Showing 3001 words to 6000 words out of 19901 words

Chapter 2 - HOORAIN MAI KUSUMBI

10 Sep 2025

1756

su sai ma kara sakin harbin da suke, nan fa zugan soldiers dinnan suka bayyana kansu kana suka cigaba da sakar musu ruwan alburushi... suma yan ta'addan na sakar musu, yan kauyen Oguma suke dawo yan kallo, tsoron daya lullube zukatan su na raguwa, wasu sojas dake tsaye a kofar ko wani gida suka umarci wadanda suka fito waje kan su koma cikin gida gudun kada harbi ya same su, ai kuwa da gudu duk suka shiga har da saka sakata, dama tsananin tsoro, rudu, da rashin sanin abin yi ne ya fito da su.

Nan fada ya dawo tsakanin SOLDIERS da yan TA'ADDA, sai musayar wuta harbi suke cike da kwarewa...
yan ta'addan nan kamar kara tunkudo su ake, ana kashe su suna kara fitowa, abu fa yaki karewa har karfen dayan dare, inda a lokacin shugaban su da wasu zugan suka kara cika kauyen, suna cigaba da harbi.

Al'amarin fa ya girmama tunanin sojas dinnan, domin basu dauka haka abin yayi muni ba.
Godiya soja da itama take cikin masu harbin ta koma gefe ta yanda ba za a ganta ba, wayarta ta fito dashi, number'n Hamdan ta yi dialing wanda Allah kadai ya san ina ta samu...



*******

Safa da marwa yake, cikin farfajiyar gidan da suke, ya kira number'n wasu sojas din da yake da shi, amma basa dagawa, ya tabbata har yanzu basu kamalla bane, gashi manyan sa sun bashi umarnin cewa kada ya shiga yakin, na shi bada umarni ne da jagorantan su kawai. Amma ya fada a ransa cewa dole idan fadan ya Ι“aci zai shiga cikin su... yana cikin wannan tunanin yaji wayar sa na ringing, bakuwar number'n ya gani, latsa kore yayi ya Ζ™ara a kunne sa ba tare da yace komai ba


Cikin muryar ta mai amon sauti da jarumta kamar ba mace ba tace
"sir! Godiya ce, yan ta'addan nan kara yawa suke, domin har sun kashe mana mutane biyar...."


Bai jira ta gama maganar ba ya kashe wayar ya jefa a aljihun wandon kakin sa, cikin zafin nama ya dauki bindigogi bayan ya cika musu bullet, tsakanin cikin kauyen Oguma da gidan da aka tanadar musu tafiyar mintuna talatin ne, ba kuma yaso yayi amfani da abin hawa, saboda hakan zai sanar wa yan ta'addan zuwan sa, so yake yayi musu dirar ba zata, da direction da aka basu ya dinga bi, cikin sauri-sauri gudu-gudu cike da taka tsantsan domin isa wajen...✍️








NoorEemaan
07082281566


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JxzoG62bUENBfExeNPbRSu
[14/12, 12:54 pm] π™½πš˜πš˜πš›π™Έπš–πšŠπš—βœ¨: πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡
HOORAIN MAI KUSUMBI
(The hunch back girl)
πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡




_NoorEemaan_




Chapter 3️⃣⏩4️⃣



"FIELD MARSHAL"

Shine sunan daya gani a rubuce baro-baro kan screen din wayar sa.

Latsa kore yayi hadi da kara wayar a kunne sa, cikin girmamawa wa marshal yace


"Good evening sir!"


"Evening captain, hope you are good?"


Hamdan yace "very well sir"


"That's nice, am... kan maganar da zaka jagoranci wasu sojas zuwa yaki ya tashi daga sati mai zuwa, domin mun samu labarin yan ta'addan nan sun sake kai farmaki wa kauyen, suna cikin wani hali matuΖ™a, dan haka jibi ne tafiyar ku in Sha Allah, domin gobe za a kamalla muku komai na tafiyar, all the Best captain Hamdan"



"Thank you sir" ya amsa yana taune jajayen labban'sa masu daukar hankali.

Ya jima yana tunane-tunane kana bacci ya dauke sa, kasancewar a matukar gajiye yake.



⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐



*WASHEGARI*
Misalin karfe goman safiya ce, zaune yake cikin motar sa yana sharara gudu kan lafiyayyen kwaltan, sanye yake da three quater wando na soja, sai singlet shi ma na sojas daya bayyana karfafan kafadun sa masu fadi, babu hula a kan shi yayi parking gashin sa as usually, kafar sa sanye da sandal fari mai igiyoyi, hannunsa dake murza sitiyarin cike da kwarewa sanye yake da tsad'add'en agogo, yayi mugun yin kyau...
Karatun Alqur'ani ke tashi cikin surutal Al-furqan, a nutse yake bi cikin zuciyar sa, wayar sa dake kan kujerar mai zaman banza ya dauka ya yi danne-danne kana ya kara a kunne sa, bayan seconds hamsin aka daga kiran daya Ι—ayan bangaren.
Kasa-kasa kamar mai tsoron kar a ji shi yace
"Assalamu alaikum, ina kwana first love, am on my way coming"
Abinda yace kenan ya katse kiran, bayan mintuna goma ya shigo unguwar su Nasarawa GRA, horn ya danna aka bude masa ya shiga, a tsakiyar gidan ya yi parking motar kana ya nufi part Ι—in Ammi.


A bakin kofar glass ya tsaya, kofar ta buΙ—e ya shiga, runtse ido yayi sak'amak'on ganin Ayiyah a Zaune, a ransa yace

"damn it! Meyasa matar nan ta dawo" domin idan akwai abinda yake gudu toh Ayiyah ce, duk da kasancewar ta kakar sa, amma mugun ciwon kai take bashi.



Ware rikitattun idanun sa yayi, kamar yadda ya saba ciki-ciki haka yayi sallama, yana k'ara daure fuskar sa tamau, gudun kada Ayiyah ta kawo masa wargi amma bai tsira ba...
Cikin muryar ta mai cike da k'arsashi duk da ta tsufa tace
"fuska Fara, zuciyar ka baka, idan ka ga dama ka dawo da fuskar ka ta shanu bai dame ni ba, wallahi sai nayi magana, domin ni idan nayi shiru ban yi magana ba bakina wari yake, wanna gantalewa da bakin halin har ina, a cewa kullum mutum fuska a murtuke kamar na kashin asuba "

Ammi dake jin su kuwa matse dariyarta tayi, Hamdan kuwa kara bata rai yayi ya nufi wajen Ammi ya zauna kusa da ita, Cikin kaunar mahaifiyar sa ya kalle ta kana yace "Ammi hope you are Fine?"


"Am very fine Dan albarka, ya aiki?"

"Fine first love"

ya amsa yana Ι—ora kansa kan kafadar ta.

Wani tabe baki Ayiyah tayi tace " haka fa, sai karyar turanci, yanzu fisabilillahi ko kunya baka ji, katoto da kai ka wani zo ka manne wa uwar ka, ko su Abbas da suke kannen ka basa wanna iyayin, ko da yaΖ™e laifin uwar ka nake gani, domin ita ke shagwaba ba" ta bantali goro tana tauna, jikake karas karas ta kuma baza kunne domin jin yayi magana amma bai kula ta ba, hakan ya dame ta, domin ita kam bata iya shiru ba, ba kuma ta so a yi shiru, "nayi magana kayi shiru kamar baka ji ba, gaskiya dai sai na fada, kuma bari ka ji ka yi ka nemo matar aure domin mun gaji da ganin ka haka, ko kuma na je kauyen su wata kawata na samo maka mata a can...."

Daga kansa yayi daga kafad'ar Ammi ya watsa wa Ayiyah, tilas ta tsuke bakin ta, domin tsoron kwayar idanun sa masu launin sky blue (kalan sararin samaniya) take, domin duk masifar da take mishi bata kallon fuskar sa.

Daga karshe ma mikewa tayi ta fara tafiya tana kananun surutai, Hadi da kwala wa mai aiki kira kan ta kawo mata abinda tace ta dafa mata.

Tana barin wajen Ammi ta saki murmushi mai sauti, sannan ta kalli Hamdan tace "ka dinga hakuri da halin Ayiyah son, ka san rikicin tsufa ke damun ta, kaji ko"


Jinjina mata kai yayi alamun toh.

Nan ya sanar da ita cewa an dawo da tafiyar su gobe, sosai Ammi tayi masa addu'a tare da fata na gari, duk da jikin ta yayi sanyi.


Suna zaune a haka su Abbas suka shigo, cikin girmamawa suka gaishe shi, hannu ya mika musu alamun su yi musabaha ba tare da yace komai ba, dadi ya kama su, Anas shine farkon mika hannun sa saboda farinciki, duk ranar da Hamdan ya shiga harkan su dadi sosai suke ji

Kallon su Ammi tayi cikin burgewa, da godewa Allah daya bata zaratan samari masu kyau da nutsuwa, duk da cewa Hamdan baya shiga harkan su, amma yana matuk'ar kaunar kannen sa, halin shi ne haka, baya shiga harkan mutane sam, ga wanda bai gane ba sai ya dauka wulakanci ko girman kai ne dashi, shiyasa a kullum take rokon Allah ya bashi mace da zata Sanja masa wanna halin nasa ko da ba duka ba, but at least ya kasance mai walwala kamar kowa..


"Anas, kabeer, Omar."

"Yes Ammi" suka amsa a tare.

"Kuyi wa Captain addu'a gobe zai jagoranci wasu sojas zuwa kwantar da tarzoma da yan ta'addan suka tayar a garin Kogi" kasancewar labarin a bayyane yake, domin duk wata kafa ta sadarwa sun fadi halin da wannan yan garin suke ciki.


"Addu'a sosai suka yi masa, a kasan makoshi ya amsa da "Ameen" sun karanci hakan ta lips din sa, sai suka kalli juna suka yi murmushi...


Anas daya fisu surutu ne yace "Ammi, ina Ayiyah?"
"Yanzu ta gama drama da yayan ku, ina tunanin tana dakin ta"

Dariya suka yi, kana suka mike, domin tafiya wurin ta, su kam suna kaunar Ayiyah a gidan, ko ba komai zasu ci dariya.


Hamdan bai bar gidan ba sai karfe biyar na yamma, bayan ya bawa Ammi makud'an kudade, sannan ya bawa su Anas har ma da Ayiyah, duk da basu rasa komai ba amma hakan baya hana shi ya basu kudi.
Domin har yau akwai kamfanunuwan mahaifin su daya bari kafin ya rasu kuma su Anas ke kula da shi.


Addu'a Ammi ta kara yi masa, ya rugunme hallita mafi soyuwa a rayuwar sa cikin jin dadi samun ta a matsayin uwa mai kulawa da tsananin son y'ay'an ta.


Da haΖ™a suka yi sallama Ammi na daga masa hannu har ya fita kana ta share hawaye tana rokon Allah ya dawo mata da shi cikin koshin lafiya.



*BUKAVU BARRACKS*

Hilux Masu dauke da zanen sojoji hadi da motocin amoka da yawa suka jeru reras, kimanin soldiers da zasu kai dubu dari biyar ke tsaye ko wanin su ya kame cikin kayan sojoji, sai jaka irin na sojas dake rataye a bayan kowanne su, ga bindigan AK-47 dake rataye a kafadar su, kawai jiran umarni suke domin su fara tafiya.


Cikin tafiyar nan tasa ta lafiyayyen namiji mai ji da kuruciya hadi da takama ya nufo inda motocin suke,...
Wajen commander dake tsaye ya nufa, ya kame hadi da tsara masa, hannu shi commander ya kama suka dan koma gefe, yayi masa wasu maganganu da basu wuce mintuna uku ba sannan suka dawo inda commander'n ya tsaya dazu, wani Kurt soja ya bude wa hamadan kofa, cikin jarumta ya yi tsalle ya fada cikin motar amoka domin irin mai tsayin nan ce, umarnin tafiya ya bayar, nan motocin suka fara tafiya, a jere...
Sauran sojas da babu su a yak'in tsaye suna daga musu hannu hadi da yi musu fatan dawowa lafiya, haka suka ratsa gate suka fice...


⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*KOGI STATE*
*(Kauyen Oguma)*

Kauye ne mai girma hadi da tarin jama'a, ga ni'ima mai sanyi da Allah ya albarkaci kauyen da shi.

A yau ya kasance ranar cin kasuwar su ne, amma babu halin hakan, saboda tashin hankali da tsoro da suke ciki, sakamakon yan ta'adda da suka kawo wa kauyen farmaki, wanda hakan ya sa suka rasa kwanciyar hankali, fuskar su a lullube da tsoro kallo daya za ka musu ka fahimci hakan, ko yaran su basa iya zuwan makaranta, dare da rana cikin addu'a suke kan Allah ya kawo musu dauki, domin har sun rasa yan'uwa da abokan arzikin da yawa.



Gida ne dan madaidaici mai dakuna biyu ginin jar kasa, irin na kauye, har rubewa ginin ya fara yi, kallo daya mutum zai yi wa gidan ya fahimci cewa ko a talakawan kauyen, wanna gidan nasu talaucin ya munana.

Yarinya ce yar shekara goma sha bakwai ta buΙ—e wata kod'add'iyar zanin atamfa daya kasancewa kofa ga banΙ—akin su da ko rufin sama babu ta fito.
Abin mamaki da al'ajabi ga wanna budurwa mai kananun shekaru shine Bata tsaya kan kafafun ta ba, ta tsunkuya irin yadda tsofaffi masu tarin shekaru da basa iya tsaye kan kafafun su haka take, sakamakon kusumbi (hunch back) dake bayanta, kusumbin ya kumburo sosai a bayanta tamkar an kifa katon kwarya.

Kyakkyawar ce, sannan fara ce, sol irin mai daukar idon nan, duk da cewa suna fama da talauci, amma skin dinta na nan fresh wanda hakan baya rasa nasaba da ni'imar kauyen da suke dashi

Butar hannun da ko albarkan murfi babu, ga shi duk ya faffashe ta ajiye a gefe kana ta yi tafiya irin na masu kusumbi ta zauna kan matacciyar tabarman dake shimfide a gefen dakin su.

Numfashi ta sauke bayan ta juya lulu eyes dinta masu girma hadi da haske...
tagumi tayi, bazata ce rayuwa bata mata adalci ba, sai dai akwai tarin kalubale a rayuwarta da take fatan ya zama nasara ko samuwar farinciki ga rayuwar ta, duk da hali da lalurar da take ciki tana godewa Allah, domin akwai wadanda suke cikin hali daya fi nata muni, sai dai raunin ta na bayyana ne a duk lokacin da ta fita, yammatan kauyen ke sata a gaba da tsokana da kiran ta *HOORAIN MAI KUSUMBI* ga zallan kishi da take hangowa a idanun su wanda bata san ko na menene ba, duk da lalurar ta...


Kara juya fararren idanun ta tayi, wanda hakan dabi'a ne a gareta, sannan ta rufe idanun ta ruf, tunanin tashin hankali da suke ciki a wannan k'auyen take, addu'a take a ranta kan Allah ya kawo musu mafita da kwanciyar hankali.


"HOORAIN!"
Taji an kira sunan ta...




Share share share
fisabilillah πŸ™






NoorEemaan
07082281566
[14/12, 12:54 pm] π™½πš˜πš˜πš›π™Έπš–πšŠπš—βœ¨: πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡
HOORAIN MAI KUSUMBI
(The hunch back girl)
πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡πŸ“πŸ‡




# _NoorEemaan_



*DEAR LOVELY FANS DA MA MAKARANTAN HOORAIN PLEASE KU KARANTA WANNAN BAYANIN NAWA IT'S VERY IMPORTANT*

_Zan yi wanna dan tsokacin ne idan ma akwai mai irin wanna tunanin a ransa_.
_Kila wasunku zaku ce meyasa Noor ta rubuta cewa HAMDAN yana da gashi, bayan ba a san sojojin da gashi ba_.

_Yeah it's possible soldiers su tara gashi, amma mafi yawa na nan Najeriya basa yi_...
_Abin da ya saba dokar soja shine askin banza ne ba a so_... _Amma bawai basa tara gashi bane, sai dai mafi yawan su basa tara mai yawa_...

_Dan haka Habibte's ina sane da abinda na rubuta, domin ina da experience a akan soldiers, ina da friends da yan'uwa sojas, and also tun Ina pre-nursery har na gama secondary school a barrack din sojoji nayi karatu na, to Cut it short_...
_Haka nake son HAMDAN ya kasance a littafin HOORAIN, shiyasa na rubuta cewa yana da suma_.
_Abu mafi muhimmanci a novel shine sakon da marubuciya take son isar wa yaje inda ake so_.

_A karshe dai makaranta na da suke bibiyata tun daga farkon book dina sun san cewa duka book dina fictional story's ne, ban taba rubuta true live story ba, Dan haka a Novel ba komai ne dake faruwa a gaske za a rubuta ba, dole akwai nishadantarwa domin kawata Labarin_.


*Thank you all da yanda kuka karbi littafin HOORAIN MAI KUSUMBI Allah ya bar kauna, son so nake Muku.πŸ’ž



Chapter 7️⃣ ⏩ 8️⃣

Tafiyar da ya kamata yayi a Mintuna talatin, a 20 minutes yayi shi.
A lokacin daya isa wajen yayi mamakin yadda abu ya Ι“aci haka, ba tare da bata lokaci ba ya shiga cikin sauran soldiers aka cigaba da fafatawa cike da kwarewa wanda hakan ya nuna cewa sun sha training mai zafi...


A takaice dai sai karfe hudu saura aka samu komai ya lafa, inda yan ta'addan nan da suke rage takwas har da shugaban su suka yi kokarin guduwa, domin bullet din su ya kare.

Cikin sa a hamdan ya samu nasarar sakarwa biyar arbi a kafafun su biyu, sauran ukun ma wasu soldiers din suka karbe su, hakan yasa suka zube a kasa suna ihu azaba...

Umarnin Hamdan ya bayar cewa a kamo su duka. Sannan ya ce wa wasu soldiers din su tsaya a kauyen har safiya domin tabbatar da tsoro, cikin girmamawa suka amsa da "yes sir!"
Bayan sun isa gidan da suka sauka nan aka kulle yan ta'addan nan a wani daki.


*WASHEGARI*
Kusan ko wani kafa da sadarwa sun samu labarin abinda ya faruwa, sun kuma bayyana wa jama'a, zuciyar mutane cike da farin ciki nasarar da Allah ya bawa wadanda jaruman sojas din masu kishin kasar su.

Field marshal wanda shine mai 5 star rank general, haka kuma shine highest rank a Nigerian army, Ya kira Hamdan ya yaba masa.


Ammin ma ta gani a news din karfe shida da ta kalla, ta kira hamdan tayi masa murna sosai da addu'ar Allah ya dawo da su lafiya.


Da misalin k'arfe taran safe yan jaridu sun cika k'auyen oguma domin cigaba da daukar rahoto, Sannan an kai yan ta'addan nan babban kotun Abuja kasancewar daga kogi zuwa Abuja babu wani mugun nisan, an saka su a prison zuwa ranar da za a yanke musu hukunci...



*BAYAN KWANA ƊAYA*.

Ta bangaren yan k'auyen oguma kuwa sosai suka tashi da nishadi a safiyar yau, tsoron da fargaban su ya kau, sun dawo hada-hadar su kamar yadda suka saba cikin walwala.



********

Tafe take cikin tafiyar ta irin na masu kusumbi, hanyar rafin kauyen su ta nufi, duk da yanda mami ta hanata zuwa, amma bazata iya kallon Mami da girman ta na zuwa diban ruwa yayinda ita ke zaune ba.


Jefi-jefi tana haduwa da mazan garin suna gaisawa a mutunce. Allah yayi wa Hoorain wani mugun farinjini wanda hakan ke bak'anta ran yawancin yammatan kauyen, ganin su lafiyayyu marasa nakasa mazan basa Kula su kamar yadda suke wa Hoorain magana.


***

babba rafi ne wanda yake kashi uku, bangaren daya wasu na wanka, dayan wasu na wanki, dayan kuma na diba ne, a sha a kuma yi girki ba a shiga cikin sa.


Ga wani babban maciji mai jan abu a kansa kamar hula yana gefen ruwa ba tare da yayi wa kowa komai ba, haka ma mutane dake rafin basa tsoro, abu ne wanda sun riga sun saba da ganin sa, domin duk wani d'a ko y'a a k'auyen haka ya tashi ya tarar da macijin nan a rafin.


Sannan abin mamaki da tsoro, ga wanna macijin shine matuΖ™ar mace na period bata wanka cikin rafin, sannan idan akwai janaba ko da datti a jikin Mutum ya shiga rafin dan wankan toh sai macijin nan ya sare shi.


Ga yammatan nan da yawa wasu na wanki, wasu na wanka, wasu na hira a tsakanin su.

Ko kallon su Hoorain bata yi ba ta cigaba da tafiyar ta a hankali domin isa wajen diban ruwa, tana jin yammatan nan na mata dariya, ta gefen ido ta ga wata na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login