Showing 3001 words to 6000 words out of 136985 words

Chapter 2 - DIJE ƘARANGIYA

09 Apr 2026

1069

yana matsowa kusa da ita ta yi wata zabura ba mutanen da ke wurin suna kallo ba har shi kanshi Liman sai da yaji tsoro, hannunshi yana rawa ya d'ora hannunshi akan goshin Dije ya fara tofa mata addu'a, Aiko Dije ta kurma kuwwa ta fara surutai tana cewa

"Ba zamu fita ba kama daina addu'ar nan ko'ina ba zamu je ba muna nan har sai Maigari ya janye kudurinshi na son d'aukar hukunci akan god'iyarmu, akanta zamu tada garin nan akanta zamu mayar da garin nan toka"

Liman dai sai zuba addu'a yake yi sai cen Dije tace

"Ayi hak'uri zamu yi magana za muyi magana nace"

Maigarin ya yi Liman alamu da Ido akan ya dakata aiko Dije ta fara fad'in

"Mune muka zama kura mune muka fito a siffar kura muka biyosu, kuma a gaban idonta muka kashe mutum biyar a farkon gari amman ba mutanenku bane mutanenmu ne, tunda ta take muna 'ya'ya muka biyosu ita da kawayenta, don yanzu haka abokan fadan nawa ya jiman raunuka saboda fad'an da muka yi da junanmu Ni da yan uwana aljanu don haka Bari in fito a siffata ku gani nasan zaku tausaya man"

Kowa na wajen yace

"A'a kar ka fito"

Wasu suka ce "ALLAH ya baka lafiya ka ja Yan uwanka ku tafi kawai mun yafe mata"

Dije ta sake cewa

"Idan na tafi kuka daketa fa ko kuka d'auki wani mataki kanta fa zan gayyato Yan uwana mu sake zama kuraye mu zo garin nan sai mun kashe kowa don kowa ma ba zai tsira ba"

Aiko cikinsu ya duri ruwa Maigari yace,

"Ba za'a tab'ata ba amman don ALLAH in kuna wa ALLAH ku yi nesa da garin nan, Kuma ku yi alk'awali akan ba zaku sake shiga shirginmu ba"

Dije tace "zamu tafi amman har sai mun mayarwa da sarkin fadawa kanshi da muka tsige"

Bafaden ya shafo kanshi da yasha mola sol! sol! yace, "Ranka ya dad'e ai ya koma da kanshi ma gashi a saman wuyan ina jinshi"

DIJE ta mike tsaye cikin zabura ta katsa masa wata uwar harara da idanuwanta da suka jajawur! Tace

"Wa ya Gaya maka kanka ne a sama to bari ka ji ku kuke ganinshi kamar Kai irin naku to wannan Yar karamar dabbarmu ce dake bacci a saman kanka, naka kan yana cen bangon duniya bakin kogin zumburbur an fara had'a kayan dafuwarshi da ka yi sake nan da safiya zaka rasa ranka da an jefashi cikin tunkunyar dafuwar"

Bafaden ya zabura dafe kan yace

"A cire man dabbar a maidoman kaina don ALLAH ka taimakeni"

Dije ta kyalkyale da wata mahaukaciyar dariya sannan ta yi shiru tana tare da Kara kunnenta a iska kamar mai sauraren wani abu sai cen tace,. "Ranka ya dad'e Sarki gani nan zuwa yanzu a yi man afuwa yanzu zan kawo maka"

Tana k'are surutan tace, "Babana Sarkin aljanu yace da Ni in tattaroku yanzun nan dukanku mu had'u a bakin Ruwa ayi shari'ar a cen"

Kowa ya gwalalo Ido waje Aiko cikin sauri ta fara fad'in

"Ya zajisu ya zurmukus banbaradusa ya zamburkusadduna ya......."

Kafin kace me duk wuri ya hautsine da k'ura saboda dan neman gudun famfalakin da mutane suke yi, Bafade dafe da kanshi yana gudu yana fad'in

"Ki tashi daga baccin nan don girman ALLAH ki dauko mani kaina, tun kafin a fara dafuwarshi a bangon duniya"

Ganin mutane da yawa sun watse sai Yan gani kasheni ciki kuwa har da Maigari da Liman sannan da Baffanta da ke nesa da su yana haki, ta k'ara keta kuwwa tace

"Ku saurareni zamu tafi amman ko harara aka yiwa god'iyarmu Dije sai mun dawo tare da gayyar rundunar Yan uwana aljanu, mun tafi Sarkin fadawa ga kanka Nan gobe ka k'ara dan gidan marasa tausayi amman ka sani za mu zo mu tafi da kai da ka kuskura ka fito fitsarin dare, mun tafi zo muje ke kuma sarkin bacci"

Sai kawai aka ga Dije ta fad'i yaraf tana fisge fisge tana wani Abu da kai ta gwalo Ido sai cen ta yi luf kamar Mai bacci.

Liman ya sake tofa mata addu'ar ya fara Kiran sunanta, Dije ta yi wukil da Ido d'aya suna had'a Ido da Liman ta zabura ta mike zaune tace

"Don Allah ka yi hak'uri WALLAHI da gaske naga Kura Ni da su Ladiyo, a tambayesu aji ai ko su zasu fadi gaskiya don ba Ni kad'ai na ganta ba har dasu, a gaban idona taci mutum biyar a farkon gari"

Maigarin yayi shiru yana nazari sannan yace,. "Ai kinci sa'a komi ya wuce tunda an wankeki tashi kije gida amman kar ki sake zuwa daji debo ciyawa"

Dije ta zaro Ido tace

"Na shiga Uku ita akuyar tawa me zata ci idan na daina fita daji?"

Maigarin ya yi Yar dariya yace

"Ni Zan sa akawo maki Ciyawar kullum ki dinga bata saboda baki da isashiyar lafiya tashi kije gida ki kwanta ki huta ALLAH ya baki lafiya"

Dije ta washe baki tace,. " Harda dussa?"

Yace "har da ita tafi gidan kawai"

Dije ta Mik'e tana tsallen jin dad'i tace

"Na gode Maigari ALLAH ya ja da nisan bacci kuma ya baka lafiya ya tsare gaba kuma yasa kar ka mance watarana kaki aikowa"

Maigari sai Ameeen yake fad'i don a matse yake da ta bar wurin tun kafin shima yayi sanadin abunda zai janyo ta k'ara kassarashi.

Dije ta nufi wajen Baffahnta tana dariya tace, "Na huta da zuwa Daji akuyata zata sami ciyawa kullum"

Baffah ya fisgo hannunta suka nufi gida, Mutane da sun hangota su yi ta darewa suna gudu Dije kam sai tsallen cin nasara take yi, Liman kam binta yayi da kallo yayi dariya don shi tsaf ya gano ba wani aljani da ke kanta tsabar iya shege ne ke damunta, amman ko ba komi ya jinjina mata tunda har ta samowa kanta hanyar kwatar kai, daga wannan gangamin jidalin data hadowa mutane a cikin gari.




Akafta😅






D/AUTA CE✍🏻

*💣DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*





*WAI! WAI! WAI RIGIJI GABJI WANI KAYA SAI AMALI LALLE DIJE K'ARANGIYA TAYI FARIN JINI BA KAD'AN BA INA GODIYA SOSAI MASOYA BOOK D'IN ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU A DUK INDA KUKE👍🏻*



*Lamba ta 4*



Ko da suka je gida suka taradda Inna tana tankaden garin masara tana yi tana sharar hawaye, Dije da gudu ta isa wurinta ta fad'a jikinta har sai da tiren garin yayi tsalle rabi ya zube rabi ciki, Inna ta saka hannu ta Kai mata wani mugun dunku a baya har sai da ta gantsara, a zabure Dije ta mike tana sosa wajen tana zunburo Baki alamar taji haushin dukan, Inna ta nunata da dan yatsa tace

"WALLAHI ki fita idona in rufe Dije na fara gajiya da rashin hankalinki, ke kenan kullum janyowa kanki abunda za'a saka ki a bakin duniya muma ki ja muna zagi a gari, to bari kiji WALLAHI kwanan nan zan sa Delu ta tafi dake birni kamar yanda kullum take rokata akan in bata ke ta kaiki aikatau, kije cen ki had'u da masu horaki da kyau tunda Ni kin renani"

Dije ta fara dire diren kafa tana kuka tana fadin, "ai WALLAHI Inna ko an kaini sai na dawo don ban zuwa birni a yanke mani Kai, Ni dai kiyi hak'uri don ALLAH na yi maki rantsuwa idan na sake ki dakeni"

Inna ta yi banza da ita ta makure jikin gina tana zunburar Baki tana mui mui da Baki tana sharar hawaye, sai ga Baffah ya fito bayi yana fad'in

"Wai ke Hasiya me yasa kullum kike tsangwamar yarinyar nan, to WALLAHI ahir dinki wannan karon don kuwa Dije dan sarkin aljanu ne a saman kanta, yanzu haka shi ya zo ya hana a d'auki mataki kanta Kan abunda ta aikata, kuma yayi gargadin ko harara wani yayi mata za su dawo su sake hargitsa garin nan, idan ke kinga ke zaki iya taron aradu da ka to karki fasa"

Ya kalli Dije yace

"Tafi ki dibi ruwa ki yi wanka ko da zakiji dad'in jikinki akan wannan sukuwar hawan dokin da aljanu suka yi akanki"

INNA Hasiya ta rik'e baki tace, "yanzu Kai Malam har ka yarda da shirmen Dije? Lalle kam, to Ni dai ina baka shawara WALLAHI ka daina goya mata baya tana k'ara zama girtsatstsa, don wannan shirmen nata ba zai hanani jibgarta ba idan tayi laifi ko da ko tsamiya ce akanta Ni babu ruwana"

Baffah zai shiga dakinshi ya waigo yace, "Kurar da kike tsoron zuwanta garin nan to ko nan gidan ma zata dira idan ta zo wannan karon, sai ki je kiyi gaggawar yin rame a karkashin gadonki kinga idan ta zo sai ki shige kawai, don kuwa ba fashi zaki janyo fushin Dan Sarkin aljanu"

Yana K'are maganar ya shige d'aki abunshi domin a matse yake da yada hakarkarinshi ya huta ya samu natsuwarshi ta dawo.

Dije ta dibi ruwa cike fam da farin bokin fenti ta kinkimeshi tana nishi ta yi bayi tana ta gunguni, don taci alwashin sai ta debe haushinta da ruwan gidan don kuwa sai ta yi wacakarta son ranta dasu tunda Innar ta yi mata fad'a.

Gashi sai sun zagaya bayan gidan suka debo ruwan ga wata rijiyar k'ofar gidansu Ladiyo kawarta, ta yi wankanta mai cike da barna sannan ta fito tana rawar sanyi daga ita sai siket a k'irji tana tsallen sanyi, Inna ta kalleta tace

"In dai takamarki mugunta kanki zaki yiwa in mura ta kamaki sai ki bidi mai ce maki sannu, sannan ruwa ma idan sun k'are ai kece zaki debosu don kinfi kowa sanin halin yayanki"

Dije ta zunburo Baki tace,. "WALLAHI Inna kar ki janyo fushin murkustus barakus bn muruddika, yanzu ya sanar dani in fad'a maki suna jin nauyinki don ke kika haifeni sunce in sanar dake daga yau kar ki koma yiman fad'a, da kyar na basu hakuri suka ce sun yafe amman kar a k'ara "

INNA ta rik'e baki tace

"Au abun har ya kai cen? To ki fad'a masu ba k'ari ba har da k'are k'are sai na yi idan sun tashi su yi kuli kulin kubura dani"

Kafin Dije ta yi magana sai ga Usmanu ya shigo Dije tana ganinshi ta yi sum sum ta sassada ta shige dakin Inna kudum, Usmanu ya bita da harara yace

"Wai Inna yaushe yarinyar zata yi hankali ne? Yanzu abunda ta janyo kenan a garin nan? WALLAHI taci sa'a bani nan da sai na kakkaryata bak'ar jidalalla, sannan wannan siket d'in da na hanata sakawa ta fito tsakar gida dashi hakanan shi kad'ai bata bari, to duk abunda na yi wa yarinyar cen Inna kar ki ga laifina tunda ta nuna cewa ban isa ba, to Ni sai na nuna mata na fita kangarewa"

INNA tace "Halin Dije sai ita abita da addu'a kawai ko za'a ci nasarar abun, amman duka yau aka Saba?"

Baffah ya fito yana saka talkaminshi yace

"Ka dai yi a hankali in har ba so kake yi garin nan ya dawo toka ba, don kuwa Dije ba ita kad'ai bace idan ka janyo aka maidaka dan duk'usurun bak'in jakki ko bunsuru shikenan Kai ka janyowa kanka"

Ya fice abinshi Usmanu yaso yayi dariya ya mazge ya nufi randar ruwa Yana lek'awa ya hango ba komi duka tukanen duk ta kwashe ta yi wanka, aiko ya fara kwalla mata kira sai gata da kwandon kayan kwalliyarta tana shafa jar hodarta, cike da bacin ran da ke kwance akan fuskarshi yace

"Uban mi kike cikin Gidan da ba zaki je ki debo ruwa ba?"

Dije ta zunburo Baki tace,. "Yanzu na fito wanka fa Yaya sannan ace inje in debo ruwa? lalle ma!"

Usmanu yayo kanta zai daketa ta yi bayan Inna ta b'oye, cikin gargadi yace da ita WALLAHI muddin bata debo ruwan nan ba sai jikinta ya gaya mata yau.

A gurguje ta gama dige digen bak'in kwallinta ta danbara janbakinta ja fam da Baki sannan ta fisgi bokitin karfensu ta fita tana gunguni.

Ko da taje rijiyar makil take da mutane wad'anda wasu da yawa duka tsararta ne, tun daga nesa suna hangota wata ta yafito wata da ke kusa da ita tace

"Ga fa K'arangiya Nan Wai ashe aljanu ne da ita shiyasa ma masifarta kullum take gaba gaba"

Kafin Yar uwar ta bada amsa Dije ta k'araso ta ajiye bokitinta ta rik'e kugu, Kai tsaye ta matsa jikin rijiyar ta ce da wata mai suna Bintalo ta bata guga ta cika bokitinta, Bintalo ta yi mata kallon banza tace

"Kina so ki cika da wuri me ya hana ki zo da taki gugar?"

Dije tace,. "Taki nike ra'ayin dibar ruwan da ita zaki bani ko sai na janyo maki asara?"

Bintalo ta dafe gugarta da k'afa ta rik'e kugu tace,. "Me zaki iya yi ko an Gaya maki Ni ina tsoronki ne kamar kowa? To WALLAHI kika kawon wasa sai na maki danbanzan duka a wurinn...."

Kafin ta Kai k'arshe sai ko taji saukar mari akan fuskarta, Bintalo ta zabura zata rama gugarta ta sub'uce ta fad'a rijiyar, cike da takaici taci kwalar Dije ta shaketa saboda tafi Dije girma nesa, kafin kace me idon DIJE sun yi ja cikin tsananin fushi tace

"Sakeni Bintalo"

Bintalo ta zakalkalo tace,. "Anki a sakeki ba za'a sake kin ba kiyi abunda zaki iya"

Dije tace "nace ki sakeni Bintalo"

Bintalo ta k'ara shaketa cikin masifa tace, "Sai kin fiddo man gugata da kika sa ta fad'a ko ina sakinki, WALLAHI yau sai na ga k'arshen rashin kunyarki ba aljanu ba ko iccen kuka ne akanki sai na ci Ubanki..... "

Karaf! Sai jin k'arar saukar bokitin k'arfe aka yi a goshin Bintalo Dije ta kwad'a mata kasan bokitin, Aiko Bintalo ta fasa k'ara kafin kace me jini ya fara wanke mata fuska.





😳na yi nan🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️wlh Babu ruwana kar ace Ina nan aka yi 🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️



Akafta🤣🙌🏻






D/AUTA ce✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*




*COMMENTERS INA MAKU JINJINAR BAN GIRMA🤣👍🏻*




*Lamba ta 5*




Bintalo tana shafo goshinta ta ga jini ta fad'i k'asa tana kururuwa, gaba d'aya mutanen da ke wurin hankali a tashe suka fara salati, a cikin matasan 'yanmatan da ke wurin wata ta zo da gudu ta cire dankwalin Bintalon ta d'aure mata goshin jabau! Bintalo Kam sai ihu take wasu suka rikata zuwa gidansu.

DIJE kam ganin an bar gugunan d'ibar ruwa an nufi wajen Bintalo ana sallallami yasa ta cika bokitinta dam! Ta d'ora akai har ta fara tafiya, hankalin mutanen da ke wajen ya dawo kanta aiko wasu da yawa suka fara jifarta da miyagun kalamai suna aibatata, ita kam ko juyowa bata yi ba ta ci gaba da tafiyarta don ita kanta ganin jinin da ke fita a goshin Bintalon ya tsoratata, sai dai ta mazge kawai don kada a gano taji tsoro ace za'a ci zarafinta a banza.

Ko da ta shigo gidan da sanyin jiki ta juye ruwan ta ajiye bokitin zata shige d'aki, Inna Hasiya ta bita da kallo tace

"Ke lafiyarki na ganki wata sukuku haka? Ko karyar ciyon ne ya tashi don ba kyason komawa debo ruwan?"

Dije ta zumburo Baki tace,. "Ba Bintalo ba ce ta jani muka yi fad'a, kuma WALLAHI sai da nace ta kyaleni ta kyaleni taki to ai gashi nan yanzu ta janyo goshinta ya fashe jini sai tsiyaya yake yi"

INNA ta zaro Ido waje dafe da kirji tace,. "Goshinta ya fashe ko dai kin fasa mata? Na shiga Ukuna Ni Hasiya wai Dije kasheni kike so kiyi ne? kulluma da sabuwar masifar da zaki jajibo muna kisa mutane su yi ta ganin kamar bama tsawatar maki, to bari kiji WALLAHI Wannan karon sai dai in kasheki za'ayi a kasheki amman Ni Kam ba hannuna ba k'afata tunda ke kunnuwan Kashi ne da ke"

Tana k'are maganar cikin k'unar Rai tayi madafi inda taci gaba da tuka tuwon masararta, tana yi tana fad'a Dije ta shige d'aki sum sum tana matsar kwallah.

Aiko minti biyar a tsakani sai ga tashin muryar Iya Mero Uwar Bintalo, tun daga farkon shigowa Gidan take zazzaga ruwan bala'i har ta shigo Gidan rik'e da hannun Bintalo tare da wasu Yan bani na'iya masu zuwa ganin k'wam.

Iya Mero tana shigowa ta fara fad'in,

"Ina Hasiya fito kiga abunda tsinanniyar 'yarki ta yiwa Bintalo, WALLAHI Ni Kam bazan tab'a lamunta da rashin mutuncin da take yiwa mutane ba, don in kowa ya kyaleta Ni bazan kyaleta ba Dole ne sai na ramawa Bintalo itama in fasa mata goshin ta ji inda dad'i"

INNA ta fito daga madafi tana sharce majina saboda hayakin da ya turnuke d'akin madafin yasa idonta sunyi jawur, ta goge fuskarta da gefen zanenta ta k'araso wajen tace

"Don ALLAH Mero kiyi hakuri WALLAHI d'a ne ka haifeshi baka haifi halinshi ba, don da ta Ni Dije take bi to ko hannu aka saka mata a baki bazata ciza ba"

Ta nufo wurin Bintalo ta rik'ota da nufin taga yanayin raunin, aiko Iya Mero ta tureta da k'arfi ta shiga gaban Bintalo tare da cire mayafinta ta sha d'amara a masifance tace

"Ba wani dad'in bakinki da zai yi tasiri a wurina don yau dole ne sai na ramawa Bintalo abunda 'yarki ta yi mata don d'a baifi d'a ba da zaki wani kalallameni da dad'in baki to bazan hak'ura din ba sai na rama mata"

INNA cikin b'acin Rai ta shiga d'aki ta janyo Dije da ke makure Kan gadon bonon Innar suka fito d'akin, Inna janye da ita har sai da ta Kai Dije gaban Iya Meron ta saketa, sannan ta d'auko bokitin karfen ta ajiye gabanta tace,

"Ga ki gata nan Mero don ALLAH ki kasheta kar ki barta da ranta"

Cikin borin kunya Mero ta d'aga hannu ta zabgawa Dije wani Uban mari har sai da ta hantsila, aiko dukawar da Dije zata yi bata taso ba sai da kafafuwan Iya Mero sai gata ko tim! A k'asa tana salati zane ya wancakale gefe, sai fad'in take yi

"Ku ke ganinmu ba mu muke ganinKu ba...."

DIJE sai harararta take tana wani ciccika tana kumbura saboda tsananin b'acin Rai.

Yara kam da ke tsaye suna kallo sai ihu suke yi suna dariyar wallen da Iya Mero ta yi, aiko suka fara fad'in

" Ku zo ku ga Dije ta yasar da Innar Bintalo k'asa"

Bintalo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login