Showing 9001 words to 12000 words out of 19901 words
ba.
Ya kasa yarda cewa mutum ke cin irin wanna abincin da a wajen shi sai dai ya kira shi guba, domin a tunanin sa zai iya sa mutum rashin lafiya, saboda ganin da yake wa abincin yanzu wani tashi zuciyar sa ke yi, dauke idanun sa daga kan abincin yayi, a fakaice ya kalli tsakar gidan su, a rayuwa bai taba ganin gida daya lalace irin wannan bare har ya shiga, amma saboda bawa abinda zuciyar sa ke so yau gashi a cikin gidan da a wajen shi gwara kwalta a kan sa.
"Tsawon wani lokaci suka dauka cikin irin wanna gidan? Allahu Akbar and they survive" Ya fada a ransa, yana jin wata matsananciyar tausayin su, dama akwai mutane da suke cikin zallan talauci haka?
Bayan ga masu hali bila adadin suna facaka da kudi kan abu mara muhimmanci.....
Ajiyar zuciya amma boyayye ya saki a Lokacin da ya ji melody voice din ta.
"Good afternoon, Please sit" tace tana nuna masa tabarman bayan ta dan matsa.
Kallon tabarman daya yayyage ga jan kasa duk ya cika shi, kamar mai tsoron kar wani abu ya cije shi haka ya fara kokarin zama, cikin sauri Hoorain ta zabe dankwalin atamfar kanta daya sha ruwa ya kode ta warware kan tabarman, ta kuma yi hakan ne gudun kada wandon shi ya bace, kana ta yafa wani bakin dankwali dake gefen ta, wanda ya dawo ruwan kasa-kasa saboda tsabagen d'ad'ewa.
Ajiyar zuciya ya sauke, kana ya zauna, amma kafafunsa na kasa, bai cire takalman sa ba.
"Bismillah"
tace tana dan turo masa kwandon samiran da duk jikin sa ya gama tsatsa.
Can kasan makoshi ya girgiza kai hadi da furta "Thanks" kasa cigaba da ci tayi, sai wasa take da hannun ta cikin abincin.
Cikin tausaya wa ya kalle ta, a ransa yake fadin abincin ba dadi shiyasa ta kasa ci, shi a hakan ma ya ga kokarin ta, domin a cewar sa ko dabbobi aka bawa bazasu iya ci ba, zuciyar sa ce ta kasa hakuri ya ce "ba dad'i ko" da dan mamaki ta kalle shi jin yana Hausa, amma bata ce komai ba, cikin murmushi daya taho da cikowar kwalla tayi, wanda ya lo6a one side dimple dinta tace "tun ina shekara biyu na fara cin irin wanna cimmar, kaga ya zame min jiki, kawai nayi loosing apatite ne"
Lumshe rikitattun idanun sa yayi kana ya bude su, Muryar ta na matukar tasiri a jikin sa...
Haka suka yi zaman kurame babu wanda ya Ζara magana, can Hoorain tace "kana cikin sojas da kuka taimaki kauyen mu ko?"
Jinjina mata kai yayi, ba tare da yace komai ba, murmushi tayi tace "mun gode kwarai, may Allah reward You guys"
"Ameen" ya amsa slowly.
Daga nan babu wanda ya kara magana cikin su, kallon hunch back din ta yayi, abinda yake ji a labarai yau gashi ya gani a bayan Hoorain, tausayi take bashi sosai da wanna abu dake bayan ta, can ya kalle ta yace
"I shall take my leave, take care"
"Toh sai anjima" hoorain replied tana kallon sa har ya fice...
Haka kawai taji ya burge ta, baya ga Mami da Aramani shine mutum na uku da ya zo kusa da ita haka ba tare da kyama ba, komai na shi ya burgeta, musamman tsananin tsafta da iya gayun sa, ajiyar zuciya ta sauke kana ta kalli dakin da Mami take, cikin siririyar Muryar ta, sannan a ladabce tace
"Mami! Bacci kika yi?"
"A'a omami" (a'a diyata) Mami ta fada tana fitowa.
"Ya tafi kenan?"
"Eh Mami, yana da kirki sosai, amma baya son magana" ta fada cikin yanayi mai kama da shagwa6a...
Murmushi Mami tayi ganin Hoorain ta sake sabanin dazu da take zaune shiru, tana son yarta, burinta ta kasance cikin farinciki a kullum, shiyasa a kowacce sallar ta Hoorain take Fara yi wa addu'a.
"Dama kin san shi ne?" Mami ta jefa mata tambayar.
"A'a faa, yana dai cikin soldiers da suka yi mana maganin yan ta'addan nan"
Jinjina kai Mami tayi cikin gamsuwa, lallai wannan yaro da abin mamaki yake, ta san dai dan mai kudi ne, domin yanayin sa ya nuna hakan baro-baro, amma gashi yazo har gidan su wajen Hoorain wanda Bata gama sanin dalilin zuwan sa ba,amma ko ma menene dai zai bayyana, domin yaron ya kwanta mata a rai..
Haka suka cigaba da hirar su gwanin sha'awa.
*BUKAVU BARRACKS KANO*
Zaune commander yake a tsararren office din sa, wayar sa ce ta dauki kara, hannu ya kai ya dauka hadi kara wa a kunne su....
Daga can bangaren field Marshal ke tambayar sa " wai har yanzu Captain Hamdan Maleek Bumsa bai dawo ba, domin na kira wayar sa bata shiga ba".
Nan commander ya sanar da shi cewa "Yes sir! har yanzu dai"
marshal yace "Yakamata ya dawo hakan nan kusan sati kenan, sunyi namijin kokari a aikin da suka gudanar, gashi ya yi shekara biyar a matsayin Captain, matsayi za a kara masa, and we can't do nothing tunda baya nan"
"Haka ne sir! Nima zan gwada kiran layin sa, idan ya shiga zan sanar da shi lalle ya dawo cikin gaggawa" cewar commander, nan suka yi sallama da Marshal.
*********
*Kogi state*
(Kauyen Oguma)
Kwance yake a kasa ba amma duka ba, domin hannu da kafafunsa ba a kasa suke ba, cike da jarumta yake yin kasa da sama, a turanci dai ana kira shi da presa up, ya riga daya saba kullum sai yayi wannan excerise din yake jin dadi...
Cigaba da yayin excerise din yayi, fuskar Hoorain na mai yawo ciki idanun sa, komai na yarinyar na yayi masa, a ganin farko ya kamu da son ta, Abinda turawa ke kira love at first sight .
Yana jin zai iya rayuwa da ita a ko wani yanayi da ko wani hali, ta samu matsayi mai yawa cikin zuciyar sa, baya ga tsananin son da yake mata, yana mata kallon kanwa, wanda bai da shi, hakika ta samu matsayi wanda babu wata mace data taba samun irin shi a zuciyar sa...
Ammi ce ta fado masa, ya san cewa matukar ta samu labarin cewa yayi masoyiya zata yi farin ciki, domin abinda ta dade tana so kenan, ko kusa bai taba kawowa zai fada so mai zafin gaske haka ba, abinda yake ji a kan Hoorain bazai fadu a baki ba. Amma babu wanda zai gane hakan saboda dakiya, jarumta, da zurfin cikin sa...
Ya jima cikin tunanin Hoorain din sa, kana ya mike, ya nufa toilet domin yin wanka, saboda a kage yake da son ganin ta, tun yana mamakin sauyawar halayen sa har ya daina, Hoorain has totally changed him from Captain Hamdan to another new person duk da ba sa wani hira, amma ganin ta kusa da shi na sanya zuciyar sa yin sanyi...
_nayi alkawari gobe
in Sha Allah zan yi update_
Share
Share
Share
Please as much as you canπ
NoorEemaan
07082281566
Thank you for reading hoorain the hunch back girl.ππ₯°
*(Not edited)*
[14/12, 12:54 pm] π½ππππΈπππβ¨: πππππππππππ
HOORAIN MAI KUSUMBI
(The hunch back girl)
πππππππππππ
_written by NoorEemaan_πβοΈ
ELEGANT ONLINE WRITER'S πβοΈ
Chapter 1οΈβ£7οΈβ£β©1οΈβ£8οΈβ£
Daga can bangaren Ammi kuwa a zafafe ta daga wayar domin sauke masu tsananin fushin da take dashi, saboda kullum cikin damuwa take, musamman data daina samun sa k'watak'wata a waya... Sabanin fadan da take da niyyar masa, sai jikin ta yayi laushi sak'amak'on muryar sa da ta ji yayi kasa sosai ya furta
"my first love".
Ajiyar zuciya Ammi ta sauke tana jin fushin da take da shi na raguwa, sosai take son Hamdan, amma ta rasa meka damun sa gaba-daya ya sauya mata, kamar ba zakin sojan ta ba, duk da babu gazawa a muryar sa amma ta66as akwai canje-canje a tare da shi.
"Captain dina, ka Ιauke ni matsayin ammin ka kuma first love dinka kamar yadda kake fada?"
"Of course yes Ammi" ya fada yana mikewa zaune, domin da kamar bacin rai Hadi da damuwa a tattare da Muryar ta.
"Then why kake boye mun damuwar ka, ko ban cancanci sani ba?".
"A'a Ammi, kin fi kowa dacewa ki sani" ya fada cikin wata murya daya kashewa Ammi jiki.
Amma ta daure tace "in hakane then tell me, me kake a kogi bayan ba dangi uwa bare na uba a can, meyasa bazaka dawo ba, na kasa gane maka fa, You re behaving strange these days, ko so kake ka samun damuwa a zuciya, baka bani ciwon kai kana yaro ba sai yanzu daka mallaki hankalin ka Hamdan? answer me am taking to you" wanna karon a dan tsawace tayi maganar domin she can't take it anymore.
A Zuciyar sa yaji wani daci sosai, idanun sa ya runtse da karfi, abu ne wanda kowa na gidan su ya sani, matuΖar Ammi ta kira real name dinsa toh lallai fushi take da shi, boyayyen ajiyar zuciya ya sauke kana cikin Muryar sa da yayi bala'in yin kasa yace "Am sorry Ammi, please karki yi fushi dani, You know I have you first love, bana kaunar ganin fushin ki..."
Numfashi ya dan sauke yana datse jajayen labb'an sa da jerarrun hak'oransa sannan ya cigaba da cewa "as soon as na dawo zan baki labari mai dadi wanda kika jima da muradin jin shi daga bakina"
Sanyin sosai Ammi taji a ranta, fuskar ta dauke da murmushi.
Hamdan ya dan yi gyaran murya yace " pray for me, ki sa ni a addu'ar ki, Allah ya bani ikon yin abinda ke raina, kinji first love?"
"My handsome son, a kullum ina maka, sannan zan dage da tashin dare domin yi maka addu'a, Allah ya tsare mun kai a duk inda kake, ya baka Sa'a, Please do take care of yourself for Ammi ok, i love You"
"I love you too first love" yayi mata reply.
"Yawwa nace yaushe zaka dawo ne?"
Shiru yayi na yan Mintuna sannan yace
"Ammi ban sani ba, but a kodayaushe zaki iya gani na, just pray for your son"
Jikin Ammi ya fara sanyi da lamarin Hamdan. Definitely something is fishy somewhere, amma bata matsa masa ba, addu'a ta k'ara masa, da haka suka yi sallama.
Ya jima zaune idanun sa a lumshe yana tunani.. can hoton fuskar Hoorain ya mamaye idanunsa, ajiyar zuciya ya sauke kamar ita din ya gani a gabansa, tuno halin daya barta a ciki ne yasa shi mikewa, yayi kewar ta ba kaΙan ba, musamman zazzak'ar Muryar ta da murmushin ta dake sanya zuciyar sa yin sanyi, mikewa yayi ya shirya, kana ya nufi cikin kauyen nasu....
*******
Kansa tsaye cikin gidan bakin sa dauke da sallama kasa kasa kamar yadda ya saba, dan tsakar gidan nasu shiru, babu motsin kowa.
Mami data ji Muryar sa kasa_kasa ta fito tana amsa sallamar, cikin girmamawa ya dukar da kansa ya gaishe ta, Mami ta amsa fuskar ta a sake, kana ta warware masa matacciyar tabarman su dake nannad'e sakamakon hakan k'urar jar dake jikin tabarman ya tashi, kawar da kansa gefe yayi, juyowa Mami tayi ta ce "zauna ko, bari na taso Hoorain, tun jiya taki bacci sai dazu na samu baccin ya d'auke ta"
Sabon tausayin ta ne ya kamashi, so yake ya ce wa Mami ta barta tayi bacci amma ya kasa magana saboda miskilancin sa da rashin son maganar sa.
*Hoorain*!
kwance take kan kafita wanda sabagen yanda kafitar ta dade gaba-daya ya cinye, har gwara tudun wani tabarman a kan shi.
Gaban kafitar Mami ta karasa hadi da tattaba Hoorain a hankali, a dan zabure ta farka, ganin Mami yasa ta saki ajiyar zuciya hadi da k'amk'ame hannun ta, cikin kulawa Mami tace
"Hoorain tashi, Hamdan yazo"
Lumshe ido tayi cikin baccin da bai ishe ta ba, amma ta ji sanyi a ranta a dalilin zuwan ya Hamdan dinta.
A hankali ta tashi, bayan ta gyara dankwalin kanta ta nufi waje...ido suka hada tayi masa Murmushi, zura mata ido yayi baya ko kiftawa, wajen da fashashen butar su yake ta nufa, ta zuba ruwa cikin tafin hannun ta ta kuskure bakin ta, sannan ta kara diba ta wanke fuskar ta, tana juyowa suka hada ido, saurin Ιauke kanta tayi ta zo gefen sa ta zauna.
Cikin siririyar Muryar ta daya dan tsarke da bacci ya kuma bada wani amo na musamman tace
"ya Hamdan! Ina kwana"
Lumshe ido yayi, kana ya ware su a kanta, kasa tayi da kanta, a ranta tana mamakin wanna yawan kallo da yake mata a yau, Hamdan kuwa abubuwa da yawa yake ji a kanta wanda baki bazai iya fada ba, sai dai a bar wa zuciya, ga wani mugun kyau da ya ga ta kara masa a yau, musamman manyan idanun ta da suka kara haske tarrr...
Dankwalinta daya dan zame kadan, wanda ya bawa gashin gaban kanta bayyana. Abin kafita ya gani makale a gashin ta, hannu yasa ya cire hadi da nuna mata sannan ya jefar, kunya taji ya kamata.
Haka suka yi zaman kurame a wajen, daman yawanci ita ke magana, amma damuwa dake manne a ranta yasa ta kasa magana a Yau din.
Bayan azahar sai ga Aramani yazo, Hoorain ta ji dadin ganinsa, tana son Aramani domin Allah, tana jin shi kamar wan ta.
Hira ya dinga janta da shi, abin ka da mai barkwanci nan da nan Hoorain ta Ιan saki jiki tana murmushi.
Hamdan yaji dadi ganin babe dinsa ta fara walwala sak'amak'on labaran barkwanci da Aramani ke bata, although Yana Jin kishin Aramani a ransa duk da yasan babu komai a tsakanin su, amma tsananin son da yake mata yasa baya kaunar ko wani da namiji ya rabe ta, amma bashi da zabi da ya wuce ta kasance cikin farinciki.
Sai bayan la'asar aramani ya tafi, duk da ba a samu cikon na bakwai ba, domin babu wanda ya yarda zai kara bin su, saboda tsananin hadarin duniyar mutuwa.
Sai bayan magriba Hamdan ya yafi cike da kewar Hoorain.
haka ma ta bangaren Hoorain sam bata ji dadin tafiyar sa ba, ga damuwar da take ciki ya dawo sabo saboda gobe ne su Aramani zasu tafi, a ranar bacci ya kauracewa idanun ta, kuka mara sauti ta dinga yi...
WASHEGARI
*5:55am*
Zaune yake kan sallayar dakin da yake kwana, ya gama addu'o'in sa da azkhar. Yayi shiru tunani mabambamta na zagaye brain din sa wanda yasa jijiyoyin kansa suka fito, wayar sa ya janyo ya rubuta wa Ammi text kamar haka...
_saba'ul khair ya Ammi, ki min addu'a kinji yau ne zamu_........
sai kuma ya kasa karasa wa ya tura mata. Dalili kuwa shine bayason ta shiga damuwa, infact ya yi imanin cewa idan tasan inda zai je bazata taba amincewa.
Kara rubuta mata yayi
_i love You so much Ammi, you re the sweetest mum ever, ki yafe min if I have ever offended you in any way_
Ganin massage din ya shiga, sai ya kashe wayar da sauran 2percent ya jefa cikin jakar sa irin ta sojoji da ya so da ita, toilet ya shiga yayi wanka hadi da brush wanda ya dauk'esa Mintuna ashirin sannan ya fito, goge jikin sa yayi da mini towel, ya shafa mai hadi da fesa body spray, wasu bakakken kaya riga da wando body hug na kamfanin DOLCE AND GABBANA (D&G) ya sanya, hair cream dinsa na kamfanin XPEL ya shafa bayan ya cire dan rubber band din, ya jefar, tajewa yayi, sannan ya kara kamawa da sabon rubber banda kamar yadda ya saba a kasan keyar sa, jelar har wuyan sa.
Wani turare mai sanyin k'amshin na kamfanin Christian Dior ya fesa sama-sama, sannan ya rufe gidan ya fito...cikin tafiyar sa ta sojojin masu ji da jarumta hadi da cikakken lafiya ya fara lafiya.
Kusan a tare shi da dan baiwa suka zo kofar gidan su Hoorain, ko kallon sa bai yi ba.
Gidan ya shiga bakin sa dauke da sallama, Mami da Hoorain ya gani zaune sunyi jugum abin tausayi, gaishe da Mami yayi, ta amsa cikin muryar damuwa, Hoorain da idanunta suka kumbura alamun ta sha kuka ta kallesa ba tare da ta samu karfin gaishe sa ba, saboda mutuwa da jikin ta yayi kamar wacce aka wa duka.
Jin hayaniyar mutane ya sa suka fahimci cewa dan baiwa yazo, a sanyayye suka fita, Hamdan dake tsaye shima ya bi bayansu, ganin damuwa mai tarin yawa a fuskar abin kaunar sa (Hoorain) ya sanya yaji wani iri ba dadi a ransa...
Suna fitowa Hoorain ta ga su Aramani, wani sabon kuka ya kufce mata, wajen shi ta nufa ta rike hannunsa gam, cikin shesheka tace "Aramani karku je, banason rasa ku, nace Muku zan rayu a haka, a hakan ma na yaba da tarin kaunar da kuka nuna a kaina. Mami! ya Hamdan! ku musu magana dan Allah" ta karasa wani uban kuka ya kara kufce mata.
Murmushi Aramani da sauran mazaje biyar din suka yi, sannan suka ce "Hoorain muna kaunar ki domin Allah, ki mana addu'a kawai, idan Allah yayi bazamu dawo ba ki dinga samu cikin addu'o'in ki kinji"
Kara raunata zuciyar ta yayi, ta dinga kuka kamar ranta zai fita, kukan da sautin sa ke fita da zallan damuwa hadi da tsoro.
Maganar dan baiwa ne ya dawo da hankali mutanen kan sa yace "Alhamdulillah! Allah yasa an samu mutane shida, sai dai babu cikon na bakwai, shin akwai wanda zai zaba cikon dan bakwai, domin taimakawa rayuwar Hoorain?"
Ya fada yana raba idanunsa kan jama'ar wurin. waje ya dauki shiru, wasu har boye fuskar su suke kamar irin za a musu dolen nan.
Hamdan da tun ranar da dan baiwa yayi wannan Maganar ya riga ya sa a ransa cewa koda babu wanda ya yarda zai je, shi din zai je domin dauko wa Hoorain magani.
Cikin tafiyar sa ta burgewa ya karasa wa wajen da su Aramani ke tsaye alamun shi din ne cikon na bakwai su, ba tare da yace komai ba.
"Alhamdulillah! Komai yayi daidai"
dan baiwa ya fada yana kallon Hamdan da fuskar nan ke daure tamau kamar ko yaushe.
Sosai sauran jama'ar wurin suka cika da mamaki, ganin bare wanda ba dan kauyen ba zai je, duk da basu san Meye alakar shi da Hoorain ba, amma sun yi mamaki ainun, domin abu ne wanda babu wanda ya ta6a kawowa ko kusa zai aikata.
Mami ma ta cika da zallan mamaki, ta bangaren Hoorain kuwa sabon shock ne ya shige ta, baki ta bude, ta kafe Hamdan da ido hawaye