Showing 6001 words to 9000 words out of 103342 words
domin a lokacin daki ya shiga ya rufo. Kawu abba kuwa yaje yana tambayar maman mu ta fada
mishi abunda ya faru amma taki gaya sai dai itama zubda hawaye take.
Da da dare.
Har wajen karfe sha daya baban mu baiyi barci ba domin kuwa yasan halin dan uwan nasa zai
iya turo mishi barayi su kwashe kudin kamar yanda ya fada. Kudin wasu filayan sa ne guda
biyu ya sayar million biyu da rabi shine kawu mansur yazo ya tsare shi wai sai ya bashi million
daya yaja jari. Shi kuwa baban mu yace yayi hakuri ba yanzu ba yanzu akwai abunda zaiyi da
kudin. Shine abunda ya faru har kawu mansur yaji haushi ya hau fada harda barazana.
Karfe 12:30am da yaji shiru-shiru ya kwanta a tunaninsa dama barazana ce kawai. Bai dade da
kwanciya bq yaji hayaniya a kofar gida kuma kamar muryan mai gadi can kuma sai yaji ya
kwala wani ihu! Wanda ya shaida mishi ba lafiya ba. Cikin sauri ya dauki jakar kudin ya nufi
dakin kawu abba wanda muma a can muke a kwance. Bayan ya tayar da mu ya bawa kawu
abba jakar kudin yace mu gudu ta kofar baya ga barayi nan sun zo wai shi zai tsaya in suka zo
yace kudin basa a tare da shi.
Kawu abba yayi juyin duniyar nan a kan baban mu ya taso ummanmu mu gudu tare amma yaki.
Jin ana bubuga kofar palo ana neman ballata a shigo yasa ya ja hannun kawu abba har bakin
kofar baya ya bude muna muka shiga nan fa muka bude yar kofar muka hau gudu. Bamuyi nisa
ba mukayi yo wani ihu wanda muka tabbata na baban mu ne. kawu abba ya mika min jakar
yace mu shiga wani dan lungun mu buya bari yaje ya gano. Haka kuwa akayi muka shiga wani
dan guri mai duhu muka boye shi kuma ya koma, ko da shigarsa palo sai ya tarar an kashe
baban mu da maman mu 'yan daban suna ganinshi sukayi chaf da shi suna cewa ga wanda aka
bawa ajiyar kudin.
Baban cikin su wani kato ne baki mumuna fuskarsa kadai abar tsoro ce. Shine ya tambayi
kawu abba cikin tsawo ya fada mishi ina kudi amma yaki. Nan fa suka hau bugo naushin sa da
mangarar sa. Hada masu yankarsa da dai yaga zasu kashe shi sai ya tsaida su yace zai fada.
Nan take ya shaida musu kudin na wajen mu kuma ya nuna musu hanyar da muka bi. Koda
gama nuna musu sai ogan barayin nan yasa hannu biyu ya murde wa kawu abba kai nan ya
fadi matacce, su kuwa suka biyo hanya neman mu.
Tun daga nesa na hange su sun nufo hanyar da torch a hannunsu suna ha haskawa da dai
naga in suka iso gare mu ba shakka sai sun gan mu. Nan take na kama hannun kanwata na
dauki jakar muka ruga a guje. Har mun danyi nisa tukun suka hango mu. Suka kuwa rufa mana
baya, tsabar gudu ban sani ba ta tsakiyar wasu masifafun karnuka na anguwar mu nabi. Ai
kuwa suka hayayako har sun nufo mu kuma suka juya sakamkon jin gudun barayin nan. Nan
muka barsu suna fama da karnuka inda mu kuma muka tsero fada mar nan yau kwana biyar
kenan da faruwar haka in mukaji yunwa sai in dauki kudi in shiga gari in sayo mana abinci.
Wata doguwar ajiyar zuciya nayi da jin labarin yaron nan. Nace "masa yanzu ina kudin?". "Zan
dauko maka ne kawai domin na yarda da kai ina ganin tausayi a idan ka kamar bazaka cuce mu
ba". A cewar yaron, kallonsa nayi nace "gaskiya ka fada yaro ni ba kamar kawun ku mansur
bane ku dauke ni kamar kawun ku abba". Nan take yaron ya tashi yaje ya daga wasu ciyayi
ya fido katuwar jakar ya kawo gabana ya ajiye. Kwata-kwata yarinyar bazata haura shekara 8
ba shi kuwa babban namijin zaikai shekara 13 ko sama da haka.
Koda ya kawo jakar gabana ya bude naga makudan kudin dake ciki kudin da ban taba ganin
masu yawansu ba a duk tsawan rayuwata. Nan take naji zuciyata ta canza daga tausayi ya
zuwa rashinsa zuciyoyi suka fara aikin bani shawar wari wasu na cewa in kashe yaran nan in
mallaki kudaden wata zuciyar kuwa na cewa in dauke su in kaisu gidana. Daga karshe dai na
aminta da shawara ta farko wato in kashe sun nan kuma na fara tunanin hanyar da zan bi dan
kashe su. Sai kuma na tuna a kusa da ruwa fa muke, banyi wata-wata ba nasa kotar gatari na
na bigi kan yaron domin nasan shine zaifi bani matsala nan take ya fadi kasa matacce, da ganin
haka sai yarinyar ta fara ihu! Ni kuwa ganin zata tona min asiri na shake wuyanta har ta langabe
gaba dayansu na kwashe su na zuba a wani ruwa dake wucewa ta tsakiyar fadama. Ruwan
yaja su ya tafi da su, ni kuwa na dauko kudin na dawo gida nayi karyar cewa gonar mu na sayar
mutane kuwa ciki harda matata da babanta gashi suka aminta sukayi farin ciki. Ba'a dade ba
na bude shago na kama sana'a dan gudun kar kudin su kare. Ko da ganin na sama wannan
kudi sai na shiga sabuwar rayuwa wato ta rashin mutunci bana ragawa kowa kuma bana san
kowa ya raga min watta matata taga canji sosai a tare dani, ko ta bangaren addini na samu
tawaya domin ko makaranta daina zuwa nayi wannan shine abunda ya faru inji Mukhtar.
"Innalilahi wa'inailaihir raji'un". Wannan kalmar ce take fita a bakin Ummiey da kuma mahaifinta.
Nan da nan ummiy ta fara kuka tana fadin "Mukhtar haka kake dama ashe zaka iya kashe
mutum ashe ba iyakar rashin mutun cin kawai kake da shi ba harda rashin imani?". Haka ta
jero mishi wadan nan tagwayen tambayoyin wanda shi kanshi baisan wace kalar amsa zai bata
ba sai kawai hawaye dake fita a idanunsa da gani kasan yayi nadama. Ummiey zata daga baki
tayi magana abbanta ya dakatar da ita. Lokacin aljanar tace ina zuwa.
Bat! Ta bace lokaci daya kuma sai gata ta dawo ita da wata yarinya wacce da gani a galabaice
take tana cikin kunci da tsadar rayuwa kaysn jikinta kadai zasu fada maka hakan. Koda yarinya
da aka kawo mai suna maryam taga Muktar sai ta fashe da kuka ta tashi ta ruga a guje, har ta
kusa kai bakin kofa aljanar nan ta mika hannunta wanda a nan take ya kara tsawo ya kamo
maryam dake shirin guduwa. Koda ji an sakalota sai ta fara kokarin kwacewa tana fadar "Shine
ya kashe yaya sadiq dan allah karku bari ya kashe ni, macuci ne".
Aljanar tace kwantar da hankalinki kawata ba abunda zai miki tsaya baya na. Mukhtar yayi
matukar girgiza da ganin maryam wanda shi a tunaninsa saida ya kasheta tukun ya Jefata
ruwa. "Wannan itace yarinyar da Mukhtar ya kashe yayan ta kuma yayi yunkurin kashe ta itama
amma allah baiyi ba. Ta kubuta da rayuwarta daga mutuwa wanda ta fada wata rayuwar kuma
wacce gwarama mutuwar da ita. Wannan yarinyar da kake gani fadamar nan ta koma mata
gida duk sanyi duk zafi a nan take da safe take shigowa gari ta nemi abincin da zataci da
dadare kuma ta koma fadama. Kwana uku baya nazo wucewa na ganta ana mata tamkar
yanda kamin wato taje neman taimako ya bata abinda zataci ya kore ta. Ta koma gefe zauna
tana kuka saboda tsabar yunwar da take ji dan duk ranar bata sa komai a bakinta ba. Koda
naga haka sai na rikida zuwa tsohuwa na kai mata abinci bayan taci ne nake tambayarta ina
iyayenta nan ne ta bani labarin duk abunda ya faru. Kaji irin tsadar rayuwar da ka jefata kai
kuwa ka shiga farinciki. Mukhtar hukuncin da na yanke biyu ne ciki ka zabi
daya....………………………
Aikin ki na kyau aljanar fatima.
Mujee zuwa.
Autan writers nee king boy
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 9-10
NA. KING BOY ISAH
✍ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍
_Wannan pagen duk girmansa na masoya king ne a duk inda kuke._
*Kowa ni yake jira to gani na iso, Samari yan mata na nesa ku marmatso. Domin kar ayi
babu ku haka sam! Sam! Bani so. Wannan pagen ku ne karku bari ya wuce wanda aka baya
nan bai more kallo ba*
wayyo my fans you will kille me with you love. Ina sanku ina alfahari daku *ANA TARE*
supports
FOLLOWING US AS:
----
Like us page.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
----
Check us blogger.
Zamaniwriters.blogspot.com
----
Email us your comment and reports.
Zamaniwritersassociation@gmail.com
----
whatsapp's number
08096831009
----
*KARSHEN PAGEN BAYA*
Kaji irin tsadar rayuwar da ka jefata kai kuwa ka shiga farinciki. Mukhtar hukuncin da na yanke
biyu ne ciki ka zabi daya.» Mukhtar ko dai ka mayarwa da yarinyar nan dokiyar ta ta hanyar
bata duk wani abu da ka mallaka ta sanadiyar dukiyar su, ko kuwa ka zame mata ahali kamar
yanda ka rabata da yayanta a baya, Dole ka bata kulawa kamar wacce zaka bawa diyarka ko
kuma ma tafi haka. Domin da bazarta kake rawa.
Malam ya kalli aljanar yace "lalai wannan hukunci yayi duk mai adalci haka zai yi, saboda haka
ni na aminta Mukhtar sai ka zaba daya kodai ka tatara duk abunda ka mallaka hatta gidan nan
dan da a gidan haya kake ka mayar mata ko kuwa ka rikr ta zabi ya rage ga mai shiga rijiya ko
ya shiga ta kai ko ya shiga ta kafa. Mukhtar yace na aminta da zabi na biyun zan riketa amana
isha'allah domin ni yanzu NAYI NADAMA sannan zan ci gaba da rokon allah ya yafe min
laifukan da nayi, Kuma na gode wa wannan aljana da ta tsamo ni daga cikin halaka. Maryam zo
mana daga yau kin zama 'yata". Ya mika mata hannu da farko taki amincewa saida aljanar
tasaka baki tukun.
Ummiey farin ciki tuni ya mamaye ta jin ta sama 'ya a bagas! Ta sama mai maye mata gurbin
yarta hawwer da ta mutu. Aljanar ce ta wani tashi saman iska gaba daya iskan wajen ya hau
zagaya ta ita kuwa ta fara wata kalar shu'umar dariya marar dadin saurare, Magana ta fara yi
muryar na fitowa uku-uku bazaka iya banbance namiji ne ke maganar ba ko mace ko kuwa
yarinya. "Nice nan aljana SUFURATU marainiyar aljana, Sai na cika burina na ganin ba maraya
da zai kasance a cikin kunci. Aikin ma yanzu na fara. Sannan Mukhtar ina gargadin ka a kan
maryam kuma ka zama mai adalci domin zan dinga bibiyar rayuwar ku".
Sama tayi kamar wacce ake ja tana tafe tana gagaba dariya, su kuwa da gaba daya in aka fitar
da malam ba wanda bai tsorata ba, domin ummiey har dan fitsari ne ya fara kubice mata. Tun
suna ganinta har ta bace cikin gajimare. Malam ya kara yiwa Mukhtar nasiha sannan ya bashi
addu'o'i wanda zai tuba ga allah ya kara da cewa ya yawaita sadaka, tukun ya musu bankwana
ya koma. Su Mukhtar sunga abun mamaki yau kam duk cikin su ba wanda tsoro ya sake shi,
nan fa aka shiga tarairaya da tattalin maryam dan gani suke kamar itace ma aljanar.
Acan gidan kamala kuwa da asuba da suka farka sama ko kasa suka nema yarinya suka rasa
sun shiga rudu da tashin hankali don har ga Allah yarinyar ta shiga ransu fiye da zato, a cikin
su ba wanda baiyi mafarkinta ba. Khadija ta zauna tayi zugum ba abunda take sai faman kuka
tana tuna yarinyar nan da irin shakuwar da ta shiga tsakanin su tun a jiya. Yau komi bata iya ci
ba har wajen karfe 9:00 ta zauna ne kawai ta zurawa kofa ido a zatanta zataga ta shigo. Kamal
da yaga abun yayi yawa yayi lalashin amma kamar kara haukatata ne yake. "Khadija tunda kinki
hakura tashi muje nemanta". Firgigit ta tashi da gudu ta shiga ta dauko hijab. Sun taho sai sauri
take tana leke-leke wani wajen ma har gidaje take tatan bayawa. Amma har wajen 11 babu
labari. Duk sun gaji sunyi tikilis. Sufuratu tazo wucewa ta hange su a karkashin wata inuwar
mangwaro da sauri ta sauko kasa tazo daidai inda suke, ita har tama manta da su, "Allah sarki
da gani nemana kuke na gode da halacin da kuka min bazan taba mantawa da ku ba. Badan
aikin dake gaban Sufuratu nada yawa ba da ba makawa DAKE ZAN ZAUNA".duk abunda take
fada baji ba suke kuma basa ganinnta. Kwasar su tayi ciki abun da baifi seconds 5 ba ta kaisu
gida. Mamaki iya mamaki sunyi shi ya akayi hakan ta faru mu da muke tsaye a gindin bishiya
kuma gamu a gida. Tambayar dake dauke a bakin ko wannan su kenan.
"Na tafi sai mun sake haduwa" gaba daya sunji an fadi wannan saidai basu san taka mai-mai ta
inda muryan ta fito ba. Nan fa suka shiga dube-dube. Aljana Sufuratu kenan yarinya ce a cikin
aljanun ma domin da kadan zata haura shekara 150 musulmar aljanace labarin ta nada dan
tsayi da abunda yasa ta fara taimakon marayu. Kasan cewar itama yarinya ce yasa tafi shiga
rayuwar yara marayu, dan a ganinta sunfi ban tausayi. Indai taga yarinya cikin wahala saita
bibiya rayuwarta ta kuma san labarinta. A yanzu haka ta bar garin abuja ta nufi bauchi.
Inda ta sauka a G.R.A anguwar masu kudi ce, kowa harkar gabansa yake yi tankama-tankaman
gidaje ne tsabar rana da akeyi yasa kowa yana cikin gidansa. A farkon anguwar Safuratu tayi
gamo da abunda ya bata mamaki wata yar digil gilar yarinya ce karama wace in tayi gudu takai
10 years ko 9 da rabi. Sanye take da kaya atamfa dinkin riga da sket sun mata kyau sosai da
gani kasan ba yar talaka bace. Kanta wani dan bokitin ruwa ne wanda da gani kasan yafi
karfinta jan haline kawai yasa take dauke da shi sai jibi take da alamun gajiya a tare da ita daga
nesa ta debo shi. Ba wani abu yabawa Safuratu mamaki ba sai ganin gari da wuta kuma zaiyi
wuya a sama gidan da ba tanki a anguwar. Hakan yasa tace a ranta bari ta bita sai taga wace
marar mutun cin uwace wannan, da take neman hallaka diyarta.
kofar wani gida ta kalla nan take ta saki murmushi, da kyar ta samu ta sauke ruwan ta ruga da
gudu kofar gidan nan wata yar baby ce (Diyar roba ta dauka) nan fa ta sama waje ta zauna ta
fara wasa da ita ta bar ruwan da ta dauko din kan titi, dake motoci basa wucewa. "Kutumelesi
lalai fatima yau kuwa zaki daku wato har kin sama damar taba yar babyn nuratu ko". Kafin ta
juyo tuni yarinyar dake maganar ta warce yar babyn hade da kifa mata mari wanda saida ta
gigice. Kuka ta farayi Wiiii!-Wiii ta juye ta kalli wacce ta mare ta din tace "Wllh sai na gayawa
mama asiya". "Jeki ki fada din kiyi sauri kar kuda ya riga ki". Cewar mai marin,
Fatimar bata kara cewa komai faman kuka da take ga hawaye ga jibi abun yayi mata biyu.
Zuwa tayi taje ta fara kikiniyar dora bokiti a kai,Da kadan ta fadi ita da ruwan badan Safuratu
tayi sauri ta tallafa mata ba. Dungwai-Dungwai ta hau titi ta tafi tana kugin kuka. a bakin wani
makeken gida ta tsaya tana kwalla kira "Me gadi bude-me gadi". Aljana safuratu dake binta a
baya ta tsaya ta kare wa gidan kallo tas! Taga a duk anguwar gida daya ne za'ace sunzo daya
da wannan gidan ta girman shi da kyawan shi, da gani kasan an kashe nera, "To ke kuwa me
zakiyi a nan gidan ko wata sabuwar tsokanar ce domin bana tunanin yar nan gidan ce ke".
Safuratu ke magana ita kadai. Mai gadi ne ya taso da sauri yana masifa "Ke ki tsaya inzo in
bude mana kin ishi mutane da kira". Bayan ya bude ya gallah mata harara wa kuma ya tabaki
kika zo kina bude mana baki?". "Zulaihat ce ta mare ni". Ta fada lokacin da ta wuce ciki, "Dan
an dan mare ki shine zaki ishe mu da kuka kuma, yarinyar nan dai anyi ja'ira".
Tun a kofar falo ta fara kira "Aunty ameera-aunty ameera". Da sauri ta fito tana mata masifa to
jarababa kin dawo wato har kinzo kin fara takurawa mutane". Ameerar ke fada haka lokacin da
ta sauke mata ruwan tana juyewa. Hanyar daki ta nufa da sauri ta kamota, ubanki nace Fatima
dan iskanci ina zaki?. Ko kina nufin wannan ruwan ne zai ishe ni wanki?". "Aunty zuwa zanyi in
gayawa mama asiya Zulaihat ta mare ni". Ta fada tana shashekar kuka "Muna fuka ai ba'a
banxa zata mare ki ba da abunda kika mata, oya ni wuce