Showing 72001 words to 75000 words out of 103342 words

Chapter 25 - ALJANAR FATIMA Complete Hausa Novel

King Boy   

13 Jul 2025

7837

bani in yaso karka bada kudin Abin
karyawa din ma". Duk masifar da take yi Mukhtar yayi shiru bai ce kala ba. Sai yanzu ne ya
dago cikin sanyin murya yace "Haba Murja ni fa mijin ki ne ko kin manta ni shugaba ne a gare ki
kike daga mun murya haka. Wallahi kiji tsoran Allah Murja". Ya nuna ta da yatsa. Makr yatsar
tayi da hannu ta rike baki "Iyeeeh daga bani kudina sai wa'azi?. To Allahu akbar amma fa in
kana so wa'azin da kake ya dinga shiga kunnena to a bani kudina". Mukhtar tsabar jin haushi
kamar wanda zaiyi kuka yace "Murja ni kike bigewa hannu?". A hatsale tace "Au! Tambaya
kake kenan, Baka ma yarda da hakan ya faru ba kenan". Bai bata amsa ba ya tashi da niyar
ya fita waje. Ya fara tafiya kenan ta shaki wuyanshi ta baya ta wani jayoshi. "Malam ba inda
zaka, Wallahi sai ka biyani kudina". Nan fa Umar ya saki baki yana kallan Muktar a zuciya yana
jin haushi abunda ya sashi yayi wa Rafy. Mukhtar da aka shake ma wuya ta baya. Dakyar ya

samu ya markayi hannunsa baya ya kwace cikin fushi yace "Cewa nayi bazan baki kudin ki
bane?. Inace dai sai naje na samo tukun zan baki?"._





_Murja tace "Kaga malam ni yanzu nake san kudina domin kaji wani yaro can ma yana a bashi
mai. Amma babu duk ka cinye min kudi a bashi. Yanzu fa dubu biyar nake binka". Muktar yace
"Naji yanzu sakar min riga Yau yau zan biya ki kudin ki in dai huta da jaraba da masifa". Zazaro
ido tayi Cikin daga murya tace "Ni kaks cewa masifafiya?. Ni kake cewa jarababiya ko
Mukhtar?". "Ni fa ba dake nake ba". Sakar mishi riga tayi hade da cewa. "Jeka ga hanya nan.
Kuma Wallahi tallahi yau in baka kawo min kudina ba zaka ga jaraba da masifa da kake fa.
Badai ni kake cewa masifafiya ba. Hmm". Mukhtar bai sake magana ba waje kawo yayo.
Zuciyar sa sai kuna take._





_Yana fitowa su Safuratu suma suka biyo shi baya. Umar ya girgiza kai yace "Kai amma
gaskiya ba karamin rashin hankali nayi ba. Wai ashe haka matar Mukhtar take mishi amma
shine har da bani shawara wai kar matata ta rainani. To dan Allah wane raini yafi wannan?. Kai
gaskiyar masu iy magana da sukace (RASHIN SANI *YAFI DARE DUHU*). Wallahi zanso inga
ya zasu karata in bai biya ta kudinta ba". Safuratu tace "ka dai gani da idanka. Idan kana so
kuma ni zan iya hana shi kawo kudin". Uamr yace "Tayaya zaki hanashi". Gaba ta shiga ta
fara tafiya. "Muje kaga ta yanda zan hanashi ya kawo kudin". Baya suka bi Umar har wajen
ogan su inda yake karbo napepk din. Nan fa Safuratu ta juya zuwa wata jabebiyar mata. Ta
shiga yar kurkurar ta zauna gaba daya ta cika kurkurar in aka cire inda umar zai zauna baza'a
samu wajen zaman wani ba. tace wa Umar ya shigo. Baiyi gardama ba ya shiga. "To kaga
yau a nan zamu ta yawo ba wanda zaima tsayar da shi in yaga mutane a ciki". Umar ya girgiza
kai shi dan a tsorace yake. Dan girman matar yayi over. Mukhtar zuwa yayi ya dan kakabe kurar
yar kurkurar ya hau ba tare da yasan Su Umar na ciki ba. Haka yata zuba gudu yana bi lungu
da sako ko mace daya bata tsayar da shi ba. Tun abun bai damunsa har ya fara damunshi.
Domin yaga abun ba kamar yanda ya saba ba._






_Haka ya ringa wuce mutane wanda kuma ya tabbata Napepk suke jira amma da sun ganshin
suka hangi Safuratu sai suki tsaida shi. Abun har ta fara bashi haushi ya fara zage-zage. Wasu

yan mata ya hanga su biyu sun ci kwaliyya abun su sai kallan hagun da dama na titi suke.
Alamu sun nuna cewa abun hawa suke jira. Muktar ya kalle su yace. "Matsala ta da mutane
kenan wasu yan rainin wayo ne Wallahi. Yanzu wadancan fa da gani Napepk suke jira amma
ina zuwa sai kaga sun ki tsayar dani. Amma bari mu gani". Ta gaban su yaje ya wuce ganin
wannan katuwar mata yasa basu tsayar da shi ba. Muktar har yayi gaba kuma cike da takaici
yayo baya. Diiiiiit! Ya musu hon hade da cewa "Tafiya ne?". Dayar tace "Eh tafiya ne ya
akayi?". Yace ok to ku shiga mujr mana ina za'a kai ku?". Yar siririyar cike da masifa tace
"Malam bamasan rainin wayo ya Napepk dinka cike kuma zaka zo kana cewa wai mu hau. To
nan ina xamu hau?. Ko kan wanna tikekiyar matar mai kama da giwa zamu hau?". Tana fadar
haka suka kwashe da dariya ita da kawqr ta. Safuratu kuwa dajin abunda suka fada sai ya bata
mata rai. Kanta ya juye ya koma na giwa. Yan matan nan na ganin kan mata ya koma giwa. Yar
karamar ta banke Mai dan jikin ta fadi itana ta wuntsila tsukakun kayan jikin su Bai hana su
zabgawa a guje ba. Dan ko tsayawa tata re sket ba wucce tayi. Takalman su kuwa tuni
kowacce a ciki ta yi wulli da nata dan tafiya da su bata lokaci ne. Wani gida suka shige a million
suka fada daki. Matar gidan na gani haka ta bisu daki itama a guje ta turo kyaure._



_Mukhtar sakin baki yayi yana kallansu. "To su kuma wannan me suke nufi?. Ko dai maciji suka
gani a ciki". Juyawa yayi baya ya leka har karkashin kujerar baiga ko kiyashi ba. Bai aminta
ba. Ya fito sai da ya zagaye Napepk din ya duduba baiga ko mai ba. Yaja tsaki ya hau Napepk
dinshi yayi gaba............................. ... .........._


���
TASHIN HANKALI
���


Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee king boy





��

*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*

��

Page 81-82


© *KING BOY ISAH* ✍


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍ *®Z.W.A*



​GIDAN MARAYU​


_Story&written by✍
​​Beauty Queen​​

​ZAMANI WRITERS ASSOCIATION

*INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIN RAJUN*

KULLUNAFSIN ZA'IKATUL MAUT.
*UMMU RUMMA,* WACCE KUKA FI SANI DA *BEAUTY QUEEN* ALLAH YAYI WA YAYANTA
MAI SUNA *ABDURRAHMAN* RASUWA. MUNA ROKON ADDU'A DAGA GARE KU ALLAH
YA JIKAN SHI YA MAI RAHAMA. ALLAH YASA ALJANNA CE MAKOMARSA AMIN. SU KUMA
ALLAH YA BASU HAKURI DA JURIYAR RASHIN SHI.

*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Juyawa yayi baya ya leka har karkashin kujerar baiga ko kiyashi ba. Bai aminta ba. Ya fito sai
da ya zagaye Napepk din ya duduba baiga ko mai ba. Yaja tsaki ya hau Napepk dinshi yayi
gaba.~

_*H*aka yaci gaba da zaga gari amma shiru. Wata mata ce ta tsayar da shi har ya tsaya kuma
sai taga su Safuratu tace, "Sannu ko baiwar Allah ai ban ganku ba". Safuratu tace "yauwa
sannun ki dai". Mukhtar yace "Yauwa hajiya shiga muje ina za'a kaiki?". Matar a fadace tace
"Kan cinyar ka kake so na hau ko ina?. Amma kai dan rainin wayo ne ma wallahi kasan napepk

dinka ta cika shine ma har ka tsaya". Muktar juyawa yayi set din baya shi dai ko kwaro bai
gani ba. "Kinga malama ba rainin hankali nace kiyi min ba. Kinga mutum ne a ciki da zakice wai
a ciki take. Kinga dallah malama ware kama gabanki tunda ba hawa zakiyi ba". Jan Napepk
dinshi yayi cike da haushi. Can wani tunanin ya fado mai. Wanda yasa ya juya kan napepk din
ya nufi gida. Da isar sa ya sauka ya shiga ciki. Su Umar suka saukko suka bishi. Murja na
ganin shi ta haushi da masifa wai ya cika lalaci tun yanzu har ya dawo. Nan yace ta saurare shi
dakyar ya samu ta dakata da masifar. Nan ya fada mata cewa tunda ya fita gashi har larfe sha
biyu ta kusa amma ko mutum daya baiyi ba. Nan fa ta sake rikicewa wai wannan karyar banza
ce yake fada. Ai ba yanda za'ayi yace wai har yanzu bai kama ko biyar ba. Tace "Wannan ai
salon munafirci ne. Wato so dai kake ka hanani kudina to wallahi baka isa ba. Tashi ka koma"._




_Mukhtar yayi ajiyar zuciya yace, "Ni fa kinji matsala ta dake kenan. Ke gaba daya baki sasauta
mun, Ji yanda kike masifa dan Allah kamar ba da mijin ki kike magana ba. To ni dama ba wani
abu ya kawo ni ba. Kamar yanda naji ance idan mutum basuyi rabuwar arziki da matar shi ba
idan ya fita kasuwa bata mishi dadi. Shiyasa na dawo domin mu fahimci juna amma kin wani
hau masifa". Murja na jijiga kamar wacce aka kunna tace."To wace irin fahimta kuma?. Ai ni in
ba kudina ka kawo min ba ba wani zancen fahimta dan ma kaji. Ni in ba Dumus! Naji ba da
matsala". Takaici ne ya cika Mukhtar yayi waje ba tare da yace mata uffan! Ba. napepk ya
dawo ya shiga yana surutai. "Wai matan yanzu me yasa basu da lura ne. Haba mutum yaje
yata fama wani idan yaje neman abincin ma har duka yake shi, Amma daga karshe in ka dawo
gidan baza'a kwantar ma da hankali ba. Ji wannan matar wai na dawo mata da laluma amma ta
wani dau zafi. Da ace zan samu mata kamar Rafy matar Umar ai Wallahi da yau-yau zan bata
takarda". Baki Umar ya rike jin abunda Mukhtar din ya fada. Nan take tsanar sa ta karu a
zuciyar sa dan ji yake kamar ya buge sa._





_Mukhtar ya koma ya hau napepk din ya sake dannawa cikin garin. Har wajen karfe daya yana
yawo amma ko an tsayar da shi ma sai ace taje abun duniya ya isheshi nan ya sama wata
inuwa ya faka hade da cewa "Yin barci na ma yafi mini da inta kone maina a banza. Nan ya
fiddo abun sallah ya shimfida ya dan ringesa. Yana ta masifa shi kadai. Bai dade da kwantawar
ba barci yayi gaba da shi. Su Safuratu kuwa suna cikin. Wasu gayu ne guda biyu dagani kasan
yan shaye-shaye ne. Gudaya ya kalle guda yace "Baabah yau fa nake gaya ma dawa tayi
nama. Kalli can". Ya nuna mishi Mukhtar dake kwance yana barci. Dayan yace "Kambuh! Laili
yau Allah ya kai damo ga harawa. Kaga zagaya ta can ka dubo mana key nasan yana jikin shi".
Wanda ake kira da Muhsan yaje jikin Mukhtar ya fara dube-dube ko zaiga makulle. Can ya
hange shi a Karkashin kan Mukhtar a hankali ya zare shi. Ba tare da Mukhtar ya farka ba.
Safuratu tace Umar ya sauka ya jire Mukhtar ita zata bi barayin. Da sauri ya sauka. Su kam

barayin basa ganin su Umar. Yana ciro makullin ya mikawq abokin nasa wanda shi tuni har ya
dare napepk din. Ai kuwa ya tayar yaja ta a guje.
Duk abun da ake Mukhtar ko motsawa baiyi ba. Barci yayi dadi. Da gudun yake jan yar
kur-kurar sai da yayi tafiya mai nisa dan har ya fara fit daga garin tukun ya ratse ya sauka daga
titi yabi wani jan birji nan ma sai da yayi nisa sosai ya kara kutsa ta cikin daji. Sai da ya shiga
cikin wasu bishiyoyi tukun ya tsaya. Kallan juna sukayi kamar hadin baki kuma suka kwashe da
dariya. "Kai baabah lalai yau dawa tayi nama yanzu ya kake gani zamuyi?". Dan siririn ya
tambaya wanda ya jawo kurkurar. "Ai nake gaya ma abun duk bige ne bari zamuyi kawai dare
yayi sai muyi wuf! Mu shiga da ita gari mu shigar da ita". Dan siririn mai suna Rafson yace kai
mutumina nake gaya maka in dai muka shigar da wannan. Kaga na daya Zan sayi kwalin sigari
giya wiwi Kai Wallahi har koken sai na saya". Muhisan yace "kaji banza gara Kai duk a yan
bushe-bushe kawai zaka kare. Ai ni nake gaya ma zuwa zanyi gidan magajiya wuuuuyyif! (Yayi
fito) ta dorani a hanya ka dai gane". Ya daga mishi gira. Safuratu kallansu kawai take suna
hirar rashin hankali. A zuciya tace yanzu su wannan shikenan fa sun bata rayuwar su da
shaye-shaye ga abun har ya kai ga sata. Yanzu haka kuma in ka bincika rashin aikin yi ne ya
jefa su".
Sai wajen karfe uku Mukhtar ya farka. A gigice ya tashi ganin ba kekenapepk
dinsa............................._

*Ayi Hakuri dan tsito ne*

��
Su malam Rafson fa an dauko babban kaya lalai yau dawa tayi nama. Dan kura da kallabin
kitse

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee king boy






��

*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*

��

Page 83-84


© *KING BOY ISAH* ✍


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍ *®Z.W.A*


� DEDICATED TO YOU �


✍ SALMA QUEEN ✍

✍ ZUWAIRA MADARA ✍

✍ ACTION BABY ✍

✍ BEAUTY QUEEN ✍

✍ FATIMA(UMMU BASHIR) ✍

✍ AUNTY MAIMUNA ✍

✍ RABI'AT SHU'AIBU ✍

✍MMN NAJWA✍

☺ NA ROKI ALLAH YA KARA MUKU BASIRA ALLAH YA TSARE MIN KU. ALLAH YA KARA
FIKIRA DA FASAHA☺



*KARSHEN PAGEN BAYA*
~A zuciya tace yanzu su wannan shikenan fa sun bata rayuwar su da shaye-shaye ga abun har
ya kai ga sata. Yanzu haka kuma in ka bincika rashin aikin yi ne ya jefa su". Sai wajen karfe uku
Mukhtar ya farka. A gigice ya tashi ganin ba kekenapepk dinsa.~

_*G*aba daya a gigice ya tashi nan fa ya dora hannu kamar ya fasa ihu! Waige-waige kawai
yake yana rasa abun yi. "Anan fa. A nan nayi parking". Juyawa yayi wajen wani mutum dake

taho wa. A rikice ya taryi gabansa "Malam dan Allah baka ga wanda ya daukar min napep ba?".
"Ban gani ba wallahi". Cewar mutumin da Mukhtar din ya tambaya. Durkushewa Muktar yayi
ya kama kafar mutumin."Dan Allah dan annabi in kaga wanda ya dauka ka taimaka ka gaya min
please wallahi ba tawa bace sojan haya na daukko". Mamaki ne ya kama shi. "Kai bawan Allah
wai napepk waya ce ko wani karamin abu da za'a sata ba tare da ka gani ba?. Abun naka rainin
wayo ne ma". Yana fadar haka ya fizge kafarsa yayi gaba. Mukhtar haka ya ci gaba da taryar
mutane yana tambaya amma kowa cewa yake bai gani ba. Duk abunda yake Umar na kallan
shi. Amma shi baya ganin Umar din. Mukhtar kamar yayi hauka duk mutumin da ya gani yaro ko
babba mace ko namiji sai ya tambaya. Da dai yaga abun bayayi sai kawai ya sama waje ya
dora hannuwa a kai ya fashe da kuka. Cikin kuka yake cewa."Yanzu ya zance wa Bash da
wanne idanu zan kalle shi ince an satace Napep dinshi tama za'ayi ya yarda". Kara fashewa
yayi da kuka. Umar ya tausaya mishi sosai a nan gurin duk da yasa Napep din bazata salwanta
ba. Mukhtar nan ya zauna sai kuka yake yana tunani ya saka wannan ya kunce ya saka
wannan. Har yamma tayi magariba ta kawo kai suna wajen. Can dai Mukhtar ya mike ya nufi
gidan yana tafe yana yan surutai yana zubda hawaye kamar wanda akawa mutuwa. A haka har
ya karasa gida sallama ciki-ciki ba'a ko ji yayi. Murja na daki batama ji sallamar sa ba. Waje ya
samu ya zauna yayi tagumi. Shi kam tunanin ya zaicewa Bash. (Mai napepk) din yake. Nan fa
ya fara zance har yana fitowa. "Yanzu Inje incewa bash duk yau ban yi ko sisi ba kuma ina barci
an sace Napep din. Kash! Sam! Bazai yarda ba wallahi"._






_Murja ce ta fito daga daki tana yan wake-wake, Tana ganin Mukhtar tace. "Au! Malam dan
karka bani kudina shine kazo ka wani zauna a waje?". Karasawa tayi gaban shi tana zuwa ta
wani gyara dan kwali daurin (Ture kaga tsiya) ta rike kugu da hannu daya. Dayan kuwa ta mika
wa Mukhtar hade da kauce kanta ga barin kallansa. Alamar ba mutunci. "Malam bani kudina
bana san wani waye ya mutu waye ya tashi. Dan Wallahi duk wani plant dinka na gama gane
shi". Cike da takaici Mukhtar ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login