Showing 60001 words to 63000 words out of 103342 words
mishi masifa. Shima dake ya iya Mukhtar ya kama mishi suka ta Bala'i da 'yan anguwa. Sarkin
bori da yaji ba haza hayaki na neman illata su da sauri yake cewa "Ku kashe-Ku kashe, Ai ga
Aljanar nan ma har mun sumar da ita, Yanzu karasa ta kawai zamuyi_
_Ruwa aka debo aka kwarayawa kaskunan suka mutu. Safuratu na dakin tana jinsu duk
abunda Suke ta kyale su. Sarkin bori yasa aka fara kida. Nan da nan Suka fara bori Har shi din
sai wani girgiza kai yake, Bori suka cika gidan sunayi. Aljanar ce ta fito yanda taga gaba dayan
su sun haukace kowa da irin haukan da yake, Wasu har tsalle suke su fado kasa. Kawai sai
abun ya bata dariya, ji tayi kawai tana so ta gwada taga shin borin gaskiya ne ko kuwa iskanci
ne. Wasu mata ta kalle su uku sai bori suke A cikin su har da mai kwantawa kasa tana
malolowa.Safuratu ta saura zuwa wani make ken Kadangare irin jankwatakwalan nan. Da
gudun tsiya kadangaren ya nufi matar nan mai birgima a kasa tana bori. Tana kyalla ido ta
ganshi haba wa sai ta saki ihu! Ta tashi a guje Taje tana kokarin Kama katanga ta haura. kamar
ba ita ke bori ba Haka sauran matan ma da ganin kadangaren suka wartsake suka tashi zasu
tsere. Sama ko kasa su kuwa su Sarkin bori basu ko ga kadangaren ba. "Mine ne?-mine ne?".
Sarkin Bori ya ke tambayar Ruzaina wacce ta nufi katanga tana kokarin haurawa. Juyowa tayi
tana dube-duben ba ko alamar Bori a tare da ita. "Kadangare na gani ya nufo ni". Cikin masifa
sarkin bori yace "Kadangaren banza kadangaren Wohi!. Ai yanzu gashi kin bata mana aiki. Ga
Aljanar har ta fara kuka, tana Bani hakuri tana cewa in kyale ta in mata Rai. Aiki yayi nisa
Amma kin dawo damu baya". "Ayi hakuri sarkin sarakunan 'yan bori, Kadangaren ne ya tsorata
ni". Dakuwa ya mata "Kinci ubanki ke da kadangaren. Yo ni ba kadangare ba ko zaki na gani
ina bori ai bazan ma kula da shi ba". Yana fadar haka yayi tsaki ya juya yace aci gaba da kidi.
Nan fa suka dora daga inda suka tsaya._
_Aljanar ta ji maganar da Sarkin bori yayi, Ai kuwa tace bari mu gani sarkin bori yana tsakar
haukansa ta bori yayi tsalle ya fado kasa dabar! kenan yaji maciji a wuyansa kamar an cillo shi.
Ihu! Ya fara yi yana kokarin kankare macijin a wuyansa. Da sauri macijin ya nanade sa cikin
hanzari. Yaransa masu bori tsayawa sukayi yana kallansa kawai domin su basa ganin macijin.
Haka Su Umar sun kwalalo mishi idanu. Macijin Ta gabanshi ya zagayo ya fasa kai dai-dai
fuskar Sarkin borin. Shaaaaaa! Kake ji Sarkin bori ya saki fitsari. "Dan Allah kayi hakuri karka
sare ni Wallahi na daina". Waaaaa! waaaaaa! Ihu! Sarkin bori yaci gaba da yi. Sulalewa macijin
yayi ya sauka ya nufi wani waje. Sarkin bori yayi ajiyar zuciya Hade da cewa "Wash!!" Sai yanzu
ma ya lurada idanuwan da aka zubo mishi kowa bakin sa da Alama dauke yake da tambaya.
Wani ne daga cikin masu kidan ya nufi gurin sarkin bori yana tambaya lafiya?. Sarkin bori da jin
haka sai abun ya bashi mamaki wannan ya tabbatar mishi da cewa basu ma ga Macijin ba.
Hakan tasa ya tashi ya takarkare ya bushe da Dariya.tukun yace "Yau naga sakarkari Wai dama
duk borin da kuke baku taba ganin nayi kalar wannan ba?". Kamar hadin baki sukace "Ina fa
muka taba gani sarki". Dan murmushi yayi tukun yace "Karku damu zan koya muku. Yanzu aci
gaba da gashi, Aljanar nan karshen ta ya zo, Yanzun nan ta tashi ta gudu daki. Dan haka yanzu
zan bita inci ubanta" Su Umar ya kalla tukun yace, "Kashe ta kuke so ayi ko korar ta?"._
_Da sauri Umar yace, "Haba a kashe 'yar banza kawai, Me ake da wannan shedaniyar Aljana".
Sarkin bori yace, "Ok ku saka kubobin ku rufe gidan dan ma kar ta sama wajen guduwa in na
furtumo ta daga daki". Shiri ya shiga yi ya dauki karin layoyi ya nufi dakin. A hankali ya dan
daga labulen ya leka. Da lekawa kuwa akayi charaf! Da kan aka rike. Nan fa ya fara kokarin
kwato kanshi, Da ake faman janshi cikin dakin. Hannu yasa a kufar dakin yana cicije wa amma
ina. Sai da aka ja shi cikin dakin da karfi._
_Kii! Ake janshi kasa ana zagaye tsakar dakin da shi. Tun yana shiru har ya fara Ihu! Domin da
gudu ake janshi bayanshi na gurzuwa a kasa. Har yanzu baiga mai jan nashi ba. Ji yayi an
kama kafarshi daya anyi sama da ita kamar wani dan akuyan da ake Fida. Kanshi na kasa yana
reto,Wata irin Dariya ce marar dadin ji ta kaurade dakin, Magana akayi wacce bazaka ce gata
bangaren da ta fito ba a dakin, Cikin wata Siririyar murya "Wai kai sarkin bori ko". "Kwarai ni ne
sarkin bori". Ya fada yana cicira ido duk a tsorace yake. Saukar Tagwayen marika yaje a fuskar
Tas! Tas!. Maganar sake ji "Kai ne sarkin bori ko". Da sauri yace, "A'a Wallahi bani bane, Ni
sunana Duna". Wani Saukar marin yaje, Abunda ya sashi saurin cewa. "Wallahi sunana na
gaskiya mamuda". Cikin Tsoro da tashin hankali yake maganar. Hhhhhhhhhh! "Makaryacin
banza makaryacin Woofi! Wai kai sarkin bori kazo ka fidda Aljana ko kama kashe ta kace ko?".
"Aa Yaseen kawai ina fadar haka ne amma a zuciya ta nufina in na ganki in miki Nasiha ince ki
fita ki bar musu gidan su". Cikin Tsawa yaji Ance Rufe min baki, Dan iskan Karya kawai, Ai
naga duk abunda kake da idanuna. wai ni in tambaye kama Me yasa ka farq bori har kazo ka
zama sarki". "Wallahi tallahi Sharrin shedan ne". Kayau! Aka sake wanke shi da mari.
"Munafuki, Ai kai ne shedan yanzu kuma tunada ka tara yaran mutane maza da mata, Kana
koya musu wani haukan banza wai bori.Yanzu abunda nake sanka da shi, Shine ka biya su
Umar kudin su sannan kuma daga yau ka ajiye bori haka suma yaranka, In kuwa bakayi haka
ba to fa ba kai bs zaman lafiya"._
_"Zanyi kamar yanda kika ce kuma nayi miki alkawari na dai na bori sai dai ma in ringa wa
masu bori Wa'azi su bar bori". Dim! Aka saki kafarsa ya fado kasa, Da ganin haka ya tashi ya
fita a guje. Har yanzu yaranshi kidan bori kawai suke ba abunda yasha musu kai. Dakatar da su
yayi yaje ya bawa su Umar kudin su yace musu Ai yama kashe Aljanar amma kyauta yayi baya
san kudin. Lafiyayun mari aka mar har biyu. "Kan uba! Wannan shine SAKAMAKON ALHERIN?
naga dai ni kyauta nayi muku Amma shine zaku mare ni?" Sukam tsayawa kawai sukayi suna
kallansa. A bayan Umar wata mumunar Aljanar marar kyan fasali mai shegen abun tsoro ta
bayyana, Sarkin bori take harara da wasu manya-manyan idanunta, Karkarwa ya hau yi Jiki na
bari ya juya. "Daga yau ina so in gaya muku cewa na daina bori Ba ruwana da maiyin bori.
Sannan kuma kudin ma ina so in kara tunatar muka da cewa wannan ba hanya mai bullewa
bace, Ku tuba ku dai na bori kuma daga yau kamar yanda nayi". Nan sarkin bori ya fara cire
kayan borin layoyi da guruka. "Shirman banza shirman wofi! Wannan ai maganar banza ce, To
in mun bar bori wacce uwar zamuyi. Kaga in bazaka iya ba kawai ka sanfe ni fa dama na dade
ina mafarkin hawa karagar nan taka ta sarkin bori Sai yau ga... Marin da aka dauke shi da shine
ya dakatar da shi. Juye-juye y fara yi "Cikin ku uban waye ya mare ni?". Gaba daya suka ce
basu bane. "Au! Dan nace bazan dai na bori ba shine k turo Aljana ya mare ni. To bazan dai
naba din kuma bori yanzu ma na fara". Ya juya ga sauran Yan uwansa yace "duk wanda yake
tare dani ya daga hannu", Kafin kace me gaba daya suka dadaga hannunwa. Da faruwar haka
sai ji kake Fass! Fass! Dum! Dum! Mari da kulli ta ko'ina kai musu ake ba tare da sunga mai
dukan nasu ba..............._
MURA
*KWANA BIYUN NAN SAI KUYI SORRY. ABUBUWA BIYUN SUN HADE GA DAUREN AURE
GOBE. GA WATA MURA SABON KAMU. IN GAYA MUKU WANNAN PAGEN TUN JIYA NAKE
RUBUTA SHI. WANI ABUN MAMAKI DAGA NA FARA RUBUTU SAI BARCI YA KWASHE
NI.HHH YASEEN KUSAN SAU UKU ANA HAKA. TO DAI IN KUNJI NI SHIRU KU MIN UZURI.
DAN YANZU HAKA MURA TAUNANA TAKE.'YAN ZUWA DUBIYA KAR A MANTA DAI DA KAN
RAGO. LOLZ*
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 71-72
© *KING BOY ISAH* ✍
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍ *®Z.W.A*
KING BOY NAYI KUKAN RABUWAR MU DAKE NI FA BAN SO BA. RAI NA YANA
RADADI NI DAKE GASHI ZAMUYI BANKWANA SAI WATA RAN!
DEDICATED TO YOU AMÆL NA GODE DA ADDUO'IN KI GARE NI ZAN IYA CEWA
KINFI KOWA KAGUWA AKAN LITTAFIN NAN. AU! ASHE FA NAKIN NA SANI BANSAN NA
WASU BA. ♂ JAMA'A NA GODE DA ADDUO'I BAZAKU LISSAFU BA DANA LISSAFA.
ANA MUGUN TARE
NA GODE AL'UMA NA GODE. NA KARA MUKU GODIYA MATAN KU DA MAZAN KU.
KING BOY ISAH, GANI INAI MAKU BAITIN GODE WA, KU FADA NA GODE.
BAN RAINA ADDU'A DA KUKAI TA YI MINI BA
MUN GODE 'YAN UWA
NAI KUKA HAR NA ZUBDA 'YAR KWALLA.
MUN GODEEE
NAGA YANDA MASOYA SUN KA MIN JAJE
MUN GODE 'YAN UWA
CUTA BA MUTUWA BA HAKAN NA FADA
MUN GODEE
DUBI YANDA NA KOMA DUK NA RARAME ...
NA GODE KU FADA.
MUN GODE 'YAN UWA
ALHMDULILAHI ALAH KULLI HALIN. ♂
*HAUSAWA CUNCE CIWO BA MUTUWA BA. NA DAWO YAU DAGA JINYAR 'YAN KWANAKI
WACCE NAYI. ALLAH YA BANI LAFIYA, SAI DAN ABUNDA BARA A RASA BA. NA GODE DA
ADDUO'IN KU A GARE NI. ALLAH YA SAKA MUKU DA ALKHAIRI. NASAN KUNYI MISSING
NAWA KAMAR YANDA NIMA NAYI NAKU.* NA DAWO GARE KU ABOKAI. ACI GABA DA
GASHI, AMMA FA BA *ALJANAR FATIMA* CE BA TA SHAKE NI. INA KAUNAR KU
MASOYA NA.
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Kafin kace me gaba daya suka dadaga hannunwa. Da faruwar haka sai ji kake Fass! Fass!
Dum! Dum! Mari da kulli ta ko'ina kai musu ake ba tare da sunga mai dukan nasu ba.~
_*N* an fa kowa ya fara neman wajen tsira, Wasu suka nufi kofa wasu kuma katangu suke
kamawa da nufin su tsallaka gidan makwabta. Sai dai duk wanda ya nufi kofa kafin ya karasa
gurin sai yaji an turo shi da karfi sosai. Wanda kuma suke kokarin hawa katanga sai sun kama
kawai suji an jawo kafar mutum yayo kasa. Umar Muktar da sarkin bori su kadai ne ba'a maka.
Suma kuwa sun sama wajen sunyi tsugunnin biri Najin sanyi. "Kaiiii! Kowa ya dakata a inda
yake ya kuma saurare ni" Cikin wata muguwar tsawa mai kamada maganar basamude suka ji
anyi maganar. Tsi! Kowa ya tsaya inda yake suka hau waige-waige matan kuwa tuni har sun
fara kuka suna dora hannun a ka!. "Nasan zuwa yanzu kunnuwan ku ba abunda suke bukata
sai sanin waye mai magana sannan gangunan jikin ku ya zuwq yanzu sun mika wuya neman
ceto kawai suke daga duka da mari. Ba wani bane mai dukan ku kuma ba wani bane mai
magana. Sai Aljanar da kuka zo gidan nan domin ku kore ta ko ku kashe ta. To in kun shirya
bari in bayyana ku kashe ni". Haba wa da fadar haka suka fara zubewa kasa ba abunda kake ji
sai bada hakuri magiya da Neman afuwa. "Munahikan banza wato kunsan bazaku iya ba kuma
kuka tarka?, Ai ni a zato na_
_Gaskiya dokin karfe ce Ko ku dubu kuka hau bazai karye ba. Ba’kon munafuki ba na mutum
‘daya ba ne". Dan haka daga yau ina umartar ku gaba daya da ku daina bori in kuwa Bah...".
Da sauri suka fara "Wallahi mun daina daga yau, Dama duk abun karya ne". Hahahhahahaha
ta saki wata uwar dariya. Kofar gidan suka ta bude da kanta. "Na bude muku gidan, Kuzo ku
wuce kuma daga nan idan kuka fara gudu bana so ku tsaya a ko'ina sai a garin ku. Ko hutawa
ban yarda kuyi ba. Sannan zan dinga bin didigen ku. Duk wanda ya yarda ya koma borin karyar
nan to fa kwanan sa ya kare". Hhhhhahaha Tayi dariya, A guje suka ringa fita gaba daya har su
umar din. Sarkin bori a gaba sai tika uban gudu yake, Bayan shi kuma jama'ar sa ne. Su Umar
kama tuni sun sabe. Matai makin sarkin borin ne ya tsaya. "Kai ku dakata Ni fa yaseen bazan
iya tafiyar nan a guje ba. Haba kawai asaka mutane gudu kamar wanda 'yan BH suka tasi
gaba. Kunga kawai mu tafi a hankali abun mu, Kai idan muka sama mota ni da kai ma ma zan
biya mana kudi mu hau". Da gama fadar haka suka hau shewa suna fadin "Sai oga". Alamun
dai maganar tashi tayi musu dadi. A hankali suka tafi suna hira abunsu. Shi kuwa sarkin bori
tuni yayi nisa sai gudu yake. Kamar ance wa daya daga cikin su ya waiga baya. Haba yana
juwa kuwa ya hangi wasu bak'ak'en karnuka wanda yawan su sunkai ashirin. Ko wanne sai
fiddo harshe yake gasu da masifar gudu. Ai bai ko tsaya gaya ma su oga ba, A million ya
zabga a guje ya wuce su. Da ganin haka sai sauran suka juyo. Lokacin kuwa karnukan sun
kusa karasowa. Duk wanda ya juya yaga karnukan nan sai ya ari ya kare. Kafin dan wani
lokacin sai gasu sun isko sarkin bori a hanya. Karnuka na biye da su baya. Ko da sarkin bori ya
juya shima yaga mugun abun da ke biye da Jama'ar tasa. Haba shima sai giya ta tsinke. Gudu
kamar wanda yaci kafar barewa._
_____________________
_Mama Asiya sarfa da marwa take kawai a falo tana jijiga diyar roba tana fadin, "Yi shiru-Yi
shiru". Su Zuwaira suka bushe da Dariya harda dage kafa. Hauwa bayan ta dan tsagaita da
dariyar tace "Aunty Ladiya kuwa ?". Harara ta watso mata ba tare da Tayi musu magana ba.
Zuwaira tace "Allah ina tunanin ba lafiya, Baki ga wai 'yar babyn Fatima bace a bayan nata".
"Humm Na gani mana yau kam, Ina ga wata sabuwar kauna ce ta kullu tsakanin Fatima da
Aunty Asiya". Nan ma harare ta wullo musu. Daga bayan ta taji 'yar tsanar tace "Yunwa nake ji
zansha madara". "To, To". Mama Asiya ta fada lokacin ta nufi dakinta da sauri. Wata sauran
madara da tasha jiya ta daukko ta sauke 'yar babyn kafin ta dungura mata kofin a saitin bakinta.
Kafin kiftawar ido taga ba komai cikin kofin, Mamaki ne da tsoro suka ziyarce ta a lokaci daya
domin har kara daga kofin take tana leka kasar kamar wata sokuwa. Shaaaaa 'yar babyn tayi
aman duk madarar. Mama Asiya bata san hauwa ba bata san sauka ba sai ji tayi an dauke ta
da mari mai karfe. Da sauri ta dafe kumatun ta. Da wata siririyar murya babyn ta fara magana.
"Muguwa azzaluma kinsan madarar ba sanyi shine zaki bani?. Wato ke gaki 'yar bak'in ciki in
sha in mutu, To ta Allah b taki ba". Mama Asiya cikin kuka-kuka "Dan Allah kiyi hakuri, Naga
sanyi sanyi ake shiyasa ma bansa ta...". Rufe min baki yanzu tashi ki goye ni mu fita waje
tsakar gida. Dan iska nake so insha". Mama Asiya jiki na rawa ta dauki 'Yar babyn ta goya ta
nufi waje. Su Hauwa na ganin ta wuce suka kara kwashe wa da Dariya. Juyowa tayi a fusace
"Zanci kaniyar mutum Wallahi, Kaji 'yan iskan karya". Lokacin ta juyo ta dawo gaban su. "In da
wacce ta isa ta sake yi min Dariyar". Shiru sukayi kowa ta matse Dariyar. Mama Asiya na
tsaye gaban su sai surfa masifa take. Bayan ta taji wani mugun tsunkuli kamar za'a ciro fatar
jikin ta. Ihuu tayib"Wayyo bayana". Ba shiri ta juya sauri-sauri gudu-gudu ta bar falon._
_Da isa tsakar gida Sai ganin matar nan tayi tsaye sai harare ta take, Yanzu kuwa tama fi abun
tsoro. Idanunta sun wani kara girma. Girman da ya haura ka'ida. Da wata iriyar murya, marar
dadin ji matar ta nuna wani bango wanda wajen yayi dukun-dukun da datti. Fetin Yellow ne
amma an mayar da gun ja. "Waya mayar da wajen can ja haka?". Jiki na karkarwa Mama Asiya
tace "Wannan