". Gyaran murya yayi tukun ya kalli mama Asiya yake cewa sunyi sakaci
da har suka bari Aljanu suka cika musu gida haka. Cikin hanzari ya nuna wani bangare a falo,
kunga ga fatalwa can ma ta fito daga dakin can zata gudu. Kunsan fa aljanu ko fatalwu basa
yarda su hada wajen zama dani in dai ba masu shegen taurin kai ba. Su Mama Asiya kallan
wajen da ya nuna sukayi wayam ba kowa, Zuwaira tace,"Allah shi gafarta malam fatalwar da ta
gudu yanzu mace ce ko namiji?". "Mace ce gata can fara ce kuma siririya". Sallalami suka fara
gabaki dayan su. Nafisat ta tambaya me suke wa sallalami, mama Asiya tace, "Kin manta
kishiyar mu uwar Fatima wacce ta mutu". Nafisat tace "Na tuna ta, ko kuna tunanin itac
fatalwar?". Zuwaira tace, "Kwarai ita muke zargi domin aljanun ma duk a kan yarta Fatima suka
tare". Aliyu yace, "Ba mamaki itace, Domin kuwa nayi mamakin ganin gadajen Aljanu ba adadi
a tsakar gidan nan. Wannan ke tabbatar min da cewa Aljanu da yawa ne ke rayuwa a gidan
nan". Asiya ta kalle shi hade da cewa, "To yanzu malam miye abun yi"._




_"Karku daga hankulan ku tunda dai gani nan na zo yau-yau sai na kore duk aljanun gidan nan.
Dan haka yanzu ku kawo min yarinyar mai suna Fatima da kuke zargin ko yar fatalwar can ce".
"Ai suna makaranta. Amma sun kusan dawowa". Inji Hauwa da sai yanzu tayi magana. Aliyu
tace, "To ai shikenan bari mu jira ta ta dawo. Dan in san ta inda zan faro". Mama asiya tace,
"Yauwa Allah shi gafarta malam, Akwai wani dana mai suna Abba da Fatima ta lankwasar mishi
da hannu. Munyi-munyi taki ta mikar mishi da hannun". Aliyu yace,"Ina yake ku kawo shi inga".
Hauwa ta tashi da sauri ta nufi dakin Abba ta kirawo shi. Yana zuwq ya zube gaban malam yayi
gaisuwa. Bayan Aliyu ya amsa, yace Abba ya miko mai makalallen hannu. Ba gardama Abba ya
mika mishi. Malam Aliyu ya ware karfin shi yasa hannaye biyu yaja hannun da niyar ya mikar da

shi ta karfi. Ihu! Abba ya kwada hade da cewa. "Wayyo zai karya min hannu". Malam na jin
haka yayi saurin sakin shi. Ana cikin haka sai ga Fatima da Fiddausi sun dawo daga islamiyya.
Da shigowar su falon, Fatima ta fara hararen malam aliyu ko ta
bare.......…………………………………………………………_

� Lalai Malam Aliyu cire Aljanu da kyau ���

DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA.
SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN
KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee King Boy Isah






��

*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*

��

Page 109-110


© *KING BOY ISAH* ✍


. ‍‍ .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​
. ✍ *®Z.W.A* .

. .
_*Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร*_

​ _*Zaku iya samun littafan mu a Facebook*_
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

_*Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu*_
Zamaniwriterassociation@gmail.com




*KARSHEN PAGEN BAYA*
"Wayyo zai karya min hannu". Malam na jin haka yayi saurin sakin shi. Ana cikin haka sai ga
Fatima da Fiddausi sun dawo daga islamiyya. Da shigowar su falon, Fatima ta fara hararen
malam aliyu ko ta bare.~


_Tunda yaga tana zare mai ido ya gane cewa itace Fatima hakan yasa yayi saurin mikewa
tsaye yana kallanta yana tofe-tofe. Su Zuwaira sukayi saurin mikewa suma. suna cewa,
"Yauwa malam itace wannan din". Malam yace ai ba sai kun gaya min ba. Domin tana shigowa
naga Aljanu da ifiritai kusan million a tare da ita. Amma ni naga ma kokarin ku da har kuke iya
kwana a gidan nan. Shin wai basa baku tsoro ne". Zuwaira tayi sauri tace,"Ai ba tsoro kadai
bama har da duka. Mu dai malam ka taimaka". Aliyu yace,"Karku damu, Yau bazan bar Aljani
ko daya ba a gidan nan. Amma aikin ku fa nada wahala sosai gaskiya domin ma yau ta kama
dole ma sai na kwana a gidan nan". Gaba saya suka ce ba damuwa su dai gurin su a fitar da
aljanu. Nafisat kallo kawai take bin Aliyu da shi.Yanda ya takarkare yana zuga karya wa su
mama Asiya. Kamar wani malamin kwarai._




_Fatima da Fiddausi basu wani tsaya sauraren su ba. Kai tsaye dakin su suka wuce. Malam na
kiran Fatima! Fatima! Ko wai-wayen shi batayi ba. Balle ya sa ran zata juyo. Zaunawa yayi
yace da su mama asiya yana bukatar kayan aiki. Domin yanzu zai fara. Su mama Asiya suka
tambaye shi dame-dame yake bukata. Nan yake gaya musu cewa Yanzu dai yana bukatar daki
guda. Sannan a sayo soyayyun kaji amma a tabbatar da farare ne.yaci gaba sa ce musu a
samo abinci kamar fillet biyar pure water leda daya. Domin ina so zan kafawa Aljanun gidan nan
tarko ne dan akwai masu shegen gudu. Wanda zan kama ta dalilin abincin nan. Sai da ya gama
lissafin shi su mama asiya suka tura mai gadi yaje ya hado duk abuda malam ya bukata. Dakin
da aka ware mai yace a kai kayayyakin. Sannan ya tashi ya shiga dakin hade da ce musu yana
zuwa. Wani mugun kallo Nafisa tabi shi da shi. Wato sai yanzu ta idasa gano tantirancin Ko ta
bare. Asiya tace "Mu ko nawa ne zamu iya kashewa, in dai za'a fitar da Aljanun nan"._

_Nafisa tace,"Karku damu ai in dai wannan malamin ne bani da shakka a kanshi. Aikin shi
kenan kama Aljanu". Su mama asiya sukace Allah yasa su fita domin kuwa yan taurin kai ne.
Aliyu na shiga dakin ya fara debar girki sanda yaci abinci sosai yaci ya koshi yaci nama san
ranshi tukun ya sha ruwa ya goge bakin shi. Filet biyu ko wanne da kaza a kai ya fito da su
yana tofe a ciki. Kamar mai addu'a da gaske. Yace wa su mama asiya su sa a daukko sauran
abincin da naman a kai bayan dakunan amma a rufe. Yake cewa yasan aljanu da shegen
kwadayi suna zuwa dauka zasu makale. Dan karfin addu'ar da yayi a ciki. Su mama asiya da
kansu suka shiga suka dakko sauran abincin sunyi mamakin ganin anci abincin har hauwa ta
kasa daure wa da ta tambaye shi. Sai yace Aljana ce taci lokacin da mai gadi ya kai su. Wai
kafin ya karasa Aljanar taci kuma ma wai ya kashe ta._





_Haka dai suka raraba abin cin nan harda ruwan. Duk abunda suke mai gadi na kallan su ga
muguwar yunwa da yake ji. Nafisa kuwa banda harara ba abunda take aikawa Aliyu. Waje ya
samu ya zauna a falo aka kunna fanka aka kawo gaban shi aka kuma kawo abinci da lemu.
Malam yace ai shi ya koshi domin Aljanu ke kawo mishi abinci duk lokacin da ya bukata. Baici
ba sai Nafisa aka bawa ta cinye. Yana nan gidan har dare yayi ita kuwa Nafisa sallama tayi
musu a kan cewa gobe zata dawo.Aliyu Da yaga ish'i tayi sai ya faki idanun mutane ya zagaya
bayan daki wajen abincin nan yana zuwa yaga duk an cicinye naman nan haka abincin ma duk
an babata gun. Daga can yaga wani flat din wanda ba'a taba ba. Sai da yaci ya koshi tukun ya
goge bakin shi yaje yace wa su mama asiya suzo su gani. Suna zuwa sukaga duk anci abincin
nan an rage wani wajen an fara cin cinya an yar. Ruwan ma duk an fafasa anyi wasa da shi.
Tambayar shi sukayi a kan waya ci abincin.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login