Showing 6001 words to 9000 words out of 19901 words
k'waik'wayon irin tafiyar ta, Murmushi Mai ciwo tayi wanda ya taho da zubar hawaye mai dumi daga idanun ta, hannu tasa ta share fuskar ta.
Saka madaidaicin bucket Mai hannu tayi ta diba ruwan ta kana ta fara tafiya domin barin rafin, ta ji sun sakar mata ihu suna karin "Mai kusumbi" cikin shekiyanci hadi da tsokana, hadiye kukan ta tayi har ta ɗan yi nisa da rafin kana ta ajiye bokitin ta fashe da kuka mai ban tausayi hadi da taba zuciyar mai sauraron ta, har wani shesheka take saki..
Ji tayi an dafa ta a baya, cikin sauri ta juyo, "Aramani!" Ta kira sunan matashin daya dafa ta tana sakar masa Murmushi, a kokarin ta na boye damuwar ta.
Wanda aka kira da Aramani ya dauki bokitin data ajiye, cikin tausayawa ya ce "hoorain kada ki min murmushin da bai kai zuciyar ki ba, bayan ga tarin damuwa kwance cikin idanun ki, kiyi hakuri da abubuwan dake faruwa watarana komai zai wuce, ki daina barin maganganun wasu yana damun ki, domin ke din ta daban ce, kin fisu komai, ki manta da lalurar ki, You re a special Creator from God, Dan haka cheers ok?"
Hannu ta sa ta kara goge fuskar ta da kyau, bayan Mamin ta, Aramani kadai ne mutum na biyu dake son ta hadi da bata karfin guiwan ta da rasa, take kuma kan rasawa a duk lokacin da aka tozarta ta a kauyen oguma.
sanyin ta ji a ranta, atleast ta dan samu karfin guiwa, cikin sanyin Muryarta tace
"Nagode omaye mie" Aramani"(omaye mie na nufin dan'uwana da Yaren Igala)
Murmushi kawai ya sakar mata, suka fara tafiya yana jan ta da hira hadi da bata labarai masu ban dariya domin ta saki ranta.
Murmushi take yi kasancewar aramani na da barkwanci sosai.
Tun daga nesa hoorain ta hango Taheer dan mai gari da zugan sa a zaune suna kallon duk wata mace data wuce, kuma matukar yana son mace dolenta ta amince masa, kasancewar baban sa mai kudi gashi kuma a Abuja yayi karatu hakan yasa matan kauyen ke rububin sa, wasu ma da gangan suke hucewa sau goma domin ya kyasta.
Gaban Hoorain ya fad'i, tana matukar tsoron Taheer domin sam baya da d'aa bare Magana mai dadi a bakin sa, sannan ta rasa me ta masa, da duk lokacin da ya ganta sai ya jefa mata kallon tsana, bata mantawa ranar da ya ke faɗin
ya tsane ta, ita din mummuna ce, mai tawayar hallita baya kaunar ganin ta, haka ya disga ta cikin tarin jama'a a ranar tayi kuka kamar ranta zai fita, ta rasa me ta tsare masa, haka suka wuce sam bata bari sun hada ido ba, sai dariyar abokan sa data ji cikin tsokana, alamun yayi wata magana data shafe ta, duk hirar da Aramani yake mata sam bata fahimta a yanzu.
Har cikin gida Aramani ya shigar mata da ruwan, suka gaisa da Mami kana yayi musu sallama ya tafi...
⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐
Press up yake cikin sauri-sauri ya had'a uban gumi domin kimanin mintuna talatin ya dauka yana yi, sai daya gaji dan kan sa kana ya mike yana goge fuskar sa zuwa wuyan sa da farin towel dake rataye a wuyan sa, direct toilet ya wuce ya yi wanka, kana ya fito, cikin blue jeans da farar T-shirt ya shirya, gashin sa daya zo masa saman wuya ya cire rubber band daya riƙe gashin, kana ya shafa oil ya taje...
As usually ya kara parking gashin a kasan keyar sa, facing cap ya sanya, ya fashe turaren sa, palm sandal ya saka a kafar sa sannan ya dauki wayar sa ya fito...
Wajen gidan da suka sauka ya tsaye, haka kawai ya ji yana son zuwa kauyen, cikin tafiyar sa ta birgewa ya shiga taka wa yana jin yanda idanun jama'a ke yawo a kan sa, bai damu ba duk da baya son kallo... abinda ya faranta masa rai shine ganin yanda yan kauyen ke ta walwalar su ba kamar ranar da suka zo ba, a ransa ya raye cewa zaman lafiya ya fi komai dadi, haka kuma yana saka al'umma samun cigaba.
*HOORAIN*
A hankali ta fito daga cikin gidan su tsintsiya dauke a hannun ta, share kofar gidan su ta fara yi...
hakan yayi daidai da lokacin da hamdan yazo wucewa, bai san me ya kai idanunsa kan farar kagun ta dake sanye da jigida(waist bead) ba, wanda ita Hoorain bata san cewa rigarta ta ɗan dage ba, saurin dauke idanun sa yayi, ya cigaba da tafiya, zazzak'ar Muryar ta ya ji tamkar busar sarewa... cak ya tsaya da tafiya saboda yanda wakar ke fita daga bakin ta kamar haka...✍️
Ga masu son shiga hoorain group ga link👇
https://chat.whatsapp.com/JxzoG62bUENBfExeNPbRSu
NoorEemaan
07082281566
[14/12, 12:54 pm] 𝙽𝚘𝚘𝚛𝙸𝚖𝚊𝚗✨: 🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇
HOORAIN MAI KUSUMBI
(The hunch back girl)
🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇
_NoorEemaan_
*The love and affection he has for her totally made him a changed person. Labarin da yazo da wani salo wanda baku taba ganin irin shi ba, fadakarwa, zafaffan soyayya, tsantsar kiyayya, sadaukarwa mai girma and a lot of more*
Chapter 9️⃣⏩🔟
🎻🎻 _I wanna come home to roses_🌹 _And dirty little notes on post-it's_📝 _And when my hair star turning grey_...🧑🏽🦳🎻🎻
🎻🎻 _He will say I'm like a fine wine better than age_🍷
_I guess i learned it from my parents, that true love starts With friendship_♥️
_A kiss on the forehead_💋 _a date night_🌃🍝
_Fake an apology after a fight..._🤫
_i need a man who's patient & kind gets out of the car and hold the door_🚗
_i wanna slow dance in the living room like_... _we're 18 at senior prom_.
_And grow old with someone🧑🏽🦳👨🏼🦳who makes me feel young_💃🕺
_i need a man who loves me likeee... My father loves my mom_♥️🎻🎻
ta kai ƙarshen wakar nan da wani slow tone mai tsayawa a rai.
*HAMDAN*
Ji yayi Kamar ruwan kan shi ya kone, wani yanayi mai wuyar fassaruwa ya dinga ratsa shi, ba tare da ya shirya wa hakan ba, kasan makoshi ya furta " ya rabb! what a melody voice"
Hoorain kuwa sam bata san da tsayuwar sa ba, domin ita kanta dake wakar ratsa zuciyar ta yake, sosai take matukar son wakar nan, wanda a wayar Aramani ta fara ji har ta haddace ta saboda kaunar da take wa wakar...
Idanun sa ya kai kan fatar hannun sa...kofofin gashin jikin sa sun bubud'e wanda hakan baya rasa nasaba da yanda wakar ta yi tasiri har jinin jikin sa, bai kara bari ya kalle inda take ba ya fara takawa cikin tafiya mai kama da sassarfa ya bar wajen.
Bayan ya isa gidan da suka sauka kan gado ya fada, yayi matashi da karfafa hannun sa, yana sauke tagwayen ajiyar zuciya tamkar wanda yayi gudun tsere, ya rasa yadda zai fassara wannan yanayin da ya shiga yanzu...
**********
*HOORAIN*
Zaune suke a karamar tsakar gidan su, kafar ta na cinyar mami tana gyara mata farcen ta abin so adorable. Mafi yawan mutane na mamakin yadda Hoorain ke fara sol, yayinda Mami baka ce.
Shakuwa da soyayyar da suke wa juna abin burgewa ne, tamkar ya da kanwa haka suke.
"Mami mie" Hoorain ta kira Mami da taushin murya.
"Na'am" Mami ta amsa cikin kulawa tana kallon ta.
A karo na uku take son furta Abinda ke ranta amma ta rasa yanda zata fara tambayar Mami amsar da ta dade tana son ji.
Numfashi ta sauke kana tace "Abbi! Mami Please ina yake?"
Kod'add'iyar rezar dake hannun ta Mami ta ajiye, damuwa mai yawan gaske ya bayyana a fuskar ta, hannun Hoorain ta rike da har ta fara hawaye tace
"Hoorain! Sau nawa nace Miki kada ki kara min maganar Abbin ki? Shin akwai abinda na gaza Miki a matsayin uwa? Akwai? Na sani cewa muna cikin matsin rayuwa wanda nake fatan ya zama tarihi watarana, ko kin gaji da zama da ni bana miki yadda kike so?".
Cikin sauri ta rungume Mami tana sakin kuka mai taba zuciya, kan kusumbin ta da kamar kullum kara masa girma ake Mami take shafawa... cikin so, kauna, da tausayin tilon yarta.
Hak'ik'a tana ganin rayuwa wanda babu wanda zai kawo mata sauyi face Ubangiji, bata damu da kanta ba, kullum addu'ar ta shine Allah ya kawo sauyi Na alkhairi a rayuwar Hoorain...
Sam bata son jin Maganar mahaifin Hoorain wanda ya wofintar da su, ko yar sa bai kara waiwaya ba yau shekaru sha biyar kenan, Meye laifin su da suka cancanci wannan sakamakon daga gareshi?...
***********
A yau su Hamdan suka samu sanarwar daga manyan sa kan gobe zasu dawo, domin an riga an yanke hukunci wa yan ta'addan nan daidai da laifin su...
Sai dai abin mamaki sai ya ji ba dadi a lokacin daya samu wanna sanarwan duk da yanda yake a k'age ya bar kauyen, gaba-daya sai ya rasa abinda ke masa dad'i, yana ji kamar zai bar abu mai muhimmanci ya tafi wanda bai san menene shi ba.
Haka ya wuni cikin wani yanayi mara dadi a gare shi.
*WASHEGARI*
Bayan sallar asuba duk suka yi shirin tafiya amma banda hamdan. Jin shiru ya sa wani soja ya zo ya k'wank'waso dakin sa, yana kan sallaya yana addu'o'i... shafa addu'ar yayi kana ya mike ya bude Kofar, cikin girmamawa sojan ya kame ya sara masa, jinjina masa kai Hamdan yayi ba tare da yace komai ba.
Sir! Kai kadai muke jira" inji sojan.
Boyayyen ajiyar zuciya hamdan ya saki kana yace "am not going with you guy's" ya fad'a yana yin hanyar waje, bayan sa sojan nan ya bi.
"Good morning sir?" Duk suka fada suna tsara masa.
"Morning!"
Ya fada cikin husky voice din sa, yayi shiru na seconds hamsin duk sun zuba ido da kunne suna jiran yayi magana.
"Ban zan tafi da ku ba, akwai abinda zan yi a nan for some days, already nayi magana da commander, safe trip guys"
Yana gama fadin haka ya juya zuwa cikin gidan, yana mamakin yanda ya kasa sarrafa kan sa, balle ya bijirewa umarnin da zuciyar sa ke ba sa.
Haka ya wuni cikin gidan, ba tare da ya sake fita ba.. ta bangaren sojas dinnan kuwa misalin k'arfe hud'u na yamma suka isa bukavu barracks motocin su a jere reras... Da ihu suka shiga babban gate din *quarter guard* suna buga band, hadi da rera wata waka ta soldiers, gaba-daya Muryar sa ta karade barrack din daya kasancewa shiru, yawancin sojas dake barrack din suka fito waje murmushi dauke a fuskar su suna daga musu hannu, domin wanna ihun da sojas din keyi ya tabbatar da cewa sun samu nasara a fita wannan yakin da suka je.
Commander dake tsaye cikin tsantsar farinciki na kallon su har suka gama faka motar su, kana duk suka zo wajen sa, cikin girmamawa suka kame kam kana suka tsara masa...
Hannu ya dora a kansa yayi musu alamun jinjina, wanda hakan yayi nuni da cewa ya jinjina wa jarumtar su, ya kuma ji dad'i, bai wani tsayar da su ba ya sallame su domin su huta gajiya...
*NASARAWA GRA SULTAN ROAD*
"Falmata! Wai har yanzu wannan gantalafaffen inuwar yakuwar Hamdan din bai dawo ba? Bayan ga shi mun samu labarin sauran sojojin sun dawo, duk da bai da kirki, amma Ni na damu da shi saboda banda bakin hali irin nasa, yadda nake fara a fuska haka zuciya ta take tas, na rantse da Assamadu da ina nan lokacin da Yaron nan zai tafi soja da ban bari ba, yo ya lafiyar kura ma, ace banda bakin hali da murtuke fuska babu abinda ya karo" Ayiyah ta karasa cikin kumfan baki, kai kace zata rufe Mutum da duka.
Su kabeer dake zaune a wajen dariya kawai suke ba ma kamar kalmar gantalafaffe inuwar yakuwa da ta ce.
Ammi dake zaune ta kalle ta kana ta ce "Ayiyah bari na kara kira number'n sa, Ni kaina na damu da rashin dawowar ta sa wallahi".
Ammi ta karasa tana latsa tsad'ad'iyyar wayar ta wanda hamdan ya siya musu iri ɗaya.
*HAMDAN*
Zaune yake ya jingina kansa da bangon dakin, idanun sa a lumshe, Muryar ta dake rera waka na amsa kuwwa a kunnen sa tamk'ar yanzu ne ta ke yi, ringing din wayar sa ne ya dawo da shi duniyar tunanin daya fada, rikitatun idanun sa da suka dan Sanja launin ya ware kana ya latse kore hadi da karawa a kunnen sa...
"HAMDAN!"
Ammi ta kira real name din sa wanda zai yi wuya ka ji ta kira shi da suna sa.
"Yes first love, good evening?"
Bata tsaya amsa gaisuwar ba tace "Are You okay? talk to me kana lafiya dai ko?"
Murmushin da iyakar sa labb'a ya saki, yana matuƙar kaunar Ammi fiye da zaton mutum, ita din rayuwar sa...
"Ammi ina lafiya"
"Then meyasa baka dawo da sauran sojas dinnan ba, am pretty sure baka dawo ba, na san da ka zo gida".
"Dan taune lips din sa yayi, cikin yanayin sa na rashin son magana yace " ina Kogi..., amma zan dawo soon, wani abu zan yi ne, amma karki tambaye ni please Ammi nah"
Jikin Ammi ne yayi sanyi, ajiyar zuciya ta sauke ta ce "kana boye min wani abu ne?"
"Not at all first love"
"Hmmmm..." Ammi tace tana sauke numfashi, kana ta kara da cewa "i wish you all the best son"
"Thank you first love, how are my siblings doing?"
"Fine alhamdulillah" daga can ya ji muryar Ayiyah na cewa
"ka ji dan k'wal uban yaro mara kirki, ina nan na tada hankalina a kan ka amma ko kace a bani way..." Ai bai jira yaci karshen maganar ba ya katse wayar, domin Ayiyah zata iya saka masa ciwon kai da surutun ta.
*******
*BAYAN KWANA DAYA*
da misalin karfe shadaya ya shirya cikin polo T-shirt black sai wando ash color, kasancewar akwai dan rana yau sai ya sanya facing cap, fess da shi looking handsome sai tashin k'amshin sanyayyar perfume yake na company'n D&G.
Hannun sa duka biyun soke Cikin aljihun ya fice daga gidan, cikin kauyen oguma ya nausa, bai san abinda zai kai shi, sai dai zuciyar sa na mamari da kwadayin zuwa kauyen.....
Bai wani hadu da mutane sosai a tafiyar sa ba sai jefi-jefi, kasancewar yau talata ranar cin kasuwar su ce, yawanci suna kasuwa yayinda wasu ke gona, daidai yazo Kofar gidan da ya ga Hoorain na shara sai ya kasa cigaba da tafiya, kamar an rike kafafun sa, mamakin yake, yadda gaba-daya ya fara sauyawa daga ainahin HAMDAN MALEEK BUMSA zuwa wani daban....✍️
_manage Please, yau nayi busy da yawa_...
Share share share fisabilillah🙏
NoorEemaan
07082281566
Thank you for reading my novel 🥰
Ga mai son shiga group din Hoorain mai kusumbi ya danna wannan link din👇
https://chat.whatsapp.com/JxzoG62bUENBfExeNPbRSu
[14/12, 12:54 pm] 𝙽𝚘𝚘𝚛𝙸𝚖𝚊𝚗✨: 🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇
HOORAIN MAI KUSUMBI
(The hunch back girl)
🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇
*Korafi ya karbu, zan kara yawan typing. Ina godiya sosai masoya da yanda kuka karbi littafin Hoorain, ku cigaba da bin alkamina domin jin yadda labarin zai kaya, wannan littafin ya sha bambam da duk wani Novel nawa, sosai na jima da son yin book din nan tun a Novel din papi, Amma Allah bai nufa ba sai yanzu, Muje zuwa... Noor na muku sahihiyyar kauna*💕😘
_written by NoorEemaan_✍️
Chapter 1️⃣1️⃣⏩1️⃣2️⃣
_________Mintuna goma masu kyau ya dauka a tsaye yana murza hannun sa cikin na juna, duk wani tunanin sa ya tsaya cak, zuciya da idanun sa ke son ganin ta, duk yanda ya kai ga son bijirewa zuciyar sa ya kasa... Kamar wanda ake bawa umarnin haka ya ga yana jefa kafar sa cikin gidan, sautin bugun zuciyar sa na sauyawa...
Sai daya tsinci kansa a dan soron gidan su kana hankalin sa ya dawo jikin sa, a ransa ya furta
"Hamdan me hakan kake yi akan mace? Please come back to your normal self, this is not you"...
Cikin sauri ya juya domin barin gidan... saura bai fi taku uku ba yace an ce
"waye nan?"
Runtse rikitattun idanun sa yayi, kana ya ware su ya juyo ga Mami dake tsaye, duk da yanayin mai wuyar fassaruwa da yake ciki ba zaka taba fuskantar hakan a saman fuskar sa ba.
"Me zaka ce kazo yi cikin gidan su?"
Wata zuciyar ta tambaye sa.
A hankali ya tako ya zo gabanta, cikin girmamawa ya dan dukar da kan sa yace
"Good morning ma" domin a lokacin sha biyu saura.
" Good Morning, lafiya dai ko?" Mami ta fada Cikin sakin fuska, a ranta tana mamakin Meye kawo shi gidan su?
Ta bangaren hamdan ma ya dan yi mamakin jin Mami tayi Hausa, kasancewar kallo daya mutum zai mata ya gane cewa ita din ƙabilar igala ce, amma bai nuna ko alama ba.
Kamar yadda ya saba yake kuma dabi'a a gareshi ya buɗe bakin sa kamar bayason magana yace "nazo ganin ta ne"
ya ji ya fadi maganar da bai san ta ina ya fito ba.
A ransa yana fatan kada ta kara masa wata tambayar, domin wanna karon bai da wata sauran amsa.
Dariya ya bawa Mami, amma bata yi ba, ta maimaita abinda ya fada " nazo ganin ta ne" ta lura kamar bai da son yawan magana,
"shigo daga ciki" Mami tace yana yin gaba, ta san cewa bazai cuce su ba, domin yanayin sa bai yi kama dana mugu ba, duk da ance mugu bai da kama. ga agogon soja dake hannunsa wanda ya tabbatar mata da cewa yana daga cikin sojojin da Allah ya aiko suka kawo musu karshen azzaluman yan ta'addan nan.
****
Da kallo Hoorain dake zaune kan yagagiyyar tabarman su ta bi su da kallo, hannunta cikin sakin masara da man ja Sai yaji... Kasa hadiye na bakin ta yi sakamakon ganin Mami da wani Balarabe a tunanin ta sun shigo...
Da kallo ta bisu, mamaki fal fuskar ta, cikin Yaren Igala tace Mami tace "Hoorain wajen ki yazo"
Duk da tayi mamakin abinda Mami tace amma bata nuna ba, cikin ladabi tace
"toh Mami".
Daga haka Mami ta shige daki abun ta.
Sauke idanun ta kasa tayi, cikin rashin sanin abinyi ta cigaba da taunan abincin ta a hankali...
*HAMDAN*
Tsurawa k'ananan labb'an ta masu kala biyu yayi, wanda ya kasance pink sai zagayen baki kamar ta zana da eye- pencil sai dai ba haka bane, naturally haka lips din ta yake...
Yanda take taunan yafi komai tafiya da shi, idanunsa ya kai kan sakin masara da yayi fari kamar ma ba a sa masa manja ba, alamun bai ji